a: MAGAJIN IZZAH!!! {CIGABA KWARKWARAH} *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ Tukwaicin gare ku! Mommyna (Aunty Zeey) Hajiya Maryam (Jikar kulu) Aunty Sa'a (Kawar Mommyna) Ummu Adam (Mama me Voice) Maman Abuna (Mamana) Maman Amatullah (Kishiyar Muwaddah) Aunty Aisha Abuja (Aunty na😍😘♥️) Tare da fatan Alkhairi a gareku. _Idan mai karatu bai manta ba! Mun tsaya inda aka sace Yarima Jalal! Kuma magajin masarautar Daura_ بسم الله الر حين الرحيم Sokoto birnin Shehu Usmanu danfodiyo! Cibiyar musulinci na arewacin kasar Nigeriya! Masarautar Sokoto 2019 Ɗaya "Kinga Hanisah! Wallahi bazan iya ba, shima mutuwa zai yi. Kawai zan guduwa wannan kaddararren auren ne! Ba zan iya auren Ikrama ba!" Zaro idanu Hanisah tayi, cikin kaduwa tace. "Amma baki tunanin yadda, Babi zai ji? Ace kin tserewa aurenki." Tsaki naja tare da juya mata, baya na turawa Ansah sakon. _Kai banza na shirya! Ina jiran ka!_ Kwace wayar tayi, cikin damuwa tace. "Wani irin Kuskuren kike aikatawa ne? Wani irin cutarwa kike shirin aikatawa ne! Saura mintinan arba'in da biyar a daura miki aure." .kallonta nayi sanin zata iya b'ata min shirina, nace mata. "Toh shikenan! Na hakura yayi miki!" Yadda nayi maganar, sai da na bata tausayi, rike hannuna tayi sannan tace. "Addah Aanih kiyi hakuri! Idan kika yi wani abu yan uwan Babu zasu iya juya mishi baya! Kuma wannan auren wata dama ce da kika samu, dan mahaifin yaron gwamnar jahar nan ne, don Allah karki zubdawa Iyayenmu kumar su." Murmushi tayi sannan tace. "Babu komai! Na fasa!" Ina gaya mata, amma kudirina yana raina. Fita tayi tace min tana zuwa, na rufe kofar dakin, shiru nayi ina nazarin abinda yake shirin faruwa, nan da minti talatin da wani abu, sakone ya shigo min. Na duba naga yace min. _Kin shirya?!"_ Da sauri na tura mishi da _Na shirya_ Shiru nayi ina tausayawa Baabi! Buga min kofar dakina aka yi, nazo zan bude nace. "Waye?!" "Me gyaran banɗaki ne ba ance pampo ya b'aci ba?!" Shiru nayi domin ban san waye ya turo shi ba, kawai nayi kumdubalar bud'e mishi, fuskar shi rufe makari, kallon juna muka yi naga kamar kasan ƙwayar idanun shi. Matsa mishi nayi ya shiga cikin dakin, yana tambayana. "Ranki shi dad'e, ina ban dakin yaƙe!" Shiru nayi sannan na nuna mishi wani kofar dake kallon gadona, shiga yayi can yace. "Ranki shi dad'e! Nace ba!" Cikin gundura da halin shi nace mishi. "Meye ne?!" "Don Allah ki shigo ki kwashe wannan abubuwan ki!" Sai kuma naji kunya ta kama ni, mace an santa da boye kome nata, bawai tallatar dashi ba, kawai ina shiga, na juya tare da kwashe wanduna. Kafin na kai da kwashewa sai ji nayi ya saka min abu akan fuskana, komawa jikin shi nayi ta baya na mike! Murmushi yayi yace. "Hmm! Da wuri haka!" A ban dakin ya kwantar da ita, ya cire abin kunenta da abin wuyar, sanan ya daukota zuwa dakin ya zage buhun shi ya nad'eta a cikin babban bargo, sannan ya dakata a cikin buhun, me L, ya sab'ata a kafad'arshi. Ya fito daga dakin babu wanda ya damu da shi, dan an san yace zai shiga gyara pampon dakin ta. Koda ya fito dauke da ita a kafad'arshi, yana fitowa harabar gidan, ya isa gurin motar shi, Bugatti, ya bude sannan ya juya yana kallon dandanzon mutanen da suke shigowa gidan. Daga nesa, sarki Jaamal na daura, yake kallon shi dai-dai lokacin da yaja abin kariyar da ya saka a fuskar shi, sannan ya rufe bayan motar ya shiga motar cikin isa da kasaita. Yadda yake tafiya yana juyawa zaka rantse a gidan iyayen iyayen shi yake. Yana shiga motar, ya bata wuta. Sai da ya finciketa, da sauri mutane suke bashi hanya, har zuwa lokacin idanun sarki Jamal yana kan shi, koda yazo zai bar gidan, sai da ya kuma kallon fuskar shi. Amma ya rufe gilashin motar da sauri sabida akwai ledar kariya wacce take sanya cikin motar baki. Da gudu ya cilla motar kan titi da masifar gudu, kamar zai tashi sama. ..... A cikin gidan kuwa babu wanda ya kuma bin takaina, sabida basu kawo a ransu za a sace ni ba, sai Hanisah da take kokwanto, kawai tazo da sauri akan zata duba abu a kayana, kawai tana shigowa, taga turus babu ni, wani irin tsoro ne ya shige ta. Ta juya dakin Mamanta da gudu, tace. "Ammih! Don Allah zo" "Kinga Nisah barni ina zuwa!" Ganin taki bata fuskata juya gurin Amaryan Baban su, Ummih Rahil, tana shiga taga nsn ma da mutane. Riko hannun ta tayi suka bar falon, d'akina suka nufa ta gaya mata kome! Wani irin dauke wuta Rahil tayi jikinta na rawa, ta kalli agogon dakin, saura minti goma daurin auren. Da sauri ta fito kafarta babu takalmi, ta nufi inda shashin mai martaba sarki Aryan yake, inda yake dauke da mutane, tana shiga ta janyo hannun shi suka fita daga gidan. Har can lambu, suka nufa. Tare da fashewa da kuka, tana gaya mishi Aanih Fatimah Khatoon ta gudu! A tsorace ya ke kallonta, sanya hannunta tayi akan fuskar shi. Tana girgiza kai tace. "Allah ya albarkace ka da yara mata biyu! Zaka iya amfani da wannan damar, karka damu, ita kuma Aanih a bazama nimanta, dan bata yi nisa ba. Kuma nafi zargin sace ta akayi dan wallahi bazata aikata hakan ba!" .wani irin yanayi ya shiga Dakyar yake d'aga kafar shi, har ya isa kofar babban masallacin da za a daura auren, ya dauki amsa kuwa. Ajiyewa yayi sannan ya riko hannun Mai girma Gwamnan Sokoto, suka fita ya fara mishi bayani, amma fir yaki amincewa karshe ya tilasta Aaryan ya fadawa kowa abinda ya faru, jikin shi a mace! Ya tako har gaban masallacin yace kuma ɗaukar amsa kuwar. Ya fara bayani kamar haka. "Assalamu alaikum warahmatullah! Ina me baku hakuri da abinda zan gaya muku! Tare da bawa Mai girma Gwamna Ziyad Almustapha hakurin abinda ya faru!" Sunkuyar da kanshi yayi, tsabar tashin hankali, muryan shi na rawa ya kuma buɗe baki zai magana. Sarki Jaamal yace. "An mai da Auren Gimbiya Fatimah kan Gimbiya Hanisah, abisa wata lalurar da ta taso, sannan kuma ina mai bawa Mai girma Gwamnan Jahar sokoto hakuri ya amshi wannan tayin da kima. ..... A dukkan sarakuna ne! Babu wanda zai so yaga kan shi a irin halin da Sarkin Yake ciki, idan bazan manta ba yau shekaru ashirin kenan! Da rasa Yarona Yarima Jalal, kuma nasan irin zafin da ake ji, don Allah kar mu kuma kara mishi zafin da yake ji." Aikuwa Ikrama yayi tsagal yace.."Kawu nifa ina son Aanih dan haka zan iya jiran har ta dawo, kawai Baba ka sanya a baza jami'an tsaron, dan wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba sai Ita." Daurin auren da ba ayi ba kenan, aka kuma baza jami'an tsaron, suka shiga nimanta. ---- Irin gudun da yake yi, zaka zata dan yana da wata abu me muhimmanci ne, sai dai kawai yau burin shi ya, isa Sahara. Ya ci mutuncin Yarinyar da ta keta mishi haddi a cikin dubanin jama'a, ta Mishi abinda ba a tab'a mishi ba. A cikin dandazon dalibai na jami'ar Calgary University Canada, ta lalata mishi farin cikin shi. Ta sanya shi fita cikin makarantar kan shi a sunkuye! ... Ta zubda mishi da duk wata ji kimar shi, na rayuwar da yake jin kan shi,. Shi din kamar sarki ne a cikin makarantar ko fada ake da zaran an gan shi toh an daina, amma sai da yarinya b'arar mishi da Izzar shi, bai tab'a jin tsanar kanshi ba, sai a wannan lokacin, inda ya ajiye muguwar tarihi ba. Dan haka dole yau ya rama abinda tayi mishi, buga kan motar yayi, tare da cizon lebben shi na kasa, sannan ya kuma bawa motar wuta, kamar walkiya haka yake tafiya, har ya isa bakin bodar najeriya da Nijar, wanda yake elaile. Suka gama duba kome, bayan motar ce basu duba ba, sannan suka bude mishi kofar fita ya cilla kan motar a guje. ..... Doguwar tafiya yayi kafin ya samu bakin iyakar Nijar din, sannan ya mika musu shedar, shi dan kasa ne, ganin takardan shi, yasa suka barshi ya wuce. Idan ya tuna abinda ya faru sake dukar motar yake, sai da yayi dogowar tafiya har dare yayi suna hanya, kafin ya sauka a gefen hanya, ya tsaya idanun shi jajjur, ya fito daga motar da abin sallar da kuma, ruwa, yana fitowa abinda ya fara shine buɗe bayan motar ya fidda ita, ya wurga ta kasa sannan ya zazzage ta kamar wata mara daraja. Yaje ya buɗe ka motar ya dauko ruwa cikin galan yazo ya bude bakin ya juye mata akanta, tsaf sannan ya d'agota yana kallon yadda take layyi cikin mayye, da marisa. Ya kifa mata Mari sai da ta nemi tambelan da take, ta bude idanun ta. Tar akan shi. Yana tuna yadda ta keta cikin dinbun Jama'a ta iso dandamalin ta kifa mishi maruka har biyu, tare da tofa mishi yawu, wani irin rintsa idanun yayi cikin baƙin ciki ya kuma tsinka mata mari, yana huci. Alola yayi tare da gabatar da sallar da ake bin shi, ina zaune kamar wata gumki, rarrafewa nayi na dauki butar na fara gabatar da alola tare da niman abinda zan kare jikina, can na hango bargona na dauka na lullube kaina, na gabatar da sallar azhar da la'asar tare da isha da magarib, ina idarwa kafin na fahimci me ake ciki ya kuma ta sowa, yazo kaina janye bargon yayi sannan ya shiga b'alle botirin rigarshi. Wani irin kuka ne ya kwace min na takure kaina guri guda ina cewa. "Don Allah! Jaheed! Karka min haka! Wallahi ba zan kuma ba! Karka manta wata rana ba zaka ji dadin kaga ayiwa Yarka haka ba, Don Allah! Mujaheed." Cukume wuyar rigana yayi ya mikar dani, sai da ya yaga rigar har kasa, da sauri na kare kirjina, ya kuma shiga yaga duk wata abinda zata rufe min jikina, sannan yace. "Boye jikinki kike?" Cikin wani irin tsoro na fashe da kuka jikina na rawa, nace. "Wallahi bazan kuma ba!" Wani irin kallo yake min, tun daga fusakana, har zuwa cibiyata. "Zazzafa! Shi yasa kike jin kanki ke wata ce ko? Toh bari na rabaki da abinda kike dashi sai mu zama (0-0)! Ban tab'a dogon magana ba sai da na hadu dake Shaidaniya! Ban tab'a fuskarta tozarci ba sai da na hadu dake! Koda yake! Akwai yan matan da suke zuwa gabana tsirara suna niman Alfarmar na kalle su me zanyi da kayan yar talatin da hudu! Dan haka ki rike aranki anan zaki dawamma, sai an jima!" #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:49 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️     Fatan Alkhairi Maryam Kolo da Maman Ummite😍🌹 BIYU Da gudu nabi bayan shi tare da rike rigar shi cikin kuka da tashin hankali nace. "Don Allah ka rufa min asiri! Bani da kowa anan! Jay! Idan Yayarka kace a wannan halin zaka tafi ka barta" Juyawa yayi cikin zafin nama, ya ture ni sai da na zube a kasa, na sake mik'ewa zan tashi har ya shiga motar shi ya bata wata irin wuta. "Jayyyy!" Na kwala mishi kira! Tare da sake kukan da yafi nada karfi, ina  da nasanin abinda na aikata a cikin shekaru uku da suka wuce, zuwa huɗu.                ........ Aanih Fatimah Aryaan! Cikakken sunana kenan!      Shekaru ashirin da biyu baya..       --- Cikin tashin hankali! Suka nufi asibiti da ni, ranar da aka sace Yarima Jalal, abinda aka fara shine kara min jini, abin mamaki jinin kowa yaki Dai-daito da jinina, sai da Aka dibe na Sarki Jaamal, aka gwada take jinin yayi daidai da nawa, hankali Baabina ya tashi, tare da Ummi, sai kaiwa da komowa suke. Sai da na kwana na wuni, sannan na farka, ina tashi a firgice, na fara ihu, tare da niman inda zan b'oya. Sai da U mmih ta rungume ni, amma a haka na ture ta sabida karfin da yake shiga na, ihu nake tare da kiran sunan Jay! Tunda Baabi yaga matsalar haka take, sai yayi maza aka mai dani Sokoto.        Inda aka kaini shashin kakata, Umman Baabi. Tunda aka kira malamin masarautar, yana zuwa yayi min addu'a, sannan yace. "Zaku yi hakuri zuwa gobe! Insha Allah zamu duba Alamarin."     Haka suka amince, dake na samu barci, har washi gari da malamin yazo shiru yayi sannan yace. "Tabbas rayuwar mu da mutuwa duk na Allah ne! Sannan babu wanda ya tab'a zanawa kanshi ƙaddara! Sai dai  ƙaddarar yarinyar nan ta shiga na shi.       Haka ya sanya masu faffutikar ganin cewa sun dauki fansa! Sun yi tarayya akan ta! Dukda ban san meye ba! Akwai matsala. Sai dai zamu iya magance abin da Allah ya nuna mana!"    Daga haka bai kuma magana ba, ya mika musu addu'o'in da zasu na bani, ina sha.           A hankali na soma samun sauki tare da samun kulawa daga Matan Babana! Ummi da Ammih.           ..... Bayan na warke na cigaba da zuwa makanta, kamar yadda na saba.     --- A masarautar Daura. Gimbiya Sarah! Sai da tayi dogon jinya dan ya hadu mata da kewar D'anta da kuma ciwon zuciyar da yake barazanar kamata! Hakan yasa ta daina shiga cikin duk wani abinda yake faruwa a cikin gidan, dukda Abba Jaamal yayi kokarin fahimtar da ita! Hakan kaddara ce, dan haka su godewa Allah tunda ya basu wasu yaran.             Cikin zubda kwalla tace mishi. "Don Allah! Kawu karka sani jin wani abu a raina domin, kuwa bana raba daya biyun, Akwai Sannun wasu manyan mutane na cikin masarautar nan!      Wanda dama basu kaunar mu! Taya zanyi hakuri bayan nasan akwai mutanen da ban san su ba, a bayan Inuwar mu!      Kawu bazan tab'a samun nutsuwa ba, sai naga yarona!"          Cikin damuwa ya zuba mata ido, tare da tausayinta, sannan yace. " Zato zunubi ne! Kuma babu kyau don Allah ki cire tunanin wani zai iya cutar da shi."               Kwalla ne ya zubo min, na ciro takardan da aka kawo min na mika mishi, kallon rubutun yayi, sannan ya kalli agogon dakin yace. "Ina mai baki hakurin abinda na gaya miki! Tabbas akwai mutanen da suke son ganin bayan mu! Ganin haka ba zai samu ba, shine suka dauke min Yarona! Tunda sun zab'i haka." Mik'ewa yayi sannan ya isa bakin kofar, sannan ya juyo tare da zuba min ido yace. "Zan  yi murabus! Kafin Allah ya dawo mana dashi! Zan ajiye mulkin amma abisa sharadin kujeran masarautar na shine! Nan da shekaru ashirin idan ina raye! Bai dawo ba a bawa wani! Idan kuma ya dawo!"    Daga hakan ya fita daga dakin, yana jin ciwon abinda aka mishi,   .kai tsaye masarautar ya nufa, yana shiga ya sami Ajiya da Sa'i suna kus-kus, zama yayi a kujeran da aka killace shi saboda tsoron abinda yake faruwa.       Sunkuyar da kai yayi, sannan. Ya yayiwa Magatakardan masarautar alamu yazo yayi Rubutu! .... Gyara murya yayi sannan ya zuba musu ido kafin yace. "Ni Jamaluddin d'a ga Jalaludeen! Na ajiye sarautar da nake rike da ita! Na barwa d'ana Jalaludeen Jaamal," jan numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa. " Na sauka zan rike mishi! Insha Allah muna zuba idanun nan da Shekaru ashirin" Mik'ewa Sa'i yayi cikin fusata yace. "Kai karka mai damu! Sakarkaru mana, taya wanda ba a sani ba ko yana raye ko yana mace! Zaka ce kayi murabus, zaka ajiye mishi har nan da shekaru Ashirin! Hauk...."     Wannan karon jifen da aka yi sai da ya watsar mishi da haƙora domin da wata ƙatuwar dutse aka yi ta. ... Zubawa Kofar ido suka yi babu kowa, take wani irin tsoro ya kama su, Tabbas d'agawa Jaamal murya dai-dai yake da wasa da rayuwar ka, dan haka suka hakura tare da sawa a ransu kota Halin k'ak'a sai sun raba shi da mulkin masarautar.                ....... Mama Sarah ta daura aniyar niman hanyar da zata warware matsalolin masarautar, inda tayi tattaki har garin katsina, dakyar ta samu inda Yar Jakadiya Sahurah take.        Koda ta isa gidan Sarkin Katsina, tasa aka kira mata yar Sahurah, bayan sun gaisa tace mata. "Daga masarautar Daura nake! Ina Niman Jakadiya Sahurah!" Cikin tsoro da shakku matar ta kalli Mama Sarah sannan. "Kiyi hakuri! Ba'bata ta jima da mutuwa."     Tana fadar hakan ta mike zata bar gurin, Sarah tace. "Baiwar Allah! Mahaifiyarki bata mutu ba! Baki son na ganta ne? Bayan tasan kome!"    A firgice ta juyo tana kallon Mama Sarah. "Don Allah ki kyale mu! Tunda na gaya miki haka ki tafi mana! Ta rasu." Daga hakan ta juya abinda ran Sarah ya b'aci sosai, amma b'ata sare ba, bata kuma ji ta hakura ba, dan tana da yakinin akwai abinda take boye mata.    ... Haka tayi ta faffutikar ganin ta samu ganin Ta samo asalin wanda yayi rubutun wasikar da aka kawo mata, amma bata samu ba.         ---- Ina da shekaru sha shida, na gama makarantar sakandare, a shekara dubu biyu da uku, jami'ar nan Sokoto na samu, inda na fara karanta kimiyyar halittu wato (micro biology) lokacin da na fara, aka samu wata matsala inda muka tafi yajin aikin wata huɗu.      Zaman gidan yasa aka fara samun kakana! Datti tsohon sarkin sokoto, da maganar na girma da yawa, ya kamata ayi min aure! Bai kula su ba. Har muka koma makarantar.             --- A gajiye na shiga cikin gidan, bayan na fita a cikin motar da take kai ni makarantar, na zube a katon falon mu.     Kallon Baabi nayi yana rike da hannun Firdausih, yar karamar yarinyar da Ummi ta haifa. "Baabi na! Na fara kishi da Janny fa"      Na fada tare da tura mishi baki. "Toh Gimbiya! An Janny wata shashi ce ta rayuwar mu! Har dake, shi yasa nake matuƙar son wannan Jannyn, sannan ina kuma kaunar Umminku! Sabida ita din Jinin Janny ce!"       Gyada kai nayi sannan na zuba mishi ido sannan nace. "Baabi na! Kuma kace ita tana da kirki ko?"      Gyara zama yayi sannan yace. "Janny! Tana da hakuri! Tana da kawaici, Janny tana da mugun zurfin ciki, zai yi wuya ta gaya maka abinda yake damunta, amma a hakan kuma tana sona tare dake da Ummana, haka yayi matukar min dad'i a rayuwata, domin bata rasu ba sai da ta nima min auren Rahil! Kinga bazan tab'a mancewa da ita ba.       Sabida macen arziki ce, me matuƙar mutunci da sanin Yakamata."           Shiru nayi sannan nace. "Baabi kuma bata tab'a Haihuwa ba ko?!"     Fuskar shi ce ta koma wata iri, daga tambayar. D'ago kai yayi, tare da zuba min ido, dai-dai lokacin da jini ya digo min daga hancina, wani irin jiri ya kwashe ni ban kuma sanin abinda ya faru ba, sai cikin dare.       Naji muryan Ummi tana kuka tana magana. "Yallabai! Wannan halin da take ciki! Tsoro yake bani! Domin kusan abinda ya faru Rahilah kenan! Tayi karama da ɗaukar wannan kasadar, ba ita ta fara ba taya ita zata zame abin tuhuma."     "Kinga babu kome! Jarabta ce! Kuma zan amsheta hannu bibbiyu. Sannan nafi ganin kamar canfe ne, da zaran munyi imani dashi wallahi itama zata iya tagayyara kamar Janny! Dan haka bamu yi imani da canfe ba, Allah ya bata lafiya."         Lumshe idanuna nayi, ina kallon wasu mutane da suka saka wani yaro a cikin buhun hatsi,  mika hannuna nayi zan rike buhun, naji kamar yana kara min nisa.         Kara mikawa nayi, Baabi yazo ya rungume ni. "Baabi na! Sun tafi dashi ko? Ka gamsu can suna saka shi a cikin buhun hatsi! Zasu tafi dashi."          Addu'a ya shiga tofa min kafin wani lokaci, barci ya kuma ɗaukata, ina ta surutu.       ...."abinda ya faru! Ranar yake yawo a ƙwaƙwalwarta, sannan kuma takan manta dashi, amma yawan bata labarin Jannart shine yake taso mata da nata Ciwon dan haka babu wani abu, Allah ya bata lafiya."               Haka suka kwana a kaina, Ummi tana gaya mishi gundarin Labarin abinda ya faru, a ranar. Sake baki yayi cikin mamaki yace. "Akan me zaki dake shi? Kome yayi mata ina ruwanki? Wato kece ma kika yi sanadin barin shi gidan? Kai Amma wallahi banda wani dalili da na mare ki! Wallahi kin bani haushi fiye da kima.    Gashi nan kin saulawantar da rayuwar d'an YAR UWARKI, ki barshi da Matar Uban shi, Mahaifin shi yaga min cewa.    Yarinyar zata iya bada rayuwarta akan Yaron, shine kika mata gori akan dan ba ita ta haife shi ba? Toh ke da kike uwa daya Uba daya da Uwar Yaron, Kinga abinda kika aikata.           Ita da bata haife shi ba, tayi abinda kowa ya gani babu me zaginta, shi yasa mana take kallon ki ranar da muka koma addu'o'in Allah ya dawo mana dashi, ashe kin san abinda kika aikata mata shi yasa take miki kallon abin.       .toh wallahi ki shirya muje ki gayawa Jaamal abinda kika aikata ba shi ba, hatta Appa sai kin gaya mishi, domin kin zalinci zuciyar kowa! Kuma kin samu zubda kwalla sabida sakarcin ki na banza, nayi imani tayi hakuri ne sabida tana miki kallon Jannart ce a gabanta, da babu abinda zai hana bata miki rashin mutunci ba, kin bani mamaki.       Aiko dan tarbiyyan da ta bashi, ya kamata ki d'aga mata kafa, bawai kice ta mishi tarbiyyan mugunta ba, dan haka ki shirya muje ki bata hakuri, tare da Uban Yaron, dan babu abinda zaki kuma yi nan gaba, sai dana sani mara iya ka da amfani.. #MI #HWA #Mai_Dambu... 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!! {CIGABA KWARKWARAH} *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ Godiya sosai Maman Abba Allah yabar zumunci!🌹😍 UKU.. Haka Baabi Yasaka Ummi a gaba da fada har karshe ya bar mata d'akin, tana kuka da dana sanin, abinda ta aikata, a cikin daren ta haɗa kayanta kala daya. Da asuba ta barni a hannun amintacciyar baiwarta, sannan suka nufi Daura. Sun isa da wuri, dan haka sun sami ganin Sarki Jaamal. Bayan sun gaisa Sarki Jaamal yace musu. "Amma kun fito wani guri ne? Dan naga kamar daga tafiya kuke?" Sunkuyar da kai Baabi yayi sannan yace. "Mun zo baka hakuri ne! Akan b'atar Jay! Shine muka zo domin mai d'akinka tasan kome!" .gyara zama yayi sannan yace. "Dan Rahil tayiwa Jay fada ya fita, shine zaku zo bani hakuri! Rahil! Kanwar Jannart ce, kuma uwa ce mishi, koda me tayi bazan tsawatar mata ba, sabida tafi ni kaunar shi, kai jinka da Jannart tana raye zata yarda na dibo jiki kazo bata hakuri ne bata borance muku ba, wallahi ban tab'a jin kome akan b'atar shi ba. Sai dai ina kyautata zaton cewa! Allah yayi hikimar haka ne dan wasu dalilai, da yana tare damu, bazai iya rayuwa babu kalubale na, dan haka babu komai." Shiru duk suka yi sannan Aaryan yake gaya mishi, ai ga halin da nake ciki, shiru Sarki Jaamal yayi sannan yace. "Karku canfeta, ku dauka jarabta ce! Domin yin haka dai dai yake da wasa da rayuwarta. Don Allah karki bari wani ya camfeta" Wannan abun da ta gaya musu, yayi matukar tasiri a zuciyar su, har suka dawo gida, sun sanya dokar kar wani ya kuma cewa akwai wani abu a tare dani. ---- A hankali rayuwa take Gara mana, har na kusan gama jami'a, a lokacin na hadu da wani soja, muka makalewa juna, a waya dan a lokacin Waya ta shiga hannun kowa, idan muna wayar nan kamar zamu cinye juna, tun ina b'oyewa har na hakura kowa ya sani. Aikuwa Adda kishiyar kakata, ta sani a gaba da Tsokana. Sai na gaya mata. "Ke yar doguwa waye ne kuke magana dashi a wancan manta sabo." "Addah ki fita idanuna na rufe ina ruwanki da darling dina, jeki gurin dattin ki, kuyi ta lallaba juna" Maka min mahuhuci, Innono tayi kamata, na tura mata baki cikin jin zafi nace mata. "Wallahi koda Baabi ya sayo miki maganin zafi ya bani, bazan kawo miki ba tunda kika buge ni!" Ina tura mata baki. "Yar kwaila kawai, dube ki don Allah waye zai yi asarar kudin shi ya auri mace ba kirji." "Innono! Wallahi ki daina wannan maganar, zaki sanya ni dai na shigowa wallahi, ai haka Allah yayi ni" "Karki kuma saka mana mijin mu" sake baki nayi tare da kallonta sannan nace. "Yanzun don Allah sabida wancan takwarkwashen mijin ku,.kike min wannan wulakancin, na zata sabida kawai na tsokani yar uwanki! Toh wallahi sai na kuma!" Make ni ta kuma, na tura baki na karar wayata ne ya katse ni, na dauka tare da sakawa a kunne na. Gyara kwanciya nayi, sannan na lumshe idanuna, tare da bude shi nace. "Barka hasken rayuwata! Muhid" Murmushi ya sake, wanda naji sautin shi har cikin jikina, lumshe idanuna nayi tare da narkewa a cikin kujerun falon. ."farin cikina! Ya yau? Da fatan kina lafiya." Juya idanuna nayi sannan na sauke ajiyar zuciya nace. "Alhamdulillah! Da fatan kai ma haka;" "Gamu nan muna fama zamu tafi gurin wani meetinga da fatan Kema haka!" Nan muka tsinke da hira, kamar me, har Addah tana dukana, ban ce mata kome ba, sai yar kukan da na saka, muhid yayi ta min dariya. Mun hadu da shine lokacin zamu aikin Hajji, shima zai tafi da Yan uwan shi da Maman shi, tun daga lokacin muka fara gaisawa sama sama, har muka dawo daga nan kuma soyayya ta bude Muhid Nasir Arkilla shine cikekken sunan shi, yana aiki da hukumar soja na kasar nan. Yanzun haka yana garin Makurdi..shine yaro na uku a gidan su, yana da yayu mata biyu a gaban shi sai shi na uku sai kanen shi biyar. Muna gama waya dashi na katse kiran na mike ina mita tare da shafa inda Addah ta zabga min duka. Shigowar Kanin Baabi, Baba Annuwar, ya sani mik'ewa da sauri, sabida ban san me nayi mishi ba, yana dan jin zafina. Tunda na gaishe shi, na sa kai zan fita. Ya bini da ido, da sauri na fice dan shine Ɗan Addah na biyu, dan haka shima yana son kujeran da Baabi yake Kai. Akwai wasu abubuwan da yake faru a cikin masarautar mu, amma bai da wani damuwa, kawai dai abin ya kasance kome sama-sama ne, kuma ana ƙoƙarin b'oyewa sabida mu yara. Baabi yana da hakuri kuma duk abinda zaka mishi bai tab'a d'aga ido ya kalle ka. ...... Muhid ya gabatar da kanshi ga gidan mu, da ahalin gidan mu baki daya, sai kuma aka yi dace shima mahaifin shi, dan yana da sarautar a cikin masarautar mu, Dan haka ba tare da wani tsawaitawa ba, aka saka komai cikin mutunci da girmamawa, domin anyi tunanin gwara ayi bikin nayi bautar ƙasa a dakin mijina. Wannan tsarin yayi mana dad'i, dan haka na mai da hankalina guri guda, lokacin bikin mu na karatowa Kakanina na gurin Uwa suna ƙoƙarin gyara ni, ga matan Baabi, suma matukar ƙoƙarin na fito Matar so. .... Haka aka yi ta shiri babu kama hannun yaro, har lokacin bikin yazo, aka fara duk wata shagalin da ake na al'ada, da sauran su a aure. Sai dai a bangarena, tun saura kwana uku bikin na soma wasu irin mafarkai, masu mugun ban tsoro. Ban damu sosai, ba har aka daura auren, ranar hankalin kowa ya tashi domin kuwa kin fita nayi ina kwance sai da Baabi ya saka aka b'alla kofar dakin, koda suka shigo sun same ni ina zaune, na cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina kuka sosai. Zama Baabi yayi tare da cewa. "Na zata zaki fi kowa farin ciki, dan zaki tafi gidan Muhid, Sai gashi kina zubda kwallarki masu daraja! Fatimah gaya min baƙi son auren ne? Idan baki so yau za a raba auren, dan nayi alqawarin bazan tab'a barinki, ki zubda kwalla ba." Ciro kaina nayi cikin kuka nace. "Baabi! Tsoro nake ji, tsoron kar wani abu ya faru." Riko hannuna yayi sannan yace min. "Kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru sai Ikon Allah, Insha Allah bazan tab'a barin ki, kiyi kuka ba, maza shirya an jima zasu zo su tafi dake! Khatoon ki taimake ni naji a raina na sauke nauyin da Allah ya daura min ne. Don Allah ki rike mijin ki da kima, yin amfani da hakan zai sani jin na cika Burin Fareeda." Gyada kai nayi cikin zubda kwalla nace. "Insha Allah Baabina!" . Bai fita a dakin ba sai da yaga na shiga ban daki nayi alola sannan ya fita, yacewa Ummi. "Ku lallabata." Ina sallah ina kuka, har na idar, sannan na zauna naci gaba da kuka, ina tausayin kaina da Baabina, Shigowar Mama Sarah da Umma Raihanah, da wasu mata dai da suke da daraja, duka shiga shirya ni cikin liffaya, tare da min wanka da turaren zamani da na hadin Maiduguri, aka kaini shashin kaka na, inda Baabina yake, tunda na shiga na matsa jikin Baabih na daura kaina a bisa cinyar shi, ina sauke ajiyar zuciya. Haka suka min nasiha sosai, sannan aka zo za a fita dani na rike shi, nace. "Wallahi bazan biku ba, shi zai kai ni!" .dayawa yan uwan shi, sun ji haushina amma ban damu ba, sabida bani da kowa sama dashi, Haka ya riko hannuna ina kuka ya amshi keyn mota ya saka Ni gefen shi, bai dauki kowa ba, muka nufi gidan su Muhid, tun kafin mu isa aka kira Muhid aka gaya mishi ga Amaryan shi babanta yake kawo ta. Yan rakiya na, sun biyo bayan mu, koda muka isa. Har cikin gidan ya kaini ya zauna a babban falon gidan yayi ce a kira mishi Maman Muhid! Cikin shigar kamala ta iso. Bayan sun gaisa, sannan yace mata. "Toh ga Fatimah Khatoon nan na kawo miki ita, Bata san mahaifiyarta ba, amma tasan Baabinta, Amma daga ganin Muhid nasan cewa! Yayi sa'an Uwa, ko babu kome zaki riketa a matsayin yar da ta taso babu uwa, nagode sosai." .ya faɗa a raunane, cikin damuwa da kewata. A hankali ya mike na kuma rike hannun shi. Cikin kuka ina cewa. "Baabi! Don Allah!" Rikon da Muhid yayi min itace ta hanani karasa abinda zan fada, haka baabi ya tafi ya barni a cikin su, Ummi da Sauran mutanen suka kai ni dakin Naman Muhid, kowa sai magana yake akan irin shakuwar da take tsakanina da baabi. Dakyar nayi barci me cike da ban tsoro da firgitarwa, cikin dare, naji ana ta hayaniya, buɗe idanu nayi naga Maman Muhid tana share kwalla, hannunta rike da calbi, tashi nayi zaune tace min. "Koma ki kwanta kinji!" Shigowar Tayar shi tana kuka wiwi, ya sani tashi zaune ina raba idanuna. "Allah ya jikan Muhid!" Wasu irin taurari naga suna yawo a kaina, daga nan yadda na bude baki zanyi magana, kawai sai bushewa nayi a gurin. Hankalin su yayi mugun tashi. Akan lokaci aka wuce dani asibitin kwararru na nan Sokoto, aka shiga duba lafiya, kafin asuba Baabi ya iso, cikin farar jallabiya. Ina kwance, zama yayi a gabana yana me tausaya min, har na farka rike wuyana nayi ina son nayi magana amma ya makale. Dakyar nace mishi. "Baabih ruwa!" Babu ruwa a dakin dole ya fita, aka nimo ruwan ya dawo ya bani nasha, wani irin kuka ne ya kwace min, ban san ya akayi ba nayi aman jini. Abin ya d'aga hankalin Baabih akwai Kanwar shi da take aure a Canada, tazo itama , dan haka zama tayi a jikina. Haka na zama kamar mahaukaciya, bana hum bana hmm! Har tsawon kwanaki bakwai aka sallame ni, daga nan gidan Mu aka wuce dani, a lokacin Ummih da Ammih suka ke kula dani, na sha matukar wahala, sabida bana iya magana da kowa, mutuwar mijina. Ya dake ni. Ashe rungume Ni da yayi shine kawai abinda zai hada mu dashi, haka nayi ta jinyar zuciyata. Na tsawon watanni sannan na koma makaranta dan saura kiris na tasa jarabawar karshe. Muna gamawa na samu damar tafiya, bautar ƙasa, har zuwa lokacin naki sake jiki da wani namijin dan gani nake kamar abinda ya faru da Muhid zai kuma faru dashi. Koda na gama bautar ƙasa, na samu koyarwa a cikin wata makarantar kwana da take nan Sokoto..... #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️       Fatan Alkhairi gare ki Mame na group ɗin Bagudu 😍🌹 HUƊU Cikin lokaci ƙalilan na fara koyarwa, bawai dan albashin ba a'a, sai dai haka yana matukar rage min kewar Muhid, sosai na maida hankali na sosai akan abinda nake.               Shi yasa sam ban kuma damuwa da kowa ba, sai dai haka kawai muna cikin wannan yanayin Sai ga Baraq ya shigo rayuwata.            Tun daga ranar da na ganshi, a daren na kwana ina mafarkin shi, inda nake ganin shi kwance cikin jini. Washi gari haka na tashi babu walwala, tunda na nufi makarantar na daure fuskana tam, duk yadda naso kauce Mishi sai da ya shige min.                   Haka muka tashi ban sake mishi fuska ba, duk yadda naso kar na shiga rayuwar shi, ina Baraq ya gama shigewa rayuwata. Shi yasa naki shi yayi juyin duniyar akan naso shi naki.      Yakan sani a gaba yana kallon tare da ce min. "Fatimah meye laifina?! Ko dan bamu da arziki ne?!"      Girgiza kai nayi, sannan na zuba mishi ido, kafin na bude baki nace. "Kawai bana jin kome akan ka ne! Kuma da zaka taimaka min ka daina damuna zai fiye maka Alkhairi."    "Toh an tab'a kin mutum babu dalili ne? Ki gaya min meye matsalar ki da ni?!"      Mik'ewa nayi ina duba agogon hannuna, sanan nayi wuccewa ta na barshi a gurin tsaye. Yana mamakin yadda nake gudun shi.        --- Baraq Nafi'u! Ya addabi rayuwata, yadda ya kai kanshi gurin Baabi ya bani mamaki, dan haka ba iya gurin Baabi ba, sai da ya gama zage dangin mu, na cikin masarautar, da nuna musu yana kaunata.     Su kuma suka mara mishi baya da taimakon Baabi, zama nayi a gaban Baabi, ina kuka wanda tun rasuwar Muhid ban kuma haka ba, kallona yayi sannan yace.           "Toh Mamana meye na kuka haka indai Baraq ne, zan ce me ya hakura, kuma zan nima miki wanda ranki yake so! Amma ki duba dakyau yaron yayi kokari domin kowa a cikin zuri'ar mu, ana son shi dan haka kiyi hakuri ki amince ayi abin." Cire kaina nayi cikin kuka nace. "Baabi! Tsoro nake ji! Ina tsoron abinda ya faru da Muhid don Allah baabi na kayi wani abu."     Jikin shi ne yayi masifar sanyi, tare da kura min ido, yana me jinjina maganar da nayi, amma da ya tuna. An hana shi camfin abinda zai faru, dani sai ya zuba min ido na wasu lokuta kafin yace. "Za ayi auren ki daina sakawa a ranki wani abu zai faru saboda babu kyau canfe!" Da haka Baabi ya kashe bakin maganan ya kuma hanani cewa kome, na cigaba da zubda kwalla, ba tare da na amince ba Baraq ya shiga niman aurena, tare da goyan bayan Baabi na, sabida lokacin, na kai shekaru ashirin da biyar, dan bayan na gama bautar ƙasa, nadan zauna na shekara daya, toh yanzun fara aikina ma yana niman shekara biyu.       ..tun ina nunawa bana so, har ta kai na hakura, sabida Baraq akwai son sanya mutum a walwala. Haka kuma Iyayen shi, suma sunyi godiya sosai da irin karb'an da aka yiwa ɗan su.              Tunda aka fara hidimar na fara mafarkin ya mutu, har aka daura auren, a tsora ce nake, kasancewar ni bazawara ce yasa aka kayi kome a ranar, sannan aka watse.           Bayan ya samu rakiyar abokan shi, tare da mana yar nasiha. Sannan ya raka su.   Bayan ya dawo, ya fara nuna min wasu abubuwan da gaskiya tunanina bai kai nan ba, kunyar shi tasa na shige ban daki nayo..ina cikin ban dakin naji yana magana a waya, ina fitowa ya janyo ni, tare da matse ni a jikin bango, ga baki daya dauke wuta nayi, sabida jin yana min abinda yafi karfin tsayuwa.     Lokaci guda naji kamar zan zube, haka ya kuma matse ni kamar zai yi kome dani a tsaye, duk da a shekaruna bai dace na razana da shi ba, amma ga baki daya sai nake ganin kamar yana wuce iyakata.     .... Ganin kamar zan zube a kasa ya sashi mana masauki a gadon, daga nan ya nime kome ya faru, sai dai buga kofar gidan da ake yi yasa Allah ya kwace ni a hannun shi, har zai fita ya tsaya yana murmushi sannan yace. "Da dai kin buɗe idanunki, domin yau zamu raya daren ne!"          Jan bargo nayi tare da rufe fuskana, ina me juya mishi baya. dan ban san ya akayi kayan jikina suka watse ba, gidan da muke hade yake da na iyayen shi, suna dan ciki damu. Dan haka naji muryan yayar shi mace da namiji suna magana da ƙarfi.                 "Yo kwaɗayin abin duniya Yasaka auri mutuwarka ita din ba macen aure bace, sabida akwai tsinuwar  mutane da aljanu akanta kazo muje cikin gida, kaji a cikin mutanen da suka zo daga kauye iskar wata ya tashi take gaya mana, wallahi kazo."                 Koda suka shiga abinda matar tace. "Ayya! Ina baku hakuri sabida sun kashe shi, kuma itama yasan ya mutu, tunda tana yawan ganin shi cikin barcinta an kashe shi, dan haka kuyi hakuri ku koreta a gidan dan zasu iya yin komai."       Kawai ganin Baraq aka yi ya yanki jiki ya zube tare da anan jini, dan haka kanen shi da mugun gudu suka yi d'akina, tare da rufewa zasu dake shi, sai dai abin mamaki sunyi bugun duniyar nan yaki buɗewa karshe haka suka hakura.               Har zuwa asuba, sai ga Baabi da Ummin suka zo, tare da zama akayi jana'izar Baraq sannan aka kai shi ina kwance ina barci me hade da mafarkin ya rasu, har ina cewa karya ne a mafarkin yanzun yanzun ya gama.      Buɗe ido nayi ga yan uwan mu, da sauran mutanen. Tashi zan yi na tuna babu kaya a jikina cikin kunya. "Ummi kayana!"       Mik'ewa tayi ta bani nasaka, sannan na sauko da kafana daga gadon, kawai naga hatta bargon jini ya b'ata, shiru nayi ina nazarin abin da ya faru, su kuma ganin haka. Sai suka dauka ai jiyan, sai da yayi tarayya dani kafin ya rasu.          Ban fahimci abinda yake faruwa ba, amma yadda naga suke kallona ya ɗan sani tsarguwa da kaina, a hankali na shige ban daki nayi wanka da alola nazo na gabatar da sallah, bayan an dawo daga kai Baraq makwancin shine Baabi ya nemi tafiya dani, sabida yadda yan uwan Baraq suke faɗa zasu kashe ni.     Tunda na zama makara, duk wanda ya aureni mutuwar shi ya aura. Babu wanda ya gaya min abinda ya faru, sai da naga suna hada min kayana, anan na fahimci akwai wata matsala. Dan haka na shiga tambayar su, ko ya sake ni ne. "Ba sakinki yayi ba, Allah yayi mishi rasuwa ne!"            Kurawa Ammih ido nayi, na kama dariya dariya kamar mahaukaciya, ina nuna su da hannu, zuwa wani lokaci na zube a gurin. Na fara ihu tare da kuka, dakyar Aka fitar dani a gidan,  zuciyar Baabi ta karaya da alamarina.       Dan haka koda muka isa gidan na kule kaina a daki, sai da Baabi ya ɓalle kofar, shi ke bani abinci a baki. Shi yake kula dani, har na sami watanin da zan gama takaba, daga nan ban kuma sha'awar fita kofar gida ba, kai ko bikin sallah ake bana fita waje.     Balle kuma wani sha'anin bana zuwa, sabida bayan rasuwar Baraq, anta yawo dani wai mayya ce ni.               Har takai a cikin Zuri'ar mu, ana zargin na da hakan sai na daina shi, duk da wasu na zuwa gidan mu dan ganin halin da nake ciki,sai Allah ya nuna musu bani da wani damuwa a fuskar sai a zuciyata.     Akwai Yayar Baabi hajiya Amina,.tana auren Wazirin sokoto, dan tane ya fara nima na, kamar da gaske, dan na fara gudun shi, kawai tasaka aka kirani, koda naje gidan, ina zaune a falon kasa wasu yan mata biyar suka fito, biyu yaranta ne, daya kuma yar kawarta ce. Biyun Kawayen su ne.        Kasancewar muna wasa dasu, suna zuwa suka zauna. "A'ah makara kece a gidan?!" Wani irin muzanta nayi domin a kiraka da makara ba abin dad'i bane.                         Ciro kaina nayi ina kallon su, sai kuwa suka kwashe da dariya, sannan suka ce. "Ban da rashin adalci! Taya kin san baki da lafiya zaki amincewa Ya Hisham! Dan ki kashe mana shi ko? Toh wallahi idan baki rabu dashi ba. Kai ku tashi muje,  ga mace har mace ta zama matar mutuwa! Kowa ya aureta sai wani bashi ba."      Shiru nayi ina me wasa da zoben hannuna, har Yayar Baabi ta sauko Hajiya Amina, kaina a sunkuye, ta zauna. "Da fatan su Khareema da Loloh sun miki kashedin kar na kuma jin labarin Hisham a cikin gidan ku! Idan kuma kina son a tozarta zumunci ne toh zamu yi hakan."          Girgiza mata kai nayi, sannan na mike tare da ce mata. "Sai an jima!"     "Ki dai k'iyayye abinda nace miki"      Tunda na fita, dakyar nake takawa, har na isa gidan daki na wuce na rufe kaina, duk sai naji Sokoto  tayi min girma, dan haka nayi kuka nayi kuka a ranar, kamar babu abinda zanyi bayan shi.       A hankali rayuwata ta zama abin yayatawa, yau saurayi zai zo gobe zai gudu bani kuma ganin shi, haka ya sa. Shiga kunci sosai.    Domin har nayi dana sanin rayuwata, bani fita bani da kowa sai kanwata Hanisah, wacce muke matukar kaunar juna da ita.    Sai Muhammad Kabir, shi ke bin Hanisah, shi kuma yaron Ammih ce, sai Janny  ita ke bin shi, kafin Kuma Kazeem, dan Ummi da Hassan da Hussaini, duk yaran ta idan aka cire kabir, Yaran Ammih biyu ne Kabir da Husnah.          Dan haka idan na shiga damuwa kanena, zagaye ni suke suna masu kwanciya a jikina, suna kuka, yawan damuwar da nake ciki yasa Baabi shirya min kayana zuwa Canada.               Haka yayi min dad'i sabida inda Zani a Canada, Yan uwan mune! Aunty Fouzia, da mijinta shima Kuma Yayan Mana na ne.    Suna zaune a jahar Calgary na kasar Canadan, sani a gaba kanena suka yi, wannan yace kaza wannan yace kaza.    Karshe ni dai kallon su nake ina murmushi me hade da kuka, sabida zanyi kewar su. Tunda muka fito, dayawa wasu sunyi farin cikin tafiya na, saboda kar na zauna y'ay'an su. Suce suna sona.        Cikin shekaru talatin na rayuwata, na fuskanci damuwa har nake ganin kamar dan ni matsalar take karuwa, sai dai tunda na bar sokoto naji matsalar ta ragu min.     Baabi da kan shi, ya kaini Canada, mun isa garin Calgary da safe, tun a filin jirgin na fahimci haduwar garin, sannan muna tsaye Aunty Fouzia da mijinta suka zo daukar mu.   Cikin farin ciki, Yanayina bani da jiki sosai, amma ina da tsayi masha Allah, sannan ina da dan karamin kyau, dai-dai gwargwado, amma ni wankar tarwada ce, bakina yana da dan fadi. Sai dogon karan hanci, bani da manyan idanu, amma yanayina ba laifi. #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ Fatan Alkhairi Fans din KWARKWARAH da MAGAJIN IZZAH ga Pagen ku nan gaisuwar taku ce😍🙈 BIYAR. Idan nace zan baku labarin yadda garin calgary yake zamu kwana mu wuni ban gama bada labarin yadda garin yake, dan matuƙar haduwa ce, koda muka. Isa gidan wanda yake.        Preston town, anan motar su Kawu Muddam ya tsaya,  a hankali ya karasa jikin kofar gidan ya tsaya, sannan muka fito. Ina kallon Unguwa, yayi min kyau, musamman iskar da take kad'awa.                Cikin gida suka mana jagora shi da Umma Fouzan, tunda muka shiga nake kallon yadda tsarin gidan yake, bayan munci abinci muka yi wanka na kwanta kenan Baabi ya turo min yar Karamar yarinyar Umma Fouzan me suna.       Ablah, da sauri na mike na fita gurin shi.     "Baabi na gaji ne! Na kwanta na huta."            Murmushi yayi sannan ya kalli agogon hannun shi yace.       "Zamu shiga jami'ar Alberta ne, mu gama miki kome zuwa nan da jibi na koma gida!"    Gyada kai nayi, sannan nace mishi. "Baabi ko nazo muje ne?!"        "Idan zaki iya muje mana!" Murmushi nayi dukda na gaji sosai, amma bana son rabuwa da Baabi na ya sani shiryawa zan fita sai ga Umma tashigo. "Ba fa inda zaki domin nace su tafi! Ko kunya baki ji ba, ƙatuwar Uwar mata, zaki bishi zokai-zokai toh sai ki kwanta ki huta"      Tura baki nayi idanuna suna kawo ruwa nace. "Ni wallahi mutum ba yazo ba, a hana rayuwar shi sukuni." Dariya tayi, abinta dan mun saba fadar mu da ita. Fita tayi yanar ni, nayi kwanciya ta..                   --- A cikin kwanaki biyar suka gama min, kome sannan Baabi yayi min nasiha. Tare da ja min kunne kar naga bana gida nace zanyi abinda rai nake so.       Naji nasihar shi, amma bazan iya bari a ci min mutunci na kyale ba, dan haka ranar da na cika sati daya, ya koma nima kuma a ranar zan fara zuwa makarantar. Da wuri na shirya cikin doguwar rigar, tare da nad'e kaina. Da farin mayafin.     Sai takalmina baki shigen kayan jikina. Tare da jakar da nad'ebi abinda zanyi amfani dashi. Na nufi waje inda Kawu Muddam ke jira na, sai danna ansakuwar shi yake.              Koda na isa waje, na kalle shi a hankali. Nace mishi. "Kayi hakuri!"    Kallon agogon shi yayi, na shiga tare da gyara zaman agogona, ina son agogona domin gadon Mahaifiyata ce, dan agogon ta zinari ce hadi da Lu'lu'u, Baabi yace shi ya sayawa Maaminah, lokacin zuwan su, Madina bayan auren su.      Shi yasa nake son agogon dan yace min, na rike shi da kima. Mun isa makarantar, shi da kanshi ya kai ni har cikin ajin bayan mun biya wani ofishin mun ajiye bayyanan na fara karatu, har kofar aji ya ajiye ni tare da bani wata takarda da zata kaini unguwar da muka fito.                     ... Bayan tafiyar shi na shiga ajin na zauna, duk da kowa harkan gaban shi yake. Nima na zauna tare da nutsuwa guri guda. Ina kallon yadda suke hidimar gaban su. Dake nima ba ma'abociyar son magana bane, ban kuma  kallon kome da suke yi ba. Shigowar wani bature, wanda zai dauke mu a darasin lissafi. Ya gabatar da kanshi. Sannan ya fara abinda ya kawo shi, yana gamawa ya fita, a hankali naga daliban nata fita, nima daukar jakata nayi na fito.                  Dandazon dalibai na gani, maza da mata, ana ta tafawa tare da kiran. "Jay!Jay!"         Ban damu da naje gurin ba, na zauna na fara abinda ya kawo ni. "Oo shit!" Naji an Fada tare da cewa. "Sarkin mu! Ka buga wasan mana, karka bari Lucky ya kwace kwallon"    Ban d'ago ba, sai da naji suna cewa. "Wowwww! Sarki Juyo kaga wata yar tsanar barbie! Dubeta don Allah, daga gani itama yar Afirka ce." A lokacin na d'ago idanuna, tare da kallon gurin, da suke maganar sai naga dayawan mutane ma nice na zame musu abin kallon.         Bai juyo ba, sai sharb'e gini yake. Ya kuma buga kwallon a kasa, tare da cigaba da wasan, a hankali ya juyo tare da kallon inda suke magana ta, ban san me ya faɗa ba tunda kaina a sunkuye yake. Sannan kuma bani tunanin ya faɗa wata kalma mai ma'ana, sai ta rashin d'a'a sam babu alamar yayi magana kawai naji sun kwashe da mugun dariya har da buga inda suke.           Sosai sai da naga wata yarinya tazo inda nake ta zauna tace min. "Barka dai!"     "Yawwa!" Nace mata ina rubutu, gyara zama tayi sannan ta fara da cewa. "Dake fa Jay yake magana baki sani ba!" Kallon waye Jay nayi mata, ta nuna min inda suke wasan ƙwallon kwando, cikin Sa'a idanun mu suka haɗu da juna, kauda kaina nayi tare da cigaba da cewa. "Idan ya isa yazo gabana yayi maganar shi, ba ya tsaya a can yayi magana ba, sanan ni karatu ya kawo ni ba fitina ba, karatu ya kawo ni!" ..ina gama gaya mata haka, na mike ba barta dan dama ina magana tare da tattara kayana ne.       Kallon juna suka yi dashi tare da d'agawa juna kafad'a. Ina aji na shiga na zauna zuwa wani lokaci aka dawo malami na biyu ya shigo inda zai dauke mu, kimiyyar lissafi.               Mun mai da hankali, kawai sai ga yaran nan sun shigo cikin ajin, koda suka shigo. Kallon Malamin suka yi, tare da hana shi yin komai, yana kallon yadda kowa yake shan jinin jikin shi, bayi magana ba sai wani takaddarin yaro irin shi yace.             "Karku damu! Shugaban dalibai! Ya shigo ya duba yadda kuke karantunku sannan kuma, yaji hujjar da ya hana d'aya daga cikin ku zuwa gaida shi a matsayin shi na shugaban ku."   Juyawa suka yi, suna kallona. Shanye da toka, na zubawa abinda nake ido, ban ko kalle inda suke ba.              Buga kujeran da nake yayi da kwallon hannun shi, ban d'ago kai ba, amma na razana, sai dai ban nuna haka ya dame ni ba, sai ma kauda tsoron da nayi naki d'ago kaina, cikin jin haushi. Dan koran shi yayi watsi da kayana, ban san lokacin da na tattaro duk wani jurinta na kifa mishi mari ba, sai da yayi taga-taga zai fadi  cikin zafin rai nace. "Kwashe min kayana! Ko na kara maka!"         "Ni kika mara?!" Ee e Ya faɗa a fusace, zai yo kaina. "Abeel!" Yana kiran sunan shi, ya kwashe min kayana,  yana huci tare da cewa. "Ki fara kuka daga yau!" Sannan suna fita, ban damu ba dan iya haukar da zasu yi kenan.             Suna fita, malamin yace min. "Kiyi hakuri gaskiya, kin lakato rigimar da tafi ƙarfin ki, domin zasu miki abinda baki tsammani ba, dan haka dabar su take."   Gyara zama nayi sannan nace. "Meye amfanin hukumar makarantar da bazata hukunta su ba."       Murmushi yayi sannan ya cigaba da abinda yake, yana fadin. "A wannan duniyar! Idan zaka mu'amalanci mutane kayi nazarin wata gudunmawar suke bawa al'umma, shi yaron da kika mara, kwararre ne a fagen lissafin kimiya, wanda nake muku, shi kuma Uban gayya su, jajjurtacce ne a kowani ɓangare, likitane yanzun haka digiri na biyu yake shida abokan shi.          Sai sauran suma muna kiran su, dan ba iya kwallon kwandon ba, jami'an mu tana alfahari da Mujaheed Harisou Agla, sabida kwazon shi. Likitane da yake da matukar tausayi, da kuma son na kasa dashi, matsalar da aka samu da tun zuwan ki, kika gaishe shi. Tabbas da haka bai faru ba."           Kallon Malamin nayi sannan nace. "Kenan abinda nayi shine kuskuren! Na taso inda aka san daraja d'an Adam ne, taya zasu shigo lokacin darasi sannan, kuma su ce zasu yi abinda suka gadama."    Daga haka ban kuma magana ba, na shiga hada kayana tare da mai da hankali na, kan abinda nake yi. Har muka tashi wajen karfi biyu da rabi, ko ta inda wad'ancan jakunan suke ban kalla ba, nayi gida abuna.           Koda na isa gidan watsa ruwa nayi, tare da sallah na kwanta.             --- "Jay! Marina tayi ga!"      Watsa mishi ruwan coffee din bakin shi yayi, tare da daka hannu a bakin shi alamun yayi mishi shiru. Ya cigaba da shan coffee din shi, wata yar karamar mage ya gani tana son tsallaka hanya, ya tashi da sauri ya tsallaka ya tsuguna sai ga wata dattijuwa, ashe itace me magen..idan tana son tsallaka wa sai ta tura yar magenta, murmushi yayi tare da mikawa tsuguwar hannu, ta taso yana tafiya a hankali har suka tsallaka yana rike da magen.        Bayan sun wuce, ya dawo ya zauna, yana kallon Abeel da Mas'ud tare da Hikmi sai murmusawa yaƙe yace. "Da alamu yau kasha yatsu biyar!"       Kurb'an shayin yayi, da bai yi dariya ba, sai yanzun da yake tunawa ya fashe da dariya, kuma dama sun san dabi'ar shi kenan, matukar aka yi maka abu amadadin ya tayaka jin haushi da mita a'a bazai yi ba sai da ya sakoka a gaba yayi ta maka dariya. Wannan dabi'ar bai hana shi idan ya gama ya fashe maka da mugun dariya ba.   Sai yayi sannan ya daure fuskar shi, haka ce ta faru sannan yace. "Gaya min me kake son kayi mata idan na kawo maka ita har dakinka na gidan hutawar mu"    Zaro ido yayi yana mamakin yadda za ayi ya dauko ta. "A'ah ba sai ka daukota ba, kawai abinda nake so ka bata wahala  a cikin makarantar idan kayi min haka shi kenan ka kare min kimata, ka wulakantata daga gobe ka nuna mata izzarka don Allah Jay, don Allah gobe ka mata sanadin da zata shiga matsala a cikin makarantar." .gyara zama yayi sannan ya daura ƙafan shi daya akan daya ya maida hannun shi baya, sannan ya kura mishi ido. "Amma kasan daga wata nahiya tazo, baka ganin tab'a mata kimar karatunta zai shafi rayuwar ahalinta! Jay ka duba magabata, sannan kuma ba mamaki daga ma'aikata, aka turo ta kaga kenan yin haka zai iya tab'a aikinta, kunga ku share wannan batun kawai mu barwa Jay wuka da nama, shi zai iya kome amma kar mu tab'a kimar karatunta, dan dukkanmu nan Abu daya muka ke yi."         Mik'ewa yayi sannan ya ajiye kudin coffen da suka sha, ya wuce gurin wata motar shi tare da d'aga musu, hannu.    Ya shiga bai kuma magana ba, yaja motar yayi tafiyar shi. "Hikmi! Baka da kirki idan kai ne akawa haka ya zaka ji?!"     "Babu abinda zan ji! Sabida kayan makarantar bata muka zubda, kuma a shashin adalci abinda ya dace tayi kenan! Kuma shima ai Jay din ya sani, kunga mu daina aikata kuskure muna ganin dai-dai ne, dan muna da yakinin zai taya mu yaki! Shi din kamar shugaba ne kamata yayi muna bashi kwarin gwiwar...." #MI #HWA #Mai_Dambu.. 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️       Fatan Alkhairi Mommy Sayyid 😍🤣😂 Na gaida Uwar dakin Jay... SHIDA Kun gane mu zame mishi  abokan kwarai, domin kuwa wannan ba adalci bane sanya shi yana aikata kuskuren, idan kuna sashi yana aikata abinda bai dace ba. Ya kuke tunanin idan ya hadu da wanda ya fishi hatsabibanci, Jay Amininmu ne, kuma abokin arziki.     Don Allah kar mu sanya shi yayi kuskuren da zamu yi dana sanin mara Amfani." Daga haka ya mike ya bar gurin. ......      Gudu yake sosai, har ya isa gidan su, tun kafin ya isa aka wangale mishi kofar shiga gidan, yana shiga ya tsaya a inda aka tanadar domin ajiyar motoci, kifa kanshi yayi saman motar, yana sauke ajiyar zuciya.    Cizon bakin shi yayi cikin nutsuwa, yana kuma nazarin abinda zai aikata ga yarinyar nan da taci mutuncin abokin shi.      A hankali ya kai hannu zai bude kofar ya fasa, tunawa da yayi yau ne, zagayowar shekarar Haihuwar Munubiya, tsaki yayi cikin miskilancin ya bude motar, ya fito bayan ya dauki wayar shi da, kuma yar computer shi ta karatu, ya shiga gidan.               Yana tafiya, kamar wani hawainiya, tafiyar anayinta ne, Amma cikin wata irin izza da sadaukata, wanda zaka dauka yakai talatin da wani abu ne, a'a kawai kuruciya, ilimi, kyau da nutsuwa suka sanya shi jin wani irin yanayi na rayuwa, amma akan fusakr shi abu daya zaka shaida!     Shine rashin walwala, wanda kamar dabi'ar shi ce, rashin magana fuskar shi kamar wanda aka zage shi, a hankali ya tura kofar tare da zubawa yan matan da suke falon kyawawan idanun shi, da sauri suka yo kanshi yuuuuu.       Suna zuwa cikin zafin nama ya kauce musu, aikuwa suka zube a gurin har suna gware da juna.     Aikuwa suka shiga fada da juna, akan shi. Shi kam har ya haura sama, a gajiye ya shige dakin shi, ya same ta tsaye hannunta hard'e a kirjinta.          Takowa tayi idanunta jajjur, zata yi magana ya zubar da kayab a saman gado  hannun shi, ya wuce ban daki.    Kuka ta sake mishi, me mugun cin rai. Bai fito ba sai da ya daina jin sautin kukan ta, sannan ya fito tare da fara kimtsa kanshi, yana gyaran jikin shi shigowa tayi tana kallon shi. Bai ce mata kome ba, ya zauna ya saka kayan shi a nutse, tunda yasan ba fita zata yi ba, dan dai wandon shi ban daki ya shiga ya saka sannan ya fito.    Kura mishi ido tayi, sannan ta taso tare da kallon. "Ya Jay! Me yasa baka damu dani bane? Me yasa baka damu da nayi farin ciki ba, kafi kowa sanin kaine muradina. Ya Jay idan kace na baka kaina a shirye nake nayi hakan don Allah. Ko yanzun kace na amince zan baka rayuwata." Riko hannunta yayi sannan ya kawo ta bakin kofar shi, yace. "Ina zuwa!" Ya rufe kofar da karfi, shi bai san me yasa Munah take mishi haka ba, amma sabida Allah me ke a cikin zina, shi da Allah ya daura mishi kyamar ta, shine mata suke mishi tsiya da ita.   Sai da ya gama, shirin da sannan ya fito sanye da wata gajeren wando, iya gwiwar shi. Sai riga mai dogon hannu, da hular (facing cap) a hankali yake saukowa, ya hango mahaifiyar su, sam bai san inda Munah ta dauko wasu mugun hali ba.    Dan yasan Ciki d'aya suka fito, kuma mahaifan su, suna matukar kaunar su, amma tun zuwan Munah biki Damagaran tazo da wata mugun hali, na kafewa sai ya sumbaceta ko ya rungume ta. Wannan kuma duk ba dabi'ar shi bace.           Zuwa yayi ya kwanta a jikin Maman su, ya kafeta da ido.     "Yarona! Ya karatun? Da fatan babu matsala."     Daukar kafar shi yayi ya daura a saman d'an tabirin da aka ajiye dan Kawata falon, narkewa tayi a jikin Maman su, tana me b'are bakinta kamar zata yi kuka, tab'e bakin shi yayi, tare da lumshe idanun shi.        Idan ka gan shi zata rantse barci yake, amma ina idanun shi biyu. "Maam! Don Allah ki cewa, Jay ya kai mu inda za ayi party mana."    "Shiiiiii! Tace mata tare da nuna mata shi alamar tayi shiru zai yi barci, tura baki tayi sannan ta mike tare da buga tabirin ta bar falon, yasan aikinta ne ko bude ido bayi ba, haka ya cigaba da kwanciyar shi.                Sam ya manta da abinda ya faru, kawai barcin shi yake.          ...... Washi gari, da wuri ya iso makarantar, yaje ya tsaya a bakin matakalar da zata kai ni tsagayar mu(wato department kenan kuyi hakuri har yanzun muna daular Hausa ce!😍😍😍 Kuma ina kishin yare na)       Hankalina yayi gaba dan haka bazan iya bada labarin abinda ya faru ba, ko kuma abinda yake gaba na ba, kawai naji kamar ina yawo a tsakanin matakalar ne, kafin na fahimci abinda yake faruwa dani, na fado akan kafana, sai da kashin kafar yace. "Kasssss!" Alamar ya b'alle kenan!  Rintsa idanuna nayi a hankali na bude su, lokacin hawaye sun fara sauka a idanuna.            Dakyar wata yarinya ta taimaka min, na mike yana tsaye a kusada mu yana cin alawar chokulet. Dakyar na mike akan kafana na kuma komawa zan zube ta rike ni, wani irin kuka ne ya kwace min.             Sosai kamar karamar yarinya, nake kukan. "Idan kina da hankali" daga haka ya wuce abinshi asibitin makaranta aka kai ni suka duba kafar tare da min hoto. ..... "Amma Jay baka tab'a b'ata min rai irin na yau ba, haba sai kace ba musulmi ba, ka karya musu yar mutane. Insha Allah sai Allah ya bi mata hakkinta." Inji Hikmi, ."toh munafuki dama kai ka fara yabawa da haduwata dan haka sai kaje can ku karata, Nagode Aminin kwarai.      Kyale wannan banzan Ni dai tunda ka kakkaro min kimata, yanzun zata gane shayi ruwa. Muje yau dole mu sha ruwa."            Kasa hakuri Hikmi yayi yace musu. "Akan me zaku cutar da ita?"        "Kanwar Babarka ce ita? Ko budurwan kace bamu sani?!" Jin Abeel, ran Hikmi ya b'aci ko gaban shi baya gani bai san lokacin da ya wankawa Abeel mari ba, dukkan su sai da suka sha mamaki.    Kallon su yayi cikin zafin rai yace. "Wallahi wani ya kuma zagar min iyayena, sai na dake shi na daki banza, kuma muna nan da ku." Yana fadar haka ya tashi daga inda suke ya dauki jakar shi, cikin kurari, Abeel ya tashi Jay ya mai dashi. Yana murmushi. Amma ran shi a b'ace yake, kamar ana gaza mishi da wuta. "Jay kyale ni!" "Barshi mu gani!" Kallon Jay sauran abokan su, suka yi.       ---- Ni kuwa ina asibiti, ana daura kafar. Hawaye ke zuba daga idanuna,tsabar azaba da nake sha. .ana gama daure min kafar muka fito tare da yarinyar da ta kawo ni, sintiri yake tayi muna fitowa ya karaso inda nake yana tambayana. "Sannun kiyi hakuri!" Ban kula shi, sai dai ya nace min da bi. Naki magana. Har inda aka ajiye motor da zata mai dani gida, tunda na shiga, shima ya shiga tashi har gida ya bini, ina fita ya tawo. "Don Allah kiyi hakuri! Wallahi ba halayyar shi bane, kawai akasin kaddara ce da..." Wani irin kallo ba mishi da jajjayen Idanuna, bai karasa maganar ba yayi wucewar shi.          Komawa makarantar yayi, ran shi na kara b'aci,Koda ya nufi ajin su an fara karatu. Dakyar aka bude mishi ya shiga. D'aga nesa ya hango Jay tsakiyar yan mata kowacce so take ta tab'a mishi jiki amma yadda ya had'e fuska sai suka kasa yin komai,.          Bayan an tashi a makarantar, kowa yayi wucewar shi, dan Hikmi mahaifin shi dan kasar Lebanon ne, kuma likita ne.             Dan haka a guje ya bar makarantar, ya kuma dawowa unguwar mu, ya gama zaman shi, ya rasa yadda zai shigo gidan.           Da dare, suna yawan zuwa gidan mashaya (wato club) wannan zuwan babu Hikmi, duk da basha kome suke ba, amma akwai bala'in son yan mata, dan haka tunda Jay ya zauna yake kallon kofin gaban shi, da Abeel da Asood suke shan barasa, kallon inda Hikmi yake zama yayi sannan ya tauna lebben shi ya kauda kanshi gefe.    Yana jin d'aci a ran shi, tunda yake bai tab'a kawowa akwai ranar da mace zata iya shiga tsakanin  amintar su ba, sai yau.           Kamar yayi ta faɗa yake ji, amma ba zai iya ba, a ran shi yana jin dole ya gyara musu zama, daga wancan me shegen tsayi kamar sallar dare nan.              Haka yan mata suka yi ta rawa a gaban shi, bai saka ya d'ago kai ya kalle su ba, karshe mik'ewa yayi ya mika musu kudin abinda suka sha, sannan ya nufi hanyar fita, Abeel da Asood suka biyo shi suna maye, koda suka shiga motar shi dake bai sha ba, sai sune suke ta tanb'le, har suka isa gida.             Ajiye kowanne su yayi sannan ya nufi gida, kamar yadda ya sab'a ya samu, Abbi a falo yana jiran shi, a hankali ya shiga falon, ba tare da yayi magana ba, yayi wucce sama. "Mujaheed!  Meke damunka? Ba haka ka saba dawowa ba meke faruwa?"      Cizon bakin yayi da karfi idan ya tuna ta sanadin wancan Yarinyar abokin su yayi fushi dasu, sai yaji ran shi ya kuma b'aci, dukar hannun matakalar yayi tare da cewa. "Babu!" Ya haura da sauri ya wuce dakin shi. Ban daki ya shiga, yayi wanka sannan ya dawo ya saka kayan shi ya gabatar da sallar shafa'i da wutiri,   Yana zaune ya haɗa kanshi da katakon gadon, yana nazarin abinda zai mata ya more.    Mujaheed wanda suke kira Jay! Iyayen shi yan kasar Damagaran ne ta kasar Nijar, amma mahaifiyar shi, yar Sarkin Maraɗi ce, Jay suka fara haifa, sai Kanwar shi mai suna Munibah, sannan Babban malamin jami'ar,  Malam Harisoun Agla suna da sarautar a Damagaran suma.       Jay matashi ne da yake masifar ji da kanshi, yana da tausayi da hakuri, amma a zahirance idan baya yinka,(🙄🤦🏽‍♀️🙆🏽‍♀️? ) ka shiga uku, domin mugune na bugawa a jarida, bai da mutunci ga girman kan Bala'i, sannan uwa uba miskili ne da bai cika dogon magana ba.        Maganar shi bata huce kalmomi biyar zuwa shida, ya taso da mugun bakin hali, na rashin magana da daukar fansa, sannan idan zai yi abu baya sauraron kowa sai kanshi.                 Abinda ya tsana a rayuwar shi, kan abokan shi ya rabu, a take zaka  ga tashin hankalin shi. Dukda yasan  Hikmi yafi su gaskiya amma bazai tab'a bude baki ya bashi hakuri ba, ya gwammace, suyi ta wannan abin, kuma yasan abinda zai yi Hikmi ya dawo gare shi. #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️   Godiya nake Yan team din Jay🙄🤦🏽‍♀️🙆🏽‍♀️? toh bari mu gani yadda wasan zata kayya.... BAKWAI Ya kuma san cewa, tunda Hikmi yayi fushi dasu, dakyar ya dawo gare su, dan haka ya fara tanadin yadda zai dawo gare shi, amma dole sai ya tsaya yaga yadda zasu kaya da yarinyar.            ...... Tafiya yake a cikin duhu, yaji an rike mishi hannu, a hankali tace mishi. "Muje na isar da sakon da na kasa, bana son yadda kake rayuwarka! Kaji."     Bude wata kofa akayi yi haske ya cika mishi ido, firgi ya mike tare da ganin Na'am tana d'aga labulen d'akin shi. "Bakwai saura kwata, shi yasa nace ka bar zuwa wayon dare amma dake kunnen kashi gare ka gashi ka rasa sallar asuba, tashi kayi sallah."          Ban daki ya shiga yayi wanka da alola, sannan ya fito daga ban dakin jallabiyar ya saka ruwan madara da hularta, ya shimfid'a abin sallah ya fara gabatar da sallar.      Yana idarwa ya mike, kamar ba zai shiga makarantar ba, ya kuma shirya cikin kananun kaya ya dauki jakar shi ya tsaya gaban madubi ya gyara gashin kan shi, sosai sannan ya sauko.     Kallon Muniba yayi sannan ya kauda kanshi, ya ja kujera ya zauna. "Amma ya dace zaman gida?" " Ai gwara kayi mata magana na rasa gane kanta, tace ita bazata bai sai ka daina kula yan mata." Kura mata ido yayi sannan ya sauke wata irin murmushi me tattare da miskilancin, sannan ya ɗan dibi abincin shi ya fara ci a hankali yana yi yana kallon agogon hannun shi.    Yana gamawa ya mike, sannan yace. "Indai akan yan mata ne!" Fita yayi har ya kai bakin kofar fita ya saka madubin shi yace. " Sai hakuri." Daga haka ya gyara zaman jakar shi yayi ficcewar shi daga gidan.        --- Fadar da Abban Ablah da kuma Umma Fouzan suka min kamar nice na karya kaina da gangan, dan haka nayi kuka kamar idanuna zai fita, daukar takardun asibitin yayi yana dubawa yaga ashe tsagewan kashi ce, ba karaya ba.    Ajiyar zuciya yayi sannan ya kuma ajiye ya fita, washi gari ina zaune Umma Fouzan ta kawo min wani kwando cike da fulawa tare da wasu takardun gaisuwa tare da ban hakuri akan abinda ya faru. Sai wasu kayan zaki.    Yadda ta kafe ni da ido ya sani kauda kai nace mata. "Ban san shi ba, ki ajiye a inda ya kawo!" Na cigaba da abinda nake.        ---- Hmm! Yaron ya takura min sosai, har takai ya shigo cikin gidan, sabida kawai ya bani Hakuri abinda abokin shi yayi min, sai da Umma Fouzan tayi min fada, sannan nake kula shi.      Tun daga ranar, yana tasowa zai tafi makaranta zai biyo ya duba ni, idan kuma ya taso ma haka zai biyo duba ni.    Har  na cika kwana sha biyar, da dauri, shi yazo ya kawo ni aka warware min suka duba ya had'e kashin.  Daga nan na tako har ajin mu, Barka yan ajin suka min, nayi godiya dake duk zaman da nayi, a gidan nan shi a banza ba. Muna karatu musamman Ni da bana makarantar, ta online Class.              ......  Hango d'an iskan yaron nan nayi, yana ajiye motar shi, addu'a nake Allah yasa nazo da wani abu me tsini, duba jakar nayi naga babu wani abu me tsine, har zan rufe sai naga ashe akwai yar roban kayan karafunan lissafi, budewa nayi na dauki Abinda zan dauka ina murna, ina maida jakar agogona yana faduwa kasa, dauka nayi dai-dai fitar malamin na fita da sauri ina gyara zaman agogona, ashe bai zauna ba, da sauri nake sauka, na shiga ts tsakanin motocin da suke gurin, ina zuwa gurin motar shi, na kace tayar gaba.       Take yayi wani fitar da iska, na kuma komawa gefe na cake tayar gefen, ina gamawa na juya zan tafi, muka yi tawo mu gama dashi, karfen da agogona suka zube na juya da sauri na bar gurin, zuciyata na wata irin bugawa, na tsoro. Bai fahimci abinda nayi mishi ba, sai dai ya dauke karfen da agogona yana juyawa, cike da mamaki.                        Ganin motar ya sauka kasa ce yasa shi fahimtar, abinda na aikata mishi daukar agogon yayi ya saka a cikin aljuhun shi, tare da dukar motar da hannun shi, ran shi na kara b'aci. Idan dalibai suka san abinda ya faru da shi, tabbas zasu mishi dariya, dan haka. A fusace ya nufi ajin mu.      Tunda ya shigo naga yadda idanun shi, suka kad'a jajjur har jini na kwantawa akai ya sani kauda kaina cikin tsoro. Ina shiga ajin naga babu agogona, kafin nayi wani yunkuri na hango shi yana tawowa.   A hankali yake takowa har zuwa inda nake, ya dafa hannun shi akan tabirin da nake yace. "Kin shirya?!" Banza nayi da shi, kawai yasa kai zai fita, kawai yace. "Toh bismillah!"           Daga haka ya fita, ban damu ba, kawai dai naji a raina bai da mutunci kuma zai iya kuma min abinda yayi ranar, shi yasa da aka tashi nazo fita na kiyayye fita da sauri.      Duk yadda nasaka rai zai min abu bayi ba, sai ma shirin da muke da Hikmi, take rashin ya kuma b'aci, dan haka ya shiga hada mana abinda zai rabamu.       ..... Bayan sati biyu. Na fito da sauri zan, isa inda muke haduwa da Hikmi domin yaron yana da ilimi sosai, sai naga baya gurin, dan haka na juya zan koma aji. Kawai naji yan mata suna ta min dariya ban damu ba, sai da wata tace min. "Amma gaskiya kina da jiki me kyau." Kallonta nayi, dariya suka saka sannan ta mika min wayar hannunta, tare da sanya min magudanar kallon, a hankali ya fara tafiya, Hotona ne gani a gaban wani Bature yana shafa jikina, a tsorace na sake wayar ya fadi kasa.        Ji nayi kamar bazan iya daukar kaina ba, na zube kamar danyen nama a kan ciyawar da take gurin, kuka yaki zuwa min, kawai na mike ban tsaya ba, sai a filin da suke buga kwallon kwando, basa gurin suna cikin makaranta dake guda biyu ne, ina shiga gurin na same su da Hikmi, sai fada suke shida Abeel babban shaidanun yana zaune. Asood da Bilal suna raba su, ina zuwa na same shi yana fadin. "Idan yar uwanka aka tozarta zaku ji dadi? Insha Allah sai kunyi dana sanin abinda kuka aikata, haba don Allah."      "Muje Hikmi! Na Barsu da Allah."           Juyawar da zanyi naga abu ya fado daga aljuhun wandon shi, kallon abin nayi da ido, naga an rubuta,(Golder ring condom) wani irin kuka ne ya kwace min, lokacin da na fahimci, sun rufe kofar da na biyo, shi kuma sun saka shi a tsakiyar su suna mishi dariya. "Ai mun gode maka, gashi nan ta yarda da kai, kai kuma kayi sanadin kawo mana ita. Jay gaya mana ya zamu yi da ita?;"         "Ku barsu su tafi!" Saukowa yayi sannan ya tako zuwa gabana, yana kallon yadda nake kuka me mugun ciwo, ya amshi jakata ya ciro wayata, ya mika min yana murmushi yace. "Ya kika ga wasan? Hmm" daga haka ya juya ya fita, raina ya b'aci dan haka na fita da sauri,  ina isa inda ya ajiye motar shi na dauki wata sandar da naga ni na buga a jikin gilashin motar sai da ta fashe.           Bai kalle ni ba, na tsaya a gaban shi, ina mishi kallon kaskanci. "Idan ka fasa daukata tsirara ka rena Iyayen ka, banza wanda bai san darajar mutane ba, wawan Yaro kawai kai har ka isa ka tozartani? Wallahi baka isa ba, kuma ni da kai shege ka fasa."      Daga nan na wuce abuna, tun daga ranar bamu kuma, yin wata rigima ba, dan hoton ya zaga makarantar mu.    Har takai malamai sun min caaa, aka kirani zuwa ofishin shugaban makarantar, koda na shiga na same su. Kallona suka yi na sanan suka shiga tambayana, abinda ya faru. Ban boye musu ba, Jay da abokan shi suka min haka, sannan Ni ba jikina bane fuskata aka dauka, dan haka suka kira Jay, ai kuwa yana zuwa, ya tsaya suna tambayar shi, yace shi yayi kuma bashi bane Abeel ne, kallon shi Mahaifin shi yayi cikin damuwa dan yasan zasu dakatar dashi na kwanaki ne. . Aikuwa haka ce ta faru aka bani hakuri na fita, bayan na tafiya suka mishi fada sosai.      ...... Wata guda suka dakatar dashi, amma yana karatun shi, a (online) haka da ya faru ya dawo min da kimata, dan haka na fita hanyar kowa, shima kuma Hikmi na rabu dashi dama shige min yayi muke karatu tare.             ...... Na mai da hankalina sosai kai karatu, dan haka koda ya dawo, bana shiga harkan kowa, sai dai wannan karon ya dawo da zafi ne.     Abinda ya fara min, shine sanyawa malamai suna hanani shiga ajin su, karshe na kuma zuwa gaban mahaifin shi, aka shiga tsakanin mu, amma bai hakura ba. ..... Haka zasu saka hotona, suyi b'atanci akaina, ban kuma magana ba, sai ma kauda kan da nayi, abin yana damuwa.          Watanni uku muka fara jarabawar zango na farko, aikuwa zance Alhamdulillah. Sai dai ranar da zamu gama jarabawa aka wurgo min, da takardan satan amsa, kawai akan idanun me kula da jarabawar.     Duk yadda naso dakatar da kar a soke min jarabWata, sai da aka yi, nayi kuka kamar idanuna zai fita. Shi kan sa da yaga yadda na rikice ina basu hakuri sai da jikin shi yayi mugun sanyi, zuwa gaban shi nayi nace mishi. "Hankalinka ya kwanta? Ka rama abinda nayi maka, toh nagode sosai, amma ka sani wallahi sai na rama."           Daga haka nayi wuccewa ta, zan koma gida, Hikmi ya biyo ni. "Khatoon! Insha Allah bazasu soke miki jarabawarki ba, kiyi hakuri na dame su, kuma anyi abinda ya dace. Ga abubuwan ki da suka kwace, don Allah karki lukace Jay wallahi sanya shi suke"     "Ai shi ba mahaukaci bane! Yasan me yake yi, dan haka yaje yà cigaba da cewa yake yi." Raina ya sosu, shi yasa amshi kayana, na nufi gida. Koda za ayi hutun kin zuwa nayi, suka gama shirya min mugunta suka ga banzo ba.      ....... Hutun sati Uku aka bamu, koda muka koma, naja girma na, sosai. Na kuma kin shiga harkokin kowa sai na karatuna.            Lokacin da muka dawo mun kuma maida hankali sosai gurin karatu kasancewar, wannan lokacin akwai abubuwa da yawa, shi yasa muka mai da hankali sosai, ranar mun fita dakin gwajin kimiyya, muka hadu dasu Hikmi tare zamu yi dasu.      Ban san ya akayi ba, dai ji nayi an tab'a bayana, ga kuma Jay a gefena fuskar shi a hade, kawai ina juyawa na kifa mishi mari..... #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ TAKWAS Daukar marin dakin yayi, shi kan shi a firgice ya kalle ni, cikin mamaki da al'ajabi, na mare shi, yadda kowa ya juya ana jiran aji abinda zai ce ko zance na bude baki zanyi magana yace. "Dalla ki min shiru, na gaya miki dole ne? Ki rabu dani kinki? Toh ya zan baki mamaki." ...sake baki nayi ina kallon shi, ya fincikoni muka fita, can inda ake ajiye aladun da ake gwajin kimiyya dasu ya kai ni cikin turb'ayan su ya jefa ni cikin su, wani irin tashin hankalin na tsinci kaina a ciki. Ya kasa magana sai huci yake, sannan ya juya ya barni a gurin,  da sauri Hikmi yazo ya rasa me zai min, inda ake ajiye mesan makaranta na gudun karta Kwana ya dauko tare da bude ruwan, da yazo da karfi yana watsa min.       Sunkuyar da kaina nayi, cikin bakin ciki da damuwa, wannan shine karo na biyu da aka watsa ni cikin kazamtar dabbobi. Dole na dakatar da haka kar a kuma yin na uku.             Kayana ya jike jagab, a hankali nake takawa, duk inda na gifta sai an bini da ido, sabida kyan surar jikina, tare da zubin halittar da Allah yayi min, dayawan mutane da suke ganin na cikin dogayen riguna, sun sauka rigar ce take rufa min asiri, basu san nice nake son boye baiwar da Allah yayi min ba,             Mika min Wata babban rigar sanyi Hikmi yayi na amsa, hawaye na zubo min, na rufe jikina saboda irin kallon da kowa ke min.       Karshe shi ya kawo ni gida, har zan sauka yace min. "Khatoon! Don Allah kiyi hakuri! Wallahi bashit bane, Asood ne yayi miki hak5ra, amma ko Alkur'ani aka bani zan dafa! Jay bai da dabi'un tab'a  mata. Mace bata cikin rayuwar shi,        Kuma da zaki bi, duk abinda yake miki zaki samu ba wai dan ke dashi bane, abokan shi yake tsayawa,              Kiyi hakuri! Abin da zance domin nasan waye Jay meye dabi'ar shi, Allah ya baki hakuri." Share kwalla da suke tsiyaya a idanuna nayi, sannan na juya na kalle kofar fita nace mishi. "Ni ba yarinya bace! Ƙaddarar rayuwa ya kawo ni nan, badan na rasa mazajena ba, babu abinda zai kawo ni, kuma na fahimci yarinta yana samun shi. Shi yasa yake min abinda ya gadama, amma ba damuwa na barshi ya cigaba da abinda yake min."    "Kayi hakuri mana, a duniya Jay ya tsani a tozarta shi a cikin mutane! Kinga kenan ba laifin shi bane, dan ya wurgaki cikin datti, ki fahimci wani abu daya, shi kimar shi yake karewa. Da ki tab'a mishi kimar shi a gaban mutane gwara ki mishi kome a bayan idanun mutane."                  Sauka nayi a motar kawai, sabida raina zai cigaba da ɓaci ne a banzan. ..... Karshe haka Hikmi ya tafi tunda baki fahimtar kome.           A makarantar ma, karshe d'aga abin da zamu yi aka yi sannan aka raba mana kwanakin da zamu yi.                  ---- A hankali rayuwa take tafiya ban kuma shiga harkokin yaran ba. Na zuba musu ido, ina kallon futsarar da suke aikatawa. Kuma ba a tab'a taka musu birki ba.        A dan rigimar da muka yi da shi na fahimci yana da mugun naci,karku ce nacin da zaka kyale abu a'a na shi kamar halitta ce.           Sai dai samun lafiyata shine rabuwa da nayi da rigima dashi, ita ta sama min nutsuwa na mai da hankali akan abin da, yake hada mu.      ...... Ban san me ya faru ba, ranar na shigo makarantar, kawai d'aya daga cikin abokan shi ya tare ni, tare da kewaya ni, da keken shi. Shi kuma yana can  ajin su, daga can yake kallon mu, zan wuce yaron yasha gabana.     "Bana son fitina! Ka bani hanya na wuce!"           Wuce shi nayi, tare da barin shi a gurin dan yana amsa Waya ce.           Ban kuma haduwa da irin haka ba, sai dai tsakanina da Jay, rigimar mu ta zafaffa, domin sun bani haushi na kai ƙarar su gurin shugaban makarantar, haka yayi masifar b'ata mishi rai, da zan koma gida yabi motar da na hau, ya tsayar damu, tare da bude kofar ya fidda ni, da karfin tsiya.     Ya mai dani cikin motar shi, sannan yaja da gudu muka bar titin. "Dalla malam ka sauke ni! Wallahi idan baka rabu dani ba, sai na maka abinda baka zata ba."        Bai kula ni ba, sai dai ya kai ni,can wata tsohuwar makabarta, ya fito tare da fincikoni waje, ya wurga a can gefe. Kasa magana yayi yana motar shi ya barni a gurin, mik'ewa nayi na bar gurin dakyar na sami abin hawan da zai  mai dani gida.       --- Washi gari! Ina shiga makarantar, na fasa mishi tayar motar shi na bar gurin, yana zuwa ya gani ina zaune ya shigo zai min hauka Malamin da yake ajin ya kore shi, har zai fita muka kalli juna gwalo nayi mishi,  juyawa yayi tare da dukar Kofar sai da na razana.       Murmushin ban haushi na mishi, tun daga ranar malamin ya saka aka shiga tsakanin mu, domin na gaya mishi irin abinda yake min, aikuwa malamai da dama sunki bada goyan baya sai daga baya, ni kuma nayi amfani da wannan damar, nayi ta mishi tsiya iri iri, wanda ya sashi kasa hakuri ya fito da halin shi yana hauka a makarantar.      Sau biyu ana dakatar dashi a kaina, na uku ne suka ce mishi Tabbas koran shi zasu yi, abinda ya masifar d'aga mishi hankali kenan, kawai ya zubda hawayen bakin ciki.      ---- Shekara daya muna wannan yanayin, kawai ina cikin makarantar su Baabi suka zo, kai murna kaman zanyi kuka.     Tunda na fito nake fad'adda murmushina, suna zaune nazo na wuce su. Ina zuwa na rungume Baabi tare da kanena, ina murmushi. " Addah Aanih! Kinga yadda kika koma kuwa! Su Ummi na gida kizo muje."     "Kai Hanisah yanzun zan dawo, muna karatu ne! Baabina ina kewarki, kuje zan dawo yanzun nan!"      Shigowar sako a wayata ya sani, duba wayar.               *_Ya zaki ji idan na sakewa wannan tsohon vedion nan ki duba na turo miki ta Whatsp_*      A tsorace na duba vedion bayan na koma gefe, hoton b'atanci be suka yi min, d'ago kai na nayi, tare da kafe shi da ido.       Sako ne ya kuma shigowa, *_Karki damu zan zo na rungume ki a gaban shi haka zai fi sauki_*     A birkice na tura mishi. *_Toh me zan maka?!_*       _Dukkan mu abu daya muke son karewa kimar mu! Dan haka kika sake yau kika zauna a cikin mutane zan baki mamaki ki tawo inda nake ajiye motana._      _Me zaka min da zanzo_ _Abin da mace da namiji suke idan sun hadu mana_       _Tir_ Raka su Baabi nayi, sannan na dawo aji.    Bayan mun gama darasi ya kuma turo min sakon. _Idan baki zo ba!_ _Ka kashe ni!" Ko a gidan Uban waye ya sami Number ta, hankalina yana gida, tunda na shiga na manta da kome na kashe wayar baki daya.     Tunda muka fita da kanena muke yawo, muyi ciye ciye. Da wasu abubuwan dan washi gari zasu koma.         Wata Mall muka shiga muna sayayya, naji kamar ana kallona, juyawa nayi kawai idanuna ya sauka akan nashi, tsaki nayi tare da cigaba da abinda nake yi.     Har zai tafi kawai ya tako har gefena, tare da ɗaukar wani, kwalin pant, ya bude sannan ya zazzage shi. "Ina kallon mace kamar yadda nake!"     Barin gurin shi nayi da sauri, haka ya zame min kamar karfen.      Cigaba da abinda ya kawo mu, shagon nayi har Hanisah tana min tsiya wai kamar ban waye ba, gani cikin turawa amma ina gidadancin irinta mutanen da. Murmushi nayi, tare da kai hannuna zan dauki kwalbar turare naji hannun shi akan nawa, a razane na cire tare da yarfe hannun, kamar na tab'a wuta. Kafin na juya har ya bar gurin mu, sako ya turo min. _Kamar yadda kika shirya fada dani haka nima sai shirya yadda zan lalata miki suna da hujjar ki!_     Na rasa yadda zanyi da Jay, domin ya dauki marin da nayi mishi da girma, dan haka a cikin satin kamar nayi hauka, domin burin shi ya haɗa ni da iyayena, Ni kuma nak'i biye mishi har suka tafi.                Sau uku yana hada min rikici, a makarantar Allah yana fidda Ni, na karshe ne ya hada min rikicin da aka kusan korana a makarantar, domin sai da Abban Ablah yaje makarantar. naji mugun tsoro.    ...sannan ya kuma sanya aka sani na bashi hakuri a gaban kowa da kowa, na yarda Jay fitinanne ne,.tun daga ranar Allah ya zuba min shakkar shi bawai dan yafi karfina ko yafi karfin Ubangiji ba, sai dai gaba ki daya, takardana nake tsoron kar yaja min sanadiyyar da zasu kore ni.        Babu ranar da zan shiga makarantar, ban dawo da bakin cikin Jay ba. Sai da ta kai ina tanka mishi muna fada sosai, mutumin da baya magana sai gashi sosai yake iya jin haushin idan na gaya mishi magana, musamman da nake ce mishi Gata tayi kishi yawa, shi yasa yake abinda ya gadama, kuma bai yi dace iyaye na gari ba.        Gashi ni da na dace da iyayen kwarai, burina na gama dasu lafiya. Wannan lokacin kamar yayi hauka, karshe aka gayawa Kanwar shi, ban san tana cikin makarantar.ba, sai ranar ina, karatu a kasar bishiya tazo.    "Ke! Naji ance kece kike bibiyar dan uwana toh ahir dinki, wallahi na kuma ganin ki dashi, sai na ɓatar dake." ..."ina da abinyi idan kin gama zan wuce! Idan kuma baki gama ba, zan tsaya ko gama."       ---- Bayan shekara daya Abin haushi haka zan ga Jay suna tsokanata bani da ikon ramawa, kawai muna cikin wannan yanayin ne, wasu da ba san suwaye ba, ba suka yiwa wata yarinya fyade. Tashin hankali garin bincike tace har dashi.               Abin ya faru bayan mun tashi mun fita,. ita kuma tana matakin degree, an fita an barta a cikin aji, tana wasu abubuwan ta, tana d'agowa tagansu..shine suka afka mata abin tausayi suka lalata rayuwarta baki daya, sakamakon kiran sunan Jay aka dakatar dashi, inda aka shiga bincike.      Muna tsaka da karatu, aka mishi wannan abin bai bani tausayi ba, sai ma murmushi da nayi dan haka yayi min kyau da dad'i, kamar zai yi hauka..dan haka ya sa aka kira mishi Abeel, aka shiga tambayar shi, dakyar ya bude baki yayi magana tare da gaya musu gaskiya,, shi da Asood ne, suka yi haka tare da wasu abokan shi.          Dan haka yan sanda suka tafi da shi,ba tare da sun kuma jin ta bakin shi ba. #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ TARA.    Wannan abin da ya faru ya sanya shi,. shiga hankalin shi da mutane, karshe dai ya rasa inda zai huce fushinsa sai a kaina, ban damu ba. Sabida Ni nasan abin da nake shirya mishi. .......... Muniba ta kan zo har gabana ta fessa min rashin mutunci,bata gabana balle ya dame ni, sabida kusan sa'ar kanina Abdul ne. .... Dan ko ina tsammani Hanisah ta girmeta. Muna gab kammala karatun, muka hadu da Dr Hanash Maisara, kamar da wasa muka fara gaisawa,      Dukda shi din dan kasar Pakistan ne, amma yana da matukar mutuncin, da sani ya kamata.     .. sosai muke dasawa dashi, a hankali d'asawar ya koma soyayya,.tun daga ranar da ya rufta yana sona. ...na shiga mugun mafarki akan shi, abinda ya sani. Amma a hakan ban fasa jin shi a raina ba. ....."Fatimah Khatoon! Har yanzun baki bani damar nayi magana da iyayen ki ba."       Ya kafe ni da idanun shi, manyan nan, kasa nayi da kaina, sannan na d'ago zan yi mishi magana sako ya shigo min.       _Lallai! Toh kin zata fadar mu ya kare ne? Bari nazo na kori wannan farin fatar da yake rud'arki_ ....a hankali na d'ago kaina na sauke shi a kan shi, yana shan coffee. Takaicin shi ne ya kamani, ina kallon shi ya mike ya bar gurin,          Bayan tafiyar shi, muka cigaba da hirar mu, dan ni wallahi na manta da shi.       .... Shakuwar da muka yi, tayi Yawwa, domin ba karamin burge kowa muke ba, kwatsam muka fara karatun yamma, idan na shigo makarantar sai dare nake fita.          Bani daya ba, hatta sauran daliban haka muke, yau mun taso ana ruwa, dan haka na fito da sauri. Dan lungun da ban san dashi ba, kawai naji an fincikoni tare da toshe min bakina, ya saka hannun shi a bakin shi. "Shiii!"          A tsorace ya zuba mishi ido, kawai sai ga su Asood, da gudu suna nima na, kamar zasu yi hauka, ashe sun zauna sun tsara yadda zasu min rashin mutunci ne, shi kuma yazo ya tare ni.       Matse ni yayi ko nace, mun matsu a lungun gashi ruwa hana jika mu, kuma zan iya cewa jikina da nashi yayi matukar haɗuwa a guri guda, a hankali na janye daga jikin shi na koma gefe, bayan tafiyar su muka fito.    Motar shi ya kaini, na mishi wani mugun kallo na nufi bakin hanya. Ina fita cikin makarantar na tsaya ina jiran motar haya, zuwa yayi ya tare da tsayawa a gaba na.     Sauke gilashin motar yayi,  tare da bude motar na kauda kaina tare da tare wani motar, shi kan shi, ya sha mamaki na, yadda naki shiga motar shi. Bayan taimakona yake son yayi.     Daga Ni har shi babu wanda yake jin a ran shi zai iyawa wani magana. Sabida kowa ji da kan shi yake.         Rufe kofar yayi tare da cilla kan motar shi zuwa gida.           --- Da sauri na fito, zan wuce Muniba ta tsare ni, Yarinyar Bata da kunya, ko nace bata jin magana, gata masifaffiya ce, kowa yasan halin ta, ashe ta bakin fita makarantar, Jay na murnan zagayowar shekarar Haihuwar shine shima, ina zuwa hango Cake din da aka yi shi da wasu abubuwan masu kyau an rubuta 27. Murmushi nayi, dan na fahimci da yarinta akan shi muka yi ta abin kunya.   Wuce su nayi, har na kusan fita wata yarinya kawar Munih tace. "Kee! Zo mu Baki cake Dan yay murna muke." Ban bi ta kansu ba, na cigaba da abinda yake gabana            ---- Tun daga wannan ranar, ya daina shiga hidima ta, nima kuma ban damu dashi ba.          Yawan mafarkan da nake da Dr Hanash ya sani rabuwa dashi babu shiri. Na mai da hankali na, kan karatun da ya kawo ni, tare da taimakon Hikmi na samu damar sanin abinda Jay baya so.     A shekara na biyu, Baabi ya kawo min magani daga gida, yace na fara amfani dashi anyi min miji, sam Banji daɗin haka ba, amma kuma babu abinda zan iya mishi.   Bayan tafiyar shi nayi amfani da maganin kuma naji dadin shi. Bayan wata shida da tafiyar shi.      Sai ga Ikrama, tunda yazo wallahi bana son shi asalima naki bashi damar da zai gayawa min yana sona, sam bai min ba, kuma Bama zai tab'a min ba. ..... domin raina bai min zan iya auren shi ba, haka yazo ya gama kwanakin shi yayi tafiyar shi, daga nan na maida hankali gurin jarabawar mu da tarage saura wata shida. ....... A iya wannan lokacin na mai da hankali na,.kan karatu. Tsakanina da Jay sai ido tunda ba shiga al'amuran juna muke ba.   .....a sannu sannu sai gashi nan har mun kammala jarabawar mu na karshe aka kuma saka ranar da zasu sallame mu, wanda yayi dai-dai da ranar zan bar kasar dan haka na gama shirya kudirina,.kome na yana tafiya dai-dai. ..... Ranar da aka shirya sallamar mu, dake gagarumin bikin aka shirya mana, dan haka a bangarena na shiryawa Jay gagarumin kyauta, muna gama amsar kyautattunakar da aka bamu, naje na taro motar da zata kaini gida a cikin yan mintuna, na gama kome, ana kiran shi a matsayin dalilin da yafi kowani dalibi hazaka. Da kome sai da ya haɗa mugu kawai.       Ya fita cikin shigar Alfarma, yana taki d'ai-d'ai, nima kuma na kutso ta cikin mutane, na nufi inda ya amshi kyautar da aka bashi, yana sake murmushin nasarar da ya samu. .... Ina zuwa ba tare da nayi wata magana ba, na tsinka mishi mari. Hatta su Umma Fouzan, sai da suka tsorata, na kuma sake mishi mari, amadadin ya b'ata rai samu murmushin da ya sake, na kai hannu zan kuma marin shi, ya riko hannuna tare da murda ni ya rungume ni ta baya, sannan ya saka baki shi a amsakuwar ya fata magana yace. "Ina me farin cikin sanar muku, Nida Fatima Muh'd Aaryaan! Zamu koma ƙasar su domin samun damar auren juna."   Abinda ban kawo ba shi yaron yayi min, tare da sake ni Nan aka shiga tafa mishi, amma a zuciyar shi ta fasa yake, kawai ya danne damuwar ce dan kar aga ya sare.         Bayan mun nufi gida, Umma Fouzan da Abban Ablah, suka yi ta min faɗa, ban ce musu kome ba, kayana na kwashe na nufi tashar jirgin sama, tunda haka muka yi da Baabi, ranar da na gama kar na kuma zama na dawo gida,     Domin shirin bikina, da Ikrama.             ---- Tunda bar makarantar, a haukace ya ke gudu, hawaye na zuba mishi, tare da dukar motar shi kamar wanda yayi Mishi laifi.   Yana shiga dakin shi, ban daki ya shiga tare da sakewa kanshi ruwa, yana yi yana zubda kwalla, sabida ba a tab'a mishi haka ba, ba a tab'a dukar shi ba, yau sai gashi a cikin mutane an karya mishi zuciyar shi. Yayi kukan da bai tab'a yi ba, ya kuma yi alkawarin sai ya lalatawa Fatima Muh'd Aaryaan rayuwarta, sai ya b'ata mata sunan ta.    Sai yayi sanadin da ta zubda kwalla a rayuwar ta.    Da wannan ya shiga nima ita din yar wata ƙasa ce, karshe Hikmi ya kira ya tambaye shi, shiru Hikmi yayi sannan yace. "Ta tab'a gaya min cewa babban Sarkin Sokoto ne! Amma ban tambayeta a wata kasa yake ba wallahi!" Kashe wayar yayi, sannan ya dauko laptop din shi, tare da saka sokoto a yanar Gizo, sai gashi ya bashi a kasar da take, ya kuma duba Sarkin Sokoton, naushi ya kai da hannun shi dayan ya kura mata ido, sabida yaga hoton su da yan uwanta.      Tare da kuma haifinta. Sai katin bikinta da za'a yi, nan da sati biyu. Murmushi yayi sannan ya mike ya fara hada kayan shi, ba tare da ya gaya musu inda zai je ba, ya ajiye musu wasikar yayi tafiya zuwa Nijar.      A ranar shima ya bar Calgary, ya nufi kasar nijar.    ......   Tunda na iso sokoto, ake hidima da ni, daga wannan zuwa wannan. Abinci kuwa naci har na koshi, sannan na nufi d'akina da Hanisah ta gyara min tsaf, nayi wanka na kwanta huta gajiya.   Dake nasan ban aikata dai-dai ba, sai gani ina mafarkin Jay yana fada min Insha Allah sai yazo ya dauki fansar abinda nayi mishi.        ---- Tunda aka fara shirin bikina, na samu wani abokin karatuna, Aansar, na biya shi akan yazo ya sace ni.     Nasan idan aka sace ni, Baabi zai iya dakatar da auren, amma ban tab'a kawowa Jay zai iya zuwa a lokacin ba. ......... Mu dawo labarin.   Ihu na kwala tare da kiran sunan shi, amma ina ko ƙurar shi ban kuma gani ba, sai tashin iskar hamada, da take saman saharar, kame jikina nayi tare da fashewa da kuka, ina danasanin mara amfani kan abinda nayi Mishi.               Kin d'agowa nai, sabida mugun tsoron da ya kamani, ina ma da zan mutu da wannan wulakancin da Jay yayi min. Kuka na cigaba da yi.   ..... Gudu yake kamar zai tashi sama, amma baya jin zai iya barinta a cikin wannan yanayin, sake dukar kan motar yayi, tare da d'aga wata irin ƙura, ya juyo. Idanun shi na fitar da wasu irin jini akwance cikin idanu.         Tun daga nesa ya hango yadda na dunkule kaina a cikin cinyoyina, kamar zai take ni ya kuma juya tare da sake motar yana kallon Yadda na kara k'amk'ame jikina,              Bude motar yayi tare da fitowa, ya tawo gabana kamar bazai magana ba yace. "Tashi!"   Jikina na rawa na mik'e, kallon yadda nake kame jikina yayi, yaga yadda nake kokarin kare kimata, yace. "Duk wannan aikin banza ne!" Takowa yayi gabana sosai, kamar zai shige jikina, yana kallon fuskana da take sunkuye d'ago shi yayi sannan ya kalli cikin idanuna, da sauri na rufe. "Bude min idanunki munafuka!" Naji ciwon abinda ya kirani dashi, amma dake ina hannun shi bani da abinda zan iya yi dan kare rayuwata, ko kaina. "Kin hada baki da abokinki! Yaje ya sace ki domin a fasa aurenki! Ni kuma na dauko ki domin na lalata miki sunanki da duniyarki, a yanzun haka kowa yasan halin da kika jefa rayuwar ki, ko iyayena ban tab'a magana dasu haka ba.      Ake dake Shaidaniya ce, kina shigowa rayuwata kika mai dani mafadaci! Kika mai dani d'an iska. Sannan yau kin mai dani me garkuwa da mutane, yau meye nayi miki kika lalata min rayuwa? Meye nayi da zafi da kika b'ata min suna haka? A tunanina babu rigima tsakanina dake! Sai da abokaina.      Amma lokaci guda, kin maida min rayuwa mara amfani, ki gaya min meye alakarki da Ni?.". Yadda ya daka min tsawa ya sani.... #MI #HWA #Mai_Dambu 10/23/20, 9:51 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ GOMA Ki gaya min meye nayi miki haka da zafi?" Ya faɗa tare da dukar motar, kamar zai fasa hannun shi.       A tsora ce k'ame jikina ina sake wata irin kuka me mugun cin rai. "Cire min kayan jikinki nan?!" A razane na kafe shi da ido, jikina yana wani irin rawa, ban san lokacin dana zube akan gwiwata ba, tare da matse jikina a guri guda, ina keerrma. "Don Allah ka rufa min asiri! Mu ahalin gidan sarauta an samu da kamewa, sabida kimarmu itace shaidar tarbiyyan mu." "Cire kayan nace ko na cire nayi abinda na gadama dake!" "Wallahi bazan cire ba, kawai ka bi takai na da motar ka, zai fi min kwanciyar hankali da ace na cire."    Lallai Jay mahaukaci ne! Ko nace d'an mahaukaciya, ba tare da jin ko Dar ba, ya tawo ya shiga yaga sauran kayan jikina.    Wani irin bakin ciki ne, ya sani kasa kuka. Ina girmama rashin mutunci irin na Jay, sai da babu wata kaya a jikina, sannan ya nuna min motar ya shige yana kallon agogon hannun shi.   Kamar na had'iye zuciyata dan bakin ciki. "Ina da abin yi!" ..kauda kan shi yayi, sabida yaga na kasa tashi, a hankali na isa jikin kofar baya na bude tare da shiga cikin motar. "Nice zan zama driven ki?!"      A hankali na fito tare da kare kirjina, na shiga gaban motar, ina kuka. Da wani mugun gudu ya finciki motar daga ni sai yar buje tare da shimin da na saka, babu yar rigar mama a cikin jikina   Sai kare jikina nake ina, kuka munyi doguwar tafiya kafin, ya taka birki sai da na tafi kamar zan hantsila. "Na rantse kika dame ni da kuka zan zane ki!"    Cike da mamaki na ciro kai na, ina mishi kallon. "Ka zane ni fa? Ai ni ba Yarka bace."    "Ficce min a mota!"ya daka min tsawa, wani irin rawa jikina ya ɗauka, na fara bashi hakuri. "Don Allah kayi hakuri bazan kuma maka magana ba."       Sake sake motar yayi a guje, kamar  zai tashi sama, gashi tsabar mugunta ya.kure karfin sanyin motar, sai rawan sanyi nake.     "Don Allah ko zaka rage karfin sanyin nan ne?!" Banza yayi dani, sai ma kure karfin da yayi. Atishawa nayi ta sakewa tare da jin wani irin sanyi yana shugaba kamar zanyi hauka, da wutsiyar ido yake kallona, tare da tauna bakin shi, sai da muka yi tafiyar awa biyu, sannan ya tsaya. Ya fita zuwa bayan motar. Ya ciro min wata ƙatuwar rigar sanyi tare da wandon shi gajere zuwa kwanji. Sai wata yar karamar riga. Ajiye min yayi tare da tadda motar dan wulakancin yace min. "Ina sauri ki fita ko saka kayan suna bayan.. idan kika b'ata min lokaci sai na tafi na barki."      Kallon wajen nayi na kuma duba a gogon motar shi, ban san lokacin da kwalla ya cika min ido ba, karfe biyu na dare. "Don Allah ko zaka, fita na saka a cikin motar." A birkice ya kalle ni, tsaki yaja tare da sake kan motar ya finciketa a guje,  karshe sai juyawa nayi na kwashi kayan, ina saka rigar ina kuka, tare da jin wani irin kunya da ban tab'a jin irin shi ba.    A gaban mutumin da ba muharramina ba, nake saka kayana, amma abin mamaki. Sam hankalin shi baya kaina, jin ya taka wani irin birki ya sani maza na d'ago kaina.             Tare da kallon gaban mu, wasu gungun mutane ne, dauke da makamai.      "Maza ki suturta jikinki!" Da sauri na saka rigar sanyin na saka tare da gyara kaina, wata mayafi ya ɗauka tare da wurga min. Na rufe kaina, jikina yana rawa. Buga motar suka yi ya bude da sauri. "Kai bamu kudi?!" Suka tambaye shi. "Babu kudi?!"   Cikin fusata suka shiga make motar, bude inda nike suka yi. "Ha? Wannan abincin kuma da toh tunda babu kudi zamu fanshe daren mu da ita." ...cikin mugun tsoro na kalle shi. Shima ni yake kallo, wasu irin kwalla ne suka shiga tsiyaya a idanuna, kamar an bude magudanar ruwa.   ..... "Zan baku kudin!"        Zasu kai mishi duka, ya daka musu tsawa, tare da dukar gilashin motar sai da ya fashe yace. "Nace zan baku kudin! Dama ai baku ji ta baki na ba, ita din mata ta ce! Kai zaka ji dadin yau ace na kwanta da matar ka! Eyye toh kar ku sani na muku abinda zai dame ku." Bude bayan motar yayi ya ciro musu wata jaka, yana wurga musu, suna bude motar suka fincikoni da karfin tsiya. Suka shiga jana a kasa. Daya daga cikin su yan magana cikin France yana faɗin. "Quand tu nous cries dessus, nous nous coucherons avec toi et devant tes yeux" (Har ka isa kayi mana tsawa, akan idonka zamu kwanta da ita)     Cikin tashin hankali da tararradi ya fara magana. " Don Allah na roke ku karku mata kome, naji nayi laifi" "Wayyo Allah na! Jayyyyy! Kazo zasu tafi dani." Na fada ina ihu, yana son ya tawo, nan kuma wasu sun rike shi, kamar mahaukaci haka yake musu ihu. "Karku tab'a min mata ta, ku barta nace baku ji ne!"                      Suna kai ni, Gurin shugaban su suka watsar dani, rigar jikina na sanyi suka cire min da karfin tsiya, sannan uku suka danne ni, shugaban ya shiga ƙoƙarin yaga min wandon jikina.    Kuka nake tare da rokon su, amma ina har sun zare wandon. "Jayyy! Don Allah zo karka basu su min haka."       Ina kallon mutumin ya cire wandon shi, tare da min rumfa da kirjin shi, ban san lokacin da kuka me ciwo ya kwace min ba, dan hankalin shi baki daya, suna kan kirjina ne.                   Hannun shi ya kai, da niyyar tab'awa, sai ganin shi muka yi yana aman jini, cikin tsoro sauran suka sake ni, tare da niman arcewa da gudu.sai ganin su muka yi suna faduwa a mace. Da sauri Ya karaso tare da cire rigar shi ya mika min, yana kauda kan shi, ina sakawa. Ya mika min hannu na tashi, sai kallon yadda mutanen suke faduwa muke, a tsora ce na koma bayan shi na boya tare da boye fuskana, a bayan shi.                       Hannuna daya a samar kafad'arshi, cikin tsoro.    Sai a  lokacin muka fahimci guguwar da ta cire guri guda take, tare a guri ɗaya tana tashi sama. "Jay!"     Ashe addu'o'in yake, kallon bakin shi nake, tsabar yadda addu'ar take fita. Da wani irin gudu guguwar tayo kan shi, na rike rigar shi tare da kwala ihu,  watsewa guguwar tayi,  a bayana naji an tab'a ni. Cikin wani irin tsoro na juya.   Wata mace na gani cikin jajjayen kaya, tana fidda hayaki a kanta da idanunta. "Dole kema ki d'andani abinda taji! Dole ki biyo ni, dole ki buɗe idanunki dole ki sadaukar da Rayuwar ki domin na shi, dole ki taya mu yaki! Tun daga farko kuka shiga zanen kaddarar juna! Babu yadda zaki yi ki fice a nashi haka zalika shima bazai fice a naki ki, dole a karasa bashin da ba kune kuka ci ba."    Kasa motsi nayi, naga ta juya tare da zama hayaki ta baje.              Ba zance na kuma fahimtar wani abu ba, amma tabbas na bude idanuna na ganni kwance a wani daki,. hannuna daya dauke da karin jini. Mik'ewa nayi zan zauna, aka ce min. "Koma ki kwanta."   Wata mata ce, cikin shigar wata irin Wutar rissa, bakin shi. Kallon na jikina naga nima an sauya min kayana, daga riga da wandon jikina, zuwa wata duguwar riga, wacce suke kiranta da Bougaje.         Fita matar tayi, can sai ga tare da wasu maza biyu. "Innaih sannu da ƙoƙari, har ta falka? Sannu ya kumarin jikin naki?"         Lumshe idanuna nayi sannan nace musu "da sauki."    Ina rufe baki jini na saukowa daga hancina.       "Ina Mujaheed din yake?! Halo dai Jinin yana zuba, kuma bamu san meke haifar da zubar jinin ba, dole a san abin yi." Suna cikin maganar ya shigo.    Fita suka yi, can ya kuma dawowa da wasu malaman jinya aka zo, suka fita dani.    Lokacin jini ke fita daga hancina, haka idan nayi tari jinin xan fitar abinda ya d'aga musu hankali kenan, baki daya. Suka rasa yadda zasu yi dani.      Haka yayi ta bincike ko zai samu matsalar da nake fama dashi, amma bai yi dace ba.            Karshe bayan an dawo dani dakin da nake. Suka mikar dani. Zasu mai dani gadon kawai na yanki jiki na fadi.     Sai da aka kira shi, yazo lokacin ga baki daya na suma.     Rayuwata ta zame mishi tashin  hankali, domin zubda jinin da nake ba na wasa bane. Shi kan sa ya fara dana sanin dauko ni da yayi.        Sai da suka hada da rokon Allah da addu'a, na farka ban kuma jin wani ciwo ba, sai na masifar jin Jay! Wani irin abu nake ji shi  kamar zuciya ta, zata fito daga kirjina.        Ban san lokacin da na shiga wannan halin ba, sai dai na wayi gari.ina ji a raina zan iya rasa rayuwata akan Jay. ....... Na ji sauki sosai, har an sallame ni. Dan wulakancin amadadin ya kaini inda zan zauna cikin gidan su. Sai ya kai ni can bayan gidan su.gurin masu aikin gidan.     Kuma ya saka aka bani dakin da bai da maraba da matattarar dabbobi, kullum da safe ni ke kwashe kazamtar su,bayan na basu abinci. Tun ban saba ba, har ta kai na saba dasu.     ...raƙumai ne suke kiwon su abakin Innaih naji labarin ai kusan rabin su na Baban shi ne! Murmushi nayi kawai, ina jin dadin idan yazo kwashe su zai tafi kiwo. Burge ni yake, domin yana saka wata shudin mayafi tare da rufe fuskar shi.    Yau ma ina cikin basu abinci,  na zubawa wata Rakuma mace ido, tana ta nishi.       Wai ashe haihuwa zata yi, kawai naji Innaih tace min. "Fadima! Kira min Mujaheed, yazo Rakumar nan haihuwa zata yi, maza yazo ya san abinyi."           Da sauri na fita sanye da kayan bougaje, bayan na rufe fuskana da wani baƙin mayafi, haka kawai yasani na dinga rufe fuskana dan cin mutumci,       Wai yake gaya min. "Ke fa bawani fasali ne da ke ba, domin tsayinki yayi yawa sai kace sallar dare, gashi kin cika yanayi da aljanu.          Idan na takura kaina da kallon ki, sai naji kamar na boye kaina dan sak kike da aljanu, don haka daga yau kar na kuma ganinki babu mayafi in ba haka ba zan iya yin komai. Musamman abinda zai samar min da nutsuwa ta. Shi zan aikata." Tun daga wannan ranar na daina, wannan gangancin. Daga nesa na hango shi.... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:51 AM - Ummi Tandama: https://my.w.tt/W07hVCuVdab MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ GOMA Last free page Ki gaya min meye nayi miki haka da zafi?" Ya faɗa tare da dukar motar, kamar zai fasa hannun shi.       A tsora ce k'ame jikina ina sake wata irin kuka me mugun cin rai. "Cire min kayan jikinki nan?!" A razane na kafe shi da ido, jikina yana wani irin rawa, ban san lokacin dana zube akan gwiwata ba, tare da matse jikina a guri guda, ina keerrma. "Don Allah ka rufa min asiri! Mu ahalin gidan sarauta an samu da kamewa, sabida kimarmu itace shaidar tarbiyyan mu. Ba iya ahalin masarautar ba, duk macen da tasan kimarta! Dole ta kare shi don Allah ka rufa min asiri." Na fada cikin kuka, "Cire kayan nace ko na cire nayi abinda na gadama dake!" "Wallahi bazan cire ba, kawai ka bi takai na da motar ka, zai fi min kwanciyar hankali da ace na cire."    Lallai Jay mahaukaci ne! Ko nace d'an mahaukaciya, ba tare da jin ko Dar ba, ya tawo ya shiga yaga sauran kayan jikina.    Wani irin bakin ciki ne, ya sani kasa kuka. Ina girmama rashin mutunci irin na Jay, sai da babu wata kaya a jikina, sannan ya nuna min motar ya shige yana kallon agogon hannun shi.   Kamar na had'iye zuciyata dan bakin ciki. "Ina da abin yi!" ..kauda kan shi yayi, sabida yaga na kasa tashi, a hankali na isa jikin kofar baya na bude tare da shiga cikin motar. "Nice zan zama driven ki?!"      A hankali na fito tare da kare kirjina, na shiga gaban motar, ina kuka. Da wani mugun gudu ya finciki motar daga ni sai yar buje tare da shimin da na saka, babu yar rigar mama a cikin jikina   Sai kare jikina nake ina, kuka munyi doguwar tafiya kafin, ya taka birki sai da na tafi kamar zan hantsila. "Na rantse kika dame ni da kuka zan zane ki!"    Cike da mamaki na ciro kai na, ina mishi kallon. "Ka zane ni fa? Ai ni ba Yarka bace."    "Ficce min a mota!"ya daka min tsawa, wani irin rawa jikina ya ɗauka, na fara bashi hakuri. "Don Allah kayi hakuri bazan kuma maka magana ba."       Sake sake motar yayi a guje, kamar  zai tashi sama, gashi tsabar mugunta ya.kure karfin sanyin motar, sai rawan sanyi nake.     "Don Allah ko zaka rage karfin sanyin nan ne?!" Banza yayi dani, sai ma kure karfin da yayi. Atishawa nayi ta sakewa tare da jin wani irin sanyi yana shugaba kamar zanyi hauka, da wutsiyar ido yake kallona, tare da tauna bakin shi, sai da muka yi tafiyar awa biyu, sannan ya tsaya. Ya fita zuwa bayan motar. Ya ciro min wata ƙatuwar rigar sanyi tare da wandon shi gajere zuwa kwanji. Sai wata yar karamar riga. Ajiye min yayi tare da tadda motar dan wulakancin yace min. "Ina sauri ki fita ko saka kayan suna bayan.. idan kika b'ata min lokaci sai na tafi na barki."      Kallon wajen nayi na kuma duba a gogon motar shi, ban san lokacin da kwalla ya cika min ido ba, karfe biyu na dare. "Don Allah ko zaka, fita na saka a cikin motar." A birkice ya kalle ni, tsaki yaja tare da sake kan motar ya finciketa a guje,  karshe sai juyawa nayi na kwashi kayan, ina saka rigar ina kuka, tare da jin wani irin kunya da ban tab'a jin irin shi ba.    A gaban mutumin da ba muharramina ba, nake saka kayana, amma abin mamaki. Sam hankalin shi baya kaina, jin ya taka wani irin birki ya sani maza na d'ago kaina.             Tare da kallon gaban mu, wasu gungun mutane ne, dauke da makamai.      "Maza ki suturta jikinki!" Da sauri na saka rigar sanyin na saka tare da gyara kaina, wata mayafi ya ɗauka tare da wurga min. Na rufe kaina, jikina yana rawa. Buga motar suka yi ya bude da sauri. "Kai bamu kudi?!" Suka tambaye shi. "Babu kudi?!"   Cikin fusata suka shiga make motar, bude inda nike suka yi. "Ha? Wannan abincin kuma da toh tunda babu kudi zamu fanshe daren mu da ita." ...cikin mugun tsoro na kalle shi. Shima ni yake kallo, wasu irin kwalla ne suka shiga tsiyaya a idanuna, kamar an bude magudanar ruwa.   ..... "Zan baku kudin!"        Zasu kai mishi duka, ya daka musu tsawa, tare da dukar gilashin motar sai da ya fashe yace. "Nace zan baku kudin! Dama ai baku ji ta baki na ba, ita din mata ta ce! Kai zaka ji dadin yau ace na kwanta da matar ka! Eyye toh kar ku sani na muku abinda zai dame ku." Bude bayan motar yayi ya ciro musu wata jaka, yana wurga musu, suna bude motar suka fincikoni da karfin tsiya. Suka shiga jana a kasa. Daya daga cikin su yan magana cikin France yana faɗin. "Quand tu nous cries dessus, nous nous coucherons avec toi et devant tes yeux" (Har ka isa kayi mana tsawa, akan idonka zamu kwanta da ita)     Cikin tashin hankali da tararradi ya fara magana. " Don Allah na roke ku karku mata kome, naji nayi laifi" "Wayyo Allah na! Jayyyyy! Kazo zasu tafi dani." Na fada ina ihu, yana son ya tawo, nan kuma wasu sun rike shi, kamar mahaukaci haka yake musu ihu. "Karku tab'a min mata ta, ku barta nace baku ji ne!"                      Suna kai ni, Gurin shugaban su suka watsar dani, rigar jikina na sanyi suka cire min da karfin tsiya, sannan uku suka danne ni, shugaban ya shiga ƙoƙarin yaga min wandon jikina.    Kuka nake tare da rokon su, amma ina har sun zare wandon. "Jayyy! Don Allah zo karka basu su min haka."       Ina kallon mutumin ya cire wandon shi, tare da min rumfa da kirjin shi, ban san lokacin da kuka me ciwo ya kwace min ba, dan hankalin shi baki daya, suna kan kirjina ne.                   Hannun shi ya kai, da niyyar tab'awa, sai ganin shi muka yi yana aman jini, cikin tsoro sauran suka sake ni, tare da niman arcewa da gudu.sai ganin su muka yi suna faduwa a mace. Da sauri Ya karaso tare da cire rigar shi ya mika min, yana kauda kan shi, ina sakawa. Ya mika min hannu na tashi, sai kallon yadda mutanen suke faduwa muke, a tsora ce na koma bayan shi na boya tare da boye fuskana, a bayan shi.                       Hannuna daya a samar kafad'arshi, cikin tsoro.    Sai a  lokacin muka fahimci guguwar da ta cire guri guda take, tare a guri ɗaya tana tashi sama. "Jay!"     Ashe addu'o'in yake, kallon bakin shi nake, tsabar yadda addu'ar take fita. Da wani irin gudu guguwar tayo kan shi, na rike rigar shi tare da kwala ihu,  watsewa guguwar tayi,  a bayana naji an tab'a ni. Cikin wani irin tsoro na juya.   Wata mace na gani cikin jajjayen kaya, tana fidda hayaki a kanta da idanunta. "Dole kema ki d'andani abinda taji! Dole ki biyo ni, dole ki buɗe idanunki dole ki sadaukar da Rayuwar ki domin na shi, dole ki taya mu yaki! Tun daga farko kuka shiga zanen kaddarar juna! Babu yadda zaki yi ki fice a nashi haka zalika shima bazai fice a naki ki, dole a karasa bashin da ba kune kuka ci ba."    Kasa motsi nayi, naga ta juya tare da zama hayaki ta baje.              Ba zance na kuma fahimtar wani abu ba, amma tabbas na bude idanuna na ganni kwance a wani daki,. hannuna daya dauke da karin jini. Mik'ewa nayi zan zauna, aka ce min. "Koma ki kwanta."   Wata mata ce, cikin shigar wata irin Wutar rissa, bakin shi. Kallon na jikina naga nima an sauya min kayana, daga riga da wandon jikina, zuwa wata duguwar riga, wacce suke kiranta da Bougaje.         Fita matar tayi, can sai ga tare da wasu maza biyu. "Innaih sannu da ƙoƙari, har ta falka? Sannu ya kumarin jikin naki?"         Lumshe idanuna nayi sannan nace musu "da sauki."    Ina rufe baki jini na saukowa daga hancina.       "Ina Mujaheed din yake?! Halo dai Jinin yana zuba, kuma bamu san meke haifar da zubar jinin ba, dole a san abin yi." Suna cikin maganar ya shigo.    Fita suka yi, can ya kuma dawowa da wasu malaman jinya aka zo, suka fita dani.    Lokacin jini ke fita daga hancina, haka idan nayi tari jinin xan fitar abinda ya d'aga musu hankali kenan, baki daya. Suka rasa yadda zasu yi dani.      Haka yayi ta bincike ko zai samu matsalar da nake fama dashi, amma bai yi dace ba.            Karshe bayan an dawo dani dakin da nake. Suka mikar dani. Zasu mai dani gadon kawai na yanki jiki na fadi.     Sai da aka kira shi, yazo lokacin ga baki daya na suma.     Rayuwata ta zame mishi tashin  hankali, domin zubda jinin da nake ba na wasa bane. Shi kan sa ya fara dana sanin dauko ni da yayi.        Sai da suka hada da rokon Allah da addu'a, na farka ban kuma jin wani ciwo ba, sai na masifar jin Jay! Wani irin abu nake ji shi  kamar zuciya ta, zata fito daga kirjina.        Ban san lokacin da na shiga wannan halin ba, sai dai na wayi gari.ina ji a raina zan iya rasa rayuwata akan Jay. ....... Na ji sauki sosai, har an sallame ni. Dan wulakancin amadadin ya kaini inda zan zauna cikin gidan su. Sai ya kai ni can bayan gidan su.gurin masu aikin gidan.     Kuma ya saka aka bani dakin da bai da maraba da matattarar dabbobi, kullum da safe ni ke kwashe kazamtar su,bayan na basu abinci. Tun ban saba ba, har ta kai na saba dasu.     ...raƙumai ne suke kiwon su abakin Innaih naji labarin ai kusan rabin su na Baban shi ne! Murmushi nayi kawai, ina jin dadin idan yazo kwashe su zai tafi kiwo. Burge ni yake, domin yana saka wata shudin mayafi tare da rufe fuskar shi.    Yau ma ina cikin basu abinci,  na zubawa wata Rakuma mace ido, tana ta nishi.       Wai ashe haihuwa zata yi, kawai naji Innaih tace min. "Fadima! Kira min Mujaheed, yazo Rakumar nan haihuwa zata yi, maza yazo ya san abinyi."           Da sauri na fita sanye da kayan bougaje, bayan na rufe fuskana da wani baƙin mayafi, haka kawai yasani na dinga rufe fuskana dan cin mutumci,       Wai yake gaya min. "Ke fa bawani fasali ne da ke ba, domin tsayinki yayi yawa sai kace sallar dare, gashi kin cika yanayi da aljanu.          Idan na takura kaina da kallon ki, sai naji kamar na boye kaina dan sak kike da aljanu, don haka daga yau kar na kuma ganinki babu mayafi in ba haka ba zan iya yin komai. Musamman abinda zai samar min da nutsuwa ta. Shi zan aikata." Tun daga wannan ranar na daina, wannan gangancin. Daga nesa na hango shi....       *K'ak'ak'ara k'ak'ai!!!! Shin kun shirya! Toh ku biyo magajin Izzah! Domin jin yadda kome zai warware* .,Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu...      #Mai_Dambu 10/23/20, 9:52 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA ƊAYA           Cogewa nayi tare da zabe mishi ido, ganin yadda suka nad'e kan su da shigar buzaye. Sun ajiye yar butar shayi, suna sha tare da hirar. Baka fahimtar kome akan abinda suke cewa. Domin yaren buzanci suke.                  Tab'a shi jibo yayi tare da nuna mishi kofar garka, ina tsaye.           Banza yayi dani, ganin yaki juyowa. Kawai na juya abuna. Tunda na fahimci bazai taso ba. Koda na shiga kasa zama nayi sai leka kofar shigowa nake.                "Yaki shigowa ko?" Gyad'a mata kai nayi, sabida tafi kowa sanin halin shi. Da kanta ta fita, can sai gashi tare da ita, wani irin kallo ya jefe ni dashi sannan ya ware rawanin kanshi ya durkusa gaban Rakumar.       Ya shiga ƙoƙarin ciro mata yaron cikinta, dakyar ya ciro mata yaron, sannan ya koma ya karasa abinda zai yi.     Takowa yayi gabana, ya shafa min jinin Haihuwar Rakumar, cikin tsantsar mugunta. "Idan na kuma ganinki a waje."     "Toh ka mai dani inda ka dauko ni mana! Tunda baka son ganin ina zuwa inda kake."                    Take min kafana yayi, na d'ago kaina ina kallon shi, cikin kuka nace. "Allah sai ya saka min."     Baki na ne ya furta hakan, amma zuciyata sam bata aminta da hakan ba.            Jay bai bar inda nake ba, sai da ya sani kuka sosai. Sannan yayi tafiyar shi.                 Innaih ce tayi ta bani hakuri, tare da gaya min bafa halin shi bane, kawai yana min haka ne dan laifin da nayi mishi. .karfe sha biyu saura. Ina kwancen ya shigo inda nake, kunna wutar dakin yayi ya ganni zaune ina ƙoƙarin b'oye  tsimar da nake goge hancina.        Takowa yayi cikin nutsuwa, ya saka hannu ya ciro tsimar, yaga yadda ya jike da jini. "Aanih! Meke damunki?!" .kallon renin hankali nayi mishi, sannan nace mishi. "Jin dadi!" Daga haka nayi shiru, tare da kwanciya na juya mishi baya. "Tashi ki rakani!" "Babu inda zani a wannan tsohon daren" "Toh ina saka miki kayan" Zubur na mike tare da amsar bakaken kayan na saka, ina mishi kallon tuhuma. "Da alamu ka fara fashi da makami ko?!" Tab'e baki yayi, sannan ya bar d'akin. Na saka riga da wandon sai yar karamar hijab.   Sannan na fito, a hankali babu kowa a tsakar gidan. "Shiiiiii! Naji kamar ana jan abu, juyawa nayi cike da tsoro, na hango matar ranar, sanye da doguwar rigar yana jan kasa, ya jike sosai da jini. Tafiya take ina bin bayanta,  dafa ni akayi na sake wata irin ajiyar zuciya tare da sake kara. "Ke dalla tafi can!" Ya gaya min,  riko hannuna yayi tare da fitar dani a gidan, har gurin motar shi muka isa, sannan ya sake hannuna ya koma mazaunin shi na shiga motar.    Tunda ya fara tuki bamu tsaya a ko ina ba, sai a wani can gidan rawa,(club)  tunda muka shiga nake jin warin giya. Da wiwi.         Kallon mutanen gurin nayi, sunata bad'alar su, can gefe na nima na zauna. Tunda ya shigo ake ihun zuwan shi.      Sai gaishe shi ake, ga yan mata sai rungume shi suke.      Da alamu ba bakon gurin bane, sannan kuma zan iya cewa duk inda yake sai ka samu ana girmama shi.                    Ina zaune maza keta kawo min hari, ban kula su ba. "Manyan a ina ka samu iri me kyau haka? Gaskiya ta haɗu."        Bai magana ba, haka suka yi ta magana, yana jin su. Mik'ewa daya daga cikin su yayi zai zo inda nake ya rike mishi hannu. "Karka fara!"      Komawa yayi ya zauna, "Toh wacece ita?!" "Ita din kamila ce! Daga gaban iyayenta na daukota."   Shiru yayi sannan ya mike, tare da mika musu hannu, sannan yazo inda nake ya riko hannuna muka fita, kallona yayi sannan yace. "Me yasa kike daukar hankalin su?!" Banza nayi dashi dan bani da amsar bashi, can yace. "Ina magana kinyi banza dani ke wacece!"             Dake kaina a sunkuye yake, yana tab'a ni ina dungurawa, abin ya dame shi.    Yana kuma mamakin yadda nake wannan abin. Har dawo dani gidan, ya zagayo tare da saka hannun shi zai dauke ni, aikuwa sai ga hannun shi ya sauka a kirjina, cike da mamaki. Ya kalle yadda nake sume ga jinin nan yana d'iga daga hancina...   .        Janye hannun shi yake son yi, amma shaidan na mishi huɗubar tsiya, kara tabawa yayi yaji yadda suke, wani irin yanayi yaji lokaci guda, d'ago fuska na. Yana kallon yadda zubda jini hanci da idanu. .janye hannunsa yayi tare da kaini d'akina, yafita. Tunda daga ranar, ban kuma ganin shi ba, shigar da yake yi ma, ya daina baya zuwa inda nake.        Sosai na damu akan rashin ganin shi, ga wani irin yanayi da nake tsintar kaina, na tashin hankali. ...... Yau kwana bakwai kenan, ina kwance ya shigo min, hasken wayar shi ya dallara min, sannan ya coge a gefe..idanun shi a kaina.     .."zaki raka ni!" "Gaskiya indai gidan rawa ne bazani ba, sabida ba tarbiyyar gidan mu bane!"    Takowa yayi gabana, cikin izza ya durkusa tare da haska fuskar mu yace. "Kalli cikin idanuna! Nace zaki raka ni!"         "Ni bazan." Fincikoni yayi har jikin shi na rawa ya kura min ido, cikin jin haushi yace. "Ki tashi kafin nayi.amfani da baiwar da Allah yayi min, na gyara miki zama!"   ... Babu shiri na mike ya watsa min kayan ya ficce a d'akin, kuka ne ya kwace min.   Sai da nayi ya ishe ni, sannan na saka kayan, doguwar riga ce har kasa, a hankali na fito daga dakin. Wannan karar da naji na ranar can. "Shiiii!"    Tsintar kaina nayi da bin inda kar'ar yake fitowa, kawai naji ya fincikoni. Tare da ja na,.muka fita.                       Sai da ya jefa ni cikin motar, sannan ya dawo yaja mu, tun a hanyar nake aman jini. Kaina kamar zata yi bindiga, buga motar yayi bayan ya tsaya, cikin jin haushi yace. "Duk abinda zaki yi, sai kin rakani party nan!"          Babu yadda na iya haka muka nufi, inda suka shirya, shirmen su. Bana jin dadin shigar da nayi. ... Tunda muka shiga, abokan shi suka ja shi can gefe. Wani cikin su yazo ya takura min da surutu. Karshe da na gaji, na silale zan gudu. Ashe sun ga fita na daga dakin party wani daga cikin abokan shi yace mishi. "Yarinyar da kuka zo ta fita fa! Kuma naga su Ghali sun bita."    Mik'ewa yayi, yaji gabaki daya, bazai iya dogon tafiya ba, komawa yayi ya kwanta a kujeran. Tare da buga kanshi, yana faɗin. "Yarinyar kamila ce! Ni ne na daukota domin daukar fansan abinda tayi min, taya zan su min haka." Dakyar ya mike,  yana buga kanshi sannan ya fito. Can nesa yaji ihuna, da sauri ya shiga niman inda nake, nan kuwa kokuwa suke dani, daya na kokarin yaga min rigar jikina, daya kuma yana me rufe min bakina.   .... Wani irin kuka ne ya kwace min, cikin tashin hankali na kwala mishi kira. "Mujaheed!" Sake toshe min bakina suka yi, tare da kai ni kasa. Allah ya bani Sa'a wanda ya rufe min bakina, na gantsara mishi cizo, sai da yayi ihu, a lokacin Jay ya iso, tare da zama a gaban su. "Karku mata kome! Domin mata ta ce!" .   Da mamaki suka zuba mishi ido, Ghali ya dauki wata sanda a gurin ya make mishi kai, tare da cigaba da dukar shi, sannan ya tura wanda na ciza, ya dauko musu ruwa.       Zuba mishi ruwan suka yi, sannan suka mike tare da cewa. "Karka kuma gigin kawota gidan casu, domin wallahi gobe zamu kuma farmata." ... Gyada musu kai yayi, suna tafiya na iso gurin shi da sauri, tare da kallon shi, dake abuge yake mika min hannu yayi da sauri na rarrafa jikin shi ina kuka sosai. "Jay! Ka kai Ni gurin Baabina, bani da lafiya! Idan baka kai Ni ba wani abu zai same ni!"        D'ago kaina yayi, giya tana gaya mishi wani abu na daban, kafin nayi wata yunkuri sai jin bakin shi nayi cikin nawa, duk yadda naso kwace kaina, na kasa.            Hancina da kunne ne, suka fara zubda jini, kafin wani lokaci, idanuna sun rufe da jinin, saukar da bakin shi yayi wuyana, tare da Binta da wata zazzafar sumbata. Sai ganin kaina yayi yana reto.     Dakyar ya mike tare da lallubar makulin motar shi, ya kunna, sannan ya nufi motar tare da daukata, shi kanshi bai san inda zai kai ni ba.     Tunda ya ajiye ni a cikin motar, ya nufi gida dani, dakyar ya isa konace Allah ya nufa muna da nisan kwana.                 Daukata yayi zuwa dakin da ya bada na zauna, ya kwantar dani, sannan ya fita. Dakin shi da yake da taga ta wajen d'akina, ya shiga. Ko cire kayan jikin shi bai yi ba, ya kwanta.             --- Washi gari! Koda ya farka, a hankali abinda ya faru daren jiya ya shiga dawo mishi.    Ganin har yayi Sallah tare da wanka bai ji muryana ina wasa da Yar Jinjirin Rakumar nan ba, ya sanya shi fitowa. Har tsakar gidan.         Gama kewaye tsakar gidan yayi kafin ya koma inda Innaih take aiki, yace. "Innaih ina wancan Yarinyar?!"     Cike da mamaki take kallon shi, kafin ta maida kanta, izuwa aikin da take sannan tace. "Faɗimah ba yarinya bace! Magajin Izzah, kawai jikinta ne da bai nuna alamar girma." Tanke fuskar shi yayi cikin jin haushin abinda Innaih tace. "Innaih! Tambayarki nayi ina take?!" "Allah ya huci zuciyar ka! Barden Damagaram."               Nuna mishi dakin tayi, cikin wani irin Izzah da jin kai, ya nufi dakin, daga shi sai 3 qrt. Ya iso bakin kofar.       Yana turo kanshi sai da ya razana, sabida yadda gashin kaina yayi buzu-buzu, ga Idanuna da suke fidda jini.             Mai da kaina nayi kasa ina gogewa. "Dama baki da lafiya ne?!" Banza dashi nayi, na cigaba da goge jinin. "Ina miki magana kinyi banza dani.!"    ... "Don Allah ka kyale ni! Ka mai dani gurin Dangina, idan ba haka ba. Mutuwa zanyi." Fita yayi daga dakin, ya nufi dakin shi. Ya shirya ya bar gidan, Bayan wani lokaci, ya kuma dawowa d'akin. Kwalayen allura da ruwa ya ajiye har ya durkusa zai sanya min karin ruwan. Kawai ya juya abinshi can ya kuma dawowa ya taimaka min tashi nayi kuma na koma zan zub'e da sauri ya rikoni kaina yayi baya.                Cikin tashin hankali, ya dauke ni zuwa dakin shi, ya shiga had'a min, maganin da alluran. Yana gamawa, ya haɗa min ruwan sannan ya zuba alluran, ya koma gefe yana kallon yadda nake fidda numfashi, jikin shi yayi mugun sanyi. Yana ji a ranshi bai kyauta ba. Sam yana ganin rashin dacewa da ya daukota a gaban ahalinta. Duk halin da ta shiga shine silah #Mai_Dambu 10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️       Wannan shafin gaisuwar shi takuce Aunty Mamie da Sister Safiya 😍🌟🤗 SHA BIYU. Zuba mata ido yayi cikin sanyin jiki, dole ya bata kulawa kamar yadda ya daukota, dole ya ji da lafiyarta, kamar yadda ya daukota. A hankali barci yayi gaba dashi wanda yake dauke da mafarkai daban daban. "Zo muje na kai ka, kaga yadda al'ummar da suke jiran ka! Taso kaga yadda kowa ya jima yana jiran zuwarka."         Riko Hannun shi aka yi, ana bude kofar haske ya cika mishi idanu, karewar da yayi kenan ya farka daga barcin.       Jin tarina ya sashi mik'ewa, koda yazo na gama b'ata mishi zanin gadon shi da jini. A rud'e ya kai hannun shi ya riko ni. "Don Allah ka mai dani gida! Kaji a can suna da maganin da suke min idan ciwon ya tashi kaji Jay!" Na faɗa cikin wani irin kuka,     Wani allura ya janyo tare da cikawa sannan ya ga yadda nake zare mishi idanu ina shirin kuka, fincikoni yayi tare da matse ni, ya tsikara min alluran, ajiyar zuciya na sauke, tare da janye jikina, zan kwanta.          "Gaya min! Meye ke damunki!"           Shiru nayi ban amsa mishi ba, can ya kuma ce min. "Me yasa kika zabi rayuwarki sama da ta iyayenki musamman mahaifinki?!"                A hankali nake bashi labarin, yadda na taso tare da kulawar da nake samu, a gurin Baabi, har zuwa lokacin da nayi ta samun rikicin aurena.        "Abinda yasa naki auren Ikrama, ba kome bane sai dan ya kasance, yana niman abinda zai hada auren mu, shi da mahaifinsa tare da kanin Mahaifina, idan suka bashi aurena, zan zame musu wani abinda zasu na aikata mugun nufinsu."                   Shiru yayi sannan na cigaba da cewa. "Nasan Baabina yana cikin damuwa, damu kuma nasan yan uwan shi zasu mishi caaa! Jay " Na tashi a hankali, tare da matsowa gaban shi nace. "Shekaru na talatin da uku! Zuwa da hudu! Gashi kaje ka sato ni, yanzun me zan gayawa Baabina, bana son yayi fushi dani!     Kuma bana son ya zarge ni, Jay kana da mugun hali, amma kuma kana da tausayi, ni Yanzun bana son na koma gida ma, nafi son na zauna kayi ta ce min aljana, idan haka zai sanya kasami farin ciki. Jay bana son kana kula...."        Zuba min ido yayi, tare da gyara min gashina. "Jay! Wai da gaske ni mummuna ce? Don Allah gaya min meye laifina."         "Ban tab'a ganin mummuna irinki ba!"              Ware shanyayyun idanuna nayi kafin na mai da su na rufe, tare da b'ata rai, na tura mishi baki. "Jay! Baabina yace! Babu kyakyawa irina, ina da kyau kamar Umma Jannart. Sannan ina wasu abubuwa irin nata." Daga haka na zube a jikin shi, na fara wasu maganganun kananu, saka kunne shi yayi, yaga naja yar bakina nayi shiru, d'ago kaina yayi, yana kallon baki. Mai dani yayi kwance.      Tare da zuba min ido, jikin shi a mace. Har zai mike na rike hannun shi. "Jayyyyy!"       Komawa yayi yana mai da min gashina baya, kamar zanyi kuka, na riko hannun shi. A kirjina na cigaba da barci, sai da yaga barcin yayi nisa dani, sannan ya zare hannun shi.       Yana me komawa kujeran hutawa, ya zauna yana me nazarin maganar da nayi.    Dole yana bukatar ya mai dani gida, amma taya!         --- Sokoto. A.S.P Habib Samim talba.     Mari ya kwad'awa Ansaar, sai da bakin shi ya fashe. "Gaya min! Ina kuka kai Fulani Aanih?"     "Wallahi! Yallabai, ban kaita ko ina ba, asalima ita ce ta nime na sace ta, ko kaza ban tab'a dacewa ba, wallahi iya gaskiyar kenan! Muna cikin haka wani yanayin wani mutum yazo daga kasar waje.     Shine ya bani kudi tare da cewa na bar mishi aikin zai karasa, shi kuma ya cigaba da gaya mata yadda zai shigo gidan da fari ta amince, amma daga baya ta turo min sakon karshe ta fasa, ashe shi bai fasa ba, shine ya shiga cikin gidan a matsayin me gyaran panpo. Iya abinda na sani kenan!"        Shiru Habib yayi tare da gyara yar gemun shi da take kara tsirowa.           Fita yayi daga dakin horon   ...... Bayan b'atar Aanih Me girma Gwamnan ya saka aka kawo Habib yazo yayi bincike, garin binciken ne ya samu sakon da aka turo a wayarta, da kuma Whatsp ɗinta, daga nan suka shiga niman Ansaar, suka kamo shi yau sati biyu kenan, suna mishi mugun duka.         --- Lokacin da ya fita daga ofishin su, Fada ya wuce, inda ya samu sarki akan maganar ko yana sane da cewa Yar shi wani tabi ta gudu.                     Sunkuyar da kai Aryaan ya, cikin matsanancin kunya da jin tozarci. .... Mik'ewa kanin shi da suke ciki d'aya yayi zai kaiwa Habib mari. "Barshi ya fadi gaskiya! Akan yarinyar da ta gama gantali, zaka  fara kokarin daukar shi, toh bari na gaya maka, wallahi ba zaka dake shi ba karya yayi muku? .kawai Aryaan yayi murabus, mulkin a matsayin sarkin Musulmai bai dace dashi ba, sai sarkin mata, tunda bai iya lankwasa yar shi ba, waye zai lankwasa ya biyu.        Dan haka ya sauka daga muqaminsa, dan bazamu cigaba da bin jagorancin sa ba."     Mik'ewa Naufal yayi Aaryaan ya dakatar dashi, cikin murmushi, me cike da tawwakali.. mike daga kujeran da yake, ya sauka a kai.           Ya kasa cewa kome, sannan ya juya ya bar fadan baki daya. Kallon kallo aka yi tsakanin Habib da Najim wanda Sarki Jaamal na daura ya turo shi domin taimakawa, Sarkin Da wasu bayyanan da ya samu.      Sai kuma yazo ya samu kome ya lalace, cikin mutuwar jiki ya bude bakin shi dakyar yace. "Habib! A dokar kasa ka taka doka sosai, domin amadadin ka nime shi cikin nutsuwa, kuyi magana kazo ka tadda husuma wanda dokar kasa ta haramta haka."        "Malam Lauya! Bazaka koya min aikina ba, dan haka abinda doka ta bani nayi, dan rashin Imani an samu mun kama wani na daban, bayan yasan Yar sh...."           Kifa mishi mari Najim yayi, cikin fusata yace. "Dan sanda ka mara?!" Ajiye jakar shi yayi yana nade hannun rigar shi yayi cikin b'acin rai yace.        "Ni a matsayin abokina nake maka magana, dan abu kazan ka, idan aka sami mahaifinka da wannan batun ya zai ji? Kasan wutar da ka hura kuwa! Ina ma da Jalal yana raye, nasan sai yaci Ubanka laada a waje, banza wanda bai san aikin shi ba."   Daga haka duk suka watse a cikin fadar, har da sauran mutanen.       ...... Tsaye yake ko kayan jikin shi bai cire ba, yana kallon hoton. Aanih cikin rauni da tausayin wani irin yanayi take ciki, yana yawan jin kewarta da shashekar kukanta. A baya bayan nan. Yana yawan mafarkin ta, tana mika mishi hannu. Ko kuma tana kwance cikin jini.   Shi yasa tunda ya shigo ya hana kowacce mace ta shigo mishi daki dan bai nutsuwar zuciya.        Kafe hotonta yayi da ido, sannan ya dauki takarda da biro,ya zauna ya rubuta takardan murabus din shi sannan ya koma ya zauna a kujeran hutawa, yana jijjiga kan shi.      Yayi imanin duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, bai lalata na kowa ba, yayi Imani Allah bazai tab'a barin a lalata mishi na shi ba.     Sake bude ido yayi sakamakon, jin muryan Hanisah tana kuka,. Kallonta yayi tare da mika mata hannu, a hankali ta karaso ta daura kanta a bisa cinyar shi, tana wani irin kuka. "Baabi kayi hakuri! Insha Allah Didih zata dawo muna da yakinin sace ta aka yi."      Shafa kanta yayi, sannan ya fara magana yace. "Me yasa kika canza abinda ya faru! Bayan kin tabbatar itace ta gudu da kafarta?!"     "Baabi! Kimar kace na kare! Taya zan yarda a zubda maka ita! Sannan kuma zai iya shafar masarautar? Nasan idan nace musu nasan da kanta ta nime a sace ta, aure zai mata wahala, amma idan na nuna ban san kome ba akan haka, duk ranar da ta dawo.   Ba zata  rasa mijin aure ba, Baabi, yaranka maza bi, mu hudu kuma mata,. Baabi dole mu koyi boye sirrin gidan mu, dole mu rufawa kan mu asiri." "Allah yayi miki albarka! Amma idan ta dawo me kika ga ya dace nayi mata? A matsayin ki na uwa mace!"     D'ago kai tayi cikin damuwa da tashin hankali, tace. "Baabi! Sabida a wanke ta daga zargi za a iya kaita asibiti ko likitan yazo ya dubata a cikin gidan, a tabbatar da lafiyarta! Shi kenan." .  "Toh madalla da shawarar ki. Jeki zan huta!"     Ya sallame ta, sannan ya cigaba da zurfaffa tunanin shi, da kuma Halin da Babbar Yar shi take ciki.        --- Daura... "Kawu! Ka rage tunanin nan haka! Don Allah, Insha Allah nima ina ji a jikina abubuwa suna dab da faruwa!" Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kuma dawowa gabanta ya zauna yana kallon ta. "Sarah! Yaron da na gani ya sace Aanih! Ƙwayar idanun shi sak Na Janny! Kuma babu abinda ya bari, da yanayin idanunta.    Cikin idanun shi, sun kasance irin nata zaiba, sai girman su sak nawa, Ina tsoron kar." "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, don Allah ka daina fadar haka, domin wallahi bana jin kome akan haka, Ni dai karka sa a fara zargin Yaron da bai san kome ba da aikata wani abu."         "Ba haka bane! Abinda nake son." Mik'ewa tayi ta bar Mishi dakin, haka kawai kullum sai ya nanata abun daya, sai kace akan shi aka fara ganin abu me kama daya, tana fama da ciwon zuciya akan sace Mata Yaronta tsowon shekaru ashirin, amma dare daya ya wurgata da wata damuwa, duk ya diririce ya koma wani irin mutum.     Dan abu kadan sai ya mai da shi kamar wani yaro karami..           Har yau bincike take, tsawon shekaru tana nan tana bin rayuwar Jakadiya Sahurah, wacce ta samu labarin tana macina taje aka ce mata bata garin, kwanaki aka ce mata tana jibiya, bata fasa tura yan aike ba, kullum abu daya take yi ko Allah zai sanyata ta sami inda take.     Sannan waye mutum na uku nan, dan kwanaki da Baba waziri ya rasu, ta dauka shine sai daga baya aka kuma turo ma ta da wani sakon, haka ya tabbatar mata da cewa. Tabbas me don ganin bayan su yana tare da su, toh waye ne shi? Wannan tambayar takewa kanta har yau bata ga alamar zata ga wanda yake wasa da rayuwarta.       Sannan bata da ikon ta tuhumi Ajiya da Kuma Sa'i, tunda basu fadi kome ba.                  --- Damagaram.. Zufa nake karyawa, sakamakon zafin da ake, sannan na farka daga barci, kallon shi nayi yana barci cikin nutsuwa kamar baya tare da wata damuwa, sai ma kara fad'adda farar da ban tab'a gani ba sai yau.             Tari nayi ya sanya shi bude ido da suka yi ja. Tashi yayi ya tawo har inda nake, ya cire min abin karin ruwan dake hannuna, sannan ya koma ban dakin shi ya dibo ruwa a wani abu ya dawo dakin, zama yayi a gabana da yar karamar tsuma, ya durkusa a gaba na. . Hannun shi ya kai zai tab'a ni na make hannun, tare da b'ata fuska.    Hannun shi ya kai baya ya zuge min rigar, ta baya. Kare kirjina nayi, cikin jin haushi nace. "Ni ka rabu dani bani ciki da iskanci, ka bar ni nace d'an iska kawai! Ban da rashin hankali da yarinta meye zai saka ka same ni a b'agas kana wulakantani, jikina da zaka tab'a."       Bai damu ba, sai ma kokarin ganin ya cire min rigar yake, na saka mishi kuka, buge min hannun yayi tare da saka yar tsuman a ruwa ya shiga goge min jikina, Allah ya taimaka bai cire min yar shimin ciki ba, da na shiga uku. Kallon fuskana yayi na wasu lokuta, kafin ya kai hannun shi bakina yana shafawa, buge hannun nayi cikin jin haushi, zan bude bakin ya kai hannun shi kirjina, buge hannun na kuma, fincikoni yayi tare da manna ni da kirjin shi, ya saka hannun shi ya cire min shimin jikina k'amk'ame shi nayi tare da fasa mishi kuka.          "Don Allah ka rufa min asiri! Karka min abinda bazan iya fuskantar dangina dashi ba."           Hannun shi ya kai wuya na tare da d'ago kai na. "D'an iska kika ce!" Rufe idanu nayi wasu irin kwalla na zuba min, tare da d'igar jinin daga hancina, tattausar bakin shi ya d'aura akan lebbena, na bude idanuna tare da sake wani irin kuka, sakamakon jin hannun shi a kirjina.           A hankali ya zare tare da ɗaukar tsumar ya shiga        goge min ina kare kirjina, karshe na bashi haushi, saka hannu. Shi yayi tare da yaga rigar,. Dauke kan shi yayi kamar  bai ga kome ba. "Mtseew, dube su kamar lemun tsami! Dalla cire hannun nan!" Ya daka min tsawa,kuka ne ya kwace min, ina son zanyi magana na kasa tsabar tsoron dan wani b'ata rai yayi sosai. #Mai_Dambu 10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA UKU. "Don Allah Jay! Ka barni na saka kayan," na fada a rauna ne.      Banza yayi min, kamar ba dashi nake magana ba, gyara min kwanciya yayi sannan.   Wani b'ata rai yayi, kamar bashi ba, kawai ya shiga kokuwar cire kayan shi. Wani irin tsoro ne ya kamani, lokacin da ya cire rigar naga haikan ni zai hakewa. "Jay! Karka min haka! Dan girman Allah karka min abinda kake shirin aikatawa, wallahi tallahi ban."    Rumfa yayi min da kirjin shi, ina kasar shi, da gaske Jay. Kuka na sake Mishi da mugun karfi.       ...ga baki daya na birkice,  zan iya cewa ban tab'a rud'ewa irin na yau ba, mara mutunci ashe zolaya ce kawai. Ganin yadda na birkice yasa sake murmushin mugunta. "Na zata ko dan kin saba da maza."         Janyo bargo yayi ya rufa min, sannan ya bar d'akin yana me jin haushin abinda yayi min.      Shi ba dan iska bane, amma lokaci guda halittar shi tana niman birkice daga tozali da surar jikina. ...... Ban san wacce irin kulawa zan gaya muku yake bani ba, amma tun da ya fahimci bani wani damuwa da namiji a keb'ence, sai ya mai da hankali gurin bani kulawa.        Wanda ta kai, wani lokaci idan jikina ya d'an tashi, yakan kwana a d'akin, wani lokaci kuma idan yaga jikin yayi zafi haurawa gadon yake, ya shiga jikina sosai yadda har zan daina jin zafin, tun ina tsoron kar wani abu ya faru a tsakanin mu, har Allah ya taimaka bai kuma yunkurin min wani abu ba. Amma bani  da lafiya! Kawai ina ƙoƙarin b'oyewa ne, sabida kar yace bazai mai da ni gida bane, amma duk wanda ya kalle ni, sai ya kuma kallo na, bani da haske sosai, amma ina da duhun fata, wannan zubda jinin ya sani nayi wani irin fayau.           .... Kwana biyar nayi a d'akin shi a cikin wannan kwanakin, na gama mutuwa akan shi kamar ji nake a duniya bazan iya rayuwa babu shi ba, duk da na fahimci shi mutum ne me tsananin kamun kai, kuma bai da tunanin wani abu a kaina,               Sau biyu, ina ba shi damar, ko zai far min amma wani ikon Allah, idan yazo yaga nayi wata banzan kwanciya, zai gyara min kwanciya, sannan yayi ficewar shi, idan ba jikina bane bai tab'a kallona a matsayin mace. Shi mutum ne dai bai cika magana ba, sam baya son hayaniya, sai dai haduwar mu tasa shi magana. Sam baya da hayaniya. A cikin kwanakin da nayi dashi zai yi wuya idan ya shigo yace min ya jiki na amsa mishi toh zai iya shafe awa biyu bai ce min cikanki ba, sabida tsabar miskilanci.            Nice ma Innaih take cewa, na sashi magana, kasancewar ita ce tayi renon shi,  dan tace har ya shekara sha shida, baya magana,.       Ina kwancen, wanda ya zame min jiki, sai gashi nan yazo min kayan daga Ashasha sai  bougaje, ya kawo min tare da riga da wandon Pakistan har da mayafin su.               Tare da wasu kaya, ya ajiye min. Kallon agogon hannun shi yayi, sannan ya juya zai fita, ya kalle ni. "Idan kina bukatar zuwa gida, ki shirya nan da minti goma, idan kuma na sake shigowa na samu baki shirya ba, zanyi tafiyata dan jibi zan koma Canada!"       Kallon shi nayi cikin wani irin yanayi, zuciyata tana wata irin bugawa. Ji nake kamar kirjina zata fashe kallon shi ne tsaya yi kamar naga sabuwar halitta. Takowa yayi gabana, tare da cewa. "Baki ji bane?!" Hawayen da nake rikewa ne suka zubo min nace mishi. "Ni bazan koma ba!" Zaro idanu waje yayi, tare da cewa. "Baki da hankali ne? Mahaukaciya ina ce ke?!"         "Wallahi bani dashi! Mahaukaciyar kace ni! Don Allah karka mai dani, kaje dani ko ina ma!" Na faɗa cikin kuka. Mik'ewa y hannun shi cikin aljuhun wandon shi yace. "Baki da lafiya! Kina b'oyewa ne, shi yasa nake son mai dake gaban iyayenki!  Sannan zama na dake akwai shaidan, dan haka bazan iya aikata zina ba.        Shi yasa nake ganin ki tafi gaban iyayen ki kawai."     Rarrafawa nayi dakyar na mike, tare da isa gaban shi. "Don Allah karka rabu dani! Ko na koma bazan iya zama dasu ba? Jay don Allah kaje dani ko ina ma, a shirye nake na bada rayuwata akan ka don Allah."                Zaunar dani yayi cikin nutsuwa, yana kallon fuskana, jikin shi yayi mugun sanyi. "Kinga ni wani abu nazo yi,"                   Shiru yayi yana kallon yadda nake kuka, sosai. Zuba gwiwar shi yayi a kasa sosai sannan ya kalle yadda nake ta kukan.                     "Toh naji idan muka je zan roki gafarar Baabi sai na tafi dake!" Ya faɗa min.         Cak kukan ya tsaya ina kallon shi, a hankali nace. "Da gaske kake ko kuma kana rarrashina ne, kake?!" B'ata rai yayi tare da cewa. "Na tab'a miki karya ne?"    Daga haka ya bar d'akin, shiryawa nayi tsaf na fito sanye da riga da wando, sai mayafin da na rufe kaina.              A hankali na shiga cikin gidan gurin Innaih na mata sallama, ta ɗauki da wo. Da madarar rakumi hadi da cukwai ta bani, nayi ta godiya. Jay Mugu ne.   Farkon zuwa na gidan, sawa yayi tayi ta bani dawo da nonon raƙumi, ba suga. Ina sha ina amai daga baya da na iya sha kuwa ko ya sayo abincin Innaih ta girka bana ci sai da wo.             Goge kwalla nayi sannan na fita da sauri ganin yana ta danna mana korototo, a hankali na shiga motar ina d'agawa Innaih hannu, a hankali yake jan motar har ya fita daga garin, dan sai yanzun na fahimci a kauye muke.      Bai kalle ni ba, muka nufi  gidan su da yake cikin Damagaram, bari na yayi a cikin motar ya shiga cikin gidan. Take yan matan dangin su tare da yan uwansa suka mishi caaa.      Murmushi yayi sannan ya kalli kakar su yace. "Annah! Zan koma inda na fito!"         Tab'e baki tayi, sannan tace. "Da fatan dai ba wani abun ka rakato ba." Mik'ewa yayi zai fita ya ajiye mata kuɗi me mugun yawa, sam bai san lokacin da zai burgeta ba,da ace tare da Munih suka zo da tuni ta shiga rawan jiki dasu.        "Ya Jay! Don Allah ka tsaya muyi hoto mana!" Inji wata yar kyakyawar budurwa.          Tsayawa yayi suka dauki hoto, sannan ya shiga cikin gidan ya gaida matan baffanin shi, kafin ya fito.   Motar shi ya shiga, gani na ina wasa da awarwaron hannuna, yasa shi tab'e baki, yaja motar da mugun gudu.                   Sanyin motar wanda yake hade da turare, yasa ni lumshe idanuna, gudu yake sosai, tare da kallona lokaci zuwa lokaci, sai da mukayi tafiyar awa biyu sannan ya tsaya tare da saya min abinci, kugun tsamiya tare da gashashen nama, tunda na sha, sai ga zufa na karyo min.        Murmushi yayi tare da share abinda yayi niyyar fada, yasan shi ba mutum me yawan magana bane, amma haduwar mu tasan yashi zama me yawan magana tare da dogon magana abinda yakewa da kallon damuwa ko ciwon kai, sai gashi yakan iya tsawaita magana kamar bashi ba.          "Shaidaniya!" Kallon shi nayi tare da b'ata fuska, "Ba dai ni ba?!" Na faɗa a hasale. "Toh cire min kayana!" Ya fada fuskarshi babu wasa. Sunkuyar da kaina nayi, cikin tashin hankali. "Kayi hakuri!" Share ni yayi kamar bazai kuma magana ba, ya cigaba da tukin shi...         Kallon shi na tsaya ina yi, kamar wata mara hankali.. "Don Allah kalli gabanki"   Ajiyar zuciya na sauke sannan nace. "Jay ince baka manta alqawarin mu ba?!"                  "Don Allah kayi min magana mana!" Janyo asusun jikin motar shi yayi tare da dauko wata yar kamar kwalba, da abin allura, yaja ruwan cikin shi.           Sai da ya gama durawa,sannan ya rufe yana tukin gangancin, sai da yaga hankalina yayi nisa, kawai ya cakka min a damtsen hannuna, sannan ya zare ya cigaba da tafiyar shi, a hankali barci yayi gaba dani, sauke min kujeran yayi sannan ya cigaba da tafiyar shi.     Tafiya muka yi wanda ni kaina ban san awowin da muka yi ba, sai dai naji yana shafa min ruwan sanyi, a fuskana. A hankali na bude idanuna ina kallon shi. Ganin har karfe biyar na yammaci ake nima, na kalle shi tare da cewa. "Ban yi sallah ba."         Fita yayi a hankali yace min. "Muna boda! Kiyi sallah ina jiranki"       Sauka nayi  na tafi wani gidan wanka nayo tsarki da alola, sannan na dawo na yadda sallah, ina idarwa yana mika min, abinci  a cikin kwalin tafi da gidanka wato (take away)        Tunda na sami guri na zauna na fara ci, shakuwa na fara ya mika min ruwa nasha, sannan ya koma ma zauna shi. Har muka isa inda ake duba kayan mu, sannan muka wuce.                      Kallona yayi, cikin ko in kula yace. "Barka da zagayowar ranar haihuwarki, ga cake can a bayan mota, ki dauka. Amma kiyi hakuri ban cika miki sauran burinki ba."    A hankali na juya naga wata ƙatuwar kwali. "Taya aka yi kasan da haka?!"             "Duk wanda ya shigo rayuwata! Ina bindidigin shi!" Ya fada min, "Kamar Y'a?!" Tun daga lokacin da kika fara fada dani! Na shiga bin dukkan tsarin ki!"    Shiru nayi dan Jay ya fara bani tsoro, ban ce mishi kala ba, sai ɗaukar cake din da nayi.. Naga an rubuta Barka da zagayowar Haihuwar ki 34, kwalla ce ta sauka akan cake ɗin. ."taya kasan ina son chocolat cake?! Naga ban tab'a gaya maka ba, sannan." ."na gaji bani son Damuwa!".     Shiru nayi ina kallon shi,"kalli gabanki" yace min.               Taya zai fahimci ainihin abinda yake damuna! Taya zan fahimtar dashi yadda nake jin shi. Da Jay zai fahimci halin da nake ciki da ya sassauta min.         Goge kwalla nayi tare da yanka cake din na sanya mishi a gefen bakin shi. Kallon yadda nayi da fuska ya sashi bude bakin shi, sai da ya ciza da hannuna, da sauri na cire hannun tare da zabga mishi harara.      Kallon madubin motar shi yayi yaga ana bin mu motar yan sanda tare da na sojoji.       Karawa motar shi gudu, yayi dan yana son yau idan ya ajiye ni ya koma nijar, gudu yake sosai kamar zai tashi sama.    Har ya b'acewa ganin su,. Ajiye min agogona yayi akan gwiwata. "Kin tuna shi?!"          Kallon shi nayi sake da baki, a hankali ya kuma fisgar motar kaman zai tashi sama,  karfe tara yayi mana a garin sokoto, kallona yayi sannan yace. "Ban tab'a sab'a alqawari ba, amma bazan iya cika miki naki ba, kiyi hakuri da abinda nayi yanzun haka ana jiranki a cikin gidan ku, suna bukatar ki."           Dai-dai ya cusa hancin motar shi cikin gidan mu,kamar yadda ya dauko ni. Cincirindon yan sanda da sojoji ne..     "Akan me zaka yaudare ni da."       A hankali ya sauko daga motar, sannan yazo ya bude min kofar,  ya riko hannuna. A hankali muke takawa, tare da rakiyar jami'an tsaro, juyawa yayi cikin damuwa yace. "Ku bar bina! Idan ba haka ba, zan iya mata wani abu." Jin haka yasa su, suka dakata da bin mu, a nutse ya nufi cikin gidan dani, Baabi na zaune da  casbi a hannun shi.       Ganin yadda yan uwan shi, suka zuba mana ido,  nayi maza na koma bayan Jay cike da tsoron abinda zai faru.                       Hannuna rike da rigar shi. "Toh Fatimah babu wanda ya isa ya dake ki, matukar ina tsaye da kafaffuna!" "Kai d'an ta'adda! Waye ya tsaya maka?! Ka sace yarinyar mutane kaje kayi abinda yayi maka sannan kazo zakawa mutane rashin mutunci, kai gaka mara kunya tsagera! !"      "A.s.p! Kaga laifin shi! Da ita ƙaruwar bata bishi ba,  zai samu damar tsageranci ne?!"inji Yayar Baabi,       Dariyar Da A.s.p yayi shi ya fusata Jay yaja hannun rigar shi sama, sannnan ya juya a fusace ya kaiwa Dan sandar wani mugun naushi, sai da haƙora biyu suka zubo, ya kuma d'ago shi yana nuna mishi yatsa!          "Ban da kana sanye da rigar hukuma! Sai na karya kashin mukamikin ka, Idan kuma wani yayi subul da baka, ya ambaci yarinya mai daraja irin Fatimah da sunan karuwanci, sai na mishi abinda bazai manta dani ba. Ficce min da gani. An san yan sanda suna kare al'umma ce akan gaskiyar su, ba dan a ci zarafin su ba. Fita nace."       Juyawa yayi ganin yadda nake shashekar kuka, riko hannuna yayi har gaban Baabi, ya tsaya sannan ya kalli yan uwan Baabi,  zama yayi saman d'aya daga cikin kujerun falon, ya daura daya akan daya.              Sannan ya ciro wasu takardun a cikin yar jakar da take rataye a gefen shi.             Shiru yayi, tare da nazarta mutanen da suke falon, ina tsaye har zuwa lokacin. "Wannan takardun na shaidan lafiyarta ce! Nayi iya bincike na ban gado dalilin da yasa take zubda jini ba. Ranka shi dad'e! Ni ban yi niyyar cutar da Yarka ba, kawai na gwada mata ne idan na saka abu a gaba na, duk duniya banda iyayena bana d'agawa kome kafa.        Kafin yau ni ban iya magana ba, amma zuwan wancan mahaukaciyar ta mai dani magananne, ban san wani irin goyan naci kayiwa yar ka, ba amma dai duk mijin da ya aureta.       Zai sha bakar azaba da nacin Bala'i, domin bata iya dogon magana bata ambaci Baabi ba, abin dariya da tace min shekarunta  amma kullum tana nan kamar jinjira, tsabar kaunar da ka gina mata a zuciyarta.                Yallabai nasan nayi maka laifi da na sace Yarka, sai da babu sauki Gaye irina a samu mace ta kwantsama mishi mari, ai kuwa kasan haka bazai ma sabu ba, shi yasa na dauketa ranar aurenta.  Domin nima na rama tijarar da tayi min.           Kayi hakuri! Sunana Dr Mujaheed Harisou Agla! Don haka ga Yarka nan zaka iya kaita asibiti a kara bincika maka ita!" . Yana gama fadar haka ya mike abinshi.                      "Jay! Don Allah karka tafi" "Ke manta dani! Zan tafi can nayi rayuwa ta, ki zauna kiyi aurenki amma ina son don Allah idan kin haifi mace! Ki ajiye min ita zan dawo na dauketa kuma ta faɗa soyayya ta." ."Jayyyyy!" Na kira sunan shi. "Don Allah ka tafi dani! Wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake ni, ban san lokacin da haka ya faru dani ba!"         Juyawa yayi gaban jama'a yana kuma kallona, ya tako gabana. "Ke zaki iya rayuwa mana, Insha Allah mijin ki zai zama mutum mai kamala." .rufe mishi baki nayi cikin wani irin kuka, jini na zuba ta hancina .. "Jay Ina sonka!" Cike da mamaki yake kallona, sabida shi duk abinda nake bai fahimci cewa soyayya bace.... #Mai_Dambu.... 10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA HUDU "Da gaske! Ina sonka ne? Don Allah karka ka min shiru."    Dariyar da ban tab'a ganin yayi ba, ita ce yaƙe yi tare da nuna ni da yatsar shi. "Meye amfanin cin fuska?! Idan baka sonta a bayyane yake tayi hakuri! Amma mu a halin babban gida mun san dajarar kanmu Yace da Mahaifinta ya zab'e ta sama da mutanen shi, zaka iya sadaukarwa haka, don Allah ka tafi Allah zai bata wanda take so." Inji Ummi Rahil,      Daga haka ta riko hannuna tayi zata ja ni. "Jay!"       Na faɗa cikin kuka, bata dube shi ba, ta ja hannuna.   Cire hannunta nayi, da sauri na sha gaban shi. "Kace wani abu! Don Allah kayi wani abu! Karka tafi ka barni. Kai kace bazaka tafi ka barni ba. Me yasa zaka karya alqawarin da kayi min!            Don Allah kayi hakuri kaso ne!"       "Kinga ni bana jin kome akanki! Asalima Ni bana kaunarki! Wallahi bana sonki! Kinga ne kiyi hakuri ki...." Kifa mishi mari nayi, kuma sai tsoro ya kamani, naja da baya. "Kayi hakuri! Bazan kuma ba kawai ina ganin abinda idanun ka suke faɗa ne! Jay karka manta ina sonka! Ka fahimci sakon da zuciyata tazo maka dashi."        "Yayi kyau! Amma bari na gaya miki! Ni bazan tab'a auren yar ashirin da biyar ba, balle ke da kika kusan haihuwa na,  talatin da hudu fa, ji min cutar kai! Ke bani hanya. Tsabar rashin tsoron Allah ina zan kai ki bazawara."    . girgiza mishi kai nayi tare da riko hannun shi. "Wallahi ba yadda kake tsammani bane, Jay"     "Ke bani hanya na wuce, na kawo ki gidan ku ga iyayenki da danginki, kiyi zaman ki."           "Babu inda ka! Ka dawo! Idan kuma kana ganin karya ne kafi daga gidan nan Mu gani! Jalaludeen D'an Jannart! Baka isa ka fita daga cikin zanen kaddarar mu. Ina sonka kuma ba zaka tab'a."      Jini ne ya shiga zuba min, daga kowani kafa ba.  Juyawa naga cikin gidan yana min, a hankali na tafi zan zube yayi maza ya tare ni.                           "Ku taimaka min! A kai ta asibiti."            "Babu inda zamu kaita! Kai kuma mun gode! Amma ba zaka bar gidan nan ba, sai Har Mahaifinka yazo." Inji Rahil! "Ban gane ba? Wallahi tafiya zan yi! Tunda na dawo muku da Yarku!"..         "Idan kasan darajar iyayenka zaka iya tafiya." Shiru yayi kamar ya fasa ihu, tare da zama yana hararar kowa a falon, karban ta suka yi tare da kwantar da ita. Maganinta suka dauko aka fara shafa min..       A hankali jinin ya fara tsayawa matse bakina suka yi zasu bani maganin, na watsar da su.            Duk yadda suka so su bani maganin na sha, naki asalima guduwa nake son yi, sai da ya taso ya matse ni sosai, tare da amsar maganin ya bani da karfin tsiya.         "Lallai!  Baka san wacece ni ba? Kuma dole itama ta mutu!"            Ga baki daya ji yayi tsigar jikin shi ya mike me haka yake nufi.          Addu'a ya fara tofa mata, wani irin ihu take tare da kai mishi duka, ina yakushin sa.      Can na koma nayi likus, ban kuma fahimtar kome ba, sai da asuba.da ba tashi sallah.        Ganin bakona ya sani komawa na kwanta, ina me jin haushin abinda na aikata na kasa b'oye son da nake mishi, yaro karami ya chaza min lissafi.       --- "Ni da na gama abinda zan tafi tunda mun fito sallah, ina son gobe na wuce Canada!"       "Kayi hakuri! Mahaifinka yana zuwa! Dan tunda na ganka a Canada na shiga bibiyarka, sai gashi kai Khatoon kake bibiya.                      Ban san me yasa na kasa daukar mataki akan abinda kayi min ba, sai dai nasanin soyayyar da nayiwa Janny gaskiya ce! Shi yasa ban ga laifinka ba.   ..bazan maka dole akanta ba, tunda baka sonta, amma ka sani abinda kayi kusan kuskuren da Mahaifinka ya kwantanta kenan!"       "Nifa ban fahimci abinda kuke nufi ba. Na bar iyayena a Canada! Akan me zan damu da wasu iyayen."              "Ta yaro kyau take bata karki! Mu shiga ka karya sai kayi Sallama da Kanwar  mahaifiyarka zaka iya tafiyarka."    Bazai iyawa Aaryaan musu ba, amma gaskiya yana jin Fad'uwar gaba, akan halin da yake ciki.             --- Karfe goma na safe, Jaamal da Sarah suka sauka tare da Aswad. A hankali suka karasa inda Motar da Aaryan ya turo musu, suka shiga.      Basu san dalilin kiran su da Aaryan yayi ba, amma tsabar faduwar gaban da Jaamal ya shiga kamar zuciyar shi zata diro daga kirjin shi.           Koda suka isa cikin gidan, wani shashi na daban aka kai su, har cikin falon Aaryaan suka isa, wanda yake zaune tare da Rahil. Tayi kuka har ta godewa Allah.         Magana take a hankali, tana fada halin da suke ciki.      Cikin sanyin jiki, Sarah ta nime guri ta zauna, tana kallon su. Abinci aka shiga jera musu.       Daga bisani yace. "Fulani Maryam ko zaki shiga daga ciki, sai su karya suma anan."            Mik'ewa Sarah tayi ita da Rahil, suka shiga. Tunda aka ajiye mata abin karyawa ta kasa ci. "Hussainah zuciyata a tsora ce take! Don Allah gaya min meke faruwa! Ina Fatimah take."           Riko hannunta yayi suka nufi d'akina, dai dai ba fito wanka kenan,ina zaune Hanisah tana busar min da gashina.             "Alhamdulillah! Yaushe aka dawo da ita!?!" "Jiya ta dawo da d'an uwan ta.      Abin da mugun daure kai,.taya aka yi suka haɗu.?" Inji Rahil,   Cikin kasaita wanda yabi jikinta da jininta, ta tako har cikin dakin. Tana kallona, "Fatimah! Ince babu abinda ya faru.da aka dauke ki?!"    Cikin jin nauyin abin na sunkuyar da kaina, kasa nace. "Hum-uhum!" "Ummin su waye d'an uwanta da ya dawo da ita haƙa?!"     Jan hannun ta Ummi tayi, suka shiga d'akin ta, ta nuna mata abin karyawa, sai da suka gama karyawa sannan ta amsa kiran Baabi.      Sun sami Jay a zaune tare da su Baabi, yaki magana. Duk yadda suka so yayi magana, yaki cewa kome. .... Karshe Mamah Sarah ta zuba Mishi ido, cikin kaduwa tace. "Tsarki ya tabbata ga Ubangiji talikai! Jalaludeen!" Ta faɗa a raunane, tare da tasowa zuwa gaban shi, ta zauna.  Hawaye na zuba mata, yau gani take kamar gata ga Janny.  Kuma rike hannun shi tayi cikin nata, kwalla ya d'aga cikin hannun su.    Ta kuma d'ago kan ta, shima kuma ya d'ago nashi kan. Abubuwan da suka gabata suka shiga dawo mata, wani irin kuka na taso mata. "Jay! Rabon ka shine ya salwanta da farin cikina, samun ka shine ya maye gurbin farin cikina, Jay don Allah kayi magana. Dani da Jannart guri guda muka zauna. Abu daya muka so! Gashi nan a gabanka. Da nayi hakuri na bar mata Kawunta da yau tana raye cike da farin ciki, da nake fatan samu da itama ta same shi nima na same shi.          Don Allah kayi min magana, kaji Yarona, kayi min magana. Idan ta kama na baka labarin amintar mu, tare da soyayyar mu. Duk zan gaya maka amma kayi hakuri kace wani abu mana."     ...... Kamar ba zai magana ba yace. " Toh me zance? Iyayena suna Canada! Yarinyar da na dauka na dawo da ita! Don Allah ku bar ni nayi tafiya."      Daga haka ya mike tare da ce musu, "ni na tafi yallabai"           Cikin wani irin kuka, tace mishi. "Don Allah ka dawo mana, wallahi ba dan na raba mahaifinka da Mahaifiyar ka ba, da yanzun kana cikin jerin masu daraja da sa'a don Allah ka dawo."    Muryan Mamah Sarah ne ya sani fitowa, ganin yadda take kuka tare da, bin shi. "Magajin Izzah!" Cak ya tsaya, nabi Abban shi da ido, ba iya ni ba hatta Baabi da Baba Aswad zubawa sarki Jaamal ido suka yi. "Maryam! Dawo barshi yayi tafiyar shi, idan har Mace jaruma zata iya sadaukar da Rayuwar ta, domin masalaha, zai dawo. Idan har Jarumin Uba irina zan kasa na kuma tsare na mallaki Uwar shi a duniya akwai adadin tafiyar da zai yi, bar shi yaje."          "Abba bazai tafi ba! A ranar da na fara shiga Makarantar Alberta, naga fuskar shi abinda na fara shine nazarin a ina na san wannan fuskar, sai da na b'ata lokaci me yawa, ina tunanin meye yasa nake damuwa da Jay!                    Sai da na dawo gida, na duba computer na, naga kamar da yake da Mai Martaba sarki Jaamal, abin ya dame ni. Dan haka sai na shiga niman hanyar da zan sami kusanci da shi, har ta kai mun fara rigima, ban kuma sarewa da al'amarin shi ba, sai ranar da ya turani cikin kazamta, abinda yazo min shine yadda yayi min ranar da muka je addu'ar Umma Jannart! Daga nan na fahimci shine na gane shine amma taya yazo Canada?! Nasan zai biyo ni.              Shi yasa ranar da muka gama makarantar, na mare shi. Abba Wallahi ban tab'a jin soyayyar kowa sama da nashi ba, a kansa na fahimci girman Soyayyar da nake mishi, Abba bazan iya rayuwa babu shi."            Shiru falon yayi, sabida kuka na. Cikin zafin nama ya tawo tare da had'a ni da bango. "Akan me zaka cutar da ni? Wato ba ni na shirya sace ki ba, kece kika shirya min haka domin nazo ku b'ata min lokaci. Bana sonki! Bana kaunar ki? Ko me zaki yi sai kiyi!       Mayya kawai, idan sona shi zai yi ajalin ki, gwara ki mutu, a rage mugun iri. Kuma babu shakka zan tafi makira Kawai."       Ya juya zai fita na rike hannun shi. "Kayi min alqawarin zaka tafi dani! Don Allah ka tafi da ni! Wallahi ba zan zauna dasu bane."              Ture ni yayi cikin fada tare da jin haushin abinda nayi Mishi.          Kuka nake kamar raina, zai fita. "Jayyyyy! Don Allah karka tafi don Allah ka dawo. Jay"        "Wallahi ko zaki mutu bazan soki ba." Daga haka ya saka kai ya fita, wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da zuɓewa a kasa, hankali kowa ya tashi, musamman Baabi.              Cikin tashin hankali, aka nufi asibiti, nan aka shiga bani kulawa. Tare da saka min ruwa. Ga koshi ga kwana yunwa, suna ji suna gani yayi tafiyar shi.              "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji ka kawo min dauki! Yau naga samu naga rashi!" "Jamal ka kwantar da hankalinka!  Insha Allah zai dawo."              Shiru yayi  kowanne su da abinda yake damun shi. Har dare suna asibiti, can suka samu shiga.                   Juya musu baya nayi, naki magana. Duk yadda suka so min magana min kula su nayi, duk yadda suka so na kula su naki magana, karshe ma kuka na saka musu dole suka hakura tare da barin d'akin, tare da fita. Sun jima suna tattaunawa, kafin suka tsayar da Magana. ..... A daren Jaamal da Aswad suka bar Sokoto har da Mamah Sarah.                   --- Damagaram        Ubangiji ne ya kai Jay gida, domin sai yana tuki, zai ga wani baƙin hayaki yana bin shi da gilashin motar, yana tsayawa zai Baje, karshe ya saka kira'ar mashawi,  shine ya samu sauƙin al'amarin.                     Amma kuma kallon kan shi yake tare da tunawa da wanda aka ce shine mahaifin shi, ganin zunzurutun kaman dake tsakanin su, yasa shi jin yana son sanin waye shi?                Kwana yayi yana juyi, tare, zubawa kofar dakin shi ido yana ganin wani bakin mutum a tsaye kofar dakin shi.        Mik'ewa yayi tare zira kafar shi kasa, yaji kamar ya saka cikin ruwa, dubawa yayi ya ji shi cikin ruwan tsundum, leka ruwan yayi cikin mamaki.    Ya ganta jawur. "Tabbas! Zubda jini bai kare ba. Kuma dole ka nesanci inda suka kai ka, musamman ita Yarinyar dan rai ce ga rayuwata! Garkuwa ce ga rayuwata. Idan kace zaka iya shiga tsakanin mu, zan kashe ka."           A firgice ya farka dai-dai kiran sallah farko, ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon kofar dakin shi, yaga ashe mafarki yake.    Tashi yayi zuwa ban daki, yayi wanka tare da alola, sannan ya fito ya nufi masalacin dake gidan su, bayan ya idar ne ya dawo ya shirya kayan shi ya nufi inda motar shi yake ya dauki abinda zai dauka ya bar key din motar a dakin shi bayan ya saka motar a gareji.               Duk da a dame yake, amma ba zaka fahimci haka ba, amma kasar zuciyarshi a cunkushe yake da damuwa.. #Mai_Dambu 10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA BIYAR. Sam baya cikin nutsuwar shi, har yazo zai wuce yaga wata mabaraciya tana niman sadaka. Shafa jikin shi yayi ko da karamin canji, cirowa yayi ya saka mata sannan zai wuce. Tace mishi. "Janimal! Kalma ce ta gamayyar soyayya! Ka rike a matsayin wani abinda zai taimaka maka wata rana, d'an baiwa."     Bai saurari zantuttunkar ta ba, dan bai mata kallon me cikekken hankali ba.  A dame yake sosai. Kawai yana tafe ne amma zuciyar shi tana aina Mishi abubuwa dayawa akan Iyayen Aanih.      Zama yayi zuciyarshi tana kokarin neman dawo Mishi da tunanin Yarinyar da babu ruwan ta, bai tab'a sanin ya shaku da ita ba, sai yanzun da yake zaune a cikin jirgin, shigowar daya daga cikin masu kula da matafiya ta juya tana Magana cikin French, kawai sai ya ga tayi mishi kama da Aanih.         "Khatoon!!" Ya faɗa da karfi, sai da ta juya, dafe goshinsa yayi tare da lumshe idanunshi, dan ya shiga ruda ni.    Wata yarinya ce tazo ta zauna kusa da shi.  Idanu shi a lumshe. "Sannu!" Bude kyawawan idanun shi yayi akanta. .... Kallonta yayi kawai tare da janye idanun shi akanta. A hankali kwanakin da suka yi ya shiga ƙoƙarin dawo mishi.        Ya kasa goge kwanakin a cikin rayuwar shi, ya kasa manta yadda ya farka ya same ta, damanmakin da ya samu a cikin kwanakin da yawa. Ranar ce ta kuma dawo mishi a hankali.       Dare lahadi, tana kwance ya shigo ya same ta tana rawan sanyi, shine ya janye bargon ya shiga ƙoƙarin ganin ya dai-daita mata yanayin da take ciki, zare rigar jikin shi yayi, duk da ran shi bai son haka amma yana jin dole ne ya taimaka mata. .    Dan haka yayi ƙoƙarin, cire doguwar rigar jikinta, a hankali ya janyo ta jikin shi,  a sannu yake juyata tare da goga jikin shi a nata, lokaci guda yaji notinan kan shin suna niman kuncewa.       Tunda ya san kan shin, bai tab'a mu'amala da mace ba, asalima jin kan shi bai bar shi ya kalle mace ba.     Domin tunda ya karanci shashin mata a likitance, yake jin babu abinda mace zata iya boye mishi, amma ina ranar khatoon ta gigita mishi hankali, domin duk yadda yaso ya taimaka mata, zazzaɓin ta ya sauka sai da takai shine ya sauka ya barta, domin ji yayi halittar shi ta d'a namiji ta hana shi sukuni, kafin wani lokaci wasu sinadaran na musamman sun koma mishi marar shi, dole ya hakura da taimakon dan ba dan ya nime tsarin Ubangiji ba, da wallahi babu abinda zai hana shi afka mata ba.               Domin tunda ya haɗa jikin shi da nata, tudun kirjinta ya hana shi fahimtar me yake shirin yi, a hankali ya shiga ƙoƙarin tab'a kirjinta.            Tunda ya fara, ta bude ido ta cikin na shi, rike hannunsa tayi tare da girgiza mishi kai, jikinta yana rawa tare da bakinta tace. "Kaji tsoron Allah! Bani da karfin da zan kwaci kai na, amma ba zan tab'a barin shaidan yayi galaba a kai na ba.        A sani na da kai, baka tab'a kama da maha'inci ba, toh yau guda me zai sanya kayi Kuskuren da zai tabibiyar ahalin ka, tunda kasan bashi ce kuma sai an biya shi.          Don Allah ka bari, zan iya jure kome amma ban da wannan abin sabida kimata tana tab'awa tankar ta mahaifina ne ya tab'a. Amma idan kaga yadda yayi maka shi kenan." Ta faɗa a sanyayye, shi kan shi sai da jikin shi yayi mugun sanyin, dole ya janye tare da fita a d'akin.          "Yallabai da abinda za a taimaka maka ne?!" A hankali ya bude shanyayyun idanun shi akan matar ya girgiza mata kai! Tare da juya kan shi yana kallon tagar jirgin.                 A iya sanin shi bai tab'a kusantar matsala irin ta kwanakin nan, Aanih ta haifa masa da damuwa, gani yake jirgin ma bata sauri.          A hankali barci yayi gaba dashi. Cikin abibds bai fi minti biyar ba, sai gashi yana jin shashekar kukanta, a hankali take kusanto shi, har ya iso dab dashi. "Ina sonka Jay!" Bude idanu yayi cikin sauri.  Tare da dafe goshin sa.         Suna tafiya har dare yayi, a lokacin ya mike tare da nufar wasu musulmai suka gabatar da sallah. Bayan sun idar ya dawo mazaunin shi. Jikin shi na kuma sanyi.        ---- "Mamahna! Amshi abincin mana!"         A sannu na bude bakina ya saka min! Ina taunawa hawaye na zuba min, kallon shi nayi ina hango juriya da jarumta mahaifina, karb'an kwanon nayi tare da gyara gashina na fara ci, hannu baka hannu kwarya.                Rike hannuna yayi tare da ce min. "Ki nutsu! Don Allah kin ji."     Kallon shi nayi tare da kai abincin bakina, a nutse? "Yace baya sona! Baya kaunata! Kuma Baabina, ina son shi. Baabina me yasa kaddarata tazo a hade da nashi bayan bazan iya jurewa ba, me yasa halayyar shi suka bambanta da sauran Mazan? .... Baabi kirjina kamar ta fashe! Baabina! Me yasa ka ajiye sarautar ka?!"       Murmushi yayi, sannan ya shiga bani abincin kauda kai nayi tare da mik'ewa. Na nufi tagar dakin ina kallon yadda garin yake. "Ban san Mahaifiyata ba? Kamar yadda shima bai san Mahaifiyar shi ba!        Mun rayu a mabanbanta duniyoyi!  Sai dai nasan bazai tab'a kaunata ba."    "Inji waye? Ai tuni ya kaunace ki? Tuni yaso ki? Ki bani aron lokaci idan bai dawo ba, ni da kaina zan dawo kawo.."           "Rahil! Ki bar maganar Jalal, Ni na miki miji!" Juyowa nai a firgice tare da rike kirjina, na fashe da wata irin kuka, ina me durkusawa a gurin, da gwiwata dukka biyu. Jan hannun ta yayi suka fita basu kuma bin ta kaina ba. Anan nayi kuma har na godewa Allah da ya halicce ni.                Kamar wacce aka yiwa fada na had'iye kukan tare da yin alqawarin idan Son Jay itace ajalina gwara na mutu na huta da bakin cikin rayuwa.         --- Daura... Tunda suka isa Mamah Sarah take kuka, kamar ranta zai fito. Janny ta shiga a hankali, tana me kallonta tare da Raihah sai Rumah.        Tsayawa suka yi daga bakin kofar, suna share kwalla, ganin yadda mahaifiyar su take zubda kwalla, haka ya kashe musu jiki musamman Rumah da taki komawa gidan Mijinta! Khalid dan gidan Mamah Raihanah, shekara daya kenan da auren tazo daga Kaduna.   Dake anan suke da zama, a hankali Janny ta karasa kusa da ita, ta fara zare mata takalmin kafarta, tare da matsa mata kafar.           "Ita rayuwa tana bamu damar fuskantar matsalolin mu, bawai mu kasance cikin damuwa da rashin nutsuwa bane! Da matukar wahala, a fahimci banbancin Ra'ayin tare da juyewar wata dab'ia, amma a yadda tsarin zanen kaddarar take.     Dole sai anyi rashi kuma anyi samu, haka ce zata damawa zukatar wasu mutanen adalci, Mama karki tilas zuciyar ki! D'anki zai dawo gare ki!"          Shi yasa take masifar kaunar Yarinyar domin gani take kamar Jannynta ce ta kuma dawo mata, hakuri kawaici zurfin ciki. Duk ta gado me sunanta.            --- "Abba! Ba zai tab'a yarda ya biyo mu ba! Sannan kuma bazai tab'a amincewa da bukatar mu ba, A wannan lokaci nake bukatar shi,  amma bazai tab'a zama damu ba,        Asalima abinda muke kokarin yi kamar tursasawa ce, shi da kan shi, zai biyo sawun mu."       Murmushi Abban Jaamal yayi tare da kallon shi wato hali a jikin rai tace. "Hmm! Mahaukaciyar Kasuwa! Sa gabanki inda kike dosa, itama Kuma Faɗimah fa? Ko ba zaka bata wata tukwaicin kaunar da ta nuna maka bane?  Ko da yake! A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari. Ba  wani sabon abu bane, domin kuwa idan muka duba."     Sunkuyar da kai Kawu yayi cikin nutsuwa ya shafa kan shi sannan yace. "Abba kenan! Karka min. An yi min sagegeduwa, halin Jalal ya sha kaina, ni ban tab'a."     "Amma wa. Dodo ɗaya ake yiwa tsafi. Idan shi bai tab'a kawowa kai ne ka haife shi ba, amma shi ya nunawa duniya abinda kayiwa Jannart! Ya nuna halin. Kaje ka sami Magaji duk yadda kuka yi ka same ni, amma bazan iya barin jini na a wata duniya domin yace bai samun ba."              Ajiyar zuciya Kawu ya sauke tare da cewa. "Toh Abba!"     Tashi yayi tare da mishi sai da an jima.            ---- Karfe shida na safe! Ya sauka a garin Calgary! Cike da son sanin abubuwan da suka boya daga ganin shi. . Kallon Asood da Hikmi yayi, tare da mika musu hannu suka gaisa. "Ya kome ya tafi yadda ya dace? Ka same ta?!" Shiga yayi Bayan motar su ya kwantar da kan shi a jikin kujerar, tare da lumshe idanun shi. Ya kasa fahimtar kome akan kan shi, amma yana jinjina qarfin shigar da shi da Fatimah tayi. "Jay! Kayi mana shiru? Jay ko baka same ta bane?!" Inji Asood, Ajiyar zuciya ya shiga saukewa sabida yadda.yake jin ya barta kenan, ba ita ba hatta mutanen da suka gabatar da kan su a gare shi!! Yana jin kowacce motsin da zai yi da mutane biyun nan yake motsawa. Sarkin Daura! Sai Ummin Fatimah! Yana jinta a ran shi sosai, sama da yadda yake jin mai martaba sarkin Daura! "Amma kai wallahi anyi d'an iska! Ka mana bayani kayi shiru sai share mu kake!" Bude idanu yayi shanye da toka, kamar bazai magana ba yace. "Ka dame Ni!" Kura mishi ido Asood yayi tare da gyara zaman shi bai kuma ce mishi kala ba, asalima tsoron kuma mishi magana yayi. Har suka iso Unguwar su Jay! Ya fita a hankali daga cikin motar, ya kura musu ido. "Don Allah ku kyale Ni!" Daga haka ya shige gidan su, bayan tafiyar Jay! Asood ya kalle Hikmi. "Hiky me kake ganin ya faru? Jay Ya sauya daga yadda yake a baya, ko dai ya fara soyayya da Aanih ce?!" ."toh laifi ne? Dan ya fara soyayya da ita? Ni ban ga kome ba, sai tashin hankali da dimauta da take cikin ƙwayar idanu shi! Sai tsantsar damuwa da take cikin ƙwayar idanun shi! Yana cikin matsala sosai! Dan haka mu barshi na wasu lokuta kafin ya samu nutsuwa." "Toh ko yayi mata fyade ne?!" Juyawa Hiky yayi cikin mamaki! "Me yasa kake danganta shi da aikata hakan? Abokin mu ne! Sannan dan kai kana ganin kana aikata laifuka bai zama dole ni dashi mu aikata abin da kake zargi ba." Cizon bakin shi yayi tare da rintsa idanun shi, tun ranar da Aanih ta mare shi, yake niman mafita da zai rama, amma bai samu ba, shi yasa ya d'aura Jay akan yaje ya mata fyade. Idan kuma bai mata ba, tabbatacciya ce shi zai mata hakan koda kuwa akan mutuwar shi ce. .... "Assalamu alaikum warahmatullah!" Kallon shi suka yi cike da mamaki. "Jayyyyy! Zo nan." A hankali yake cire kafar shi, har ya isa gaban su. "Ya mutanen gidan?!" "Ya Jay! Zauna mana!" Inji Munih. "Yarona zauna mana!" Kura musu ido yayi kawai ya nufi sama abin shi, yana shiga ya rufe dakin shi, tare da sulalewa ya zauna. Abinda ya dawo kan shi, shine kamar shi da Sarkin Daura, babu kamar da yake da Baban shi na nan Canada, amma me yasa suka mishi haka? Waye shi? Me yasa suka raba shi da dangin shi! Me yasa suka sami damar nisanta shi da ahalin shi. Shi yasa yake jin cewa, akwai abinda ake boye mishi, musamman idan Kaka tana mishi kallon bai cika ba? Ashe itama bata amshe shi a matsayin jikarta bane. Shi yasa Munih take son sakar mishi jiki dan tasan babu wata alaƙa a tsakanin su! Lumshe idanunshi yayi tare da kwanciya a kasar dakin shi. Me yasa shi kaddarar shi tazo mishi a kaikace!? Me yasa kome ya lalace mishi lokaci guda? Taya Haka ta faru ba tare da ya fahimci cewa shi din d'an wasu ne?.... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *HAZAKA WRITER'S ASSO* (HWA) *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA SHIDA. Dafe goshin sa yayi tare da fadin. "Nayi hauka!" Ya kuma mik'ewa daga kwancen ya shiga ban daki, cika ruwa yayi a cikin abin wankar ya shiga ciki.    Ya kwanta ruwa na ratsa shi, kamar yadda yake takura Ƙwaƙwalwar shi da zurfaffa tunanin halin da yake ciki. Ya jima a cikin ruwan kafin ya cud'e jikin shi ya fito. Yana shiga dakin shi yayi arba da Munih.   Kauda kan shi yayi kamar baya Dakin, takowa tayi har gaban shi ta mika mishi madara mai zafi tayi tana kallon hadaddiyar surar jikin shi, wanda yake cike dam da gashi, sun kwanta luf luf.           Saukar da idanun ta tayi kan k'uguna shi, tare da d'ago kai.          Amsar madarar yayi tare da ajiyewa a saman mirror din shi. Sannan ya juya mata baya tare da goge jikin shi. Ya jima sosai yana gyara jikin shi kuma tana d'akin.     Yasan tana kallon shi dan yana jin haka a jikin shi. Bai gama ida tunanin shi ba, sai jin hannun ta tayi tana me rungumo shi ta baya, rintsa idanun shi yayi tare da janye ta daga jikin shi, ya nuna mata hanyar fita.                  Ba musu ta fita tana murmushi, tun da ya zauna a bakin gadon, yake kuma jinjina qarfin hakurin Aanih! Yarinyar tasan darajar kimanta ta kuma san hujjar da zata kawo maka dan ta kare kanta, duk da tana ganiyar matantakar ta.            Amma ba tab'a d'aga kai ta kalle shi da wata manufa ba, asalima idan ta ga yana saka kaya juya mishi baya take.         Fatimah tana da mugun kunya da kawaici, amma soyayya ta sata bude baki ta gaya mishi sirrin zuciyarta.       Bayan ya gama saka kayan shi ya dauki madarar ya sha, sannan ya tattara kome na d'akin ya gyara sabida Allah yayi shi mutum me mugun tsafta, baya son kazamta ko na miskala zarratin.        Yana gama sha ya kwanta, abin shi a d'akin. Bude kofar d'akin aka yi, ya d'ago kan shi, ya zuba mata ido.   Juya mata baya yayi dan bai shirya tambayar su,  abinda suka adana mishi ba.           A hankali ta shigo, tare da zama a gefen gadon, tana kallon shi. "Jaheed!  Meke faruwa ne?!" Rintsa idanun yayi kamar zai nutse cikin matashin ya furta da huci me zafi! Sannan yace. "Babu!" "Jay! Nasan kan! Na kuma san halin ka! Me zaka iya boye min bayan naga dimauta a kwaryar idanun ka! Bayan naga tarin tashin hankalin da suke cikin idanun ka. Ba a b'oyewa uwa ko uba tashin hankali."        Tashi yayi zaune ya kura mata ido, idanun shi suna kyalin kwallar da suke cike fam da ruwan hawaye. A hankali ya bude bakin shi zai magana sai kuma ya fasa tare da mik'ewa ya shiga daukar yar falmarar rigar shi!(Jacket top)    Sannan ya dauki takalmin shi na sawu ciki. Ya juya tare da barin d'akin. "Jay!"      Cak ya tsaya yana jin hawaye na sauka akan fuskar shi, ya d'an juyar da kan shi kad'an yana me d'an wai-waiye kad'an, dafa kafadar shi tayi ya sashi jin wani irin b'acin rai. "Shin ban cancanci jin meke damun D'an nawa bane?!" Ta faɗa a sanyayye. "Kiyi hakuri!" Daga haka ya saka kai ya fice daga gidan ma baki daya, yana zuwa inda ya ajiye motar shi ya sami Munih a cikin motar tana kallon shi.   Shiga yayi  tare da kwantar da kan shi.       "Ina zamu je namijin Zaki!" Kwantar da kan shi yayi tare da lumshe idanunshi,  ya d'aga mata yatsun shi biyu.         Sosai take jan motar bata tsaya ba, sai gidan Asood! Wanda yake Alberta town south.          Wata irin kasala yake ji, tare da tsintar kan shi cikin wata irin buƙatar mace wanda bai tsammaci haka ba,. Buɗe ido yayi cikin nutsuwa yaga ta koma Mishi Aanih.       Hannun shi ya kai kan cinyarta tare da matsawa, a cikin wata irin bugawa zuciya.            Murmushi Munih tayi tare da bin shi da wata yaudararriyar murmushi. Fita tayi ya biyo ta, har zuwa cikin gidan.       Tunda ya shiga, suka zube a falon, sam bai jin ya aikata abinda zuciyarshi take muradi! Amma halin da yake ciki ya wajaba akan shi ya sauke ajiyar da take jinin shi.   .....matse cibiyar shi yayi zuwa marar shi, ya zuba mata ido. "Jayyyyy! Ina sonka!"       Lumshe idanunshi ya kuma yi a karo na ba adadi. Ya sauke wata irin ajiyar zuciya.          Mika mata hannu yayi tare da b'alle rigar jikin ta, ya rungume ta.       Jin wani irin yanayi yake kamar ba zai. Amma yana ƙoƙarin ganin ketare iyakar shi, kamar wanda aka watsawa wani abu, ya fara wani irin barci. Me dauke da mafarkai.                    Yau ma ri ke da hannu. Shi take har bakin kofar da kullum sai an bude mishi haske yake hana shi ganin mutanen cikin su. A hankali aka bude kofar yana me addu'ar Allah ya bashi sa'ar kallon meke cikin gurin, kawai yaji an rufe kofar tare da cewa. "Babu wani magajin Izzah sai Zulum! Doly na cigaba da mulkina ko na sake aikata abinda zai zame muku mafarin bala'i."           Kamar giftawa sai tsintar kanshi yayi a wata masarautar na daban wanda shi kan shi ba zai iya cewa ga abinda yake gani ba, zuɓewa suka yi a gaban shi tare da bashi hanya matar tana rike da hannun shi har bisa wata kataga da akayi ta da d'anyen azurfa, sai kambu da aka sanya mishi. Akan shi wanda ya haifar mishi da wata irin yanayi na musamman, bude idanun shi yayi ya kafe shi akan ta, sanye cikin kaya me launin ruwan ja, kanta sanye da wata irin kambu duk inda ta wuce sai ka ga mutanen sun zube akasa rigar jikinta ja ne.     ....kuma yana haifar da jini sabida jikewar shi, tana nisa gaban shi ta kalle shi tare da zare siririn jar igiyar da take gaban rigar ta. Taja rigar ta zube daga jikinta kyakyawan surar jikinta me cike da kyau da kuma haiba.        Suka bayyana mishi. "Jalaludeen! Karka kuskura ka amince da shi ba Ziryana bane Zulum ne!"              Juyawa yayi tare da lek'awa yana kallon su, a daidai lokacin da ta dauki hannun shi ta sanya a k'ugunta, kallon fuskar ta yayi, tana murmushi tace mishi.. "Jayyyyy! Baka yarda Aanihn ka bace?!"              A hankali ya shafa k'ugun shi, jin wani abu yayi tare da fidda shi, kafin ta fahimci kudirin shi, tuni ya soka mata sai da ya biyo ta bayan ta, daidai shigowar wasu wanda ba zai iya cewa gasu waye ba, kawai sai ganin yayi Fatimah ta yanki jiki zata zub'e ya riketa a kirjin shi, gefen shi kuwa matar nan ce ta fashe da Dariya bayan ta rikid'e zuwa wani baƙin bamaguje tare da girgiza jiki ya b'ace yana faɗin.       "Indai zaka iya kashe Macen da kake so tabbas Ni d'aya zan cigaba da mulki tare da...."              "Jayyyyy! Dole kai.... Har olau  baka kaunata?!" Tayi mishi tambayar hancinta yana zubda jini, haka ma gefen bakinta yana zubda jini.          "Rayuwata! Farin cikina! Sadaukarwa ce a gare ki, Aanih kar ki manta i...." A firgice ya farka daga mafarki da yake, tsintar Munih ba yayi a kirjin shi tana wani irin barci me cike da nutsuwa tare da jin dadi, d'agota yayi tare da ganin babu kome a jikin shi, daga shi har ita.     Mamaki ce ta kama shi ya daki kanshi tare da tir da abinda ya faru.         Hankad'e ta yayi cikin tashin hankali ya dira daga gadon, yana tangaɗi har ya shiga ban daki, ruwa ya sakarwa kan shi tare da sake kuka.. sabida ganin yadda  tsinci kan shi cikin mummunan yanayin.          A gurguje yayi wanka tare da tsame jikin shi ya fito,ko inda take bai kalla ba, ya shirya tsaf sannan ya nufi waje ɗaukar wayar shi tare da mukulin motar shi yayi ya fito a sanɗa kamar wanda yayi wani mugun abu, yaba gudun kar asirin shi ya tonu. "Jay!!! Ina zaka tafi ka barni cikin wannan yanayin! Bayan ka lalata min rayuwa ta! Shine zaka gudu kabar ni!" Ta karshe maganar cikin Kuka, me mugun tasiri a zuciyar wanda ya saurara, cak ya tsaya tare da juyawa yana kallon yadda jikinta yake rawa, hatta halittar jikinta girgiza yake. Cikin matuƙar bakin ciki da nadamar rayuwa, zuwa yayi gabanta ya tsaya tare da taimaka mata ta saka kayanta, ganin yadda jikinta ya b'aci da jini ya sanya shi zaro manyan dara-daran idanun shi akanta, yana kallon fuskarta! Jikin shi kamar wanda aka jona mishi lantar ki haka yake rawa. "Munubiya! Gaya min me ya faru? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji wani laifi nayi haka. Ka jarabce ni da zina! Ya Allah na tuba ka yafe min!" Rungume ta yayi hawaye na zuba daga idanun shi, yana d'aga a bayan ta, ya kuma k'amk'ame ta, sabida bai zaci haka ba. "Shi kenan! Ya Jay, ka raba ni da abinda ko wacce mace take takama da shi! Wani namijin ne zai yarda banin aikata ba, ka rabani da wanda zai zame min abokin rayuwata! Ya Jay nasan ba aurena zaka yi ba! Me yasa kayi min haka? Me yasa na cancanci haka daga gare ka! Meye laifin kaunar da nayi maka. Nagode zaka iya tafiya, nima zan iya tafiya. Tunda ka iya tafiya Nigeria da baka da kowa kabi wata mace ai ba damuwa me zaka yi da ni!" Ta faɗa cikin wani irin kuka, tare da kifa kanta a kirjin shi, shafa bayan ta yayi, sannan ya fara da cewa! "Inji waye yace bazan iya aurenki ba? Kiyi hakuri! Insha Allah zan duba Alamarin amma muje asibiti!" "A'ah ba zan iya zuwa ba, in kara tozarta kaina! Bazan kuma na wulakanta kima ta ba, kawai ka kai ni gida, ka mai dani gida." A birkice tayi maganar ga baƙi ɗaya ya gigita mishi hankali, ga kukan da take, kasa motsawa yayi yana kallon abin da yafi karfin tunanin shi. Shi ba abin yayi ta kuka ba, sai na bakin ciki. Kamar wanda aka wurgo Asood ya shigo, ganin halin da take ciki ya sashi juyawa da sauri, yana faɗin. "Jay! Me ka aikata haƙa? Ƙanwarka ciki d'aya itace ka haƙewa, haba Jay!" .wani irin firgici ne ya kuma cika zuciyar shi, a take ya juya da sauri yana son yayi mishi bayani ya dakatar da shi, yana faɗin. "Amma kasan Ni nake sonta? Shi ne ɗan bakin ciki, ka raba ta da abinda nake burin samu a jikinta! Toh ka sani ban yafe maka ba! Kuma daga yau babu wata aminta a tsakanin mu! Kuma sai na gayawa kowa ya san abinda ka aikata min." "Don Allah ka saurare ni? Ka. Fahimci abinda zan gaya maka, bana cikin hankalina nayi a..." "Fitar min a gida! Nan kayi ta ihu sai ka lalata min rayuwar Khatoon! Ashe ba nata zaka lalata ba, rayuwa na zaka lalata me zaka gaya min maciyi amana, haka kaje ka dawo baka rama min ba." "Asood! Ban aikata kome ba, batun Aanih kuma ka ajiye a gefe! Wallahi ban aikata kome ba, Aanih ta fito daga cikin babban gida ne! Matukar na tab'a wani abu da yake kimarta toh kamar na tab'a kimar masarautar suce, shine masarautar ta uku mafi kafuwar tarihin musulunci a kasar hausa! Don Allah karka min haka.!" "Kai jin ka zan zuba maka ido ne bayan ka lalata min rayuwa, wato nice mara daraja! Aanih kuma itace mace mai daraja! Nagode da ka fada min bani da daraja! Asood kaga sonkai ko? Dake ba iyayena suka hai....." Shiru tayi tare da rab'a gefen shi, zata wuce ya dawo da ita sa karfin bala'i! "Me kika ce? Gaya min me kika faɗa? Me naji zaki ce? Wato dan ba iyayenki bane suka haife ni ba ko?" Wani irin tsoron shi ne ya kama su dukkan su... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *HAZAKA WRITER'S ASSO*      (HWA) *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA BAKWAI. Kafe su yayi da ido, a sannu ya riko hannunta suka fita tun kafin ya isa inda motar shi take jefata yayi cikin tashin hankalin. A da yana jin zai iya magance matsalar shi, amma jin abinda Munih ta faɗa ya kuma sanya mishi tashin hankali sama da wanda yake ciki, domin bai tab'a kawowa kome zai lalace mishi lokaci guda ba. Taya ma haka zai faru? Bayan shi. Dukar motar yayi cikin tsawa. "Ki min shiru" ya daka mata tsawa, had'iye kukan da take yayi cikin tsananin tsoro, tana kallon shi har suka isa gida. Kuka take, ga baki daya baya cikin nutsuwar shi dan haka bai damu da halin da take ciki ba. Yazo ya fincikota tare da nufar cikin gidan da ita, Sai dai duk da wannan wulakancin ya samu. Baban su da Maman basa nan, dakin shi ya wuce tare da barin Munih a falo, itama ta lallaba ta shige tare da fad'awa ban daki tayi wanka. .... Tunda ya shiga cikin dakin shi, ya zauna yana nazarin abinda ya faru. Tare da girmama laifin da Munih take zargin shi ya aikata. In dai zai iya hakuri bai tab'a kusanci Fatimah Khatoon ba, toh baya jin zai iya aikata abin da Munih take zargin shi. Tafka yake yana kuma warwara, mik'ewa yayi tare da safa da marwa. Karshe ya zube a gadon tare da zuba tagumi yana nazarin tashin hankalin da yake ciki, idanun shi ne ya sauka akan kofin madarar da Munih ta kawo mishi, cikin nutsuwa ya isa gaban kofin ya dubi kofin da kyau. Sannan ya ajiye shi dan bai ga abin da yake nima ba. Yana jin an buɗe kofar d'akin shi, bai kai da ya juya ba, ya cigaba da abin da yaƙe. "Ya Jaheed!" D'aga mata hannu yayi tare da nuna mata hanyar fita! Sannan ya cigaba da kallon madubin. Yana kuma hango iyakar kamar da suke da mutane biyun da ya gani a nigeria, indai har zasu iya samun shi a matsayin d'an su, ya ga kuma tarin soyayyar da suke mishi a kwayar idanun su, tabbas. Har abada ba zai tab'a rasa mutanen da zasu yi kuka bayan mutuwarsa ba. "Ya Ja...." D'ago kai yayi cikin nutsuwa, ya zuba mata rinannun idanun shi. Tunda taga haka da sauri ta juya zata fita. Bai damu ba har ta fita. Hannu bibbiyu ya saka a kan shi, yana me jin haushin abin da tayi mishi (😒🤣 dan banza me halin gado) --- Sokoto... Wani irin zazzaɓi ne ya rufe ni, tun bayan fitar su Baabi. Nake kwance a kasa, ina shashekar kuka. Ina ji ina gani, sun kasa bani abin da nake so. Wuni nayi a d'akina ko waje naki fita, Abinci kuwa da Kan shi yake kawo min, ina kwance sai ga Aunty Aina'uh tazo. Kanwar Mahaifiyata ce, kauda kai nayi naki kallonta, domin babu abinda zasu iya min a wannan lokaci. Kura min ido tayi na wasu lokuta kafin tace. "Yarinya!" Yarinya suna ne da suke kirana da shi, sabida Sunar kusan kakata mace wacce ta haifi Mahaifiyata itama Fatimah ce, haka ma Umman Baabi itama Fatimah ce. Shi yasa suka tsayar da Yarinya kawai kira na dashi dashi. Kuma bayan haka Ita kakata da ta Haifi Mamana, Kanwar Kakata da ta Haifi Baabi ne, haka ma Dattijo Ƴaƴan kaka na ne. Tsura mata ido nayi, sannan na juyar da kaina. "Ki shirya kayanki, zamu koma Abuja dake" Juya mata baya nayi tare da cewa. "Babu inda zani, sabida na san Jay zai dawo." "Ai kuwa, da kin cire yaron nan a ranki domin babu wanda zai bashi ke, sabida babu aure a tsakanin ku" Mik'ewa nayi zaune ina kallon ta. Cikin jin haushi nace. "Ba zaku ba shi ne ba? Akan me ne? Gani nai rayuwata ce, kuma ina da yadda na tsara. Dan haka duk abinda zaku yi sai dai kuyi hakuri amma kamar na sami Jay. Kuma babu inda zani," Kura min ido tayi sannan ta fita ranta a b'ace, ina zaune Baabi ya shigo cikin b'acin rai yana kallona. Sunkuyar da kaina nayi. "Shirya kayan ki, zaki tafi abuja." Ya faɗa min cikin tsawa, a matukar tsora ce na hada kayana ina share kwalla. "Baabi na!" "Fito nace" "Amma Baabi.... Id.." "Fatimah bintu Zahrah." Cike da mamaki nake kallon shi, kwalla na zuba min daga Idanuna. "Daga yau kar na kuma jin sunan Jalal a bakin ki, idan kuma na kuma jin wani abu makamancin haka! Toh Insha Allah zan baki mamaki, na fasa aurar dake ne, sabida wasu dalilai. Kije kema ki samu nutsuwar zuciya. Idan Jalal mijinki ne, wallahi duk inda kike zai zakulo ki, idan kuma ba mijin ki bane, Allah ya baki wanda ya fishi. Bana son kina kuka akan d'a namiji, sai naga kamar na kasa amsa sunar Ubane" A hankali na isa gaban shi, nace. "Baabi, idan na tafi zaka yi farin ciki ko? Toh zan tafi. Kuma zan rufe batun Jay!" Dafe kafad'ana yayi cikin jin yace. "Dakyau Sarauniyar Aanih muje ku tafi." A sannu muka fito, Baabi yana bani labarin abin da ya shirya min, murmushi nayi tare da goge jinin da yake d'iga daga hancina, dan ya zame min jiki zubar jinin daga hancina, kuma ina kan magani. "Wallahi yau naji zafin abin da Yarinya tayi min, dan nace ta shirya kayanta zamu tafi Abuja sai ya zama laifi. A gani na wannan damuwar da kike ciki, har da rashin dumin uwa, dan da Yaya Fareedah tana raye ba zaki zauna kina hauka akan Yaron karami ba. Kin zauna kina kuka akan shi kina asarar hawayen ki, gaki kamar babba a ido, amma shirmen ki yafi karfin ki, sakarya." Masifa take tare da watsa hannunta kamar zata buge ni, haka ta gama jarabar ta ban kulata ba. ...... Har bakin motar da zai kai mu tashar jirgin sama,Baabi ya raka mu. Tunda muka shiga na juyawa Aunty Aina'uh kai, naki kula ta. Tayi mita tayi masifa, kai karshe ta watsar dani bata kuma bin ta kai na ba. Har muka isa tashar jirgin, bayan wasu mintuna muka bar garin sokoto. --- Kwantogora... _"gadon hari sai fana! Ramin kura sai Y'ay'an ta, wutsiyar raƙumi tayi nesa da kasa, tauraruwa me wutsiya! Ganinki babu Alkhairi! An gaida Uwar makirai! Shugabar munafukai! Ranki shi dad'e Fulani Hasiyah"_ Duk wannan kirarin wani tsohon mutum ne yakewa Fulani,, zama ta gyara cikin Izzah tare da zuba mishi ido, tayi tana watsar da hannunta. " Fawa biu tana ɓata hankalin kuɗa" Dariya mutumin yayi sannan ya cigaba da cewa. " Allah ba ya ba gwanni'n tona tsaba. Dan haka dukkan ku lokacin ya karato!" Wani irin kallo take mishi, tare da kura mishi ido. "Me kake nufi?" Ta faɗa da mugun karfi. "Idan rana tafito tafin hannun bai kare ta! Duk yadda kike tsammaci abin ya zarta haka! Shi daya jinin shi a tafashe yake." Murmushi tayi cikin mamaki sannan tace "Ai ba domin tsawo a kanga wata ba, Ka fahimci hak?" Dariya ce ta kama shi sannan ya kalleta kafin yace. " A yi, a gamma, ta fi takamma, gobe a koma." Cikin jin haushi abinda bada yake gaya mata tace. "A dade a nayi saikaskiya, karya fure take bata yaya, dan haka nayi da wanda suka zarta Jaamal. Balle kuma Ubanshi!" Girgiza kai yayi sannan ya fara magana cikin budadd'yar murya yace. "Tabbas! Gamayyar halittar shi sak take da halittar mutanen b'oye! Shi kan shi har yau bai san kan shi ba, karki kuma sakewa ya cimma matsaya akan kan shi! Matukar haka ya faru! Toh tabbas a cikin ido, ake tsawirya." "Kana nufin akwai abin da zai razana ni ne?" Ta tambayi mutumin. "Ashe ana tsoron inna? In ji 'ya'yan mayya! Me yasa kika razana? Bayan ke kanki baki da hanyar kare kanki, kiyi mubaya'a, domin shi ba gama garin mutane bane! Murucin kan dutse ne!" Ya gaya mata haka cikin nutsuwa ba tare da yaji kome ba. "hmmm!Abin kasuwa, na mai ciniki ne. Wasa farin girki, a shirye nake na kutsa cikin majalisar masarautar Daura na dakatar da d'an iskan da zai kawo min iyaka da mulkin masarautar." Ta faɗa tare da sake wata ƙatuwar huci. "Ba zaki iya ba, sabida daga ranar da ya shiga masarautar muryan kowa zai sauka kasa, sannan shi kan shi zai kasance Sarkin da ba a tab'a samun irin shi ba tsawon karnika ɗarai. Shine sarkin da yake da gamayyar halittar Mutum da aljan! Kuma shine sarkin da zai jagoranci al'ummar alkarya guda biyu, soyayya da sadaukarwa itace zata kuma dakatar da wannan matsayi biyun da zai taka. Da a ce uwar shi ta sami damar kusantar kujeran mulkin kasar dafur, toh da babu hatsabibiya irinta, shi kuma zai kwantatta wani kuskuren da ba kowa ya tab'a aikatawa ba. Tabbas zai aikata! Kaunar da aka yi shi domin Ziryana da Fairo zai tabbata! Zai bar mata kambun wanda haka shine abu mafi daraja a duniyar aljanun! Kuma kuskuren ga rayuwarta, idan ta saka kambun zata iya karban sadaukarwa! Kuma zata iya bin sahun Ziryana da Fairo! Matukar ya fahimci hannunki a illatar mishi da ahalin shi. Azzabar zata rub'anya, ina jin kamshin tozarci, ina jin kamshin mutuwar ki! Dan sai kin gwammace, mutuwar sau dari sama da rayuwa sau daya! Amma ba zaki fahimci haka ba, sabida baki ga zahiri ba, baki ga abinda yake tunkaro ki ba, Magajin Izzah yana tafe nan da wani lokaci, zaki fahimci haka ne lokacin da kika tsinci kanki a gaban shi." Wani irin zufa ke karyo mata kamar an watsa mata ruwan zafi, tsoro da tashin hankali, sun kamata. Bata san meye mafita ba. Amma dake zuciyar ta, ta gama kangarewa daga aikata laifukan son zuciya ya sata mikewa. "Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne. dan haka bazan sare daga cikin tafiya ta ba, na Barka lafiya " tana fadar hakan ta bar dakin baki daya. Dukar kasar shi yayi tare da fashewa da dariya. "Hasiyah! Kinyi gaggawar buɗewa makiyarki dama..." --- Daura.. "Jaamal! Insha Allah yaron zai dawo! Amma shima kaddarar shi, akwai ban tausayi, dan ba lallai bane. Ya sami soyayyar shi, koda ya samu akwai yuwar ya iya rasa kome na shi. Jalal! Sarki ne da wasu suke jiran shi, kuma muma nan muke kiran shi, ban san yadda zan maka bayani ka Fahimta ba, amma an sami gamiyyar halittar shi. Yaro karami amma ya taso tare da kadarorin Mahaifiyarshi, kayi hakuri zai dawo da kanshi amma kafin nan ka nime Najim ya tafi niman shi, ka kuma tabbatar da ya janyo hankalin shi gida. Mahaifiyarsa tayi iyaka kokarinta na dakatar da wasu abubuwan, daga ciki kuwa har da aikin da ba nata ba, da ta rayu da duk wannan fitinar bai wanzu ba, da tun shekaru ashirin da bakwai kome ya zama tarihi, sau uku tana zuwa nan domin ta dakatar da matsalar da take bibiyar mijinta da kuma masarautar baki daya. Sai dai abinda na gani ya sani kin gaya mata gaskiya. Domin na fahimci bazata iya kawo karshen rikicin masarautan ba, amma Insha Allah itace zata haifi wanda zai dakatar da abubuwan da yake faruwa. Yarinyar tayi nisa, gurin son dakatar da kome, amma Allah bai nufa ba, sannan kayi ƙoƙarin shiryawa Najim tafiyar dan haka ne zai samar maka bayanin da kake bukata." Shiru Kawu yayi tare da goge kwallar idanu shi, sannan yace. "Baba, shima Jalal din rasa shi zanyi ? Kamar yadda na rasa Mahaifiyarshi" Girgiza kai yayi, cikin damuwa yace.. "Bana tunanin haka! Amma tabbas shima zai rasa nasaba da yadda ka a rasa rayukan wasu! Idan ta kama abinda yake so ne tilas zai iya rasata. Amma muna namu, Allah yana nashi, kuma nashi ne gaskiya. Amma tabbas zanen kaddarar ku, kusan guda ce.... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!    {CIGABA KWARKWARAH}    *HAZAKA WRITER'S ASSO*      (HWA) *Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!* Mallakin   Mai_Dambu Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️ SHA TAKWAS. "Karka damu, kome zai zo mana da sauki Insha Allah zamu tsaya da addu'a Allah yana sane da kome."      Magana masu dad'i da ma'ana Baba Magaji yayi mishi, tare da nuna mishi kar ya takura kan shi akan lallai sai Jay ya dawo.            ---- Calgary.... Yau ya cika kwana bakwai da dawowa, doguwar magana bai hada shi da kowa ba, asalima zai fita da sassafe zai kuma dawo sunyi barci. Duk suna lura da shi.        Karfe sha biyu na dare, ya tura kofar falon ya shigo a hankali, tare da rufe kofar. Sannan ya cire takalmin shi, ya fara takawa a hankali kamar mara gaskiya.       "Bamu san laifin mu ba? ranka shi dad'e! Shi yasa muka tsaya jiranka ko zaka dawo da wuri ka gaya mana me muka yi maka da zafi haka?"          Cak ya tsaya bai kuma juya ba, kawai tsoro ne ya dabaibaye zuciyar shi, idanun shi suna cika da kwalla.               "Mujaheed me muka maka da zafi?"  Mamah ta tambaye shi, a sanyayye ya juya tare da zuba mata ido, kafin ya sunkuyar da kan shi.        "Na kasa fahimtar kome, na gaza gane waye ni? Taya zan iya fuskarta ku na tambaye ku wanene Ni? Ba zan iya tuna kome na rayuwa ta ba, amma Mamah ina jin waɗancan mutanen sune Ahalina!" Ya faɗa a sanyayye kamar zai fashe da kuka. ....cikin tsananin mamaki tare da kallon Juna miji da mata suka yi tare da isa gaban shi, suka rike hannun shi, suna cewa. "Mujaheed! Gaya mana waye ya faɗa maka ba mune muka haife ka ba? Waye ya gaya maka?"       Zama yayi cikin tashin hankali, sannan ya fara basu labarin abinda ya faru! Har zuwan shi nigeria. Shiru suka yi kafin suka mike tare da ce mishi. "Kaje ka kwanta, zamu duba Alamarin nan da wani lokaci."   Girgiza kai yayi tare da zama a bakin matakalar benen yace. "Hmmm! 'Yar bori, ba ta kallon bori. Ku fidda Ni cikin duhun damina mana"                Takawa baban shi yayi sannan yace. "Ba a hana ma bada rago, fata. Dan haka kaje kamar yadda muka ce! Domin gudu da wai-waiye shi ke kawo zargi"               Mik'ewa yayi cikin nutsuwa bai kuma magana ba, amma tabbas ya fahimci abinda Baba yake nufi ba lallai bane yaji abinda yake bukata ba.       .... Koda ya shiga cikin dakin shi, wanka yayi tare da alola, yana fitowa ya gabatar da sallar isha tare da nafilla, sannan ya kuma jima yana addu'a.      Allah ya kawo mishi dauki cikin duhun da yake ciki. Sannan ya kwanta. Yana ta sake sake, har barci yayi gaba da shi.          --- 3:38am. "Jalal! Jalal!! Jalal!!!" Yaji ana kwala mishi kira, buɗe ido yayi a hankali yaga wannan matar ce da baya ganin fuskarta.       Riko hannun shi tayi suka fita, a hankali tare da barin d'akin. "Jayyyyy! Jayyyyy!!! Yaji ana kiran shi a wani daki can da kofar shi yake rufe da katon kubba(wato katon kwad'o)           Kallon matar yayi cikin son yin magana kafin yace wani abu ta buɗe kofar me cike da haske, da sauri ya kare fuskar shi.  Da gudu ya koma dakin da yake jin ana ihu ya buɗe, ganinta yayi cikin jini, a kwance. Cikin tashin ya shiga ƙoƙarin daukar ta sai ji yayi an rufe kofar d'akin, duk yadda yaso ya fita ya kasa.                    Girgiza kanta yai tare dakyar ta bude ido tana ganin shi ta sake murmushi. "A sauran abinda ya rage min, har yanzun baka sona!"       Cikin wani irin tausayi ya d'agota,  ganin hannunta yayi sun yi baya, alamun ta rasu. "Fatimah!!!" Ya kwala mata kira, kallon dakin yayi tare kallon Muniba da ta makale shi kamar zata shige jikin shi. Yakince ta yayi da karfin tsiya, tare da kifa mata mari, sauka tayi da sauri, tana kallon shi. "Fita!" Babu shiri ta kwashe kayanta tayi waje.   Tashi yayi tare da yin alola, sannan ya gabatar da sallar nafilla, sannan ya zauna har zuwa lokacin sallar asuba.     --- Daura... "Zaka iya, toh gashi ka Fatimah amma bari na kira mahaifinta naji." Wayar shi ya ciro a cikin aljuhun rigar shi, ya danna Number Aaryaan sun jima suna magana sannan ya kalli Najim ya gaya mishi kome akan Jay.       Da inda zai sake shi. ..... Sallama Najim yayi mishi sannan ya bar gidan.                   --- Yau ki manin sati biyu, rabona da sokoto, kallon yadda kome ke tafiya cikin wani irin yanayi ya sani jin kewar Jay!    Ruwa ake tsugawa, kamar da bakin kwarya. Na nutse cikin bargo ina kuma tuna kwanakin da muka yi dashi a Damagaram, wani irin son shi da kuma kaunar shi suka kamani.         Abubuwan da suka shiga tsakanin mu, ya fara dawo min. A hankali, kafin zuwa wani lokaci kasala da bukatar abokin rayuwa ya taso min, lumshe idanuna nayi cikin jin haushin abinda ya faru. Da ya saurari abinda yake raina ince da haka bai faru ba.            ... Shi kallon wacce maza suka gama hawa da sauka akaina yake bayan ni nasan ba haka bane hatta iyayena kallon bazawarar da tasan mu'amala da namiji suke min.       Shi yasa ma nake kokarin b'oye yanayin da nakan tsinci kai na, sabida gudun kar su min wata irin fahimta na daban.    Lumshe idanuna nayi lokacin da wani irin sanyi yake ratsa tafin kafana, tare da wani uban dad'i, a hankali barci ya fara dauka na, tare da saukar min da wata kasala me mugun cin rai,  idanuna nake son budewa amma na kasa, sabida jin wani karsashi kamar ina tare da D'a namiji.     Kafin wani lokaci, na sauke wasu ta tagwayen ajiyar zuciya, tare da rike zanin gadon da karfi.  Ba zan iya cewa kome ba. Amma na farka naga na ɓata jikina, wani irin kunya ce ta kama ni lokaci daya na hango zanin gadon a can kasa.     Rigar jikina kuwa ban san ya akayi na cireta ba, wani mugun tsoro ne ya kamani, yaushe na aikata wannan tashin hankalin?      Kamar mafarki nayi? Na tambayi kaina, kafin na kuma mik'ewa zuwa ban daki nayi wanka  na fito. Kallon agogon dakin nayi tare da karfe huɗu da wani abu.        Shiryawa nayi cikin doguwar rigar, na yafa mayafin shi na gyara fuskana sannan na tako a hankali.            Na nufi falon kasa, inda nake jin muryan ana hira, tun daga matakalar nake kallon mutane.              Kamar na juya sai kuma na daure na sauko, ina jin ba dad'i a raina. Kallo daya nayi musu ban kuma marmarin kallon su ba, na wuce inda aka jera abinci. Kofi na dauka na zuba kunun tsamiya dan ban karya ba, har huɗu na yamma.           Sai farfesun kayan cikin da na zuba, na wuce abuna ban kuma kallon inda suke ba, dan son magana.       "Yarinyah baki ga mutane bane?!" Inji Aunty Aina'uh, idanuna ne suka cika da kwalla nace. "Ina wuni ku?!" Daga haka ban kuma na wuce sama.       "Amma kamar yar Fareedah?" Matar ta faɗa dan su uku ne da wasu yan mata. "Wasilah ita ce, Aanih Fatimah Khatoon." Aunty Aina'uh tai maganar cike da takaici. "Ba naji anyi mata aure ba? Kamar an sami matsala ranar auren?" Numfashi Aina'uh ta sauke sannan tace. "Sace ta wani yaro karami yayi, shine dalilin da aka fasa auren, amma mahaifinta ya ajiye sarautar sabida ita, amma dake bata da mafadi shine har take kukan tana son wancan yaron da ya sace ta, shi kuma baya sonta"           "A'ah yana Sonta, kawai bai san meye ake kira da soyayya bane, kawai yaƙi amsawa ne sabida ba zai iya daukar laifi biyu bane." Inji matar.         "A gaban Jama'a yace baya kaunar ta, ya kuma ce ba zai tab'a auren bazawara ba, toh meye yafi haka muni? Don Allah ki bar wannan maganar" inji Aina'uh,              Gyara zama matar tayi sannan ta kalli Aina'uh kafin tace. "Ba dan tayi girma ba, da na nimawa Asood auren ta, sabida ina Son ya nutsu. Macen da tafi shi hankali ta dace dashi ba wacce ya fita wayo ba, don Allah ko zan sami wannan kyautar daga gare ku?"          Shiru Aina'uh tayi sannan ta kuma kallon Hajiya wasilah, sannan ta sauke numfashi kafin tace. "Mai ido daya ba ya gode Allah ba, sai ya ga makaho. Me yafi haka dad'i? Wasu na gudun ta ke kuma kin daukawa d'an mijinki. Gaskiya mun gode sosai. Kuma ita ma zata amshi tayin da amfani."         " Alkama bissa dutse, Allah shi kan bashi ruwa. Karki manta d'an tsakon da uwar shi ta kasa Allah ke ci da shi ba mutum ba, ni a gurina babban alfarma ce kuka min, na bawa Asood ita ko babu kome zata zame mishi garkuwa."       Sun jima suna tattaunawa akan abinda ban sani, dan haka bayan tafiyar Hajiya Wasilah,Aunty Aina'uh ta shigo min ina cin abinci, wanda kusan na saka tunanin akan abincin.         Zama tayi bayan tayi sallama, sau daya na kalleta gabana ya fad'i, sannan na cigaba da cin abincin. "Yarinyah, ina son muyi magana dake, wanda zai taimaka miki."      "Uhm!" Nace mata ba tare da na kalle ta ba, ta tsani yadda nake mata wannan uhhm da hmm, Ni kuma dabi'ata ce nayi hakan. "Hajiya Wasilah ce take son ko zaki amince da d'anta da yake karatu a Canada?"                 Furza da namar bakina nayi tare da juyawa na zuba mata ido, sannan na kuma mai da hankali na, kan abinda nake ci.           Cigaba tayi da magana tana faɗin. "Amma nayi tunanin kafin nayi miki magana na Fadawa Ya Aaryaan."       Cikin bakin ciki na zuba mata ido, kafin nace mata. "Hmm!"      "Kamar ya hmm? Ki buɗe bakinki kiyi min magana, bawai kice min hmm.         Kamar yadda taso nayi magana fir naki kula ta, kuma nayi nasarar kular da ita, karshe ta fita a dakin tana banbami na rena ta, bayan ba reni bane iya gaskiyar kenan.   ........          Ta kira Baabina ta gaya mishi abinda nayi mata, kai tsaye ya gaya mata gaskiya babu ruwan shi, tunda bana son haka ta barni. Ai kuwa ta cika ta batse.       --- Ƙarfe sha biyu na rana ya sauka a garin Calgary,  Kawun Muddam shi yazo ya dauke shi, cikin girmamawa ya gaishe shi tare da gabatar da kan shi.   Murmushi suka yi lokaci guda sannan Muddam yace mishi. "Kar ka damu, tunda Aaryaan ya gaya min kana zuwa, na sanya aka shiga niman inda zaku haɗu, wannan takardan shine inda yake yawan zuwa shan coffee, nan kuma gurin da yake zuwa motsa jiki. Da sauran su dai zaka gani."       "Amma bai da abokai ne?" Shiru Muddam yayi na wani lokaci, kafin ya ce. "Akwai wani abokin karatun Aanih Me suna Hikmi, ina ga zan duba maka shi."              "Haka yayi min!" Daga nan suka wuce gida.            --- Zaune yake a gaban ruwa, yayi nisa sosai cikin damuwa, shi kan shi bai san lokacin da ya b'ata a gurin ba.          D'aura kanta tayi a kafad'arshi. "Ya Jay! Ina sonka. Kuma ina,"             Juyawa yayi tare da zuba mata ido, kawai yana jin wani irin zafi akan ta. "Fatimah!"         Da sauri ta d'ago kanta idanun ta cike da kwalla. "Ya Jaheed, sabida bana gabanka shine kake min kallon wacce karuwa....."                   Kallonta yayi na wasu lokuta, kafin ya mike tsaye tare da riko hannun ta, ta mike tsaye tana kallon shi, jan iska yayi cikin nutsuwa sannan ya riko hannunta suka nufi cikin gidan, ba tare da wani damuwa ba ya nufi dakin shi da ita.       Cillata yayi saman gadon shi, sannan yabi kanta. Idanun shi rufe kamar yadda yake tunani.   Kuka tasaka tare da rike hannun shi, tana me cewa. "Don Allah karka min haka, bana so"        Jan rigar ta yayi wanda yayi dai-dai da shigowar Mamah,  a tsora ce ta sake kara tare da, isa gadon da karfin ta. "Mujaheed! Sakamakon da zaka mana kenan? Haba Jaheed meye laifinta? Zaka iya tafiya ka bar mu, amma bamu ne muka haife ka ba. Kaje ka nime... #Mai_Dambu... 10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: SHA TARA. Cak ya tsaya kamar wanda aka watsa mishi ruwan zafi, haka ya sauka daga kan Munih ya kalli Mama hawaye na zuba daga idanun shi.               bude baki yayi zai magana. Ta d'aga mishi hannu.     Shekaru Ashirin da daya Baya. (Mu koma kwarkwarah 🤣) ..... Shekarun mu bakwai da aure, Allah bai bamu Haihuwa ba, dake Harisou yana aiki a Saudiyya a matsayin malamin Faransaci a wata jami'a, haka ya samu Bama zuwa ziyara akan lokaci sai bayan shekara daya. Muke zuwa, haka yayi matukar tasiri a rayuwar auren mu, ga kuma Innar shi da take takura mana akan haihuwa, shi yasa ya dauke ni muka daina zuwa. A shekarar ne Allah ya dube mu da rahama, mun zo hutu Damagaram..har mun gama zamu koma amma dole sai mun je gida gurin dangina, koda muka zo sai da muka yi kwana uku, a ranar da zamu koma ne Allah ya bamu kai, tun daga nesa nake gano tsuntsaye suna ta shawagi, kawai sai naji ina son na isa inda kake duk da a mota muke. Har zamu wuce nacewa Harisou. "Kalli can kamar wani abu ne don Allah kar mu wuce mu duba." "Bana son damuwa! Yanzun sai ki ga ba kome bane kawai dai shirme ne." "Don Allah kaji" dakyar ya amince min. Tsayar da motar, da sauri na fita, koda na isa saman sahara kawai me zan gani, bugu har na juya zan bar gurin kawai sai naji ina da shakku akan buhun da na gani. Dan haka na dauka tare da bude bakin buhun, abin mamaki. Kawai ido biyu muka yi da kai, kana jan numfashi. Kafin ka suma. Sabida zafin sahara, dan haka cikin tashin hankali na dauke ka, tare da nufar cikin motar da kai, daga nan muka nufi garin Damagaram da kai, inda muka sami likita ya duba ka tare da sanya maka ruwa. Koda ka farka kaki magana duk abinda zamu ce maka shiru kake mana. Kwanaka biyu aka sallame mu, ba tare da damuwa ba muka kai ka gidan iyayen Harisou, duk da sunyi maraba da kai, amma mahaifiyar shi taki magana akan ka, dan dole muka tafi da kai Saudiyya. Sai a lokacin ka fara magana, shima sunanka ka fada mana daga kace Saraki, sai kace Magajin Izzah, sai kuma Jay. Da zaran mun matsa maka da tambaya sai ka fita daga cikin gidan. Tunda muka fahimci haka sai muka daina, damun ka. A hankali ka taso cikin kulawa har kasami shekaru goma sha daya, kafin muka sami haihuwar Munih. Tunda na haifeta ka rage shiga cikin mu, kawai dai kana taimaka mana da renonta, har zuwa lokacin da ta fara tafiya, Jay sai da ka shekara sha shida kafin muka san cewa kana magana kawai baka cika surutu bane, ka taso baka da kiriniya baka shiga hidimar yara, ko a makarantar ku. Malamai suna fada cewa kaina rayuwa ne kamar Basarake. Baka son reni, kuma baka rena kowa, a shekaru sha bakwai, ka kammala sakandare. Lokacin an dawo damu nan Canada. Baban Munih yaso kayi soja kace kai likita zaka yi. Dan haka ya kyale ka, shekara ashirin da hudu cik ka gama matakin farko na digirin ka, daga nan kuma, muka so gaya maka waye kai sai muka fahimci kana farin ciki da yadda kake rayuwarka, dan haka muka bar maganar bamu ne muka haife ka ba. Abun da muka so shi kake mana, dan haka muka sanya ka koma mataki na biyu na digirin ka, tunda a bangaren da ka karanta, duk wannan abin da muka yi shine zaka saka mana da lalata mana Yar mu? Mun gode amma zaka iya tafiya tunda mun gaya maka waye kai zaka iya tafiya don Allah ka bar mu karka lalata mana rayuwar ta." Ta karshen maganar cikin Kuka, da ban tausayi. "Bani da inda yafi nan! Amma dole zan tafi naji me yasa aka min haka, nagode kuma ina baku hakuri da abinda nayi muku." Daga haka ya fice daga gidan baki d'aya, tafiya yake da kafa. Idanun shi jajjur. A wani ƙwana suka haɗu da Najim! Inda suke ta tafiya a tare. "Saraki!" Juyawa yayi tare da kallon Najim, mai da hankalin shi yayi gaban shi, har zuwa wani shagon coffee. Zama suka yi Jay yace a bashi coffee me zafi, Najim yace a'a me sanyi dai. "Saraki! A yadda kake a tafashen nan idan ka sha ruwan sanyi, yafi na zafin da zaka sha. Ai sai ka iya tadda gari guda." Bai ce kala ba, haka ya cigaba da shan shayi me sanyi, har suka gama Ya mike zai tafi. Najim yace. "Ranka shi dad'e! Idan aka cigaba da haka wallahi muna cikin wani yanayi, ka taimaka min na samu gurin fakewa." Iska yaja sannan ya zuba mata ido, yace. "Ina cikin damuwa!" "Na sani, amma al'ummar daura da Mahaifinka tare da kakanni ka, suna zuba ido tare da saka tsammanin Magajin Izzah! Ban san me yasa kowa yake dauki da son ganin ka ba, amma Shehun Borno da wasu daga cikin dangi suna maraba dakai, Sunana Brrst Najim Aswad Magaji, ni ne lauyan masarauta. Da fatan zaka Duba alamarina. Ga takardan jirginka bazan iya zama na wasu lokuta ba, idan ka shirya jibi zamu sauka a Lagos." Cikin hasala ya kalli Najim, "Umarni kake bani?" "A'ah Saraki! Abinda ya dace nake, Saraki tun ranar da ka b'ata nake tare da Abba Jaamal, dan bana son ya duba gurbin ka, ya ga baka nan, idan kayi ra'ayin tafiya shi kenan, amma zukatar mutane suna dayawa akan ka. Sa ran su yayi matukar tasiri akan zukatar su. Ya zaka ji labarin Jarumar Uwar da ta tabbatar da kaine zaka kawo karshen rikicin masarautan da Insha Allah, faffutika tayi tare da sadaukarwa. Ko kasan ciwon da miji yake ji a lokacin da ya rasa matar da yake matukar kauna! Sannan abin da tabar mishi aka wayi gari ya b'ace, ka san nauyin da zuciyar Wannan uban yake dauke da shi. Ka duba yadda duniya take, ka dubi yadda kowa yake tattalin abin da yake na shine. Zaka iya rasa yau a rayuwar ka, amma gobe idan kayi ƙoƙarin gano bakin zaren zaka rike shi da daraja. Mu ahalin sarauta an san mu da tsage gaskiya,.tare da fadar ta, bama gudun abokan gaba. Domin da su aka halicce mu, abinda muka sani zartarwa. Hukuntawa, adaltawa Dai-daiton laifin tsakanin talakawan mu da attajiran mu, don Allah idan kana son Ahalinka su kare rayuwar su cike da kunya bismillah idan zaka iya zuwa ka tsayawa mutanen da suka saka rai. Da zuwan ka, koda yaushe mafarkin su Magajin Izzah zai dawo. Ashe ba haka bane domin sarakin da nake gani a gaba na lusari ne." A fusace ya makure wuyar Najim. "Toh idan har zaka iya fusata kamar yadda kayi a nan. Saboda kimar ka ka bi mace har nigeria, toh lallai Jarumin da ya wurga yarinyar nan wancan ranar a cikin kashin dawakai! Ya kuma sake nasarar sanya ta cikin kashin aladu. Wannan jarumin da ya kalli idon Sa'i yace mishi ya kiyayye harshen shi da fadar magana ga mahaifin shi, ba tare da yaji d'ar ba. Toh gobe da karfe biyu na yammaci ina jiran shi a tashar jirgin sama, nasan Saraki baya sab'a magana, amma naga isa da ikon nan da na sani a da. Ina nan ina jiran mai martaba sarkin Daura." Daga haka ya dauki rigar shi ta sama, ya bar inda Jay yaƙe. Yana tsaye kamar bishiya. Tsigar jikin shi mik'ewa yake. Wani irin jin kai tare da Izzah musamman wanda yake cikin kowani jinin sarauta, cikin ƙasaitar da bai zaci yana da ita ba yake tafiya, tare da wani irin yanayi wanda yake cike da mulki tsantsar ta. Koda ya isa gidan. Ganin kowa yayi shiru, suna ta harkokin su, sai dai Munih da take bin shi da ido, har ya shige dakin shi, bai kuma fitowa ba. ..... Har washi gari, yana dakin ya gama had'a kome nashi, sannan ya fito da manyan jakukkunan shi, tare da kallon agogon hannun shi, karfe biyu saura minti sha biyar. Koda ya fito ya same su, suna cin abincin rana. Zama yayi har suka idar yana yi yana kallon agogon hannun shi, tare da sake murmushin takaici, dan ya fahimci sabida shi suke kin gamawa, amma bazai iya barin su ba, zai zauna dasu. Har su gama. Koda suka gama kowa kama gaban shi yayi zai tafi yace musu. "Ku dakata mana!" Cak suka tsaya, kwaso takardun shaida karatun shi yayi, sannan ya mikawa Baba furofesa, ya mika mishi, kafin yace. "Nayi Kuskure, kayi hakuri ka amshi ban hakurina, gasu kaine ka bani so cikin so da kauna, yau na dawo maka su a matsayin tsintaccen nan. Nasan nayi kusakurai masu yawa, amma ina rokon Allah ya baku hakuri, zan tafi naga Ahalina Insha Allah zan dawo saboda shagona da yake nan, Bama iya shi ba, sabida ku zan dawo. Nasan nayi laifi me girma, don Allah ku yafe min." Daga haka yaja jakunan shi zai fita, da mugun gudu Munih ta rungume shi tana faɗin. "Wallahi mutuwa zan yi idan ka rabu dani, don Allah ka dawo ina sonka." Janye jikin shi yayi bai kuma sauraronta ba, ya fita abin shi ihu take tare da cewa a dawo mata da shi, shine abokin rayuwar ta,. ......... Karfe biyu saura minti biyu, Najim ya hango shi, yana shigowa, cikin sauri ya isa gurin shi tare da rungume shi. Mara mutunci. B'ata rai yayi kamar ba shi ba. Har inda aka duba kayan shi, sannan ya wuce abin shi suka nufi cikin jirgin. ---- Abuja.. Tunda Aunty Aina'uh ta zo min da maganar d'an mijin kawarta, naki bata fuska. Har dai ta gama damuwarta sannan ta kyale ni, yau da wuri na tashi sabida ina Son na fita, naje na duba mai na da sabuluna, sun kusan karewa. Sosai na shirya sai dai fuskana babu kwalliya, sai man baki da na saka, ko kallon inda Aunty Aina'uh take banyi ba, nacewa karamar yarinyar ta, dan itama Aunty bata haihu da wuri ba, kuma tsakaninta da Maama wato Mamana shekaru uku ne, sai da ta shekara sha takwas, kafin Allah ya basu Haihuwa. Babban yaron yana makarantar king Abdul Azeez riyadh, sai kuma wacce take bin shi tana nan turkish, na abuja. Sai wanna yar karamar wacce taci suna Mamana, suna kiranta da Hanan. Dan haka na riko hannunta tare da janta muka fita. ..... Sahad store muka je, Nan na sayi kayan amfani na, muka nufi gurin biyan kudi. "Kowa yafita ga dan gidan ministan Abuja zai sayi kaya!" Lokaci guda mutanen cikin, shagon suka fara fita ban dani da na ke biyan kudi. "Ke wacece da ba zaki fita ba, ana magana." Mikawa matar katina nayi, sannan na kwashi kayana tare da riko hannun Hanan, zamu fita. Kamar ance na d'aga ido na, sai akan Asood. Ban yi mamaki ba. .kawai nasaka kai zan fita ya tsare hanyar fita, cikin isa ya iso gabana. "Karuwar mu!". Rintsa idanuna nayi tare da kawar da kai na. "Ina abokin ciniki ki? Koda yake naji ana min tayin auren wata bazawara, amma bazan ki tayin ba. Idan na duba yadda ko ina yake cike tam!" Ya kai hannun shi kamar zai tab'a ni nayi baya, cike da bakin ciki. .. ..".karki damu! Zan zo har gidan na kwashi rabona abin da Jay ya bari zan tattaro na karasa" Takowa yayi gabana, tare da min kallon kaskanci. "Karki manta nan ba Calgary bane! Nan birnin tarayyar mu ce! Muke fada muke yadda muka so! Kudi mulki Izzah mun gaje shi, ki kalli Asood Ahmad Buba Yaro kika mara, idan zaki iya ki fara gudu, karki tsaya karki tsaya karki tsaya, domin sai na jiyar da ke, zafin da bazaki iya kwatanta ya yake ba. Sai na gama miki azzabar da ba zaki iya kwatar kanki ba, kina da sauran lokaci, na gudu ki nime matsirata. Sabida shi wancan da na turo ya kasa min yadda nake so! Fatimah Khatoon fara gudun ceton rayuwarki. #Mai_Dambu 10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar..... *Cusa Kai* "Ba zan tab'a gudu sabida kai ba! Ba zan nemi maboya sabida kai ba, abinda na sani Allah yana tare da mai gaskiya kai baka isa kayi min abinda bai min ba, kai ba kowa bane facce mujirimi, baka isa ka tozartani ba, sabida Allah ya kare mutanen da suka yi imani da shi.                  Idan ka isa kabi layyin unguwar mu tukun sai na san kai na musamman ne! Har ila yau yarintar tana kwance cikin jini ku."       Daga haka na wuce abi na, ban ma bin ta kan shi ba, sabida ba zan iya karar da wani abu bayan wanda idanuna suka gane min ba.      .... Koda muka isa gida, Aunty Aina'uh taso fahimtar halin da nake ciki, amma naki bata fuska, dan na fahimci ita ke son b'allo min ruwa. .......     Ranar Laraba jirgin su Najim ya sauka a garin Lagos, cikin nutsuwa suke saukowa tare da jin dadi. Shaƙar iska yayi cikin nutsuwa sannan ya fesar yana me ɗauki ganin mahaifar shi.          Kallon shi Najim yayi kafin yace mishi. "Abba ya gaya min cewa, garin Lagos yana daga cikin garuruwa masu dinbun tarihin rayuwar ka, domin anan aka kafa soyayyar da ta samar da kai.                 Dan haka idan zamu dawo nayi kokarin ganin mun sauka ta nan, domin ka fara jin ƙarfin shigar masarautar daura"            Tab'e baki yayi cikin ko in kula, kamar bai damu da yadda yake so garin ba, yanzun burin shi su isa garin daura yaga yadda mahaifar shi take. Wannan itace muradin zuciyar shi. Zaman minti goma suka yi sannan suka nufi wata jirgi da zata kwashi fasinjojin Abuja sannan ta ajiye su daga can su sami jirgin da zata dauke su zuwa daura.                      Tunda suka taso kirjin shi yake bugawa, tun yana zaune har ya tashi zuwa ban dakin cikin jirgin. Bai yi kome ba ya kuma fitowa.           Ya zauna, har suka iso abuja, anan suka sake samun wani jirgin zuwa katsina, kafin nan jikin shi ya jike jagwa da gumi.       Karfe biyar da minti goma jirgin su ya sauka a garin Katsina, suna isa suka sami. Fahad.    Cikin wani irin farin ciki idanun shi cike da kwalla ya rungume Jay, duk da ya manta fuskar shi, amma ya rike shi sosai.           A hankali ya juya ga Najim yana cewa. "Aminin Arziki Barka da hanya. Babban lauyan mu!" .  Ya sake Jay ya rungume Najim, murmushi yayi sannan Najim yace mishi. "Ni ba surukinka bane da bazaka gaishe ni da da'a ba?"         "Banza Bakwai, ba zan gaida ka ba, mara mutunci. Jannart ce ko zaka mutum ka dawo sai an bani ita ko Saraki?"       Murmushin yake Jay yayi tare da juya idanu,  motar Fahad suka shiga.        Suka fara tafiya, suna hira sama sama,  tunda suka fara tafiya Najim ya fahimci ana bin bayan su, dan haka yacewa. "Kai Uban Maganannu tsayar da motar nan" Tsayawa Fahad yayi motar tazo ta wuce su da gudun tsiya, murmushi Najim yayi sannan yace. "Kasan me zai faru? Mu koma gidan sarkin Katsina"        "Malam Lauya!" "Nace muyi abinda na gaya maka," ya faɗa da matukar muhimmanci. "Toh" Da sauri ya sake hannun da suke, sannan ya koma daya bangaren, tun kafin su bar layin gurin Najim ya kira wayar wani kafin su isa wata mota kirar toyota, tazo tare da wani saurayi.   Canza motar suka yi sannan Najim ya mika mishi kudin da zai hau wata yana cewa.. "Mansoor karka shiga motar ka bar shi anan, sabida wani dalili.       Wannan kuma zamu tafi da ita, dan haka ka kiyayye yan sanda zasu zo nan!"    Daga haka suka koma cikin motar, Jay na kallon su, har suka fara tafiya Fahad yace. "Najim! Kaina ya daure da sauya motar nan, sannan kuma kace a nima mana me bakin gilashi. Me yasa?"             Banza yayi da shi yana wani aiki da yar na'urar computer din shi. "Saboda banzan surutun ka, baka san ana bibiyar motar ka ba, banza kawai baka san kome ba sai yadda kudi yake shiga da yadda kudi yake fita."      Shiru yayi can ya kira wani a waya, suka sake magana..sannan ya kashe wayar. Tare da cewa Fahad. "Kashe wayar ka, wasu babin didigin layinka." Da sauri ya kashe wayar dan Allah ya daura mishi masifar tsoro.   ......    Sunyi dogon tafiya kafin suka kuma haduwa da mutanen suna jiran motar su, koda suka wuce su.     Najim ya kuma kiran abokin shi ta intanet, daga nan suka ci-gaba da tafiya, har suka haɗu da wata motar kirar sieena, anan suka tsaya tare da sauya motar baki daya, sanan suka bar wannan toyotan a gurin.                  Suna shiga wannan motar Jay ya zuba mishi ido. "Saraki wannan kallon naka damuna yake, don Allah tambaye ni kome zan gaya maka banda wannan irin kallon."                  "Me ke faruwa?" Inji Jay, Shiru yayi sannan yace. "Wato abinda yake faru, duk shiri ne na dakatar da kai, karka shiga masarautan."   Kura mishi ido yayi, sannan ya kuma mai da kan shi yana fad'in. "Suwaye suke son ganin bayana?"           "Akwai mutane da yawa, matsalar wasu ba a san fuskar su ba."         "Toh taya aka yi na bar gida?" Ya kuma wurgawa Najim tambaya. "Bamu sani ba" Najim ya bashi amsa a takaice.     A hankali suka shiga garin daura, tare da sauke ajiyar zuciya. Dukkan su uku suna fadin Alhamdulillahi!           Tun kafin su isa fada Jay yake kallon garin, cikin wani irin yanayin farin ciki, ya kasa fahimtar halin da yake ciki har suka isa cikin Masarautar, wanda aka shagali.       Tsigar jikin shi ne, ya mike sakamakon busar alkaki da kakaki da ake, tare da buga tambura.                    A hankali yake sauka daga motar bakin shi dauke da addu'ar da Manzon Allah ya bada da zaran zaka shiga cikin jama'a.            Kallon shi ake ana faɗin. "Lafiya d'an sarki jikan sarki! Lafiya Sarakin Asali, taka lafiya me Shehun Borno me Sarkin Musulmi, Lalle maraba da namijin duniya! Murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya! Zauna lafiya d'an karamin su kuma Baban su! Lafiya Kanin Ummu Rumana Jikar Ummu Rumanah!  Takawar ka dodon su.                     Barka da zuwa Magajin Izzah! Barka da zuwa Magajin masarauta! Barka da Zuwa Yayan Gimbiya Jannart Yayan Gimbiya Jannart, An gaida D'a ga Gimbiya Sarah! Takawar ka lafiya Barde namijin zaki.                    Wuwuwu ina gwani ganawa ina maji kira ga nawa, Chau namijin Giwa."         Duk sai yaji shi kamar bai cika mutum ba, a hankali yake takawa, yayinda Najim da Fahad suke taka mishi baya, dogarai suna rike da jakkuna shi, da gudu  tawo tana fadin. "Yaya Jayyyyy!"     Ba tare da ya ganeta ba, ya tsaya cak yana jin kiran yarinyar har cikin kwakwalwar shi, da gudu ta faɗa kan shi ya rungume ta. Fashewa tayi da kuka, tana son magana kuka yaci karfinta, sai nuna mishi hanya take tana son tayi magana takarda saboda kukan da take dakyar tace. "Ni...ce ....Ja...nan... Kanwar ka da ka tafi ka bari, Ga Raihanah can ga Kuma Ummu can muna kewar ka"      Rungume ta ya kuma yi yana fadin. "Ba zan yafe masu ba! Ba zan tab'a barin hakkin hawayen ki ba..gani nan na dawo Noorie!"       Cikin wani irin murna tare da ihu tace. "Ya ce min Noorie."      Aikuwa take masu shela suka fara kara bisa suna fadin cewa. "Saraki ya kuma kiran Gimbiya Jannart da Noorie haka ya sata farin ciki." Aikuwa dake ana son karawa magauta haushi aka shiga sake ganguna, jan shi tayi har babban falon tsohon sarki Jalaludeen. Tare yake da yaran shi tare da jikokin shi, ga kuma Aminan shi, a hankali ya shiga dakin tare da sallama, ya tsaya zai cire takalmin shi.         "Barka da Zuwa Amale!"          D'ago kan shi yayi cikin nutsuwa ya kalle ta, murmushi yayi tare da zubar hawayen, sannan ya cire takalmin ya isa gaban Jaamal ya zuba gwiwar shi a kasa, tare da sake wata irin kuka. Wanda ya kuma saka kowa a falon kuka, sunkuyar da kai Jaamal yayi tare da tuno Jannart din shi, shekaru Ashirin da bakwai.                   Rungume shi yayi tare da ce mishi. "Ban san yaushe mutumin nan ya koyi kuka ba, dan a sanina baya kuka sai dai ajiyar zuciya."                     Murmushi tsohon sarki yayi sannan yace. " Idan gora tana rawa ba a cika  bane, dan haka ban ga jarumi a gabana ba Ragon mata na gani, wanda mace ta sanya shi biyota."         Janye jikin shi yayi daga na Kawu, sannan ya share kwalla da take fuskar shi, ya sake murmushi. Yana shafa kan shi. Tare da kallon kakan shi ya matsa kusa da shi, ya zauna ya kasa magana sai shafa yalwatattacen gashin kanshi yaƙe cikin wani irin farin ciki mara iyaka.          "Yanzun ina Iyayenka na can?" Kakan shi ya tambaye shi. Kallon Jama'ar dake falon yayi sannan ya sunkuyar da kan shi kasa.      "Nayi rashin adalci, har na dawo basu tsaya nayi sallama dasu ba." Ya faɗa a sanyayye,                  Share batun kakan shi yayi sannan ya kuma mai da hankali gurin tambayar shi. "Me ka karanta?"    Murmushi yayi sannan ya shafa kan shi yace. "Likitan mata da yara ne Ni!"              "Matakin digiri ko ka kara gaba?" Gyara zama yayi sannan yace. "Zuwa mataki na biyu na digiri."           "Kana da ra'ayin aiki ne ko zaka..." "Yallabai! Bako ne kamata yayi a bar shi ya tafi ya huta da iyayen shi sauran tambayar ya biyo baya."     "Toh Rumanah!" A hankali ya sallami kowa har Jay wanda Sarah da kanta ta shirya mishi abinci, bayan ya wuce dakin Kawu ya zauna Kawu ya dauko mishi hotunar Mahaifiyarshi. Tare da wasu abubuwan da yake mata hatta Littafin da ta bar Mishi.  Sannan ya kuma dawowa dashi wani daki dake can sama kusa da na Sarah ya bashi key din dakin.        Sannan ya bude kofar ya shiga, kome na d'akin a shirye yake.... Ban daki ya shiga,       .--- Buga cinyar shi Ajiya yayi cikin jin haushin kowa, yana huci kamar zai tashi sama. "Amma!"      "Me zaka ce Sa'i? Amma me? Bayan ka san Yaron nan takaddari ne, sannan mara jin magana ba ma zai tab'a kyale mu ba, bana rena kankantar allura."      "Ajiya me kake son nayi bayan ka gaya maka nima ban san kome ba! Kawai naji labarin zai dawo ne, kuma." "Kuma ka tura sakarkaru su tare su a hanyar zuwan su ko? Sabida an ce maka Wancan shadanin lauyan zai taso babu sanin abinda ya dace. Kaga bamu da lokacin da zamu ɓata, akan wannan al'amarin kawai kaje zan nime ka." ..jiki a mace sa'i ya mike tare da kad'e babban rigar shi, sanan  ya nufi hanyar fita.                  --- Abuja... Zaune nake ina ƙoƙarin shan tea, kiran Hanisah ya shigo min. "Ke yan mata! Ina Baabi da Ummin tare da Ammih na,"      "Addah ba shi ya kawo ni ba, albishirinki"      Juya ido nayi sannan nace. "Katon farin goro!"         "Wayyo Hamma Jay ya dawo Wallahi, yanzun haka yana daura."             Idanuna ne suka cika da kwalla, kamar zanyi kuka nace. "Hanisah ina wasa dake ne?" Dariya ta saka tare da cewa. "Malama Addah kin fada soyayyar Hammana, ki min magana cikin da'a in ba haka ba, zan iya."    Hawaye ne ya zubo min kashe wayar nayi tare da sake wani irin kuka, na rasa meke damuna akan shi.             Bude data na nayi tare da duba Hanisah a Whatsp, na tura mata da cewa. _Bani Number Ummu Rumanah!_       *🤣🙄 akan me zan baki number ta? Kinga malama Addah kiyi hakuri kawai dan na lura*             _😒😠 Ina wasa dake ne wai?_ Na tura mata,                *😡😜🤭 Gayawa keya labarin! Bazan bada ba sai an bani cin hanci*          _🙆🏽‍♀️🤦🏽‍♀? Abinda ya kashe kasar mu wannan cin amanar kasa ne! Bazan bada ba_       *🙅🏼‍♀️Tun muna shaida juna nemi wacce zata baki ba dai Jikar Shehun Borno ba*       _🤔🤔🤔 Yau naga abinda yafi zare tsayi, toh wallahi duk ranar da muka jone dashi Hammanki sai na gaya mishi hassadar da kike mishi dan kar ya sami kyakyawan mace irina_            *Haba? 🙄🤣 Toh maza gaya mishi Addah ina son zoben hannunki nan, shi kawai nake so, sai na tura miki number*     _🤦🏽‍♀? Kaico kin dage sai na baki cin hanci dai? Toh na baki amma ki duba yana nan a cikin dakina ban tawo dashi ba_        Turo min Number tayi cikin sauri na ajiye shi a wayata, sannan na kuma kirata zuciyata tana bugawa, tana dauka murya na yana rawa nace. "Hmm! Hmm! Dama ina son magana da Kanin ki ne"       "Toh dan kashe bari na bashi yana falon Abban mu ne"            Cikin sanyin jiki na kashe ina jin wani irin tsoro, yana kamani, can ta kira ki da sauri na .kashe kiran sannan na kirata, "Gashi nan!"       "Waye kuma Ummu?!"         Naji muryan shi me matukar daɗi ta daki kunne na. "Jayyyyy" Sauke numfashi yayi, sannan yacewa Ummu. "Kinga ban san me wayar ba jeki dashi!" .kamar na fashe da kuka, na kashe kiran.   Sake kirana tayi, cikin damuwa tace. "Aanih kiyi hakuri, wai bai gane ki ba!"      "Ba damuwa Rumah ya oga Khalid,"   Dariya tayi sannan tace. "Muna lafiya,kina Abuja amma baki son zuwa gidana, idan na dawo don Allah kizo"   "Insha Allah, zan zo.... #Mai_Dambu         10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar..... *Kamar Kombo kamar kure!*   "Insha Allah idan kin dawo zan shigo miki da Yardan Ubangiji."         Haka tayi ta jana da hirar, ina kaucewa. Amma babu yadda na iya, har zuwa wani lokaci. Sannan muka yi sallama.          Kifa fuskana nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka, me mugun cin rai, sai da nayi ya ishe ni sannan na mike na wanke fuskana.             Sannan na cigaba da zama a dakin dan nafi son zaman dakin sama da zaman waje.   --- Daura. "Saraki! Baka da kirki amma kasan wacece ta kiraka, amma kake nunawa baka santa ba, Toh Aanih Fatimah!"      Cigaba yayi da cin abincin shi ba tare da ya kalli inda take ba. "Amma baki da hankali, mutum yana cin abinci kina cika shi da suturan banza." Inji Mama Sarah,       "Kai Mama! Meye laifina dan na tuna mishi ita, Yau kina gani. Shine ta sanadin ta, da bata yi dalilin zuwan shi ba, da babu ku babu labarin shi.       Mama ko da yaushe kamata yayi kina abu babu wani fifiko, sabida shi aka fasa auren ta, yau ta kira tayi mishi Jajjen ya dawo cikin dangin shi sai yaki kulata. Shegen girman kan shi nan zai janyo mishi asara wata rana."                    Tana gama fad'ar haka tasa kai zata fita, Mahaifin su ya shigo. "Mamahna keda waye haka?"      Cike da jin haushi, ta gaya mishi abinda ya faru. "Amma Ni banga laifin Khatoon ba, dan yarinyar tayi kokari sosai. Kuma ina sha'awan ta shigo gidan nan a matsayin surukata!" Da sauri ya d'ago kan shi yana kallon Abban shi kafin ya ajiye cokalin. Shiru yayi bai ce wani abu ba. Sai mik'ewar da yayi abin shi.   ....... A cikin kwanaki ƙalilan ya saba da kowa, sannan Raihanah tazo daga Abuja ita da sauran yaranta har da Aliyah da yaran ta.               "Yawwa Mamah don Allah kice Abban Jannart ya kara min kwanaki."       "Ina ruwana, lokacin da kika zo kunyi shawara dani ne? Kawai kika bar min wannan janny da shegen farin idanun ta, tayi ta saka min kuka, dauketa kafin nayi mata."       Shigowar Jay tare da Najim yasata zuba musu ido, cikin farin cikin da ta kasa b'oyewa. Suna shigowa sai ga Jaamal da Aswad suma sun shigo, a hankali tace. "Alhamdulillahi, naga wanan amintar yau gashi Ƴaƴan ku ma suma sun haɗe kan su. Allah ka jikan Jannart da Rahama, duk wannan aikinta ne."     Shigowar Sarah tare da bayi mata dauke da manyan ture har uku, yasa ta zuba mata ido. Ta zauna a hankali bayan an ajiye tiren, kar'ar wayar Sarah yayi ta dauka tare da cewa. "Alhamdulillahi barkanku da zuwa."      Mik'ewa tayi tana gyara zaman Alkyabar ta, tana kallon Raihanah karama tace. "Maamah tashi maza ga Ummin ku na sokoto sun iso, maza kuje ku gyara mata d'akin dake shashina, tare da ke Maman Kawa."        Mik'ewa Aliyah tayi suka nufi shashin Sarah aka shiga gyara, duk sai jikin su yayi sanyi. Sakamakon abinda Jaamal ya faɗa. "Yau shekaru talatin  da  bakwai, haduwa ta da Jannart! Ranar da bazan manta ba, mun fito cikin gari daga aikan Baba. Muka same su tana kuka, lokacin da muka tsaya Domin taimakon sun muka kalli juna."    Murmushi yayi sannan ya zuba idanun shi akan kofar shigowa falon yana kallon Rahil tare da Hanisah da Jannart karama, buɗewa Jannart karama hannu yayi, ta shiga tafiya a hankali tana kallon kowa, a hankali ta shiga jikin shi.         Ya mai da idanun shi kan Jikar shi ta fari itama Jannart ce ya kirata, ta mike da sauri. Sai Yar gurin Aliyah itama Jannart ce, ta isa jikin shi sannan ya shiga duba Jannart babba yar aurar shi. "Aura!" Ya kira ta.       Shigowa tayi tare da Fahad, sai nokewa take. "Zo nan." Da sauri ta isa gare shi.    Dukkan su, sunan mutum daya suka ci, kallon Rahil yayi cikin kulawa yace. "Ina Yar Jannart?!"     Murmushi tayi tana goge kwallar da ta cika mata idanu, tace. "Tana abuja, gurin Kanwar Mahaifiyarta."                    Da sauri ya zuba mata ido, kafin ya mai da idanun shi kan Jay wanda jikin shi yayi mugun sanyi kafin yace. "Me yasa ta tafi can?"        "Tun bayan fasa aurenta, Ikrama yace matukar tana Sokoto, zai ya tozarta ta."        Da wani irin yanayi Jay ya kalle ta, bakin shi na rawa yace. "Akan me?" "Kan abin da kayi mata! Dauke ta da kayi ranar auren ta."      Jan numfashi yayi tare da kau da kan shi, tare da mike yana me tauna bakin shi yace. "Ita ce ta shirya ni kuma na gabatar." Daga haka ya bar falon. "Kamar kumbo kamar kure! Halin uban halin d'an." Inji Mama Raihanah,                 "Toh itama tazo nan ayi bikin dawowar d'an uwanta da ita."              Ba tare da sanin Jay ba, Abban shi ya turo Najim suka tazo da Aani.              ..... Da yamma muka iso Daura, dan haka yan matan suka ja ni zuwa dakin su, yayinda Rumah da Aliyah suka ce na fita cikin su ba zan zauna a cikin yara ba.                   Murmushi nayi kawai, nan muka shiga hira, akan wasu abubuwan har lokacin cin abinci yayi.           Sanye nake da jar doguwar riga, muna shigowa suma suka shigo tare da Kamil Mijin Aliyah, sai Khalid dan Mamah Raihanah, mijin Rumah, suka shiga.                 Sai Najim, Fahad, Da Shi kan shi Jay din. A hankali yake tafiya suna biye da shi, har inda aka zuba abincin, babban teburin cin abincin.      Tunda muka zauna nake kokarin b'oye yanayin da nake ji a raina, har muka fara cin abincin. Kallon shi nayi lokacin da naji kamar shi tana yawo akan nawa, sai da na kware, murmushi yayi ya cigaba da cin abinci.             "A ci abinci a hankali bazai kare ba." Kura mishi ido nayi, cikin bakin ciki,, idanuna na cika da kwalla. Mik'ewa nayi yayi maza ya hard'e kafarshi da nawa.         Komawa nayi tare da zama na kasa cin abinci. "Kici kar ya kare!"     Toshe baki na nayi, tare da barin gurin da sauri kuka yana zuwa min, a hankali nake tafiya. Dake nafita daga gidan, duhu ne a gurin.       A hankali nake tafiya ina kuka, daga nesa na hango wata mace tsaye, tsigar jikina ne ya mike.                 A hankali ta fara tafiya, kamar wanda aka sani dole sai na bita, har muka kusan barin masarautan, ji nayi an dafani wani irin tsoro ne ya kamani tare da sake wata irin kuka da ajiyar zuciya.. kamshin galaxy naji na juya da sauri na fada jikinshi ina me rufe fuskana a kirjin shi. Kuka na saka me mugun karfi jikina yana rawa.        Kasa cire ki yayi a hankali yana kallon yadda na razana, "Me ya kawo ki nan?!"        Fincike hannuna nayi tare da zabga mishi harara nayi, ina kuka tare da cewa. "Ba kallon yunwa kake min ba, ace mutum yazo gidan ku kana wulakanta shi."      Juyawa yayi tare da barin na a gurin yana fadin.. "Toh ki koma gidan ku mana" "Ai ba kai ne ka kawo Ni ba!" Juyowa yayi tare da takowa gabana, ya zuba min ido. "Ina son a rayuwata, idan nayi magana kar a maida min!"      "Sabida ka girme kowa? Toh ka tambaya da kyau na baka shekaru shida!"             Takowa yayi ina ja da baya, har na dangana da wata bishiyar durimi. "Haka nake son naga tsorona a cikin idanun ki, baki girme ni ba! Sabida zan iya sarrafa ki a kowani ɓangare."    Ture shi nayi tare da cewa. "Tir! Ni ba yar iska bace." Na rab'a zan.wuce daga gurin shi. Fisgo ni yayi jikin shi tare da matse ni, ya saka kan shi ta wuyana yana faɗin. "Waye d'an iska?!" "Wanda ya tsargu!" Na bashi amsa. "Toh bari na nuna miki Iskanci." Lokaci guda ya saukar min da kasala, cizon shi nayi da mugun karfi sai da ya sake yar nishi, sabida zafin.           Kwace rikon da yayi min nayi zan gudu, ya samun kafa ai kuwa na zube akan kafaffuna. Tare da sake kuka. Kallon hannun shi yayi tare da shafa gurin sabida zafi da azabar da gurin yake mishi, a hankali na mike ya kuma saka min kafa, cikin kuka. Na fara magana, ina cewa. "Allah ya isa min! Tunda ban san abinda nayi maka ba, kake ta samun kafa ina Fad'uwa, ba zan yafe maka ba.".              "Ban nemi yafiyarki ba! Kuma sai na rama cizon da kika min."   Zaro idanu yayi cikin tsoro, yadda ya murtuke fuska zaka dauka da gaske hakan ne a ran shi, sunkuyowa yayi Allah ya bani Sa'a na ture shi na kwasa da sauri sauri gudu gudu.       Mik'ewa yayi tare da kwafa, akan sai ya rama abin da nayi mishi. ..... A cikin kwana biyu mun zama wasu irin abokan fada, kamar wuta da auduga, yana gani na zai ce zai rama cizon shi. Ji min Iskanci sai kace Yaro.          Ranar Juma'a aka yi walimar dawowar shi, bayan an gama nasiha da fadakarwa, kawai Galadima ya tashi yayi sallama tare da godiya, sannan yace. "Ina farin cikin dawowar Abokina, Jalaludeen ina kuma kara mishi wata kyauta ta musamman, na Jikar da nafi so yar wajen Umar, wato Husnah. Tana gurin Nanah Khadijah. Ku dai-daita kanku." Zufa ne ya shiga sauko min ina kallon shi daga can sanye da alkyaba ruwan madara wanda yake sirke da zaren gwal. Kurawa juna ido muka yi, sannan na kauda kaina, Sunkuyar da kaina nayi hawaye na zuba min, sabida bakin ciki. Kusan har aka tashi ban iya kallon kowa ba. Sai dai an shirya wasan dawakai ne. Kuma shima zai hau dokin. Bakin ciki ya sani ko zuwa gurin kallon dawakan ban yi ba, na nufi can bayan gidan, na zauna a lambu. Ina kallon ruwan da ya taru a gurin da wasu manyan agwagi ke wasan ruwan dasu. "Shiiiiii!" Na juya ina kallon inda nake jin karar, matan nan ce sanye da jajjayen kaya, jini na zuba a jikinta duk inda ta wuce jinin na b'atawa, hannunta rungume a kirjinta, ga kudar zuma bakakke da suke shawagi a kanta. Kukan doki naji, ya shiga wani irin mik'ewa. Da gudun gaske yayo kaina, tun kafin ya iso, naja zuwa zuciya tare da zuɓewa a gurin, ban san lokacin da na dauka ba, sai dai na kuma ganin matar ne, a kusada ni tana shafa fuskana. "Wani lokaci bayyana cutar da take ran mu, itace igiyar farko da take fara illatar mu, ko da kuwa zaka fadawa duniya girman halin da ka wanzu a cikin shi ba Lallai bane kowa ya fahimci bashin da ba kaine ka ci ba. Taya duniya zata fahimci girman Soyayyar da Sadaukarwa? Taya duniya zata gane halin da zuciya take ciki? Maza ki dakatar da wannan Kuskuren da ake shirin saka shi a ciki, idan ba haka ba. Daukar nauyin kasadar yana jingine bisa kafadarki!" Bude idanu nayi, tare da tashi zane. Jini ne ya digo daga cikin hancina, ga kaina yayi wani dum. Da sauri na fita daga lambun dan ina iya hango abinda yake shirin faruwa a filin nan da wasu mintuna masu zuwa. Ganin shi nayi yana ƙoƙarin hawa doki, na rike shi hancina na saukar da jini. Girgiza mishi kai nayi cikin zubda kwalla, sabida jin wani irin karfi da nake ji a jikina, tare da wani irin yanayi me tadda hankali. Zuba mishi ido nayi dakyar bakina ya iya furta. "Jay! Karka tafi." Cikin ganin yafi karfin ya saurare ni yace min. " Koda zaki ya zamma wulakantace, ba ya yi wasa da khinzeri ba! Dan haka ki sa kai ki bar nan kafin na miki abinda baki zata ba." "A'ah Jay, Bera yana gani'n raminshi, bazai yarda wuta ta cishi ba. Me yasa?" "Ke bana son shirme da yayyafi kogi yake cika, ke kin isa ko dakatar da ni ne?!" Murmushin takaici nayi tare da zuba mishi ido, sannan nace. "Allah ba ya ba gwanni'n tona tsaba.! Ai ya fishi sanin dalilin da ya hana shi, don Allah karka tafi." Ture Ni yayi tare da hawa dokin shi... Paid before read 🕊? 10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar..... *Jiki Magayi... Duka da d'anyen kara*    Da gudu ya zaburi dokin, ji nayi kamar ance min. "Ki dakatar dashi!"       Da sauri na mike na nufi hanyar wajen. "Karku sake tafito!" Ya fadawa Fadawa masu tsaron kofar shiga filin, ina zuwa suka hanani shiga, kamar zanyi hauka haka nake kuka. "Don Allah ku barni na je, wallahi akwai abin da zai faru mara daɗi ne!" Na fada musu ina rokon su. Juya min baya suka yi, alamar ba zasu saurare ni ba, sunkuyar da kai nayi, dai dai fitowan Abban shi dasu Baba Aswad, suna zuwa aka bude musu kofar kafin suyi wani yunkuri, na shiga filin da sauri. Tattaro alkyabar jikina nake, tare da niman in da yake. Hango sahun farko nayi nasu Fahad, tare da Mijin Rumah sahu na biyu kuma shine akan doki, wata irin guguwa ce ta taso tare da mamaye filin baki daya. Kafin ya lafa, tawagar farko suka fara suka juya da gudu sannan suka koma, tawagar Jay suka tashi amma dokin shi yaki tafiya sai mik'ewa take, abinda ya d'aga hankalin Iyayen shi. Kowa so yake ya kai mishi dauki, shi kuma yana hankoron ya jan linzamin dokin yake, amma dokin yaki sai ma mik'ewa da dokin yake. Ban san lokacin da na cire alkyabar jikina ba, babu takalmi a kafana, nake keta dandazon mutanen da suke kokarin ganin sun dakatar da mutane shiga. Tsalle yake tare da walagigi da shi, kamar wacce ake cilla ni cikin filin. "Hasssss! Kunba nuba! Jiyya hiyya, huuuuuuuuuu, ja hass bam da..." Na daka mishi tsawa, wani irin tsalle dokin yayi suka zube a gabana, durkusa nayi a hankali tare da riko hannun shi. Jini na d'iga a hancina tare da idanuna, dakyar ya mike tare da fisge hannun shi, yana harara na. D'igin shi ya fara a hankali lokacin da su Abban shi suka iso filin. Guguwa ce ta kuma tashi da karfin tsiya zata sure shi. "Zulum! Ka Raf ka, atɓa di na, fass haya mi ro, fur ab fuuwa" Cak guduwar ta tsaya tare da zuwa ya kuma dungulewa da karfi ya sure ni a guje. Hankalin kowa ya tashi, sabida ganin yadda iskar take kwantawa dani,.kafin ta watsar dani can gefe. Dakyar na cire kaina na mika Mishi hannu. Kallona yayi sannan ya kauda kan shi, kamar bai ga halin da nake ciki ba. "J...a..y!" Na Kira shi a gajiye da kuma wahalar da nasha. Banza yayi kamar bai sanni ba, sai da Baba Aswad ya nufoni da sauri tare da Najim, Suna isowa Najim ya kai hannun shi da niyyar dauka na, ai kuwa Jay ya doke shi sai da ya fad'i, sannan ya durkusa ya dauke ni, tare da b'ata rai da fuskar shi, sai ka rantse mugun abu ya dauko. A hankali ya nufi cikin gidan, ina hannun shi sai aman jini nake, tare da mik'ewa ina kokuwa da numfashi na, Kai tsaye shashin Mamah Sarah yayi da ita, inda aka shiga bata kulawa, yana tsaye a kanta. Har ya juya zai fita ta rike hannun shi. Cikin tausayawa kanta ta bude ido, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta sake shi. Ya fita da sauri yana me jin ɗacin abinda tai a gaban jama'a, babu dan mayafi, ai haka bai dace ba. Tsaki yaja tare da tunawa toh meye matsalar shi da ita, haka yayi ta sakawa yana warewa, har Najim yazo ya zauna kusa dashi sannan ya kalle shi kafin ya kauda kanshi, yana me kallon sama. "Inji Baban Sarki wai kazo!" Inji Najim. Mik'ewa yayi, sannan ya mike tare da barin gurin, Najim yana bin shi. "Amma Fatimah tayi kasada da rayuwarta fa?" Cewar Najim, "Toh ina ruwa na, meye matsalata da ita." Murmushi Najim yayi sannan yace. "Amma kamar naga wani abu na daban a cikin ƙwayar idanun ka" Shiru yayi sannan yace. " Ganin ka ya gano karya! Malam Lauya" "Malam likita me yasa bazaka amshi batuna ba!" "Ban iya dogon magana bane!" Da sallama suka shiga falon, kowa kallon shi yake, sai a lokacin ya kalli kan shi da jikin shi sun yi butubutu, sunkuyar da kai yayi cikin nutsuwa, dan bai lura da suwaye a falon ba, sai da yayi an ce mishi. "Jaheed!!" Da sauri ya d'ago kan shi da sauri, yana kallon Baban shi na Canada. Kau da kan shi yayi sabida har yanzun yana jin zafin abin suka mishi. Kallon kasa yayi cikin nazarin meye ya kawo su Daura. "Jalaludeen! Ga Babanka na canada, tare da sauran iyalan shi suna cikin gida. Abin mamaki ashe ma d'an ne ga Yayan Rumanah kakarka, matar shi kuma kanwa ce ga Balkisu. Kai dai Allah ya dauke ka ya kai ka cikin dangi da yan uwa." Shiru yayi kamar ruwa cinye shi, ya rasa abinda zai ce bai kuma firgice ba, ya d'ago kan shi yana kallon su. "Gashi ya baka yar shi Munubiya! Sannan mun nima maka auren Fatimah." "Wallahi bana sonta! Bana kaunarta don Allah karku haɗa mu, dan zan zalince ta." "Baka isa ba, idan an daura maka ita ka mutu." Kamar wani karamin Yaro. Ya b'ata rai mik'ewa yayi zai fita Najim ya zaunar dashi yana kallon fuskar shi. "Ahalin masarauta an samu da kamewa da kuma ɗa'a yin haka sam bai dace ba." Kallon iyayen su Najim yayi cikin nutsuwa sannan ya cigaba da cewa. "Ku iyayen mu ne, sannan kun fimu sanin dalilin da yasa kuke son a nima mishi Aanih Fatimah Aryaan, mu bamu sani ba. Amma ko a musulince, shi yake da ikon nimawa kan shi mata, dan shi waliyyin kan shine! Dan haka don Allah ku dakatar da nima mishi ita, tunda ya ce baya yinta a barta kowa ya hakura tunda ya amince da sauran zab'in ku." Jikin kowa yayi matukar sanyi sabida abinda Najim ya faɗa. "Kuje!" Mik'ewa suka yi, ba tare da anyi wani magana ba. Har suka fita babu wanda ya tanka musu. "Abba haka zamu bar shi babu wanda ya isa dashi." "Kai ma haka kayiwa uwar shi, ai gado ba karambani bane!" Shiru suka yi ba tare da cewa wani abu, ba. Har dai suka watse. --- A hankali maganar ya watsu a cikin gidan, kamar wutar daji. Jay kan babu abinda ya dame shi. Koda aka ce ya samu Husnah shareta yayi ya cigaba da abinda ke gaban shi, Munih ce ma tayi ta shige mishi. Tare da nunawa ai ita ana sonta. Ina kwance a dakin Mamah Sarah Hanisah tana hada min kayana, Munih ta shigo cikin wani rawan kai tana kiran. "Janna!!!!" D'aga kai muka yi tare da zuba mata ido, kamar taga kashi haka ta kalle mu, shigowar Jay ya mai da hankalin shi kan mu, fuskar shi babu fara a ya shigo. Har gabana ya iso, kaina a sunkuye, zama yayi a kujeran dake gaba na ya zauna. "Assalamu alaikum! Abba gata nan!" Ajiye min wayar yayi akan cinyata yayi tare da tsare ni da ido, mun jima muna magana ban gama magana da Baabi ba, wayata da take cikin shiru tayi haske, ina dauka naga Asood Buba Yaro, dake data na yana kune. Domin na cusawa Jay Haushi cikin sakalci na kashe kiran Baabi ina ce mishi. "Baabina zan kiraka an jima." Da sauri na dauki wayar ina me sake murmushi. "Sahibi na! Ya kake? ya kwana biyu?" Sake murmushin jin dadi nayi tare da mai da kai na jikin matashin ina sauke yar karamar dariya nace. "Hmm! Toh me ka shirya min idan na dawo daga daura wanda zai zame min na musamman?" Wani shegen shewa na saka, nan kuwa bakar magana Asood yake gaya min. "Kasan yadda nake kokarin na dawo mu hadu! Ayya Asood tun a Canada kak...." Jikin shi na wani irin rawa, ya fauce wayar hannu na, ya shiga gayawa Asood bakar magana,.karshe suka yi fada kaca-kaca. "Malam bani wayata! Kuma wallahi sai na kai karar ka gurin Ummi." Kallon Hanisah da Munih yayi cikin nutsuwa, take suka fita, kasa magana yayi yana kallona. "Wallahi idan baki rabu da yaron can ba!" Daga haka ya shiga ya kulle hanyar da Asood zai dame ni, kasa hakuri yayi ya fita da wayar, ban kuma ganin shi ba. Sai da aka gama hada min kaya a mota yazo ya same ni a falo ya cilla min kwalin sabuwar waya, tare da sabin layi. " Ki Cigaba da kwashe kwashe!" "Idan nayi akan ka nake? Ina ruwanka dani? Wai in tambaye ka Jay zaman ka nake da ba zanyi kwashe kwashe ba. Ince nan kace min baka sona Ina ruwanka da samarina!" Duk kanen shi sun zuba mana ido, ran shi ne ya b'aci. "Uban me kuke jira da bazaki bar falon ba!" A tsorace suka bar falon, yana zuwa ya dauke ne da mugun mari, sai da bakina ya fashe rike kuncina nayi! Kuka ya kwace min. "Allah ya isa min! Mugu kawai." "Kika kuma gaya min magana sai na zane ki!" "Sabida kai ne Ubanta? Wallahi Deen ka fita hanyar Fatimah ina ruwanka da ita, baka ce baka sonta ba? Uban me tayi maka da zaka mare ta!"Inji Rahil Kanwar Jannart, "Wai meke faruwa Rahil?" Inji Mamah Raihanah tare da Sarah. Cikin b'acin rai take nuna musu ni, ina kuka sosai. "Kawai ya bani wayata da layinka!" Na fada, banza yayi dani. "Baka ji bane? Ina wayarta da layinkanta?" "Na wurga a rijiya!" Daga haka Yasaka kai ya fita, kuka nake ina fadin. "Allah sai yabi min hakkina, lokacin da aka saya min waya babu shawarin wani banza balle ya dauki wayata ya wurga min, wawa kawai." Su kan su basu yi tsammanin zai dawo ba, sai ganin shi muka yi ya kamar zai rufe ni da duka. Da karfin tsiya ya janyo ni zai fita dani, Mamah Raihanah ta tsinka mishi mari, sai da ya sake ni. "Ta gaya maka wawa! Wanda bai san inda ke mishi ciwo ba, wani shegen ne yace ka yarda mata wayarta, ina ruwanka da ita? Toh wallahi ahirr dinka Ubanka ma bai isa yazo gabana yayi min rashin kunya ba, balle kai sakarai kawai kuma na kuma ganin ka daki wata a cikin masarautan nan sai na baka mamaki." Yana fita ta juye kaina ta balbale ni da fada, sannan ta dauki wayar da ya kawo min, ta mika min, dukda tafi rawa tsada da kyau amma bai burge ni ba. Da wuri na bar garin daura, shi kuwa uban yan ɗacin rai, haka ya wuni cikin dakin shi, fita masalaci yake sanya shi fita. Dayawan mutane, sun watse su Ummi ma sun koma Sokoto. Yana zaune, rike da yar na'ura me ƙwaƙwalwa, yana dube dube. Yaga sakon Munih. _Barka Jay😍_ Share ta yayi tare da cigaba da aikin shi, sake turo mishi wani tayi. _Ayya Jay kayi hakuri mana😭_ Bude sakon yayi tare da cigaba da abin aikin shi. _Jay ina sonka☺️_ Murmushi yayi sannan lashe bakin shi ya kashe wayar baki daya. ..... Abuja Bayan na dawo gida, sai da na kuma rashin lafiya, kamar bazan rayu ba, sannan naji sauki. ...... Yau muka yi da Rumah zan zo gidan ta, dan haka da wuri na gayawa Aunty Aina'uh, ita kanta taji dadin ganin na cire Jay daga cikin rayuwa ta. Da sauri na fita ina ce mata. "Uwata sai na dawo!" "Allah ya k'iyayye hanya, ki kula sosai don Allah." "Amin Ya Allah." Da sauri na nufi inda motar take, sanya driven ya kai ni Unguwar su. .... Karfe biyu na isa gidan, a hankali na fito daga motar nayiwa driven sallama, sannan na nufi cikin gidan, cikin nutsuwa. A farfajiyar gidan, na hango Khalid da wani mutum bayan shi kawai na iya hangowa, ban kuma kallon su ba, har na iso inda suke, gaishe da Khalid nayi ya amsa. "Gimbiya Aanih Fatimah! Kece a gidan mu?...." #Mai_Dambu... 10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar..... *Yariman Zazzau* Cikin zazzakar muryana nace Mishi. "Abban Maam nice ya aiki dasu Maam da Mamanta?"             Murmushi yayi sannan yace, "Alhamdulillahi, ya gida da jikin ki da fatan kin ji sauki ko?" "Gyada mishi kai nayi,.ina murmushin takaici. "Toh ki shiga tana cikin"      A sanyayye yayi wucewa ta,.ina ji a jikina ana bina da kallo, bayan na shige ya kalli abokin shi su cigaba da hirar su, ya ga yana bin bayana da ido. "S. Yarima! Ya dai?" Khalid ya tambayi abokin shi, lumshe idanunshi yayi wanda suke kamar yasha wani abu na maye.              "Kayi shiru kuma? Bayan kana bani labarin." Inji Khalid, "Wannan yarinyar daga wata masarauta take?" Tambayar yayi tare da kafe Khalid da ido, zuciyar shi tana wani irin rawa. Lumshe idanunshi yayi na wasu lokuta kafin ya bude ya kuma mai maita tambayar da yayiwa Khalid.        "Yar sarkin sokoto ce!" Ya bashi amsa a takaice,      Zubawa Khalid ido yayi sannan ya taɓe baki tare da shafa kan shi, sannan yace. "Ok wacce ta gudu  ranar aurenta?" Yayi tambayar tare da zubawa Khalid ido. "Ba gudu tayi ba! Sace ta aka yi."           Basar da zancen yayi kamar bai damu ba, ya cigaba da ta daddana wayar hannun shi.             Can ya d'ago kan shi kamar me ciwon baki yace. "Ina fatan ban mata tsufa ba? Don Allah Khalid gaya min gaskiya."         Gyara zama khalid yayikafin yace. "Ka tsufa dayawa! Kuma kaga zaka ba'a mata lokaci, kyanta ta sami wanda"     Harara ya watsawa Khalid, sannan yace. "Meye alaƙar ku da ita?"      Nan ya gaya mishi yadda suke tare da kuma zumuncin da ya kullu a tsakanin su.       Murmushi yayi sannan yace. "Yarinyar bata da kauɗi da rawan kai, ina son mace me kamewa haka saboda duk inda kuka shiga bazata baka kunya ba!" Nan yayi ta bayani tare da nunawa Khalid yadda Aanih ta kwanta mishi. .....    A cikin gidan kuwa tunda na isa,.muka yi sallah. Muka kuma tsinke da hira tare da shiga dakin girki, muka gama abincin rana sannan muka fito tare da shirya tabirin abinci.              Ta shiga wanka ina zaune a d'akinta, can tana fitowa nima na fito, ta kimtsa kan ta.             ..... Tana gamawa ta fito falon inda ta kira mijinta suka shigo da abokin shi, wanda yana shigowa ya zuba min ido, kamar zai cinye ni.  Sunkuyar da kaina nayi ina wasa da  bakin mayafina, har ta min magana. Koda na isa gurin abincin nace mata. "Kinga zuba min na koma falo zanfi sakewa."    Zuba min ido yayi sannan yacewa Khalid. "Kaga nima zuba min na koma falon."      Sake baki nayi ina kallon shi, b'ata rai yayi sannan ya kuma cigaba da latsa wayar hannu shi, tana gama zuba min sai da nace mata. "Nifa abincin yayi min yawa kuma bana cin namar kaza, sabida kiba. Ganyen ma ya ishe ni."     "Madam nima daga yau na ajiye cin namar kaza, sabida kar nayi kiba, zuba mana ganyen zamu ci a madadin nama," ya faɗa tare da tsume fuska, tana zuba min na mike.              Shima kuwa ya mike tare muka dawo falon, zama nayi ina kallon ikon Allah. Yadda na zauna a haka shima yazo ya zauna, haushi ya bani ban san lokacin da nace mishi. "Kai mayye ne?" "Eh ni mayye ne! Amma sai da na ganki na fara maita, sabida kurwanki zata yi zaƙi"    Sai kuma naga rashin dacewar abinda na fada, na kuma cigaba da cin abincin ina wasa da wayata, shi kan bai iya cin abincin ba, sai ma zuba min ido da yayi yana murmushi. Kar'ar wayar Ummu yayi yana kusada ni, ina duba fuskar wayar naga tasa. Saraki!   ... Tab'e baki nayi tare da mika mata wayar. "Assalamun Alaikum! Barka dai Saraki" Juyawa tayi tana kallona, kafin tace mishi. "Bana son damuwa! Wani munafuki ne ya gaya maka tana gidana? Saraki ka raba kanka da wahala, dan qaniyarka baka ce baka yinta ba, toh ina ruwanka da ita."                Can da taga hankalina ya fara zuwa kan ta, mik'ewa tayi ta shiga cikin dakin ta, nan suka yi ta faɗa da shi, kafin tafito ranta a b'ace, ina zaune naga sakon karta kwana.                  _Kiyi gaggawar koran mutumin kusa dake! Domin wallahi zan dauki mataki akan shi_   Sakon renin hankali na tura mishi kamar zai yi hauka, nace mishi. *Ayya ban gane wake magana ba, ko Baabina kai ka canza layi*   Nan ya shiga cikin tashin hankali tare da turo min sako yafi karfin goma, nima kuma yana isata na rufe shi baki daya, amma dake bai da zuciya ya kuma turo min sakon ta wayar Najim. ....karshe rufe wayar nayi baki daya, yayi ta kiran Ummu taki dauka karshe itama kashe wayar tayi itama tunda yace bayayi. Kuma muka rasa ta ina ne aka gaya mishi akwai wani a tare da mu.   ...... Ban wani ci abincin ba, na  kai dakin girki, na rufe sannan nazo muka koma d'akinta nan muka shiga hira kamar ba gobe.                   Anan take bani labarin abin da  Jay yayi mata, d'azun murmushi nayi sannan nace mata. "Ayya ya kyautawa kan shi." Ban kuma magana ba, har dai la'asar nayi sallah, muka d'an tab'a hira sannan na mike zan tafi.       Nan muka fito falon, kamar wanda na ajiye shi ya jirani, ina fitowa ya mike shi ma, har waje suka rakomu, sannan ya nace min na shiga motar shi, dakyar dai na shiga.        Kamar ba zan shiga ba, kawai Ummu tasani na shiga. Ina tuna hirar da muka yi da ita tana bani labarin wannan mayyen da ya addabi rayuwata yau ɗaya.        --- *Masarautar Zazzau* Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci. Zazzau Emirate Yadda kalmar  ‘Zazzau? ta samo asali Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau? yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo?, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro. A wani kaulin kuma ‘Zazzau? na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau?, wato ‘Mai Dauke da Zazzau?. Asalin Kalmar Zariya Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina Bambancin Zazzau da Zariya Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan kasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni. Kafuwar Masarautar Zazzau Mahaya dawakin Zazzau A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu  ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma kaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo?, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci. Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Habe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama. Kuma Zazzau na daya daga cikin kasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki. Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi. Wadanda suka biyo bayansa sun kafa biranen  mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin su je Zariya. Nohir ta auri wani bako, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa dan suna dan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536. Bakwa Turunku ya yi sarauta ne a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can kasan tsaunukan da suke shimfide  a yankin gabashin Zariya. Kafuwar birnin Zariya Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta. Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537.  Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya. Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da Sarauniya Amina, wadda ita ce 'ya a wajen Zariya, ta dawo daga yake-yakenta, sai ta ce wurin ya yi fadi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan zamani na yake-yake, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da Fulani suka karbi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki. Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya.  Don ta girmama suna ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau.  Ana kiran gidan da sunan ‘Gidan Bakwa?. *Asalin Ganuwar Zazzau* A zamanin da,  mai karfi shi ke da iko a kasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce kungiyar al’umma da suke so su yi karfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a kasar Hausa, kuma inda duk aka yi ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen. To, a Zazzau wadanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata, wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina ta Zariya.   Ganuwar Zariya, ita ce ta dauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta Kofar Galadima, ta Kofar Kona, ta hada da rafin Saye, sannan ta koma ta Gwargwaje, ta hadu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaki, sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a tsakiya ya kewaya aka yi kofofin garin guda takwas, wadanda suka hada da Kofar Kibo, da Kofar Kona da Kofar Galadima, da Kofar Bai, da Kofar Doka wadda a da ake kira Kofar Kano, da Kofar Jatau, da Kofar Kuyambana da kuma Kofar Gayan. *Sarauniya Amina* Sarauniya Amina Habe ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a jerin sarakunan Habe. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a karkashin sarautar Habe. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya, akwai Madanni, da dai sauran su. Duk wadannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan Habe. Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban dan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji na wannan masarauta. To, ita Amina ita ke rike da wannan kambi, kuma ita ta yi ta yake-yake. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare iyakokin masarautar Zazzau. Ta yi kudu da yamma, don kara fadi kasa da karfin mulki, kuma da haka ne ta dangana da kasar Naija ta yanzu, ta dangana da kasar Idah, wato kasar Attah Gara a jihar Kogi. Ta je har kasar Nasarawa ta yau, saboda karfin yaki da iya gudanar da yaki da jaruntaka. Tana da rundunoni da take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi ya nuna. *Sarakunan Habe* Tarihi ya nuna cewa, an yi sarakuna sittin na Habe, wadanda suka mulki masarautar Zazzau tun daga kan Gunguma, wanda shi ne ya fara yin sarauta a matsayin ‘Madau-Zazzau? na farko a wancan lokaci, kuma shi jika ne na Bayajidda. Habe sun kwashe shekaru fiye da dari suna mulki, har ya zuwa lokacin mulkin Sarkin Zazzau Makau, wanda shi ne na karshe a jerin sarakunan na Habe, wanda shi ne ya fara zuwa Suleja (wadda aka fi sani da Abu-Ja tun asali). Ga kuma jerin sunayen sarakunan na Habe: Gunguma Matazu Tumsah Tumusa Suleman Maswaza Dinzaki Nagogo Katchina Nawanci Macikai Kawo Bashi Kar Majidadi Dihirahi Jinjiku Sakannu Monan Abu  daga shekarar 1550 zuwa 1530 *Gidan Dan Masukanan  daga shekarar 1530 zuwa 1532* Nohir  daga shekarar 1532 zuwa 1535 Kawanissa daga shekarar 1535 zuwa 1536 Bakwa Turunku daga shekarar 1536 zuwa 1539 Ibrahim daga shekarar 1539 zuwa 1566 Karama daga shekarar 1566 zuwa 1576 Kafo daga shekarar 1576 zuwa 1578 Bako daga shekarar 1578 zuwa 1581 Aleyu I daga shekarar 1581 zuwa 1587 Isma’ilu daga shekarar 1587 zuwa 1598 Musa shekarar 1598 Gadi daga 1958 zuwa 1601 Hamza shekarar 1601 Abdullah daga shekarar 1601 zuwa 1610 Burema daga shekarar 1610 zuwa 1613 Aleyu II daga shekarar 1613 zuwa 1640 Muhammad Rabo daga shekarar 1640 zuwa 1641 Ibrahim Basuki daga shekarar 1641 zuwa 1654 Bako II daga shekarar 1654 zuwa 1657 Sukana daga shekarar 1657 zuwa 1658 Aeyu III daga 1658 zuwa 1665 Ibrahim  daga shekarar 1665 zuwa 1668 Muhammad Abu daga shekarar 1668 zuwa 1686 Sayo Ali daga shekarar 1686 zuwa 1696 Bako Dan Musa daga 1696 zuwa 1701 Is’haq daga shekarar 1701 zuwa 1703 Burema Ashakuka 1703 zuwa 1704 Bako Dan Sunkuru daga shekarar 1704 zuwa 1715 Muhammad Dan Gunguma daga shekarar 1715 zuwa 1726 Uban Bawa daga 1726  zuwa 1733 Muhammad Gani daga shekarar 1733 zuwa 1734 Abu Muhammad Gani shekarar  1734 Dan Ashakuku daga shekarar 1734 zuwa 1737 Muhammad Abu daga shekarar 1737 zuwa 1757 Bawo daga shekarar 1757 zuwa 1759 Yunusa daga shekarar 1759 zuwa 1764 Yakubu daga shekarar 1764 zuwa 1767 Aleyu IV daga shekarar 1767 zuwa 1773 Cikoku daga shekarar 1773 zuwa 1779 Muhammad Maigamo daga shekarar 1779 zuwa 1782 Is’haq Jatau daga shekarar 1782 zuwa 1802 Muhammad Makau daga shekarar 1802 zuwa 1804 Yadda wasu wurare suka fita daga masarautar Zazzau Lokacin da Shehu Usman Danfodiyo ya kawo jihadi a wuraren Hausa Bakwai da Banza Bakwai, Malam Musa yana jagorancin yaki. A tarihince, an ji cewa an kama Zazzau ba tare da an kashe ko da mutum daya ba. Malam Musa ya shiga Zazzau ta Kofar Bai, a lokacin sarkin Zazzau na karshe na Habe, Sarki Makau ya fita da dakarunsa, ya bi hanyar Hunkuyi, hanyar Kudan, hanyar Kano, tun da an ba shi labari cewa, Malam Musa zai biyo ta hanyar Kano, to sai ya bi wannan hanya. Shi kuma Shehu Usman Danfodiyo, sai ya ba Malam Musa shawara to ya kauce wa wannan hanya. Ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin ilhamar manyan malamai na da, bayin Allah, suna addu’a, suna rokon Allah Ya ba su haske da ilhamar yadda abubuwa za su kasance. Sai aka fada wa Malam Musa, cewa kar ya bi waccan hanya ta Kano, ya zagaya ya bi ta garin Likoro. Kuma haka ya bi, ya zagaya ya bi Farin Kasa da ke kasar Soba ta yanzu, sannan ya bullo wa Zariya ta Kofar Bai, ya kuma shiga garin. Bayan shi kuwa Sarki Makau yana ta baryar arewa maso gabas, yayin da Malam Musa ya bullo ta arewa maso yamma, saboda haka ba a hadu an gwabza yaki ba. Da haka Malam Musa suka shiga cikin birnin Zariya, suka rufe kofofin birnin, Sarki Makau na waje, yana jira, sai labari ya isa gare shi, cewa ai Fulani sun shiga Zariya sun kulle kofofi, wato an kori su Sarki Makau kenan. Daga can Sarki Makau ya gudu, ya nufi kudanci, ya je nan, ya je can, don a lokacin akwai sarakuna irin su Sarkin Fatika da Sarkin Kajuru da Sarkin Kauru da sauran su, wadanda duka da suna bin Sarkin Zazzau na Habe. Amma da Fulani suka zo, sai suka yi wa Sarki Zazzau Makau tawaye, suka bi Fulani. Suka ci gaba da biyayya, suka kuma zauna a karkashin Sarkin Zazzau musulmi, Bafulatani. Da haka fadin kasar Zazzau ya fara raguwa. Bayan da Sarki Makau ya bar Zazzau, ya nufi kudanci yana neman goyon bayan kananan sarakunasa da ke can gefe,  wadanda tun zamanin Sarauniya Amina aka ci su da yaki, suna biyayya ga masarautar Zazau. To, Shehu Usman Danfodiyo ya ce, idan mayakan Malam Musa sun sadu da wani wuri da wani babban dutse a kudu maso yamma da Zazzau, su tsaya a wurin. Iyakar daular da yake so ya tabbatar kenan. Inda Makau ya tafi, ya wuce wannan wuri, to, kar su bi shi. Hakan ne kuma aka yi. Wannan shi ya sa aka kafa Zazzau Suleja a wurin, shi Sarkin Zazzau Makau shi ya tsaya a nan, kuma dakarun Malam Musa ba su ci gaba da bin su ba, suka koma Zariya. Saboda haka, ba a yi yaki da ya wuce wannan wuri ba. Wato dai masarautar Suleja daga Zazzau ta fito, don haka har gobe masu sarautar Suleja suke kiran kansu da mukamin Sarkin Zazzau, amma Suleja. Shi ya sa za ka ji ana cewa, Sarkin Zazzau Suleja. Kuma duk sunayen unguwannin da ke cikin birnin Zariya, su ne za ka samu a Suleja, kamar su Kwarbai, Anguwan Fatika, su Kusfa, Anguwan Iya da dai sauransu. Saboda sun maimaita wadannan abubuwa da suka baro a Zariya. Sai dai kuma a wani kaulin, an ce Malam Musa ya ziyarci Zariya ne tun kafin jihadin Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya zauna a birnin yana koyar da karatun Al-Kur’ani da sauran littattafan addinin musulunci. To, da jihadin ya shigo, ya kasance yana cikin mukarraban Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya sami matsayin ja-goran yaki. Da haka Malam Misa da mayakansa suka kai hari ga Muhammadu Makau, Sarki na  sittin a jerin sarakunan Habe, a ranar Asabar goma ga watan Zulhaji a shekarar 1804, lokacin yana filin sallar Idi da ke wajen garin Zariya. Duk da yake dai Muhammadu Makau yana tare da dimbin mazaje tare da shi a lokacin harin, an ci shi da yaki. Saboda ba sa iya komawa cikin gari su dauko makamansu. Don haka aka tilasta masa tserewa tare da wasu magoya bayansa zuwa  Zuba da ke kudancin yankin masarautar Zazzau, inda a can ne ya yi tirjiya ga hare-haren Fulani. Daga cikin mutum dubu uku da ke tare da shi akwai ‘yan uwansa Abu-Ja da Abu-Kwaka. A wannan wuri ne Sarki Makau ya zauna, kuma wadanda suka gaje shi suka  karfafa, suka kafa wata sabuwar masarautar Zazzau ta Habe mai cin gashin kanta a kasar da daga baya aka rika kira Abuja. Da ma kuma jama’ar yankin suna biyayya ga sarakunan Zazzau. Wannan masarauta ta Habe ta rayu har ya zuwa lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, duk kuwa da matsanantan hare-hare da Fulani ke kai masu. Kuma sarakunann Zazzau na Abuja, sun rike mukaman da suke da su na asali tun daga Zariya. Sarakunan Habe na Suleja (Abu-Ja) Sarakunan Habe na Suleja (Abuja), sun samo asali ne daga tsatson Is’haq Jatau, Sarkin Zazzau na hamsin da tara a Zariya, wanda ya yi sarauta daga shekarar 1782 zuwa 1802. Ga kuma jerin sarakunan da suka yi mulki a wannan masarauta ta Suleja (Abu-Ja) daga farko zuwa yau: Muahammadu Makau daga shekarar 1804 zuwa 1825 Abu-Ja daga shekarar 1825 zuwa 1851 Abu-Kwaka  daga shekarar 1851 zuwa 1877 Ibrahim Iyalai daga shekarar 1877 zuwa 1902 Muhammad Ganu daga shekarar 1902 zuwa 1917 Musa Angulu daga shekarar 1917 zuwa 1944 Suleman Barau daga shekarar 1944 zuwa 1979 Ibrahim Dodo Musa daga shekarar 1979 zuwa 1993 Muhammad Awwal Ibrahim daga shekarar 1993 zuwa yanzu A yanzu dai akwai masarautu biyu na Zazzau, wato Zazzau ta Fulani da ke da hedikwata a Zariya, da kuma Zazzau ta Habe mai hedikwata  a Abuja wato wurin da a yanzu aka fi sani da Sule-Ja). *Sarakunan Fulani* A lokacin da Shehu Usmanu Dafodiyo ya yi jihadi daga shekarar 1804, kasar Zazzau ta dangana da inda Habe suka tsaya, wato kasar Idah a jihar Kogi ta yau A zamanin Sarkin Zazzau, Malam AbdulKarim, daga baryar kudu masarautar Zazzau ta dangana da har zuwa inda a yanzu ake kira Nasarawa, kuma har zuwa gabar kogin Benuwai. A baryar arewa kuwa ta yi iyaka da sauran kasashen Hausa bakwai, kamar Katsina ta fuskar arewa, da Kano ta fuskar arewa maso gabas, sai Bauchi da Filato a arewa maso yamma. Kuma daga Zazzau ne ake nada sarakunan kasashen da ke karkashin masarautar ta Zazzau Sarkin Zazzau na farko a karkashin daular Usumaniyya, shi ne Malam Musa, wanda Shehu Usumanu Danfodiyo ya ba tutar jaddada musulunci a kasar Zazzau, kuma na karshe kuma shi ne Sarkin Zazzau Makau wanda Turawan mulkin mallaka suka kawar. Ga kuma jerin sunayen sarakunan Zazzau na Fulani: Malam Musa daga shekarar 1804 zuwa 1821                                                     Malam Yamusa deaga shekarar 1821 zuwa 1834                                                           Malaam AbdulKarimu daga shekarar 1834 zuwa 1846 Malam Hammada daga shekarar 1846 zuwa 1853                                                  Mamman Sani daga shekarar 1846 -1853 Sidi AbdulKadir daga shekarar 1853-1853 Malam AbdusSalami daga shekarar 1853 zuwa 1854 Malam AbdulLahi (nadi na farko) daga shekarar 1857 zuwa 1871 da (nadi na biyu) daga shekarar 1874 zuwa 1879 Malam Abubakar daga shekarar 1879 zuwa 1888 Muhammadu Sambo daga shekarar 1888 zuwa 1890 Muhammadu Yero daga 1890 zuwa 1897 Sarki Malam Kwasau daga 1897 zuwa 1902 (shi ne sarki na karshe kafin zuwan Turawa) Zuwan Turawan mulkin mallaka Alu Dan Sidi (shi ne Sarkin Zazzau wanda Turawan mulkin mallaka suka fara nadawa) daga shekarar 1903 zuwa 1920 Sarki Dalhatu daga shekarar 1920 zuwa 1924 Sarki Ibrahim Dan Sarkin Zazzau Kwasau daga shekarar 1924 zuwa 19337 Sarki Jafaru daga shekarar 1937 zuwa 1959 Alhaji Muhammadu Aminu daga shekarar 1959 zuwa 1975 Alhaji Shehu Idris (wanda ke kan karagar mulki yanzu) daga shekarar 1975 zuwa yau *Gidajen Sarautar Zazzau* A karkashin Daular Fulani, masarautar Zazzau tana da gidaje hudu, wadanda  suka hada da: ·        *Gidan Mallawa* wanda Malam Musa ya kafa, 1. Sarkin Zazzau Malam musa 2. Sarkin Zazzau Malam Abdulkadir dan Musa 3. Sarkin Zazzau Malam Abubakar dan Musa 4. Sarkin Zazzau Malam Alu Dan Sidi. ·     *Gidan Barebari* wanda Yamusa ya kafa, 1.Sarkin Zazzau Malam Yamusa 2. Sarkin Zazzau Malam Hammada dan Yamusa 3. Sarkin Zazzau Malam Mamman Sani dan Yamusa 4. Sarkin Zazzau Malam Abdullahi dan Hammada                                                          5. Sarkin Zazzau Malam Yero dan Abdullahi 6. Sarkin Zazzau Malam Kwasau dan Abdullahi 7. Sarkin Zazzau Malam Dalhatu dan Yaro 8. Sarkin Zazzau Malam Ibrahim dan Kwasau 9. Sarkin Zazzau Malam Ja'afaru dan Isiyaku ·        *Gidan Katsinawa* wanda Malam AbdulKarim ya kafa, 1. Sarkin Zazzau Malam Abdulkarim 2. Sarkin Zazzau Malam Sambo dan Abdulkarimu 3. Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Aminu 4. Sarkin Zazzau Malam Shehu dan Idrisu Auta ·        *Gidan Sullubawa (Fulani)* wanda Malam AbdusSalam ya kafa. 1. Sarkin Zazzau Malam Abdulsalam Kowanne gida dai ya biyo asalin inda wanda ya kafa shi ne ya fito. Mallawa Fulanin Futo Toro  ne da suka fito daga kasar Mali, Barebari kuma sun fito ne daga Kukawa a yankin da a yau aka fi sani da Jihohin Barno da Yobe, amma asali su Fulani ne, kuma ana kallon su ne a matsayin Fulani. Saboda haka ne ma ake kiransu da Fulata-Barno. Haka Sullubawa Fulani ne da suka fito daga yankin jihohin Sakkwato da Kebbi, kuma yadda AbdusSalami Basullube ya sami sarautar Zazzau kenan. *Yadda aka sami gidaje hudu na sarautar Zazzau* Gidan sarautar Zazzau ya kasu hudu ne, saboda Zazzau kasa ce wadda ta tattara dimbin al’umma da suka fito daga wurare daban-daban, don neman ilimin addinin musulunci. Saboda haka, a lokacin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya zo, an sami malama ne masana  ilimin addinin musulunci, da shari’o’i, da kuma ka’idar mulki na musulunci. A lokaci ba wai ana la’akari ne da cewa wane ya gada ko wane ne ya gada ba, ana neman wanda zai zama khalifa, don tabbatar da kafuwar addinin musulunci a Zazzau. Zazzau wata cibiya ce, tun ma kafin jihadi Shehu Usman Danfodiyo, saboda kasancewarta ‘Zo-zo?, kasa mai albarka, mai daukar komai da komai na noma, tana da laima da ni’ima. Kowa yana son ya je ya zauna a Zazzau, ya amfana ta fuskar noma da kiwo. Wannan ya sa Fulani da yawa suka zauna a Zazzau tun zamanin mulkin Habe, kuma da yawansu abin da suke yi baya ga kiwo, shi ne karatun addini. Kuma lokacin da dan uwansu Shehu Usman Danfodiyo ya bullo, sun kai masa gaisuwar caffa, suka yi masa mubayi’a, ya yarda da su. Suka zauna da shi, suka yi karatu tare da shi, suka yi yake-yaken da aka yi tsakanin Sarkin Gobir da Usman Danfodiyo. Tun kafin a yi ganuwa, akwai mutane, wato Fulani, irin su Malam Musa da Yamusa da Malam AbdulKarim da su AbdulSalam da ke zaune a cikin garin Zariya, suna koyarwa ta addinin musulunci. Da suka ji bullowar Shehu Usman Danfodiyo yana zuwa wurare daban-daban yana kira da a gyara addinin musulunci, suka yadda da abin da yake yi, suka yi masa mubaya’a Tarihi ma ya nuna cewa, Malam AbdulKarim ya zauna da Shehu Usman Dan Fodiyo, ya yi karatu a wajensa. Shi kuwa Malam Musa kusan tsaran Shehu Mujaddadi ne, kuma tare suke tafiye-tafiye. Gidan Malam Musa Malam Musa shi aka ba tutar sarauta a lokacin da jihadi ya iso Zariya, Malam Musa shi aka ba wannan tuta, don ya yi jagoranci, kuma bayan mutuwar Malam Musa, ba a mayar da sarautar ta zama gado ba. To, bayan mutuwarsa ba a mayar da abin ya zama gado ba, sai aka ba wani daga cikin malaman da suke tare da Shehu Usman Danfodiyo, wato Malam Musa. Kuma Shehun ne da kansa ya ba shi tutar halifanci. Gidan Malam Yamusa Kana sai Shehu Usman Danfodiyo ya ba Malam Yamusa shugaban rundunar sojojin yaki na Malam Musa a matsayin Madakin  Zazzau.                                                  Gidan Malam AbdulKarimu Shi kuma Malam AbdulKarimu, Shehun ya ba shi sarautar Sa’in Zazzau, wato mai ilimin rabon arzikin kasa.Ya san masu dabbobi da suka cancanci bayar da zakka, ya san manoman da suka cancanci bayar da zakka, ya san nisabin dukiyar da za a fitar wa zakka. Ya kuma san su wa ya kamata a ba zakkar. Gidan Malam AbdulSalam Shi kuwa Malam AbdulSalami yana cikin dalibai Fulani wadanda suka yi amfani wajen taimakon Shehu Usman Danfodiyo a yake-yaken da ya yi tsakaninsa da Sarkin Gobir. Amma shi ba ya bullo ne kamar yadda su Malam Musa da Yamusa da AbdulKarimu suka bullo ba. Hawan Malam AbdulSalam kan gadon sarauta ya kasance raba-gardama ne, saboda lokacin da sarautar Zazzau ta koma gado, ’ya’yan gidan sarakunan guda uku suka fara cewa sai daga cikinsu ne za a sami wanda zai zama sarki a Zazzau, sai ‘ya’yan Sarkin Zazzau Yamusa suka fara irin wannan  sarautar. Inda Hammada ya fara sarauta, daga nan sai kanensa Mamman Sani. Bayan Mamman Sani ya kau, sai Sidi AbdulKadir, babban dan Malam Musa da Shehu Usman Danfodiyo ya ba tuta, ya zama sarki bisa gado. Shi ma yana da ilimin addini, kuma ya cancanci rike sarautar. Sai dai bayan da Sidi AbdulKadir ya zama sarkin Zazzau, an yi ta samun kwamacala da rigingimu, tun da abin ya zama gado kowa ma dan gida yana ganin ya cancanci rike sarautar. Daga nan aka fara samun rashin yarda da juna, har aka kai kara Sakkwato, aka dakatar da Sarkin Zazzau Sidi AbdulKadir daga sarauta. Shi kuma ya ce, duk zargin da ake masa na sarautar ba shi kadai yake sarautar ba. Tare da shawarar dukkan ’yan majalisarsa ake yi, wato su masu son a ba su sarautar nan. Saboda haka, ba wanda ya cancanta a cikinsu, kamar yadda shi ma bai cancanta ba. Saboda haka, sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ga ya fi dacewa a dauko wani malami cikin daliban Shehu Danfodiyo a ba shi jagoranci, duk da ya manyanta a wannan lokaci. Kuma lokacin ya yi tsawo, Malam Musa ya yi shekaru goma sha, Yamusa ya yi shekaru goma sha, AbdulKarim ya yi shekaru goma sha, Hammada ya yi ’yan kwanaki, Mamman Sani ya yi shekaru, Sidi AbdulKadir ya yi wata takwas zuwa goma a gadon sarauta. To, idan ka tara wadannan shekaru, ka ga an dumfari shekaru arba’in. To, shi Malam AbdulSalam idan ka dora shekara arba’in a kan shekarunsa, ka ga ya manyanta. Amma sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ce a ba AbdulSalami sarautar Zazzau ya rike. Da haka ya zama raba-gardama. Ba a ba kowa ba daga cikin ‘ya’yan wadancan sarakuna. Wannan kuma shi ne dalilin zuwan gida na hudu a sarautar Zazzau kenan, wato don a sami natsuwa.                                                                                                                                                                                                             Ta haka ne aka sami wadannan khalifofi guda hudu, kuma kowannensu an ba shi sarauta ne a matsayin kansa na masanin addinin musulunci, na mai biyayya da gaskata abin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya kawo bisa koyarwa Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau. Ina Sarki ya taso? Shi Mai martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini. A nan dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira ‘Town School one?, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School?. Yanzu ana ce mata ‘Waziri Lawal Local Government Education Primary School?, a nan ya fara karatu. Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School?.  Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers? College?.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda shi ne babbar sana’arsa ta farko da ya iya. Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a kasar ta Osireliya Wuraren da ya yi aiki Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar ‘Town School No.3’?. A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma karkashin hukumar ‘NA? (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA?, kuma yana aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa. Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority? a wannan lokacin.                                                              Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau. A shekarar 1975 likafarsa ta yi gaba, aka ba shi a sarautar Sarkin Zazzau. Sauyin da ya kawo a sarautar Zazzau cikin shekaru arba’in da biyar yana mulki Makusantan Sarkin suna ganin ba wani al’amari da ya shafi rayuwar Zage-zagi a birnin Zariya ko a masarautar Zazzau ne da ba a sami ci gaba ba. Ta fuskar ilimi, tun daga kananan makarantun firamare zuwa sakandire, zuwa na gaba da sakandire, zuwa jami’o’i, makarantun sojoji da sauransu da aka yi a masarautarsa, akalla ba za a rasa makarantu ashirin ba. Iyalin Sarki Allah Ya albarkaci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris da iyali masu yawa. Yana da mata hudu, da ‘ya’ya maza da mata da yawansu ba zai gaza arba’in da biyu ko da biyar ba. Dabi’u da halayen Sarki Daya daga cikin hakiman masarautar Zazzau, Salanken Zazzau, Dokta Muhammadu Bello AbdulKadir, ya ce, babbar baiwar da Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shi ne hakuri, yana da hakuri matuka. Ga shi kuma yana da kawaici, wanda a sakamakon haka ne ya kai kusan shekara ashirin yana sarauta, amma bai nada kowa daga cikin ‘ya’yansa sarauta ba, saboda kawaici. Sai da dattawa suka matsa masa, cewa idan bai nada ‘ya’yansa a sarauta ba, wa zai nada masa su. Hakurinsa da dauriya suka sa Zazzau ta zama kowa ya zo karbabbe ne, zai zo ya sami karbuwa wajen al’umma ya yi kasuwanci, ko ya nemi ilimi, ko ya yi kasuwanci ko sana’a da sauransu. Don haka, birnin Zariya ya zama wata matattarar kowacce kabila daga sassa daban-daban na Najeriya; ba kabilar da ba za ka samu ba a masarautar Zazzau. Masallacin Juma’ar masarautar Zazzau Zazzau wurin ne wanda tun kafin bullowar jihadin Shehu Usman Danfodiyo akwai rukuni-rukuni na Fulani a cikin gari da kauyuka wadanda aikinsu shi ne bayar da karatu na addinin musulunci. Kuma tun a wannan lokaci akwai masallacin juma’a a unguwar Juma cikin birnin Zariya, wanda aka gina a zamanin mulkin Isiyaku Jatau wanda Habe ne. Malaman unguwar Juman nan ko da aka yi jihadi sun ci gaba da limanci, kuma har yau su ke limanci, tun da su ma Fulani, kuma an same su da iliminsu. Ko da Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim ya gina masallaci a kofar fada, wancan masallacin na unguwar Juma ya rushe, an ci gaba da yin sallar Juma’a tare da limanci wadannan Fulani na unguwar Juma.Har yau zuri’arsu ke limanci.  Abin da kasar Zazzau ta ginu a kai Ita Zazzau kasa ce da ma da ta ginu ne a kan abubuwa biyu, wato ilimin addinin musulunci, da harkar noma da kiwo. Kuma ko da Shehu Usman Danfodiyo ya yi jihadinsa abin da ya karfafa kenan. *Wasan Kanawa da Zage-zagi* Kamar yadda masana tarihi kan fada, mai karfi shi ke da iko. To, a wancan zamani, daular da ta yi karfi sai ta yunkura ta je ta mamaye wata. To, inda aka yi nasara, sai ka ji, amma inda aka gwabza, aka yi kare jini biri, ko kuma kowa ya tare kan iyakarsa, sai ka ji irin wadannan wasannin suna aukuwa. Haka ma inda aka sami nasarar cin su da yaki, sai ka ji irin wannan wasa yana faruwa. Misali za ka ga Katsinawa da Gobirawa ana irin wannan wasa. To, Kanawa da Zage-zagi ma akwai wannan wasa, cewa ita Sarauniya Amina ta kai hari Kano har Kofar Mata. Wannan kofar ai ana cewa nan ne aka dakatar da Sarauniya Amina, aka hana ta shiga cikin birnin Kano. A wancan zamani na mulkin Habe dai, an ce an wani sarkin Kano ya kawo farmaki har Zariya, amma aka tare shi a tsakanin yankin da a yanzu aka sani da karamar hukumar Kubau, wajen garin Kargi. Aka yi ba-ta-kashi. Saboda haka, ba mamaki ka ji ana wasa tsakanin Fulani da Barebari, tsakanin Katsinawa da Gobirawa, tsakanin har Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga irin wannan wasa yana dada dinke zumunci ne, ba yana batawa ba ne. Wannan dai duk a zamanin mulkin Habe ne aka yi ire-iren wadannan hare-hare. Amma yayin da aka sami shigowar daular Usumaniyya, back kasashen suka zama daya, addinin musulunci ya hade su. Saboda haka, wata kasa ba ta kai wa wata kasa farmaki ba a cikin titocin da Shehu Usumanu Danfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan hulda, kuma abokan shawarar juna. *Girman kasar masarautar Zazzau a halin yanzu* Sauyin da aka samu bisa sabon tsari na gwamnati, a yanzu a kowacce karamar hukuma ana da gundumomi ashirin da uku wadanda hakimai suke mulki a karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau. Kamar dai yadda gwamnatin jiha mai ci yanzu ta mayar da su. Amma gwamnatin baya ta nunnunka wadannan gundumomi, saboda ana shigo da harkar siyasa a cikin masarautun. Wata gwamnatin ta zo ta kara gundumomi, har sun kai tamanin da shida, ita kuma wannan gwamnati da ta zo sai ta rage su zuwa ashirin da uku. A zamanin mulkin soja an yanke wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Kaduna, wadanda ke lardin Zazzau, wadanda suka hada da Kaciya da Zonkwa. Ta yankin kudu, sai aka bar lardin na Zazzau da kananan hukumomin Igabi da Kaduna ta kudu da Kaduna ta Arewa. Ta arewa akwai kananan hukumomin Giwa da Kudan, ta gabas kuwa akwai Makarfi da Ikara da Kubau. A yankin tsakiya kuwa akwai kananan hukumomin Soba da Sabon Gari da Zariya. A yanzu kananan hukumomi goma sha daya da gundumomi ashirin da uku kenan suke bin masarautar Zazzau a yau. A da kuwa tun daga karamar hukumar Kaciya, zuwa Chikun, har zuwa Kagarko, duk suna bin Zazzau ne. Amma daga baya aka sami wata gwamnati ta soja ta yanke wadannan kananan hukumomi, ta yi wasu sababbin masarautu, abin da ya sa aka sami masarautu kusan talatin da biyu. Saboda ra’ayin siyasa na son a ba kowacce kabila ‘yancinta, kar a ce an Dianne wa nice yanki a jihar. ---- Mu koma labari... Saifullah....... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....   *Ma sha ruwa.. magirbi* *Saifullahi Ahmad sullubawa* Shine d'a na biyar a gidan sarautar Zazzau, mahaifin shi sarki Ahmad Abdullahi Sullubawa, shike mulkin Masarautar Zazzau a yanzun, sarki me matukar adalci, Sarkin da talakawan shi ke matukar son shi da kaunar shi.       Mutum me kawaici da rikon amana.     Sarki Ahmad yana da mata hudu russ, da yara Kimanin goma sha biyar.             Maza da mata kuma, Saifullahi shine d'a na biyar, kafin shi akwai hudu a saman shi biyu mata biyu maza, Abdullahi shine na fari, sai takwaran Sarkin Kano wanda ake kiran shi San kano, Adamu. Sai Mariya, sannan Asma'u.   Sannan Saifullahi, dakin su Saifullah su maza uku ne da mace daya ne sai sai sauran goma sha daya, sun kasance dakunan. Inda me bin mamansu Saif tana da yara uku mata biyu namiji ɗaya, sai me bin ta tana da yara maza biyu rak. .sai amaryan da take da mata uku namiji ɗaya.      Duk da ana zazzafar kishi amma haka bai hana kasami hadin kai a gurin Yaran su ba, domin su saif sune manyan, dukda akwai wasu a gaban shi.      Amma a halin yanzun anfi mishi kallon shi zai gaji mahaifinsu. Sabida hakuri da juriya,          Sannan masarautan tana da wani irin tarihin al'ajabi na rasuwan tsohon sarki, Shehu dan idrisa. Yakasance sanda uwarshi ta haifrshi a ranar kudan Zuma sukazo gidan har kofar dakinta sunata yawo daga sama zuwa kasa daga baya suka rankaya suka tafi, Haka ranar da aka bashi mulki na sarautar kasar zazzau ma wannan kudan zuman sunzo mashi suntafi, Ana jibi ze rasu Dan kadan sunzo ana gobe zai rasu masu yawa sukazo sunata shawagi suje sama su dawo kasa kamar masu Kai gaisuwa za a kashe su girgiza kai yayi sannan yace. " kowacce rayuwa tana tafe ne da mahadin ta, a'' a barsu  suma iya wannan shine wa adin da ya rage tsakanin mu, muyi sallama. Dan haka kar a cutar dasu idan sun tafi ba lallai bane su kuma dawowa"haka  suka zo . Daga bayan sun tafi seya girgiza Kai kawai ya cikin matsanancin jin jiki ya kalli  uwargidansa yana  cewan. "Nifa  lokaci yayi Daman inata ganin wasu halittu daban masu cutarwa Amman basumin komai harda maciji.  Dan Allah bai nufa zasu cutar dani ba, kome na rayuwa yana da iyaka, dan haka zan tafi." (Wannan labarin da na bada na Sarkin Zazzau! Gaskiya ne domin nima haka aka turo min sakon, kuma Alhamdulillah naga ya shiga cikin labarin) ..... "Aanih Fatimah! Baki cewa zararre irina kome ba!"  Da wutsiyar ido na kalle shi, sannan na kauda kaina, tare da kallon gefe na.           Shiru yayi bai kuma magana ba, tunda yaga naki magana,  juyawa nayi na kalle shi. Murmushi yayi sannan yace. "Na zata zaman kurame zamu yi."               Juya idanu na nayi, sannan na mai da kaina inda nake kallo nace. "Ka tsaya daga bakin kofar gidan tunda ka fahimci inda na fito."            ... "Duk inda kike fito! Ya nuna min cewa an shuka bishiyar zinariya ce ta bada Lu'ulu'u, dan kinfi karfin jauhari ko azurfa."         Muna shiga kwanar gidan, na nuna mishi inda zai sauke ni.         Bai kula ni ba, har cikin gidan ya shiga dani, bud'e motar nayi zan fita najita a rufe, juyawa nayi muka kalli juna. "Koda baki magana ba, zan isa sokoto na gabatar da kaina."       Shafa kan shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya lashe bushashen lebban shi, yace. "Balle kuma nasan kina yina!" Sake kallon shi nayi a karo na biyu, kaifin idanun shi ya sani sunkuyar da kaina.            Na shiga wasan dole. Saif ya haɗu, babu karya ya kai a so shi, kawai zuciyata bata yin shi ne, tana can manne da Jay. Bude baki nayi zance mishi yayi hakuri, sai na kasa magana. Kawai nace mishi.         "Allah ya tabbatar da Alkhairi!" Daga haka na fito daga motar da sauri, zuciyata tana harbawa.                   Ba wai ina son shi bane, amma ko babu kome ya dace na amshi tayin shi, tunda wanda nake dawainiyyar so yace baya yina.      Sai da yaga shiga na cikin gidan, sannan ya juya kan motar shi yayi tafiyar shi,   ina shiga cikin na sami Aunty Aina'uh, na zauna muka tab'a hira sannan na wuce daki har na shiga sai naga bai dace naki gaya mata Saif ne ya dawo dani ba.          Dawowa nayi ko zama banyi ba na gaya mata, zuba min ido tayi kafin tace min. "Amma ya zanyi da wasilah?"   Dariya ta bani sannan nace mata. "Ai hakuri zaki bata tunda bana son D'anta." Bata zata da gaske nake ba, sai da aka kwana biyu, lokacin wakilan shi sun isa gurin Baabi, ya amshi tayin su, amma ya basu hakuri tare da ce musu, zai kirani yaji ta bakina.              Duk yadda muka yi zai musu magana, dan haka suka tafi tare da Alkhairi, bayan tafiyar su ya kirani, mun jima muna magana, bani da zab'i haka na nuna mishi ina son Saif. Shima kuma Baabi yasan na amshi tayin Saif ne kawai, amma bana son shi. Dan haka bayan sati biyu Baabi ya kira Sarkin Ahmad ya gaya mishi zasu iya turo duk wani abinda ya dace.        Haka yayi musu dad'i, tun daga ranar muka shiga ƙwarya ƙwaryan soyayya, wanda ya shiga jan hankali na, da kuma nutsuwa ta, Saif yana da kirki. Yana da mutunci sosai.             ....... "Kaga abinda nake ta gaya maka, kaje ka sami yarinyar nan kuyi magana, gashi nan ta tura wani gidan su"      A razane ya d'ago kan shi, daga cin abincin da ya mik'e, tsaye bai kuma wani abu ba, ya bar gidan.                      A hankali ya shiga duba wayar shi, hotunar bikina da Ikrama ya shiga dubawa, kafin ya shiga niman inda zai samu Ikrama, sun jima suna magana kafin ya kashe kiran.                Huci yayi tare da shafa fuskar shi.           ....... Daura. Yana kwance a dogon kujera, wayar shi tana gefe yana sauraron tafsirin din malam Jafar Muhmood Adam, wanda yayi na hadisin Ummu Zarr.       Zama Jannart tayi tare da kallon shi, tace. "Hamma!" Bude ido daya yayi, tare da d'aga mata gira. "Ka sami labarin wata me zuwa za a yi baikon  Addah?"            Bude idanu yayi tar akan ta yace. "Toh Noorie me zanyi? Ina ruwana da Addarku, ko gatari ce bata gaba na."     Zare ido tayi tare da rike baki tace. "Hamma!" "Noorie!" Yakira sunanta a gajiye, sannan yace. "Don Allah jeki d'akina zaki ga ipad din da kika ce kina so"      Rau-rau tayi da idanunta, sannan tace. "Ni wallahi bana son Husnah da wancar buzuwar, ni nafi sonka da Addah."       "Wayyo Allah na!" Ya fada a hankali. "Kina son ipad din ko na bawa Raihah."       Da sauri ta mike tare da nufar dakin, tana murna ganin sabuwa ce dall, ta fito da gudu, tana murna.                Ajiyar zuciya ya sauke,  ya cusa hannun shi dukka biyu cikin gashin kanshi, yana yatsunawa, kamar ya fasa ihu tsabar rashin sanin cikakken fahimtar abinda zai yi, shi bawai sonta yaƙe ba, kawai bai ga wani dacewar tayi wani aure a yanzu ne idan duniya da gaskiya ai bari zata yi yayi aure tukun tayi nata.(🙄🤔🤦🏽‍♀? Sonkai)        Shiga dakin shi yayi tare da kwanciya ya zuba kafar shi a kasa, sannan ya saka hannun shi kasar matashin sa, ya ciro wata yar karamar wayar kirar nokia.              Dan danne danne yayi sannan ya kira. Sai da yayi shiru na wasu lokuta kafin ya iya buɗe bakin shi yace. "Ke wacce irin mutum ce da bata da cikakken hankali, aure zaki yi? Ko sanin ya kamata baki yi ba, yaushe kika tsarewa aurenki da har zaki so wani auren?"        Kashe wayar aka yi, ya kuma kira yaji taki shiga nan haushi ya kama shi, ba tare da ya kuma wani abu ba, ya rufe wayar. ...... Abuja. Ina aiki a kicin kawai naji kiran waya ina dauka, ya fara gaya min magana. Da na fahimci cewa zai b'ata min rai shine na kashe wayar baki daya, na cigaba da aikina. Indai halin jay ne babu bukatar na damu kaina, ba yau muka saba ba. Kuna wayar na kuma yi dan nasan ya hakura ba zai kira ba. Dan haka na ajiye na cigaba da aikina. Sake kira aka yi na share, karshe ina na kuma dauka, ina sakawa a kunne na, ya shiga masifa. "Kaga Ni bana son shirme da yaranta, dan na fahimci baka san ciwon kan ka ba, don Allah karka kuma kira na, mayye mara zuciya, kaje kayi rayuwar ka mana, Asood kafita harkokina." Daga haka na katse kiran Asood, na cigaba da abinda nake. Dan da farko na zata Jay ne ashe ba shi bane. Asood ne. ---- Wasa wasa, aka saka bikin Jay, yana cika yana batsewa aka fara kai kayayyakin auren daya gidan Galadima, daya kuma aka wuce dashi Damagaram, cikin wata uku da aka saka bikin anata hidimar gidana sabon Asibiti dan baban shi na Canada ya kawo mishi takardun shaida karatun shi. Dan haka aka shirya mishi tafiya Maiduguri, sun zo su amma shi bai samu damar zuwa ba, sabida ana tunanin kar a kuma dauke shi. ... Tunda ya shigo garin, aka karb'e shi cikin gata da farin ciki, ga uban dangin Maman shi da kuma gidan sarautan da aka shiga mishi hidima da biki. Anan Ministan harkokin lafiya Dr Bulama yake tambayar shi matsayin Karatun shi. "Yallabai! Na karanci ɓangaren mata da yara ne," gyada kai yayi sannan yace. "Zaka yi aiki da mune ko zaka gina naka na kanka?" Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi.. Yana faɗin. "Nafi son nayi aikina da kaina, amma naji ance sai naje Nsukka nayi jarabawar gwaji." "A'a mun dawo da ita gwagwalada, zaka iya zama a cikin gidana na can kayi jarabawar a can, idan ka gama sai ka dawo gida. Sannan kuma asibitin zan so kayi mana anan, amma nasan mahaifinka yana kewarka kuma zai bukaci kayi a daura, dan haka ga zamu bada gudummawar mu." Nan ya dauko takardan cheq ya rubuta mishi kudi masu yawa, yayi godiya sosai.. lokacin da ya shiga sauran gidajen, dangin Maman shi haka suka yita bashi gudunmawar su na Asibitin da za a gina mishi karshe ya nuna musu kudin yayi mishi yawa. Nan suka shiga ba shi labarin, rayuwar Mahaifiyarshi, tun daga kakar shi da tafita da Jannart, har zuwa irin sadaukarwa da mahaifiyar shi tayi, sannan suka zuba mishi ido. Yana kallon su bai ce kome ba, a hankali ya sunkuyar da kan shi, kasa, sannan yace. "Kenan masarautan zagaye take da ruffenfen sirrin da suka kasa cimma matsaya akan shi?" "Masarautan cike take da tsinuwar mutane da aljanun." Inji Umma Kaltum, kanwar Mahaifiyar Jannart, Sun jima suna tattaunawa kafin yayi mata sallama, ya nufi gidan kakan shi, ya same shi. Shida wasu malamai, juyawa yayi zai fita wani Dattijon a cikin malaman, ya kira shi. Shiga yayi ya zauna tare da sunkuyar da kan shi Sarki Kazeem yace musu. "Shine Jikana na fari, dan gurin Jannart Hassanah, bai jima da dawowa kasar ba." Gyada kai malaman suka yi sannan suka zuba mishi ido kafin suka ce ya tafi, yana fita babban cikin malaman yace musu. "Wannan yaron yazo rusa tarihi ne! Bayan shi kan shi tarihin ne, karfin hali da juriya duk yana da ita, kafiya da naci ya dauke kome. Sai dai kuma ban san wani irin yanayi zai kasance ba, daga ranar da taurarin su ya hadu guri guda. Domin duk matan shi babu wacce zata iya daukar nauyin kasadar da take cikin rayuwar shi. Idan kuma aka samu toh tabbas tarihi zai iya mai maita kan shi, domin masu fushi da fushin wani suna fusace akan shi, sannan wata duniyar tana niman shi domin dai-dai mata alkaryanta, kada ku sake yin wasa da rayuwar shi, koda kuwa yanayin tafiya ce ta kama shi, yayi ta Addu'o'i. Domin akwai matsala ba akan shi zata faru ba kan duk wacce tsautsayin... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: *Ba domin tsawo a kanga wata ba* "Duk wacce tsautsayin ƙaddara ya shiga tsakanin su da shi, dole itace zata maye gurbin da aka rasa amma muna namu Allah yana nashi.'"        Cikin tashin hankali, Sarki Kazeem ya zuba musu ido, had'iye yawu yayi sannan yace. "Babu yadda za a dakatar da al'amarin?"        Mik'ewa babban yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali zuwa bakin kofar fita yace. "Idan guguwa ta taso ka tab'a ganin an dakatar da ita? Idan ruwa zata yi ambaliya ka tab'a ganin an sanya mata shinge, toh kamar yadda mutuwa take zuwa babu sanarwa haka kaddarar su ta haɗa lokaci guda.         Dan haka Allah shi yafi mu sanin abin da dace."      "Sheikh Muhammad, a yanzun haka shirin auren shi ake, mun zab'a mishi mata, ya amshe su amma daya daga cikin su yaki amsar tayinta ." Inji Kazeem.    Girgiza kai Sheikh Muhammad yayi sannan yace. "Karku manta, tunda ya amshi tayin sauran haka yana nufin kaddarar su da ita wacce yaki amsar d'aya ce. Haka yana nufin tarihin masarautar su zata kuma mai-maita kanta kenan" Daga haka suka ficce, daga gidan. Shigowa Jay yayi jikin shi a mace dan ya hadu da su Sheikh Muhammad suka mishi wani irin kallo. Sannan zasu wucce Sheikh Muhammad yace mishi.             "Tauraron ka yafi nata karfi! Ka nisanceta domin kusantarta dai dai yake da tab'a karfin haskenta, daga ranar da kayi gangancin tarayya da ita. Toh daga sannan kome zai iya faruwa da ita. Ka rabu da ita tayi rayuwarta domin ta hanyar zata kuɓuta daga kaddararku"         "Kai waye da zaka dakatar da ni abin da ban damu dashi ba? Wacece kake tunanin ta isa nayi rayuwa da ita?  Idan ina son Mata dubu zan iya mallakawa kai na, amma mace bata gabana zaka iya tafiyar ka"           Yayi gaba yana jin babu dadi, murmushi Sheikh yayi sannan yace. "Tabbas rayuwar wannan Yaro cike take da Izzah, shi yasa yake jin kome akan shi."     Daga haka suka bar masarautan baki daya.     ---- Cikin sauri na fito daga cikin gurin wanke kai, da nazo yi. Ina kallon wayar dake hannuna naga kiran Saif ne, murmushi nayi zan dauka naji an rike hannuna.                  D'ago kaina nayi naga wata tsohuwa, tana rike da sanda. Ajiyar zuciya na sauke tare da zuba mata ido tsigar jikina yana mik'ewa.            Murmushi nayi mata a sanyayye na zare hannuna daga nata, na bude jakata zan dauki kudi ina kawai naji wani abu zummm, naji jikina yayi min wani mugun sanyi. Kallon matar nayi kamar zanyi kuka nace mata. "Me kike bukata?" Dariya tayi idanuna yana fidda wani irin yanayi shi ba kore ba, shi ba shuɗi ba, shi ba rawaya ba. Kafin ya koma fari.         "Lallai zaki mutu! Domin kuwa kina dab da zama fanko. Ki biyo ni domin kuwa ni ce bazan tab'a."            "Fatimah!" Naji muryan Saif wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da juyawa gare shi, ya ganin idanuna cike da kwalla ya kara leka inda na juya babu kowa, nima juyawa nayi babu matar babu dalilinta. "Zo mu tafi!" Ya ce min.      A hankali na isa gaban motar ya bude min na shiga tare da zama sannan ya rufe, ya dawo inda yake ya zauna sannan yaja mu. Kallona yayi sannan yace min. "Ina ji a jikina kamar bazan same ki ba"              "Hmmm!" Nace mishi, "Zahrah!" Ya kira suna na a sanyayye. "Ina sonki" juya kaina nayi sannan nace mishi. " bai zama lallai na maida maka abin da ka bani. Amma ina mutunta duk wani alamarin ka."      "Aanih ko dole nayi Miki ne?"       Juya kaina nayi tare da kallon farce na, ina tuna lokacin da Jay ya sace ni, har ya mai dani dakin shi, na tab'a farkawa naga yana kallon zanen fulawar hannuna, tare shafawa. Koda na farka b'ata rai yayi sannan tare da barin d'akin.     Yau ma sai da na saka aka min zanen lallen dake ja ne, kai hannun Sa'id yayi tare da shafa hannun, cikin jin haushi na harare shi. Sannan nayi fiki-fiki zan mishi masifa ya zuba min ido, karshe tamke fuska nayi cikin b'acin rai, har muka isa gida.             Hannuna na kai domin bude kofar motar yace min. "Ai ko babu kome zaki min sallama ko Zahrah?"        "Sai anjima!"nace mishi a dakile, ya fahimci naji haushin abinda yayi min ne yasani jin ba dad'i. "Toh kiyi hakuri bazan kuma." Ya faɗa min a sanyayye, zuba mishi ido nayi naga ya wani narke min.    Sai ya bani tausayi, na sake murmushi nace mishi. "Wannan satin zan shiga sokoto" "Na sani ai shi yasa nake ta tambayarki."          "Toh ba damuwa zan zo can."       Daga hakan na juya cikin gida, shi kuma yayi tafiyar shi.     .....-- Kwanan Jay biyar a Maiduguri, har da sarautar Yariman mai Borno aka bashi, sannan ya dawo inda ya narkewa Abban shi akan gina mishi asibiti, da farko Jaamal yaki amma ganin sam Jay bai san meye ake kira da mulki ba, yasa Baba Sarki yace a barshi Nan da wani lokaci. ...... Zaune yake suna cin abinci, kamar wanda aka zage shi sai cika yake yana batsewa,  Kallon Juna Sarah da Jaamal suka yi kowa ya d'aga kafada, sanan suka ci gaba da cin abincin su rai a sake.   Ture abincin yayi alamun ya koshi kuma ko rabi bai yi ba, ya zubawa Sarah Ido cikin nasara yace. "Mama! Dama wancan Yarinyar aure zata yi?!" Kallon mamaki suke mishi tare da tambayar. "Wacce Y'a kenan?"     Shiru yayi abin shi bai kuma magana ba, har ya mike, Jaamal yace mishi. "Ya zaka mai da kowa sa'anka!? Wannan rashin girmamawa ba daga cikin ahalin gidan mu bane ko na mahaifiyarka." .mik'ewa Jaamal yayi yazo gaban shi ya tsaya suna fuskar ta juna. "Jannart har ta koma ga mahaliccin ta, bata tab'a banzarta da Aminiyarta ba, duk wani abu da zata yi cikin mutunta Sarah. Jannart ta hakura da rayuwarta sabida Sarah kai har ka isa tayi maka magana kayi banza da Ita?    Zan dauki kome amma ban da...."         "Nagode sosai Kawu, ka nuna mishi bani ce na haife shi ba, ka nuna min cewa ba."   D'aga mata hannu yayi sannan ya juya ya bar falon, a sanyayye ya bar falon har zai shige shashin sa, ya juya tare da cewa Jay. "Idan har zaman ka zai janyo min fitina da Iyalina na roke ka da ka fita ka koma inda ka fito.                  Ban haifi d'an da zai tozarta ni a gaban jama'a ba, kana da damar kayi kome, amma ban da wulakanta min mata na ba."          Yana gama fadar haka ya wuce dakin shi, ya zauna a bakin gado tare da zubawa hoton Jannart ido, yana jin babu dadi a ran shi.      ... Shiru Sarah tayi tana me share kwalla, sannan ta kalli yaron, tare da mika mishi hannu, dawowa yayi ya zauna a kujeran kusa da ita, yace. "Kiyi hakuri Mama!" "Babu komai!" Ta faɗa a sanyayye, dan ta lura miskilancin da Jay yake halayyar Jannart ce, rashin magana da kafiya da naci halin Jaamal ne. "Wacce yarinya ce ake maganar ta?". Tab'e baki yayi sannan yace. "Wancan yarinyar ta sokoto!"      "Fatimah ce yarinyar? Jay ka cika renin hankali, Fatimah ba yarinya bace, ba kuma sa'arka bace, Sa'ar Aliyah ce, don ka ganta kamar lomar tuwo."                    Shafa kan shi yayi kamar bai ji haushin ce mishi ba yarinya bace. "Mamah yarinya ce ai." "Hmm! Yayi maka kyau! Tunda ka haife ta ba?" "Me yasa bazaki bata shawara ta hakura da auren ba." Yana fadar haka ya mike yana dariya, sakamakon kallon da take mishi.            "Toh bamu bata shawara ba sai ka dauki mataki ko?!" Ta gaya mishi a fusace, dan ya fara bata haushi. "Afuwa! Amma ki duba dakyau, ta sanadin auren maza ke mutuwa me zai hana ta hakura, koda yake tsugune bata kare ba, tunda." ."amma me yasa da aka ce ka aureta kace baka sonta?" Ta tambaye shi,     "Nifa bana da ra'ayin bazawara ce! Kawai nafi son wacce bata kai ashirin zuwa da daya, sunyi hankali, amma ita fa? Tab." Baki sake Sarah ke kallon shi tana gyada kan ta, kafin tace mishi. "Allah ya kawo maka sauki cikin abubuwan ka". Dariya yayi, tare da barin shashinta, ya nufi hanyar da zata kai shi cikin gidan, haduwa suka yi da Husnah. Ta tsura mishi ido, babu kyaftawa tace. "Yarima Jalal, Barka da maraici."    Watsar da ita tayi tare da tsuke fuska, kamar bada shi take ba. Shan gaban shi tayi tare da tsare hanyar da zai kai shi shi cikin gidan.        "Yarima Jay! Meye laifina, ban fi guzuma da buzuwar da aka had'a ku b..." Take mata kafa yayi tasaka kara me shegen karfi wanda yasaka dogaran da suke kofar farko lekowa ganin shugaban su yasa su juyawa da sauri,suna fadin. "Hutawarka lafiya magajin garin daura!" Murmushin ban haushi yayi wanda ya kuma bashi damar mutsuke kafar Husnah tana kuka.              "Buzuwar bata da matsala domin zata iya karban kanta." D'ago fuskarta yayi wanda ya jike da kwalla, ya cigaba da cewa. "Koda wasa kika tab'a Lu'lu'ah sai na baki mamaki."     Daga haka yayi wucewar shi cikin gida, inda ya samu Kakar shi ta dama mishi fura tare da gasasun zabbi.     Zama yayi ya sha sosai ya kuma ci zabbin.     --- Shiga shashin sa tayi taga Balkisu tana fitowa rai a b'ace.       "Aikin banza kiba a kunne! Mun san kome, matar cushe." Inji Balkisu.    Dariya Sarah tayi sannan tace. "Banza ba shi kai zomo kasuwa. Ko baki fada min ba, nasan kwanan zancen Balkisu."            "Oho dai koma me zaki ce sai dai ki fada. Kowa ya ga shamuwa da kwushinta ya ganta haka zaki ganin ki bar ni. Sannan shi Yarima da kike takama dashi ai ba d'anki bane? Dan haka ki bar ganin karenki ya kama kura, da sannu zan mai dake abin kwatance."         "Asha Ramanme kada mai kibba. Allah daya gari banban, ranki shi dad'e, zan shige dan ina da abinyi."                Daga haka tayi wucewarta, bata kuma tankawa ba.           --- "Ina lauya ne? Ban gane shi ba kwana biyu?"  Inji Baba Sarki. Gyara zama Jay yayi sannan ya shiga matsawa kakan shi kafar shi da take ciwo. "Wai yana da aiyuka ne."          Daga haka ya cigaba da abin da yaƙe, har zuwa lokacin da Kakan yace Mishi ya isa. .... "Jalal! Har yanzun kana kan bakanka baka son Faɗimah?"    Lashe bakin shi yayi sannan ya zubawa kasa ido. "Kaka Ni bana sonta ne? Kuma bazawara ce"           Shiru falon yayi sakamakon bayanin da Jay yayi, "Allah ya sa haka shine mafi alkhairi."          ..... Ta same shi tsaye ya zubawa hoton Jannart. "Kawu!" Ta kira sunan shi a hankali bayan ta rungume shi ta baya.        Ajiyar zuciya ya sauke, tare da cewa. "Na rasa inda Jalal ya dauko rashin hankali, Jannart bata da matsala, amma shi ga baki daya ba tarbiyyar mu yake nuna mana ba.        Yayi min wannan rashin girmamawan a gaban mutane, naji ba dad'i, mu iyaye ne. Kome lalacewar muna bukatar mutumtaka, balle kuma yadda muka kasance ahalin babban gida."         "Karka ga laifin shi banbancin al'adun da dabi'un mu ya sha banban da na shi, halayyar shi ba daya bane da wanda ya fito cikin babban gida. Banda zanen kaddarar mu ta shafe shi ai da a cikin mu zai taso da irin namu AL'ADUN, toh Matsalar da aka samu ya taso da aladun wasu ne, Insha Allah bazai kuma ba."        "Toh me yasa baya magana?" Ya tambaye ta a sanyayye. "Amma inji ka ko? Domin kuwa ban ga wani rashin maganar shi, kai ma haka kake da wannan wulakancin, sannan kuma Janny. Itama ai ba tayar baya bace gurin miskilancin da zurfin ciki.      Kai kuma naci da kafiya, shi yasa banyi mamaki ba da aka ce min ya sace Fatimah, domin kuwa tayi mishi laifi kuma ya rama."      Juyawa yayi yana kallon fuskarta, tare da sake murmushi yana cewa. "Wacce yarinya ce yake maganar ta?!" ...... Dariya tayi sannan ta gaya mishi ai da Fatimah yaƙe. Zaro ido tayi waje, yana faɗin. "Yau naga abin mamaki! Ba cewa yayi baya sonta ba??"        Dariya tayi tana fadin. "Kamar kumbo kamar kure!"      ......... Yana fitowa daga cikin gidan, ya dauki wayar shi ya latsa can ya manna a kunnen shi..... Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu                10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Kowa ya rena tsayuwar.... Wata ya hau ya gyara* "Zan ga yadda za ayi da.." Katse shi tayi cikin jin haushi. "Ba zaka fita hanyata ba? Ba zaka dai min shishigi kwala kai a faranti ba" "Ke da wa kike?".kashe wayar tayi abinta. Shafa fuskar shi yayi cikin jin dadi, ko babu kome yasa ta tayi magana, da muryanta irinta yaran nan. Tsaki yayi tare da fada a ran shi. "Zai ga uban da zai aura mata wancan mutumin."       Yaja tsaki tare da barin guri .     --- Tunda na shirya kayana, nake kallon su jikina yana kara sanyi, sabida faduwar gaban da nake ji. Haka na fito ina kallon Aunty Aina'uh, na kakaro murmushin dole.                  "Yau kam zaki koma gida, sai murna kike kamar kin zauna akan ƙasa!" Inji Aina'uh, Tab'e baki nayi tare da fita waje, ina faɗin. "Baki kuma gani Nana gidan ki sai nazo da mijina."      Zaro ido tayi waje, na d'aga mata gira, a hankali tayi min fatan Alkhairi, sannan na shiga mota, tunda muka isa Airport naga kamar ana bina, ban damu ba, kawai na tsinci kaina da turawa Saif sakon karta Kwana.         _Bam san waye ba! Amma yana bina, kuma ban yarda da shi ba_     Bayan kamar minti biyar, sai ga kiran shi. Sai ga kiran shi, ya shigo min tare da cewa. "Kamar ya baki san shi ba? Zai biki, ki gayawa yan sandan da suke gurin zasu taimaka miki da wani abu."                    Ban ce mishi kome ba, dan koda na juya ban ga mutumin ba, haka muka taso ina duba shi ban gan shi ba, har muka iso sokoto, kafin tashi na hango shi tsaye yana kallona, tsoro ne ya kuma kamani, garin na turawa Saif sako, ashe wai Jay na turawa.          _Don Allah kayi wani abu kaji sace ni zasu yi gashi nan yana shirin tawowa inda nake don Allah kayi wani abu_           Fita mutumin. Yayi nima na fita, koda na iso inda za a zo dauka na, kawai naji an watsa min abu a jikina, ina dubawa naga madara, dan haka na juya da sauri na nufi ban daki domin na goge jikina, ina shiga kaina a sunkuye, kamar ance na d'ago kawai naji an toshe min bakina da hancina, shaƙar hodar bilis nayi ban  kuma sanin abin da ya faru ba.        Sauke numfashi Asood yayi tare da sanya min nikkaf ya fito dani a hankali har inda suka ajiye motar su.              ---- Yana aiki da laptop din shi ne ya ga sakona,kamar bazai bude ba kawai ya buɗe. Sharewa yayi ya cigaba da abin da yake can yaji zuciyar shi tana girgiza, gwada kiran layin yayi. Ta katse, ya kuma kira ta katse.        Saka smart watch din da yake hade da wayar hannnta yayi ya shiga ƙoƙarin gano ainiyin inda take, bai samu nasarar gano kome ba, amma wayar tana airport.     Mik'ewa yayi a hankali ya shirya cikin kananun kaya, bakakke, sannan ya dauki duk wani abin da yake bukata, yana fitowa ya kira Najim. "Duk abin da kake mu hadu yanzun nan zaka kai ni tashar jirgin sama"    Fitowan yayi har falo ya sami Mamah bayan sun gaisa da Mamah yace mata. "Bari na dan fita bazan jima ba Insha Allah."              "Ubangiji ya tsare, ya kare ka da kariyar shi. Allah ya dawo da kai lafiya!" "Amin Ya Allah! Nagode sosai Mamah na!" Daga haka ya fita. Ya sami Najim yana jiran shin. Koda ya shiga yayi ƙoƙarin tambayar shi inda za shi amma yayi banza da shi.         Tun da suka fita yake tsaki yana ce Mishi ya tsaya yayi musaya shi ya dawo gurin zaman shi Najim yaki tare da cewa. "Wa? Ni zaka kashe wallahi ban isa ba"    Dan haka ya kara gudu sosai, kamar zasu tashi sama, Allah ne ya kai su airport yana zuwa dakyar aka sami jirgin da zai isa sokoto, sabida sun  gama diban fasinja.         Ji yaƙe kamar ya riga jirgin isa Sokoto, koda suka isa abin da ya fara shine kiran layinta da yake cikin airport din, haka ya isa ya samu suna, ana niman ta sabida kayanta da aka gani. Nan ya gaya musu abin ta tura mishi.   Nan aka nimo yan sandan, tare da danginta, Baabi ne ya zo, bayan an mishi tambayoyi ya tabbatar da sunyi magana da ita.      Kallon Jay yayi cikin nutsuwa yace mishi. "Kai kace ta tura maka sako?!"  Nuna mishi wayar yayi sannan ya ce. "Ban san a akayi ba amma Tabbas ta turo min sakon, kuma wayar har yanzun a bude take."          Nan aka kuma gwada kiran wayar tana karar, dan haka aka shiga tambayar mutane, wani ne yace yaga wucewar ta ban daki daga nan bai ga fitar ta ba, sai wani mutum rungume da wata mata me sanye da nikkaf.               Shiru Jay yayi da a rikice ya shige ban dakin, wayarta ya shiga kira. Can yaji "ziiiimmm" Yana dubawa yaga wayar ce a kasa, da sauri ya ɗauka, tare da duba wayar akwai ki. Goge fuskar wayar yayi bayan ya fito, ya tsaya yana gwada budewa.           Duk taki buɗewa, dole ya haɗa da agogon hannun shi ya shiga niman yadda take cire key din wayar.              Yana sakawa kuwa, wayar ta buɗe. A hankali ya shiga bin sakon wayar har idanun shi ya sauka akan sakon da Ikrama ya tura mata. Da cewa. _Yadda Mahaifinki ya hanani aurenki haka nima sai na lalata miki roman ki_ Sai sakon Asood da ya tura mata, _Kamar yadda kika ki amincewa da ni! Haka kina ji kina gani zan,,,, karasa abinda wancan jahilin yayi miki wato Jay_        Kallon sakon yayi lokacin kusan daya suka turo mata, fitowa yayi ya sami Baabi ya ja shi gefe suka yi magana, sannan Jay na zuwa ya sallami yan sandan, da wani abu aka kashe maganar.     Sannan ya dauki kayanta, suka nufi gida da Baabi, ya kalli Baabi kadan sannan yace mishi. "Baabih, kasan me yasa nace kar yan sanda su shiga Maganar?!"    Girgiza kai yayi yana jiran ta cewar Jay. "Sabida darajarta! Sabida wnada zata aura, bai dace ace sunan ta yana b'aci ba, sabida faduwar kimarta. Idan aka bar abun a rufe babu wanda zai tab'a sani, sannan Insha Allah nan da awa goma zan dawo maka da ita, kaga maganar aure ba abin wasa bane.                Dan haka Insha Allah zan dawo da ita!"   ..... Har cikin gidan ya ajiye baabi, sannan ya cewa driven yazo ya raka shi, suna fita. Duk wani inda ake harkan banza sai da Jay yayi, kan shi ya kulle. .a karon farko da yaji yana son Hikmi ya taya shi aiki. Ya kira shi ya gaya mishi.        Sannan ya tura mishi sakon Number Asood da Ikrama, bayan wani lokaci ya turo mishi inda a suke tare da Asood a guri guda, har da tasiwerar gurin.             Kamar mahaukaci haka ya finciki motar.         --- Lokacin da aka kaini inda suke, wurgani suka yi, sannan fita.           Ruwa suka, watsa min me shegen sanyi, sannan  Ikrama yazo ya tsaya a kaina, tsare da zuba min ido.     Nan ya saka hannun shi, ya gaya min rigar jikina, dake har zuwa lokacin ban farka dai dai ba.     Haka suka yi ta, tozartani ba tare da na san abin da ke faruwa ba.                Har kusan karfe bakwai na dare, ina yashe a kasa, kafin Asood ya taso ya fara kokarin tsinka bra din jikina, lokacin na bude idanuna da suka min nauyi dakyar na had'iye yawun baki na nace mishi. "Don Allah karka min abin da, zai wulakanta ni!"                Haka nayi ta rokon su, ba iya shi ba hatta sauran abokan shi, dariya suke min.        --- Jay ya sami shigowa unguwar sai dai babu yadda zai yi ya shiga dan kofar gidan yan sanda ke tsaron shi, dan haka ya kira Baabi suka yi magana tare da niman ya bashi Number Habib, can kuwa aka turo mishi ya kira shi suka yi magana.     Can ya kashe wayar, bayan kaman minti sha biyar, suka iso tare da Habib, suka samu shiga gidan, kai tsaye ya shiga bin inda Asood yake, sai da suka yi tafiya me nisa sannan suka shiga gidan, kallon Habib yayi sannan yace. "Bana son a kama su! Kawai ka koma gefe kaga yadda aka fara dole na gyara musu zama."     Gyada kai Habib yayi dan ya sha kirb'a a habbar shi.      Wani katako ya cire, a jikin wata teburi, ya bi bayan Ikrama ya zabga mishi a gefen fuskar shi, haka ya fadi tim, ganin shi a kasa, yasa sauran suka fara niman hanyar gudu sabida hannun Jay rike yake da katako, ba ga kuma yan sanda a bakin kofar fita, ai kuwa dole suka koma, lokacin yana dukar Asood. Matsalar su shine duk sun bugu ne da giya, haka yayi musu likis, idanun shi jajjur, sannan ya cire rigar jikin shi, ya mika min. "Saka bamu da lokacin da zaki yi kuka, shi yasa ake cewa kuna saka Hijab gashi nan babu wani abin da zaki kare jikin ki. Da shi aikin banza kawai.     Taya maza ba zasu dinga kawo miki Hari ba, dube ki fa. Sabida  Allah? Ko kishin kan ki baki yi, balle kiyi kishin mutumin da yake shirin aurenki,    Ban tab'a haduwa da mara amana irinki ba, dube ki fa."      Yadda yake sauke min Bala'i sake baki nayi ina kallon shi.. "Jay Kana sona? Jay kishina kake fa?" Wani irin kallo ya watsa min kafin ya juya zuwa dakunan da suke cikin gidan, ya samu wata daki ya ciro wata sabuwar rigar shadda yazo ya mika min na saka.     Sannan ya dauki gyale na ya mika min na yafa, a sannu ya riko hannuna muka fara tafiya, ina kallon fuskar shi. Da take tamke.        "Jayyy!" Na faɗa da karfi sakamakon, sukar wukar da Asood ya kai mishi, juyawa yayi ya kalle ni a sanyayye, kafin yace min. "Rufe idanunki!"   Jikina na rawa, idanuna yana tsiyayyar da hawaye, ya juya tare da sake ni, ya rike hannun Asood. Juya hannun yayi idanun shi jajjur.          Sai da ya karya hannun sannan yace mishi. "Kai Abokina ne? Ita kuma Fatimah mata tace! Ko ya wani yazo keta mata haddi sai inda karfina ya kare. Don Allah mu dakatar da wannan abin daga nan, bana son ya tab'a mutuncin gidajen mu."     Daga haka ya sake hannun Asood, sannan ya shafa cikin shi yaji ba wani ciwo bane dan yanka ce a samar fatar shi.            Sai dai jinin da yake zuba, jan hannuna yayi muna bar gidan, Habib yana kallon mu, murmushi yayi sannan yace mishi. "Ban da wani abu ai kun dace da juna" tsuke fuska Jay yayi kamar wanda aka zagi babar shi.            Koda muka iso gidan, yana son ya fito, amma jiri ya hana shi fitowa, zama nayi ina goge fuskana, ya lumshe idanun shi. Tare da d'aga kan shi sama.      "Jay!" Bude idanu yayi tare da zubawa akaina.          "Kije ki cigaba da abin da, ya dace miki na shigar banza, fitar min a motar." Ya fada min,   ."bazan iya barin ka cikin wannan yanayin ba, don Allah kazo muje cikin gida, a kira likita ya duba ka."       "Fita nace." Ya fada tare da fisge dan kwalinta, ya nuna min hanyar fita, jikina a mace na fita, sannan ya cewa driven. " Zo mu tafi!"        Dan kwalin ya daure cikin shi da ita, sabida jinin da yake zuba sosai. Suka fita daga gidan.                  Ina tsaye hawaye na zuba min, daga cikin idanuna ina ji ina gani suka bar gidan, a hankali na juya zuwa cikin gida. Ina kuka kamar karamar yarinya.   Falon Baabi na shige yana tsaye, da sauri na isa gurin shi na fada jikin shi ina kuka, tare da nuna mishi hanyar. ."ina yake?" Dakyar na iya tsayar da kukan na shiga bashi labarin yadda muka yi, koda Baabi ya kira shi wayar shi bata shiga, dan haka ya amshi key mota ya bi bayan shi, koda ya isa airport din sun tashi, yaji babu dad'i.                   Ina zaune nayi tagumi hannu bibbiyu, Baabi yana shigowa na mike tsaye ina leka bayan shi nace. "Yaki zuwa ko?"      Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace min. "Kiyi hakuri!" "Baabi! Toh ai zuciyata taki ta hakura, Baabi wallahi ina son shi sosai. Ka fahimci abinda nake nufi....,Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu...      10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Kowa yaci zomo.... Yaci gudu*      "Zuciya ta bata san hakuri ba, zuciya ta, bata san meye babu ba. Don Allah Baabi ka bani abin da nake so" na fada cikin kuka.     Zuba min ido yayi cikin damuwa, yana kara girmama abinda nake cewa. "Kiyi hakuri da Jay ba samun shi zaki yi ba, sabida bana son zama karamin mutum, na rigada na gama kome.   .... Kawai biyayya zaki min, shine abin da nake bukatar ki dashi." Sunkuyar da kaina nayi ina wani irin kuka, tabbas tawa kaddarar kenan soyayyan Jay, dan haka na mike tare da nufar cikin gidan, babu wanda ya san nazo amma sheshrkar kika na ya sanar musu da zuwa na.          Duk yadda suka so sanin abinda ya ke faruwa ban iya magana ba, karshe gurin Baabi suka je ya gaya musu abinda ya faru, amma bai gaya musu soyayyan Jay ce ta sani kuka ba.   *** Tun kafin ya isa airport,. yasa driven gidan su Aanih ya kai shi i da ake sayar da kaya, ya sayo mishi wasu riga da wando, sannan ya sake daure bakin ciwon da wancan kayan tare da dan kwalin Aanih.        Dakyar yake takawa, bayan ya shiga cikin jirgin ne, ya turawa Najim sako! _Gani na taso!_ Daga haka ya kashe wayar shi, koda jirgin ya isa Katsina, daurewa yake, har ya fito inda Najim ke jiran shi.         Mikawa Najim hannu yake, domin ya fara ganin shi yana mai nisa, da sassarfa ya isa gurin shi, tare da rungume shi.       Zuɓewa yayi a jikin Najim yana fadin. "Yankar bata shiga ba, amma jini na ya zuba sosai."    D'ago shi Najim yayi cikin damuwa yace. "Waye yayi maka wannan aikin?" Yana tambayar shi tare da saka shi a motar. Da sauri ya zagayo mazaunin shi, tare da jan motar da gudu.       "Yarinyar Sokoto aka sace" daga haka bai kuma magana ba, burin Najim ya sami asibiti a garin katsina, kafin su kai daura.       Cikin ikon Allah suka sami wata asibiti na kuɗi ya kai shi da sauri, kamar ba zasu amshe shi ba, suka kuma karb'e shi sabida jinin da suka ga yana zubdawa.       Sanan suka shiga dashi dakin aiki aka wanke ciwon tare da dinkewa sanan suka duba jinin shi basu ga wata damuwa da za a kara mishi ba, kawai suka mai da shi dakin hutu.           ** "Kawu har yanzun Jay bai dawo ba, kuma dare yana kara yi." Inji Sarah,        Zare madubin idanun shi yayi cikin nutsuwa sannan yace mata. "Jalal ba yaro bane! Da zan dami kaina bai dawo ba, dan haka ki zuba mishi ido dole zai dawo ai."       Gyada kai tayi sannan tace. "Amanar da Allah ya bamu zamu sauke bawai yana ji ko baya ji ba, dan haka ni ka kira min shi, dan wallahi zan iya kowa barci."     Kallon ta yayi yaga yadda ta coge mishi a kofar daki, ya kuma san kad'an daga aikinta kenan. Dan haka ya shiga niman layin Jay bai samu ba, karshe Na Najim ya samu.          Bai gaya musu halin da Jay yake ciki ba, amma ya tabbatar musu, suna tare amma sai gobe zasu dawo.    .....          Da haka Sarah ta hakura, amma zuciyarta ta kwana cike da damuwa.           --- Dakin duhu ya mamaye ko ina, sannan yace. "Ka san me yasa naki raka nan? So nake a kashe min wancan yaron!"           "Ranka shi dad'e!  Yawa shi kan sa zarre ya ja dutsu," Sautin murmushin da yaji sashi fahimtar maganar da yayi tayi amfani. Gyaran  aka yi sannan aka ce mishi.     " Ba samun abinci ke da wuya, wurin da zaka je ka cishi shi ke da wuya.! Dan " shiru yayi sannan ya cigaba da cewa. Ka fake shi dare da rana! Ka sanya idanun ka akan motsin shi. Wanda ya ci da kansa, shi ne sarkin noma. Zaka iya tafiya."        *** WASHI GARI. Da karfe goma Najim ya nemi sallama, bawai dan shi ba sai dan Jarabar Jay, dan ya ishe shi da masifa shi ayi a sallame shi ko ya bar asibitin. Koda aka sallame su, b'ata rai yayi wai kar Najim ya tambaye shi meye sanadin jin ciwon shi.    Shi kuwa Najim bai bi takan shi ba, har suka kusan isa gida. "Amma me zaka ce musu idan ka isa gida? Zaka gaya musu ka tafi sokoto gurin Yarinyar da kace baka so...." .a fusace ya juya tare da aunawa Najim kallon banza yana fadin. "Inji wani algungunmin yace naje sokoto gurin ceton rayuwarta?" Ya fada tare da zare manyan idanu shi akan shi.            "Ranka shi dad'e!  Uban doma, don Allah bar zare min ido. Da bakin ka, ka gaya min a nan motar.'" ban za yayi da Najim dan ya fahimci so yake ya takurawa rayuwar shi.       *** Sun isa gida lafiya, amma Jay ya boye musu, halin da yake ciki, dan haka babu wanda ya sani bayan Najim.          *** Masarautar Zazzau. "Yarinyar nan da kake so bafa matar ka bace! Asalima matar mutuwa ce, duk namijin da ya aureta mutuwa yake.     Gashi har ankai Sadakinka,! Ka hakura da yarinyar ka nemi wata."         Sunkuyar da kan shi yayi sannan ya shafa kan kafin yace. "Fulani yarinyar ta warke, kawai dai an camfeta ne." D'aga mishi hannu tayi, sannan tace. "Ba zan maka tilas ka rabu da ita ba, amma duk wanda ya ki ji!" Nuna mishi hanya tayi akan zai iya tafiya,          Sam bai ji dad'in yadda taki fahimtar zuciyarshi ba, kawai ya mike tare da cewa. "Allah ya huci zuciyar ki!"                  "Hmm!" Tace mishi, tare da ɗaukar tufa, ta gutsira. Tausayin shi take ji duk cikin yaranta shi ne yaron da take sanya shi yayi ya kuma yi, ya bari kuma ya bari, dan haka bata jin zata bar shi ya auro mutuwar shi. Domin bata shiryar daukar wannan kasadar ba.             *** Bayan wata uku.. Aka fara shirin bikin Jay, wanda tsiran shi da nawa sati biyu.      Tura mishi sako nayi ta manhajar Whatsp. _Barka dai Saraki!_        Budewa yayi sannan ya turo min da cewa. *Yan mata*        _Hmm! Sunan yayi ma'ana_ *Ko??* _Kana tanka min ne?_          *Ina na isa tankawa jarumar mace irinki* _Saraki kenan_ *Fatimah kenan!*    So nake muyi magana amma kamar ya fahimci haka yaki kula ni, sai ma share ni da yake,  da na fahimci haka sai na tura mishi takardan sanarwan auren mu da Saif.           Sauka yayi daga nan nima na rufe wayar, tare da lumshe idanuna, ƙara wayar tayi naga Number shi. "Saraki!" "Karki yarda ki kira suna na, tsabar kin rena ni, shine bari ki turo min katin aurenki wato ga d'an iska mara mutunci!"       "Toh amma ai ba wani laifi bane, naka da kaki nuna min shine naga Ni bari naci girman na nuna maka nawa, shine laifi." "Zahrah karki min rashin kunya!" "Toh saraki bazan maka rashin kunya ba, tuba nake."       "Wallahi sai nayi maganin d'an iskan da zai aure ki!" "Jay bana son damuwa! Daga abun arziki sai ya koma na tsiya, Insha Allah zan yi aurena lafiya,, kai kuma ka cigaba da tsiyar halinka wawan Yaro kawai, baka da hankali gata tayi maka illa."   "Khatoon!!! Ni kike kira da wawan Yaron?!" "An gaya maka ban kaddarar so me zanyi da Kanin bayana, kana dan mitsitsi da kai, me zaka iya yi da mace irina, kaje kayi da kananun kwalayen matanka da aka dankara maka su. Sha-sha-sha kawai."     Huci yake kamar zuciyarshi zata diro, mafi girman cin fuska da aka mishi a duniya, shine nayi mishi. Dama kuma na saba, dan haka Ni ban wani damu can ba.       *** Wani irin haushi yake ji, kamar ya rufe mutane da duka, shafa ciwon shi yayi. Tare da kallon kan shi a madubin dakin shi, yana son hango ta ina Yaron yake.              Karewa kan shi kallo yayi yaga babu ta inda yayi alaka da yaro Aanih ta kira shi da yaron da rashin sanin hakkokin dan adam, shine Yaro.         Marin kan shi yayi, tare da kwafa.         *** Bikin Jay  ya zama bikin da ake mishi wani irin tanadi na musamman, kasancewa Jikar Tsohon sarki kuma mahaifin shi yake rikon kwarya, uwa uba. Kakan shi na gurin Uwa sarki ne dangin Mahaifiyar shi kusan manyan attajirai ne a garin Borno.     Haka yayi mugun tasiri a kan bikin, domin kuwa kowa murna yake da bikin kafaffen sadarwa ake shelar auren, ta ko ina na'am ake da al'amarin. ... An kai kayan auren Munih Damagaram, sannan aka kai Na Husnah, kuma dukkan su biyun babu wacce ya tab'a kira da sunan soyayya, haka ya kuma sanya kowacce tana zargin ko yafi son yar uwanta da ita.       Abinda ya shiga kawo musu kishin juna da kuma tsana na musamman. Kowacce tana jin itace. ....... Saura kwana biyu bikin muka tawo daga Sokoto tare da Ummi, da yamma likis muka shiga gidan, a gajiye nake d'aga kafana sabida tafiyar motar da muka yi.              Ummi ce a gaba, sai Hanisah da kuma Janny a kusa dani. D'aga kaina nayi muka yi ido biyu da shi.       Ya kara wata irin girma, a raina nace. "Jibgege!"     Kallon banza yayi min, sannan ya kauda kan shi, a ran shi yana aiyana yadda zai samu damar mun rashin mutunci. Ko sau daya ne.             Zama muka yi aka shiga gaisawa, tunda muka gaisa da Mama ban kuma bin takan shi ba, sako ya turo min. *Gayyar soɗi! Kin zo cin shinfaka da miya ne?!* _Haba Yaro kaine baƙon aure,.Ni wani irin aure ne ban gani ba, wani irin abu ne ban gani ba_       D'agowa yayi muna kalli juna, cizon bakin shi yayi tare da mik'ewa zai bar falon.       *Hmm!*      _Inji me Ciwon hakori_      Fuuu ya bar falon, kamar wanda na mishi zagin ƙare dangin. Kara wayata tayi na dauka. "Fito ki same ni" "Bazan fito ba" Kafin ya kuma magana na kashe wayar, haushi ne ya kuma kama shi.         Tunda aka fara shagalin bikin ban kuma ganin shi ba, amma kullum muna nan muna fada a waya, har ranar daurin auren.          Bayan an daura auren shi a Nijar aka kuma daura anan naji ba dad'i, amma na share batun shi, na shiga mutane akayi  hidima dani.              --- Da dare bayan kawo amare aka tafi liyyafa, dama munyi da Saif zai zo. Dan haka na ci uban kwalliya muka fito gurin, tunda na shigo gurin na hango shi dunkule yana hura hanci, Ni kuma na zauna kusa da Saif..muka shiga hiran kamar ba gobe wallahi na manta da batun Jay.              Dan na fahimci nice nake haukata, kawai mun yi nisa a hira sai ganin shi nayi akan mu. "Malam bata gaya maka cewa tana da aure ba?" Da sauri na d'ago kai ina kallon shi, murmushi yayi sannan ya zaro takardu daga aljuhun wandon shi ya direwa Sa'id duba ka gani. "Har da shaidar cikina a jikinta, kai duba."      Kallona Saif yayi sannan ya sake murmushi, yace. "Toh Naji amma ban ji daga bakin mahaifinta ba!" Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauke tare da murmushi nace. "Kasan lissafin yaro ba daya yake da na manyan ba! Shi yasa ya kwaso jiki ya kula min makirci. Yaro man kaza. Da an saka a rana ka narke. Tashi muje." Muka mike tare da barin shi kamar ya fasa ihu, sabida bakin ciki. Har muka bar gurin, a fusace  Saif ya juya kamar zai buge ni. "Meye alaƙar ki da shi?! Ba na rabaki da shi ba, ko bance bana son alaƙar ku da shi ba? Fatimah ina zuba miki ido ne bawai dan bana son damuwa bane kawai ina kallon ki ne na kuma ganin ki da yaron can zan baki mamaki. Na rabaki da yaron nan."     "Idan kuma baki rabuwa da ita ga?"      Inji Jay, " Tsoro ne ya kamani! Don Allah Saif muje ka rabu da shi yarinta ke dawainiyya da shi bazan kuma kula shi ba.".      " Ni kike kira da yaro? Ni kike cewa fuska? Lallai kin tsokanowa kanki abin da yafi karfin ki."     Kai hannu shi yayi zai riko ni,Saif ya janye ni da sauri, ai kuwa Jay ya kai mishi duka. Shima ya rama, kai naga tashin hankali. Domin dambe ne ya sarke a tsakanin su. Na rasa yadda zan raba su,suka ture ni.         Ana cikin haka sai ga Baba Aswad yazo wucewa yaga suna dambe tsawa ya buga musu, suka rabu.  Jay na faɗin. "Wallahi na rantse maka baka da rabo a jikinta idan kuma kana ganin  karya ne, nan da sati biyu zamu tabbatar da waye d'an halak." "Yaushe d'an kwarkwarah yasan hallaci? #Mai_Dambu... 10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Wawa ana sonka, amma ba a son haihuwar ka.* Ban san wani irin yanayi muka shiga daga ni har Jay da Baba Aswad ba, sai dai lokaci guda kome ya tsayawa Jay cak. Kurawa Saif ido yayi, cikin kaduwa da tashin hankali, ya taka har gaban Saif. "Kace me? Maimaita min naji?" "An gaya maka d'an." Toshe mishi bakin shi nayi, cikin tashin hankali, sannan na koma bayan Jay na tsaya. "Jay ina tare da kai. Ka rabu dashi kawai." Janyo ni yayi tare da ture ni, gaban Saif. "Gata nan amma baka da rabo a jikinta kai. Na yarda ni jinin Kwarkwarah ce! Amma sai na nuna maka Ni ban tab'a niman abu a gurin Ubangiji ya ki bani ba! Dan na yarda da shi. .....zan nuna maka yadda ake Kwarkwarah yake amsar abu a hannun d'an halak." Daga haka ya juya abin shi bai kuma magana ba. Bayan shi zan bi Baba Aswad ya yace min. "Dawo!" Kallon shi nayi zan sake kuka. "Saifullah! Kayi Kuskuren, ba Jalal kad'an bane Kwarkwarah daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, nasarar su daya ne. Tun da ya dawo muke niman hanyar da zamu gaya mishi maganar amma yau kad'ai ka ruguzama mana, tanadin mu akan shi. Ka fita a masarautar nan kafin Mahaifin shi ya hukuntaka," Yana gama fadar haka ya sani a gaba muka bar Saif ya tsaye, cike da Mamaki. Muna shiga falon Abban Jay muka same kowa a tsaye sunyi jim, suna kallon Jay da ya sunkuyar da kan shi kasa. Jikina ne yayi wani irin mutuwa, a sannu na taka har gaban shi, na dauki ruwan da aka zuba mishi yasa yaki na mika mishi. D'ago fuskar shi yayi ya zuba min ido. "Tashi ki bar nan!" Muryana yana rawa, nace mishi. "Jay ban san kome ba." "Ki fita yace! Mayya mata zuciya, an ce ba a sonki dole ke sai ya soki ko kunya baki ji ba, kanin bayanki, kike likewa mara zuciya kawai ki tashi min a gaban mijina kafin na nuna miki abinda zai baki tsoro." Inji Munih. "Ke dalla kiwa mutane shiru, banza matar cushe, Hamma Jay baya son wata mace Sama da Addah Aanih, idan kuma kina musu na gaya, Ka bar boyewa duniya SOYAYYAR da kake mata. Sau nawa kana gayawa mutane matar kace ita! Kana yaudaran kanka baka sonta. Wata biyu da suka wuce sabida ceton rayuwarta kai ma aka yanka ka a ciki duk wannan kiyayya ce? A yayinda Allah baya bamu dama a rayuwar kama ta yayi mu gode mishi ba butulce mishi ba. Kowa ya kalli Addah Aanih yasan tana haukar sonka bata da zab'i ne tsayar da wani dan ta nisance ka. Har yau Abba yakan saka hoton Umma Jannart a gaba yana kallonta ba dan kome ba, sai dan abinda kake aikatawa shi ya aikata. Idan ka gadama ka fadawa kowa kana son Aanih Fatimah, idan kaso kayi shiru. Wanda haka shi zai sanya ka zubda kwalla na tsawon karshen rayuwarka. Amma tabbas Zuciyarka nata ce." Inji Jannart karama. Har zata fita yace mata. "Noorie! Dama Ni din Mahaifiyata Kwarkwarah ce?" Juyawa tayi sannan ta sake mishi murmushi wanda ya sanya ta zubda kwalla, ta tako a hankali gaban shi. Ta durkusa, a gaban shi. Tana kallon shi sannan tace mishi. "Mamah Raihanah da Abba dukkan su y'ay'an Kwarkwarah ce, Ummin sokoto da Umma Jannart duk Y'ay'an Kwarkwarah ne. Su wad'ancan matan sabida masalaha aka samar dasu, ita kuma ta samar da daidaiton zaman lafiya ne da fahimtar juna, ta kuma warware matsalolin rayuwar wasu!" "Indai haka ne, toh ki ce mata ta je bana sonta." Mik'ewa tayi sannan tace. "Hamma yayi maka haƙan." . Kauda kan shi yayi, dan baya son ma ya kalle ni. A sanyayye na bar falon, jikina ba karfi, hmm Jay kenan na barshi har Abada, na rabu dashi kenan, idan son shi shine ajalina gwara na mutu na huta. ..... A sanyayye kowa ya bar falon, Kawu zai mishi magana Mamah Raihanah ta d'aga mishi hannu tare da cewa. "Zuru, ta ishi ɗan kunya.! Kyale shi barin gado asara ce." Babu wanda bai ji zafin Jay ba, sai aka kyale shi. ..... Ina kwance kowa na barci amma ni idanuna biyu, juyi nake a hankali, karshe na mike tare da nufar ban daki nayi alola nazo na gabatar da sallar dare. Na jima ina kaiwa Allah kuka na, har zuwa wani lokaci, kafin nayi sallama, tare da mik'ewa. Na nad'e abin sallah. Kwanciya nayi ban cire hijab din jikina ba. Na gyara kwanciya ta. "Aanihhhhhhhh! Shiiii." Naji kamar ana kirana tare da jin karar matan nan, a hankali na mike na sauka a gadon, na fita daga d'akin, sannan na nufi hanyar fita daga gidan baki d'aya. Har na isa bakin kofar fita na sami kofar a bude, a hankali na saka kai na fita daga cikin gidan baki daya na hango ta tsaye, gurinta na nufa tare da bin bayanta har can karshen gidan. Yana dakin shi bai yi barci ba, sai ganin wuccewa yayi dan haka yayi maza ya d'aga labulen tagar shi, sai hangota yayi tana tafiya kamar wacce aka tura ta. Da gudu ya fito daga cikin gidan ya leka dakin yaga duk suna kwancen, tsawa ya daka musu duk suka mike ya gaya musu ga Aanih can ta fita, sannan shima ya fita da mugun gudu, suka biyo bayan shi Rumana da Aliyah. Bayan shi suka bi, yayi musu nisa, har ya cimma. Lokacin da suka iso, sun same shi da ita, suka dambe, lallai ya kyaleta ta tafi. Yadda take kai mishi duka tare da yakushi, sai dai ƙoƙarin janyo ta daga jikin itacen da ta makalewa, ita sai ta isa jikin ganuwar gidan, ga gurin ya zama sunkuru. Lokacin da ya fincikota har su Mamah Sarah da Raihanah sun iso, tare da Kawu. Da shi da Kawu suka janyo ta da karfin tsiya, suka nufi cikin gidan tana ihu tare kuka tana faɗin. "Wallahi sai ta mutu! Sai na kashe ta. Sai ta sadaukar mana da rayuwarta." Share zufa Jay yayi, tare da kallon Kawu, sannan yace. "Idan na fahimta akwai abinda kuke boye min, meke faruwa a cikin masarautan nan?!" Ajiyar zuciya Kawu ya sauke sannan ya mike tare da shiga dakin shi sa ya dauko wata ruwan addu'o'in ya kawo ya shafa mata, da taimakon Raihanah aka dura mata ta shanye. Bayan sun bata ta watso musu tare da komawa ta kwanta sai barci. "Abba me kuke nufi dani da ba zaku gaya min me ke faruwa ba?!" ... "Idan kana son sanin meke faruwa sai dai ka auri Yarinyan haka ne kawai zai taimaki rayuwar ta, in ba haka ba toh kuwa mutuwa itama zata yi." Inji Kawu. ...."kamar mutuwa zata yi? Kenan akwai bashin da kuka ci, wanda sai ita da bata ji ba bata gani ba? Me yasa kuke ruffenfen sirrin boye? Ku gaya min abin da yake faruwa" Shiru yayi sakamakon kallon da Rahil tayi mishi, dan yasan bata sakewa kowa fuska. "Babban Rumah ina ga tunda ta sami barci, ku koma cikin Ni zan zauna da ita." "A'ah muma zamu iya zama ai. Sauran su shiga cikin gidan, mu sai mu zauna." Shiru kowa yayi, dan yan matasan sun razana, kawai sai suka zauna a gurin dan tsoro ya hana su shiga dakunan su. ...... Tsura mata ido yayi, yana juya amsar da Abban shi ya bashi akan ta, shi dai baya sonta amma a duk lokacin da zata shiga wani irin yanayi sai yaji ba zai iya jurewa ba, shi yasa baya kaunar yaji wani abu ya same ta, amma ba damuwan shi bane yayi ta kirb'a mata rashin mutunci, koda kuwa zata na kuka yana masifar kaunar kukan ta, dan burge shi take. Baya kaunar macen da bata da raki, ya na son mace me raki. Musamman wacce take da saurin fansa tare da fada, yana son mace me addini da ibada, Aanih kuwa yaga har tabon Sallah ce da ita, shi duk da ta haɗa abubuwan da yake so. Sam baya ra'ayin bazawara, duk abinda zai mata yana mata ne dan tana ramawa. Ya jima yana nazarin wasu abubuwan akan ta, wanda suka mishi amma shi baya kaunarta ko kadan. Har aka kira sallah farko sannan ya mike ya nufi shashin sa, yayi alola tare da saka jallabiya ruwan toka, sabuwa kal. Haka ma Abban shi, ya fito sanye da farar jallabiyar, suka nufi masalacin tare. Karfe bakwai saura Kwata na farka tare da dafe goshina, ina ƙoƙarin tuno abinda ya faru amma ya tafi kamar mafarki, tashi nayi Ummi ta rike ni muka nufi ban dakin dake dakin da muka kwana. Ita ta haɗa min ruwan wanka, na shiga nayi tare da alola nazo nayi sallah, sannan aka kawo min abinci na ci, kadan ina kallon Ummi ta hada mana kayan mu, sannan aka fitar da shi waje. Bayan an shirya mana, na mike a sanyayye, na saka hijab dina. Ina gyara zaman shi yana shigowa cikin ɗakin, wani irin bugawa kirjina take kamar zata fashe. Sunkuyar da kaina nayi kasa. Jikina a mace. A hankali ya tako gabana, tare da zura hannun shi a cikin aljuhun rigar shi. Shiru yayi na wani lokaci sannan kalle ni a karo na biyu. "Ban san me yasa haka ke faruwa damu ba, amma ina miki fatan Alkhairi." Ya faɗa min , da sauri na d'ago kaina na kalle shi da idanuna wanda suke cike da kwalla. A sanyayye na raba gefen shi zan wuce, ya rike min hijab. "Bana jin zan iya samun damar maimaita abinda ya faru a cikin rayuwar mu ba. Daga jiya zuwa yau, Zuciya ta ta haneni da na barki kiyi rayuwarki kamar kowani me Yanci, nasan na baki wahala,. amma ina niman haka ya zame mana abinda zamu tuna muyi dariya da farin ciki. Nasan na sanya ki kuka, amma ba zan iya baki hakuri ba, amma zan iya ce miki ina miki fatan Alkhairi. Ki fahimci..." "Toh me yasa kake fada ni matar kace? Me yasa kake son kare martabata da sunan matar ka ce ni, Jay da zaka zauna dani ba zan tab'a barin ka kamani da laifi ba. Da zaka zauna dani, ba zan tab'a barin ka kayi korafi ba. ..... Jay shin son ka da nayi laifi ne? Meye kuskure na? Gaya min meye laifina? Meye baka bukata a tare dani zan gyara, saura kwanaki ƙalilan." Takawa yayi har jikin tagar dakin, yana me d'aga labulen yana kallon waje. "Ba zan iya baki abin da kika bani ba! Ba zan iya tisassa zuciyata kaunar abin da bana son shi! Zan iya kome amma banda dolantawa kaina abinda bana so? Kije Allah ya baki zaman lafiya da mijinki. Tare da zuri'a na gani." Ji nayi kamar nuna juya na rungume shi, ina sake wata irin kuka. Ji nayi kamar na bude mishi kirjina yaga yadda sunan shi take rubuce jikin allon zuciyata. Bana ɗebe tsammanin koda zan rasa kome, indai zan same shi zanyi maneje da shi a haka, koda zan iya samun tawayya daga dangina zan rungume Jay a matsayin abokin rayuwata. Zan yi hakuri akan shi kuma zan kauda kaina akan shi, bazan tab'a zama mishi azzalumar mace ba. Iya abinda zan iya yi akan shi ya hadda har da sadaukar da Rayuwata da farincikina akan shi, amma ina lura da yayi ina mutuwa akan soyayyar shi itace makulin rashin mutuncin da yake min, lura da yayi ina kassara zuciyata akan shi itace zaren azabarin janyowa yake azabtar dani ta hanyar cewa baya yi na. Me yasa mace bata da kima a duk lokacin da ta cewa namiji tana son shi! Me yasa mace bata da wata daraja dan tace tana son namiji, wannan al'amarin yana matukar damuna, a duk lokacin da mace ta furtawa namiji ina sonka toh daga ranar duk wata kima nata ya kare. Koda kuwa yarinya ce qarama, toh da zaran ta fadi haka toh magana. Ya ƙare sai na miji ya bijiro da wulakancin yayi ta mata gashin kuma,.yana wulakanta ta, yana mata abinda ya gadama... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi* Ban kuma tsinkewa da Jay baya yina ba, sai da na fito matar shi ta tsare ni zata min rashin mutunci, Rumah ta dakatar da ita. "Kina wani abu kamar Jahila! Kina hauka akan mutumin da ya kusan kare minti arba'in a cikin d'akin ta.        Haka bai ishe ki ba? Haka bai nuna miki ita ce abin da yake bukata ba." "Rumah! Bana son damuwa, mata ta zo muje." Ya mika mata hannu! Cikin dauki da murnan ta mika mishi hannu. Yadda ya rike ta sai da ta kalle shi.        Suna barin shashin, ya makureta a jikin bango, tare da zare mata idanu. "Wallahi Munih kina kure hakurina, idan na kuma ganin kin zagi Aanih sai na karya miki hannun ki. Wacce bata san ciwon kanta ba."                   Sake ta yayi ta fadi kasa, sannan yayi wucewar shi, sashin sa. Yana shiga dakin shi ya d'aga labulen da yake kallon inda su Aanih take, a sanyayye yake kallon yadda take niman shi. Tana duba ta inda zai ɓullo amma har ta shiga cikin motar babu shi babu alamar shi.   .... Har ta zauna ta kuma fitowa, domin gyara zama. Kamar ance ta d'aga kai ta hango shi yana kallonta, sake labulen yayi tare da juya bayan shi, ga tagar.      --- Tunda na gan shi yana leke na abin ya bani mamaki da al'ajabi, kawai na shiga motar tunda ba zai min amfani ba.           Tunda muka dauko hanyar gida, na shiga damuwa sosai. Domin naga sakon Saif da ya turo min akan gashi a gaban Dangina, ya kawo ƙara na akan abinda muka mishi ni da Jay.         Tunda naga sakon jikina yayi sanyi, na rasa yadda zan gaya mishi abin da min bai kyau min ba. Haka nayi shiru, can naji Ummi tana magana a hankali. Tare da bawa Baabi hakuri.        Can ta kashe wayar sannan ta juyo gare Ni tace min. "Meye amfanin abinda kika yiwa mutumin da zaki aura? Kin ja min Bankad'a  a cikin danginki. Sunce nice nake sanya ki abubuwa saboda d'an yar uwata meye yayi zafi da Mahaifinki yake min barazana akan aurena?"   Shiru nayi tare da sunkuyar da kai na ƙasa, har muka isa sokoto.. Ummi waya take cikin harshen kanuri, ban san meke faruwa ba, amma naji Hanisah tana ce min.         Baabi ya haɗa Ummi da Babanta ne shi yasa take ta magana tana faɗin gaskiya.. har muka shiga cikin gidan. Inda na samu yan uwan Baabi da Saif ana jiran mu, Ummi bata tsaya ba tace zata yi sallah idan zasu iya jiran mu toh.    Tsoto ya kamani musamman da naga dangin mu baki d'aya, har da kakata Ummi.         Bayan mun idar muka nufi inda ake tattaunawar,.ina bayan Ummi. Dake ranta ya b'aci sosai zama tayi tana kallon kowa a wajen tarr.           "Assalamu alaikum jama'a Barkan ku, ba wani abu ya hada mu anan ba, sai magana akan abin kunyar da Fatimah take shirin aikatawa a cikin masarautan nan! Jiya da dare Saif ya kirani yana gaya min Ya kama Fatimah da D'an Sarkin daura da ita suna masha'ar su." Ba iya Saif ba hatta ni sai da muka kalli Bana Annuwar, jikina ya dauki rawa sosai, kamar wacce aka jona min lantarki.           Kallon Baabi nake kam shi a sunkuye, tare da kallon Saif shima na shi a sunkuye, wani irin kuka ne ya kwace min.  Na shiga rantse rantse.         "Wallahi babu abinda ya haɗa Ni da Jay, asalima fada suka yi Saif ka fada musu gaskiya mana"   ..shiru yayi, sannan Baba Annuwar ya shiga fadar wasu abubuwan masu daure kai da muni, wanda sam ban aikata ba, kallon Baabi nayi tare da son ganin shin ya yarda da abin da suka ce, amma yaki kallona.        Nan kowa ya shiga fadar albarkacin bakin shi. Daga nan suka min cin mutuncin akan Jay. Juyawa da suka yi zasu zagi Jay Ummi tace musu. "Baku isa ba! Baku haifu ba, yar ku dai ku mata fada amma duk wanda ya Kuskura ya zaga min d'a ko ya sake kazamar bakin shi akan Jalaludeen. Toh na rantse da Allah sai masarautan nan ta tashi tsaye da kafaffunta.      Sannan kai Annuwar da kake maganar cewa Jay da Aanih suna masha'ar su, kai meye ribar tozarta d'an uwanka a gaban jama'a?   Meye amfanin cin fuska haka, sabida yana da hakuri ko? Sabida baya fada baya kome duk abinda zaku mishi akan ta bazai tab'a cewa kome ba.        Toh wallahi ku kiyayye abinda zai sanya shi yayi magana, kai kuma Saifullah zaka aureta ko ba zaka aureta ba?"     Bakin shi na rawa yace. "Zan aureta!"       "Tashi kar na kuma ganin me kama da kai sai ranar auren ku" da sauri ya mike, yana fita ta shiga gayawa yan uwan mu magana, tare da cin mutuncin su. Kamar yadda suka yiwa Baabi, cikin izza tace musu. "Ban da nima a cikin nima, haramun ne da sai an nimawa Jalaludeen auren yarku muga ta karshen tsiyar ku, kuma a biya sadakin da ba'a tab'a biyan wata mace da shi ba a cikin masarautan nan ba." Korata tayi sannan ta zauna tayi musu wankin babbar riga, sannan ta bar falon abin ta, tana zuwa ta amshi wayar hannu na, tare da kashewa.    Bayan tafiyar ta, nan suka shiga fadan abin da yayi musu, har da cewa. "Matukar  Aanih ta auri yaron nan babu mu babu ita. Taje can su kara ta, dan bazata  ja mana faduwar daraja ba, daga masarautan Zazzau ba."                       "Hmm! Ban san me yasa Rahil take takama ba, ban san me yasa take jin ita wata ce ba, ko ce mata aka yi muma sakarkaru ne da zata zauna yana gaya mana magana, son ranta wato d'an Yar uwanta shine abin burgewa ta kare laifin shi.         Toh Wallahi duk abinda take ji zata samu, dan.." Shiru tayi sakamakon haɗa ido da suka yi da Ummi tazo gurin Baabi. "Hajiya kenan! Da fatan na barki da ɓaɓatu! Duk ba laifi bane, amma kin san kome lalacewar gawar Giwa tafi kwando tara," Gaban Baabih taje suka yi magana sannan ta d'ago kanta. Mik'ewa yayi sannan ya basu hakuri da abinda ya faru. ...... .  Haka da yayi musu ya masifar d'aga musu hankali, nan suka fita daga gidan. Aka shiga yawo damu a cikin Zuri'ar mu.    Su lallai Baabih ya min fada tare da Ummi, shi kuma bai ce komi ba, sai ma zuba ido da yayi.     Abun ya zama rikici da ya janyo aka hanamu shiga cikin gidan kakanmu, hatta wasu abubuwan an hanamu shigar cikin shi, balle kuma irin su Suna da wasu abun. ..... Matar kanin Mamana ta haihu dan haka nayi ta rokon Baabih ya bar ni naje, ni da Hanisah. Muka tafi mun je an karb'e mu hannu bibbiyu. Muna zaune a dakin Ayyah kakanta ta gurin Mahaifiyata. Sabirah da Hoor, suka shigo y'ay'an maza muke dasu, Baban su ke bin Mamana, suna gani na suka fara dariya tare da faɗin. "Makara! Kece a gidan sunan bayan an hanaku fita sabida ana gaya muku gaskiyar da baku so?"       "Shi yasa naga ganku cikin sanin ya kamata, zancen manyan na manyan ne, mu yara ina ruwan mu."inji Hanisah, wata irin B'oyayyen ajiyar zuciya na sauke tunawa da nayi ita din gwana ce a masifa, gyara zama nayi tare da zuba musu ido.          "Ke karki min rashin mutunci!" Inji Sabirah. Budar bakin Hoor tace mata. "Ai gado ba karambani bane, abinda aka sha a non..."    "Ni rawa gadon mai kyau ce? Wasu tasu gadon har abada ba zasu iya sakewa da mutane ba, Ni Yanzun idan Uwata ya zo nan an santa da zafi yanayinta kenan, uwar wata kuwa sai dai kaga ana tattara kome saboda dabi'ar bera gareta."       "Kan uban can! Ni kika zaga?"  Inji Hoor!                 "Bafa zagi nayi ba, wai ina gaya miki gadon da muka yi ne, ke baki fahimtar Yaren ne."     Ai kuwa suka fita, can sai gasu tare da dangin Mahaifiyata, suka shigo zasu dake ta, kallon su tayi sannan ta girgiza kanta, tace musu. "Ko kunya baku ji ba, kun dibo jiki zaku wulakantata sabida an gaya muku karya da Karerayi akan yar yar uwan ku, ko tausayin rashin uwa da bata dashi baku yi. Kun zauna akan abinda aka gaya muku sabida ranku yana sosuwa da SOYAYYA da ta samu a gurin mahaifinta.        Da yau dukiya tana dawo da mutum tabbas Hassanah Ummina zamu bada duk abinda muka mallaka daga masarautan daura har zuwa masarautan shehun Borno, tun duniya tana kwance ahalin mu suke taka rawan gani a kasar nan.           Dukiya mun gan shi mun kuma san shi, soyayyar da Zuri'ar mu takewa Hammah Jay, ya wuce yadda kuke tsammani..akan shi kuke tsanar Mahaifiyata? Sabida son kai da son zuciya, toh ku dake ni, sabida nice nayi magana ba mareniya ba. Ko kunya baku ji ba, ku iyaye kuna fadan abubuwan da basu dace ba akan yan uwanku, wallahi matukar Fatima ta shiga cikin Zuri'ar mahaifiyata sai kun gane cewa shi mulki da dukiya al'amarin Ubangiji ne, yau muna kallon Hammah Jay a matsayin Mahaifiyarshi ce, sabida shi daya ta bari.    Bamu da madadinta sai shi, mahaifiyarta ta rasu ta bar muku  ita, domin idan kun tuna da ita ga madadinta sai ku mata addu'a, amma sai gashi babu wacce kuka tsana sama da ita, da yau ana mutuwa a dawo baku ji kunyar Mameeh ta dawo ta ga abinda kukewa Yar ta ba. Burin ku sunan ta ya b'aci ace sabida rashin amana mahaifinta ya gaza bata tarbiyyar da ya dace. Ku ji tsoron Allah akan zalunci da kuka mata. Allah sai yabi mata hakkin ta, karku manta akwai rayuwa akwai mutuwa.". Daga haka ta riko hannuna zata fita ta kalli Hoor tace mata. "Kuskuren ki tab'a min ji kimata! Shi yasa na tab'a naki, ba kare bin damu!" Daga haka muka bar gidan. Ina kuka Allah yasa ita ke jan motar dan dukkan mu Baabi ya saka an koya mana mota.              "Nagode kanwata Kawata." Na faɗa mata cikin kuka, girgiza kai tayi sannan ta cigaba da tuka mota tana faɗin. "Ban san me yasa baki iya karban kanki hannun mutane ba, nifa ba zanyiwa kowa kuka ba"        "Sabida kuka da gadon taurin zuciya ba! Kuna iya boye kaunar abinda kuke so ba! Da zaki ji yadda nake son D'an uwanki da sai kin tausaya min."   "Mun sani mana, toh ya zamu yi da dangin Baabi? Kin san Ummi ma ba sha tayi a hannun su ba, kawai tafi su baki ne. Wallahi kaf dangin Ummi babu wanda baya mutuntaki, ana ganin darajarki fiye da yadda baki zata ba, ko jiya sai Da Kaka Bana ya tambayi Hammah Jay, akan da gaske yana sonki? Yaki bashi amsa. .da ya bashi amsa toh ina gaya miki sisin gwal ne sadakin ki.      .ko Ni bana tsammanin zan sami sadaki sisin gwal, amma ke naji har kowa ya gama hada kome na sadakinki.. amma mara kirkin nan ya ce baya sonki."      Lumshe idanuna nayi sabida kalmar baya sona ba sabon kalma bace da zan ji haushinta, kalmar ta jima da zame min Alakakai. Bude idanu nayi lokacin da naji ta ja burki.           Ikrama ne ya sha gaban mu, da sauri nace. "Ke tadda motar mu bar nan mahaukaci ne." Sai da ta barshi ya kusan zuwa dab damu, kawai ta finciki motar da masifar gudu, ya kuma koma cikin nashi ya rufa mana.   Da sauri na shiga lallubar Number Saif, ban san na fada kan Number Jay ba, kawai na shiga kiran shi..... Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu... 10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari.*   "Saif! Ikrama ya biyo mu!" Na fada a rikice, muryana yana rawa,        "Da alamu baki duba wanda kika kira ba ko?" Yana fadar haka ya kashe wayar. Kafin nasan abin yi ya daki motar mu, wayar ta fadi nida Hanisah muka saka salati. Sai lallubar wayar nayi cikin tashin hankali, na kuma kiran Jay.  Naji yana waya.         --- Yana zaune a dakin shi, dan sunan yayi aure ne, amma babu abinda ya dame shi da matan shi,   suma tsoron shi suke dan Munih ta tab'a gaya mishi magana akan ya ajiye su babu abin da yake tsinana musu. Shi kuma da Iskanci yayi mata alluran fitina.           Tayi ta hauka yana kallon ta, sai da ta gama fita hayacinta, sannan ya mata wani alluran da ya Sata barcin dole, shi yanzun burin shi a gini mishi asibitin shi ne baya son kome sama da haka.    Ya zaune Aanih ta kira shi,  kamar ba zai dauka ba, dan yasan sarai yanzun zasu raba hali, da ita tunda daga shi har ita. Basu rena abun faɗa.   Ganin kiran yaki karewa ne ya dauka tare da mannawa a kunnen shi, jin yadda take fada mishi halin da suke ciki sai da ya sanya shi tashi ya zaune. Sannan ya gaya mata ba Saif bane.    Katse kiran yayi, sannan ya kira   Habib, sun jima suna magana. Kafin ya sashi ya had'a shi da mai girma Gwamnan Sokoton.      "Barka dai yallabai!" Shiru yayi sannan yace. "Ka kira yaron ka, kace mishi ya daina bin yarinyar nan ko kuma ni nasa a kwashe mishi kayan aikin shi baki daya, idan kuma kana ganin karya ne ka bani nan da awa daya zaka sami gawar d'anka!"      Daga haka ya kashe wayar abin shi ko ta kan Aanih bai kuma bi ba.           *** Gudun da muke wanda ya kusan fitar damu garin sokoto, gashi yamma ta fara yi, ganin shi muka yi ya juya da gudu, muma kuma muka juya da gudun.  Gida muka nufa.      Tunda muka shiga, a tare muka sauke ajiyer zuciya, nace mata. "Na yafe fita ko ina, Insha Allah."          Har zan fita Hanisah tace min. "Addah! Ki kira Hammah Jay kiyi mishi godiya dan nasan wannan aikin shine da taimakon Allah, ya kub'utar da mu."      Murmushi nayi sannan na fito daga motar. A raina ina kara jin son shi, Jay kenan, ga dad'i ga tsiya.          Koda muka shiga cikin gidan, kowaccen mu daki ta wuce, muka yi alola da sallah magarib, sai bayan isha na kira shi, kamar yadda nai tsammanin zai dauka. Sai jin muryan Munih nayi Allah ya taimaka ban yi magana ba, kome ta ganin a jikin sunan wayar ta fara zagina. Kashe kiran nayi ban kuma gigin kiran shi ba.     .......     Lokacin da da yazo yaga wayar shi a hannun Munih, kallonta yayi sannan ya kura mata ido. Dake bata da kunya ce mishi tayi. "Wata karuwa kasa batun?!"      Kallonta yayi sannan yace. "Ruhi ga ruhina! Haske ga Haskena? Ko zaki hanani kula mata ne?" Ya gaya mata, "Toh kuwa naci Ubanta? Domin na zage ta!" Ta gaya mishi tare da wular da wayar a bisa gadon shi.          Bai damu da ita ba, har zata fita ta juya tana faɗin. "Wallahi tallahi billahil azim, idan ka kuma auro wata mace cikin masarautan nan, nice ajalinta. Domin zan kasheta har lahira."    ... Sake baki murmushi yayi sannan yace. "Insha Allah, saura kwanaki ƙalilan ki samu amarya domin zanyi kuwa."     ..nan tafita tana banbami, kallon wayar yayi yaga batul! Tsaki yayi tare da kiran wayar aka ce ana amfani da wayar.        --- Bikina ya kankama, dan ana ta hididdinmu, kamar yadda ake ina can an sanya ni a daki, ana ta dirka min kayan gyara, tun ina jin haushin su, har na hakura da shan su, domin kuwa na gaji da kayan gyaran. ....ranar Laraba, aka yar ƙwarya ƙwaryan walima, ranar Alhamis. Kuwa aka mana lalle. Kin bakin nayi nace a min ja.    Sabida lokacin da Jay ya tafi dani, abu ba abu ba, zai ce jan lalle nan tayi min kyau. Kawai sai na tsinci kaina da sawa a dauke ni a hoto da jan lallen na tura mishi tare da mishi godiyar da banyi ba, sannan na mishi fatan zama lafiya da matan shi.    ..... Can ya kuma turo min sakon da cewa. _Allah ya bada sa'a! Ya kuma baki zaman lafiya! Ya kuma tabbatar miki da auren nan jibi._      A rikice, na kira shi yaki dauka ya turo min. _Karki dame Ni don Allah! Kiyi aurenki mana, ni dai Allah ya tabbatar miki da Alkhairi ayi shi ranar da Saif_      *Don Allah karka lalata min rayuwar aurena! Fatan Alkhairi kawai na tura maka da godiyar abin da kayi min*   _Ni nace miki zan lalata miki aurenki ne? Kar ki min sharri mana_   _😭Don Allah kar ka min haka, wallahi zaka ja min magana a gurin dangin Mahaifina da Mahaifiyata_     *Ai kuwa! Ni ban isa na lalata miki suna ba, kawai nayi abin da ya dace tunda gashi na miki fatan Alkhairi, amma kina zargina*   _Nasan halinka! Na kuma san waye kai! A zamana da kai babu cutarwa! Amma kai_     *Toh nagode daga abin arziki zaki bini da Sharri.* Ya rufe wayar abin shi, shigowa Husnah tayi ta zauna a kusa da shi. "Allah ya huci zuciyar Saraki!" Tace mishi, "Don Allah jeki kaina yana ciwo! Bana son magana." Ya gaya mata.          Bata damu ba, ta mike ta bar d'akin. Bin bayanta yayi da ido. Yarinyar tana da kawaici ba kamar Munih da take mishi kallon kamar zata cinye shi ba.          --- Yau Jumma'a, baƙin daga wasu sassa na jahar Najeriya suka fara zuwa, domin halartar daurin auren mu.          Ina zaune Bayan sallar isha, ana min kwalliya, dan zamu tafi liyyafa, hankalina yana kan kwalliyar da ake min, tare da sauraron hirar da Hanisah suke da mai kwalliyar take cewa. "Nifa turo min sako aka yi tare da kudi masu yawa, wai zanyiwa Yar Sarkin Musulmai kwalliyar bikinsu."    "Ba kuma baki san shi ba? Zaki tawo?" Na tambayeta da sauri bayan na dakatar da. "Gimbiya! Ni ai turo min sako aka yi ta email! Sannan aka ce na tura account dina, Ni kuma nayi kome, har da kuɗin jirgi aka biyan min. Kuma da na iso ya turo min da wancan kayan wai shi zaki saka. Ina ga angon ne!"   Shiru nayi kafin na duba kayan, aikuwa munyi da Saif da na tura mishi kayan nake son sakawa yace ban fada Da wuri ba, ba zai samu saya min ba,  Ni kuma ina jin kunyar Baabi, domin yana ta tambayana me nake bukata nace babu, sai gashi Saif din ya kuma cika min alqawarina."   Kamar zan yi kuka na dubi kayan, doguwar riga ce, ruwan kore mai duhun shi wanda ake kira(royal green) sai tare yake zuwa da wasu yan kunne da sarkan su na azurfa wanda aka samu su Duwatsu masu daraja.  Ji nayi kwalla ta cika min ido, lokacin da naga har da takalmin su dan iya rigar kawai na bukata, ina da wasu yan kunne da abin wuyan da zan saka.             Dan nasan idan nace ya saya min gabaki daya zai ce a'a, kamar yadda nayi tunani haka ya faru, sai na share ban kuma cewa kome ba, ashe zai saya min.    "Hanisah! Kin san lokacin da na gaya mishi cewa, ina son kayan ce min yayi bai da kuɗi amma kiga bazara da yayi min naji dad'i wallahi."      "Ai kin gaya min. Ko kin manta ne. Kinga har da jakar kayan. Gaskiya Saif yayi Namijin ƙoƙari da ya saya miki kayan nan." Haka na koma aka cigaba da min kwalliya na, sannan na tura mishi sakon. _Nagode_      Bayan an gama gyara min kwalliyar, aka shirya ni tsaf. Sannan muka fito, juyawa nayi naga Hanisah da Jannart karama na Katsina sun d'aga min rigar, ina saukowa daga shashin Ummi, wani irin kyau nake fitarwa, har falon kasa.        Na samu yan uwan da kawayena na cikin masarautar suna jirana, kowa ya kalle ni sai yace masha Allah, sannan muka fita.          A motar da Saif ya turo na shiga, ana gyara min zaman rigana.  Kafin Hanisah ta shiga ya ja motar da gudu muka bar gurin..kallon shi nayi tare da lek'awa. "Jay!!" Na daka mishi tsawa. "Kar ki kuma min tsawa."     Gabaki daya ya dauke ni daga inda ya dace, can wani wani otel ya kai ni. Ya kama mana daki, sannan yazo ya ja ni ya kai ni da farko naso taurin kai, kallona yayi sannnan yace min. "Wallahi zan dauke ki cak, na shiga dake."       Ko tari banyi ba, na fito a hankali ya saka hannun shi ya tattara min jelar rigana, muka nufi cikin otel din, muna shiga dakin na zauna tare da fashewa da kuka. .... Sosai har jikina yana rawa, bai damu ba kawai fita yayi a dakin na wani lokaci. Tun ina kallon agogon bangon dakin, har na daina, sabida tashin hankali. Jay bai dawo dakin ba, sai sha biyu da rabi ya zo ya dauke ni muka koma gidan. Bai damu ba,ya nuna min hanyar na fita. "Allah sai ya saka min! Wallahi na yi dana sanin, sonka da nayi a rayuwata, Jalal kai mugu ne! Azzalumin wanda bai san kome ba sai son kan shi, me zancewa Mutane! Me zan gaya wa mahaifina da yan uwansa?"     "Shi ya fiki sanin waye ni! Ya kuma san abinda ya dace? Fita ko na baki shaidar da zai tabbatar miki tsaf nake na kira kaina mijinki!" Da sauri na balle motar. "Insha Allah ba zaka tab'a zama mijina  ba, kaje can gurin kwailolin ka, ku cinye kanku. Yaro karami da kai sai tsageranci, da rashin kunya."    Dukar motar yayi, tare da sako kan shi zai fito, na juya da sauri ko tsayawa ban yi ba, dan nasan ba kunya ce ya wadace shi ba. Ina shiga falon, na sami yan uwan Baabi, suna jirana, ban tab'a fuskantar cin mutuncin irin na yau ba, tare da yan uwan Maamana, sun zage ni tare da min mugun fata, Baabi kan bai ce musu kome ba, burin shi kawai gobe a daura min aure na bar gidan shine fatan shi. Nayi kuka kamar me kusan kwana nayi a zaune sai da asuba na kwanta, shima ban jima ba. Aka tashe ni da wani mugun zazzaɓi na tashi. Wanda yayi sanadin dole aka hakura da kwalliyar da za a min,          Na cigaba da kwanciya, ina kwance Ummi ta kawo min abin karyawa sai da ta sani na karya dole ina ci, na fara kwara amai. Lokacin, Aunty Aina'uh ta shigo ita da Aunty Barakah, ganin ina amai kamar hanjin cikina zai fita ya sasu tsaki. "Abin da ake gudu, gashi nan ta sake mishi jiki ya gama da Ita!"          "Zazzabi ne kuma haka take zazzaɓin ta, Yarona ba FASIKI bane kamar yadda itama ba fasika bace, kuna da Yara maza da mata me yasa baku tunanin goben su? Me yasa baku tab'a tunanin Fareeda sai kanku?." Nan suka shiga gaya mata magana, ita kuwa bata kula su ba, ta mai da hankalinta kaina.         ---- Karfe sha daya aka fara shirin daurin auren, wanda sai da aka fara karanto siga, sannan kuma aka kuma sanar da kuma daurin.     Kallon Juna Saif da Jay suka yi, kafin Jay ya matso kusa da shi yace. "Na gaya maka ban tab'a niman abu a gurin Ubangiji ya hanani ba, saboda nayi imani dashi, karfina bashi zai bani ba, da naso bar maka ita! Amma da nasan cewa kana tare da wancan munafukin Kanin Babanta ya sani dawowa na maka dukar da zaku fadi har kasa, ya kaji sigar Jalaludeen D'an Jaamal! Jaamal d'an Jalaludeen, har zuwa kakana na biyu. Ko bazan ya kome da ita ba, zan ajiye ta kamar fitila a cikin gida na. Alhamdulillahi na mallaki Fatimah, na gaya maka baka da rabo a jikinta. *D'an karamin su! Babban su nake* Daga haka ya wuce gurin mutane, yana mika musu hannu, ana gaisawa, fuskar shi sai fidda annuri yake, kamar wanda aka bashi wata abu bayan Fatimah. Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *Abokin damo, guza* Murmushin sa kawai zaka kalla ka fahimci yana cikin farincikina, yana tsaye dasu Najim da Hikmi wanda ya samu labarin auren Aanih Fatimah.        Daga nan aka suka wuce, wata yar karamar wani Baabi ya haɗawa Jay. Na daurin auren, sosai aka yi wa'azi sannan aka taso. ..... Ina kwancen Yayar Baabi ta shigo Hajiya hafizah kallon banza tayi min. "Kinyi asarar rayuwa! Kanin kannin bayanki kika dage aka baki. Toh ki shirya dan matan shi babu jahillai irinki bane, wacce bata da aiki sai son zuciya." Haka ta gama zage ni tass, tare da mugun nufin akan auren da aka min, wallahi ban fahimci sabida Jay take min wannan diban albarkan ba.      Bayan fitar ta, na kumshe idanu na, ina jin d'aci a rana. Tare da jin zafin abin da suke min, can naji an rangad'a gud'a tare da kirari, tunda naji haka na fahimci tabbas an shigo da Sadakina ne, kuma tunda naji haka.     Da gudu Hoor suka shigo dakin tare da janye min bargon suka yi tare da d'aka min duka, suna fadin. "Sisih gwal na miliyan daya da rabi. Wai waye Mijin nan baki da ya rikita miki lissafi.           Lallai kin haɗu, waye ma angon ne haka?" Suka tambaye ni lokaci guda.  Wani irin sanyin nake ji wanda ya tilasta ni jan bargon na rufe kaina, ina rawan sanyi.         Kallon juna suka yi sannan suka fashe da dariya, jin ana buga tambura tare da kakaki, can kuma aka fara busa algaita, ya sasu da sauri, Ni kuwa wani irin kuka ne me ban tausayi ya kamani, tare da sabon zazzaɓi.                 .... Suna sauka kasa, Jay da abokan shi suna shigowa, zuga guda. Domin wasu da safe nan suka iso daga nijar. Dan bai gaya musu auren shi na Daura ba, amma wannan ya gaya musu tun sati daya da ya wuce.                 Aikuwa suka tawo, yanzun haka wasu zasu wuce Daura sabida akwai liyyafan da za ayi a can.       Tunda ya shigo falon, duk yan uwan Baabi sai da jikin su ya mutu, musamman yadda ya shigo da abokan shi wanda suka kasance yan boko ga samartaka, uwa uba, kyau da haduwa. Wannan yasa yan uwan mu, shiga hankalin su.        Haka suka gaida kowa, aka kai su falon Ammih da Ummi, suka yi gaisuwa, kafin suka wuce cikin gida, inda anan suka yi wasa da kuɗi kamar basa so. Domin kakanina da abokan wasa suka tambaya. "Waye Jay din nan ne?!" Nuna shi Najim da Fahad suka yi.             Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai yana gyara babban rigar shi.     "Ai dole Yarinya tayi hauka! Toh munji ka biya sadaki da sisin gwal! Mu kuma bazamu baka ita ba sai ka biya mu, ladan mu."     Murmushi yayi bai ce kome ba, take Hikmi da Fahad, suka yi magana. A hankali Hikmi ya ciro musu bandiri na dollas, ya ajiye musu.     Wani irin guɗa suka yi tare da jinjina musu, har zai mike Umman Baabi tace. "Jalaludeen!!" ... A sanyayye ya d'ago kan shi. Tare da saukewa a kan Umma, sannan ya kuma sunkuyarwa yana sauraron ta.         "Kayi hakuri! Kayi hakuri!! Kuma nasan Takwara tana da hakuri da nutsuwa,  nasan zaka yi dace da samunta, zai yi wuya ta botsare maka, amma Insha Allah zaka same ta a macen rufin asiri. Macen da zata boye laifin mijinta, zata zame maka garkuwa, a yayinda Duniya ta juya maka baya, nasan halinta ba zata tab'a ketare iyakar da ka shinga mata ba. Ga Fatimah nan ka riketa amana, Allah ya baku zaman lafiya."         "Amin kowa yacee."  A hankali Najim ya isa gabanta ya ajiye mata yan dubu dubu, har uku. Sannan yace. "Gashi nan ki kunsa lalle, inji angonki."           "A'ah Ni bazan amsa ba dan mutum na baku, bance ku mai da.."   "In dai nida Batul d'aya ne toh babu amfanin ki dawo mana da shi." Ya faɗa a sanyayye. Albarka aka shiga saka mishi,  basu fita daga gidan ba, sai da sukawa yan uwan Baabi da yaran su Alkhairi. Wani abin mamaki kamar yasan basa kaunar shi. Amma yayi ta sawa ana basu kudi.      Bayan sun fita yaji wayar shi tana kara, dubawa yayi yaga Ummin dauka yayi tare da sakawa a kunne yace mata. "Barka!" "Abbalawan kazo Fatimah bata da lafiya fa" Shiru yayi sannan yace. "Toh ai gidan.." "Matar kace da bamu da matsala akan..." Katse kiran yayi sannan ya kalli abokan shi tare da kallon agogon hannun shi yace musu. "Bari na duba wancan matar." Dake sun fishi Iskanci suka juya tare da cewa. "Wacce mata??" Banza yayi da su, ya juya a hankali yana shafa fuskar shi, dan matuƙar ya tsaya zasu mishi maganar banza ne.            .....koda ya shiga ya samu falon a cike da mutane, cikin tsananin kunya ya koma tare da kiran Ummin shi, turo Hanisah tayi suka haura dakin, ina kwance na dunkule sai rawan sanyi nake.     .... "Assalamu alaikum!" Yayi sallama, duk da ina son d'aga bargon amma babu karfi a jikina, dan dole na koma tare da rufe idanuna.    .  A hankali ta ajiye maganin tare da abincin da tasa Habisha ta kawo min, yana tsaye Baabi ya shigo. "Jay! Kai ma ka shigo ne?" Cike da kunya ya sunkuyar da kan shi, yana sosa keyar shi. Fita yayi kawai. "Toh ka duba ta mana, idan kuma za a mata karin ruwa ne sai kayi magana."    Gyada kai yayi sannan ya matsa jikin gadon, yana ganin sun fita ya koma jikin kofar ya rufe, a hankali ya cire babban rigar shi, sannan ya isa bakin gadon.    Zama yayi  tare da yaye bargon yana kallon fuskana, a sannu ya kai hannun shi kan fuskana. A hankali na bude idanuna, muka zubawa juna ido. Hura min iskar bakin shi yayi, na kumshe idanu na.        "Yan mata! Meye na kwanciya haka? Ko baki son Saif ne?" Lumshe idanuna nayi tare da mai da kaina cikin matashin, murmushi yayi sannan ya kuma tab'a wuyana, zuwa kirjina da yake bugawa.             Kallon shi na kuma yi, kafin na janye hannun shi daga jikina, a hankali ya zare rigar jikin shi, bayan ya cire aninin rigar shi, sannan ya janyo ni jikin shi tare da had'a jikinmu. A hankali yake zame min rigar jikina.             Cikin sauri na d'ago kaina, tare da kallon shi, sunkuyar da kaina nayi. Sumbatar goshina yayi cikin jin tausayina, yana shafa bayana.                        Rabani da rigar jikina yayi sannan ya ja bargon ya rufe ni, sannan ya shiga ban daki ya haɗa ruwan zafi tare da dauko karamin tawol ya fito dashi. ...... Yazo ya shiga goge min jikina, tare da kallon jikina. Yana goge min wayar shi tayi kara, dauka yayi tare da sakawa a kunne, sannan ya cigaba da magana yana goge min jikin. Cak ya tsaya. "Muniba! Idan kika Kuskura kika min rashin hankali, wallahi idan na dawo sai kin koma Canada, ina gaya miki."        Shiru yayi tare da wurga wayar saman gadon, sai da ya gama goge min jikin sannan ya dauko abincin ya fara bani, ina yunkurin amai, dole ya mike tare da fita.              Can ya kuma dawowa, ya sanya min ruwa sannan ya ajiye min sauran maganin da zan sha, kafin ya kalle ni, barci na shirin dauka na, yace. "Bakin ce min wawan Yaro ba? Ki shirya daren gobe zamu raba reni!" Daga haka barci yayi gaba dani.    Ban farka ba sai karfe uku, lokacin har an gama tattara min kome nawa, sannan aka fita dashi.         Ina tashi na wuce ban daki nayi wanka da alola, dakyar nayi sallah, ina idarwa na shiga ɗura abincin kamar wacce ta shekara bata Ci ba.           ---- Tunda ya gama kula dani, ya isa gurin abokan shi, ya uzura musu lallai su wuce Daura, bai tab'a jin son kusantar matan shi ba, sai yau da ya goge min jikina, anan yaji lallai ya dace da zama angon gaske.       Tunda suka biyo jirgi suka nufi Daura, yake ɗokance da Husnah dan baya ta Munih.      Koda ya isa, ya sami gidan a cike mutanen borno sun zo, masalaci ya nufa yayi sallah, sannan ya nufi gidan shi, kiran Husnah yayi suka shiga shashin sa.       Hmmm! Sai da ya zama angon gaske sosai sannan ya fito, suka haɗu da Munih zata shiga dakin shi ya dakatar da ita.              "Zan shiga naga Uwar me..." Buge mata baki yayin sannan ya nuna mata hanyar fita. "Allah zai saka min!"     Bai kulata ba yayi ficcewar shi, tana ganin ya fita, ta shige dakin shi, taga meke faruwa. Aikuwa hango Husnah tayi tana barci tare da sauke ajiyer zuciya. Tsaki tayi tare da barin d'akin. Kamar ta fashe da kuka.               ........ Yau jikin shi yake a nitse, sabida yaji abin da kowa yake ji, wani gani gani yakewa abokan shi.     .--- Hudu aka shiga dani shashin Umman Baabi, tayi min nasiha akan zaman aure shiru tayi bayani akan rayuwar aure da ma'aura, musaman yanda aure ya koma a wannan zamanin, Da tazo magana akan Matar So, kuwa har wani take tayu musu... MATAR SO SUNANE DA KOWACE KE SON AKIRATA DA SHI . Babban gishirin Zaman aure Wanda zai kaiki da mallakar zuciyansa tamakar kin wanke kin bashi ne. 1.Hakuri, 2 .juriya,. 3. ladabi da biyayya. Sai kin jure Zaki Iya hakuri Sai Kuma kinada hankuri zakiya may Ladabi da biyayya. Babban makamin mace agidan miji Kuma sune ADDUA ADDUA ADDUA DA MIKA LAMARINKI GA ALLAH. *BABBAN HANYAR MALLAKA KUMA* 1. Iya girki (ba indomie ko spaghetti ba nope 2. Iya sarrafa Shi a shimfida (Iya jima'i) karki/ka zama lusari 3. Iya Magana. Kisan irin kalaman da Zaki dinga furtawa. Iya mu'ala da mutane. Yin adalci kyautata zato da Kuma yin uzuri. Ta cigaba da cewa. "A wannan zamanin iyaye muna sakaci da yawa yarinya ta girma har tayi aure baki nusar da ita rayuwar aure da rayuwar da zatayi anan gaba ba, maxan ysnzun basu damu da ki musu, wani abin azo a gani matuƙar zaki riƙe girki iya sarrafa harshe, ya sarafashi a gado, mutunta danginshi maida damuwarshi naki, ki kambama alamarinshi fiye dana kowa, Karki ce ya cika fushi ko yana da miskilanci a'a ke zaki koya mishi sakewa dake dakuma sauran mutane, Matar fari itace ke fara lalata alamarin namiji duk yanda kika ɗaurashi haka zai mike, sannan akwai kura kuran damuke aikatawa, rashin yin kwalliya a gidajenmu sai zamu fita unguwa, zan muku misali dani kaina, na zauna a cikin gidan nan dadda tun kuruciyar mu har girman mu ko jagira banyi nafita dashi toh waye zanwa a waje ? bayan ina da wanda ya ajiyeni namishi,! wannan ɗabi'ar tasamu mazauni a cikin zukatar Yarana baki ɗaya, idan mace takai mace kuma ta amsa mace babu malamar da zata zauna da ita tace mata ga yanda zatabi da namiji, sabida rayuwarshi kamar na ɗan shekara uku ne, da zaran ya tada rigimar shi, sai ki duba dabi'ar karamin yaro ki gani, da zaran ya fara kuka zan faɗi a kasa yayita shureshure, a lokacin zai baki haushi kaman ki jibgeshi amma idan kika tuna da, cewa kukanshi kara miki zafin kai zaiyi, niman alewa ko wani abu zaki fara dan ku rabu lafiya, Toh namiji ma haka yake shi bazai faɗi ba, amma zai koma gefe yayita huci idan kina da wayo, a lokacin sai ki saukar da kai ki bashi hakuri, idan kika ga yaki sa shi a gaba kita rarrashinsa, wanda idan kinga zaki iya saka mishi fitinanne kuka shi akawa laifin tuni zai manta da wani rigima ya sauko, toh a lokacin sai kiyi amfani da damar haka ki bashi hakuri dan zai damu shi akawa laifi ke kuma kike kuka, Mata muna da matsala a rayuwarmu sosai bazamu iya rarrashin miji ba amna zamu iya rarrashin mai saida ɗan kunne dan yayi mana sauki,, haba mata ina hikimar tamu take ina kwarewar tamu take, tunda Asiyah ta iya bawa fir'auna shawara ya ɗauka waye ne mijin naki da bazai ɗauka ba, Ummu Salma an karɓo daga gare a hadisin da buhari da musulin suka rawaito. Tace manzon Allah yana zama yayi shawari dasu, akan alamuran addini ko, kuma wani yaki, indai manzon Allah zaiyi shawara da matarshi ke wacece da bazaki bawa mijinki lokacinki ba, ina kira gareku mata yan boko karki ce aiki ya hanaki kula da miji, zakiyi kuka nan gaba idan ya auro undergrad, kina ji kina gani zai, mai dake gefe ya saka wancar a gabanshi idan bai yi haka ba toh yar aikin gidanki da kika bar mata gidan ita zai aura, idan mai tunani da tsoron Allah kenan idan kuma aka rasa haka, kina ji kina gani zai na bin yar aikinki suna masha'arsu, ko kuma yaje waje nima, wallahi muji tsoron Allah, wai tsabar rashin daraja a gurin mace mijinta zai raba gurin kwanciya da ita, sabida tana wari da hamami, wai nikam mi kuke shirin zamane matan arewa, tun a gida zaki koya mata gyaran jiki girki tareraya, iya magana, sabida sha'anin rayuwa baki san inda xata zauna ba, amna ina sai dai ki koya mata shan maganin mata, karki manta kishiyoyinki can yayi kyau amma rayuwarta ba kyau, wannan zuri'anmu guda biyu ɗaya take cewa. "Ana surutun Aanih ta lalace, abinda da wasu yaran suke a cikin Zuri'ar waye ya isa ya faɗa? Ko su da suke auren wani kwanciyar hankali suke samu da ake mata gorin taki aure!. Abin tausayi, sai nayi murmushi sannan nace musu suyi hakuri, Fatimah karki manta wacece ke? Shin idan kika zauna lafiya a dakin ki, hankalin waye zai kwanta? Idan kika kaso auren ki suwaye zasu miki dariya Da haka nake miki nasiha ki gyara rayuwar aurenki kija mijinki da danginshi a jiki wani sabon salo wai kuna kiran iyayen miji da ulcer ko hawan jini, a'a kuskure ne, ke zaki rushe dangantsrku ke zaki gini, ina da suruka, naki na saka ido akanta da mijinta, ina da yara mata baxan so nimaa cutar min dasu ba, akan Yan ukuna zan kwaɓe hijab da rigar malamta na gurzawa surukina rashin kirki, dan ni nasan abinda na bashi, idan yace min bata da kunya shi xan fara tuhumq kafin na tuhumeta, sabida karfe ɗaya baya amo sai da wani a kusa da shi, karki manta shi tashi Uwar bata raye sai mahaifin shi,.da matan Ubanshi. Sannan zaki zauna da yara ƙanana masu karancin shekaru irin naki, shi zaki zauna ki biye musu ne kuyi ta abin kunya, kin san waye mijinki, dan akan laifin mari kawai ya iya wargaza miki lissafi toh idan kuwa haka ce Tabbas idan ya birkice miki zaki iya dakatar dashi. Toh dole kiyi amfani da shekarunki, na farko kija girman ki, na biyu ki zauna lafiya a dakin mijinki koda kuwa matan shi suna tsaye akanki, zaman shi suke zaman shi kike, ke baki isa koran su ba, haka kema baki isa koran shi ba. Akan me zai saka ki d'aga hankalinki. Fatimah Aryaan yana bukatar ki nutsu a dakinki, yana bukatar hakurin ki, hakurin nan yake bukata, shi yake son kiyi! Ana ce muku... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *Ba a yi ciki dan tuwo kawai ba* Dole kiyi hakuri da shi sabida kin fishi shekaru, matan shi kuma kusan kanen ki ne, shima din haka, duk wanda ya ce miki zaki yi aure dan jin dadi yaudarar ki yayi, domin ita rayuwar auren domin hakuri aka gina ta. Dole harshen ki ya zama yana tafiya da kamaninki, ki zama wacce fuskarki bai tab'a nuna damuwarki ba. Karki bari abokan zamanki su fahimci ma'ana fuskar ki, ya taimakawa kanki gurin, adana damuwarki, domin ita ce hanyar da zata kawo zai iya amfani dashi dan cutar dake. .... Gidan aurenki ki zauna koda kuwa hakan yana tab'a ki, Allah yana sane dake, sau dayawa muna ganin dan ana cutar mu, zamu iya kwatar kanmu. Hmm ba haka bane, idan kika fito an cutar dake wanda zaki aura me zai miki! Karki zama macen da bata san meye ke damunta ba, domin yin haka tankar tallata kanki kika yi, idan kika zama haka toh ko ruwa baki isa sha ba, mijinki yarone eh kar haka ya baki damar da zaki rena shi. Domin duk wani abinda ya dace na hakkin shi yana wuyarki kuma dole ki bishi. .zaki ga abin da ranki baya so, amma ki gani da idanunki toh ki zama makauniya, ki zama kin ji amma ki zama kurma, kar ki yarda dangin shi su zarge ki da mara hakuri, ki zauna kiyi hakuri domin su akan kansu zasu yarda kinyi rawan gani. . masarautan cike take da kalubalen rayuwa, amma dole ki zama macen da tasan darajar kanta da kuma mijinta. Duk abin zaki yi a rayuwa ko nime taimakon Allah, ki kuma kiyayye abinda Ubangiji yace, karki manta Allah yana sane dake, da kuma sauran mutanen baki daya, karki yarda Shi kan shi ya fahimci baki da'a domin yin haka tankar zubda kai ne. . Rayuwar aure kamar littafi ne,har ki gama rayuwarki ba zaki tab'a karance shi. . Kalubalen rayuwa kin gan shi, kuma har yau akwai mutanen da basu yi fatan ki zauna lafiya. Ban gaya miki don ki zaka a ranki ba a kaunar ki a'a na gaya miki ne dan ki fahimci wani abu a rayuwa. Za a ce miki mijinki yarone! Eh kin yarda yaron ne. Akwai masu fatan niman hanyar da zasu sami irin shi ma babu. Sau dayawa kowa yana jin yayi Sa'a, amma mafi girman Sa'a ita ce Ubangiji ya baka hakuri da juriya irinta rayuwa, Idan kika saka Allah a cikin lamurran ki, wallahi babu wanda ya isa ya cutar dake ba tare da Allah ya kawo miki ɗauki ba, idan kika dauki dangin shi da iyayen shi babu abin da zai miki Allah bai saka mishi ba. Karki yarda ki cuce shi ko abokan zaman ki. Ita Sakayya a duniya ake yinta, dan haka idan kika yarda da Allah babu wanda ya isa ya miki haushi ki kula shi, Ubangiji baki zaman lafiya! Ki ga dai yadda Allah ya tsara miki rayuwa kiyi hakuri, Allah yana tare dake. Kuma rike wannan Alqur'anin, tare da duk wata azkar, Ubangiji zai zame kawo miki ɗauki a duk halin da kike. Tashi ki tafi Allah ya miki albarka yasa kin tafi a sa'a." Kasa tashi nayi ina kuka kamar raina zai fita, saboda ba a tab'a min nasihar da ta shiga cikin jikina da rayuwata irin na yau ba. Ba a tab'a gaya min meye rayuwar aure da hakuri irin na yau ba, har muka fita daga falon, kuka nake ina jin wasu na kus-kus akan nasihar da Umma tayi min, wai tana gwada fifiko akan jikokinta, tafi sun Yaran Hammah Aaryaan. ...... Tunda naji haka na saka a raina, zan zauna da Jay tsakani da Allah, kuma zan bawa dangina mamaki. ... Ina jin ana wurga min magana, ban kula su ba. Karfe shida muna sauka a Katsina, daga nan muka wuce zuwa Daura, sai magana suke gaya min, kasa kasa. Har muka isa gidan sarautan. Tun daga bakin kofar masarautan ake karban mu cikin mutumtaka, har muka shiga cikin gidan, aka fidda ni a sanyayye nake takawa. Shashin sa dake sama aka wuce dani, yayinda Munih da Husnah suke shashin kasa. . Bayan mun yi sallah magarib muka shirya aka nufi gurin walimar da aka shirya mana, tare da yan uwana, tare da dangin shi. Kaina a sunkuye rufe da mayafi fari kal. . Karfe goma aka tashi, ko ta kaina bai bi ba, ya nufi inda abokan shi ke nan, suka yi sallama. --- Tunda muka dawo naji wasu na cewa Munih tayi musu rashin mutunci, sai mita suke Ni dai ban ce musu cikanku ba. Washi gari. Aka yi wuni da sannan yan uwana suka tattaro kayan su da Alkhairin da aka musu, suka dawo Sokoto suka bar ni bayan sun gama gaya min cutar dake ran su. ..... Har dare babu ango babu alamar shi, sai kusan asuba, Ina kwance naji ana buga min kofa, na tashi na bude naga fuskar Munih ya kumbura saboda kuka.. "Mayya dama an gaya mishi cewa ke din Makara ce, shine daga zuwa zaki kashe mana miji, toh Tabbas zaki bishi inda ya tafi dan bazamu cigaba da kallonki ba." Kawai ta d'aga sabuwar wukarta zata soka min na farka tare da tashi zaune, juyawa yayi ya kalle ni tare da harara na, ya juya yace. "Kema sai kace yarinya karama. Kin kwanta babu addu'a, ba dole ki farka da ihu ba." Ajiyar zuciya nayi tare da kallon agogon dakin karfe shida da arba'in da biyar komawa nayi na kwanta ina kallon shi yana gyara zaman rigar shi nace mishi. "Shine baka shigo da wuri ba, ko farkawa ban yi ba sai yanzun." "Baki gajiya da magana ne?" Sauka nayi a gadon, ina kallon shi nace. "Ina zan gaji! Wai kai ne mijina?" Juyowa yayi hannun shi a kirjin shi, yana kallona. "Nayi karami ko?" Juya ido nayi sannan na wuce ban daki ina ce mishi. "Toh me zance bayan ka bawa kanka amsa" "Famkan famka bata kilishi! Buleliya!" Ya gaya min, ban samu bashi amsa ba, sabida na shiga ban daki. Ina fitowa na samu yar karamar takarda. _Mun tafi rakiya abokaina!" Kirga rubutun nayi ina murmushi, kome na shi baya wuce iya ka. Sallah na gabatar sannan na mike na shiga gyara dakin, kafin wani lokaci gidan ya dauki saiti domin na saka turare lungu da sako na gidan. Lokacin da na gama na shiga wanka na fito na caɓa ado cikin riga da zani na lace, bayan na zauna na buga kwalliya na fitar Hankali, ina gamawa yan Maiduguri suka zo min sallama,. Jikina yana rawa. Na shiga kawo musu kayan Gara, tare da duk abinda hannuna ya kai kai. Na shiga d'akina na duba kayan da aka kawo min na aurena, na kwaso wasu kayan kwalliya, tare da turarruka, sai wanda Baabina yayi min na kwaso na zuba a jakar da Hanisah ta kawo min na bikin mu. Sai da na fito dashi naji suna cewa. "Aha ashe kunyi jaka ne, Wallahi kunyi kyau." Duba hoton nayi ina tsaye a saman shi, na zuba hannuna a kafad'arshi ina dariya shi kuma murmushi, kasa magana. Nayi toh yaushe aka yi wannan hoton. "Kun dace sosai! Dake da Abbalawan, gashi yafiki cika ido. Don Allah ki rike shi da amana, Maraya ne da ba a yi tsammanin zai zama mutum ba, Yaron da aka ciro shi cikin Mahaifiyarshi ta rasu, ai kinsan Allah ne ya nufa zai yi nisan kwana. Fatimah gashi nan don Allah karki bari wasu su juya miki tunanin a kanshi idan yayi miki laifi mu zamu hukunta miki shi. Kina da daraja a cikin Zuri'ar shehun Borno, dan haka ga Maiborno ki rike mana shi da amana." Inji dattijuwa, kunya ya sani sunkuyar da kai, koda na bawa Jannart kayan su, kasa magana suka yi sai godiya suke min, da zasu sauka na raka su, sai da suka ce min na koma cikin gidan, sannan na juya. Ina shiga cikin gidan na hango Munih tana tsaye da wasu kayan fitsara. Ban kula ta ba, har zan wuce tace min. "Guzuma! Ke ko kunya baki ji ba. Yaro karami kika nacewa dan bakar fitina, toh wallahi sai na hanaki zama a cikin gidan nan, dani kike zancen." Murmushi nayi a hankali nayi wuccewa ta, sabida bani da lokacin ta. "Tsohuwa kawai, sai da kika gama yawon dandinki kika makalewa mijina." Ko a jikina. Fitowar Husnah sanye da doguwar rigar, ta kalle ni ina haurawa tace min. "Addah Aanih ina kwana? Ya bakunta?" Fuskarta cike da fara'a. Cikin jin dadi na tsaya muka gaisa nace mata. "Alhamdulillahi, Yayar mu ya aka ji da jama'a." Dariya tayi sannan tace min. "A'a! Duk wacce namiji ya kwana a d'akinta itace uwar gida. Ke kuma Ya Jalal ya fara kwana a d'akin ki, dan haka kece uwargidan." Murmushi nayi sannan nace mata, "A'ah." "Toh munafuka, uwar shishigi kwala kai a faranti ince shekaranjiya ya kwana dake! Kuma kice itace uwar gida, bana son kinibibi, sai na zagi mata." Wucewa nayi d'akina, Husnah ta wuce kicin domin niman abinda zata ci, kai Munih yar Bala'i ce. Ina kwance sai ga Jannart tare da kayan abin karyawa ni da Jay, tashi nayi na amsa, sannan na ajiye a gurin cin abinci, sannan na zo na zauna ina kallon ta,sai murmusawa take nace mata. "Mamanmu! Meke saki dariya." "Daga karshe dai Ya Saraki ya mallake ki, ji nake kamar yafi kowa dace." "Toh uwar yan gulma, ina abincin mijina." Babu wanda ya kulata ta nufi gurin abincin zata diba. Rumah ta shigo cikin b'acin rai tace mata. "Wallahi kika tab'a sai na sab'a miki wato ke mara kunya ko? Sai kin sha mamaki, mara mutunci kawai idan ke aka kawowa sai ki ci yar Banza, kawai." Dake tana tsoron Rumah kuma yayar miji dole ta hakura. Ta fita tana tsaki. Nan muka sha hira, har Husnah ta shigo muka Cigaba da hira, kafin ta fita sabida yan uwanta da suka zoe. Ranar anan muka wuni, sai yamma likis ya shigo tun daga bakin kofar ya zuba min ido, suka zaune. A sanyayye na mike na amshi kayan hannun shi tare da ce mishi. "Barka da dawowa, Saraki." "Hmm! Na same ku lafiya," wuce mishi da kayan nayi can d'akina, ina faɗin" Alhamdulillahi, sannun da dawowa." Daga nan na kai kayan na dawo na durkusa na fara warware mishi igiyar takalmin shi, ina murmushi tare da ce mishi. "Amma yau kasha hanya." "Hmm! Bari ke dai" A hankali ba nufi kitchen, na duba abincin da muka yi d'azun yayi sanyi, ruwa na kawo mishi me dan sanyi, na kawo Mishi, sannan nace mishi. "Kayi hakuri, abincin yayi sanyi. Me zan dafa maka domin." "Ki bani tea da kayan fulawar nan, zanci dan hanci abinci ba." . Da sauri na nufi kitchen na hada mishi shayi me kauri, nazo mishi da ita da kuma kayan fulawa, sannan na nufi kicin din na daura mishi, dafa dukar makaroni, tare da kayan kamshi, kamar ance min na bude firij din tsaye naga bakar leda a kunshe, buɗewa nayi naga kaza gashashe. Dauka nayi na zuba mishi ruwan zafi, sannan na wanke na zuba a cikin abincin. Sai da na tabbatar abincin ya hau wuta, sannan na fito na nufi dakin shi na hada mishi ruwan zafi, na juya zan fita daga ban dakin, muka yi kawo dashi. Ya tsare kofar fita. "Don Allah bani hanya na wuce, na bar abinci akan gas." Jingina yayi da jikin kofar, yana faɗin. "Taimaka min nayi wanka." Ware idanuna nayi akan fuskar shi, shima kuma ya ware shanyayyun idanun shi akai na, yana kallon cikin ban dakin. Tare da narke min kamar wani karamin yaro. . sunkuyar da kaina nayi ina wasa da hannuna, shigowa yayi tare da mai dani cikin bayin, sannan ya rufe tare da jingina da kofar. "Zahrahhh!" Ya kira suna na a sanyayye tare da jan sunan. Tsigar jikina ne ya mike, na d'ago tare da zuba mishi ido, wata irin kasala tana sauko min cikin kankanin lokaci. "Kiyi min wanka." Gyada mis..... #Mai_Dambu.... 10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *Iya ruwa, fidda kai..* Gyada mishi kai nayi tare da komawa cikin bayin, takowa yayi har gaba na, na d'an ja da baya, ya kuma matsowa na kuma ja da baya. "Ba zaki min bane!" Muryana yana rawa nace mishi, "Ban tab'a yiwa Babba wanka bane"       "Yau zaki fara." Had'iye yawu nayi, tare da zare mishi idanu, sai da muka dangana da jikin bangon sannan ya saka hannun shi yayi dafe bangon tare da kallon fuskana.     Sunkuyar da kaina nayi ina me matukar jin kunyar yadda muke tsaye, sai da ya Bari kaina na kasa kawai mutumin nan ya kuna ruwan me bala'in sanyi ban san lokacin da na d'ago da sauri. Jin labben shi akan nawa ya sani jan wani irin numfashi, tare da kallon cikin idanun shi.           Lumshe idanun shi, yayi tare da cigaba da abinda yake yi, na rasa me zanyi dan na dakatar dashi ga wata irin bugun da zuciyata take.            Duk mun jike sosai, a sannu ya shige jikina, ban dawo daga inda yake shirin kai ni ba, sai da naji yana zuge zip din rigar jikina, ban san lokacin da na hada karfina guri guda ba, na ture shi. Tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.   ...sannan nayi mazan zan fita daga ban dakin ya kuma riko hannuna, yana murza min, ya janyo ni ta baya, tare da rungumo ni. "D'azun tambayana kika yi fa!"       Juyawa nayi na kalle shi tare da rasa abin cewa. "Kin ce Yaro dani!"           Yana fadar haka, tare da zare min rigar zuwa kasa, kallon shi nayi na kasa magana, mara kunya sai shagalin shi yake kawai, kamar ba shi yace baya kaunata ba.             Sake mishi nayi ya gama bada himma da abin da yake shirin min, kawai nayi maza na ture shi tare da fita daga ban dakin, tsayawa nayi na nemi wata karamar tawol na rufe kaina, na fita daga dakin shi.     Ina zuwa falona na samu duk basa nan, da sauri na shiga kitchen, na samu an rage min wutar girkin tare da ajiye min yar karamar, laida aka ce min. _Daga Rumah! Asha soyayya lafiya a jiyar da Kanin mu dad'i na musamman, sannan ga wannan a dama a sha da madara, don Allah a yi hakuri da Kanin mu kar a mishi bulala_ Kunya ce ta kama ni, kamar tana gaba na, haka na gama abin cin sannan na juye zan fita na gan shi ya fito yana digar ruwa, kwantaccen gargasar jikin shi yayi luf..   .... Haka kawai naji ina shakkar shi, bawai dan kome ba, sai dai idan na duba yadda yake tsaye a gabana, daga shi sai yar tawol a k'ugun shi, tawowa yayi tare da matse ni da jikin firij din tsaye, rintsa idanuna nayi tare da kai hannuna biyu kirjin shi.         Shigowa kicin din aka yi duk mu biyu muka juya tare da kallon Muniba, ni kallon tsoro. Jay kuma na b'acin rai. Da sauri ta fice, garin na ture shi naji abu ya sauka a kan kafana, a firgice na leka! Sai dai kash (🤦🏽‍♀?) idanuna sun yi mugun gani.      Numfashi na da wata irin tsoro ne suka kama ni lokaci guda, na ture shi tare da guduwa d'akina, ina sauke hakki.   Rufe kofar nayi naki bude mishi, kamar zanyi kuka. Yau naga abin da ya dame ni, ina jin fitar shi nazo na saka mishi abincin shi sannan na koma dakin naki fitowa, har ya gama ya shirya ya tafi cikin gidan.               ..... Da dare da wuri na kwanta, ina cikin barci ne ya shigo dakin, tare da haurawa saman gadon, ya kwanta bai tashe ni ba, sai ma shigewa da yayi min, ban sani ba sai can cikin dare naji kamar ana min wasu abubuwan da ya sani bude idona cikin barci na sauke akan shi, wani irin bugawa kirjina yayi tare da zare idanuna.    Zan mike ya kuma matse ni, dole. Ayi shiru, jikina yana rawa.        "Jay!" Na kira sunan shi. "Babu abinda zan miki;" ya faɗa min a takaice, tsabar tashin hankali kasa yarda nayi, kawai ina jin shi yana kai Gwauro ya kai mari, can da naji yana shirin wuce gona da iri, kawai na sake Mishi wani irin kuka, har jikina yana rawa. Kuna wutar dake jikin gadon yayi, tare da kallon fuskana wanda nake kuka sosai.              Hannun shi cikin rigar barcina, sai shagalin shi yake. Sai da ya gama abinda yayi niyya sannan ya janye daga jikina ya juya min baya, yana jin na sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi sannan yace. "Fatimah! Ban miki kome ba fa". Share shi nayi, na cigaba da  kwanciya na, zan iya cewa Barci barawo shi yayi gaba dani.         Ban farka na sai da gari ya fara wayewa, shima Bugawar da Munih take ya sani, bude idanun mu.        Gani na nayi na baje a jikin shi na wani nad'e shi kamar zan shige cikin shi.     Kallon kyakyawan fuskar shi na zubawa ido, ina girmama kyan shi da tsarin shi.    "Malama! Ido guba ne!" Ya gaya min, cike da kunya na janye jikina da fuska na zan sauka daga gadon, ya rike ni. "Yau mun makara" gyada mishi kai nayi.. "Jin ki da nayi a jikina, ya sani jin wani karsashi, ko zaki." Da sauri na sauka a gadon na nufi ban daki, nayi wanka da alola, ina cikin alolaya shigo min          Mai dani yayi cikin nutsuwa muka yi wankan tare da naga zai cire yar karamar wandon shi na, yi maza zan fita dan ban shirya ganin abinda ya turewa buzu nadi ba.    Karshe dai dole ya zauna a cikin bayin na fito na barshi a gurin.     ..... Ina shiryawa ya fito, jallabiyar da ya shigo da ita jiya ya dauka tare da jan mu Sallah,bayan mun idar ya, shiga tambaya nayi sauka ko banyi ba. Wata uwar hararar da nayi mishi sannan na nufi kitchen, na daura abin karyawa. Ina kitchen ɗin ya gama kwanciyar shi ya kuma fitowa, ya zo ya rungume ni ta baya, muka Cigaba da aikin mu amma a takure nake, can dana gaji da abinda yake min kawai na ture shi tare da koran daga kitchen ɗin na gama aikinsa, sannan na zubawa Mamah tare da na sauran matan gidan namu.          Na kawo na mu, da shi na ajiye sannan na koma kitchen ɗin na gyara tsaf, kafin na kuma fitowa na shiga wanka na gyara jikina tare da ɗaukar kwalliyar daukar magana, riga da skirt. Irin me tsagun nan ta baya, sai rigar da aka dinka gabanta a kwai tsagu har tsakanin kirjina, dake rigar anyi irin (breast cap) aka mishi ban saka (bra) ba nayi shiri na tsaf, sannan na fito ya same shi yana tsaye da tawol kamar wani abu, kallon juna muka yi sannan na kauna da kaina.    ."kai kuma meye haka?" Na tambaye shi, "Muje ki taya ni Niman kayana.". Yana gaya min na fahimci renin hankali a maganar shi, amma ban damu ba, na bi bayan shi, mutumin da ya gayyato ka niman kayan shi, sai gashi ya buge da min shirme. Dakyar ya barni na dauko mishi kayan shi.        Ko tsayawa ban yi ba na fito, ina jin kamar zuciyata zata buga, daga jiya zuwa yau kirjina har ciwo yake min, gashi bai san kunya ba, duk abinda zai yi kai tsaye yake aikatawa.         ..... Yana fitowa ya same ni, ina jiran shi, kallo na yayi sannan ya zauna yana kallon yadda nake zuba mishi abinci jikina yana rawa.           Rike hannuna yayi a hankali ya shiga zuba abincin sannan yace. "Jiya kika ajiye min abinci kika yi tafiyar ki!"    "Kayi hakuri ba zan kuma tafiya ba." Gyada min kai yayi, sannan na shafa gashin kan shi ina murmushi, zama nayi muna cin abinci muna d'an tab'a hira, har muka gama. Sannan yaci sosai. Daga nan ya mike zai fita na dauko gyalena, tare da amsar jakar kayan da zai fita da ita. "Saraki! Ko zaka d'an kira min Jannart!" Juyawa yayi tare da zuba min ido,  ran shi a b'ace, a rude na shiga tambayar shi. "Wa kika ce na kira miki?" Take sunan da na kira ya fado min a raina. Sunkuyar da kaina nayi sannan nace. "Ka kira min Ummul khair." Takowa yayi gabana, sannan ya riko hannuna yana faɗin. "Sunan Mahaifiyata ce da ita! Don Allah ko a wani gurin karki kuma kiran sunan nan haka" ."Insha Allah!" Nace mishi, har kasa na rako shi, ina kallon Munih ta tare shi na mika mishi jakar shi zan dawo daki ya riko hannuna. "Jay! Ka dai sannan ban iya girki ba, kuma naga alamar zaka kashe ni a gidan ka, dan haka ka nima min abinda zan ci ko kuma wannan guzumar tayi girkin da nayi." "Wuce ki koma, zan turo miki da Noorie din." .yana gama gaya min haka, na juya da sauri shi kuma ya riko hannun Munih, ban san ya suka kare ba, sai dai Karamah tazo ta amshi kayan abincin ta kai cikin gida.    Can ina zaune sai ga Mamah Sarah da Mamah Raihanah, sun shigo,  ina kwance Husnah tazo ta kirani, har na canza kayana zuwa doguwar rigar material.             Babban mayafi na yafa, sannan na  fito, na same shi a falon shi na kasa, ashe har dashi. ...    Cikin jin kunyar su na gaishe su, sannan suka amsa suma cikin fara'a, sannan suka yi shiru. Kafin suka hada mu suka mana nasiha sosai. Sannan suka kuma tambayi Munih abinda ke faruwa. Kai yarinyar nan bata da kunya, dan a cikin abinda bai fi minti goma ba. Ta fadawa su Mamah wai bai tab'a kusantar ta ba. . Sannan ya kusanci dukkan mu, amma ban da ita. "Kuma yasan ban iya girki ba,sai wancar guzumar ta girka mishi ya cinye ya hanani, wallahi ba zan yarda ba. Tunda Husnah ba bani nata zata yi ba. Ina laifi ita wancan babbar banzan ta girka dani." "Ai kin san zamanki nake da zan girka abinci na baki, toh bani Husnah Umar ba."          Kai na a sunkuye suka shiga rashin mutunci a gaban surukan su.      Zai magana Mamah Raihanah ta dakatar da shi. "Aanih ko Husnah ba bayinki bane? Suna iyaye ne suka haife su, dan haka ki mike ki shiga kicin ko koyi abinda zaki dafawa cikin ki, kuma idan kin san kin auri Jalal dan ki d'aga mishi hankali ne, ki gaya min yanzun na saka shi ya sake shi tunda ke baki san yadda zaki zauna dashi ba.mara kunyar banza da na wofi.    Ke gaki me baki, kin zagi Aanih a gaban mu, kin san yadda muke da Ubanta, sannan Husnah da kike gani Ubanta kanina ne, dan haka ko shiga hankalin ki, ko a tura ki inda kika fi wayo. Sakarya kawai. Wallahi koda wasa naji wata ta kuma cutar da dayan ku, sai ba baku mamaki. Aanih kiyi hakuri. Kece babba a cikin su dole zaki yi hakuri da halin kanenki, sannan ki rike su da zuciya daya." Nasiha bayin Allah nan sun mana shi, sannan zasu mike Mamah Sarah tace min. "Sai ga abin karyawa, muna shirin kawo miki."    Murmushi nayi, tare da wasa da hannuna nace mata. "La babu komai." "Allah yayi muku albarka!" Daga haka suka fita har dashi, Ni kuma na koma d'akina ina me shigewa kitchen na shiga ƙoƙarin daura na rana, ashe wai kai karar shi Munih tayi ya make ta, ina wanke  tukunyar da zanyi amfani da shi, naji ya rungume ni ta baya, yana lasar wuyana zuwa kunne na, da sauri na ture shi ya sake murmushi yana cewa. "Nazo da cefene, sauko ki raba muku!"    Zuba mishi ido nayi kamar zance a'ah yadda ya narke min sai naji babu dad'i. "Toh ina zuwa." "Don Allah muje!" Haka na bi bayan shi tare da samun kayan abincin a shirge a gefen falo, ina gani ya wuce kowani bangare ya fito da su, akan idanun su na raba kome Dai-daiton yadda zai musu.            Amma uwar marasa kunya tace min.. "Kwai da kika ajiyewa kowa kiret uku, ai raba shi zaki yi a kirge." Buge mata baki yayi sannan yace min. "Kaji ba sai kin raba ba, kowa ya dauki haka daya. Haka kwalin kifin da namar ma kowacce ta dauki ledar gabanta,kayar miyan ma haka, tunda Aanih bata iya rabo ba.. Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu 10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Baya bata zani* "Daga yau babu wacce zata kuma muku rabo, wallahi Munubiya. Idan kika kure ni."    Daga haka ya juya ya fice abin shi, ina kallon yarinyar nan tasaka kafa zata taka min kwai, Allah ya taimaka sai ga Jay, ai kuwa ran shi ya b'aci, sosai dan tun daga bakin kofar yake falla mata mari, nima da naje kwatar ta, sai da ya ture ni na fadi, na buge gwiwata.      Ran shi ya b'aci, sosai. Ganin yana shirin illata musu yar mutane, Husnah ta fita da sauri. Zata cikin gida ya daka mata tsawa, tare da cewa. "Wallahi kika bar Bakin kofar nan kin tafi kenan." Bai da hankali, akan haka zai iya sake mace, mari kawai yayita mata, sai da fuskar ta ya kumbura sumtun, sannan ya fita ya bar mana gidan, kowacce taja tsimar kafarta tayi shashin ta.                Karshe bata dauki kayan abincinta ba, ta bar mishi a gurin. Da ta dawo yagan su a gurin bai mata magana.       Dan haka ya kwashe kayan baki daya ya raba mana, ya kuma buga mana kashedin kar mu bata abincin, haka bai min ba, dan haka nace mishi. "Ba zai yiwu ba, sabida hakkinta ne da yake kanka, kuma dole ka sauke, kai kana jin cewa zaka zauna ne cikin farinciki babu tashin hankali, ai kasan haka ma ba zai faru ba."        Bayan mun gama magana, bai ce min kome ba ya ficce. Can sai ga Fulani Balkisu tazo. Ganin yadda fuskar Munih ya koma ta sakata a gaba suka nufi cikin gidan.     ...... Har falon Abba suka nufa, ta zauna a kujeran dake kallon Abba, Fulani Nanah da Yahanasu suna zaune. "Yallabai! Kaga abinda Jalal yayiwa Munubiya! Don Allah kalli fuskarta! Idan baya sonta babu dole, meye na duka kuma?!"      Shiru yayi sannan ya kira, Jay yace. "Kazo nan!"     Bai jima ba, ya isa falon ya nemi guri ya zauna. Tare da sunkuyar da kanshi.    Shiru yayi yana sauraron abin da Abban shi kece mishi. "Babana! Yanzun a matsayin ka na me hankali meye Munih tayi maka haka."   Kasa magana yayi, sabida bai taɓa tsammanin zasu iya kawo karar shi ba. "Afwa Abba" Nan Fulani balkisu, ta shiga faɗa  kamar me, Abban shi ya zuba mata ido, shima jay din bai magana ba, har ta gama masifar ta tayi shiru dan kanta. "Toh kaji abin da kai mata don Allah ka zauna da matan ka lafiya mana."   Duk laifin na shine, sannan Abban shi ya sa shi ya mai da mata abincinta da ya raba, bai ce mishi kome ba, da zai bar falon ya bawa Abban shi hakuri sannan ya bar musu falon. Nan itama suka bar falon da Munih, inda tayi mata alkawarin sai ta samo mata kan Jay duk bala'in taurin kan shi. Sannan ta kuma ce mata karta ragawa kowa har shi.   ........ Ina kwance ya shigo min yana huci, tashi nayi na zauna. Sannan na mika mishi hannu, ya tawo a sanyayye ya zauna goran ruwan da ke kan Yar teburin kwalbar falon na dauka na mika mishi sai da ya rabi, sannan ya sauke a bakin shi, amsar kwalbar nayi na ajiye kuma.            Sannan na rike hannun shi ina murzawa, kallon yadda fuskar shi ta sauya. "Kayi hakuri! Yanzun nauyin mu da duk wani abu ya haura kanka, dole kayi hakuri da halin mu, sannan ka san yadda zaka iya biyar da kowaccen mu, ba sai lallai ka d'aga hannu akan mace ba.    .... Na san dukiyar ka zata ɓannatar kai kuma ka hukuntata, amma kuma hanyar da kabi ba zai kare ka da kome ba sai zuɓewar kima!" .d'aga kai yayi tare da tsare ni da ido.       Gyad'a mishi kai nayi cikin nuna mishi, gaskiya ne nake gaya mishi.. "Me yasa kike ce haka?"   Hannuna na saka a cikin gashin kanshi, tare da hautsina shi, nace. "Yau ka dake ta! Gobe kuma Ni zaka daka, jibi kuma Husnah. Kafin mu ankara, mijin mu ya zama maduki, kaga kenan mutum daya ya koya maka mugun aiki."          Shiru yayi yana kallon yadda nake kokarin fahimtar da shi abin da ya sani.      "Toh nagode tunda kin san da haka toh bari na.." Da sauri na kalle shi, kamar zan yi kuka. Tare da ture hannun shi da yake kokarin cusawa a cikin rigana.         "Ni don Allah bana son haka, kai ba halin kaga mutum sai ka nemi tab'a mishi jiki."  Na faɗa ina mik'ewa, dawo dani yayi sannan yace. "Waye yace ki makale min?"          Dan renin hankali, kawai shige min yayi tun ina ture shi da jin haushin abin da yake min har dai na zuba mishi ido, dan ban san lokacin da nabi jirgin shi ba, sai da aka bankad'e kofar da mugun karfi, tare da wani irin iska, muka mike daga ni har shi, gyara zaman rigana nayi cik'e da kunya, zan bar falon.     Shi kuma ya zubawa kofar ido babu kowa daga ni sai shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo gare ni har na shige d'akina.        Bai shigo ba, kawai ya fice daga gidan.                         .... Kwatarkwashi.    A kauyen garin, kwance Jakadiya Sahurah take, idan ka ganta tsufa ya cimma ta, amma har yanzu tana nan a tsayen ta.          Abu daya take fama dashi shine makanta, wanda tayi rashin lafiya ta sanadin haka idanunta suke daina gani.           Mik'ewa tayi tare da kallon kofar d'akin ta kamar tana gani, kafin ta lallubi sandarta, tace. "Har ila yau, bai zo ba. Koda ba a haife shi bane? Ina tsohon shekaru ashirin da takwas, sai dai ko mace. Ina indai ita ce, tsuguno bata kare ba.               Idan kuma na miji ne! Karshen zamanin yazo, waye zai isa Daura."    Gyada kai tayi tare da mik'ewa ta fito bakin kofar ta, tana surutunta, mutanen gidan da take kallon hauka suke mata, yayinda ita take ganin kamar basu san meke damunta ba shi yasa suke kiranta da Mahaukaciya.       --- "Saurin me kike? Bayan shi zai zo! Karki damu kanki tabbas zai zo nimanki, kuma har ya saka a tafi mishi dake, da dai kinyi hakuri ne dole zaki fuskanci kalubale daga gare shi." Inji wani algungunmin tsohon wanda yake sanye da fatar ɓauna.             "Hmm! Kawai ka kife shi! Yadda ba zai iya zama a karagar mulkin, ka haukata mishi Ƙwaƙwalwar shi, yadda." Ta faɗa. "Dakata!" Ya d'aga mata hannu.. "Ba Jaamal bane! Jalaludeen ne, karfin tsarin da yake nima zai iya kashe min aljanuna da suke min aiki. Daf yake da zama me cikakken iko da nasara, karki yarda ya kasa wannan damar zuwa gida biyu.            A sannan ne babu wanda zai dakatar dashi ko ya hana shi, sai dai har yanzun muna da damar niman Sahurah, domin itace take da masaniyar akan yadda zai dakatar da kome, kuma naga baku son dakatar da abin da yake faruwa a masarautan.       Dan haka dukkan ku, ku bazama niman Sahurah yadda zaku iya dakatar da ita, idan shi ya same ta. Tabbas zai nimo ki, nake ba hatta sauran wanda yake boye a bayan idanun jama'a. Amma kafin nan ku fara mishi bayani Yaren da zai fahimta  haka zai sanya a fara wani tunani na daban."       Ajiye mishi jakar hannunta tayi tare da barin d'akin. Da sauri.   Tana isa gurin motar ta shiga, tare da zama ta dauki alkalami ta fara rubutu, da ajami.     اسلام الاكة بي غيثو إرت الدنم مسلث، دفتن سشقن ييث غزك. كمر يدد كدقك عن كو في ابين د يدث. كغرغطس يدد ءٱخ سير تاكررم غب. كركگشيس كبر شي يري ثكد شيرم، دغن دمطر دغ إدمكثي دغ فلن طثي.... Daga haka ta nade takardan sannan, mikawa driven tace mishi. "Idan mun isa ka kai daura." Amsa yayi sannan yajata suka nufi cikin garin kwantagora. *** Kwana biyu da rikicin Jay tare da Munih ya sauka a d'akinta, Allah sarki, yau munga feleke. Shiga da ficce, shan kamshi habaici da rawan kai. Dake ina sama, ina jinta ban ma leko ba balle tace an zo saka mata ido..          Har dare, ana girki can da ta gama zagayenta ta gama ihu da zage zage, babu wanda ya kulata.                     Har ya shigo, ina zaune akan kafet, hankali na yayi kan na'ura me ƙwaƙwalwa, ji nayi an tab'a ni, na d'ago kaina daga shi sai yar gajeren wando tare da farar riga, ya gyara fuskar shi da kasumbar shi, mika mishi hannu nayi. Ina murmushi, buge hannuna yayi da sauri na mai da hankali na kan shi, tare da zuba mishi ido. "Zo d'an kanina!" Kamar na zage shi, ya buge hannuna. "Toh meye nayi kuma?"  A sannu ya mike zai bar d'akin nace mishi. "Don Allah, kayi hakuri ba san laifina ba."        Mik'ewa nayi na isa gare shi, ya riko hannuna, cikin na shi, yana me kaiwa fuskar shi. Kashe mishi ido nayi sannan nace mishi. "Au! Yallabai aski kasha haka, shi yasa naga kana kyalkyale amarci."      Saka hannun shi dukka biyu yayi ya rungume ni, yana murmushi sannan yace min. "Yau wuni guda, ina kallon wayana ko dan sakon nan babu, sam baki damu dani ba."           Hada goshina yayi da nayi, ina yar karamar dariya nace. "Ina zan iya da shariyar ka, idan miskilancin ka ya motsa baka ji baka gani, shi yasa naki kula wayar ma, ai fita kayi kana fushi dan nace zan shiga cikin gidan gaida su Mamah."      Daura bakin shi yayi saman nawa, a lokaci guda muka kalli cikin idanun juna.  Nice na fara kasa da kaina, kafin na janye bakina baya nace. "Jay! Kana sha'awan jikina ne fa! Sam baka tunani na, jikina shine muradinka, tunda da bakin ka kace baka sona." "Eh shi yasa lokacin da kika turo min Hanisah ta gaya min kina son kayan fitar liyafa, baki yi tunanin bana sonki ba!" Da sauri na kalle shi, murmushi yayi sannan ya d'aga min gira daya. "Ni ban tura ta ba! Taji dai muna magana da Saif.." Cizon bakina yayi, tare da b'ata fuska. "Karki kuma kira min sunan wani kato a cikin gidan nan!" "Toh Naji, amma." "Baki tambayi taya aka yi na kasa wancan tuzurin saurayin baki ba?" Ya faɗa min. "Toh ni nuna ruwa na" "Zaki ga baki da ruwa."         Ƙoƙarin kwace kaina nake yi, yaki sake ni, "tun daga ranar da kika shiga rayuwata nake jin duk yadda aka yi, ina da nasaba dake.             Na rasa fahimtar haka, sai ma rigimar da kika ta takalowa,  haka bai ishe ki ba, sai da kika kwafta min mari, sannan kika yi sanadin haɗuwa na da iyayena.                  Ana saura sati daya bikinki, Baba Sarki yake gaya min shekaru Ashirin da daya, da suka wuce, sun daura mana aure. Bayan b'atar da nayi da shekara daya aka raba auren, iyayen mu basu sani ba, daga kakanin mu, babu wanda ya sani.            Sai gashi kin nimo mijinki, ko kunya baki ji, Baba Sarki da yake gaya min, nayi mamaki dan haka nazo har sokoto, na sami Dattijo, muka yi magana. Na kuma ce ko bana sonki a bani matana ko kuma a tashi Sokoto a tsaye da kafarta.     Ranar da na sauke ki, ai sabida kar wancan banzan ya kare miki kallo ne, dan haka ki ji a ranki ni har yau ina kan bakana, bazan tab'a sonki ba. Dan bana jin kome akan ki, sai yan uwanta ka." Wani irin abu naji a raina, ban san lokacin da na ture shi ba, nayi juyawa na kwashi kayana, yana min magana tuni na isa d'akina na rufe kofar, na zauna a jikin kofar, tare da cusa kaina cikin cinyoyina. Wani irin abu nake ji a raina, me mugun ciwo, tare da jin tsanar Jay a zuciyata.   Bai bi takaina ba yayi ficcewar shi, kasa. Haka na kwana da b'acin rai da asuba nayi mafarkin wai an kawo min shi cikin jini baya numfashi. A firgice na farka na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallar nafilla, da sauri na shafa addu'o'in na fito kasa, na tsaya a bakin matakalar benen, ina jin ya fito daga dakin Munih na sauke ajiyar zuciya. Sannan na juya abuna, ya hango Ni, amma ya share ni kamar bai ganin ba.               Bai dawo gidan ba sai da gari yayi haske, ina kwance a saman... 07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha.... 10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Zuma, ga zaƙi ga harbi* Ina kwance ya shigo, dake Allah ya daura mishi niman rigima, idanuna na lumshe ya shiga ja min babban yatsar kafana, bude ido nayi tare da lumshe su, dan bana son damuwa. Da sauri na kuma buɗewa tare da b'ata fuska kamar zan yi kuka.          "Dan nace bana sonki shine kike fushi?" Ya faɗa min, "Toh ina ruwana da kai, karka so ni mana, idan baka soni ba, dubunka sun so ni, dan haka ka kyale ni naji da abinda yake damuna." Fadar haka da nayi ya bashi haushi amma jin na fadi ya barni naji da damuwa ta, ya sashi zama kusada dani. Yana kallon fuskana.     "Batul!" Tsigar jikina ne suka mike sosai, a hankali na tashi zaune. " Matso kusa dani naji meke damunki!" Ya fada min tare da mika min hannu, kamar zan yi kuka nace mishi. "Babu kawai bana son magana ne!" "Zo ki gaya min meke damunki!" Ya mika min hannun, babu yadda zan yi haka na isa jikin shi. Kawai naji zuciya ta tayi mugun rauni, kuka ne ya kwace min. "Ya ilahi! Dan nace bana sonki?" "A'ah, ba haka bane kawai ina jin wani irin yanayi ne, da ban saba jin shi ba, sai da rasa wani abu daga jikina nake ji shi." .zuba min ido yayi sannan yace min. "Kamar Ya? Kawai naji kamar zan rasa wani na jikina ne"      Murmushi yayi sannan yace. "Har yanzun akwai masu yarda da canfe kenan? Toh babu abin da zai faru sai Ikon Allah, dan haka karki kuma zubda wannan hawayen masu mugun tsada, kin san nawa darajar su take, da kike zubda min su?"      Girgiza mishi kai nayi, a hankali ya janyo hannuna yana fadin "yau ban yi sallama da." Buge hannun shi nayi tare da dariya nace.. "Kai angon Munih ce, dan haka me zaka dauka a jikin yar tsohuwar da zata haife ka, kawai jeka gurin yan matanka." "Lallai kin gaya min magana, Insha Allah zan nuna miki abin da zai baki mamaki."     Rufe idanuna nayi cikin jin kunya da dariya nace. "Kai kan inda kunya tabi ina da yakinin baka bishi ba, kawai sai ka sake magana kamar yadda yake babu sakewa." "Hmm! Da bance a bani wannan abin na tab'a ba." Ya faɗa yana nuna min kirjina, wani irin kunya ce ta kama ni, da gudu na bar mishi falon, Jay bai ga inda kunya ba, ina ga kunya na gabas shi yana yamma, biyo ni d'akina. Haurowa gadon yayi, ya janye bargon, ya shiga min chakulkuli. Wayyo Allah na, kamar zan yi hauka, sabida tsabar dariya da wani irin farin ciki. Tsabar ya addabi rayuwata da chakulkuli, karshe zuɓewa nayi a jikin shi, tare da k'amk'ame shi..ina sauke wata irin ajiyar zuciya.     Bakin shi a kunne na, ya sauke min wata irin numfashi, wanda ya saukar min da kasala, na kuma narkewa a jikin shi, d'ago kai na yayi tare da kallon fuskana, tare da zaro harshen shi yana lasar bakina, a hankali na bude idanuna akan shi. Ina jin hannun shi yana yawo a jikina, Ji nake kamar a cikin Ƙwaƙwalwata yake min yawo dashi, kare narkewa nayi a jikin shi,.kirjina na wani irin bugawa, kallon fuskana yayi cikin nutsuwa yace min. "Ina son kasancewa dake, amma ina ganin yin haka kamar cutar wa ce." .... Kifa kaina nayi a kirjin shi, na rasa me zance mishi, duk yadda nake ji akan shi bazan iya sakewa na bashi kaina da jikina sabida yayi farin ciki ba, indai da gaske yana yina toh dole sai ya yarda da hakan tare da gayawa mutanen da yace musu shi yana yina. Hmmm lallai kuwa, ba dai wannan Jalal din ba domin baya jin zai iya ƙaryata kan shi....     D'ago kaina yayi tare da sumbatar goshina, yace min. "Zanyi tafiya Katsina! Insha Allah yau zan dawo, d'azun na ganki ne shi yasa na zo duba lafiyar ki."           Mai da kaina kirjin shi nayi, wani irin tsoro na kuma kamani, mafarkin da nayi akan shi ya shiga dawo min,  rintsa idanuna nayi cikin tashin hankali na bude baki zan yi mishi magana ya rufe min da nashi.           Tare da kashe min ido, dole nabi shi ba dan naso ba, ya gama cinye min bakina, kafin Allah ya kwace ni sakamakon bugun kofar da matar shi take kamar zata fasa mana dodon kunne.           ---- Bayan ya janye daga jikina, ya fice da sauri, shi nan yana ƙoƙarin ƙaryata zuciyar shi, har ya isa bakin kofar ya same ta, da kayan barcin da ya barta, ko sallah bata yi ba, daure fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba, sannan ya sauka kasa, taso shigowa ta zage ni, bai bata damar haka ba, dan haka ta sauko ta biyo bayan shi, lokacin ya wuce dakin Husnah, itama tana barci a cikin bargo yaga alamar tayi sallah.   Dan haka ya fita bai gaya mata zai yi tafiya ba, har ya nufi dakin Munih tana kallon shi ya shiga yayi wanka tare da gyara zaman tawol  ya fita daga dakin ya nufi dakin shi. Ya saka kayan shi tsaf ya shirya, sannan ya kuma dawowa d'akina, Tabbas da kayan na gan shi a tsorace nake kallon shi jikina kamar wacce aka tsoma cikin kankara, kayan cikina sun cure guri guda. Ga wani sanyin da yake damun jikina kamar ana kusanta ni da kankara. Bakina yana rawa nace mishi. "Karka je ka hakura da zuwa katsinar nan yau!" Wata uwar harara ya watsa min tare da kauda kan shi yana min wani,. gargad'i sannan ya ficce daga d'akin, ko sallama bamu yi ba. Yayi ficewar shi, ina kwance a gurin har wani barci ya rufe ni, kamar yadda nake cikin tashin hankali haka nake barcin cike da tashin hankali sabida miyagun mafarkin da nake wanda ya sani farkawa ina kwala mishi kira, zaune na tashi naga kamar giftawar mutum ta tsakanin baranda na, na sama mik'ewa nake son yi naji kamar ana wasa da ruwa a ban d'akina, wani tsoro ya kamani, dan dole na mike tare da lek'awa ban dakin babu kowa. .ina juyowa naga wucewar mutum da sauri, a firgice na kuma juyawa. Kai karshe da tsoro ya gama kamani da gudu na dauki mayafina, na sauko daga sama, kasa ina sauke ajiyar zuciya.   Tsabar tsoron bala'i. Da sauri na yafa mayafin zan fita, naga Munih ta fito tana waya tare da yatsina fuska kamar yaga mugun abu, bata gabana dan haka na saka kai zan fita ta kalle ni. "Gidan Uban wa zaki?" Murmushi nayi tare da saka kai zan fita ta riko min mayafina dina, da sauri na juya muka kalli juna, sake min da sauri.             Saka kai nayi zan fita, tare da fita filin gidan, tunda aka kawo ni gidan ban tab'a lekowa waje ba, kallon kaina nayi a madubin daya daga cikin motar shi, na kalli fuskana.             Murmushi nayi naga uban kumatan da na tara, a hankali na gyara zaman mayafina, sannan na nufi kofar da zata kai ni cikin gidan, tsabar na kwana biyu ban fita ba sai nake ganin gidan yayi min nisa, da sauri sauri na isa cikin gidan. Duk inda na gifta sai an zube an gaishe ni har na isa. Da sallama na shiga falon. Naga sun juya a firgice.     Tare da zuba min ido. Murmushi nayi na karasa a hankali na durkusa tare da gaishe su. Yadda suke amsa min gaisuwar yaci ace na fahimci rashin nutsuwa a muryan su, sai kawai na nime guri na zauna a kunyace.                 Kowa sai kallona yake, karshe Mamah ta jani zuwa shashinta, na zauna sannan ta kuma fita ta barni can naga Raihanah karama, ta shigo fuskarta yayi jajjur, murmushi na mata tare da tambayar ta. "Lafiyanki naga fuskarki tayi haka." Cikin tausayi da damuwa ta kalle ni sannan tace min. "Babu komai mura ke damuna." "Allah ya sauwaka, kuma kisha magani zaki ji dad'in jikinki." Daga nan tafita, sai bayin da suka shiga kawo min abin tab'awa har zuwa wani lokaci, naga babu wanda ya kuma shigowa, zuwa wani lokaci.       Na jima a dakin kafin Karama ta shigo, muka zauna muna yan hira dan itama bata jima da dawowa daga cikin gidan ba, muna zaune na duba yar qaramar jakar hannun da na fito da ita, na shiga duba wayata, kafin na turawa da Jay sakon. *Da fatan ka isa lafiya?" Babu amsa, ne kuma tura mishi bai dawo min da amsar ba, kawai sai na shiga kiran shi. Bai dauka ba, har zuwa wani lokaci bai dauka ba, mik'ewa nayi na fito zuwa babban falon inda naji abin da  ya kusan tarwatsa min kunne na. "Eh toh! Har yanzun bamu ji labarin halin da yake ciki ba, amma munfi zargin cewa sun wuce dashi katsina tunda dama can zai je, yanzun na bar Fahad da Najim a gurin dayan su zai wuce Katsina daya kuma zai duba mana nan asibitin daura dan munje mun sami motar shi."            Zubawa Baba Aswad idanu nayi cikin tashin hankali na karaso tare da zuba gwiwata a kasa, na fashe da kuka. Na kasa cewa kome. Kuka nake har da shasheka, domin tabbas abin da na gani, ne yake faruwa. Kiran layin Abban shi aka yi, ya saka a kunne, kawai ya furta. "Alhamdulillahi! Toh gamu nan zuwa."               Kallon Mamah Sarah tayi sannan yace. "Maryam, ko zaki zauna da Fatimah." "Don Allah, Abba kuje dani.. Don Allah karku bar ni a gida zan je na gan shi."             Babu yadda suka iya dole suka tafi da ni, a wani asibitin kudi aka kai shi. Koda muka isa zuciyata kamar zata fado kasa, har bakin dakin da aka shiga dashi.       Idanuna sai zubda kwalla yake tare da niman hanyar da zasu fito dashi, can bayan awa daya suka fito dashi kamar yadda na gani, hakan suka fito dashi rike bakina nayi wani irin kuka ya kwace min.     Mutumin da ya kawo shi yake bada labarin yadda akai hatsari, wai wata motar diban kasa ce, da wata motar itace, suka saka shi a tsakiyar su, suka yi ta make shi,karshe dai suka juye mishi kayan su akan shi, sannan wata mota yazo ya kuma buge shi ya faɗa a rami, Allah ya nufa zai yi nisan kwana. Kan shi kuwa yasha wata uban bandaje.             Abin tausayi, haka nake kuka duk yadda aka so na dawo gida naki, na kasa hakuri da halin da yake ciki, dan gani nake da zaran na dawo gida wani irin labari zan ji mara daɗi.      Ina zaune har aka kawo su Munih da Husnah, sun gama tsora ta, da halin da yake ciki. Muniba tace. "Dama ai an gaya mana ke matar mutuwa ce, duk namijin da ya aure ki, sunan shi gawa, wallahi wani abu ya same shi kema mutuwa zaki yi."           Ban tab'a yarda da maganar ba sai yau, domin daga auren mu, har ya faɗa cikin wannan hatsarin. Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, a gigice na zuba mata ido, na mik'e tare da fita daga dakin, na nufi Ofishin likitan da yake da ya duba shi. Ina shiga na fashe mishi da kuka tare da cewa. "Don Allah a wani hali mara lafiyan nan yake ciki? Don Allah karku bar shi ya mutu, don Allah ka taimake ni kar ya mutu."     Zare madubin shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya kura min ido. Duk yaga yadda na birkice da kuka yace min. "Ranki shi dad'e, babu abin da ya dame shi, kawai dai muna zargin ya bugu ne a kan shi. Wanda bamu tabbata ba, sai zuwa nan da wani lokaci."         A rikice na zuba mishi ido, kamar yadda yake kallona, sanan na sake kukan da nake ta hadiyewa nace. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Na zama annoba. A cikin al'umma, idan Jay ya mutu me zancewa mutane, da wani ido zan kalli iyayen shi, wato nice dai damuwa." Mik'ewa nayi na fito daga ofishin sa, na tsaya daga jikin tagar dakin da yake ina kallon yadda yake cikin halin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai.       "Kin shigo rayuwar shi, dan ki kashe shi, meye ribarki?....           07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha.... 10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: _Kowa yaci ladan kuturu! Dole ya biya da yatsu_ Tafiya nake amma zuciyata cike da wani mugun tsoro, koda na shiga ji nake kamar zai fado kasa, haka na rike kirjina numfashina yana kaiwa da komowa, najima ina kiran sunan Allah kafin na samu sukuni, kasa kuka nayi, na zauna kwayam a dakin ina zare idanuna. Ina ji ina gani aka fara kome babu sanina.       ... A hankali kome ya sauya, Jay bai damu dani ba, koda kuwa zamu hadu da juna kamar zamu buge juna matsawa yake ya bani hanya, wani lokaci haka zai ta kallona kamar yaga bakuwar fuska.         .... Can fada kuwa, abin da basu tsammani ba, shine ya fara faruwa. Domin cikin iya taku tare da Najim suka shiga gwara kan mutane, musamman ajiyar da Sa'i,  yayinda suka hade kan su da Sa'i, haka ya bawa Ajiyar haushi, har ta kai sun fara rigima a tsakanin su, rigimar da ta kai har a cikin fadar suna iya yi a gaban kowa.            Idan suka yi fadawa ke musu magana tsawa su bari, sosai abin ya fara tab'a ahalin  gidajen guda biyu. Yau ma Juma'a sun gama abin kunyar su a gabab Jay, yabi Sa'i har gida bayan sallar esha, bayan ya samu shiga Sa'i yace mishi. "Jalal kai ne a gidana? ban kawo zaka zo ba, kai Nagode sosai."  Cikin murmushi Jay yace. "Haba Ranka shi dad'e gani nan, kawai nazo ne mu d'an zanta, na kuma baka hakuri da Abinda Ajiya yake maka ina ga zan dakatar da shi ma baki daya."       Nan Jay ya shiga tona mishi magana a bakin shi, tare da nuna mishi yadda yake jin haushin rigimar da suke da Ajiya, sannan dole ya dakatar da Ajiya, ai wannan bayi bane. Sosai ya zage yana fada.  Fir Sa'i yaki magana, sai da Jay yace mishi. "Karka gayawa Ajiya nazo gurinka, dan wallahi zai iya jin haushinka, domin shi yaso na zama yaron shi naki yarda dashi na sabida ina Son zama da manyan masu hikima da hangen nesa."  Nan ya shiga yabon yadda Sa'i yake, take kan shi ya fara kato yana jin shi wani ne. "Wato idan kana niman munafuki ka sami Ajiya ka samu." Mik'ewa Jay yayi sannan yace mishi. "Kayi hakuri zan wuce gida! Idan na sami lokaci zan kuma kawo maka ziyara." Daga haka ya fice ko dogon sallama bayi ba.            Har ya fito daga cikin gidan, yazo gurin Najim ya ciro yar wayar shi, ya mikawa Najim sannan ya  suka bar gidan. Shiru suka yi kafin Najim yace mishi. "Kar muje gidan Ajiya! Ni na jima ina zargin su, amma dole sai ka shiga jikin su dukkan su biyun, dole ka hade kan ka dasu. Ana zaka kuma sanin abinda yake faruwa." Sun jima suna tattaunawa, kafin suna iso gida, daga nan kowa ya kama gaban shi, dake dare yayi dan haka na yanke shawarar zama na jira shi ya gaya min meye nayi mishi ne? Ina zaune har Allah ya kawo min shi, mik'ewa nayi tare da zuba mishi ido, murmushi nayi a raina nace. "Abinda kake so yafi kome baka wahala." Da sauri yazo zai wuce nasha gaban shi, ina kallon shi kauda kan shi yayi sannan yace min. "Malama bani hanya don Allah." Ya faɗa a uzurance! "Jay meye nayi maka?" "Baki min kome ba, kawai bana son ganinki ne kusa dani!" Ya faɗa min kwalla ne suka zubo min, nace mishi. "Haka kawai kace min baka son gani na! Jay ko na maka wani laifin ne ban sani ba?" Saka kai yayi zai wuce na rike hannun rigar shi. "Ka rufa min asiri kar duniya tayi min dariya! Ka gaya min meye laifina da Kuskure na!"   Gyara tsayuwar shi yayi sannan ya zuba min ido, kafin yace min.. "Baki da matsalar kome! Sai dai kina w...!" Shiru yayi zai wuce.. "Me nake yi Jay?" Na tambaye shi a sanyayye. "Wari kike min! Kuma wallahi bana son ganin ki dan kamar wata dodaniya nake ganinki, don Allah ki rabu dani!" Maganar shi kamar ruwan zafi ya watsa min, kallon shi nayi, a hankali na sake Mishi hannun rigar shi.          Kasa gayawa kowa nayi, na shiga gayawa Allah kuka na, ina yin ibada ina azumi, a hankali. Na fara lalacewa, ina addu'o'in sosai.      Amma karshe sai na fahimci, gabaki daya ne bana cikin duniyar shi, bana cikin tunanin shi bai damu dani ba. Baya tunani na, sai na goben shi ga cikin Husnah da ya taso Sosai, nan rikicin da Munih take dani ya koma kan Husnah, tunda nice na tsare mata mijinta...    Ban tab'a yunkurin gayawa wani ba, haka ya sa nake cikin damuwa, domin yadda na koma ko fita nayi cikin gidan sai Mamah Sarah ta tambaye ni ko ciki ne dani.             --- A wannan karon bayan sati biyu, Jay ya nufi gidan Ajiya domin kuwa ya shiga jikin tsofin sun a tunanin su yana bin su ne, sabida sun fi shi,basu san cewa wannan din bom ne da kan sa... Haka ya gama shigewa jikin su, ana haka. Gwamna ya kawo wani abun cigaba, daura dan haka da aka zo kaddamar da abun ne Jay yace ba zai samu zuwa ba ya. Wakiltasu, na, yana sane ya hadu da aikin fidda wanda zai je taron . Aikuwa Sa'i yace shi yafi dacewa da zuwa. Ajiya yace bai iya ji ba. Karshe sai gashi suna shirin komawa yara ƙanana zasu daku da juna. Budar bakin Sa'i yacewa Ajiya. "Munafuki me fuska biyu, ince kai ne kasaka a buge shi ranar! Kace kar a kashe shi?" Cikin fusata Ajiya yace. "Naji amma kai ne ya dauke shi shekara ashirin d'aya da suka wuce?" "Eh naji ai Fulani Hasiyah ce ta sani tare da cewar wani wanda bamu sani ba, ashe bani kadai bane fitinanne.". Shiru Jay yayi yana kallon su, ba iya shi ba hatta sauran mutanen da suke fadar, sai da suka gama sannan suka fahimci abinda suka aikata.      Take kunya ta kama su, tare da mik'ewa zasu bar fadar Jay yace musu. "Ku kama su?" Mik'ewa yayi bai tsaya ba, sai cikin gidan. Inda ya sami Umma Rumanah kakar shi, zama yayi tare da zuba mata ido. "Wacece Fulani Hasiyah?" Kallon shi tayi sannan ta zuba mishi abinci ya fara ci, a hankali ya fara ci tana bashi labarin abinda ya faru, da kuma yadda Zuwan Jannart kome ya zama tarihi.       Murmushi yake yana cin abincin sannan yace mata. "Ai kuwa za a dawo da ita! In dai har tana can tana iya shirya yadda kome zai tafi mata dai-dai toh Tabbas ina bukatar ta a raye yazo ta koya min muna kisa.". Duk yadda taso fahimtar dashi yakasa fahimtar ta, shi kawai zai dauko Fulani Hasiyah ne. Daga nan gidan su ya wuce, yaje ya sami Mamah Sarah, sun jima suna hira har ta kawo mishi batuna. "Jay meke Damun Aanih? Naga ta lalace ne!" Shiru yayi sannan ya mai da kan shi inda yake kallo ya tabe baki yace mata. "Tana da mugun hali, bata son zama a waje sai zaman daki kamar daddawa, ba dole mutum yayi wari ba." Nan ya shiga yayi ta mita, wai din nayi mishi laifi." Hakuri ta bashi dan bata zata abun ya kai inta haka ba.        Bayan ya gama hira ya koma cikin gidan shi. Yana zuwa ya sami tashin hankali, domin kuwa  Husnah ya samu suna Fada da Munih, saura kadan su kaure da dambe. Gata dama da cikin shi, kallon su yayi yaga da gaske fadan zasu yi sai ya wuce su bai kuma bin takan su ba, har ya kusan kulewa yace musu. "Wallahi kuka barni na sako na same ku! Sai na lahira yafiku jin dad'i, kuyi kokarin tab'a min cikina ku gani sai na lalata musu rayuwa". Daga haka yayi wucewar shi bai kuma jin ko tarin su ba. ....yana isowa bakin kofa na ya kurwa kofar ido, cikin sanyin jiki, kafin ya saka kai ya wuce abun shi, dan ji yaƙe wani irin wari yana tasowa dole ya kauce dan zai iya kwara amai. ---- Yau da gobe bai bar kome ba, an dakatar da Sa'i da Ajiya, kuma Jay ya tura da sako Masarautan kwantagora a turo mishi da Fulani Hasiyah. Duk da taso kin zuwa, amma ya kuma tura mata da sakon shi kamar haka. ان كركا كذ ثكطا امد كككسك نذ طكن تبس ابمب ذمكقب فتم ألكرن سرك جللدن _Ina kiranki da kizo da kafarki cikin da'a idan kika sake nazo da kaina tabbas abin ba zai miki kyau ba! Sarki Jalaludeen_ (Wannan karon ma na kuma amma ga na asalin harshen Hausan da muka sani) Shiru tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya, Tabbas Jinin Sarautar ke huda jikin shi, babu tsoro a cikin kalaman shi, sai tsantsar Izzah! Idan kuma tace ba zata ba, tayi imani da Allah zai zo da kafar shi Hmm ance mai laya ya kiyayyi me zamani, da badan haka ba ba zata je ba. Kuma toh amma kuma ai korau ya gaya mata.! Da sauri ta mike tare da saka alkyabar ta ta nufi inda ake ajiye mota ta kira a kaita can inda korau yake. Tafiyar awa daya da wani abu ya kaita garin, tun da ta shiga, yake dariya sannan yace. "Da na gaya miki zai nime ki, ai ƙaryata ni kika yi! Babu inda zaki iya kaucewa tarkon yaron, domin zai ji dake fiye da yadda baki zata ba, Yaro ne da ya tsaya da kafarshi yaki tallafin kowa balle a sauya mishi akala. Yaron ba zai tab'a sarewa akan mulkin shi na, dole idan kin isa kiyi muba'yi a, dole idan kin isa ki saukar da kanki, sai kin amince da muradin shi sannan zaki fahimci meye tsoron shi! Meye amfanin shi, meye raunin shi idan ba haka ba, ba zaki tab'a tsira daga dukka uƙubar shi ba. Kamar yadda Uwar shi take, haka shima yake, kuma yana dab da kara samun karfin Sarauniya ZIRYA! Domin tana faffutikar ganin ta kuma shiga tarihin shi, dan haka kiyi kokarin dakatar da shi, idan halin haka ya samu. Karfin mulkin shi zai kuma bunƙasa ne daga ranar da yayi wata yunkurin da babu Sarkin da yayi sai shi a karnin shi. Kayi ƙoƙarin kare kanki da kuma gano meye burin shi ta haka ne zaki iya samun damar juya hankalin shi." Daga nan ya bata abun da zai iya bata, sannan ta bar gidan shi. ......... Daura. "Kasan tayi imani da bokaye! Kuma abin da naji a bakin Baba Magaji yace min zai yi wuya bata nemi wanda zai bata Sa'a ba, dan haka meye ka shirya mata?" Inji Najim. Juya kujeran shi yayi cikin nutsuwa, yana wasa da wata abin wasa, na lissafi sai juyata yake. Yana kuma kallon Najim. Sannan ya cilla mishi ya mike! Ya zaga kujeran. Tare da zama a kusa da Najim! "Kai lissafin ka Fulani Hasiyah ce! Ni kuma lissafina kujeran da na taso a kai. Misali zan maka sai ka fahimci wani abu wanda tun daga ranar da na shigo cikin masarautan nan na gama gabatar da kome. Wannan shine kujeran da ake kawo min farmaki a kai! Sa'i shine wannan! Wannan Ajiya. Ga Fulani Hasiyah! Nan Jakadiya Sahurah bata nan! Sai mutum na ƙarshe." Dariya ya saka, sannan ya cigaba da cewa. "Akwai mutanen da bakin su yake shiru a masarautan nan! Kuma suna sane da wasu abubuwan! Misali Baba waziri na yanzun wato Baba Hashim! Baba Shamaki! Wato Baba Umar. Basu san kome ba. Har zuwa kan san madami dan baram, kan magatakardan masarautan, Akwai fitinannen a cikin gidan nan, matsalar yaki bayyana kan shi ne. Amma idan Hasiyah ta shigo ya tabbatar tana cikin masarautan zai b'ata kamar masarar da taji wuta! Zai magantu makara wanda yaji dukar bayyanan shi daga bakin Fulani Hasiyah." Shiru Najim yayi sannan yace. "Wa kake zargi?" "A'a ban isa can ba! Amma ina da yakinin cewa yana sane da ni, Yardan shi da yayi a kaina ya sashi sake min wani shashinsa.. .yana tsaye a kaina ba dare ba rana." "Amma naga ba wani" "Ina sane da ba wani jimawa nayi da tashi daga jinya ba ko?" 10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: *_Tabur man kunya... A nad'e shi da hauka._* "Ba jimawa nayi da dawowa daga jinya ba ko? Toh amma ka sani dole ce Kanwar naki. Ta sani fahimtar haka." Daga haka bai kuma magana ba ya cigaba da juya kujeran shi can ya mike zai tafi Najim yace mishi. "Ina ganin mu fara bin su Baba Hashim mana!"  Juyawa Jay yayi sannan yace mishi. "Na yarda da shawarar ka! Amma taya? Ba lallai bane ya fahimce mu!" "Fahad! Zai iya mana kome! Zai iya taimaka mana! Shima zai iya tsayawa sabida kakan shi yayi ƙoƙarin inganta gaskiya a masarautan nan!" Inji Najim. "Baka tunanin ya iya cewa ba zai iya shiga matsalar ba, domin bai da wannan zuciyar! Kasan me yasa su Abba suka nace maka ka zama lauya?" "Sabida na kasance, me kare masarautan idan bukata haka ta taso!" Ya faɗa yana kallon Jay. Jan kujeran yayi ya zauna sannan yace mishi. "Ko daya ba haka bane! Sabida ka zame min garkuwa ne, sabida ka tsaya min a koda yaushe! Domin taya Ni yaƙi da abokan gaba na, dan haka bana gayyatar kowa, kai ɗaya na yarda da kai, kuma bana tunanin zan iya yarda da wani bayan kai. Duk faffutikar da nake sabida masarautan ta kafune da kafarta, kafin ma shiga cikin alamarinta."           "Haka yayi amma kuma kasan akwai abinda baka tabbatar ba shine matan ka ka zabi Fatimah. Kome ya dalili?" Inji Najim.     Lashe bushashen lebban shi yayi sannan ya tattaro duk nutsuwar shi ya zubawa Najim ido kafin yace mishi. "Zan rabu da ita! Bana sha'awar zama da ita.! "Akan me? Kuma meye laifinta? Kasan girman kasadar da ta dauka akanka kuwa? Haba Jalaludeen, wannan ba adalci bane!" "Toh ya zanyi bana jin ta ne a raina, kuma zan cigaba da zama da abinda bana ra'ayin shine? Kaga ai haka ba zai ma taɓa yiwa ba."    Sosai Najim ya tsorata da abin da Jay yake fada akan Aanih dan tsakanin shi da Allah yake fadar zai rabu da ita. ......... Kwana goma tsakani sai ga Fulani Hasiyah, duk abinda take bukata Jay sai da yasa aka ajiye mata, sannan yasa Fadawa suka tsare shashin da take, sosai ya tara shiri akanta, tana zuwa kuwa ya kaita nan, kallon shi tayi iyaka kokarinta da ta gano wani abu daga gare shi. Zama yayi ya daura daya akan daya! Yana murmushi sannan yace mata. "Barka da zuwa,!" "Yaro man kaza!" Kafin ta rufe bakinta ya amsa da cewa. "Idan yaji rana zai narke! Ci abinci, dan ina karb'an bakina da soyayya ne!" Yace mata. "Gashi nan ga wannan soyayyar ba! Naga wutar fansa a idanun d'an kwarkwarah!" Ta gaya mishi, "Na jima da jin sunan, sannan ina alfahari da sunan, sabida mu din na musamman ne! Ranki shi dad'e kici abinci." Ya gaya mata bayan ya tura mata kwanon gabanta. "Bana cin abin da ya fito daga hannun mutumin da ban yarda da shi ba!" Ta faɗa kai tsaye, gyad'a mata kai yayi sannan ya janyo kwanon miyar ya zuba a cikin wata faranti, sannan ya zuba tuwon shinkafa wanda aka kwashe da man shanu, a hankali ya saka cokali ya fara cin abincin yana gyada kan shi tare da kallonta. "Wannan girkin Mamah Sarah ne! Uwata kenan" ya faɗa a hankali. "Kuma itace sanadin mahaifiyarka!" Sake cokalin yayi cikin mamaki, kura mata ido yayi cikin fusata yace. "Ki iya da harshen ki, bani da wata uwar da tafi Mamah Sarah." Ture abincin yayi tare da mik'ewa, jikin shi na rawa. Ya saka kai zai fita. "Zaki! Irin wannan fusatar! Toh idan kaji da saka hannun mahaifinka yayi sanadin mahaifiyarka me zaka yi? Ka zata kowa sha-sha-sha ne, toh kaje ka nime tarihin masarautar zaka ji abinda suka mata." Fita yayi bayan ya gama jin abinda tace. Murmushi yayi, sannan ya murda hannun shi tare da barin gurin a nutse. --- A hankali Fulani take gayawa Jay magana tare da son hada shi da kusantar shi, har aka ta samu ya fara biye mata. .... Alamarina da shi kara gaba yake domin kuwa Jay ya manta dani, ko zamu hadu sau dari Wallahi kallon bakuwa yake min, na rasa wanda zan gayawa, sau da dama za a kawo kayan abinci ni bana zuwa sai dai bayina su kwaso min, dan me gidan baya yina. .... Ana haka kwatsam Munih ta fara laulayi, cikin wata biyu. Amma zo kiga yadda gidan mu ya koma kamar Husnah bata da cikin, tun ina share su har na daina fitowa falon, sabida habaicin da suke min yasani daina shiga harkan kowa. .ta Gurin miji ban huta ba, ta gurin kishiyoyi ban huta ba, kafin wani lokaci magana ya fara fitowa wai ni juya ce, Mamah Sarah bata san meke faruwa ba, ta sani a gaba muka je har Asibiti aka shiga min gwaje-gwaje, sun tabbatar musu da lafiyata lau, koda muka dawo cewa aka yi dan tana kare ni yasa ta shirya karya dan ka rufa min asiri. .........bayan wata takwas, Babu abinda ya canza, ga rigimar da ta Kunno Kai a masarautan, domin Jay ya hana kowa sukuni, kuma ya hana kan shi shima sukuni, take aka fara korafin a tsige shi. Wasu suka yi na'am da batun wasu kuma suka koma bayan shi, kasuwar masarautan gida biyu ya kuma d'aga musu hankali. Ana cikin wannan yanayin Husnah ta haihu, ga Munih da tsohon ciki. Nice hidima idan na gama su fashe da dariya, yan uwan ta suna faɗin. "Ba dole ba, ta sami Yaro sabon jini ga aiki kamar me, dole ta hakura da wulakancin sa dan haka Husnah mike kafa kiyi ta haihu, ita kuma tana muku bauta miji na wulakantata" Murmushi nayi daga ranar ban kuma saukowa nayi musu aiki ba, Yau na sami saukowa ne sabida zuwan su Rumah da Karama, tunda gobe suna sai naga Zabba'u tana ta aiki ana mata tsawa, ba ita ba hatta su Larai. "Zabba'u!" Ajiye aikin tayi. Ban tab'a jin zafin lusarancina ba sai yau, dan haka nace mata. "Ajiye aikin!" "Ke Aanih ina ruwanki da aikin da take mana ba bayin...." "Inji wani d'an iskan? Bayi na ne, daga masarautan mu aka kawo min su. Ni jinin Sarauta ke bin jikina, ba daurin dausono kunun bayan ludayi ba, duk wata yar iska ina dai-dai da ita kuma kar na dawo daga rakiyar bakina ba same ku kuna aikin nan in ba haka ba zan sa akawo min Barde ya hukunta min kowacce ku." Daga haka nayi wuccewa ta na raka su Qarama, tun da na juya da sauri suka bar aikin kowacce tabi Zabba'u zuwa Shashina. Nan suka shiga zagina wai na kwashe bayina dama basu da bayi ne, karshe dai maganar aka yi ta ririta alamarin har washi gari suna. Mamah Nanah ta shigo da safe tayi min cin mutuncin na fitan hankalin, har da min gorin haka zan zauna ban haihu ba. "Ai Nagodewa Allah, dan ban samu ba amma ai bayi barci ba, kuma ban makara ba. Yana sane dani, kuma ina ganin girmanki dan haka ki fita kafin na kasa sarrafa fushina." Na gaya mata sannan na wuce d'akina, can sai ga su tare da Jay da Husnah, Mamah Nanah tana kuka take gaya mishi naci mutuncinta. Ina cikin daki ina cire kayan da zan saka kawai naji ya fincikoni zai mare ni, na rike hannun shi. "Tsakani na da kai shekaru shida zuwa bakwai! Ashe kuwa baka isa ka d'aga hannu ka dake nie ba, wallahi baka isa ba. Na kuma gaya maka baka isa ba, kana tab'a ni zan rama." Na sake hannu shi na cigaba da abin da nake. Nan ya shiga gaya min magana. Har da ce min dan ya rufa min asiri yana zaune dani duk da ina matsawa rayuwar shi da wari bai tab'a jin ya rabu dani ba. Kai abubuwa marasa dad'i haka ya gaya min. Tun ina iya jurewa har na kasa na shiga mayar mishi, abin da ya haifar mana da zazzafar sa'in'sa, kamar zai dake ni kuma kuma na kafe bai isa ba. Kawai muna cikin haka Mamah Raihanah da Mamah Sarah suka iso, ban san waye ya gaya musu ba. "Wawuya sakarya wacce ta rasa mijin aure ta makale min." Juyawa nayi ina kallon shi, murmushi nayi domin su Mamah sun shigo, kawai sai ji nayi an kifa mishi marin da ya sashi tsorata, ba kowa bane sai Abban shi. Domin yana tare dasu Mamah aka gaya musu muna fada, ban ce kome ba, kawai na shiga hada kayana, kallon Abban shi yayi idanun shi jajjur, sannan yace. "Ni dama na jima da saketa, domin wari take min!" Sake kwalbar turaren hannuna nayi ya fadi a kasa sai da ya tarwatse, wani irin hawaye ne ya zubo min, na shiga ta cikin kwalbar na wuce na ka rasa kwashe kayana na cikin ma'ajiyar kayana, ina kwashewa ina zubawa a cikin kwatinae. Waya tace ta kawo wuta, na dauka tare da sakawa a kunne na. "Na'am Baabina!" Shiru nayi hawaye na zuba min cikin karfin hali nace mishi. "Laa babu komai, wallahi kawai muna magana ne akan sha'anin sunan da za ayi ya fara fada, amma wallahi babu kome dan har ya fita ma!" Sake jadadda min yayi idan akwai matsala na gaya mishi. "Wallahi na rantse maka babu kome, yanzun ya fita da na bashi wayar." Addu'a yayi min tare da saka min albarka, suna tsaye na kwashe kayana, na zuba a cikin jakkuna na, sannan na dauki babban hijab dina na saka, na shiga ban daki na wanke fuskana na fito, kallona suka yi na sunkuyar da kaina kasa. "Fatimah! Zaki wuce sokoto yau Insha Allah. Sannan kiyi hakuri Nagode da rufa min asirin da kika yi dan bashi kika rufawa ba wani ne." Tunda Abban shi ya mare shi yafita, har zan fice Mamah Sarah tace. "Dawo nan! Mamah ki tafi da ita, Amma wallahi ku duba Alamarin Jay ba haka kawai bane yayi wannan aikin, bamu san me aka gaya mishi ba, kuma kunji yace tana wari akwai matsala fa!" Juyawa Mamah Raihanah tayi ta sauko, tare da kiran matan shi ta zauna tare da daura daya akan daya tace musu. "Zan tafi kuma Fatimah zata bar muku gidan ku! Na baku sati Uku! Wallahi tallahi billahil azim, na koma dawowa gidan nan, Jay bai zo Abuja niman Fatimah ba, Na rantse da Sarkin sarauta. Wallahi sai kun bar gidan nan, kuma sai na baku mamaki," daga haka tayi kiran mu, Har zata fita tace. "Ku ajiye magana ta, kar na riga shi zuwa gidan nan, domin kuwa zuwana babu Alkhairi a cikin ta " daga haka ta haura zama muka sauko, tana rike da hannuna, a ranar muka bar garin, su a tunanin su Sokoto na wuce nan kuwa wucewa tayi dani Abuja. Bayina kuwa cikin gidan suka koma. Nayi kuka tun kafin na isa, har ina jan zuwa, ai kuwa muna shiga gidan ta fara min balbalin Bala'i. "Sha-sha-sha, kin zauna hanjin cikin ki, suna saki kuka kekan baki yi kama da jinin sarauta ba, share hawayenki zai zo nan kuma ina nan ina jiran mara kunya." Tayi min fadar yadda na bari ya rena ni, sannan kuma ta kuma kara min da nasiha, tun daga ranar take yawan jana hira. --- a can daura kuwa, daga Husnah har Munih kowacce zargin yar uwarta take dan gani suke kowacce tana da wata mummunan manufa, dan haka suka shiga nuna junar su... Bayan anyi suna, aka watse saura Munih ba, Jay kan Abban shi fushi ya dauka dashi, abin da ya shafi rayuwar shi na yau da kullum, har kowa ya fara fahimtar haka, kuma ya kira Rahil ya gaya mata, itace ta kira babanta ta gaya mishi nan suka dukufa da addu'a da sadaka, ba dare ba rana, kullum yi ake..cikin niman Yardan Ubangiji. Nan ma Daura ba abar su ba, haka ma Sokoto Ummin itama ta maida hankalinta sosai gurin sauka da sadaka. ... Abin da ya matukar d'aga musu hankali, shine yadda wasu abubuwan suke bayyana daga cikin masarautan.... 10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: *_Ana zaton wuta a makera... Sai a kasame shi a masaka_* Abin da ya faru ba kome bai ne shine fitowar Hashim baban Fahad yana kalubalantar Jay da rashin adalci, takanas yaje ya sami Jaamal da Aswad da zance bayan sun gaisa. Nan suka shiga hirar duniya. Daga nan ya kawo batun Jay. "Jaamal da zaka bashi shawara akan ya daina zurfaffa bincike akan iyayen mu, da kome yazo da.." Ruwan dake gaban Aswad ya sauka ya watsawa Hashim a fuska, tare da mik'ewa ya d'ago kwalar rigar Hashim zai mishi magana Jaamal yace. "Kyale shi! Manta dashi, kaje ka gaya musu nace bazan iya dakatar dashi ba, duk wanda ya isa namiji ne ya dakatar da shi." Kallon su Hashim yayi sannan ya juya zai fita. Jaamal yace mishi. "Albasa bata yi halin ruwa ba, amma mun maka Uzuri." Haka ya fita ran shi a b'ace, yana komaws gidan shi ya sami Fahad yana waya da Qarama, bayan ya gama ya sami Hashim a falo yana gayawa mahaifiyar Fahad abin da Jaamal da Aswad suka mishi, Shiru tayi kafin tace. "Amma sun fika gaskiya, taya zaka ce a dakatar da yaron daga aikin da yaƙe? Bayan kai da kanka kake cewa, Yaron yana abin da ya dace, don Allah karka bari haka ya shafi zumunta dake tsakanin mu, domin ko babu kome, mun zama daya ga kuma Fahad da Jannart, don Allah domin yaran mu kar mu girmama abin ya zama babba." Jikin Fahad yayi mugun sanyi, dan haka ya fita daga gidan baki daya ya koma kofar gidan su ya zauna yana nazarin abin da ya faru da Mahaifinshi. Kuma yayi imani haka kawai mahaifin shi bazai tab'a juya halin shi ba. Dan haka Ya turawa Jay sako.. dake kan shi a sunkuye yake yana d'agowa yaga wasu kartin maza akan shi, kafin yayi wani yunkuri har sun rufe mishi bakin shi. Tare da wurga shi cikin mota, haka suka tafi dashi. Babu wanda ya sani. Cikin abin da bai fi minti arba'in ba sun bar unguwar baki daya. --- Jay yana zaune yaga sakon Fahad, koda yayi kokarin kiran Fahad din wayar taki shiga sabida rashin yanayi me kyau, dole ya hakura, sai bayan awa biyu ya samu wani sako daga Fahad din da ya turo mishi. *_Wasu mutane da ban san su ba sun dauke ni. Amma ina da yakinin zaka iya kub'utar dani, idan kuma haka bai samu ba! Jay ina maka fatan Alkhairi sannan ka gayawa Firdausih Qarama ina son ta_* Turawa Najim sakon yayi, sannan aka shiga bibiyar sakon, abin mamaki a cikin masarautan yaƙe domin har yanzun lokacin Wayar bata daina aiki ba. Dan haka Najim ya turowa Jay sakon. Allah ya taimaka bai fita fada ba,dan haka ya badda sawu tafi cikin masarautan yana bibiyar bayyanin da ake mishi.. ...... Bayan awa daya Allah ya taimaka ya sami Fahad a can a yashe, sannan aka kira shi da wayar Fahad din yana dauka aka ce mishi. "Ta yaro kyau take bata karko, gashi mun shirya maka gadar zare! Kuma ka fada ka wanke kanka idan ka isa." "Tsoho me ran karfe na same ka! Ka jira zuwa na katsina." Daga haka ya kashe wayar, yana mik'ewa Najim suna isowa. Aka ɗauki Fahad zuwa asibitin masarautan. . A nan aka kwantar dashi, dake an kunsan gama wasu shashi na asibitin, dan ma ana wasan kwaikwayo da Jay dan yace babu abinda zai hana shi aikin shi na likitanci, shi yasa yake gayyatar, su Hikmi Abeel su zo suyi aiki a cikin asibitin shi. Lokacin da ya dawo, zai haura sama yaga wuccewa mutum, bai kawo kome ba, ya nufi dakin Munih me fama da dan karamin ciki, tana zaune sai waya take tana gayawa Mamanta irin kayan da za a saya mata, zama yayi yana kallonta, kashe kiran yayi ya zuba mata ido cikin takaici, domin wallahi bai tab'a jin sha'awar Munih a matsayin matar shi ba. Amma kaddara ta riga fata, tunda shi har da cikin shi a jikinta, *Khatoon* sunan da zuciyar shi ta ambata kenan, ya mike da sauri, ya nufi sama, yau sati Daya kenan, baya ganin wuccewarta. Bude kofar ta yayi ya shiga yaga yadda kome na ciki yayi kura, sannan kamar ance ya kalli dakin yaga alamar an shigo an fita. Share batun yayi ya koma dakin shi ya zauna, yana nazarin wasu abubuwa, kamar wanda aka tuna mishi ya mike da sauri ya koma d'akinta Littattafan shi ya gani a kasar matashin ta, Janyowa yayi yaga wata farar takarda..ajiyar zuciya yayi sannan ya shiga karantawa. --- _A yanzun na san nayi nisa da kai! Amma zan tuna maka wani abu da baka sani ba, Jay Ina sonka! Amma zan tafi na Barka! Masarautan ku cike yake da abubuwan damuwa, koda yake bashi bane damuwar rubuta maka wannan sakon tun ranar da ka kawo min Littafan nan nake ta yawan nazarin yadda zan buɗe nayi nayi amma na kasa, abin mamaki juya na zauna na gwada sa'ata kayi hakuri zan kira sunan Ammih! Jannart+ Jamal! Ka gajerce sunayen mu gani, idan aka Cire Janjamal_ Jikin shi na rawa ya gwada yaki, shiru yayi, tare da sake duba wasikar! Dariya tayi mishi da _Hahaha! Nima haka na gwada, akwai wani sunan da su Mamah suke kiran Ammih dashi, wato Janny, muma haka muke kiran Autan Ummi, idan aka gajarce Jan! Aka kawo harafin i aka saka zai bada Jani! Kaga kenan sunan Ammih yafito saura sunan Abba wanda su kuma zasu kasance harafin uku ka na karshen sunan shi Jay Ina matuƙar sanka da wannan nayi lissafin bude Littafin labarin Amminka, amma ban karanta ba. Nagode daga Sakakkiyar matar ka Wacce kayiwa gorin aure._ Wani irin kunya ce ta kama shi, a hankali ya tuna abin da wata tsohuwa ta tab'a gaya mishi a lokacin da zai bar Nijar.... *karike kalmar Janimal zata amfane ka wata rana* Bude Littafin yayi na farko, ya bude shafin hoton Abban shi lokacin yana matashin sa, hoton baki da fari, a kasar hoton ta rubuta. *Kawu kenan! Mutumin farko da naso shi a rayuwata ya kuma ce baya sona!* Bude shafi na biyu yayi hotonta, ya gani, sanye da kayan makarantar ta Rubutu.. *Jannart Jamal Jalaludeen J³ wasu suna kirana da Janny amma nafi son Firdausih dan Kalmar daga bakin Kawuna, Kawun JANNART* Shafi na gaba ya bude sai ga hoton Sarah, *Aminiyata ce ita Kawata ce ita Dole abin da na haifa yayi biyayya da da'a a gareta. Dan yar uwata ce* Shafi na hudu hoton Aaryaan ne, ta rubuta a kasar tace. *Yaso ni! Ya kuma kaunace ni, ina umartan abinda na haifa ya girmama al'amarin Aryaan, dan mutum ne da bazan manta dashi ba.. Ita al'amarin kaddarar a cunkushe take da soyayya sadaukarwa, farin ciki bakin ciki, kuka dariya, mugunta hassada kyashi. Rikid'ewa zuwa wata siffa ta cutuwa. Laifina da Kawu babba ne, da yau na fito na gayawa Sara ina son Kawu da bata shiga rayuwar mu ba. Amma na boye mata bayan so shi bai iya boye kan shi, babu ruwan shi da babba ko yaro, so dangin mutuwa ce, da zaran ta zo maka babu makawa sai. Ta same ka. Daga nan zaka ji yadda kome ya kasance mana, da kuma yadda zaka kawo karshen rikicin masarautan... A hankali yake bin shafi zuwa shafi. Har zuwa shafin karshe ajiye Littafin yayi, dan tun daga farawa har ya gama, idanun shi basu daina zubda kwalla ba, wani irin yanayi ne haka? Me yasa zuciyarsu take rufewa daga matar da suka dace dasu? Dake labarin bai kare ba, ya bude daya Littafin ya fara karantawa, a wannan ranar Jay yayi kukan da na kasa dainawa ji yaƙe mutuwar Mahaifiyarshi kamar yanzun aka mishi daga karshe inda zata tsaya tace. _Ban sani ba ko mace ko namiji zan haifa, koma waye don Allah karki / karka wulakanta duk wanda zai ce yana sonki ko yana sonka, Ni nasan ciwon da mutum yake ji idan aka ce ba a son shi, duk wanda zai soka ya gama maka kome a duniya._ tayi nasiha sosai har da misali da rayuwarta, tayi fatan da tana raye taga me ta bari, tayiwa abin da ta bari addu'o'in, sannan ta roke shi da ya nemi ilimi Addinin domin da ita zai yake abin dake faruwa a cikin masarautan, daga haka ta rubuta zan koma mahaifata Maiduguri. Kifa kan shi yayi a jikin Littafin ya fashe da wani irin kuka, sabida tausayin Mahaifiyarshi, da Aanih, anan ya fahimci zubda jinin da Aanih take yi da, sabida shigar ta rayuwar shine tun farko. .mik'ewa yayi lokacin da ya fahimci, bata ga gidan. Da sauri ta sauka kasa. "Kee ina Aanih Fatimah Khatoon take?" Cikin gangancin tace mishi. "Taje koyar sallama,!" "Ni zaki gayawa maganar banza!" Ya daka mata tsawa, "Jay nifa bana son fitina, kaje ka nimo Matarka inda take karka dame ni don Allah." Da sauri ya fita, zuwa cikin gidan su. Kamar wanda aka wurgo shi ya zuba musu ido, kafin ya wurga musu tambaya. "Ina Aanih Fatimah Khatoon?" Shiru suka yi suna kallon shi, kafin ya kuma tambayar su.. cikin rashin damuwa Abban shi yace mishi. "Ba ka saketa ba? Ai tayi komawar ta sokoto!" A kidime ya zuba musu ido, yana kallon su, bakin shi na rawa yace. "Yaushe? Ni da hankali na zan sake abin da nake s... Abba Wallahi ban saketa ba!" "Amma kafara shaye shaye ko?" Inji Abban shi, "Wallahi ban tab'a sha!" Ya fada musu a raunane, share shi suka yi karamin hauka ne bai yi ba a masarautan, sannan ya nufi gurin Baba Sarki, shi kuma ya mishi fata fata, tare da koran kare. Haka ya isa cikin gidan gurin kakar shi Umma itace tayi ta rarrashin sa. ....... Washi gari ko asibiti bai leka ba, ya jajjibi Najim, sai Sokoto. Kasa hakuri yayi ya gayawa Najim abun da aka mishi, aikuwa Najim yace. "Yau kenan! Ba kai kace zaka sake ta ka huta ba ka tsane ta, tana maka wari ba!" Sake baki yayi, cikin bakin ciki yace. "Mara mutunci ashe dama kana sane da abin da aka shirya min algungunmin lauya kawai, kai baka dace da mataimakin shugaban lauyoyi na kasa ba, kafin dacewa da shugaba algunguman Daura baki daya.. mai Najim zai yi ban da dariya. Sabida Baban shi ya tab'a bashi labarin yadda Jamal yake kiran shi da Shugaban munafukai daura. Yau kuma Jay ya kira shi da shugaban algungunman daura. Haka suka isa sokoto Najim yana kara kular da Jay, dan yake bashi labarin wanda zai auri Aanih karshe yaji haushi yace mishi. "Kai dan ubanka a wani birnin jahilan ake aurar da mace bata yi idda ba? Dan haka babu wanda zai aure..." "Bayan da kanka ka gaya min babu abinda ya haɗa ku! Idan ka samu damar samun ta, baka cire kazamin kishin da ke cinka ba, har abada ba zaka iya amfanan kanka ba balle kuma wanin ka." Jikin shi ne yayi sanyi, ya kalli Najim sannan yace. "Hala na gaya maka wasu abubuwan ma ko?" "A'ah aminin Arziki! Iya k'iyayyar Aanih ce baka iya boye min ba, shima ba k'iyayya bace lalura ce, amma kayi hakuri ɗan ba zasu baka ita ka cigaba da mata gori ba" juyawa yayi ya zubawa Najim ido sannan ya sauke ajiyar zuciya yace mishi. "Na gaya mata magana marasa dad'i ko?" Domin ya kuma kambama al'amarin yace mishi. "Ina dad'i ai ta kare maka wallahi.." gaban Jay ne ya fadi cikin tashin hankali yace. "Kuma Wallahi ina sonta" "Son banza dai da kaga zaka rasa ba! Ai duk me sonka bazaka wulankata shi ba, balle kuma fatima shi yasa baba sarki yace yayi mata miji!" Inji najim. "Wallahi zanci Ubanka dan 'iska, a gidan wata uwar za a mata miji wallahi zan kafta maka rashin mutunci, matar yawa shugaban algungunman daura kawai! Idan na gama da su Fulani dan ubanka kai ma sai na maka rashin mutunci, sauke ni na tafi da kafana, mara mutunci na fasa bink" 10/23/20, 10:04 AM - Ummi Tandama: *_Kura da shan bugu! Gardi da amsar kuɗi_* "Toh Yallabai! Zan sauke ka amma kasan dole sai ka biya ni kudin tuka ka da nayi, dan wallahi bani aikin banza!" Inji Najim wanda yake cike da jin daɗin ya kular da Jay. "Sauke Ni nace!" Yadda yayi maganar sai ya baka dariya, haka suka yi ta faɗa har suka isa cikin Masarautar Sakkwato, kallon Jay yayi sannan ya kunshe dariyar shi yace mishi. "Me zaka gayawa Ummin da Baabina?" Shafa kan shi yayi cikin nutsuwa sannan ya juya yana kallon Najim yace. "Wallahi Malam Lauya ban sani ba! Ga baki daya kome ya tsaya min cak, ji nake kamar nayi ta fasa ihu ko zaku ji yadda nake ji. Ina sonta! Wallahi bazan iya rayuwa babu ita ba, don Allah ka taimaka min kar na rasata." D'aga mishi gira yayi sannan yace mishi. "Tunda ka iya tafiya babu masu tsaron lafiyar ka, sannan ka tawo niman abin da zuciyarka keso ai ka shiryawa yaki akan ta." Shiru yayi bai bar Najim Amsa ba, sabida zasu shiga cikin gidan, bayan sun shiga cikin gidan, aka gaisa sai raba idanu yake ko zai ganta, amma babu ita babu labarin ta, nan yayi ta kame kame, yana wasa da Jannart din Ummin shi, dan ta kure shi tace mishi. "Ina Khatoon? Da fatan tana lafiya" Dakyar ya iya amsawa da cewa, "Tana lafiya! Tace a gaishe ku!" Yana fadar haka ya mike tare da cewa zasu wuce dama sun zo wani abu ne suka ratso nan, suka shiga shashin Baabi suka gaida shi sannan suka fita, a waje ya hadu da Muhammad kanin Aanih nan Jay ya ja shi da hira dan yana sane da Muhammad yacewa Noorie yana son irin ipad ɗinta, har take gayawa Jay, yace idan ya samu lokaci zai saya mishi irin nata, aikuwa Mutumin Najim na kallon shi ya dauki Muhammad suka nufi cikin gari, acan yayi ta latsa Muhammad bayan ya saya mishi ipad din ya gaya mishi inda Addah take, nan kuwa yaron ya sake baki ya bashi labarin abinda yake ji abakin su Ummi, amma yacewa Jay. "Hamma don Allah karka bari a san na gaya maka domin Ammihnmu hannunta zafi idan tana zaneka wallahi." "Babu ma wanda zai ji sirrin mu." Haka ya dawo da yaron sannan Najim ya shiga motar Jay na tuka su, sai wani gudun gangancin yake musu, tunda Najim yaga haka ya fashe da dariya yana faɗin.. "Hala baka san wacece Mamah Raihanah ba ko? Allah ya bada sa'a!" "Yayar Abbana ce ita! Sai dai nima muka baka san waye ni ba, Jini Insha Allah zan dawo maka, nan da karshen wata naje na kuma dauko Matana." Ya fada yana wani jin nishadi. "Baka ce kome ba akan Fulani?" Najim ya tambaye shi. "Bata da wani amfani sosai, nima ina jin ba dad'i akan riketa da nayi, amma wanda nake son ya fito yaki fitowa, shi yasa na ajiye ta, kuma naji wasu bayanai na ban mamaki, ashe kafin a haife ni Ammina tasha wahala a hannun Wani wai Shamaki tare da Dan shi Abdul, shi yasa nake son datse wanda yake saka su aiki." Shiru yayi..Najim yace mishi. "Kasan wanda yake sasu kenan?" inji Najim. "A'ah ban ce na san shi ba, kawai ina kintatta muryan wanda ya kirani da wayar Fahad." "Jay! Anya baka aiki da mutanen boye!?" Inji Najim, . Dariya yayi sannan ya isa tashan jirgin saman, ya fita da komin shi, sannan suka yi musabaha da Najim, kafin suka yi sallama. ...... Jirgin Abuja ya nima kuma Allah yasa aka samu, dan haka yana shiga ya a sauke ajiyar Zuciya, tare da fadin. "Yan matan Saraki ga sarakinki nan zuwa gare ki." Ya sake wani kad'aitaccen murmushi, yana hango yadda zai yi wasan kura da yar tsohuwar matan shi. ....... Sosai na sake amma bawai dan Jay baya raina bane, kawai ina jinjina yadda ya iya furtawa ya sake ni ne! Sai naji abin yayi min girma, a hankali na gama abin da zanyi na fito daga cikin dakin girkin, ina fitowa na dauki yar jakata tare da hijab dina na saka, na haura zama da sauri na gayawa Mamah zan tafi inda ta biya min ina koyan girki, dan tace. "Ni gidana ba a zama babu abin yi, dan haka ki shiga makarantar koyan girki, zaki kara kwarewa." Kuma nasan gaskiya ta faɗa, dan Jay yana gaya min shi yana son abincin gargajiya da rana, da dare kuma ya samu tuwo kadan sai Y'ay'an itace, Ina shiga na zauna jin tana dan faɗa, tana idarwa ta kalle ni, dan waya take. "Har zaki tafi? Toh gashi nan Baba na ya baro Sokoto, kuma da Alamu niman ki yaje." Da sauri na dube ta, sai kuma nayi kasa da kai na. "Ki tsaya kiyi mishi girki, gobe sai ki tafi, dan bazan bashi ke ba, sai na zabga mishi rashin mutunci, dan ko Ubanshi bai isa ya wulakanta mace ba balle shi.." Ban kuma ce mata kome ba, ta gaya min abin da zan mishi, nace toh. Tun da na fara aiki, nake jin raina babu dad'i, kawai aikin nake har na kusan kammalawa, sannan naji muryan su,shi da Khalid, nan kuwa Mamah tayi mishi wulakancin da ya damu da kan shi, sannan tace. "Kaci abinci kayi gaba akwai abokin Khalid yace yana sonta tunda ka saketa. Dake ka ga baiwa tana binka kana wulakanta ka, ka godewa Allah da gwiwata take ciwo, da ban san haka ba wallahi sai na baka kashi ka tambayi Ubanka shima ban kyale shi ba akan Jannart da Sarah balle kai dan banzan me idanun a tsakar ka, sai anyi magana kai ta hura hanci kai gaka mara kunya, toh ba zata koma ba kuma sai ka sake min ita na nima mata mijinta gangariya wanda ya fika a kome mara kunya, maza kaci abinci kabar min gidana" Shiru yayi tare da saukar da kan shi, yayi ta lallashinta. Tare da gaya mata shi fa dama bai sakeni ba, kawai ya fadi haka ne ba tare da sanin shi ba, amma tayi mishi Uzuri idan ya kuma ta hukunta shi. "Don Allah Mamah karki manta ni Maraya ne! Ki taimaka ki bani ita, wallahi bazaki kuma jin kan mu ba. Wallahi ba zan kuma b'ata miki rai ba. Don Allah ki taimaki takwaran baban naki!" Daukar matashin kujera tayi ta wulla mishi, tare da nuna shi da yatsa, sannan ta share shi. Karshe ma kin kula shi tayi tare da cigaba da abin da take yi, karshe bayan na gama jera abincin nima nayi wuccewa na d'akina na fada wanka, ina fitowa na sama shi a zaune a bakin gadon, tasowa yayi zai tab'a ni na kauce mishi. "Amma dai kin san babu wanda baya kuskuren, sannan kuma da sani na bazan ce kina wari ba, wallahi haka ba zai kuma faru ba." Tab'e baki nayi na cigaba da gyara jikina, nan kuwa kamar Mayye yake manne min, kasa magana nayi bayan na ture shi. "Don Allah ka kyale ni, ina dalilin wannan abin da kake min, kasan zaka dawo kana yar murya ka d'aga hannu zaka mare ni, ko Uban da ya haife ni bai dake ni ba, ga jaka an haifa maka. Toh don Allah ka rabu dani ai kace ka jima da sake ni don Allah ka bar ni na sami Yancina. Kaje Jay bana son ka, bana son ganin ka. Na gaji da damuwarka. Kayi min matan ka suyi min, ina zaune da kaine sabida kar Dangina su sami abin gorantawa a gare ni ashe kai da kanka zaka goranta, gaya min meye ban maka? Meye laifin na, ba zaka tab'a sona ba. Sabida ka fadi haka, don Allah ka sake min mara nayi fitsari, dan na hakura da gidanka koda zaka min kome ba zan koma ba" Daga haka nayi wuccewa ta, na karasa shiryawa zan fita ya ci da zuci zai fita kallon shi nayi, sannan nace. "Dama kazo rena min hankali ne, ba canzawa zaka yi ba! Dole na rabu da kai. Wallahi sai na baku mamaki da kanta zata dawo min dake kamar yadda ta dauke ko" A masifance ya juyo min jikin shi na rawa. "Naga dan iskan da ya isa rab'anki domin kece numfashina. Wallahi zan aikata kome domin samunki a rayuwata! Ki daina gaya min abinda ya fito bakinki" ya faɗa min a hasale. Nima kuma na saka dariya nace.. "Sai kayi amma aure nayi shi na gama, ai bazawara sai bazawari, saurayi sai budurwa." Sannan nayi ficewa na na bar shi a gurin. Har dare rigima muke dashi, washi gari nice na shirya musu abin karyawa ina gamawa kafin ya tashi nayi ficcewar makaranta. Amma abin dariya ina shiga motar naga ashe ba driven mu bane Jay ne. "Tsaya na fita." "Daga baya kenan, Yar nan. Zamu je yawon cin amarci ne, yar guzuma ta" Ya bawa motar wuta muka bar garin, bai tsaya a ko ina ba sai a suleja. Wani karamin otel ya kama duk da maganar da nake mishi tare da masifa, bai sanya ya kula ni, haka ya kama mana daki, a ciki. Ya tasani a gaba har dakin sannan ya rufe kofar. "Ka mai dani gida! Bana son abin da kake min ka maida ni inda ka dauko ni." Bai kula ni ba, har yayi wanka ya fito, sannan ya tawo gaba na, ya tsaya, tare da cewa.. "Yau ina son mu raba reni ne!" Banza nayi dashi, ina cika ina batsewa, Jay ya sani a gaba tare da tsara ni, tun ina kin biye mishi, har na tafi baki ɗaya, sai da muka zube a gado na fahimci, kuskuren biye mishi, domin ya shagaltar dani da Soyayyar shi ne shiga rai. Hmmm! Wani kayan sai Amale, babban goro sai magogin karfe, gadon hari sai fana, ramin kura sai Ƴaƴanta, a yau Jay ya isa inda bai tab'a tsammanin ba, bai tab'a kawowa zai ji haka nake ba, bai tab'a tunanin cewa Ni din Casssssss nake, sai da ya dagargaje ni dan bakin mugunta ya zata bazawarar ce da gaske mutumin yayi ta wasan kura dani, bai kyale ni ba sai da ya sami nutsuwa fiyye da tunanin shi, a nan ne ya juya yana kallon fuskana, cikin tausayawa, kamar ya mai dani cikin jikin shi ya boye ni, dan wallahi tun da yake zai iya cewa, hmm! Babu wacce yaji ya dauki dogon zango da ita kamar ni, sai kallon fuskana yake wanda ya haɗa gumi sosai. Tare da wasu siraran kwalla da nake fitarwa. "Gaya min taya haka ya kasance?" Ban bude ido ba balle Yasaka ran zan mishi magana, sai ma kauda kai da nayi, matsa min yayi da tambayoyi kuma yana makale dani, karshe da ya bani haushi na fashe da kuka, ina ture shi, da sauri ya rabu dani, tare da bani hakuri. Abun da Jay ba yayi ya baka hakuri tab, sai gashi rana daya Ubangiji ya sauya kome. Duk da yana juna a ran shi, ya gaza furta yanayin da yake ji sai kallona da yake yi kamar zai mai dani cikin jikin, a hankali na sauko daga gadon, na nufi ban daki, ina jin abu na sauka a tsakanin kafana. "Fatimah!" Ya kira suna na da karfi, sabida jinin da ya gani yana bin kafana, yaso ya taimaka min, naki. Amma haka ya nace min, har muka gama wankar, ina fitowa shima ya fito, shiryawa yayi sannan ya fita. Can sai gashi da leda, har nasaka kayana na zauna ya sani na cire mishi wandon, kamar zanyi kuka. Haka na cire, ya gama duba ni sosai, sannan yayi min alluran kashe zafi. Kafin ya dawo ya rungume ni muka kwanta. Duk da na gaji, amma ina son komawa gida. Haka yayi ta lallabani har muka yi barci ina kwance a jikin shi. Karfe biyu na rana muna farka wanka muka yi tare da sallah, duk abin da yake min na kasa sake jiki dashi, haka ya fita ya sayo mana kaya, wasa wasa, ya shiga min wani irin salo, wanda ya sani jin wani irin tsuma sosai a raina. Bai nemi kome ba, amma Tabbas salon shi mai tsayawa ne a rai. Na kasa magana biye mishi nake, da zaran naga zai sab'a Number, sai nayi maza na dakatar dashi. A hankali muke ta shagalin mu, har dare. Kasa hakuri nayi na mishi magana akan ya mai dani gida, cewa yayi. "Ni ban gama amarci ba, idan na gama da kaina zan kai ki." Haka muka kwana, washi gari ne na fadi gaskiya na, domin Jay ya biyar dani, hanyar da ya dace sai da nayi kuka wiwi, sannan ya kyale ni, muna yi wanka. A hankali nake tafiya sabida yadda nake jin jikina. Kasa wani dogon motsi nake ina zubda kwalla. Har na shirya ce min yayi. "Idan baki daina kuka ba wallahi bazan mai dake ba." Haka naja baki na shiru. Har yanzun lokacin ya gama mulkin shi sannan ya sani a gaba muka dawo Abuja, tun a bakin kofar nake tsoron shiga sabida Mamah da fadar da zata yi...🙄😸😹 Honeymoon honeywahala 10/23/20, 10:04 AM - Ummi Tandama: *Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi* Ban kuma tsinkewa da Jay baya yina ba, sai da na fito matar shi ta tsare ni zata min rashin mutunci, Rumah ta dakatar da ita. "Kina wani abu kamar Jahila! Kina hauka akan mutumin da ya kusan kare minti arba'in a cikin d'akin ta.        Haka bai ishe ki ba? Haka bai nuna miki ita ce abin da yake bukata ba." "Rumah! Bana son damuwa, mata ta zo muje." Ya mika mata hannu! Cikin dauki da murnan ta mika mishi hannu. Yadda ya rike ta sai da ta kalle shi.        Suna barin shashin, ya makureta a jikin bango, tare da zare mata idanu. "Wallahi Munih kina kure hakurina, idan na kuma ganin kin zagi Aanih sai na karya miki hannun ki. Wacce bata san ciwon kanta ba."                   Sake ta yayi ta fadi kasa, sannan yayi wucewar shi, sashin sa. Yana shiga dakin shi ya d'aga labulen da yake kallon inda su Aanih take, a sanyayye yake kallon yadda take niman shi. Tana duba ta inda zai ɓullo amma har ta shiga cikin motar babu shi babu alamar shi.   .... Har ta zauna ta kuma fitowa, domin gyara zama. Kamar ance ta d'aga kai ta hango shi yana kallonta, sake labulen yayi tare da juya bayan shi, ga tagar.      --- Tunda na gan shi yana leke na abin ya bani mamaki da al'ajabi, kawai na shiga motar tunda ba zai min amfani ba.           Tunda muka dauko hanyar gida, na shiga damuwa sosai. Domin naga sakon Saif da ya turo min akan gashi a gaban Dangina, ya kawo ƙara na akan abinda muka mishi ni da Jay.         Tunda naga sakon jikina yayi sanyi, na rasa yadda zan gaya mishi abin da min bai kyau min ba. Haka nayi shiru, can naji Ummi tana magana a hankali. Tare da bawa Baabi hakuri.        Can ta kashe wayar sannan ta juyo gare Ni tace min. "Meye amfanin abinda kika yiwa mutumin da zaki aura? Kin ja min Bankad'a  a cikin danginki. Sunce nice nake sanya ki abubuwa saboda d'an yar uwata meye yayi zafi da Mahaifinki yake min barazana akan aurena?"   Shiru nayi tare da sunkuyar da kai na ƙasa, har muka isa sokoto.. Ummi waya take cikin harshen kanuri, ban san meke faruwa ba, amma naji Hanisah tana ce min.         Baabi ya haɗa Ummi da Babanta ne shi yasa take ta magana tana faɗin gaskiya.. har muka shiga cikin gidan. Inda na samu yan uwan Baabi da Saif ana jiran mu, Ummi bata tsaya ba tace zata yi sallah idan zasu iya jiran mu toh.    Tsoto ya kamani musamman da naga dangin mu baki d'aya, har da kakata Ummi.         Bayan mun idar muka nufi inda ake tattaunawar,.ina bayan Ummi. Dake ranta ya b'aci sosai zama tayi tana kallon kowa a wajen tarr.           "Assalamu alaikum jama'a Barkan ku, ba wani abu ya hada mu anan ba, sai magana akan abin kunyar da Fatimah take shirin aikatawa a cikin masarautan nan! Jiya da dare Saif ya kirani yana gaya min Ya kama Fatimah da D'an Sarkin daura da ita suna masha'ar su." Ba iya Saif ba hatta ni sai da muka kalli Bana Annuwar, jikina ya dauki rawa sosai, kamar wacce aka jona min lantarki.           Kallon Baabi nake kam shi a sunkuye, tare da kallon Saif shima na shi a sunkuye, wani irin kuka ne ya kwace min.  Na shiga rantse rantse.         "Wallahi babu abinda ya haɗa Ni da Jay, asalima fada suka yi Saif ka fada musu gaskiya mana"   ..shiru yayi, sannan Baba Annuwar ya shiga fadar wasu abubuwan masu daure kai da muni, wanda sam ban aikata ba, kallon Baabi nayi tare da son ganin shin ya yarda da abin da suka ce, amma yaki kallona.        Nan kowa ya shiga fadar albarkacin bakin shi. Daga nan suka min cin mutuncin akan Jay. Juyawa da suka yi zasu zagi Jay Ummi tace musu. "Baku isa ba! Baku haifu ba, yar ku dai ku mata fada amma duk wanda ya Kuskura ya zaga min d'a ko ya sake kazamar bakin shi akan Jalaludeen. Toh na rantse da Allah sai masarautan nan ta tashi tsaye da kafaffunta.      Sannan kai Annuwar da kake maganar cewa Jay da Aanih suna masha'ar su, kai meye ribar tozarta d'an uwanka a gaban jama'a?   Meye amfanin cin fuska haka, sabida yana da hakuri ko? Sabida baya fada baya kome duk abinda zaku mishi akan ta bazai tab'a cewa kome ba.        Toh wallahi ku kiyayye abinda zai sanya shi yayi magana, kai kuma Saifullah zaka aureta ko ba zaka aureta ba?"     Bakin shi na rawa yace. "Zan aureta!"       "Tashi kar na kuma ganin me kama da kai sai ranar auren ku" da sauri ya mike, yana fita ta shiga gayawa yan uwan mu magana, tare da cin mutuncin su. Kamar yadda suka yiwa Baabi, cikin izza tace musu. "Ban da nima a cikin nima, haramun ne da sai an nimawa Jalaludeen auren yarku muga ta karshen tsiyar ku, kuma a biya sadakin da ba'a tab'a biyan wata mace da shi ba a cikin masarautan nan ba." Korata tayi sannan ta zauna tayi musu wankin babbar riga, sannan ta bar falon abin ta, tana zuwa ta amshi wayar hannu na, tare da kashewa.    Bayan tafiyar ta, nan suka shiga fadan abin da yayi musu, har da cewa. "Matukar  Aanih ta auri yaron nan babu mu babu ita. Taje can su kara ta, dan bazata  ja mana faduwar daraja ba, daga masarautan Zazzau ba."                       "Hmm! Ban san me yasa Rahil take takama ba, ban san me yasa take jin ita wata ce ba, ko ce mata aka yi muma sakarkaru ne da zata zauna yana gaya mana magana, son ranta wato d'an Yar uwanta shine abin burgewa ta kare laifin shi.         Toh Wallahi duk abinda take ji zata samu, dan.." Shiru tayi sakamakon haɗa ido da suka yi da Ummi tazo gurin Baabi. "Hajiya kenan! Da fatan na barki da ɓaɓatu! Duk ba laifi bane, amma kin san kome lalacewar gawar Giwa tafi kwando tara," Gaban Baabih taje suka yi magana sannan ta d'ago kanta. Mik'ewa yayi sannan ya basu hakuri da abinda ya faru. ...... .  Haka da yayi musu ya masifar d'aga musu hankali, nan suka fita daga gidan. Aka shiga yawo damu a cikin Zuri'ar mu.    Su lallai Baabih ya min fada tare da Ummi, shi kuma bai ce komi ba, sai ma zuba ido da yayi.     Abun ya zama rikici da ya janyo aka hanamu shiga cikin gidan kakanmu, hatta wasu abubuwan an hanamu shigar cikin shi, balle kuma irin su Suna da wasu abun. ..... Matar kanin Mamana ta haihu dan haka nayi ta rokon Baabih ya bar ni naje, ni da Hanisah. Muka tafi mun je an karb'e mu hannu bibbiyu. Muna zaune a dakin Ayyah kakanta ta gurin Mahaifiyata. Sabirah da Hoor, suka shigo y'ay'an maza muke dasu, Baban su ke bin Mamana, suna gani na suka fara dariya tare da faɗin. "Makara! Kece a gidan sunan bayan an hanaku fita sabida ana gaya muku gaskiyar da baku so?"       "Shi yasa naga ganku cikin sanin ya kamata, zancen manyan na manyan ne, mu yara ina ruwan mu."inji Hanisah, wata irin B'oyayyen ajiyar zuciya na sauke tunawa da nayi ita din gwana ce a masifa, gyara zama nayi tare da zuba musu ido.          "Ke karki min rashin mutunci!" Inji Sabirah. Budar bakin Hoor tace mata. "Ai gado ba karambani bane, abinda aka sha a non..."    "Ni rawa gadon mai kyau ce? Wasu tasu gadon har abada ba zasu iya sakewa da mutane ba, Ni Yanzun idan Uwata ya zo nan an santa da zafi yanayinta kenan, uwar wata kuwa sai dai kaga ana tattara kome saboda dabi'ar bera gareta."       "Kan uban can! Ni kika zaga?"  Inji Hoor!                 "Bafa zagi nayi ba, wai ina gaya miki gadon da muka yi ne, ke baki fahimtar Yaren ne."     Ai kuwa suka fita, can sai gasu tare da dangin Mahaifiyata, suka shigo zasu dake ta, kallon su tayi sannan ta girgiza kanta, tace musu. "Ko kunya baku ji ba, kun dibo jiki zaku wulakantata sabida an gaya muku karya da Karerayi akan yar yar uwan ku, ko tausayin rashin uwa da bata dashi baku yi. Kun zauna akan abinda aka gaya muku sabida ranku yana sosuwa da SOYAYYA da ta samu a gurin mahaifinta.        Da yau dukiya tana dawo da mutum tabbas Hassanah Ummina zamu bada duk abinda muka mallaka daga masarautan daura har zuwa masarautan shehun Borno, tun duniya tana kwance ahalin mu suke taka rawan gani a kasar nan.           Dukiya mun gan shi mun kuma san shi, soyayyar da Zuri'ar mu takewa Hammah Jay, ya wuce yadda kuke tsammani..akan shi kuke tsanar Mahaifiyata? Sabida son kai da son zuciya, toh ku dake ni, sabida nice nayi magana ba mareniya ba. Ko kunya baku ji ba, ku iyaye kuna fadan abubuwan da basu dace ba akan yan uwanku, wallahi matukar Fatima ta shiga cikin Zuri'ar mahaifiyata sai kun gane cewa shi mulki da dukiya al'amarin Ubangiji ne, yau muna kallon Hammah Jay a matsayin Mahaifiyarshi ce, sabida shi daya ta bari.    Bamu da madadinta sai shi, mahaifiyarta ta rasu ta bar muku  ita, domin idan kun tuna da ita ga madadinta sai ku mata addu'a, amma sai gashi babu wacce kuka tsana sama da ita, da yau ana mutuwa a dawo baku ji kunyar Mameeh ta dawo ta ga abinda kukewa Yar ta ba. Burin ku sunan ta ya b'aci ace sabida rashin amana mahaifinta ya gaza bata tarbiyyar da ya dace. Ku ji tsoron Allah akan zalunci da kuka mata. Allah sai yabi mata hakkin ta, karku manta akwai rayuwa akwai mutuwa.". Daga haka ta riko hannuna zata fita ta kalli Hoor tace mata. "Kuskuren ki tab'a min ji kimata! Shi yasa na tab'a naki, ba kare bin damu!" Daga haka muka bar gidan. Ina kuka Allah yasa ita ke jan motar dan dukkan mu Baabi ya saka an koya mana mota.              "Nagode kanwata Kawata." Na faɗa mata cikin kuka, girgiza kai tayi sannan ta cigaba da tuka mota tana faɗin. "Ban san me yasa baki iya karban kanki hannun mutane ba, nifa ba zanyiwa kowa kuka ba"        "Sabida kuka da gadon taurin zuciya ba! Kuna iya boye kaunar abinda kuke so ba! Da zaki ji yadda nake son D'an uwanki da sai kin tausaya min."   "Mun sani mana, toh ya zamu yi da dangin Baabi? Kin san Ummi ma ba sha tayi a hannun su ba, kawai tafi su baki ne. Wallahi kaf dangin Ummi babu wanda baya mutuntaki, ana ganin darajarki fiye da yadda baki zata ba, ko jiya sai Da Kaka Bana ya tambayi Hammah Jay, akan da gaske yana sonki? Yaki bashi amsa. .da ya bashi amsa toh ina gaya miki sisin gwal ne sadakin ki.      .ko Ni bana tsammanin zan sami sadaki sisin gwal, amma ke naji har kowa ya gama hada kome na sadakinki.. amma mara kirkin nan ya ce baya sonki."      Lumshe idanuna nayi sabida kalmar baya sona ba sabon kalma bace da zan ji haushinta, kalmar ta jima da zame min Alakakai. Bude idanu nayi lokacin da naji ta ja burki.           Ikrama ne ya sha gaban mu, da sauri nace. "Ke tadda motar mu bar nan mahaukaci ne." Sai da ta barshi ya kusan zuwa dab damu, kawai ta finciki motar da masifar gudu, ya kuma koma cikin nashi ya rufa mana.   Da sauri na shiga lallubar Number Saif, ban san na fada kan Number Jay ba, kawai na shiga kiran shi..... Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa.... 07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.... #Mai_Dambu... 10/23/20, 10:05 AM - Ummi Tandama: *_Shiru kake ji... Malam yaci shirwa_* A hankali ya fito cikin motar ya rike hannuna muka shiga cikin gidan. Tana zaune akan daya daga cikin kujerun falon, tun da muka yi sallama ta amsa tare da  kauda kan ta. "Shine kika bishi! Bayan ya gama tozarta ki, a gaban jama'a ya wulakantaki, sannan yace ya sake ki, ...... Idan har yana da damar da zai wulakantaki ba kowa bane ya bada damar haka sai ke! Sabida baki san Darajar kanki ba balle shi yasan naki, ya dibo jiki yazo ke kuma kika bishi wannan wani irin hauka kike yi ne da sunan so? Ka fita ka bani guri, idan na kuma ganin ka, ranka zai b'aci sosai wallahi." "Allah ya huci zuciyar ki! Ayi min afwa amma wallahi ina son Mata ta," ya faɗa a sanyayye, d'ago kai nayi ina kallon shi. Ya gyada min kai. Sannan ya juya ya bar gidan. Ni kuma Mamah ta cigaba da min fada. Daga nan gidan bai tsaya ba, ya wuce katsina, ta jirgin sama, yana sauka, ya kira Murad ya kai shi har gidan da Baba Galadima yake kakan Husnah yaba son suyi magana akan matsalar masarautar su. Daga nan suka juya zuwa cikin gidan sarautar Katsina, anan ya wuni yana ta wasu shirya shiryen yadda zai zauna gana yaƙe. Dan yana son fidda mutum na ƙarshe. Yana zaune yaga wasu yan mata zasu wuce, daya tana cewa. "Ina son zuwa kwatarkwashi, naga jikin Kakata Sahurah." "Kai Aminatu! Itace wacce ta zauna a masarautar Daura ba?" Cikin jin dad'i yarinyar ta gyadawa yar uwarta kai,, har suka wuce. Sauka yayi ya shiga motar, ya nufi garin. ---- Dakyar ya same ta, koda ya isa gabanta, jan tsaki iska tayi sannan tace mishi. "Sun nisanta ka daga Ziryana! Sun hanaka fahimtar inda matsalar take. Sai dai kash sunyi kuskuren, domin yanzun haka kome zai iya faruwa daga zarar ita wacce take haɗe da rayuwarka ta mike da kafarta." Daga nan ta shiga mishi bayanin abubuwan da suka fara da abin da ta aikata, sannan ta kuma jadadda Mishi irin abubuwan da suke faruwa da wanda zasu faru ma nan gaba, ta kuma gaya mishi dole ya nimo mutanen da suke niman rayuwar shi. "Ko zamu tafi sauran dake?" Girgiza kai tayi sannan tace Mishi. "Ni mahakauniya ce! Bani da karfin da zan iya kare kaina, itama Fulani da take hannun ka ba lallai ka koma ka sameta a raye domin sun shirya maka yadda baka yi tsammani ba." Daga haka ya mik'e tsaye, sannan yace mata. "Ni zan tafi!" "Nagode ranka shi dad'e, kayi ƙoƙarin gano waye ki bibiyar ka!" "Insha Allah!" Ya furta a hankali. ---- Washi gari. Ya samu ganin Baba Galadima. Sun tattauna sosai, har ya mike zai bar gidan Baba Galadima yace mishi. "Ka shirya niman wanda baka sani ba?" Juyawa Jay yayi sannan yace mishi. "Yallabai tsaf na shirya niman shi, na shirya cin kaniyar shi, sai na gyara mishi zama, idan na kama shi sai na haramtawa Zuri'ar shi mulki baki daya, sai na fitina kome na shi muje zuwa." Daga haka ya fice daga gidan.. Kai tsaye daura ya wuce abun shi. ---- Tun da ya isa, ya shiga yiwa manyan masarautan, lokaci guda ya shiga amsar duk wani abun da aka yi ba bisa ka'ida ba. Wasu abubuwan ma kawai jin su ake amma Jay ya Bankad'o su. Ana cikin haka Allah yayi wa Ajiya rasu, take aka mai da mutuwar kan Jay, inda suka ce da hannun shi. Sai dai bai ce musu kome ba. Yana sane amma yaki magana abin da ya kuma basu haushi yadda yasa aka kwashe kayan fadar aka kuma saka wasu, abin ya basu haushi domin a garin cire wasu abubuwan aka yi zaro layyu, da wasu abubuwan murmushi yayi sannan ya bada aka kaiwa Baba Magaji. Gefe gudakuwa Ba komai ke damun shi ba sai kewar Yar guzumar matar shi, ta tsaya mishi a rai. Ban da yana matuƙar kunyar Mamah Raihanah ba, da yake ya dauko matar shi, amma cike yake da kewarta. Nutsuwar da ya samu da ita, ba na wasa bane shi yasa yake kuma jin lallai zai koma Abujan. ..... "Jay jiya na sami wannan takardun a hannun Baba Hashim, ya bani kuma abun mamaki sunan Galadima ne ya fito a cikin. Meye alaƙar shi da mutuwar Ajiya dan Abba ya gaya min cewa akwai matsala a tsakanin su. Kafin wannan abun ya fito." Karb'an takardan yayi sannan ya duba kana ya dube Najim yace mishi. "A bisa binciken da nake, Galadima yana cikin magadan masarautan nan! Domin shi kakan shi na uku shine Zulum, Ziryana itace kakar Ammih na uku. Abun da na kasa anan wancan lokacin da lokacin Ammina akan ta akayi rigimar! Wannan lokacin kuma akan wacece za ayi rigimar?" "Eh amma, ina ganin babu mace a wannan karnin da za ayi rigimar akanta shine ya koma akan karagar mulkin ka." Inji Najim, "Nima na fahimci haka," Shiru yayi sannan ya cigaba da dube dube, har zuwa lokacin da suka bar fadar. ..... "Fulani! Dama ina son muyi tsayayyar magana. Waye ya.." . "Jalal ban san kome ba!" Ta gaya mishi haka tare da kauda kanta, dan dole ya hakura ya fita, yana shiga gidan shi, ana kiran shi a waya yazo ga shi an shigo an kashe fulani. Wannan tashin hankali yayi matukar tasiri akan shi, yasan suna fakon mutanen da yake zargi ne, shi yasa. Haka ya isa yaga irin kisan da aka mata, sawa yayi a kama masu kula da kofar ta, yayi ta azabtar dasu, har sai sunyi magana. .... Kusan mutane goma, aka yi ta basu wahala, kuma sun kafe basu bane. --- Tun ranar da ya dawo dani, nake yawan mafarkin gani cikin jajjayen kaya, hannuna da kafana cikin jini ysna zuba. Kaina kuwa wani irin kambun jan zinariya ce, me katon tagulla a gaban kambu. Yau kam ina zaune naga suna jan wani mutum, duba shi nayi naga Jay ne, anje an saka kan shi a saman katako, wani kato ya d'aga adda zai sare shi na fasa kara na farka. Cikin tsoro na duba naga karfe biyu na dare ne, a hankali na sauka naje nayi fitsari na dawo na kwanta, a sannu barci yayi gaba dani. --- Washi gari ina fitowa Mamah Raihanah take gaya min abin dake faruwa. Yaki sauraron kowa . Dan haka ina son nace mata ko zamu tafi can ne ina tsoron kar ta ce na cika damuwa da shi. Juyawa nayi zan fita tace min. "Fatimah! Jay yana bukatar me taimako, barcin da kike yaci ace kin farka, ki taimake mu mana." .kallonta nayi sannan nace mata. "Insha Allah, zan tsaya mishi." Daga haka nasa kai zan fita tace min. "Ki shirya muje." Kaina a sunkuye na gyad'a mata kai, sannan na koma d'akina nayi wanka na shirya, bamu bar Abuja ba sai karfe hudu, koda muka iso yana can gidan horo yaki fitowa. Matsawa Najim nayi ya kai ni har bakin kofar shiga cikin gidan. Da sauri na shiga, na same shi a tsaye ya juya musu baya, ana ta zane mutanen. "Ku dakata!" Na faɗa musu. "Ranka shi dad'e! Meye amfanin haka?" A fusace ya juyo min. Tare da zuba min ido, tattare alkyabar jikina nayi na isa gaban shi, cikin damuwa nace mishi.. "Kazo muje kaci abinci." "Taya? Ya kike son nayi? Ya zanyi da jinin da ake zubdawa ba bisa ka'ida ba?" Ya faɗa min a tsawace. "Amma bayyana fushin ka, kasawa ce! Taya zaka biyewa mutane kana aikata kuskure talakawan kane fa! Kuma mutanen ka da ka yarda dasu don Allah kazo muje, taya za'a ce babu wanda zai dakatar da Kai." Rigima sosai muka yi kafin ya riko hannuna a fusace, ya nufi cikin gidan sarautar bai zame ko ina ba sai a fadar shi, ya juyar dani yana faɗin. "Kalli kujeran da ake zubda jini sabida dashi, ki duba ki gani sabida wannan ake kashe masu yunkurin gaya min meke faruwa, ya kike so nayi?" Naushi ya kaiwa bango Ya fita hayacin sa, sai illata kan shi yake. A tsorace na shiga ƙoƙarin rike shi, kamar mara hankali haka yayi ta jima kan shi ciwo, yana yi yana faɗin. "Sun meye ke damun su? Meye nayi musu, da basu son a fadi gaskiya, yau sati Uku da dawowa daga gurin ki, kin san yadda nake rayuwa kuwa, abu daya ya gaggara, sun Kashe Ajiya. Sunce ni ne, jiya na shiga gurin Fulani Hasiyah sun bi sahu sun kasheta meye nayi musu da zafi?" Ya faɗa da karfi, cikin wani irin tausayi shi, na mike a hankali na isa gurin da yake ta dukar bangon na riko hannun shi, zan hana shi, juyawar da zai yi ya ture ni, Allah ya takaita ban fadi akan kome ba sai akan karagar mulkin masarautan. Mik'ewa zanyi naji kamar an mai dani, cikin kujeran da karfin tsiya. Wani abu da bazan iya cewa gashi ba, yana bin jikina da mugun gudu, wanda yafi na fitar numfashi. A hankali mafarkan da nake yi, ya shiga dawo min. Ji wani abu nayi yana haura min saman kaina, a hankali nake jin kamar ba dai-dai nake ba, ihun mutane da Hayaniyar dawakai suna kara kusanto ni. A sannu nake jin duniyar tana juya min, kome yana zuwa min daki da daki. Tun daga wasu karni har zuwa karnin goma sha tara, izuwa yanzun da kome yake faruwa.(wato tun daga karnin Ziryana zuwa karnin kwarkwarah) Karan bushe bushen algaitu, nake ji. Tare da ganguna, a hankali na bude idanuna da suka rine zuwa jini, wani irin dakiyar zuciya nake ji, bana jin kome akan kowa musamman da na bude idanu naga wasu irin mutane sunyi sahu a gabana. Sannan suka dunkule hannun su, suka saka a gefen kirjin su na dama. Sannan suka zube a gabana alamun girmamawa. "Muna maraba da Sarauniya Aanih Fatimah Khatoon! Sarauniya ta hudu daga cikin al'ummar bani Adam! Kuma Matar korarren Sarkin mu, Jalaludeen Jamaluddin! Muna jiran cewar ki, domin isar da umarnin ki! Ranki shi dad'e shekaru dari uku da ashirin muna jiranki." Kallon su nayi, sannan na kalli yadda kayan jikina yayi ja, hannuna da kafana sun yi ja kamar an kwara min jini. A hankali aka kawo wani tire da wani abu lullube da jan mayafi, suna kawowa suka janye kambun jan zinariya ce, sannan wani dattijo ya dauki kambun da wata sandar tsafi ya daura min a kaina, a hankali kome na jikina yake komawa ja. Juyawar da zan yi naga Jay yana kallona da sauri ya tawo gani na a tsaye ya tun karo inda nake, cillar dashi suka yi zasu far mishi nace. "Ku dakata!" Da sauri ya kuma dawowa ya rungume ni, tare da kallona yana fadin. "Aanih lafiya kuwa?" D'ago kaina nayi zan mishi magana naga kamar abin da ya faru ya b'ace min daga idanuna. A hankali jikina ya sake tare da zuɓewa a jikin shi ina mai da idanuna na rufe, da sauri ya dauke ni, dakyar muka bar fadan. Gida ya kai ni, falon Mamah Sarah, ina sume. Nan suka shiga ƙoƙarin ganin na farka, koda na farkan ma da ciwon ciki tare da yunkurin amai, basu kawo kome a ransu ba, sai ma komawa da nayi ina Barci, shida Mamah Raihanah suka kaini daki. Daga nan ya zauna a bakin gadon yana rike da hannuna. Magayen mafarkan da nake ya hani barci, karshe wanda yafi munin shine wanda nayi ana kashe mutane, sannan Jay shine wanda ake bi zasu kashe shi, haka sukayi ta bin shi garin gudu ya isa gaban wani katon rami, sake biyo shi suka yi na fada ramin, shine suka juyo kaina. Zasu sare ni. Wasu irin halittu, suka far musu. Gurnanin halittun ne ya sani farkawa da mugun kara tare da rike kunne na, ina niman inda zan b'oya. Rungumo ni yayi cikin nutsuwa yana cewa. "Fatimah ni ne, ki nutsu!" Ina ganin shine na kifa kaina a kirjin shi zuciya ta tana wani irin bugawa. "Jay na gaji kullum sai nayi wasu irin mafarkai masu mugun ban tsoro, wallahi na cigaba da haka haukacewa zanyi na gaji!" Shafa bayana yayi sannan ya shiga rarrashina, yana gaya min nayi addu'o'in Insha Allah bazan kuma ba. Alola ya raka ni nayi, sannan muka yi sallar dare, barci ne ya sa stfffffgtfgni dole na tashi, har asuba n .. Fitan Da ya tafi masalaci, bayan an idar da sallah ne ya samu ne Baba Magaji da sauri. "Ranka shi dad'e! Lafiya?" Numfashi yaja sannan yace mishi. "Wallahi Baba Fatima ce take wasu irin abubuwan masu ban mamaki, sannan tana yawan mafarkai masu firgitarwa jiya take ce min ta kusan haukacewa, sabida abinda idanunta suke gani cikin barcinta." Shiru Baba Magaji yayi yana jinjina al'amarin, idan ya kintatta dai dai, Tabbas abin da bai faru a baya bane ya faru jiya da Aanih toh taya? "Kaje kuzo da ita bayan sallar isha.... 10/23/20, 10:05 AM - Ummi Tandama: *Birnin kura Akuya bata dilanci* "Me kike nufi? Me zan yi musu!" Na tambayeta muryana yana rawa, had'iye yawu tayi sannan tace min. "Sun san cewa makarin bame wahala bace, shi yasa suka zabi bashi yaci, sunyi haka ne dan ki kalubalence su, kuma haka shine suke bukata! Idan kika yi magana ban san me zai faru ba amma tabbas abin ba zai miki dad'i ba"   Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, haka yayi matukar tasiri sosai dan ya sanya zuciyar mu cikin damuwa da nazari, d'ago kai nayi na kalleta, sannan na mike. "Meye kuke ganin ya dace nayi?" Na tambayeta, Murmushi tayi sannan tace min. "Karki damu, ba zan iya saka ki ba ke da kanki zaki aikata hakan." Shiru tayi sannan tace min, "ranki shi dad'e. Zan tafi masarauta.". Gyada mata kai nayi, kaina a sunkuye. Kwalla na kuma cika min ido, toh meye na kuka? Lokaci ne da zan kwaci mijina, daga halin da yake ciki. Lumshe idanun nayi sannan na bude shi. A hankali na fito daga dakin ina zaga ko ina, daga nesa na hango Mamah Nana.     Ita da Husnah, banyi mamaki ba. Amma kuma meye suke a bayan gidan, a hankali na sauko daga sama na fita. Tare da bin hanyar da ba zai hada mu dasu ba, na d'an rabe da bango ina kallon su,kamar abu suke tsara wa.                 "Mamah ni fa na gaji wallahi Aanih fa kamar ba mutum ba, wani lokaci sai kiga kwarya idanunta yayi jajjur." Murmushi tayi sannan tace mata. "Karki damu! Baba Galadima yana shiri akanta, fatana dai yaci abincin yau."     Ta mika mata wani kumshe idanuna yana kansu, murmushi nayi sanan na juya tare da barin gurin, bayan wani lokaci ina zaune a falo ta shigo, kamar ba zan mata magana ba, nace mata.. "Barka dai!" Yake tayi min sannan tayi maza ta wuce, yar karamar dariya nayi.             --- Ina fakon ta da zaran tayi girki zata ajiye mishi sai na san dalilin da na zub da abincin, tun tana daukar haka a matsayin tsautsayi har ta fara zargin na fahimci shirin su, ganin haka ni kuma sai na kauda kai akanta.                A hankali fitinar Jay yayi kamari, dan abu kadan za ayi mishi ya hau fada ko yayi zuciya, gabaki daya ya kwayance mana, yau yana zaune shi da ita Munih ta je sunyi fada da shi, tazo tana kuka. Take gaya min halin da take ciki, ga rashin mutunci da ya tsiro mana, sauka nayi na zuba mishi ido ina kallon yadda yake wasa da Maryam wacce ake kiranta Saddiqah.     Kawo mishi abincin Husnah tayi, na zubda mata ido. Tana ajiyewa nace mishi. "Baka kyauta mana! Kuma ka hana mu. Muyi Magana wallahi mu da kake cin mutuncin mu, mune bazamu tab'a cutar da kai ba.         Idan nayi karya ka ce Husnah taci abincin da ta kawo, wani irin B'oyayyen firgici tayi wanda yayi masifar tasiri a idanun ta, sabida na gani sosai a idanunta. "Me yasa kika ce haka?" "Sabida na fahimci cewa laifin mu kake so gani a koda yaushe!"       Kallon Husnah yayi cikin nutsuwa yana jiran me zata ce. "Hamma! Ban tab'a jin a raina na cutar da kai ba, sai dai ban sani ba ko da nake girkin ta turo Zabba'u ta zuba min wani abu.     Dan sau uku ina kamata tana yunkurin zuba min wani abu. Ban gaya maka bane, sabida gudun tozarci daga jinin sarauta, masu ƙarfin iko." Ya karshe maganar tana me kallon cikin idanuna. Lumshe idanunshi yayi sannan ya zuba shi a kaina. Ban yi mamakin abin da tace ba.      Domin fadar da suke ban ga hujjar yin shi ba, amma a haka suke yaki domin kare kansu. "Baki ce kome ba?kin kura mana ido, ki kira Zabba'u." Sunkuyar da kai nayi sannan na juya na koma sama, na kira Zabba'u, tare muka sauko, Jay ya bukaci Husnah ta mai-maita abinda ya faɗa.     Tana faɗa tana Zabba'u ta fashe da kuka, zata rantse na dakatar da ita, sannan nace mishi. " Jalaludeen! Ana ciyar da kai guba! Kuma nayi magana ta juya laifin kan Zabba'u."               "Hamma! Wallahi ka tambayi Munih, ita kanta Aanih tasha bata abu ta zuba min cikin abincin da nake dafa maka." Kallon mu yayi daga Ni har Zabba'u tare da Munih da take saukowa daga sama, rike da baƙinta.          Rashin Maganar Munih shi ya sanya Jay ya amince da abin da Husnah ta fada. "Daga yau kar na kuma ganin kafarki a kasa! Kuma kar na kuma ganin Munih taje gurinki, sannan bayin da aka kawo miki a  maida su bana son ganin su,  na kashe wannan maganar daga nan kar na kuma jin wani ya zo da batun."             Juyawa nayi zan bar falon, yace min. "Nace ki sallami mutanenki" "Naji ranka shi dad'e!"             Kwalla ne ya cika min ido, sannan na juya na bar gurin, ina jin. Kamar na shake Husnah da Munih , banzaye kawai. Na faɗa a raina, haka nayi ta sintiri daga d'akina zuwa falo..kaina ya kulle. "Karki damu! Amma maganar bata mutu ba, domin haka gobe zata kuma kamawa da wuta."        "Akan me? Ba yace a bar maganar ba.!" "Tuba nake sarauniya ta." Tsaki nayi na kwanta, har washi gari naki cewa kome, ina jin bakin cikin abin da suka min, kawai sai ga sako daga cikin gidan wai nazo.     Dama kuma ina kallon yadda kowa yake sunkuyar da kan shi, ina shiga na sami Jay a kwance, ana mishi karin ruwa, a hankali na zauna, tare da gaishe da manyan fadan. Kallona suka yi sannan suka yi shiru, dake a falon bana sarki suke.             "Fatimah! Meye amfanin gubar da kika saka mishi?" Inji Baba Galadima, zaro ido nayi akan shi, kafin na rike bakina, sannan na kalli bakin shi yayi fari. Girgiza kai nayi sannan nace mishi. "Kaji tsoron Allah!" "Ku fito min da Ita!" Fito da Zabba'u aka yi! Jikina ya dauki rawa, domin kuwa sun mata duka na fitar hankali, ta zube a gabana. "Uwar d'akina! Kiyi hakuri sani aka yi." Lumshe idanun nayi sannan na mai da tambayar da Baban Fahad yayi min. "Ke baki haihu ba, sannan baki bar shi ya rayu cikin salama da aminci ba,.meye ribarki."            "Kuyi hakuri! Nayi Kuskure. Ba kuma zan kara ba," cike da mamaki Galadima ya kalle ni, sannan yayi kwafa domin yaso nayi musu, ya sami hujjar da zasu kafa a kaina.        Kuma na san cewa hakan dole ce zata faru. "Zamu haramta miki shiga cikin mutane, sannan bamu yarda ki yi mu'amala da kowa ba, sabida karki kara sa mana shi." "Toh da aljanu zanyi rayuwa, kawai ku janye sharadin ku na farko, shine gaskiyar magana, amma ba makawa wallahi zan yi mu'amala da mutane, idan ta kama nayi da irinka ma zanyi ."          "Kee mara kunya, ki iya da bakin ki,".juyawa nayi na kalli bafaden, da kan shi ya fasa ihu..sannan na nuna Galadima ina kallon Bafaden, nace mishi. "Me kace ma?" "Ranki shi dad'e! Kina da damar kiyi yadda kike so." "Tashi kabar nan!" Da sauri ya mike zai fita aka taɗe shi ya fadi, sai da kashin kafar yayi kara, sannan na kalli Baban Fahad, nace mishi. "Me kace?" "A'a! Ban ce kome ba, kawai abun ya bani mamaki yadda kika iya cutar da mutumin da kike so?" "Ka yarda kenan?"na jefa mishi tambayar, girgiza min kai yayi sannan. Yace min "Bani da zab'i da ya wuce na amsa!" "Haka yayi kyau, shi yasa Galadima zai bawa Fahad Shkurah! Bayan anyi maganar shi da Jannart?" "Wannan tsakanin mu ne! Bata shafe ki ba," Gyada mishi kai nayi, sannan nace mishi. " Zaka iya tafi." Jikin shi a sanyayye, ya fita tare da rike hannu Galadima suka fita daga gidan, zuciyar su na kara ruruwa. Kallon sauran nayi wanda dama su kansu a haɗe yake, jini ne ya digo min a hancina,nace musu. "Kuyi hakuri! Ba zan tab'a cutar da karen Jay ba, balle shi.na amsa ne sabida. Bana son a cigaba da wulakanta wannan baiwar Allah, don Allah kuyi min afuwa zan kula dashi." "Babu damuwa zaki iya kula dashi, amma sarki Kazeem ya nemi da akai shi borno suyi jinyar shi a can." "Don Allah ku barni na bishi." "Zaki iya shiryawa ku tafi tare!" Dan haka na fito daga cikin falon, ina fita suka yi shiru, Abban Jay ya kalli Jay da ya bude idanun shi taree ya zauna, yace musu. "Don Allah wai meye Galadima yake nima dani?" "Kai zamu tambaya tunda kai ne ka shirya ka kuma bamu damar mu zama kananun mutane." Shafa kan shi yayi sannan ya janyo laptop din shi, ya tura musu suna gani, shigowar Najim, ya kara musu bayanin abinda yake ganin ya kamata ayi. "Munih ta zauna a gurin Mamah, ita kuma Husnah zata cigaba da amsar shirin Kakanta ba tare da tasan mun sani ba, sai dai akwai matsala" "Wacce irin Matsala?" Suka tambaye shi. "Dole zan raba Aanih da abin da suke damunta, ku duba na'ura zaku ga tana magana, har tana kuma nuna dagaske akwai wani a kusa da ita. Sannan kadan idan kuka isa zaku ga wani abin mamaki." Aikuwa sunyi mamakin ganin abinda yake son gaya musu, kallon shi, Baba Magaji yayi sannan yace mishi. "Dole idan za a raba ta dasu, zai zama tashin hankali, domin tana faffutikar ganin ka samu kome naka, ita kuma suna kokarin ganin ta koma musu, matukar aka bar ganuwar nan dole zata bisu, idan kuma aka rushe zata rayuwa sai dai zata nakasa, dan ba lallai bane tayi lafiya kamar da." "A'a bana son ko daya, kawai ta zauna dani yafiye min Alkhairin akan ta tafi tabarni don Allah karku raba mu." Ya fada a sanyayye. "Jalaludeen! Kuje ku dawo, amma kai da kanka zaka bukaci haka, domin tayi nisa a mu'amala dasu, tunda tana iya sawa ayi hukunci a can fadar Ziryana." "Taya haka ya faru?" Ya faɗa bakin shi yana rawa. "Ta sakacin ku da ambaton Allah! Gidanku ya zama kango, kowa yana rayuwa a inda yake, babu kome. Har gwara ita, tana mai da hankali akan ibada, shi yasa wancan mutanen basu yi tasirin juya tunanin ta ba, amma da sunyi nasarar tafiya da tunanin ta zuwa ga duniya, zai yi wuya ta iya fahimtar kome akan su. ... Kana tare da ita sai da na gaya maka, karka bari wani alamun ciki ya bayyana a tare da ita, shine kayi wannan kuskuren, har kake tuninanin dakatar dasu, ba zai yiwu ba, sabida ta rigada ta amshi kambun su, kuma abu me wuya kenan, rabata da wannan kambun, cikin ruwan sanyi. Kuje da ita Maiduguri idan kun dawo kazo mu san me zamu yi, karka manta ka dawo nan da wasu kwanaki uku, karka yarda ka wuce haka, sannan itama sayare ka dawo da ita, cikin gidan ku. Kun dai ji....kuyi hakuri don Allah har yanzun sai a hankali 🤦🏽‍♀? 10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: *_Daminan bana ba irin ta Bara bace._* "Da yafi maka!" Har ya juya zai tafi ya dawo da baya, cikin jin haushi riko hannuna zai yi nayi maza na dakatar da shi. "Karka tab'a ni!" "Kee wai meye nayi miki ne da zafi? Na lura haushina kike ji!" Juya mishi baya nayi na cigaba da abin da nake, haka ya karaci tsayuwar shi ya bar dakin. A hankali kome ke tafiya, Jay kuwa, idan zai fita nakan ce mishi, ka dai dage da addu'a, kawai. Idan na fadi haka mamaki yake ji, sai ya tafi zai kuma turo min sako ga abin da yake faruwa a cikin fada Habu da kan shi ya gaya musu shi ya kashe Ajiya sannan ya kashe Fulani Hasiyah. Tun kafin ya dawo gida ya turo min sakon abin ya faru. Tura mishi sako nayi nace mishi. _Ka hana Najim fita daga cikin masarautan nan sannan ka kula da shi._ Sake turo min sakon yayi tare da tambaya na *Lafiya?* _Babu_ na tura mishi sannan na share batun shi. --- Wata na hudu da dawowa, Munih ta sauka lafiya, Yaron kyakyawa da shi, dan har yafi Yar Husnah kyau da kama da Jay, tun da aka yi haihuwar danginta na Nijar suka zo, tare da iyayen ta. Ina sama ake hidima dasu, ranar da ta haihu na tura Zabba'u ta amso min Yaron tace min "toh ranki shi dad'e!" Sannan ta mike da sauri, ina zaune can sai gata jiki a sanyayye, ta durkusa tare da cewa. "Allah ya kara miki lafiya! Gimbiya munih tace ba zata nada Yaron ta ba." D'aga mata hannu nayi da sauri ta fita daga d'akin., Godiya. Ina zaune a gurin da rabon, raina zai b'aci na tashi na nufi d'akina, sauya kaya mai sannan na tako a sanyayye har kasa, dakin Munih na nufa, dan yau kwana uku da Haihuwar. Ina zuwa na kalli matan d'akin. Sannan na zauna.. zuwa wani lokaci na mika mata hannu ta bani Yaron. "Fatimah ni bafa tsoron ki nake ji ba, kawai ina kyale ki ne! Don haka bazan bada Yarona ba duk abinda zaki yi sai kiyi, idan fitsari banza ne kaza tayi mana!" Kallon bakin Munih nayi a hankali na mike daga kujeran dake falon zan tafi d'akina kamar xan mata magana sai na fasa, na nufi hanyar d'akina da sauri kuka nake son yi amma sam zuciyata taki raunana, sai wani irin bushewar za tayi.. Ban kuma lekowa ba,.ina zaune har Jay ya dawo, zama yayi muna kallon juna, a hankali yace min. "Me yasa kike son zama ke daya a dakin ki?" Matsawa nayi kusada shi, a kwantar da kaina, sannan nace mishi. "Jay Haihuwa nake so! Don Allah ka taimaka min!" Juyo dani yayi tare da matsoni jikin shi yana shafa bayana, yana kallon cikin idanuna. Bakin shi ya daura akan nawa. Cikin salon shi na musamman yake cinye baki na. A hankali yake biyar dani Hanyar da ya dace, sannu a hankali jikina yayi sanyi na kuma bi jirgin shi muka nufi duniyar sama. Sosai Jay ya darje ni, domin bai daga min kafa ba, sai da yaga na barshi yayi yadda yake so, sannan ya janye daga kaina, yana me sumbtar goshina, riko hannun shi nayi cikin damuwa nace mishi. "Baka ce min kome ba?" "Toh Aanih Haihuwa dai ta Allah ce ban isa na baki ba sai idan Allah ya baki.. kiyi hakuri da sauran lokaci." Haka nayi hakuri tunda bani da abin da zance mishi, amma maganar gaskiya ina son haihuwa sosai. --- Ana gobe suna da dare, muna kwance shi kam yana dakin Husnah, sai ihun Munih naji da sauri na sauko rike Yaron tayi tana jijjiga shi, Ya rasu. Ihu ta kuma zata fadi na rike ta. "Aanih d'azun na bashi nono na shiga ban daki kafin na fito na sami gawar shi, bayan barci nake don Allah waye yayi min wannan aikata min wannan rashin Imani?" Kallon Jaririn nayi abin tausayi, kai ma sun tab'a ka, kallon yaron nayi sannan na taka har dakin na zubawa kome na dakin ido, a hankali na juya na kalle ta sannan nace mata. "Baki ba shi ruwa ya sha bane?" "Wallahi a'a ban bashi ba!" Karb'an yaron nayi..na kalle shi na kuma kallo matan da suke daki, bugawa su Jay kofa nayi dan dole suka bude na gaya musu. Ina jin kamshin wacce ta kashe yaron amma wallahi babu ita cikin gidan. Juyawa nayi zan fita, ina jin raina na b'aci, har na kai bakin kofa nace mata. "Kiyi hakuri! Jinin shi ba zai tafi a banza ba sai abin miki hakkinki." Daga haka na bar dakin,ina shiga na yanki jiki na fadi babu kowa sai Zabba'u da ta biyo bayana, da sauri ta sauka ta kira Jay, lokacin da yazo ma bana cikin hayacina, abu goma da ashirin. Shi abin mamaki ya bashi taya aka yi aka shigo gidan shi aka kashe mishi Yaro ne bayan shi da kan shi ya rufe gidan. .... Addu'o'in ya fara min, har zuwa lokacin da na sauke ajiyar zuciya. Yana ganin na fara barci ya mike ya fita, haka yayi ta sintiri har asuba, inda ya samu.an shirya Yaron. Allah Sarki, ba yi sunan yaro na sai Jana'izar shi aka yi. Yaron da yaci sunan Sarki Kazeem, aka kashe shi. Bayan anyi sallah aka tafi kai shi makwabcinsa, suna dawowa suka sami Munih ta fita hayacinta, tayi kuka har ta godewa Allah. Abun tausayi ta kasa magana, gashi ta wahala a haihuwar, shi kan shi sai da ya kusan kuka. ........ Lokacin da ya shigo ina zaune kallon shi nayi ya zabge kisar mummuke ake mishi, sun kasa fitowa su mishi gaba da gaba. Kwantar da kan shi yayi akan gwiwata, yana sauke ajiyar zuciya. Shafa kan shi nayi a hankali nake jin kaunar shi na kara huda duk wata kafar dake jikina. A sannu na share mishi kwallar da ta cika mishi idanu, nace mishi. "Saraki! Karka yi kuka! Idan kayi haka nima zan ji babu dad'i." "Aanih ya zanyi? Bana ganin mutanen da suke min wannan rashin Imani, yanzun zuciyata ta gama karayewa a cikin masarautan nan, kema gaki ba lafiya." "Karka daka ta tawa! Domin ni na riga da na.." kallona yayi sannan ya rike hannuna ya zauna, buga kofar aka yi, nace. "Waye?!" "Ranki shi dad'e! Zabba'u ce! Mai Martaba yayi baki ne." Mik'ewa yayi sannan ya kalle ni yace min. "Ina son hutawa amma jama'a ga kuma." "Kaje don Allah!" Haka ya fita, kawai ina zaune naji kamar ance min naje, babban mayafi na dauka sannan na fita ina sauka naji Baba Galadima yana fad'in. "Matsalar ka ai tamu ce, da ka gaya mana halin da ake ciki da mun baka shawara domin ina tunanin masu baka shawara basu baka dai dai, sannan ka janye idanun ka da jikinka akan wasu alamarin da suke cikin gidan sarauta domin haka zai iya tab'a kimarka, tun..." "Tunda mai magana ya san yadda kome yake tafiya ko? Ba laifi bane dan an ba shi shawarar ya janye daga cikin matsalolin masarautar, kuskure a dubi idanun shi ace mishi kimar shi zata zube! Yin haka idan ya kuma faru harshen mutum zan saka a yanke mishi." Na fadi haka ina daga tsaye! Kallona Jay yayi zai min magana na dakatar dashi.. "Ta'aziyar rashin d'an shi kuka zo! Ku tattara ku bar gidan nan ƙafin fushina ya kwace." Na daka musu tsawa, lokaci guda idanuna suka sauya daga fari zuwa jajjur. Kallon kallo muka yi da Galadima! Ya taso zuwa gabana yace min.. "Sarauniyar Ziryana! Tana tare dake. Tabbas dole ayi ta ta ƙare, baki isa ba!" Ya fada kasa kasa, dafe hannun matakalar nayi tare da sake murmushin mugunta, yayi yayi ya taka ya kasa, yana tsayar a gabana, karshe durkusawa yayi cike da bakin cikin yace min. "Nayi mubayi'a," "Ku sake shi. Amma kasan da cewa Ni garkuwa ce ga Jalaludeen, ka cigaba da bashi wahala. Idan na fusata ba zai maka Kyau ba." Da sauri ya fita, zuwa gurina Jay yayi. Jini ya digo daga cikin hancina. Goge min yayi da hannun shi, yana kallon fuskana. "Fatimah! Duk meye amfanin haka?" Juyawa nayi zan bar gurin ya rike hannuna. "Me yasa?" Ya kuma tambayana, "Jay kenan!" Jinin ne ya kuma digowa daga kofar hancina, na juya zan bar gurin ya hauro shima, ya fisgoni na fada kirjin shi kamar zamu fadi. "Ban cancanci sanin kome ba?" Sunkuyar da kai nayi sannan na sauke ajiyar zuciya, nace mishi. "Ina son ka saka ido sosai akan Baba Galadima! Jay zan tafi amma ina son nayi maka abin da zaka tuna dani." Daga haka na juya da sauri na bar gurin shi, ban san lokacin da kwalla suka zubo min ba, jin hannun shi nayi a cikina, tare da saka kan shi kafad'ana. ..."me kike bukata?" Ya tambaye ni, juyawa nayi na kalle shi. "Ina son ganin Baabina da kanena." Zuba min ido yayi sannan yace min. "Bayan su fa?" "Ina son zuwa Maiduguri." Hade goshin mu yayi guri guda, yana kallon cikin idanuna, yana faɗin.. "Kece kwarin gwiwa ta, taya ba zan tsaya miki ba, ina tare dake!" Janye kaina nayi na saka akan kafad'arshi na sauke wani irin ajiyar zuciya, tare da rungume shi sosai. A hankali ya janye ni, muka koma daki hira da muka bude wanda kusan dukkan labarin mu ne da abun da yake faruwa damu, har muka gama, zan tafi madafi ya biyo ni. Ina aikin yana me kara rikon cikina da hannun shi. "Jay! Haka zan rayu babu ɗa ko ƴa da kai." Yadda nayi maganar ya sanya shi jin wani irin tausayina juyo ni yayi sannan ya kalle ni cikin damuwa yace. "Kina son Haihuwar ne?" Murmushi nayi sannan na gyada mishi kai. "Fatimah! Haihuwa a tare dake akwai mugun hatsari ne! Shi yasa amma zan duba abin da ya dace." Yadda yake a dame ya sani fahimtar akwai matsala, sai na barshi a haka. ......... Bayan sati biyu, ya shirya min tafiya sokoto, tare da rakiyar jami'an tsaron har tashar jirgin sama. Bayan tafiya na ne, aka fara shirin aikin ganuwar, wanda Baba Galadima yace ba za a ture ba. Yadda ya kawo dalilan shi Yasaka mutane suka yi na'am da ra'ayin shi. Jay kamar zai yi hauka, haka ya kirani, bai gaya min ba amma daga yanayin Muryan shi na fahimci akwai matsala, dan haka na shiga bashi hakuri da labari. Karshe haka ya share batun, nima haka naji batun. .... Kwana goma nayi a Sokoto, na bi yan uwan da dangina tare da kawayena, dayawan su gani na, ya kashe musu baki, sabida yadda suka ga na sami nutsuwa a rayuwar aurena, babu birkicewa wanda zai nuna damuwa a jikina. Sai tambayana suke meye Jay yake bani nayi kiba haka, murmushi kawai nake, bana cewa. Sabida Allah ya kawo min mafita a rayuwata, naje gidan su Muhid na gaida Mahaifiyarshi, sannan na dawo gida. Ana gobe zan tafi Umman Baabi yayi tasaka aka bani maganin mata, (🙈🙊) kamar me ta kuma koda min na sha, sannan ta bani wani na dawo dashi. Gidan mu nan ma Ummi tasaka min gyaran jiki, sai da Ammih ita kuma ta haɗa min duk wani abun da uwa take haɗawa Yarta idan yazo ganin gida. ........ Washi gari aka kuma hada min kome Baabi ya bani kuɗin wai kar na tambayi Jay, naji kewar su Sosai, kasa boye kuka na nayi SOSAI.. *Kuyi hakuri! Insha Allah mun kusan kammalawa!* 10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: _Ansan da wuyar biri ake daure shi a k'ugu_ Tun da muka fito, daga gidan mu za a kai ni tashar jirgin, na fahimci ana bin mu, lumshe idanuna nayi na kwantar da kaina, haka kawai naji wani abu yana haurowa daga kafana zuwa kaina. Bude idanu nayi cikin wata irin murya nace. "Barde! Tsaya." Kafin mu tsaya sun wuce mu da mugun gudu, "Bazlah, a kona motar da mutanen cikin su"  da sauri Barde ya juya yana kallona, ban d'ago na kalle shi ba nace mishi. "Muje ko!"  Jiki na rawa ya tadda motar muka bar gurin, muna isa gaba kadan muka ga motar ta kama da wuta,.kauda kai nayi tare da mai da hankali na kan wayar hanuna na turawa Jay sakon abin da ya faru.      *Wasu sun biyo ni! Amma nasaka an kona min su* Kira na yayi na .kashe wayar baki daya domin idan bana hayacina bana son a min magana, sai dai Ni na yi maka. Muna isa tashar jirgin sama, Barde da yake tsorace dani ya kwashe min kayana zuwa cikin tashar, daga nan yayi komawan shi gida, tun a hanya ya manta da duk abin da ya faru.                  .... Bayan jirgin mu ya tashi, naga wasu mutane suna kallona, sau daya na kalle su. Na kauda kaina, har muka iso katsina, na samu Najim yazo dauka na, mutanen nan suna biye damu, kallona daya nayi musu naga sun firgici, haka muka dauko hanyar katsina, suna kallona Najim yayi cikin damuwa yace min. "Akwai matsala!" "Kyale su! Zasu mutuwa zasu yi!" Kafin yayi min magana motar ta kwace musu, duk da idanuna a rufe suke sai da nace mishi. "Ka yarda da abin da na gaya maka?"  Cikin wani irin azzaben tsoro yace min. "Eh..eah e.h" "Ka nutsu babu abin da za a maka! Duk wanda yake tare da sarauniyar mu yana cikin kariyar mu." Aka fada mishi haka dai dai kunnen shi. Kamar kan motar zata kwace a hannun shi nace mishi. "Kiyashin gidan ku ba zan tab'a barin a cutar dashi ba balle kuma kai." .... Mun iso daura lafiya, cikin nutsuwa, har kofar gidan ya kai ni na fita. Kallon gidan nayi nace mishi. '"bari a gyara gidan domin akwai ƙura da Datti, zan karasa cikin gidan."    Gyada kai yayi, sannan ya fito zai bude min kofar na hana shi na bude abuna. Na fita, cikin gida sun yi murnan dawowa ta, kowa yaji dad'in ganina, ni kuma ina kewar mijina, kamar yasan ina nan sai gashi nan, tashi nayi na nufi dakin Karama, sai gashi ya biyo ni yana shigowa na rufe kofar tare da rungumo shi ta baya, juyawa yayi yana kallona. "Aanih Fatima Khatoon!" "Na'am Jay dina." Juyo ni yayi yana kallon fuskana, yace. "Nayi kewar ki!" Dariya nayi sannan na rike hannun shi na saka a fuskana nace mishi. "Nafi ka!" "Anya kuwa? Dubi yadda kika kara kiba! Ni kuma fitinar mutane yana hanani sukuni!"      "Sabida ka kasa tunkarar Galadima ko? Shine damuwar ka, ba kowa ba, ni bana jin kome, amma babu ruwanka akan abin da zan yi tunda kai ba zaka iya ba." "A'a! Ke mace ce ba zaki iya dasu ba" kallon shi nayi a nutse, sannan na janye jikina. Zan bar dakin. "Kace ni mace ce? Toh bari na nuna maka wani abu!"  Fitowa nayi dashi har shashin masu girkin su Mamah amintacciyar baiwar su, da take musu abinci ita na je na tsayawa, nace mata. "Umma Hari! Bani ladan kisar da aka saki kika aikata?" A razane ta juyo tana kallona zufa na karyo mata jikinta yana rawa, nace mata. "Zan kyale ki idan kika gaya min suwaye suka saka ki, idan kuma ki ka ki. Tabbas zan sanya ayi ta zane ki har sai kin daina numfashi."           Jikinta ne ya dauki rawa, ta mike a hankali hawaye na zuba mata, na kalle ta wani irin tausayi ta bani, saboda bana tunanin kwadayin ne yasata ta aikata haka sai dalili mai karfi. "Me yasa kika yarda da aikin kisa?"   Kanta a sunkuye ta zube a gabana ta kuma fashe da kuka, tana fadin. "Bani da hanyar taimakawa yarinyar da nake rike da ita bata da lafiya, shine na sami Fulani Nanah na gaya mata, ita kuma ta bani aiki ita da Gimbiya Husnah."                  Kallon Jay nayi wanda yake bayan mu can, naje na same shi, yana kallona nace mishi. "Mutanen nan sun yi nisan da koda ka kama su baka da hujjar, koda bamu mata kome ba, ina tabbatar maka  gobe ba zata kai labari ba, domin ana bibiyarta, idan namu son faruwar wannan al'amarin dole mu tafi da ita cikin gidan mu."   ..."ban fahimci abin da kike nufi ba?" "Hamma Jay!" Karama ta kwala mishi. Da sauri ya juya gurinta kasa magana tayi tana nuna mishi hanya, juyawa nayi gurin Umma Hari, ta kuma sake wani irin kuka, tana me rokona tana faɗin. "Ki cewa mijinki ya hakura da fada da Galadima, sabida taurin kan shi matar Uban shi matar da ta rene shi itace aka sani na zuba mata gub..." D'aga hannu nayi zan mare ta aka rike hannun. "Ki godewa Allah da bata mutu ba, sannan gubar ba me tasiri bane, tana shan danyen madara zata amayar dashi, ban da haka." A fusace na juya ga Mamah Nana, kallon ta nayi. Zan yi magana ta saka min hannu a baki. "Ki bar ni na d"aga muryana, domin Tass nake na aikata kome. Da alamu kina son dan yaron mijinki, dan haka kiyi kaf kafa dashi kafin fushin mu ya ta'azara akan shi, ke kuma hari. Kamar yadda kika sake bakin ki, haka zaki karasa rayuwarki babu harshen magana." "Karki kuskura ki mata wani abu dan zan iya sakawa a.." "Ayi me? Toh bari naga idan kin ji labarin na tura mijinki da uwar goyan shi duniyar mutuwa ya zaki ji, kiyi maza ki dakatar dasu tafiya asibiti domin sunan shi gaw." Rike mata wuya nayi tare da jingina ta da bango. "Duk wanda ya Kuskura ya taba min miji, sunan shi gawa kuma ki jira dawowa na." Da sauri na bi hanya da zata kai ni, gurin Mama Sarah na samu ya bar gidan da sauri. Komawa cikin gidan nayi. Na kuma kowa waje da sauri. Kamar Mahaukaciya. Tsayawa nayi na takarkare na fashe da wani irin kuka, tare da zuɓewa a kan gwiwa ta, Bazlah ce ta bayyana da wasu da ban san su ba. "Sarauniyar ki gaya mana me kike bukata." D'ago jajjayen Idanuna nayi, wanda jini ya kwanta a cikin su. "Husnah! Nanah, Galadima! " Ku kai min su baitul azab, karku rangwata musu, ku shayar dasu madarar azaba, ku horasu babu dare babu rana. Kuyi musu mafi munin azaba, wanda zasu Fahimci girman laifin su. Idan ta kama ayi ta yanka namar jikin su, ana bawa dabbobi suna ce a aikata." "Mun bi umarninki mun kuma tabbatar zamu aikata." Daga nan wasu suka suka tashi zuwa cikin gidan, suka dauki Nanah da Husnah, can wasu suka dawo, tare da Galadima. "Baki son su rayu ne? Ko baki son mahafinki da yan uwanki su rayu? Tunda kin zabi haka bari na tabbatar miki da abin da zan iya aikatawa. Ziryana ki hada hannu dani. Na amshi masarautan. Ni na cigaba daga inda na tsaya." "Bakin Azzalumin ba zan tab'a baka wannan damar ba, zan saka a sake ka sabida Aanih amma ba zan kyale ka ba." Daga nan na mike zan tafi, rike hannuna yayi ina juyawa na wanka mishi wani marin da sai da bakin shi ya fashe nace mishi. "Kul!" Daga nan na juya abuna. "Ranki shi dad'e! Zaki iya rufe idanunki, yanzun haka Yariman da Mamar shi sun isa Asibitin kema idan kika rufe idanunki zamu kai ki can." Gyada musu kai nayi tare da rufe idanuna. "Mun iso!" A kofar shiga asibitin na ganni, sannan suka tsaya a gurin ba iya su ba, wasu ma dayawa suna. Nan a bakin kofar asibitin, har dakin da aka kwantar da Mama Sarah, a bakin kofar naga Jay a tsaya, a hankali na isa gare shi na kwantar da kaina abayan shi, na sake Mishi kuka a hankali nace mishi. "Jay naji tsoron kar wani abu ya same ka." Janyo ni yayi sannan ya riko hannuna, yana faɗin.. "Babu abin da zai same ni facce Allah ya rubuta min a zanen kaddarata dan haka ki daina damun kanki Insha Allah kome zai zo da sauki." Har likitan ya fito, yana kallon mu yace mana Jay yaje, ni kuma na shiga d'akin, na sameta hawaye na zuba daga gefen idanunta, rike hannunta nayi, ta bude ido a hankali ta zuba min su..sannan na tace min. "Aanih kin zo kema? Aanih masarautan Akwai fitinannu dayawa, basu son gaskiya. Gashi nan suka son nasara mu. Ina da yakinin zaki taya shi kafa gaskiya, don Allah." ..... "Mama irin wannan maganar kamar kina rokona ne, Ni kuma kunyar haka nake ji. Zan bawa Jay goyan baya har ya kafa adalci Insha Allah " A hankali take gaya min, sakon Maman Jay, kallonta nayi da jajjayen Idanuna nace mata. "Kiyi hakuri! Ba zamu rusa Ganuwar ba! Yin haka dai dai yake da zunubi domin akwai shugaban mu a gurin,.kuma kar mu kuma jin maganar rushe ganuwar nan,?" Wani irin tsoro e ya kamata, daga haka na juya mata baya, kuka ya tawo min, ina gaya mata cewa. "Zan iya miki kome amma bazan rushe ganuwar ba, domin akwai masu ibadar su a gurin, yin haka zunubi ce Babba." .haka na fita na barta, har Jay ya shigo.. Kwananta daya, aka sallame ta, tunda muka dawo Jay ya saka ni a daki ya hanani fita ko falo sai ya biyo ni, maye ya hanani sakat, tun da yaji yadda na koma akwanakin da nayi a Sokoto, sai wani rawan kai yake shi nan wani ango. ........ Tsakanin shi da Galadima rikice ne ya girmama, dan Galadima ya sako Jay a gaba, nan ya fita hayacin sa, sai da na tafi har gidan Galadima da kaina. Ban same shi ba, wai bayan na, ina tsaye a gaban wasu lambobin girmamawan da ya samu a shekarun shi na aiki ya shigo falon shi. "Da alamu dai kaje ta'aziyar abokin cin mushen ka ne? Koda yake kai da kake da yakinin saka yaro karami gaba, ina kuma shi da yake da goyan bayan Sarauniya irina da." "Aanih Khatoon! Idan da zaki bani hadin kai, me zai hana na ture wancan yaron ai naga ba wani abu zai iya miki ba?" Juyawa nayi gaban shi ina kallon yadda yake bina da kallo. "Me yasa baku iya tsayawa ga abin da yake naku sai kun tab'a rabon wani?" "Fatimah! Kin yi min laifi, amma a hakan nayi shiru, idan na fadawa manyan mutanen cikin masarautan nan cewa Jalal ya auro mace mafi hatsari a cikin masarautan nan ba zaki sha da dadi ba, amma sabida ina yin ki, ba zan fada ba." "Aikuwa zaka mutu baka samu abin da kake bukata daga gare ni ba, dan Ni sabida Jay aka halicce ni, idan kuma kayi kuskuren shiga inda babu hurumin ka, zaka bakunci lahira, domin ba zan tab'a barin ka ba, ka kyale Yaro yayi aikin shi yadda ya fara." "Ziryana ki hada kai dani muyi tsayayya mulki tare!" "Da Aanih Fatimah Khatoon kake magana ba da wata can ba, ka sakewa mijina mara yayi fitsari idan na haka ba, wallahi abin da zai faru ba zan maka kyau ba." *Don Allah kuyi hakuri bamu da wuta ne chajina yayi kasa sosai!* 10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *_Rijiya ta bada guga ya hana_* *ALHAMDULILLAHI MUN GODE SOSAI ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI JIKI YAYI SAUKI... "Baraxana kike min?" Ya tambaye ni, yana me karasowa inda nake, wani irin kallo nayi mishi ya tsaya cak. Ya kasa motsawa, sai zare idanu yake. "Meye nufin ki? Rike ni da kika yi! Toh sake ni Nima zan rabu da mijinki! Ki sake ni nace Ziryana." Juya baya nayi dan a iya zuwa yanzun bana jin kome idanuna sun kad'a jajjur, jini yake d'iga a hancina.                  "Ranki shi dad'e! Nayi mubayi'a!" Juyawa nayi na ganshi duke akan gwiwar shi, dan dukawa nayi ina kallon fuskarshi. "Idan na gadama, zan iya sanyawa a kama min d'an iskan da yake tare da kai, idan kuma naso zan Barka nayi ta matse bakin ka, Kana sake magana kowa yasan halin da kake ciki.           Amadadin gidajen ku ya samu zaman lafiya sai a iya samun tashin hankali da rashin zaman y, ka sani bana da zab'i a rayuwata sama da na bada rayuwata domin Jalal, idan na kuskura na kuma samun wani shirme har naga canji a fuskar shi.            Na rantse da karfin kujeran da na gada, sai tsuntsaye sun tsatsagi namar ka, a samar sahara kamar yadda ka kai shi ka ajiye shi a gurin." Cikin wani irin bala'in sauri ya ke kallon da fuskana, tare da ganin gaskiyar maganar da nayi, Uwa Uba, jinin da yake fita daga hancina.         Cikin tsantsar rashin yarda da abin da yake gani, yace min. "Toh Ziryana ki kashe ni mana!" "Ba zan kashe ka ba! Domin nasan kai ka saka Abdul kashe Ubanshi! Ka kuma kashe Gamji! Ka kuma kashe Abdul din, Kayi a hankali ni ba zubda jini nazo ba.dan haka ka kiyayye abin da zan ce maka.  Kafita harkokin shi" Daga haka nayi feccewar zan bar gidan yace min. "Ya tsawon shekarun yake?" "Dai-daiton da tunaninka!" "Me yasa kika fusata?" " Bazlah ki sanya a mishi horo na musamman bakin shi yana nan!" Ina fadar haka na bar gidan.                ---- Allah ya taimake ni, Jay baya gida dan haka nayi kwanciya ta.      Kwanaki sunyi tafiyar bazata, sati sun koma watanin, watanin sun shuɗe, Shakara ya kuma sako jikin.  Muna dab da fara azumin watan Ramadan. Na fara wani irin ciwon ciki, kasancewar Munih tana dauke da wani cikin, kusan wata biyar, sai ni da nake fama da ciwon ciki.       Ranar da na fara, kamar ba zan rayu ba, haka nayi ta juya. Bazlah kuwa haka suka yi ta kawo min saiwa,ina ganin shi zan fara amai. Data ga haka sai ta dakatar da kome.  Duk suka zuba min ido,  Jay baya gari ya tafi Maiduguri. Dan haka zan iya cewa kamar jira ake ya bar gidan suka dauke ni. ......... Shigowar wani tsoho cikin dakin, ya gama dubani sannan ya cewa bazlah. "Ba zai yi tasha maganin mu ba, domin ita bani Adam ce, kuma Sarauniyar mu, dauke take da juna biyu, iya abin da na gani kece Uwar Fada!" Ya gayawa Bazlah, cikin wani irin farin ciki. Ta kalle ni ina barci wahala sannan ta kalli tsohon tace mishi.         "Ka gama naka,kuma masarauta tayi maka kyauta, kaje kofar taskar masarautar nan a baka zinari da lu'ulu'u."   D'an dukawa yayi sannan ya mata.           "Ranki shi dad'e! A kula da cikin domin zai iya samun matsala, idan da hali a bar bayyana mata masarautan nan, shima cikin a adana shi yadda babu wanda zai san dashi har sai ya kai matakin da ba zai iya salwanta ba.". Jinjina mishi kai tayi sannan tace mishi. "Na baka damar haka, ka gwada sa'arka."         Daukar wani magani yayi ya shafa min akan cikin, sannan ya dauko wani abu ya shafa min a goshina,  ba zata kuma ganin masarautan ba, amma zata na yawan kawo shi a cikin ranta. Idan ta haihu sai mu bar musu abin da ta haifa, ita kuma mu dawo da ita duniyar mu. Amma ki nazarci abinda nake nufi."           "Kaje zan duba abin." Godiya yayi sannan ya bar d'akin, Ni kuma bazlah ta shafa fuskana, sannan tace. "Ranki shi dad'e! Zamu yi kewar ki, muna tare dake domin bawa baki kariya."           Mai dani d'akina suka yi, sannan takira wasu manyan bayinta tace musu. "Ku kula da cikin jikin ta! Sannan ku saka ido, akan wani a cikin gidan. Idan kunga abin da bai muku ba, ku gaya min." Daga haka suka b'ace.            Wuni nai ina barci, har zuwa lokacin sallah, sannan na farka dakyar babu ciwon yanzun, ban daki na mike zan shiga naji motsin ruwa, ina shiga na samu an cika min ruwa har da wasu fure akai, ga kamshin turaren da yake fita a dakin, tunani na ne ya tsaya cak ina niman inda na tab'a jin kamshin..     Wanka nayi sosai, sannan na hada da alola na fito. Lokacin da na fito, naga kayana har da abin sallar, sam ba zan iya cewa nice na ajiye ba, amma kaina ya daure. Kawai na share tare da sakawa na gabatar da sallah. Ina cikin addu'o'in barci ya dame ni ga yunwa. Mik'ewa nayi zan fice falo Zabba'u ta shigo, kallon ta nayi sannan nace mata. "Zabbah ina jin yunwa! Nima min wani abu koda dan wanke ne, domin Allah, a saka yaji da kayan lambu. A dafa min kai a saka a kai."             "An gama ranki shi dad'e!" Ta fita da sauri, ji nake kamar bata sauri dan haka na nufi kitchen ɗin na shiga aikin nima,.tunda muka tsame na farko, na juye a yar kwanon tangaran na fita waje, na cinye shi tass,  na kuma tasowa lokacin har ta gama, tana fitowa na zauna a kasa, hada min tayi sannan na shiga ci a hankali. Ina lumshe idanuna, ga wani abun dad'in da yayi min, ina gama ci na fara yunkurin amai, a hankali naji yana sauka, sakamakon jin ana min fita tare da jin wasu abu kamar ana shafa bayana.              Kallonta Zabba'u nayi sannan nace mata. "Baki ji abinda nake ji ba?" Cak aka bari, "A'a ranki shi dad'e!" Turo kofa aka yi Munih ce da cikinta, zare ido ta fara yi kafin idanunta ya sauka akan kwanon abincin dauka gama ci, dan na saka Zabba'u munci tare.        Allah Sarki kamar wata mayunwaciya tazo ta ɗauki kwanon har tana had'iye yawu, dariya ta bani nace mata. "Ranki shi dad'e! A miki zaki ci ne?" Murmushi tayi wanda ya janyo zuba kwalla daga idanunta, na kalli Zabba'u, nace mata. "Tashi ki hada mata itama, irin namu da muka ci "      "Toh uwar d'akina." Ta nufi hanyar kitchen, kallon yadda Munih take zaune a dame ya sani kallonta a fisge, ba laifi Yar buzayen akwai kyau, kome nata me sanyi ce, kawai matsalarta bata da mutunci ne, ba a bin damuwa bane tana gama ci ya kafta mana rashin mutunci, amma dan nutsuwa akwai shi.          "Aanih Khatoon! Kamar kina da ciki?" Murmushi nayi mata zan ce mata eh sai ji nayi kamar an rufe min bakina, na girgiza mata kai, nace. "Babu kome!". Shiru tayi sannan ta cigaba da jana da hira ina biye mata, har aka kawo dan wanke ta zauna taci sosai. Sannan ta mike zata fita. Naji bana son ta fita sake janta da hira nayi har can wani lokaci, sannan muka sauko tare, ganin mu tare da Husnah tayi ya sanya mata wani irin tsoro, dan haka ta kasa boye b'acin rainta. Zama muka yi a falon muna tab'a hira dasu Zabba'u, Haka tazo ta wuce mu, fuu. Kota kanta ban bi ba.           ...... Ranar da Jay ya dawo a dakin Husnah ya sauka, ban mu san meye ya faru ba, sai kawai ganin shi nayi ya hauro yana huci. "Meye Husnah tayi muku da kuks hada ta da bayinki suka mata barazanar cewa zasu kasheta?" Tashi nayi zan mishi magana, ya dakatar dani, haka yayi ta masifar shi, tsabar ya bani dariya, juya mishi  baya nayi, tare da fashewa da dariya. Fincikoni yayi tare da kallon fuskana. "Ga mahaukaci nan ko?"     Rike dariyar da nake nayi, sannan nace mishi. "A'ah Hamma!" Na faɗa ina dariya. "Wai meye matsalar ki ne? Dariyar me kike min?" "Dalla sake ni, kaje an baka aji garau, tare da tafiya birnin dad'i shine zaka zo kana min ihu, Ni babu abin da nayi mata, kuka babu abinda suka mata, idan baka yarda ba ka tambayi Munih!" "Wacce Munih? Bayan an gaya min kun hade mata kai, keda Muniba, kuka ci mutuncinta."     "Ka godewa Allah, iya mutuncinta muka ci fa." Na faɗa mishi ina kauda kaina, dan na fara jin haushin sa. "Ni kike gayawa magana!" "Toh kayi hakuri!" Tsaki yayi min sannan ya bar d'akin, zan  ci qaniyar Husnah, dan  gidan su. ...... Fushi Jay ya dauka wai yazo yana magana na mai dashi dan iska, har da kai karana gurin Ummin, kirana tayi cikin fada wai na bata kunya, tayi ta min faɗa akan Jay. Haka bai mishi ba ya kuma hada ni da Mamah Sarah, ita kan bata bi bayan shi ba sai ma tambayar shi da tayi akan me ya faru, yana gaya mata, ta harare shi. Sannan tace masa. 'baka da hankali har yanzu, A madadin ka tara su kaji ta bakin kowa shine zaka yanke musu hukunci kai tsaye. Ba ayin haka domin ba adalci bane, kuma zan je gidan naci mutuncin kowacce ce munafukar zan mata diban albarka."       Fadar da tayi mishi ya sashi jin wani abu a ranshi har yake tuninanin dan ba ita ta haife shi ba, dan ko da tayi fadar sai da fuskar shi ta nuna bai gamsu da haka ba,  bayan ya bar gidan ne ya nufi namu..ya sami Munih da Husnah suna faɗa.             Har suna tana gaya mata cewa. "Kiyi fatan ki haihu lafiya! Sai kiyi tunanin fada akan mijin ba wai kina nan miji yana juya muku bayan.." Shiru tayi naja hannun Munih, kawai bazata yarinyar nan ta fashe da kuka, tare da ɗaukar yarta me sunan Mamah Sarah, zata fita daga gidan, kallon ta yayi. Sannan ya zuba mana ido.. "Nagode da kuka ci mutuncin Yarinyar da babu ruwanta." "An cin kaci namu!" Inji Munih, dariya ya bani, nacewa Munih. "Muje kici dan wanke, zan yanka miki har da gurji da ganyen latas."     Juyawa yayi kamar wanda aka aiko shi kaina, zai mare ni. Sai kwashe shi aka yi ya zube a gurin. "Kafin kayi fada dani, ka shirya da kyau." Na rike hannu Munih muka haura sama, muna dariya, tun daga lokacin muka manna musu hauka, bawai na jone da Munih dan na cutar da mijina bane, a'a itama tana fada ne akan mijinta, dan haka ba wani shirin azo a gani bane, kawai abin da Bature yake fada nan ne (Fight for Survive) shine abin da muke tsakanin mu da Husnah, ita dan ta bakanta mu a gurin shi. Mu kuma sai muka hada har dashi muka bakanta musu, idan ya ga ina mishi dariya haushi yake ji yayi ta masifa kafin wani lokaci sun sussuta shi, ya zama wani mara hakuri. Idan aka mishi a fada anan gidan kuma Husnah ta hada shi damu, ba zan mata wani mafarki da nayi ba akan shi, tun da na farka, na taka har dakin Husnah tana ganina ta fara kame kame, sawa nayi Zabba'u, ta daure min ita. Na shiga tambayar ta. "Meye kuke mishi haka? Me ya same shi kuke sanya shi haushi." "Ya rabu da kaka na! Idan na haka ba, iya haushi yake yi? Gaba hauka tuburan zaiyi." " Saketa Zabba! Kika ce hauka tuburan ko?"      Daga haka na fita a dakin hankalina a tashe, shiga d'akina nayi Zabba'u zata bini nace mata. "Jeki!" Juyawa tayi tare da cewa.. "Allah ya huci zuciyar ki!"   Yana fita na zauna kamar mareniya. "Ranki shi dad'e! Ciyar dashi suka yi, ta cikin gida can. Saboda nan an zuba nasa an kwashe, ki bamu izinin mu sanya ta tayi magana mana."     A hankali na d'ago tare da zuba mata ido, sannan na sunkuyar da kai na kwalla na cika min ido. "Bazlah kina ganin babu matsala."    "A'ah akwai! Sai dai zaki yi hakuri ne, dan domin kayi nasara sai ka fadi a gaban abokan gaba! Domin ceton rayuwar shi! Dole ki fuskanci tozarci! Shine makarin...." 😪😓😭😭😭 Alqur'an labari ya sauya ku bani shawara Oum Nass na datse musu na gudu 😜🤣  naji ance Dambuje buje 🤨🙄 10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *An san da Allah bai hana damo shan sanda ba* Tunda na shiga cikin gidan, na sami Munih a tsaye, kallona tayi a sanyayye, har zan wuce ta rike alkyaba ta, had'iye yawun b'acin rai nayi sannan na juya na kalle ta. "Na san ba zaku dawo ku same ni ba, Aanih ga shi abin cikina bai kai na Haihuwa ba da na bar miki, don Allah ki taya ni, niman gafaran Jay, kuma ki gaya mishi ina son shi sosai, Aanih domin kawo karshen wani labari dole sai an gina wani labari." Saukowa nayi daga matakalar, na zuba mata ido, tausayi ta bani. Rike hannunta nayi muka wuce d'akinta, na shiga hada mata kayanta. Har na gama sannan muka fito tare ban iya mata magana ba, zan haura sama tace min. "Kina jin haushina ko? Na san da haka ai, amma idan kika yi hakuri zaki ga rayuwar duniya babu kome a cikin shi sai hakuri da nasara, kafin mutane suyi nasara dole sai sun fad'i, kiji a ranki nasarar da kike son Jay dashi ne ya zo!" Murmushi nayi sannan nace mata, "Babu kome! Insha Allah zan dawo na same ki, kin sauka lafiya." Daga haka na haura sama, ina gama abin da zanyi na dawo na shiga dakin shi na zubawa hotuna na, ido "yaushe aka yi su? Ta ina ya same su?" Abin mamaki bani da mai bani amsa, wasu a Calgary, wasu a Sokoto, wasu ban masan ta ina ya same su ba, yayi yan rubuce-rubuce a jikin shi a hankali na isa jikin wani wanda nayi ana ruwan sama a Calgary, ina rike da lema. Kasan hoton ya rubuta wata yar karamar kalama. *SAU DAYAWA BAKA SANIN WAYE ABOKIN RAYUWAR KA, SAI DALILI ME KARFI YA GIFTA KE ALKHAIRI CE AANIH BINT AARYAAN.* A hankali na shafa rubutun ina kallon yadda yayi wasu rubuce-rubuce a gaban wasu, dama ina haukana ashe shi yafi ni haukacewa taya? Kwalla ce ta cika min ido, a hankali na gama hada kayan, idan nace zan karance wasu kalaman soyayya shaukin soyayyar shi ba zai barni na gama ba, haka na tattaro abun da zan iya na fito muka fita da cikin gidan, juyawa Munih tayi sannan ta kalli gidan, kwalla na zuba daga idanun ta. Rike hannunta nayi sannan fadawan da suke jiran mu, suka kwashi kayan mu. Muka nufi cikin gidan. Na sami Jay kamar yadda na barshi. Jay ya gama da kowa da renin hankali, haka Najim ya kama shi zuwa mota, muka wuce katsina. --- Bayan kwana uku, ban fahimci shiga da fitar shi ba, sai dai na lura da yau yake son barin Maiduguri, kallon shi nayi sannan nace mishi. "Ba dai tafiya zaka yi ka barni ba?" "Me kika gani?" Ya dawo min da tambayana, Jim nayi sannan na kuma kalle shi nace mishi. "Bana ganewa jikina ne, jina nake a daudaure!" "Alhamdulillah! Baki fara shan ruwan addu'o'in bane, kuma kin ce kina son ki haihu, shine aka baki addu'a ko zamu dace da rahamar Ubangiji." Daga haka yaja jakar kayan shi, zai fita. "Tafiya zaka yi?" "Aanih!" Ya kira suna na a gajiye da tambayar da nake mishi. "Ki zauna zan dawo." "Shikenan!" Nace mishi,sannan ya fita da sauri. Tunda muka shigo gidan ake yawan sauka da sadaka, tare da bani addu'o'in, ban kawo kome ba amma na fahimci kodan cikin jikina ne da nake yawan jin naushin. .kafib zuwan su Aanih Maiduguri, Jay ya dauki Munih ya kaita gidan Baba Magaji ya bata ruwan addu'o'in, har zasu fito sai yace Jay ya tsaya. Shine ta fita, Kallon Jay yayi sannan yace mishi. "Na samo mafita! Amma yana da hatsari!" Cikinr zakuwa ya kalli Baba Magaji yana jiran me zai ce mishi. "Ka nisanta Aanih da Daura, Insha Allah za'a dace, idan akayi addu'o'in ranar jumma'a, yau Litinin, gobe ya kamata kubar garin nan, amma kuma idan ita ta rayu kai zaka mutu! Idan kuma kai ka rayu ita da abu cikin sun zama fansa daga abinda aka yiwa Ziryana!" Wani irin zufa ke karyo mishi, kafin yacewa Baba Magaji. "Na amince?" Da haka ya fito, daga cikin gidan suka dawo gidan su, Jay ya kasa barci domin sintiri yake tsakanin dakin shi da falo. Shigowar Husnah dakin Munih yasata mik'ewa, tana kallon ta. Murmushi Husnah tayi, sannan ta ajiyewa Munih wani abu tace mata. "Ranar jumma'a, zaki yi amfani dashi, domin raba Jay da Aanih. Idan kika ki kuma kece zaki rasa shi ne na rigana da na same shi!" Daga haka ta fita, Munih bata tab'a abun ba, kawai dai ta cigaba da kallon abun har gari yawaye, daga nan ta samu ta fita da abun zuwa gidan Baba Magaji. Ta samu bayanan, dan haka ta dawo dashi, sannan ta maidawa Nanah abinta, yawan ganin Jay yana cikin damuwa yasata bin shi har falon shi ta zauna a kusada shi. "Jay! Nasan nayi maka laifi amma ka gaya min halin da kake ciki ko zan iya taimaka maka?" Ajiyar zuciya yayi sannan yayi wani miskilin shiru, kafin ya shiga gaya mata halin da suke ciki, rike hannun shi tayi cikin nata, tace mishi.. "Bafa abin damuwa bane! Kawai kai ka dami kanka, Insha Allah Ubangiji zai kawo mana mafita, ai kun dace da Aanih, kawai ka ji a ranka kana tare da Aanih ka." Daga nan ta koma d'akinta tayi ta kuka, sabida tana jin abun da zata yi shine zai iya bawa Jay da Aanih daman cigaba da rayuwar su, dan haka ita ta kasance a tsakanin su babu wani riba sai faduwa, haka ta kifa hannun ta akan fuskarta tayi kuka kamar ranta zai fita,. Washi gari da zasu bar garin ta sami Aanih tana rokonta ta nima mata yafiyar Jay.. Bayan koma gidan su Mamah, tana kwance tana shafa cikinta, tana kallon agogon bango, takwas, da rabi na safiyar Jumma'a, dan haka ta mike tare da shiryawa cikin doguwar rigar fari, ta cewa Mamah Sarah zata taza ta gaida Baba sarki da Umma. Tana fita ta wuce gidan Baba Magaji, inda ake ta Addu'o'i. Tana zuwa ta wuce dakin Baba Magaji tasamu yana ta Addu'a, A can gidan sarautar kuwa manyan motar rusa gidaje ne aka shigar dashi tun daga shashin bayi ake rusa gidan har zuwa kan tsuhuwar bishiyar tsamiyar da take gidan, duk da ana aikin amma motar suna tsayawa, suke tsayawa sabida motar su haka kawai zata kashe kanta dakyar suke aikin. --- A can gidan Baba Magaji kuwa, wasu abubuwan da ake Munih ta dakatar tare da bashi damar ayi sadaukarwa da ita, duk da yaki amma haka yasa ta bashi hakuri tare da kafewa tace. "Kayi hakuri kawai kayi dani,". .duk yadda yaso kar a sami matsala, dole aka samu sabida bukatar da ta bada, ana sakata cikin addu'o'in kuwa inda suke gidan ya shiga zubda jini sosai, kamar ana yanka dabba, Jay yace su cigaba. ---- A dakin Nanah itama kokuwa take da numfashinta, sabida rashin wadatar shi, karshe duk yadda taso fahimtar da mutane halin da take ciki babu wanda ya gane domin mutuwa tayi, . Haka Zalika Galadima shima a dakin shi ya rasu. "Zan tafi ba zan kuma wai-waiyar Zuri'ar ku ba, Sai dai kaucewa Aanih Fatimah ta rike Gaskiya ta kuma tsayawa mijinta, dan ya tsaya mata. Ya kuma sota, ina kuma baku hakurin tafiya da Munih. Amma ga yarinyar da ta bari dan bazan iya tafiya da rai biyu ba." Daga haka Ziryana ta koma cikin madubin da ta fito, tare da ɗaukar wani abu tayi tafiyar, kafin tayi magana lokacin da aka mai da aikin Kan Munih, nakuda ya taso mata gadan gadan, dole aka mai da ita cikin gidan, inda tasha wahala, sannan ta haifi yarta mace yar karama da ita. Sabida bata kai watanin Haihuwar ba, bakwai kawai takai. Yarinyar tana faduwa ana rufe ganuwar tare da fitar ran Mahaifiyarta. Dama ta faɗa tace. _Domin karshen wani labarin dole a kuma gina wani labarin_. Labarin ta ya tafi, shima Jay yankar jiki yayi ya fadi, tare da aman jini. Zulum kuwa kama shi Ziryana tayi sannan ta saka shi a cikin wani sunduki, suka kai shi karshen wata rijiya da take can karshen Dafur dab da iyakar Madinatul Noor, iyaka da Birnin kisra, aka saka shi a ciki sannan aka rufe shi, sawa Bazlah tai aka dinga zuwa duwatsu a cikin rijiyar tare da shafe bashi labarin. Sannan itama Ziryana suka baje a iska, dama ita fansa haka take. Sabida buri yana zama a zuciya, da zaran aka samu wanda yaji zai iya tayaka yakin da ka gaza yakan shiga zuciyarka yaji meye kake bukata, meye fatar ka! (Wannan shi ne abinda masana tarihin aljanu da dangogin su suka tabbatar, fansan yana rayuwa ne akan muradin ramuwa.) Daga nan Dafur suka nime d'aya daga cikin jinin Sarautar birnin suka bashi rikon kwarya kafin a fidda sarauniyar su, dama dayawa basu son Aanih sai gashi an musu iyaka da ita... --- Ina wanka a ban daki nima na yanki jiki na zube a gurin, ina aman jini, babu wanda ya sani. Sai da Ya kaka taji shiru yazo duba lafiya, suka shigo bude ban dakin tayi ta hango ni kwance babu b'ata lokaci ta fita tare da kiran Gimbiya Zainab, aka tafi da ni asibiti. Tun da aka kai ni, nake kwancen ban san waye a kai na ba, abun ya dame su, ga jinin da yake zuba. Sheikh Amin Kawu yakewa Jay, yana zuwa yaga irin yadda fatar jikina yake tattarewa ina kara komawa ruwan rawaya, yasa aka yi maza aka mai dani gida. Anan aka cigaba da kulawa dani ana min magani. -- Daura Anyi Jana'izar Munih, cikin tashin hankali Jay yake kallon Jaririyar da aka bar mishi, hawaye na zuba mishi, ta tafi ta bar masarautan shikenan haka ya rike yarinyar yayi mata huduba da sunan Munubiya, wanda asalin sunan ta A'isha ne suka boye shi, lokacin da iyayen ta suka ji mutuwar sun dimauta, sosai dan haka suks tawo daga Canada, aka yi addu'ar rana bakwai dasu, da zasu tafi ne suka roki Jay ya basu yarinyar idan ta kara girma ya amsheta, bai hana su ba dan shima zai so haka. Dake da aka yi rasuwar bai shiga gidan shi ba, sai da aka ji kukan Maryam yayi yawa aka shiga aka samu uwarta itama ta mutu, har ta fara lalacewa, amma Allah da ikon Allah inda yarinyar take shan nono, babu matsala, haka itama aka tattara bayan an yafa mata ruwa..aka mata yar Sallah dan wasu sunki yi mata sallah. Aka suka kai ta, makwancinta..yana dawowa ya dauki yarinyar Jaririyar ya bawa Mamah Raihanah, ta tafi da ita akan idan ta cika shekara biyu zai amsheta. Haka gidan yayi mishi fad'i babu Munih babu Husnah, Aanih Fatimah Khatoon kuma tana can itama a halin jinya, a lokacin da kome ya faru, dayawa sun fito sun yi korafin abin da Galadima yayi musu tare da barazanar da yayiwa rayuwa su. Jay ya amsa musu da cewa zai saka a duba Alamarin, Insha Allah zai musu adalci, bayan kowa ya watse a fadar ya rage daga shi sai Najim, kallon Najim yayi sannan yace mishi. "Aanih tayi kokari! Amma Munih tayi Jahadi! Duk wannan abun ya faru ne sabida kujeran mulki. .. kowa nason shi, gashi anyi fadar soyayya an kuma yi fadar akan kujeran, Yau gashi bani da damuwa da kowa,.kasan me ya kawo haka, sabida rashin bawa kowa damar yayi abin da yake so! Dan haka zan bawa kowa damar yayi yadda yake so..kasaka hannu a wancan takardan Zan bawa Fadah Waziri na amsa a hannun mahaifin shi. Kai kuma na baka galadima, na amsa daga cikin gidan su. Sai wani abu da ban sani ba ko zaka amsa, Yar uwata Raihanah da fatan zaka amshi amshi aurenta. Hikmi na bashi Hanisah, Insha Allah zaku ji dadin haka" Murmushi Najim yayi, sannan yacewa Jay. "Amma kai ma zaka." "Na sani! Akwai Inam! Yar Mamah Jamlah, zasu dawo daga Germany. Yarinyar tunda taga Hotona, take kuka. Har ta kai an nima mata Number na,.yarinya ce karama sha biyar ce, na kuma san Aanih zata fahimci ni." *Barka da sabuwar gabatarwa Inam🤣* 10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Kowa ya daka ta wani! Tabbas zai rasa turmin daka tashi* Sake baki Najim yayi yana kallon Jay, jikin shi a matukar tsora ce, ganin babu karya a maganar da yake yi ne, yace mishi. "Ni babu ruwana! Kaje ka sami su Baba sarki, da Abban ka. Kai ko wata guda ba ayi da mutuwar matanka ba ka fara tunanin aure, irinku ne suke jawo mana iftila'in rayuwa a gurin matan mu, ban isa ba kaje can kuyi yadda kake so." Dariyar mugunta Jay ya saka, sannan ya mike suka bi ta kofar baya zuwa cikin gidan, tun da suka shiga falon suka kuma gaida iyayen su, sannan Jay ya Zungure Najim, Najim ya girgiza mishi kal. Jay ya kuma tab'a Najim, ya kuma girgiza mishi kai, duk suna kallon su, can dai Jay ya ce musu.. "Najim ya zo da magana!" "A'a bani bane kai ne!" Sosa kai yayi, sannan ya gaya musu abin da yake bukata,mik'ewa Jaamal yayi tare da Aswad suka bar musu falon da Baba Sarki, wani irin kallo Baba Sarki yayi musu. Sannan ya musu zagin kare dangi kana ya gargad'i Jay da ya bar maganar nan tun a gurin, sannan ya rabu dasu. ......... Yau wata na shida, ina jinya zuwan jay hudu kuma duk yana fushi,ban san laifina ba. Sai dai haka ya matukar tab'a ni domin ciwon kai da jini ne ya sako ni a gaba, kafin wani lokaci na fara kumburi. Dalilin da yasa aka kira shi. Amma Jay bai zo ba sai da ya gama abin da yake gaban shi sannan yazo, yana gani na yace zamu koma, babu wanda ya hana shi tafiya dani tunda Alhamdulillah na warke sosai. Koda muka biyo jirgi, haka yayi ta cika yana batsewa, share shi nima nayi, har muka iso daura. Inda na samu Mama Jamlah sun zo da yarta me mugun rawan kai. Kallo daya yayiwa yarinyar ya shiga cikin nutsuwar shi, sam bata mishi ba. Duk da bai so Munih ba sai dai baya jin zai auri me rawan kai, dan haka ina lura dashi ya fara kaf kaf dani, lokacin da muka isa gidan mu ne naga yayi min fili, babu Munih babu Husnah ko babu kome ai zaka so ka sani abokin sa'in'sa. Share kwalla nayi d'azun Mama ta bani sakon Munih. Tunda nayi wanka na shiga kitchen na girka mana tuwon shinkafa miyar kuka. Wanda yaji daddawa. Habbatu sauda. Curry da sauran kayan hadi. Namar miyar ma daketa nayi sannan na burgeta a miyar kukan. Ni daya na a cikin gidan babu kowa, haka na gama aikina na nufi ban daki nayi wanka sannan na fito, ganin shi nayi zaune ya zuba min ido, shi kan shi yayi kewata amma tsabar shariyar ta motsa, kauda kai yayi sannan ya cigaba da latsa wayar hannu shi, ina budar da gashi kaina, kawai naji an karb'a ya shiga busar min. "A ina ka koyi gyaran gashi?" Na tambaye shi, daukar mai yayi yana shafa min a kaina, a sannu Yaren shi ya shiga sauyawa. Karshen shariya dai ya tafi domin kamar zautacce haka ya koma min. Sai da ya gamsu dani sannan ya koma gefe ya rungume ni yana shafa bayana, dan ma cikin jikina ya takura shi, amma ya samu nutsuwa sosai. "Kin san me?" "Sai ka faɗa!" Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, sannsn yace min. "Wallahi naso kara aure!" Wani abin naji ya tsaya min, a makoshi na shiga kokuwar cire numfashina sai da ya fahimci haka ya d'agani, tare da jinginar dani a allon gadon. "Ban fa yi auren ba! Irin wannan kishin! Don Allah rufa min asiri babu aure a yanzun tunda wancan tsohon sarkin yana raye toh baki da matsala." "Idan ya mutu ina da matsala kenan?" A rud'e ya mike tare da rikicewa, ya ma rasa yadda zai min bayani. Kafin ya min bayan yadda na yarda. .... Yarinyar tana zuwa tayi ta min hauka da shirme, amma ban tab'a damuwa ba, saboda yarinya ce karama, kuma tana fama da fallin balaga, kanta hayaki yake, idan ta shigo kitchen ta dinga min bude bude. Irin dai abun da mutum zai maka ya gundure ka, haka tayi ta min, ni kuma ina jin kunyarta. --- Yau za a saka ranar bikin su Najim, na shirya da wuri, zan tafi gidan sai gada sanye da wata fitinannen gown, ta zuba kwalliya ni kuma ina daman taimaka mishi da links yana tsaye, kawai Yarinyar nan ta danno mana d'akin. Juyawa nayi ma watsa mata harara, nace mata. "Dan gidan ku, haka ake zuwa cikin gidan mutane? Fita idan na gama mishi..." Rike hannuna yayi, na d'ago kai ina kallon shi, a hankali ya zare hannun ya kai tsakanin cikina zuwa k'uguna, tare da kara janyo ni jikin shi, cike da mamaki kawai naji bakin shi a saman nawa, wata irin ajiyar zuciya na sauke tare da rike kwalar rigarshi, muna kallon idanun juna. ..... Kafin kace me yarinyar ta gudu, dama yau ina lura dashi niman hanyar da zai turmushe ni yake sai ga Inam ta kawo mishi sauki, yau naga kayan haushi kamar zanyi kuka, bayana ciwo yake tun jiya kuma na gaya mishi, sai duba ni da yayi yace wai ba Haihuwa bace da sauransu, aikuwa yana gama ikon shi ciwo na danno min kai. A daddafe na samu na shiga ban daki nayi tsarki, har shima ya shigo, ganin ina durkushe ban tashi ba ya taimaka min mik'ewar da zanyi kawai naji abu ya tawo min baƙi daya a hankali nace mishi. "Bari ga wani abu zai sauko min!" A hankali ya kyale ni aikuwa, na rarrumi kafar shi na matse gam, ina kiran sunan Allah, yana son ya taimaka min amma na rike shi. "Yawwa yi nishi," ya faɗa min kamar wanda ya zage ni naji kalmar. Haka ina fama yana kira min nayi nishi, karshe da ya ishe ni nace mishi. "Fita fita! Bana son ganinka, maza waje." Ture shi, a hankali ya riko ni,.muka fito dakin sannan ya dauko matashi ya jera min a bayan, kafin ya fita zuwa dakin shi. .... .sai da ya gama shirya duk abinda zai bukata, sannan ya dawo dakin, yana kallona. Sai nayi yunkurin zan fita ya koma, yana dawowa ya shiga duba ni a hankali, yana cikin dubawa yaji na fara nishi, lokacin su Karama sun zo kirana wai nazo inji Mamah Raihanah. Zasu shigo ya daka musu tsawa suka juya da sauri. Suna isa Karama tace. "Hamma yace mu tafi!" "A'a koran mu yayi,matar shi tana nish..." Rufe mata baki Karama tayi, cikin jin haushi. Sannan ta bangaje ta tare da barin falon, dake bata da hankali sai da ta gaya musu abin da muka mata da kuma wanda suka ji. Ran Mamah Sarah bai yi dadi ba, kawai jikinta ya bata babu lafiya dan haka ta mike tace musu. "Bari na duba su, ko haihu ce!". "Maryam ki kyale su karki ga abin da zai dame ki!" "A'ah babu komai!" Ta fita, da sauri. Tana shigowa gidan taji ina cewa. "Jay ba zan iya ba,.karfina ya kare ni kam ba zan iya ba,.tunda Haihuwar ta gaggara ina ga abokin tafiya ce, Jay ka yafe min," ... Duk jikin shi ya b'aci da jini, ga haihuwa amma babu hali ga abin cikin ya matso babu yadda zai fita, da sauri ta shigo d'akin cikin tashin hankali tace. " Baka da hankali, haihuwar fari a gida, dan kana likita, waye ya gaya maka ana daukar wannan kasadar?" Kiran Mamah Raihanah tayi a waya, suka tawo aka kamani zuwa asibitin shi ne cikin masarautan da aka kammala ginawa, saura bikin budewa, dai gashi nice na farko da za a fara dubani. Cikin minti arba'in ya kira duk wasu masu aiki a babban asibitin daura, suka shigo aka fara duba ni, ana suka tabbatar mishi da cewa. "Matar bazata iya Haihuwa ba, dan halittar ta irin taka ce, xata iya daukar ciki amma ba zata iya Haihuwa ba, idan na sauran matan ya kasance V ne, ita nata W ne, ka Fahimta ai tunda kai ma likitan ne shi ya janyo tsaiko amma Insha Allah yanzun zamu mata aikin." Cikin sanyin jiki suke shiryawa, tare da niman karin kayan aiki, suna kuma tattaunawa akan aikin da zasu yi min, kafin wani lokaci yan uwan da abokan arziki sun cika asibitin, suna tattaunawa..akan aikin tare da tabbatar da dalilin da yasa a za min aikin, ina kwancen ya shigo min, zama yayi a hankali ya rike hannuna tare da sumbatar shi, yace min. "Kamar yadda zasu shiga dake shekaru ashirin da takwas, haka suka shiga da matar arziki." Jan hancin shi yayi, yana ƙoƙarin mai da kwallar shi, tare da jan numfashi, ya kuma rike hannun gam ya manna da fuskar shi, yana kallon yadda kwalla take zuba min, lumshe idanunshi yayi na wasu lokuta..kafin ya bude akai na, "tayi gwagwarmaya! Tayi faffutika, ta tsaya da taimakon namijin duniya, amma koda tafiyar tazo dab- da - dab, sai gashi ta sare, ta kasa." ...hawayen da yake tsarewa ne, ya shiga sauka, sosai sabida jikin shi ya gama sanyi, gani yake itama labarinta zai shafe gani yake kamar bazai kuma ganinta ba, zuciyar shi ta karaya ainun, yarda da saka ranshi ya raunana, a yau yana jin kamar ya cire rawanin sarautan da aka bashi ya ajiye musu, gani yake matukar bai gaya mata wacece ita a duniyar shi ba, ya tabbata asararre mara amfani a cikin al'ummar shi. " Kin tab'a kallon sama? Kin tab'a tunanin yadda Ubangiji ya tsara taurarri? Da ace ina da wata dama,.na jingina ƙaddarata da na jingina na nime taki ƙaddaran ta shafe tawa, na gama sarewa daga sha'anin rayuwa! Na gama karaya daga cikin darasin rayuwa. ... A kowani mata ki, a kowani ɓangare. Rayuwata kara barazana take," yaja wani irin kuka me sanyi. Wanda sai ka matso kusa dashi zaka fahimci cewa kuka yake. Kara damke hannunta yayi cikin nashi. "Ke baki san so ba? Baki san meye ake kira so ba! Kinyi hauka amma ni Soyayyarki anan yake!" Ya taba kirjin shi da hannunta, yana zubda kwalla. "Kinji yadda take bugawa,. Dama ke raine ga raina! Nasan haka ce ta sami ni, tun daga ranar da Hikmi yace min! Jay kana son Yarinyar nan, shi yasa ka hana su Abeel cutar da ita, shi yasa ka damu da kar wani ya tab'a ta! Jay marin da tayi maka hawai cikin k'iyayya bace, Akwai so da kuma sako? Ta isar maka da duniyarta..kayi ƙoƙarin gano ainiyin wacece ita? Idan kuma kayi kyakyawan katari, karka manta da wannan maganar! Kinji ko? Tun daga ranar da na ganki, kika dagula min lissafi, tun da na ganki ko rubutu nake sai an tab'a ni domin ke kawai zan ta zanawa, Ban tab'a kawowa ƙaddarar aure ta haɗa mu ba, sai da Baba sarki ya gaya min shekaru ashirin da daya, mun kasance inuwa d'aya! Taya zan ga matar da aka bani ban da wayo na kasa kare kimarta! Taya zan bari wani ya kalli matar da aka bani tun ina shekara bakwai? Alamarin mu daga Ubangiji ne, shi ya haɗa mu ta hanyar da bamu zata ba, bayan iyayen mu, sun zo junan su, sai gashi muma mun. Kafa tarihi, mun kuma nunawa duniya cewa, Mu ƴaƴan masoya ne! Soyayyar da iyayen mu basu gina ba, sai gashi ya ginu kan mu. Koda na rasa A'isha da Husnah, kuka na ƙalilan ne, amma yau ina kuka ne dan kar rasa ki, Fatimah idan kika fito. Zan iya kiran kaina da Basarake, idan kika sare kamar yadda wancan matar tayi, tarihina ya shafe, duniyata ta wargaje. Mafarkina dake ya rushe, don Allah ki dawo gare ni, shirya sabon duniya sabon rayuwa." Yana kallo aka shigo aka shirya ta, hawaye na zuba mata, bakinta amsa bututun numfashi babu halin magana, riko hannun shi tayi, sannan ya sarke karamin yatsar su, kamar masu kulla alqawari. Kallonta yayi sannan yace min. "Alqawarin Allah gaskiya ce! Allah ya bada sa'a!" A hankali suka turata aka fita da ita, dafe bangon dakin yayi tare da kallon tagar dake dakin kwalla na mishi wasan tsare. A sannu ya goge fuskar shi sannan ya fito daga dakin, yana kallon yadda kowa jikin shi ya mutu, fitowar wata malamar jinya da sauri ya katse musu shirun su, taje ya dawo da wani abu a hannun ta, cikin sauri. Duk sai hankalin su ya kuma tashi, cikin bayan awa daya sai ga kukan jariri, sosai kowa ya sauke ajiyar zuciya, suna jiran a gaya musu me ta samu. Fitowar Dr Fatihu. Rike da kayan aiki shi sai wata Malamar jinya rike da Jariri a farin kyalle, yazo ya tsaya a gaban su, ya mikawa Najim Hannu dan dukkan su kowa ya gama tsorata, yace musu.. "Kuyi hakuri bawa bai tab'a kaucewa kaddarar shi, tun ran gini tun ran zane Allah ya baku hakurin rashin da kuka yi Ubangiji ya...". Sai ganin Jay akayi ya zube..... *Kunsan ba a mutuwa a dawo 🙄🤨 Allahu Akbar! Aanih Khatoon an rigamu gidan gaskiya shi kenan 😭😓* 10/23/20, 10:10 AM - Ummi Tandama: *_Mai rabon ganin... Badd'i ko ana daka a turmi ne sai ya kai_* Kallon  Baba Magaji yayi sannan cikin damuwa, sannan yace. "Ba halin na kawo ta?" Girgiza mishi kai yayi sannan shima yace mishi. "Dole sai zuwa daren!" Da haka Jay ya hakura har zai fita Baba Magaji yace mishi. "Ka kula fa! Karka yarda wani damuwa ya karu mata, dan kamar ita ba zata iya boye tata yanayin ba."     Jinjina mishi kai yayi, sannan yayi tafiyar shi. Tun da ya bar gurin Baba Magaji yake jinjina al'amarin, a hankali ya nufi gida shi da Najim, tun da ya shiga d'akin shi na zaure, ya jima bai fito ba har kusan karfe ɗaya na rana, sannan ya fito jikin shi a sanyayye, zama yayi yace. "Ku bani ruwa na sha" Matar shi ta mike ta kawo mishi, tunda ya sha ya dauke ajiyar zuciya sannan ya kalli matar yace.     "Ziryana ta mutu bata zauna a kujeran mulkin ta ba, Jannart ta rasu bata samu damar zama haka ba, tare da burin Jannart ta kawo sauyi! Yau gashi Fatimah itace ta sami damar zama a kujeran, yau rayuwar ta, yana cikin hatsari." Ya faɗa a sanyayye, "Allah ya kawo musu mafita!" Inji matar shi, haka ya zauna yaci abinci, kafin ya nufi masalacin, tun biyu da ya tafi bai dawo ba, sai la'asar sannan ya kuma shiga dakin shi yau ko Daliban shi bai samu lokacin su ba.         --- Ina idar da sallah asuba, barcie nauyi ya dauke ni ko addu'o'in ban yi ba. A hankali na bude idanuna na ganni a wani daki me dauke da wata irin gado na alfarma, cire kaina nayi daga matashin da nake kwance na  tashi zaune, gadon dauke yake da wani mayafi ja. Tun kafin na sako kafana da sauri wasu yan mata masu sanye da fararr kayan sun tashi tare da bude labulen gadon, kallon su nayi dan kyau ban tab'a ganin mata masu kyan su ba, domin su hadu ne na karshe.        A hankali na zuro da kafana, suka yi maza suka zuba min wasu kyawawan takalma, tare da wasu irin fure me kamshin dadi. Sannan suka mike, wasu yan mata uku suka kawo wani yadi suka lullube ni dashi, tare da d'aga min hannu suka zare min rigar jikina.      Kafin suka daura min yadin, a jikina suna masu cewa. "Sarauniyar mu! Mun gama umarnin ki muke kira!" "Wanka" nace musu, bude min hanya suka yi sannan suka shiga min jagora har gaban wani ban daki, jan wani kujera suka yi sannan suka sani na zauna a hankali, kafin suka wuce ban ɗakin. Tun daga wajen nake jiyo kamshin turaren miski, suna gamawa suka fito tare da cewa. "Mun gama!"  Kafin na mike sun rike hannuna, muka nufi ban ɗakin,  muna shiga suka juya min baya a Sannu na sake zanin jikina sannan na shiga ruwan na zauna. Kafin suka juyo nan suka shiga goge min jina suna wanke min kaina, har muka gama sannan suka kuma rufe min jikina.   "Aanih! Aanih!! Aanih!!! Tashi daga barcin ya isa haka, kinji." Ya fada tare da d'ago kaina jin kamshin tare da jekar da gashina yayi ya sashi zuba min ido, sake tab'a ni yayi na bude idanuna naga babu kowa daga ni sai shi. "Jay ka daina tafiya kana barina! Tsoro nake ji." Daga haka na kuma bigewa da barcin,  wunin yau baki daya. Zan iya kiran shi da a mafarki nayi shi. Dakyar Na samu  na tashi zan yi alola da wanka ina shiga ban dakin naga har an zuba  min kome, shi kanshi ban dakin kamshi yaƙe.        A hankali na fara wanka, kafin na goga sosa zanji an goga min, tare da zuba min ruwa, ga wani irin tsoro ya kamani, a daddafe nayi wankan sannan na yi alola na fito, ina idar da sallah azahr na zauna dan yanzun  bana son kwanciya kar na fara mafarkin.       Bayan isha ya sani na shirya ba tare da na kalle shi ba nace mishi. "Zaka kai ni gurin Baba Magaji ko?" Juyowa yayi cikin nutsuwa da mamaki akan fuskar shi. "Taya kika san da haka?" Ya zuba min ido tare da tambayana na, Sarawan da kaina ya fara ne ya sani, jin wani irin jiri zan fadi. "Fatimah!" Ya shiga jijjiga ni, dakyar na bude idanuna nace mishi. "Ni bazan je gidan Baba Magaji ba" Daure fuska yayi, sannan ya dauke ya ajiye ni a gadon ya saka min hijab, kafin ya tallafo ni muka fita. "Jay! Ka mai dani gida! Babu inda zani!" Na gaya mishi a hankali. Banza yayi dani, na dinga rokan shi amma bai kulani ba, har muka isa gidan Baba Magaji, tun a zauren gidan nace bazan shiga ba. Da karfin gaske ya dauke ni muka shiga kokuwa da shi, har cikin gidan ya dire ni. "Ko da ka kawo ta nan, an ce maka kome zai sauya ne? Tabbas rayuwar ta na mune! Kuma ka saka ido sai mun dauke ta" ina gama fadar haka na zube a jikin shi kuma. Nuna mishi gurin da zai kwantar dani baba Magaji yayi sannan ya kalle shi. "Me ka Fahimta akan ta?" Lashe bakin shi yayi sannan ga gyara zaman shi yace. "Ban fahimci kome sai dai na san tana fama da irin wannan matsalar, haka Baban ta ya gaya min." Kallon shi Baba Magaji yayi sannan yace mishi. " Matsalar daga gare ka ne! Kai ne mafarin matsalar ta, shekaru ashirin da takwas, lokacin Mahaifiyarka tazo min nan domin dakatar da matsalarta." (Mu koma Kwarkwarah) --- "Baba Magaji! Nazo ne akan sha'anin Ziryana da Fairo! Baba ina son a dakatar da wannan bibiyar da suke min, ina tsoron kar su juye kan cikin jikina, bana son matsalar da na samu abin da zan haifa ya fuskanta." Ta kai aya cikin kuka, tausayin jarumar mace irinta ya sani daukar kasadar cewa. "Ki je gida zan nime ki nan da jibi!" Bayan tafiyar ta, na shiga dakin ibada na, na jima sosai har ta kai da mun yi magana da su wad'ancan mutanen, abun da suka gaya min ya bani tsoro. "Magajin Malam! Zamu iya hakura da ita, amma ba zamu hakura da abun cikinta ba, ita bata da hurumi da mu, sabida abinda zata haifa shine zai zame mana abinda muke bukata. Ai ita kan fanko ce! Koda mun dauke ta ba lallai tayi nisan kwana irinta mu ba, da ace Ziryana tana raye ba zamu bayyana kan mu ba, zamu cigaba da zama da ita, amma bata nan kuma gangan jikinta yana cikin masarautan ku, dan haka kuyi kokarin sanyawa kanku hakuri domin kuwa mu ai mun gama kome namu saura abin da zata mahaifa muke jira." Na tausaya mata, domin tana matuƙar son abin da zata haifa, dan haka na roke su da karsu taɓa abin da yake cikin. Dan haka nayi ta faffutikar ganin cewa na dakatar da wannan matsalar amma bai samu ba, daga baya tazo min da wani batun da ya bani tsoro. Ranar da ta gaya min nima sai da nayi jinyar kwanaki sabida wahalar da nasha a hannun mutanen boyen da suke tare da ita. Daga haka na ajiye, batun na zubawa sarautar Allah ido." ..... Shiru Jay yayi, kafin yace. "Meye wannan abun?" Shiru Baba Magaji yayi sannan yace. "Dole sai an ture katangar ganuwar da take gidan bayi, tare da.." Tari ya fara yana kakari, sabida shake shi da Aanih tayi, dakyar Jay ya kwace shi a hannunta, nan ta kuma dawowa kan shi shan gabanta yayi. "Karki tab'a shi! Idan har ni ne zan iya kawo karshen rikicin masarautan na yarda kashe ni!" Zuɓewa tayi a gurin, ta koma barcin ta, sannan ya koma kan Baba Magaji, ya dauke shi ya fito dashi cikin gidan, kafin ya fito gurin Aanih. Sai da yayi musu bayanin sannan ya fito gurinta. Abin mamaki babu ita babu dalilinta. Da sauri ya leka waje, ya ganta a zaune, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya zo gurinta yaga tana kallon sama,, rike hannunta yayi yaji yayi mishi mugun sanyi. Da sauri ya sake ta, yana kallon yadda take zaune bata kalle shi ba. "Fatimah! Muje gida!" Ya fada mata a hankali, mik'ewa tayi suka fara tafiya, a sanyayye suna isa Munih tana fitowa daga dakin ta. Kau da kai tayi tare da jan tsaki, zata bar gurin, cak ta tsaya tayi tayi juyawa tayi, abin mamaki Aanih ce a bayan ta, "ki godewa zuciyarki da bata kai ki ga aikata shirme ga Sarauniyar mu ba, da yau sai kin haifi abin cikin ki bai isa Haihuwa ba." .... Daga haka ta koma hanyar sama, tana ganin kulewar Aanih sannan taji kafarta an sake shi. .. tun daga ranar kome na gidan ya zama wani iri, cikin dare Idan Jay ya kwanta ko a dakin wata, toh shi zai yi barci babu wani abu, amma daga Husnah har Munih basu iya barci, gwara Munih ana d'aga mata kafa, sabida cikin jikin ta. Amma Husnah saka yarta barci. Ita kuma a sakata a gaba har kusan asuba, Munih kuma kafaffunta ke matsewa ana ja, washi gari ta farka kafaffuna suna mata ciwo, --- Bude idanu nayi cikin nutsuwa nagan ni kwance a wani daki, kome na ciki ja da ratsin ruwan gwal, a hankali na mike zan tashi, sai ga mata hudu suka zube a gabana tare da cewa. "Ranki shi dad'e! Umarnin ki muke jira!" "Ina ne nan?" Na tambayeta, "Nan daular ki ce! Al'ummar ki suna jiran ki, ana bukatar zuwan ki." ...... Ban daki suka kai ni nayi wanka sannan na fito, a hankali suka gani na suka shiga ciro min wasu kayan sawa, ana ajiye min, ana kuma dauko wasu manyan dogayen riguna, kallon wata doguwar riga nayi sannan na nuna musu shi. Da sauri suka sauko turarruka zasu shafa min nace musu. "Karku shafa min masu ƙarfin kamshi, ina bukatar marasa karfi sosai, wanda iya hancina zan ji." "Ran ki shi dad'e an gama!" Haka suka gama shafa min, sannan suka saka min kayan, a gaban madubin naga yadda kirjina ya fito na kalle su nace musu. " Ina bukatar mayafi! Sannan mijina fa?" "Ranki shi dad'e! Za ayi yadda kike so! Batun Yarima Jalal! Ba a bukatar shi a masarautan nan, domin an sha gayyatar shi nan yana kin zuwa." Ina gama saka kayan nace mata. "Ina son mijina anan nace! Idan ba haka ba zan saka sare min ke!" ",Tuba nake sarauniya Aanih ba zan kuma ba" daga nan ta fita da sauri. Bayan kaman minti goma sai ga su tare da wata tsohuwa. Ta shigo kallon juna suka yi sannan tace mata. Dukawa tayi ta gaishe ni, sannan tace min.. "Bazlah!" "Na sani! Meke tafe dake dan zan shiga fadar ne!" Na faɗa kai tsaye, "Ranki shi dad'e! Akan Yarima Jalal ne! Masarautan nan tayi mishi Shamaki da shigowar shi cikin ta, sabida ke ake bukata zamu iya mai dake gurin shi ba wai dukka ba. Dan muma al'ummar mu suna bukatar ki!" Kura mata ido nayi sannan na rufe jikina. Muka tafi a hankali duk kofar da muka wuce sai masu tsaron kofar sun zube kasa. Wata ƙatuwar Fada muka isa. Inda ake ta muhawara tsakanin manyan Fadar.. "Taya zaku ce bil Adam ne zata mulke mu! Bayan bata da alaka na jini da masarautar Dafur? Idan an bawa Sarauniya ZIRYA damar zama sarauniya sabida ruwa biyu ke yawo a jikinta, Aanih Fatimah Khatoon kuma wacece ita? Bama bukatar bil Adam a cikin daular mu, domin zata iya zab'ar son zuciyarta sama da al'ummar ta. Idan kuma kuka dage sai ita Toh Tabbas zamu bukaci a sare mana kan Yarima Jalal! Shine Yarima na goma sha biyar dake bin bayan Aanih Fatimah Khatoon! Sarauniyar zubda jini! Yayi muku ko kuma me zaku ce!" "Ba za a kashe Jalal ba! Amma kuma ni zan rike Aanih Fatimah Khatoon! Ziryana Burbasa Fairo..... Chaiiii 🤦🏽‍♀️? 10/23/20, 10:10 AM - Ummi Tandama: *_Banza ta kori wofi_* "Itace zata ta rike abin da na kasa! Itace zata iya abin da banyi ba, dan haka kar naji wani yace bil Adam bazai iya ba, ina kuka kai rashin imani irin na d'an adam!? Ina kuka kai rashin tausayin irin ta d'an adam!.... Shiru Aanih tayi sannan ta cigaba da cewa. "Zata iya! Tabbas zata iya! Nasan zata iya!." Tun tana fada da karfi har ta daina karshe na zuba a gurin ina kiran "Jay!!!" Kafin wani irin barci ya dauke ni. "Bazlah ai sai ki maida ta, d'akinta." Sunkuyar da kai tayi cikin girmamawa tace. "Ya shugabana ina niman Alfarmar ko za a maida ita gurin mijinta, inda yaso sai ayi ta bude mata idanu, amma ku duba Alamarin da idanun basira!" ... "Wannan maganar ki gaskiya ne, a maida da ta a dawo da bazirqa!" Gyad'a mishi kai tayi cikin girmamawa, sannan ta dafa goshina tayi wasu kalamai sai ga mu a cikin d'akina, a kan gado ta kwantar dani, sannan ta shafa cikina tana faɗin. Yana yin bai nuna akwai wani abu a tare da ita ba da zai tabbatar musu da ciki ne da ita.. A hankali take shafa kai na, sannan tace. "Mun barki lafiya! Sarauniyar mu!" Daga nan suka b'ace baki abin su. ......... Farkawa Jay yayi ya ganni kwance, dan d'azun dake bazirqa ce, yayi juyin duniyar nan tazo ta kwanta, amma fir taki. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya shafi fuskana, tare da shigewa jikina yayi tare da gyara min kwanciya, a jikin shi. Bayan yayi fatali da rigar jikina. Da asuba, muka farka kunna wutar gadon yayi tare da leka fuskana, ya duba agogon gefen gadon, huɗu da minti biyar. Shigewa yayi jikina sosai yana kallona, tare da kallon yadda nake yatsina fuska, a hankali yake bin ilahirin jikina, har ya kai na ture hannun shi. Tare da zuba mishi ido. "Aanihhhhhhhh! Don Allah karki min horo da hakkina." Yadda ya kira suna ya sani jin wani irin. Shiru nayi tare da lumshe idanu na.. Ina jin shi yana kidar shi, har zuwa lokacin da ya samu nutsuwa dani, gumi nake zubawa. Sabida turmushe da yayi. Gyara min kwanciya yayi tare da shafa kaina, a sannu na mike tare da barin gadon nayi wanka da alola tsaf sannan na fito. Kallona yayi tare da isowa gabana ya zuba min ido, kauda kaina nayi, na wuce na shiga niman kayana na saka, sannan na gabatar da sallar nafilla, shima yana fitowa ya nufi masalacin. .........bai shigo ba sai karfe bakwai saura, yana zuwa bai ce min kome ba, yaja alluran da ya shigo dashi ya kalle ni ba tare da yace min kome ba, ya koma ta baya na zai min sai lokacin nace mishi. "Karka fara dan bana so!" Bai kula ni ba, ya min alluran. Sannan ya fita ya bar ni a gurin. Har dakin shi ya koma ya shirya, kafin ya dawo har barci yayi gaba dani, bai tsaya yayi feccewar shi. Sai gurin karfe biyu na rana ya dawo ya samu na farka, ina zauna akan abin sallah. Mika min kunun gyada yayi wanda ya amso min daga cikin gidan. A hankali na ke sha. Kallona yayi sannan yace min. "Meye matsalar ki? Bana son shirun nan." Kallon shi nayi na wasu lokuta, kafin na sunkuyar da kaina kasa. "Jay! Kawai ina hango tarin banbancin dake tsakanin mu ne!" "Kamar Ya?" Murmushi nayi me ciwo, sannan nace mishi. "Kawai ina jin ba zan yi nisan kwana bane! Domin nasan dole zan rabu da kai. Akwai mutanen da suke son ganin bayan ka! Amma yanzun ba zasu iya ba. Ban sani ba, amma ina da tabbacin, wani zai zo da tuhumar laifin, idan suka zo ka basu wannan." Karba yayi yana kallona baki sake, sannan zai magana na d'aga mishi hannu. "Mutanen da ake hukuntawa basu da laifi! Mai Baya cikin masarautar, sannan wanda yayi laifin yana cikin masarautan. Ga wannan shima ka bawa Habu!" Daga haka na ajiye kofin kunun, na zuba mishi ido. "Jay! Duk abin da zaka yi ka tabbatar da gaskiyar, domin gaskiya bata karewa, amma karya tana karewa a duniya, don Allah karka.." Tashi yayi tare da barin d'akin, jikin shi a sanyayye, yana son Aanih amma tsoron kar wani abu ya same ta shine burin shi, lumshe idanunshi yayi can ya kuma dawowa ya dame ni a kwance. Karb'an kofin yayi ya kalle ni, ajiyar zuciya ya sauke, ganin yadda nake barci, ciro Alluran yayi ya min, sannan ya fita daga dakin. Cikin barci na farka sabida ciwon ciki, a hankali na nemi tashi zaune na kasa sabida jikina yayi min nauyi, idan ban ƙaryata kaina ba, kamar abu ne ke zuba a jiki, ina cikin wannan tunanin sai gashi ya shigo ganin halin da nake ciki ya sa shi sauke ajiyar zuciya, sannan ya taimaka min bayan yayi min wani allura, ya taimaka min nayi wanka, sannan ya hadu min ruwan zafi nasha, sannan ya bani magani, sai da ya tabbatar nayi barci kafin ya fita. Wanke kayan da ta bata yayi sannan ya dauki kayan cikin ta Yar karamar wando da dan kamfen ta ya zuba a wani baƙin leda ya haƙƙa rami ya jefa, sannan ya dawo cikin gida, ya gyara ko ina, yana aiki Zancen da suka yi da Baba Magaji na dawo mishi. "Toh baba taya zamu kare lafiyarta da rayuwarta? Wallahi tausayi take bani!" Girgiza mishi kai yayi sannan yace. "Hanya daya! Kar ka bari ciki ya shiga jikinta, tunda suka fara bayyana ta sanadin zama a kujeran toh karshe idan suka fahimci zamu raba ta dasu, zasu shiga niman daukarta ko kuma su kashe mu baki daya." "Ba dai har da ita ba?" "Eh toh idan ta kama haka za su iya aikawa" jikin Shi ne yayi sanyi, dan haka yana barin masalacin, sai da yaje ya sayo alkura. Yayi mata nafarko, kuma bata tambaye shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya cigaba da zama a d'akin ta, yana zaune yaji motsin mutum a saman yana lek'awa ya hango Munih yayi dan haka ya share ta, ya cigaba da zaman shi a d'akin.. --- Washi gari.. Da taimakon Husnah ya shirya, ya fita. Ina kwancen naga kamar ana shigowa da fita a saman kuma da gudu ake kome. "Waye?!" Na daka tsawa, cak aka kuma daina, sannan nayi kwanciya na, ina kwance kawai na kuma jin wannan gudun, zanyi magana aka ce min. "Kee ƙamar mara kunya! Yau..." Kwala ihu aka yi, barci ne yayi gaba dani, bud'e idanuna nayi na ganni a zaune. Samar kujeran. "Wayyo mun tuba!!" "Ranki shi dad'e wannan shine gulab, ranki shi dad'e! Me zamu mishi?" Kauda kai nayi nace. "Ku Azabtar dashi mafi muni? Karku sassauta mishi, har sai ya fadi suwaye suka aiko shi." Daga haka na mike zan bar gurin, kamar wacce aka yasha a barci haka na bude idanuna akan wayata da take haske. Dauka nayi tare da sakawa a kunne. "Aanih! Kamar yadda kike ce Habu ya amshi zoben shi da wannan igiyar, toh ku kai shi inda zai baku bayani a nutse domin kuwa yana cewa zai magana a gurin sai gawar shi, Habu yayi muku illa sosai, domin shi ya karb'owa Fulani Hasiyah maganin da matan Abba ba zasu tab'a haihuwa ba. .... Yana da wasu abubuwan da zai fada muku, idan kuka kaishe karku ce yayi bayani zai yi da kanshi." Kashe kiran nayi na kwanta, ina jin babu dadi, kawai na share ina kwancen har aka kira sallah, shiru nayi na wani lokaci kafin na nufi ban daki na duba jikina har yanzun da akwai jinin, madafi na wuce nayi mishi abinci, dan na san gobe zai koma dakin Husnah, wacce da muke kirki da ita, yanzun kuwa kaf kafa take dani, Bata son mu hadu ma. Uwar marasa mutunci ne dai idan ta ganni koda zata ji wani abu sai ta harare ni. --- Ina idarwa yana shigowa gidan, a hankali na gama kome na fito na same shi ya fito wanka, a d'akina hade hannuna nayi a kirji nace mishi. "Yallabai sarki! Baka da daki ne?" "Ina dashi amma ana mata na nake son yin uzurina ko zaki hanani ne?" Ya kafe ni da idanu. "Gaskiya ana shiga hakkina, kuma wallahi kayi na karshe ka zauna a dakinka duk macen da take da bukatar ka ta bika ba kai zaka bi mace ba, meye amfanin turakar, haka kawai a hanani sukuni, ni gidan ma yayi min kaɗan, Yawwa domin d'akina na Dafur ya ci uban wannan da nake ciki sau biyar, kar na kuma ganin kafarka, kuma ka jawa matan ka kune, wallahi na kuma ganin wata ta turo min shirme zata gayawa makotan su, Babu abin da ya dame ni. Mata zata ji a jikinta ne, kuma kuma ka dai ja musu kunne." Cike da Mamaki yake kallona sannan ya sauke ajiyar zuciya yace min.. "A takaice ki ce min kar na sake zuwa miki daki, bawai ki kawo dogon magana ba, tunda bani da gata shi kenan..🤦🏽‍♀? kuyi hakuri gaskiya na gama gajiya 10/23/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: *A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.* "Ka kyale ni, bana son damuwa tunda ni ban ya kula da kai ba, kaje ka sami matan ka, tun...."           Murza hannuna yayi a hankali, tare da d'ago kaina. "Ke kam! Yaushe zaki daina kukan banza ne? Dube ki katuwa, dake kike kuka, idan kika cigaba, zan ga yadda zamu yi dake, nan gaba. Toh ba zan kuma maganar su ba, saboda karki yi min yaji na rasa inda zan fake." Kifa kaina nayi ina jan majina,  murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa. "Tun haduwar mu nake jin na zama magananne! Toh meye na jan majina kuma."         Shigowar Abba da sallama, da sauri ya juya abin shi, yana murmushi. Kunya ta sani saurin kwace kaina. Na shiga ban daki da sauri. Hannun shi biyu yakai wuyar shi tare da sakala hannun, ya sake murmushi, me cike da jin wani irin farin ciki.     Sannan ya buga min kofa yana fad'in. "Zaki fito ko na shigo" da sauri na bude kofar ina zare idanuna, a hankali ya fincikoni, kirjin shi yana kallon yadda nake murmushi. "Kina da matsala!"  Kiciniyar kwace kaina. "Toh kuma! Me aka yi? Kina son kirkiran rikici." Cikin jin haushi nace. "Kace ina da matsala!" Waje yayi da idanun shi, sannan yace. "Akan wannan al'amarin shine kike fushi? Toh ranki shi dad'e, ba zan kuma ba."               Juyawa nayi zan koma bakin kofar dan na san Abban shi yana gurin, yayi maza ya dawo dani jikin shi. "Hala kun hada danganta da mage ko?"     Gyara rikon yayi sannan yace. "Tayu kece magen ba!" "Saraki! Abba yana waje fa." Sako kan shi yayi kafada na, tare da faɗin. "Ina zan sani, kin same Yaro qarami kin sanya shi a lungu kina lugwaigwaita shi!"    "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Allah ya shirya ka." Na saka kai na fice bayan na saka hijab dina, baya asibitin baki daya, har zan shiga wani mutum ya mika min wata jaka. "Inji mutumin da kuke zaman jinya dashi, wai na baki." Amsa nayi sannan na duba, jakat akwai kudi sannan yar takarda. Ciro takardan nayi sannan na bude.. _Duk wani abun da kike bukata daga ke har shi, zaki iya amfani dashi kafin ku dawo, sannan ki gaida min shi zan koma tunda jikin yayi sauki._           . Sarki Jaamal... Kunya ce ta kama ni, ina shiga dakin ya dauke ni cak ta baya, zuɓewa kayan yayi, na saka yar karamar kara. Dariya yayi sannan yace min. "Matsoraciya kawai! Ina Abbana?"        Juyawa nayi na kalle shi, kafin na sami damar bashi amsa, nace. "Ya koma gida." "Allah Sarki, Abbana kamar kasan Yaron ka yana son girma". Girgiza kai nayi na barci a gurin, Hannun shi ya saka a baki, kamar me nazari kafin yace. "Abba yace min lokacin da ban da lafiya binki nake kamar jeka" Juyawa nayi tare da zuba mishi ido, sannan na juya na cigaba da abinda nake yi, a sannu ya tako, yana zuwa bayana kawai ya kwanta a bayan, ban san lokacin da na sake kwalbar hannuna akan kafana ba, da sauri na daka tsalle. Ina yarfe hannu na. Idanuna suna cika kwalla.            Cak naji yayi sama dani, a bakin gadon ya ajiye ni. Sannan ya rike kafar a tafin hannun shi, yana murza min, cikin nutsuwa.  A hankali yake min tafiyar tsutsa, kallon shi nayi zan kwace kafana ya rike gam.                      "Don Allah! Ka bari." Na faɗa muryana yana rawa, sake kafar yayi a hankali ya taso inda nake, zai had'a bakin mu na kauda kaina. Sumbatar wuya na yayi na rike rigar shi, naji sakon har cikin raina. Da sauri na juya ina kallon fuskar shi, lebbena na kasa ya kama, nayi maza na rufe idanuna, ina sauke ajiyar zuciya kamar wacce nayi tsare.              A hankali ya janye daga jikina, ya juya min baya. Nima haka ce ta faru, na rasa wani irin kunya nake ji, lokaci guda na kasa sake jikina da shi, sai da na kwashe minti goma sannan na mike daga gadon, yaki ya juyo min kawai nace. "Wasssssh kafana!" Da sauri ya juyo gare ni, kashe mishi ido nayi tare da sake mishi dariya na shige ban daki, sai da na gama na fito.                     A bakin kofar shiga na same shi, cikin nutsuwa na ture hannun shi zan fita ya dawo dani da hannu ɗaya. Ya hada ni da kirjin shi. "Ina son abubuwa akanki, sai dai bazan iya ba! Ina da matukar kishi. Ina son kasancewa dake!  Ina kishin ki, bawai dan ina son ki ba, a'ah kawai ina ƙyamar abin da wani yaci ya bari ne." Mutuwar tsaye nayi domin ban sannan zai iya gaya min magana haka ba, gyada mishi kai nayi sannan nayi wuccewa ta nayi sallah, ina zaune da yar karamar Alqur'ani, malamar jinya tazo ta bashi yace ya ajiye ni yake bukata na bashi. Ina jin shi nayi banza da shi. Da gayya baki kammala karatun dan kar ya dame Ni.   Shiru yayi shima, ya gabatar da sallar da yake kan shi, wasa wasa har lokacin shan maganin shi ya nemi wucewa, bai ce min kome ba, ran shi ya b'aci dan haka da kan shi ya sha maganin, da gayya naki kula shi, har dare muna nan a gurin.          Koda lokacin bashi na dare yayi sun zo bai hana matar ba, ya amsa nata, da dare ina kwance. A dogon kujerar dake cikin dakin, sai ji nayi ya d'aga ni cak, zuwa gadon. Buge hannun shi na fara ƙoƙarin yi, amma ya danne ni da kirjin shi, tare da mai damin  hannuna baya, kauda kaina nayi  raina na kara b'aci nace mishi. "Sake ni!" "Ba zan sake ki ba, kin zata wani abu zan nima a jikinki? Ko ce miki aka yi zan ratsa hanyar da wasu kartin maza suka bi ne, ni zaki ne, duk abin da zanci mike fara farautar shi, idan na gama na barwa sauran kananun namun daji suci, ke har kin isa kiyi fushi dani, dan na kyale ki, ina wasa dake?      Wallahi ki shiga hankalinki, ko kuma na baki mamaki, zan miki abin da ko suna na aka kira sai kin rintsa idanun ki, dan haka ki cigaba da abinda yayi miki Bazan hanaki ba."        Kallon shi nayi cikin wani irin kuka, na buge hannun shi da yake rike dani, na shiga ƙoƙarin ture shi, mutum sai kace bishiyar kuka. Sake danne ni yayi cikin ko in kula, yake azabtar dani. Kuka nake sosai tare da  ture hannun shi, murmushi yayi sannan yace. "Ina jin kunyar ki sosai! Ki k'iyayye haka, kuma ki bani abinda zanci."      "Bazan baka ba, kaje ka sami matan da kake so su baka, me zan maka ina sauran wasu." Had'iye kukan nayi sakamakon, (🙈🙊🙉) yunkurin amai nake, amma mara kirki sai da ya tura min bakin shi cikin nawa, kai....kai.. abu dai bai dad'i ba. Domin Jay ya rena ni, sai da ya tara min gajiya sannan ya kyale ni ya sauka daga gadon, ya koma saman kujeran yayi kwanciyar shi. Saboda kuka idanuna har yaji suke min. Mai da al'amarin babba yayi dan fushi ya dauka dani, sai nima na share shi, ko ya zata bazan iya share shi bane, wasa wasa. Har muka kwana, washi gari ma muka tashi da fushi da juna. ...... Kwana uku da suka biyo baya na sauko na fara gaishe shi, wai nan na kuma ganin rashin mutunci sosai. Domin kuwa tsakanin shi da Allah ya dauki fushi.        Dakyar da sudin goshi na samu kan shi ya sauko, tare da gaya min maganar da yafi na da muni, ba dan yace baya sona bane yaki tab'a ni sai na k'iyayye kome nashi, a cikin kwanaki da muka yi a Amurka nayi kokarin koyawa kaina hakuri dashi, domin na kasance ina gani naki gani, ina ji naki ji. Haka yayi mugun sanya samun nutsuwa. Satin mu biyu aka sallame shi muka koma hotel din da yake kusada asibitin, anan muka cigaba da kulawa da lafiyar shi, kullum zamu shirya mu fita, tare da shi, muyi ta daukar hoto. Mutum kamar me aljanun. Yana ganin wasu mazan suna bina da ido zai rufe ni da fada, sai fushi yau ma haka ce ya faru. Tunda wani baƙin fata ya kafe ni da ido, mutumin nan ya shiga masifa karshe dai, muka dawo gida sai ya fara fushi, da dare na matsa kusa da shi, na kwanta. ... .... Tare da rungume shi, ta baya, amma ya cire hannuna, a hankali nake wasa da gashin kanshi. Ya juya a fusace, kawai na tura mishi, bakina dole yayi shiru. Daga nan kuma ya shiga shagalin shi.   Kome ya tuna sai gashi nan ya ture ni, tare da juya min baya, dariya ya bani sabida ya iya bori, a cikin Jay babu iya ka, kai jama'a.           A cikin kwana biyu muka shiga tattarowa zuwa gida, dan dukkan mu, mun yi kewar gida, a hankali yake gaya min yadda yayi kewar Najim da Fahad, kuma Nima na fahimci haka daga yadda yake jidar musu tsaraba, nima ya sani dole na kwashi kaya da kudin da yake hannun mu, turarruka da kayan kwalliya kawai na diba.      Sai kaya masu kyau na zamani wasu Rumah da Hanisah da Jannart da Raihah. Na sayawa Iyayen mu maza suma turarruka tare da matan. Sai Husnah da Munin suma na diba musu, har muka bar kasuwar zamanin.         .... Washi gari muka bar garin, kaina na kafad'ar shi, muna hira har muka gama kome, sannan muka shiga jirgin mu.              --- Ranar juma'a muka iso garin Abuja, da karfe tara na dare, a gajiye muka fito, daga gidan Minista Dr Bulama, aka zo daukar mu. Tare da wasu yan mata fannah da Ammah, Sun hadu ba laifi tun da muka shiga gidan.     Matar gidan jikinta yake rawa,tana hidima da mu, ta kawo wannan ajiye min wannan.    Sabida ganin Jay a cikin gidan kawai, Yaran matasa da yan mata na gidan sun saka shi a tsakiyar su ana hira dashi. Ni kuwa matar nan bani kulawa tayi ta hanyar sani nayi wanka ta bani wannan naci na shafa wannan sannan take ce min. "Zahrah! Duk cikar mace matukar ta gaza daukar nauyin cikin mijinta sunanta sakarya!    Kiji a ranki ki macece, kiji a ranki ke zaki iya sarrafa abinda mijinki zai iya ci, bawai wanda ba zai iya  ci ba. Karki yarda wata mace ta hango kasawar ki, ki nuna mata ko a gidan giya akwai babba, bana son naji ace akwai wacce zata iya karban matsayin ki, Mu Ahalin Jannart, Uwar mijinki muna matukar kaunarki da kuma girmama duk wani abinda ya shafe ki, karki ji kome duk abinda kike bukata ki gaya min, za mu miki." Kwalla ne ya cika min ido, zuciyata ta kuma cika da kaunar Jay, Kaf dangin Mahaifiyar shi suka matukar kaunata. Na rasa wani irin so suke min, suna matukar girmama alamarina, kamar su goye ni suke ji, bani da Uwa amma Allah ya bani su ta sanadin Jay.      Daga nan ta bani wata lafayya, na saka bayan na shirya cikin riga da skirt, na atamfa sannan na nad'e kaina da laffayar ta ja hannuna zuwa. Babban Falon Dr Bulama..da sallama muka shiga cikin. "Ango ba cefene, yau kaine a garin mu, na zata ba zaka tsaya anan bane!" Shafa kan shi yayi sannan ya sake wata lallausar murmushi, sannan yace. "Uwargidan Amaryan, duk ke daya. Babu me kwace miki fadar ki." "Aikuwa na iya kishi Dan wannan jaja amaren ka, waka zan mata da ruwan sanyi." Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, sannan muka gaisa da baba Dr, muna cikin gaisawa yace min. "Maamah! Baki ba shi labarin yadda yayi jinyar shi bane!" Kallon juna muka yi da Jay ya sake min murmushi, nima na maida mishi, tare da gyad'awa Baba Dr kai nace mishi. "Idan na fada ba yarda zai yi ba, shi yasa na bar maganar, dan zai ce ba gaskiya bane"   Gyada kai yayi sannan ya shiga bamu labarin, rikicin da muka yi ta yi, akan ya kirani Maamah, murmushi kawai yake, yana kallona, ganin har lokacin yana me kafe ni da ido, kawai naji a raina da zan iya jin abinda yake ran shi nasan yabo ne da jinjina... 07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha.... 10/23/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: *Allah, ya maida ƙoƙo masaki.* _Ke Alkhairi ce duk namijin da ya same ki a rayuwar shi, yayi sa'a_ yace a ranshi, yana murmushi.     *Akwai sa'ar da mutum zai yi bayan ya sami nagartaccen mutum irinka? Ai kai ne sa'ata baki daya* na fadi haka  a raina, ina me sunkuyar da kaina, hira sosai aka bude tare da tattaunawa akan asibitin shi da za a bude mishi, amma kuma naji Baba Dr yana cewa. " Bai zama dole a bude maka ba, dan naji suna wani batu akan ka Allah ya tabbatar da Alkhairi." "Amin Ya Allah," Muka amsa baki dayan mu,   Dakin abinci muka nufa, anan muka ci kad'an sannan muka fito,  ina kallon yadda yake bina da ido, kin kula shi nayi. Har muka nemi kwancin mu, daki daya aka bamu, dan haka muna shiga.    ..Na shige ban daki, na watsa ruwa, ina fitowa na same shi, ya rage kayan shi zai shiga wanka, janyo ni yayi tare da kallon fuskana. "Ki shiryarwa daren yau! Dan ina ganin zan rage za...." "Yallabai! Kwantar da hankalinka, Ni hutun sallah ma nake, yanzun na gani." B'ata rai yayi wucewar shi abin shi. Bai kuma kulani ba.     Har ya fito ya samu na fara barci, shiryawa yayi sannan yazo ya kwanta a bayana, tare da janyo ni jikin shi, a hankali barci yayi gaba dashi, sabida mun rigada mun gama gajiya, shi yasa bai dame ni ba.          --- A can daura kuwa, sun san mun sauka a Abuja, dan haka Abba da kan shi, ya saka aka kira su Husnah. Bayan sun shigo suka gaishe shi, kallon su yayi sannan yace musu. "Allah yayi muku albarka." Ya fada a sanyayye, sannan ya kuma cigaba da cewa. "Gobe Insha Allah, Mijinku zai dawo suna Abuja ne, da yayarku!"       "Allah ya dawo dasu lafiya, muna jiran su." Inji Husnah, Kallon su yayi sannan yace musu. "Ko kuna da bukatar wani abu ne?" "A'.." "Eh! Muna da bukatar kudi." Inji Munih, bayan Husnah tana son cewa a'a, murmushi yayi tare da dauko wata takarda me kunshe da kudi ya mika musu. Suka amsa suna godiya, sannan suka mishi sallama, tare da barin falon, murmushi yayi yana jinjina qarfin halin Munih, yana kuma girmama hakurin Husnah.   ... .. Yadda take murmushin mugunta bayan sun fito. "Insha Allah saura kiris naci qaniyar wata, idan na gama da ita na dawo kan farar angulu." Daga haka tayi wucewarta, Husnah bata kulata ba, dan tasan da ita take. ......        Washi gari Farkawa yayi ya kalli yadda gashina ya rufe mishi fuska, yana fitar da wani daddar kamshi, shafa kaina yayi sannan yace min. "Nanah Fatimah!" Tura mishi baki nayi tare da gyara kwanciya ta a jikin shi, sake shafa fuskana yayi zuwa wuya na yace. "Zuhruyyah! Tashi zan tafi sallah ne!" A hankali na d'ago kaina  sannan na janye daga jikin shi, cire matashin kan shi yayi ya cusa min a jikina, sannan ya daga gadon, kallon yadda na k'amk'ame matashin yayi.    Murmushi yayi sannan yazo ya sumbaci bakina, zuwa goshina, kafin ya shiga ban daki. Sai da ya watsa ruwa, sannan ya dauro alola tare da saka jallabiya ya nufi masallacin da yake cikin gidan.                     --- Kafin ya dawo nayi wanka, ina fitowa yana shigo min d'aki, zama nayi a gaban  mudubi na shiga gyara jikina, ina gamawa na dauki kayana, ina sakawa ya matso kusa dani.  Rungume ni yayi tare da cewa. "Kina da jiki me kyau! Shi yasa baya nuna tsufarki"     ..... Gyada mishi, kai domin Jay bai iya magana ba, kuma duk abin da zai fito bakin shi, Alhamdulillah Nagodewa Allah, kawai yankota yake.      Ina gamawa na shirya cikin doguwar rigar yadi me tsantsi, duk da na saka wando da rigar mama, amma haka Jay ya hanani sukuni da surutu. "Wallahi baki isa ki fita gidan nan da dan jinjirin mayafin nan ba, sabida rashin sanin ciwon kai, toh wallahi naga kafarki  a waje zan zane ki kinji na rantse da Allah."   Zuba mishi ido nayi,  gaban madubi na duba kaina naga dole yaji Babu dad'i, domin kuwa duk inda na juya jikina sai ya girgiza,  dake ina da ƙaruwar jiki ne, cire kayan nayi sannan na nimo wata atamfar riga da zani, na saka amma dake yau yana jin rikici ne, nan yace bai iya ji ba.    Na nimo doguwar rigar na saka, na atamfa, na saka ina sakawa ya kare min kallo, kauda kai yayi sannan yace min. "Shima ai ya fidda kirjin ki, Ni kam na shiga uku, wai ke dama haka kike a hanaki sata ki koma sane, toh cire rigar ki saka riga da zanin can." Kwalla ce ta zubo min, dole na cire na saka. Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya matso kusa da ni, idanu shi akan kirjina. "Wannan ma an mutu ba a tsira bane toh amma da sauki tunda ya.. kai ina zo nan daga yau zaki daina saka rigar mama masu fitar da mama nan!" Ya faɗa haka tare da fita.    Har ya isa bakin kofar yace min. "Kuma ki saka babban mayafi irin na juya, yawwa."    Banza nayi dashi, a hankali na gama shiryawa na fito, muka karya, muna hira har kusan karfe  goma sannan muka dawo shiryawa, ina cikin shirya kayan ya shigo, a zafaffe ya juyar dani. Tare da bina da wasu zazzafar sumbata. Kamar zai cinye ni. Tun ina kau da kai na, har na kasa na shiga biye mishi, kamar ba zamu bar juna ba, ban da ina hutun salla da babu abin da zai hana Jay karb'an hakkin shi domin ban tab'a ganin shi  cikin damuwa da kumar bukata irin na yau ba,        Ture ni yayi gefe, tare da rike hannu na gam, ina mamakin abin da ya kawo mishi sauyi, lokaci guda. Dan haka wuta wuta ya fitar mana da kayan mu, dan yana fama da ruwan kashe gobara ne koda kuwa ta kwata ce zai iya watsawa. .....idan har wutar zata mutu toh bukata ta biya shi kenan, dan haka muka shirya sai filin jirgin sama. Kamar zai yi hauka. Sabida yadda yake jin shi.               --- karfe sha biyu muka sauka a Katsina, ba tare da ya gayawa Najim mun taso ba, haka ya kira. Murad karamin yaron Sarkin Katsina ya gaya mishi isowar mu, mota biyu aka turo suka kwashe mu zuwa daura      ....... Karfe biyu yayi mana a cikin masarautan, ko cikin gidan bai shiga, ya nufi cikin gidan shi. Wani abu naji ya tsaya min a rai. Take na fara niman taimakon Allah.    Kafin na shiga cikin gidan, na nemi kome na rasa sai ma nutsuwar da zuciyata ta samu, shi kuwa yana zuwa. Ya taradda Husnah tana lalle, afujajjan ya kwace kome ya cire sannan yaja ta zuwa d'akin ta.        Anan ya gurje ta son ran shi, tare da sauke nauyin da ya kwaso baki daya akan ta, ajiyar zuciya ya sauke, lokacin da ya fahimci ya sauke gajiyar shi akanta, yana kallon yadda take sauke numfashi. Tausayi ta bashi,  duk da haka yayi fatan ina ma Da Fatimah ce zata kasance haka da yafi kowa amfana da ita, Husnah ma ba laifi dan ta haɗu.      Ban ɗakin ta ya shiga yayi wanka sannan ya fito abin shi ya shiryawa ya barta kwance, bayan yace mata. "Ki tashi kiyi wanka bana son kazamta." Yana fita,ya nufi cikin gidan su anan ya taradda ana ta hira yaushe gamo, zama yayi cike da kunya, dan alamun wasu abubuwan da yayi suna bayyana, kasa magana yayi duk da tambayar shi lafiyar shi da ake, Ni Ko ban kalle shi ba, dan na san juyen bakin mai yayi, dan haka ban koma sha'awan kallon inda yake ba balle na kula shi.             Mik'ewa nayi na Barsu a falon na shiga dakin su qarama na rufe kaina na fashe da kuka, sai da nayi me isata sannan nayi kwanciya ta a d'akin.   A gidan na wuni,naki yarda na koma gidan shi,ina jin shi yana kaiwa da komowa, akan mu tafi nace bazan koma ba yayi tafiyar shi.            Har dakin ya biyo ni, ina kwance, juyar dani yayi tare da zubawa fuskana ido. "Kinyi kuka? Me aka miki?" Wani kukan ne ya tawo min, na kuma rushewa da shi, ina yi ina shasheka, nace mishi. "Don Allah yaushe zaka kaini gurin Baabina?" Zuba min ido yayi sannan yace min. "Babu rana! Balle wata. Indai dan haka kike kuka toh ki shirya domin kuka yanzun kika fara, kuma babu wanda ya isa ya juya ni baki isa ba, dan haka ki taso mu tafi ko raina ya b'aci na miki abinda baki zata ba. Tun dake baki da burin kome sai na sanya Ni a b'acin rai.        Ban san me na miki kike aikata min wannan mugun abin ba,daga ki sanya ni cikin damuwa sai ki sanya ni cikin b'acin rai, abinda kananun yaran da kika samu basa min, shine ke bari ki min, wallahi baki isa ba. Kin kasa, kuma babu wanda ya isa ya juya min baya a wannan lokacin. Ki fito ina jiranki." Daga haka yayi ficcewar shi, kuka nake har da shasheka, ina ji ina gani bai damu da alamarina, ba, koda na fito na same shi suna magana da Mamah Sarah, tana mika mishi wata littafi, tana faɗin. "Ina ga akwai wani a hannun Kawu, kuma tun shekarun baya naso buɗewa, na kasa amma tace min a wani takarda dole sai na nimo Jakadiya Sahurah, ka duba yadda zaka bude Littafin yana da amfani. ..... Naso baka tuntuni sai wannan hatsarin ya faru, toh yanzun kuma naga kasami lafiya kuma ina jin Kawu yace wata me zuwa zasu baka sarautar bana son abubuwa su maka yawa, ba tare da ka duba ba."   Amsa yayi tare da kallon bangon littafin an rubuta, kundin tarihina! Me kunshe da al'ajabi. Murmushi yayi sannan yacewa Mamah Sarah. "Rubutun Ammih na, irin nawa ne. Tun ban karanta ba, naji ina kewarta." Murmushi Mamah Sarah tayi, sannan ta goge kwallar da ya zubo mata, tace. "Idan kuma ka karanta, sai kaji dama zata dawo ne, sabida Jannart tayi min kome!"                 Girgiza kai yayi sannan  yace mata. "Toh Mamah zamu tafi."      Daga haka Yasaka kai muka fita, tunda muka nufi gidan yake duba yadda zai bude Littafin, wanda aka rubuta cewa. *Sunan Kawu da Nawa ne, mukulin bude littafin, sunar da ya bani ranar da muka rasa junar mu! Kalmomin masu Harafi bakwai* Har muka shiga gidan, zama yayi a falo ya mika min, tare da cewa. "Sunan Ammih da Abba! Ki hada ya baki ma'anar kuma kalmomi masu Harafi bakwai. Tayani dubawa." Duk da ina jin haushin sa, amma haka muka raba dare muna duba  cikakken sunan da zamu bude Littafin.     Wasa wasa muna gurin, har kusan asuba, sanan ya jani zuwa d'akina, anan muka kwana. Da asuba muka daura har kusan karfe ɗaya na rana babu karya ba.          Abu kamar wasa sai da muka dauki kwanaki, dan Munih bata nan, ranar da Abba ya bata kuɗin suka yi tafiya da safe da zamu sauko, ina kallon Yadda ya gama shan wahala sannan. ya ajiye Littafin. Yana me cewa. "Wallahi na gaji, Littafin babu wani abun da zan iya buɗewa."       "Ka dai tuna da kyau! Babu mamaki tasan zaka san sunan ne ko kuma kaje ka tambayi Abba!"          Aikuwa ya fita zuwa gidan Abba, ya sashi a gaba ya bashi daya kundin tarihin Maman shi, sannan ya bashi ya kuma makelewa Abba sai ya gaya mishi Mabudin, ya rasa meye kalmar da Zata bude littattafan guda biyu... _Kuyi hakuri mura ya dame Ni_ 07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha.... 10/23/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba* "Kai amma abin yayi kyau,Yanzun aiki ne babba a gurin ki, kiyi hakuri da halin shi da duk wani abinda zai miki,  ki daina kuka domin shima zai yi duk abinda kika yi dashi zai cigaba hakuri kawai yi kina nuna mishi abin da ya dace a rayuwar shi." Yayi bayani sosai, sannan ya kuma yi gargadi kar a kuskura abar shi yayi wani abin da zai shafi jima'i, dan bai cikin hankalin shi, kuma matukar aka ce zai yi jima'i da mace toh akwai matsala. Domin zuciyar shi  ba zata iya sarrafa sakonni Ƙwaƙwalwar shi ba. Dan haka ayi takatsantsar dashi. Idan kuma haka ya faru.          Toh tabbas karfin shi da lafiyar shi zasu rubayya zuwa kashi tamanin cikin dari, kuma idan hakan ta faru.    Likitan yayi bayani sosai, kafin ya fita. Kallona Abban shi yayi a raunane yace min. "Ina ga zaki..." "Ina ruwanka? Meye matsalar ka dasu? Fatimah zaki iya zama da Jalal?" Inji Baba Aswad, Gyad'a mishi kai nayi, wasu siraran hawaye na zuba min, nace.. "Don Allah ya bar kirana da Mama!"           Murmushi Baabina yayi sannan yace min. "Ciwo ne ya mai da shi haka, Insha Allah ya warke bazai kuma kiranki Mama ba"   Gyad'a kai nayi, shi kuwa ganin na daina kuka, yazo ya mannu da jikina tare da saka hannun shi a bakin shi, yana kallon su Baabi.                             Gani yake kamar, sune suke bata min rai dan haka ya narke a jikina, kamar wani mara lafiya, karshe haka Baabi yayi min nasiha, sannan suka tafi. "Maamah!" Cikin shashekar kuka, na kalle shi.  Kwantar da kanshi yayi  a kafad'a na, yana shafa cikin shi. Jan hannuna yayi tare da daurawa akan cikin shi, janyewa nayi da sauri. Sakamakon jin gargasa har saman cikin shi..        Zamewa nayi daga gadon, zan nima mishi abinci shima kuma ya sauka daga gadon, ina d'aga kafana yana saka nashi, ina juyawa kawai muka yi karo da shi.             Shafa cikin shi yayi, tare da kallon abincin. Zama nayi a kujeran jikin gadon shi kuma na nuna mishi bakin gado, nokewa yayi. Naga ya fara kokarin zama akan cinyata. Zubur na mike tare da zare mishi idanu, na nuna mishi bakin gado.          Kamar yadda nayi mishi haka yazo ya zauna tare da kwaɓe fuska zai min kuka, na shiga bashi abincin yana ci yana tura min baƙi.       🤦🏽‍♀? Dakyar ya karbi abincin, sannan na tuna ko wanke mishi baki banyi ba, tsawon kwanaki yana kwance.     Barin shi nayi na wuce ban daki, ina shiga yana bina, a fusace na juyo. Kwantar da kan shi yayi, na juya ina hada mishi ruwan zafi wanda zai yi wanka, Allah yaso ni da arziki, ruwan babu wani zafi sosai. Jin ina ta haɗa ruwan tare da saka hannuna ina tab'awa, kafin na fahimci me ake ciki sai ji nayi ya jefa ni cikin ruwan.        A razane na kalle shi, na fita da sauri, tare da Zungure mishi goshi.       "Ka cire kayanka, wanka zaka yi" na fada mishi.         "Ka cire kayanka wanka zaka yi" ya mai-maita, takaici ya bani na shiga kukuwar cire rigar, karshe da yaga zan takura mishi ya ya galla min cizo, a hannuna idanuna ne suka cika da kwalla.     Na kalle shi yana rike da hannun, da hakoran shi. .wani irin tausayin kaina ne ya kama ni, na zare daga bakin shi ya ture shi ina duba gurin, jingina nayi da bango a hankali na sulale kasa, tare da sake wani irin kuka mara sauti.            Shima zama yayi a gaba na, yana kallon yadda nake kuka. Shima kuma ya kama kukan. Haushi ya bani, na mike tare da kallon shi kamar na daka mishi tsawa, sai kuma na shiga kiciniyar cire mishi rigar jikin shi.        Fisgo ni yayi tare da kallon fuskana, yana murza idanun shi.       Kallon juna muke, na wani lokaci. Sannan na kuma mik'ewa, na saka cire kayan shi na bar shi da yar gajeren wando. Nasha wahala kafin nayi mishi wanka, da na gama kuma. Na rasa yadda zan mishi bayanin ya cire wandon shi.  Karshe dai haka na kauda kaina na zare mishi wandon shi, da sauri na daura mishi tawol idanuna a rufe.               Riga da wando, ruwan sararin samaniya na saka mishi, kalar kayan marasa lafiya,       Ina gama shirya shi malamar jinya tana shigowa da maganin shi, tana bashi yaki amsa sai da na karb'a na bashi.         Can ya saka mana rikici, dakyar ya tsaya na bashi ya sha, zuwa wani lokaci ya kama barci, akan cinyata.         ...... Washi Gari.        Ya rigani ya tashi, hannun shi ya kai, yana lallubar hannu na. Tare da kaiwa cikin shi yana shafawa, a bisa kuskure na ya kai hannuna saman marar shi, wani irin yanayi muka ji babu shiri na bude  idanuna, ina kallon shi.     Shima Ni yake kallo, sa sauri na ciro hannuna daga cikin wandon.                "Hmm!" Ya furta yana kallona.         Da sauri na mike ba kalli agogon dakin, ban daki na shiga ban kai ga rufe kofar ba sai gashi nan ya shigo.                  Takaici ya kamani na ce mishi. "Jay don Allah fita." "Jay don Allah fita!" Ya faɗa min. Tsaki naja shima kuma yayi. Mik'ewa nayi tare da turo shi waje, na rufe kofar.      Ina tsaki, sai da na gama uzurina, sannan na fito.            Kallona yayi har da sauke ajiyar zuciya, idanun shi yayi jajjur. Alamar zai fara kuka..    Kai shi nayi tare da zare mishi wandon shi, na nuna mishi yadda zai zauna, kamar wanda zan daura shi akan mugun abu na gudu haka ya ririke ni.    Kwalla ce ta cika min ido, domin hannun shi ya damki, kirjina. Kallon juna muka yi da sauri na buge hannun shi, kallona yayi tare mai da hannun shi kirjina, na kuma make hannun. Kamar zararriya haka ya manna min hauka, nayi ta faɗa. Ni daya na.         Ko ya fahimci bana son ya tab'a min ne, aikuwa sai da ya barni na manta, kawai naji hannun shi a gurin, cikin wani irin yanayi yake tab'a min su. Zabura nayi dan yadda yake tab'a min ko lokacin da yake da cikakken hankali bai min irin wannan tab'awar har cikin jinin jikina nake jin hannun shi a gurin.      Dakyar na kwace kaina a hannun shi.    Na juya mishi baya, kwalla na zubo min. Hannun shi ya kai tare da dafa kafad'ana, cire hannun shi nayi tare da cewa. " Ka rabu da ni! Tunda baka jin magan...."       Cak ya na had'iye maganar, rungume ni yayi tare da saka kan shi a kafad'ana zuwa wuyana, ina jin saukar hawayen shi. Tausayi ya bani na janye jikina daga gare shi, na matsar da shi gefe. .a hankali na nuna mishi abin da nake bukata, bawai yayi bane, domin kuwa ya sani kuka yafi sau goma, kafin muka fito.     .kuma bai yi kome ba, muna zaune dashi kawai naga yana matse cinyar shi, kallon shi nayi, cikin fargaba, a hankali na kai hannuna tsakanin cinyar shi da sauri na cire, sabida wani abu na daban da naji, na zuba mishi , mik'ewar da zai yi kawai ya fara saka fitsari a jikin shi. Kai shi ban daki nayi. Tare da jan kunnen shi na zaunar dashi bayan na cire mishi wandon shi nace. "Idan kana jin fitsari kace min zaka yi wiwi! Idan kuma zaka yi!"       Shiru nayi sabida ya taso ko gama bukatar shi bayi ba, na zuba mishi ido, garin diban ruwa na wanke mishi jikin shi, muka fara kokuwa, sai da ya buge ni,  dakyar ya wanke jikin shi muka fito bayan nayi alola shima yayi, sallah kan Sai godiyar Ubangiji.         Domin kuwa, bayan na idar haka yayi ta bankauran shi, muna idarwa ya kamo hannuna zai kai cikin shi. Nayi maza na kwace tare da dalla mai shi harara. Sunkuyar da kan shi yayi, Na mike tsaye..kamar jirana yake ina mik'ewa ya mik'e.        Yana biye dani, har na hada mishi ruwan zafi, na ajiye na fara kokarin cire mishi maganin da zai sha. Ban san me ya faru ba sai ji nayi an watsa min ruwan zafi a jikina ya sake kofin a kasa ya fashe, shi kuma ya rike bakin shi da hannun shi. Juyawa nayi na kalle shi, takaici ya hanani magana, haka na tattara kofin, haushin sa yasani kin bashi maganin, na cigaba da hada nawa, ina gamawa na koma gefe ina sha ina kallon yadda yake wangale bakin shi, hawaye na zuba mishi. .. sai da na karya da ruwan shayin sannan shima na hada mishi nasa. Ina bashi yana zubda rabi a jikina yana shan rabi. Koda ya gama sha, nazo bashi magani nan ya kwara min amai, dai dai shigowar su Baabi.             Tashi nayi na shige ban daki raina yana kara b'aci, dakyar na fito,  na same shi ba zaune a bakin kofar, yana jin na buɗe ya mike da sauri zai sure ni na. Dakatar da shi da sauri, dan dole ya koma gefe tare da rab'ewa. Yana kallona a sace. .. can ya kama kuka, irin kukan nan me shegen ban haushi, dakyar na samu yayi shiru, bayan na zauna ya daura kan shi akan cinyata, can ya fara barci.     Fita suka yi ban san ya aka yi ba, sai gasu da takardun wai nan da wata uku za a kuma mishi aikin, amma an sallame mu.             Kamar na daka tsalle dan murna, na shiga hada kayan mu, duk inda nayi yana bina, har na gama muka fito, dan sun ga dacewar mu koma gida, babu amfanin zaman nan ɗin, tunda aikin sai nan da wata uku..kuma za'a ta kashe kudi ne.           Masaukin su Baabi muka koma, tun a bakin kofar mashigar yaga wata mata, sanye da irin riga me bayyana kirjin nan, Allah yasa idanuna suna kan shi, kawai kafin su Abban shi ya taro shi ya kaiwa matar nan cafka nayi maza na buge hannun.     Kallona yayi tare da saka dariya, dakyar muka shiga otel din.      Abubuwan ban haushi Jay yayi shi cikin rashin damuwa, tunda na lafiyar ce ta ishe shi ba.            WASHI GARI Tun asuba, muka bar ƙasar, yana barci na tashe shi, dan bama kwanciya guri guda, gudun faruwar wani abu.      Tunda na samu yayi uzurin shi, muka fito. A tashar jirgin yaga wata yarinya da yar dolinta aikuwa ya saka min rigima sai na saya mishi, haka Baabi suka shiga cikin kasuwar tashan jirgin suka sayo mishi, aka bashi.        Ana bashi ya saka dariya ya mika min. "Maamah!" Ya miko min, kamar bazan amsa ba na karb'a na duba, matsowa yayi jikina ya daura yar dolin akan cinyar mu dake manne da juna, sannan ya daura kanshi a kafad'ana.      "Maamah!" Kallon shi nayi, ya kuma kirana "Maamah" "Ki amsa mana, mahaifin shi bazai ji dadi ba." .d'ago kai nayi na kalle shi nace mishi. "Meye ne Jay?" "Ki amsa mana mahaifin shi ba zai ji dadi ba" "Toh kayi hakuri, ba zan kuma ba."      Dariya yayi sannan yace min. "Toh kayi hakuri bazan kuma ba" Jan kumatuna shi nayi tare da cewa. "Yaron kirki" Ja min kumatu yayi sannan yace min. "Yaron kirki!"        Share shi nayi ina zaune can sai ga wata yarinya da roban guguru, tana ci. Yana ganinta ya fauce. "Bata kafin na maka bulala!" Na daka mishi tsawa, tare da zare mishi idanu. Da sauri ya mika mata, kamar na had'iye zuciya ta na huta da ban haushin jay, can muna zaune Baba Aswad ya fita, sai gashi da gugurun, ya amsa yaki yana kallona. Amsa nayi nacewa Baba Aswad. "Mun gode!" Shima kuma yace. "Mun gode!"        Bude mishi nayi ya kalla, a hankali nasaka hannuna na diba, na fara ci, da sauri ya diba ko nace ya dunbula, ya kai baki. Yayi na farko duk ya watsar a kasa, zai kuma na biyu na rike hannun shi. Tare da nuna mishi yadda ake ci. Babu musu ya shiga duba shima yana ci a hankali. Tausayi yake bani.   Har jirgin mu ya taso, karshe biyar na safe, muka nufi Dubai daga can kuma muka nufi gida.   Kafin mu iso gida, raina ya b'aci... Paid Before read 07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha.... 10/23/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *Alhamdulillahi* Cikin tashin hankali suka nufi Jay, tare da jijjiga shi, ina yayi nisa. A rikice Najim ya riko wuyar Dr Fatihu, cikin b'acin rai yace. "Gaya min me ya faru da Anih Fatimah?" Cikin mamaki yake kallon su, kafin shima ya kuma tambayar su. "Me kuke nufi? Matar lafiyar ta kalau, yanzun za a fito da ita. jariran biyu aka cire mata, dayan bai fito da rai ba, daya kuma Alhamdulillah lafiyayyen ne. Shine nake shirin muku bayani da." "Toh ai sigar da kake bayani bai bada ma'ana ba dan ga Jay can sume," Dole aka kai Jay dakin da aka dauko Aanih aka shiga bashi kulawa, (Romeo and Juliet) bayan wasu mintuna aka fito da Aanih. Dai dai shigowar Baabi da Ummin. Suka nufi dakin da aka kwantar da Jay san sunji Jikin Aanih da sauki, shine dai ake tsoron kar wani abu ya same shi. Sai da aka kwana aka wuni, dan ita Aanih ta farka, Jay ne dai a cikin tashin hankali, sosai suka damu da halin da yake ciki, har zuwa wani lokaci..kafin likitoci suka dukufa akan shi. ...... "Ummi ina Jay? Bai zo ba," Na fada a hankali, shafa kaina tayi sannan tace min. "Yana nan lafiya akwai abinda ya tsayar da shine." Shiru nayi kafin na kuma kallonta nace mata! "Jikina yana bani akwai matsala, meke faruwa dashi?" "Babu komai!" Ta bani amsa a takaice tana goge kwallar dake idanunta, shiru ne ya kuma gifta tsakanin mu. Har Abban Jay ya shigo cikin murmushi ya dauki Yaron, yana jijjiga shi yace mana. "Allah yasa yayi gadon sunan Takwaran shi, Aswad." Had'iye yawu nayi tare da kallon yaron, da yake hannun Abba. Ni na zata zasu ce sunan Baabi zasu saka sai kawai naji sunan Abokin Abba. Share batun nayi dan kar shaidan yayi tasiri a zuciyata, sannan ya kuma cewa. "Alhamdulillah shima sai da sauki, dan ya farfaɗo yana barci!" Hannuna nakai baki nace.. "Waye?!" Dafe goshi Ummi tayi sanan tace mishi. "Kawu! Baka san yar taka bata san mijinta babu lafiya bane, ai sai ka mata bayani," Daga haka ta fita tabar mana d'akin, kallona yayi cikin nutsuwa sannan ya min bayanin halin da Jay yake ciki, goge kwallar idona nayi, sannan nace mishi. "Allah ya bashi lafiya!" "Amin Ya Allah," kallona yayi sannan yace min. "Kingan shi kamar mijinki ranar da aka haife shi, amma shi bai ji dumin jikin uwa ba, don Allah kiyi hakuri dashi, Insha Allah zaki yi nasara a rayuwarki. Ina miki kallon Jannart ne, banbantata soyayyar ki da ta Jay ba, sabida dukkanku abu daya a gurina, Fatimah zanyi farin ciki idan kika rike min Jay bisa amana da gaskiya, har Abada ba zan tab'a barin shi ya kuntatta miki ba, koda kuwa haka zai sanya nayi fushi dashi. Fatimah Nagode. Nagode sosai da kawo min shi har gida." Wani irin kukan farin ciki ne yazo min, cikin jin dadi. Wai ni ake bawa Jay, lallai mata zasu buga mulkin mallaka. Wani dad'i naji tare da sake murmushin mugunta. Har na shiga duniyar tunani, gani nan dashi yana shiryawa zai tafi fada. Na shigo rike da Yaron nace mishi. "Saraki!" "Na'am!" Ya amsa min, "Toh yau bazaka fada ba!". Cikin wata irin soyayya yace min. "An gama ranki shi dad'e!" "Karbe shi!" Naji muryan Abba da sauri na amshe shi, na ajiye shi a kusa dani. Har Abba ya fita, wani dad'i ya kuma kama ni. ..... Jay bai farka ba sai dare, yana tashi ya zuba musu ido. Cikin karaya yace musu. "Ta rasu ko?" Zama Najim yayi kusa dashi ya dan kalle shi yace mishi. "Toh baban soyayya, kayi wanka kaci abinci sai na kai ka makabarta kaga." "Zan saɓa maka Najim! Saraki kayi wanka Fatimah da Takwara lafiyan su lau, kaji." Ya rasa abinda zai ce musu, amma maganar gaskiya yana cewa wani irin yanayi, dakyar yayi wanka da alola, sannan ya gabatar da salollin kan shi, yana idarwa Najim ya haɗa mishi shayi me kauri, ya sha. Ko hutawa bai yi ba, ya mike babu wanda ya hana shi, suka nufi dakin da Aanih take. Cike dakin yake da Iyayen su mata. Yana shigowa ya tsaya a bakin kofar, cikin nutsuwa ya kura mana ido, ina shayar da jaririn, sai nuna min yadda zan rike kan Yaron Ummi take, farin cikin da yake ran shi ya gaza boye shi, sunkuyar da kai yayi, Duk da yana da wasu yaran Amma yaron da yafito jikin Aanih fansar kaunar su ce. "Saraki shigo mana." Kamar wanda aka doke kafar shi ya shigo d'akin, ya zauna. Tare da kura min ido, a hankali kowa ya watse daga d'akin, zama yayi sannan ya rungume ni tare da yaron. "Nagode!" Kwalla ce ta cika min ido, nace mishi. "Shine zaka tafi ka barni!" Shafa hannuna yayi sannan yace min. "Gani nan ai babu inda zani, tunda kaunarmu daya ce." Wasa wasa, Jay ya hana kowa zama a d'akin. Shi ya makale mana, har aka sallame mu. Inda muka koma shashin Mamah Sarah, nan aka shiga bamu kulawa har muka cika sati daya aka yiwa Yaro raɗin suna, ranar inda muke kiran shi da Jaish, kowa sai da yayi ta magana wai da fatan sunan me kadari ne, shiru muka yi bamu kula su ba. ... Bayan suna akaso mai dani Sokoto Baabi yace a barni kawai, kyauta kayan alfarma tare da kyautar arziki na same shi a hannun dangin Maman Jay, har kuka nayi, sabida kayan har mu shekara uku muna amfani dashi, tsabar wasa da kuɗi har da motar wasa wanda sai ya kusan shekaru biyar yana fama dashi ga keken zama, abubuwa dai gasu nan kayan suna nawa da na samu ba a cewa kome. Domin suna min Son so ne, musamman da suka ga ina son jinin su, kuma bani tab'a ganin laifin shi, haka ya kuma kara min kima a idanun su, koda aka bawa Jay kyautar mata daga gidajen sarautar Hausa bakwai. Kakan shi sarki Kazeem ya hana su, yace jikan shi ya gode ba zai kara aure ba, dan tsiya yayiwa Jay tare da tambayar shi ko bana wadatar dashi ne da zai amshi wasu matan. Dariya yayi kawai, dan yasan babu abinda zai cewa yar Guzumar shi(🤣🤦🏽‍♀?) Watan mu biyar aka fara bikin Yan mata, na rasa inda zan tafi gashi Jay da masifa dan ina cika wata uku ya tadda rigima wai a dawo mishi dani ko yayi aure. Baba shiri aka mai dani. Fitinanne daren ranar na fadi gaskiya na dan Mamah Sarah ta gyara ni yadda ya dace, nan yayi ta shagalin shi.. Batun Haihuwa kuwa, da kan shi ya saka aka sanya min abun hana daukar ciki, haka yayi matukar bani haushi. Da nayi magana yace wai dan lafiya ta yayi haka. Dole na hakura aka yi bikin ina domin Hanisah Lebanon aka wuce da ita, Raihanah kuma aka kai ta gidan Najim. Jannart karama kuma aka wuce da ita Kaduna. Allah Sarki Fahad, kamar yayi hauka, dan ma wanda ya auri Jannart din Habib ne dan gidan Baba Samim, an yi bikin sosai. ..... Juyi nayi sabida gajiyar biki, na zabgawa Jay harara. Sai murmusawa yaƙe hankalin kwancen. "Tashi ki hada mana ruwan wanka!" "Jay Ni gaskiya a cire min wannan roban wallahi damuna yake!" Ajyar zuciya ya sauke, sannan yace. "Karki damu! Insha Allah gobe zasu cire miki!" Gyada mishi kai nayi cikin farin ciki, dan Allah ya gani bana son tsarin iyali, shi kuma yace bai shirya rasa ni ba a rayuwar shi. Shi yasa takura aka zo gida ka kwafkuma min (implant) ranar da aka saka min yaga rashin kirki dan fushi nayi dashi sosai na kwana biyu, kafin na sauko. Dake yasan bai da gaskiya rimi rimi yayi ta bina,ana haka Jay ya tsiro da wata hali, baya zuwa Fada da manyan kaya, sai da suit, anyi magana yace zamanin shi ne, a barshi da sabon tsarin, haka aka barshi yayi ta mulkin shi babu wanda ya damu dashi tunda bawai zai fasa ba ne. Dangin Galadima ya hana su mulkin anyi juyin duniyar nan ya bada yace suyi hakurin sai yi a gaba amma ba a mulkin shi. Masarautan ta sami zaman lafiya, da kwanciyar hankali yayi da y'ay'an masarautan suka kasance wasu jigogin jagorancin al'umma, sosai Jay yake amsa lambobin girmamawa daga ƙasashen waje, musamman members na ECWAS, sannan tarayyar Turai sun bashi lamban yabo, na gwarzon Sarki me zaman lafiya a cikin yankin shi. Jay yana da matukar kokari wajen bawa talakawan shi lokacin shi, yana amsa kokensu. Wanda haka ya karawa mishi soyayyar shi a zukatar mutane. Har yanzun Ina da yaro daya, nabi Jay akan Yasaka a dubani da kanshi yace min. "Yan matana lafiyarki lau, nine nake amfani da abin hana daukar ciki, dan haka abar tambayana ko bani da lafiya. So nake Jaish ya cika shekara bakwai, sai ki dauki wani." Takaici ya kama ni nace mishi.."da girmana zan ta Haihuwa? Kasan wahalar da zan sha nan gaba idan na samu cikin? Dake ba.." Shiru nayi sakamakon bakin shi ya daura akan nawa, cikin kwarewa da iyawa yake sumbatar, kafin wani lokaci har na manta da fadar da nake mishi, ba laifi ina samun nutsuwar shi, amma ba shi zai hana idan na bashi haushi ya kafta min rashin mutunci ba. Kai Jama'a Jay sai hankali, Jaish yana niman shekara biyu da rabi, Yaron yana da Hakuri, tun bai da wayo nake barin shi a gurin Mamah, ita take gaya min wai halin Ammin Jay yayi tana da hakuri bata da kwaraniya. Gata da bata cika son mutane ba, haka Jaish shima baya son mutane. Bayan shekara biyar cif, Yau ake sunan Raihanah ta haihu sai hidima muke, mu shiga mu fita har mun gama shiryawa Ya shigo min, zai kwanta nace mishi.. "Saraki lafiya?" "Zazzabi nake ji!". Tab'e baki nayi abin mamaki, yau kusan sati Daya Kenan, kullum sai ya dawo ya kwanta bai da lafiya, abin tausayi da al'ajabi Jay baya. Son warin girki, baya son kamshin turare. Bayan son magana, ga tashin zuciya. Yayi ta yunkurin amai, ranar nayi dariya da yake lissafo min halin da yake ciki, nace mishi. "Gaya min gaskiya yaushe nayi maka ciki!" Duk da yana fama da zazzabin sai da yayi dariya yace min.. "Da alamu kai tunda kece kike lafiya ni ne akwance gaskiya kin gama haihu indai Ni zan cigaba da ɗaukar nauyin laulayin ki, gaba zaa iya cewa Ni zanyi nakudar. Allah hudu sun isa babu Allah yayi musu albarka." Tausayi ya bani, Jay bai son hayaniyar yara, kota mutane ne sai ya bar gurin, balle ta gidan, tunda aka dawo da Munih ya tattarata ya mikawa Mamah Sarah, Dama Maryama tana hannun Mamah Raihanah. Sai gidan yarage Jaish. --- Tare da Jay mukayi renon cikin jikina, ko nace cikin mu. Tunda tare ake laulayin,(🤣😹) Shima tun kafin na fara nakuda aka cire min shi, inda samu Y'a mace, ana bashi bai amsa ba, ya nuna musu kofar ni yake jira. Yana ganin Dr Fatihu ya juya mishi baya, har ya wuce. Yana tsaye bakin shi dauke da suna Allah aka fito dani, ina barci maganin. .... Bayan kwana bakwai. Yarinya taci sunan Ammin Jay, muna kiran ta da Jal Pharih, kyakyawar mu, dan kusan ta dauko Jay da Abban shi, har da Umma Rumana, tsohuwa. Haka dayawa mutanen sun zo suna, (Yo nima dai naga Yan Group din MI! Da Fans din KWARKWARAH! Ana ta dambe da kaza! Lekowa nayi nace kai mata dai ba a barin mu a gurin diban Gara! UmNass tace kedai bari Ai naga sunan har dasu Aaryaan Sultan! Da Neemrah, nace mata Eh ga AMIDUD da Matar Shi tayi Takwara Jal Pharih, Mommy Kautharh ta tab'e baki tace. Oni y'asu Addah Ramlat, Allah yasa karta musu halin Pharih! Kamar kin sani! Inji UmNass! Yan fitilar Hikayata suka ce! Addar mu, don Allah wacece wancan zinariya sai kyalkyali take, dariya nayi nace musu daya me alkyabar itace SAFINAH Ashraf! Wancan me doguwar rigar itace Amrah Sadeeq, Addah Amrah. Zasu kuma tambaya ta nace musu don Allah Mommy Sayyid kiji da Aunty Fatimah Mom Abul, sanan ki taimakawa Sister Maryama kolo da Maman Ummita da ruwa, idan zaki wuce akwai Mama Mai Voice ita da Aunty Sa'a mika musu wancan ruwan sanyi! Sannan na juya gurin Mommy Kautharh nace taimaka min kibawa Naman Abunah wannan kayan sunan) Anyi shagali sosai, sai dare aka watse duk na gaji wallahi, niman guri nayi zan kwanta, Jay ya shigo wai yana son shayi, haka na wuce dakin girki na dafa mishi, ina kaiwa ya wani langwabe min, ajiyewa nayi zan fita yace min. "Yan mata! Ko irin na yan gayu bazaki min ba, ki dan rungume ni sama sama!" Dariya ya bani, nazo na rungumo shi tare da shafa kan shi ina dariya sosai, d'agowa yayi sannan yace. "Kece sa'ata! Kuma nasara ta yana hade da taki, ban tab'a gani. Mace me kirki irin ki ba Nagode Binta!" Da wayo da hikima na gudu na barshi, --- Watan mu uku muka je Sokoto,duk da Jay yana matukar kokarin zuwa duk bayan wata shi, idan bai zo ba ni zan zo da Jaish. Hanisah tana nan Daura, sabida nan Hikmi yake aikin shi, kuma itama ta haihu yaranta biyu tana renon cikin na uku. Karama itama yaranta biyu, ne tana goyon na biyun kenan, Matar Fahad itama ta haihu, kuma muna zumunci dashi sosai, karshe naji ana cewa zai Auri Inam, Barka dan har yau bata hakura da Saraki ba, Yarinyar tasawa Dan jinjirin mijina ido, .... Tunda na isa sokoto, dayawan Yan uwan Baabi da na Mamana kasa hakuri suka yi inda suka fito da halin su a fili, na hassada, wai ai bana zaman dad'i maneji nake, wanda suka zo sunan Jal Pharih suka ƙaryata su, dan sun zo sunga yadda Jay yake makale ni idan na kai mishi abin karyawa ba. Ban san me yasa mutanen mu. Suke son ganin mace ta samu damuwa a gidan mijinta ba, sun fison kayi ta gayawa duniya mijina bai kyauta min ba, mijina ya cutar dani, Eh akwai haka amma muna biye Alkhairin su mu fidda sharrin su, ban.yabi maza ba amma dayawan mutane suna son jin mace tana kawo korafin mijinta, ba burgewa bane. Akwai damuwa a tsakanin mu, amma bana jin zan iya gayawa kowa. Allah yana sane dani. Haka na gama kwanaki na na dawo, suna son na gaya musu aibun Jay. Ni kuma nak'i sam, haka ya basu mamaki. Dan dai baki gaya musu kome akan mijina, duk wacce ta matsu ta biyo ni gidana. *** Bayan kwanaki da dawowa na, muna kwance yake gaya min ai Baban Munih bai da lafiya zai je duba shi a Nijar ko zan je. Cikin jin dadi nace eh. A cikin kwanakin muka dauki hanyar nijar har da Munih karama, muka je muka gaishe shi, daga nan muka shiga wannan kauyen da muka zauna da ya satone. A dakin muka kwana. --- bayan mun dawo ne ya dauke mu, muka tafi Umrah.. kwanan mu goma, muna gurin cin abincin, Sai ga Saifullah da matar shi tare da yar shi. Wani saka fuska Jay yayi tun da suka gaisa na kuma gaida matar ya sani dole muka mike, Jay akwai zafin kishi. Bayan mun dawo daga Umrah. Al'amuran yau da kullum sun cigaba da tafiya yadda ba'a tsammani. Kuma budi yana samu mu, dan Allah ya wadata mu da samu dai-dai fahimtar mai karatu. Dai dai gwargwadon, akwai bude kuma babu laifi. Ina samu a ta ko ina , musamman haihuwar Jal Pharih, na samu abin da bai tab'a zato ba, dan a ranar Jay ya mallaka min asibitin shi. ......Shi kuma Bana Bulama, ya bani kyautar fili a garin Abuja, tare da wani katafaren gida a garin Lagos, mai martaba sarkin borno ya bani gida da fili, yace a tambaye ni me nake so da filin, nace makaranta a ginawa marayu, Allah yakai ladan ga Iyayen mu mata. Filin Abuja kuma aka gidana asibitin JaiPhari, Baabina ya kuma bani shawara na fara kasuwanci, inda ya tambayi izinin Jay, akan tunda ina da dukiya ko za a fara min kasuwan ce daga ƙasashen waje, Jay yace ai duk abinda yayi duk me kyau ne. Haka kuwa aka fara kasuwancin cikin Yardan Ubangiji, sai ga Albarka ta ko ina. ...... Allah ya albarkaci rayuwar mu, ya inda Ni kaina ban yi zato ba, mijina dangin shi na gurin Uwa da na gurin Uba, kamar su lashe ni, dan ban iya son kaina ba, ina Alkhairi sosai. Mijina kuma ina alfahari dashi, tako ina rayuwa ta mike mana shima mulkin shi babu zalinci.... Yarana sun girma, kuma rayuwar su gwanin ban sha'awa. Alhamdulillahi nan na kawo karshen Kwarkwarah ( wato magajin Izzah) kuyi hakuri nasan wasu zasu ce bai musu ba, nima wallahi bai min ba.... Amma Insha ALLAH mu hadu a wasu musamman zanen kaddarata... Idan na samu lokaci na fara muku Insha Allah december, idan ban da lokaci zan ajiye Insha Allah mu shiga sabon shekara lafiya kuyi hakuri bana iya rike mutane, duk dadin labari nakan rabu dashi na huta kai ma ka huta... Thank You 🙏🏼💝 Thank You....