Showing 1 words to 3000 words out of 4770 words
Chapter 1 - BAKAR ANIYA 2 Writing By Alan Waka .docx
BAƘAR ANIYA 2
Hausa Novels
Writing by
Aminudden Ladan Abubakar Alan Waka
08137237071
Kamar kullum yauma mita ake tai mata da ba a farkon abin sun farashi ne da gaske amma da suka tsinka yi abin ba na kare barne, sai kuma suka saduda, daga haka abin ya koma barkwanci a tsakaninta da mutanen gidansu. Sun dade suna mamakin kafewarta akan saurayi daya, kowa ya zo bai koma dawowa, sannu a hankalima da kansu šamarin da suka fuskanci haka, sai suka daina zuwa, tun abin na hata wa iyayenta rai, har dai suka zuba mata ido. A bisa hujjarsu ta cewa ba a san inda rana zata fadiba.
Ta tsantsara kwalliya mai daukar hankali, tare da tanadin kayan tande-tande, don tarbar masoyinta Auwel, saurayi guda tamkar da dubu, a gurin lauwa'u mutum kwya daya wanda bata gajiya da gani, kyakkyawan duba a idaniyar Hauwa'u, wanda ako yaushe idan ta daga ido
yayin da ta kau da ido kuma ta sake dubansa, sai ma ta ga ta dube shi, sai ta gan shi kyakkyawa fiye da kullum, a Amintacciyar kaunar da suke yiwa junansu, ta sanya har har ya liye mata dazu kyau, don kauna mai aminci an gaza gane wanda ya fi wani son dan uwansa, a tsakaninsu.
Abu ne wanda ta sani, duk inda Auwalu ya je ya komo ba zai kwashe minti talatin a cikin unguwa da komowa, ba tare da ya zo sun gana da juna ba. Don haka to yi masa kyakkyawar tanadi na irin abubuwan da ta san yana so.
Wani dan yaro ne ya shigo, a shekaru ba zai wuce sha biyu ba, bayan sallama da 'yan gaishe-gaishe, sai ya bayyana cewar Auwalu ya yi hatsari yana asibti. A guje ta fito daga cikin daki, hankalinta a tashe da abin da kunnuwanta suka jiyo mata.
'Kai ya mutu. Ta fada a san da ta zazzaro ido, hannunta a dafe da kirjinta.
'A'a, bai mutu ba, amma an ce ya jijji ciwo, kuma an kwantar da shi.'
Ta fashe da kuka, mai tada hankali, zuciyarta ba ta yarda da abin da yaron ya fada ba. Ita a ganinta rufe mata aka yi amma Auwalu ya mutu.
***
Awanni basu fice biyar ba da afkuwar abin, amma idan ka dubi Hauwa'u sai abin ya nemi ya saka kuka, don
tausayi, duk ta fita kamaninta ta rame kai ka ce ta kwanta ciwo. Duk sun yi zungum-zungum a gefe guda, likita ya hana kowa shiga, lokaci zuwa lokaci ita kadai ke safa da marwa, a farfajiyar asibtin, irin yadda fluskarta ta nuna damuwa ko uwar da ta haifi Auwalu fuskarta bata nuna haka ba.:
Ba' jimawa sai ga Abbas, ta yi maza ta isa gurinsa, tana mai mayar masa da jawabin yadda abin ya afku kamar yadda wadanda abin ya afku akan idonsu suka bayyana, shima abin ya yi matukar kada shi, har sai da ya yi hawaye don jimatawa.
Kowanne bigire na dayan biyun bangarorin da ke kokarin kulla alakar auratayya, a tsakanin 'ya'yansu, abin ba karamin dagula musu lisafi ya yi ba. Ba'ada bayan komowar hannun agogo bay, a bangaren shirye-shirye, suna cikin tashin hankali da ta rarrabin samun lafiyar yaron. Domin kuwa yau an kwashe tsawon sati biyu, amna yaron ko magana ba ya yi balle ya sar wanda ke tsaye akansa, a cewar likita dai wai saukl na samuwa ta fuskar raunukan da ya ji a jikinsa, kuma zai warke sarai.
Amma abu mafi firgice da tsoratarwa, shine kalamin likita na karshe, na cewar kansa ya bugu, in ba a yi sa'a ba, kwakwalwarsa ta dan tabu, a cewarsa wai kada a sami damuwa komai zai yi sauki cikin yardar Allah.
Duk da kokarin likita na amfani da kalaman kwantar da hankali, hakan bai sa sun yi tasiri a zukatan bangaren iyayca yarinyar ba, don su har sun saduda, da maganar aure, tun da yaron ya sami tabin hankali. A tunaninsu na cewar ba a Sari a kwashe dai-dai.
Hauwa'u ke ta faman dawainiya da shi, kullu yaumiu, tun daga safiya har zuwa dare. Wanda bai sani ba idan ya ganta zai dauka ita ce mara lafiyar, duk ta fita
kamaninta. Ta kuma kudurcewa zuciyarta cewa ko da Allah bai nufi Auwalu da tashı ba, ita da aure sai a kiyama, a tunaninta na cewer samun miji irin Auwalu a wannan zamani sai mai rabo, kuma idan Allah Ya tashi kafadunsa ko babu hankali, ita sai ta aure shi haka nan, domin kuwa bata ga dalilin da zai sanya ta yi masa butulci ba don kaddara ta haukansa.
***
Alhaji Yakubu ne da uwar gidansa, ke tattaunawa akan rashin lafiyar Auwalu, abin ya yi mutukar damunsa, ya kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, tun daga lokacin da abin ya faru. Shia ganinsa shi ke da hakkin bin duk wata hanya da za a bi don ganin an sada Auwalu da lafiyarsa.
Alhaji sauki na Allah ne, duk inda ka daukíAuwalu ka kai shi yana iya samun sauki. Kuma ana iya samun akasin haka. A saboda haka ne nake shawartarka, da ka kara hakuri kamar yadda likita ya ce, zuwa dan wani lokaci, in ya so idan bata sake zani ba, sai a canza masa asibitin. Uwar gida Zainab ta fadi.
'A to ni dai na riga na ka'ide musu lokaci, daga yau zuwa sha biyar ga watan hudun (15th April). Idan bai sami saukiba zan dauke shi zuwa kasar Indiya. Allah shi ne mai bada sauki. Shi kuma ke shirya duk abin da ya so ga hawanSa, amma ni a gurina duk abin da ra yiwa Auwalu ban fadiba. Auwalu ya cancanci in yi masa abin da ya fi haka, samun yaro mai nutsuwa da kamala da son
addini, irin Auwalu sai an tona, kwarai kuwa fada yake yana nanatawa.
1 GA AFRILU, 1988
Tsawon watanni uku da Auwalu ya kwashe a asibiti, har izuwa yanzu, bai san a halin da yake ciki ba. Dukkanin wani sashi da ya sami rauni a jikinsa ya warke, sarai, kamar dai yadda likita ya ambata inda har yana iya zama yana iya tashi tsaye. Amma kuma fatar bakinsa dai dai da motsi, ba ta yi da sunan magana, sai dai kallo da ido kawai.
Wani abin ban tausayi da kan iya sanya duk wani mai imani, yanke kauna da duniya, ya ji a ransa da ma ba a yi shi ba, har ya yi burin mutuwa, shi ne. Idan ka dauki cokali ka mikawa Auwalu bai san shi ba bai san abin da ake da shi ba, kai bai ma iya gane ma'anar mikawa karbi. Sai dai kawai ya bika da kallo, tamkar yaron dan wata uku da ya fara gane mahaifiyarsa, a lokacin duk da ya ji yunwa sai ka ga yana ta bin gilmawarta da. kallo.
Auwalu bai iya gane mahaifiyarsa ba kuma ya iya rabewa da 'yan uwansa, hatta Alhaji a yau Auwalu bai san shi ba wannan dalili shi ya samawa wata cuta muhallin zama dirshan a cikin zuciyar Hauwa'u (Heat attack).
A lokacin da sauki ya samu a gare shi, aka fara fuskantar wannan matsala, Hauwa'u ta zo gaban Auwałta yi magarar duniya Auwalu bai tanka ba, ta gwada shi fă abubuwa da dama, sai ta gama kwata-kwata tamkar a lokacin ne Auwalu ya fara dora idonsa a kanța, Auwalu ba zai iya tuna wata alaka da ta taba shiga tsakanitisi da ita ba, don shi gani yake baj ma santa ba, a wannan lokaci.
Dai-dai da second ko minti lauwa'u ba "an taba mantaki ba, babu wani abu da zai gudana a tare da ni, ko a na nake, face, tunaninki na manne a cikin zaciyata, kin lini bayyana kauna ne a zahiri, ni kuma na fiki a zuci.
Ta fasa kuka, mai tsuma zuciya, mai razanarwa, mai kidima wanda duk ya ga faruwar abin da idonsa. A lokacin da tunanin wadannan kalamai na Auwalu suka fado mata.
Amadadin wadanda ke gurin a sami masu bata baki, a'a, sai suma suka bada gudunmawar da nasu hawayen.
Tun daga lokacin da Auwalu ya zama haka, sai al'amura suka sauyawa Hauwa'u, sama da watanni biyar da suka wuce bata taba fashin zuwa asibiti ba, amma daga sanda Auwal ya zare, sai ita ma ta zama yau lafiya gobe cuta. Wani lokaci matsanancin zazzabi da ciwon kai ke addabarta, wani lokaci kuma ciwon ciki da amai (Kunnallo)
Hankalin iyayentá ya yi mutukar tashi tsoro ya baibayesu, ganin irin yadda take ta faman karewa tamkar ruwan guzuri. Ko in ce mai (HIV). Hauwa'u ba ta iya cin abinci, ko kanshinsa ma ta ji sai zuciyarta ta rinka tashi, wani lokaci ma har sai ta yi hararwa.
***
Ranar laraba rapa ce wacce ta zo dai-dai da 14 ga watan Afiritu, wato jajiberin ranar da Alhaji ya dauki alkawaria canzawa Auwału asihti kamar yadda ya yi
alkawari. Haka kuma rana ce da ta yi dai-dai da ranar da rikirkitaccen al' amarin ya fara bayyana.
Domin kuwa wannan rana ne aka nika Hauwa'u ga likita, don ya binciko a ga ni ko wacce irin cuta ce ke shirin nakasa Hauwa'u ba kamar yadda wadansu ke rayawa ransu, abin da tunaninsu ya doru akai ba, irin masu hangen cewa ai ciwon son Auwalu shi ya harbi Hauwa'u.
ANA WATA GA WATA
B ayan 'yan aune-aune da likita ya yi, a kokarinsa na gano cutar da ke kokarin karar da Hauwa'u sai kuma ya ajiye kayan aiki ya nemi su dan tattauna ya yi mata 'yan tambayoyi.
Matsala ta farko, dai baya bukatar ya yi mata tambaya akai domin ya san abin da ya gadar mata da cutar, sai dai kawai ya yi mata 'yar nasiha da gargadi. Akan hakuri da dangana, gami da gargadin samun hutu, da kawar da damuwa a rai da rage yawan tunani. Har ma ya kara da sanar da ita illolin da rashin kiyaye wadannan za su ci gaba da haifar wa idan ba ta kiyaye ba, na daga cikin irin matsalolın cutar hawan jini da ke shirin afka mata daga yanzu zuwa kowannen lokaci.
Likita ya nisa a karo na farko, a yayin da yake dubanta ido-da-ido.
'Wannan bawan Allah da aka kwantar, wanda ke da matsalar (Memory Gland) (Lossion memery) dan uwanki ne ko kuma mijinki ne?' ya tsareta da ido yana sauraron abin da za ta fadi.
Gabanta ya fadi don rashin fahimtar dalilin da ya sanya shi yi mata wannan tambayar. Amma kuma har kullum a shiye take, da toshe duk wata kafa da ka iya bawa wani damar ya ce yana sonta, ko wani abu mai kama da haka, bisa wannan dalili sai kawai ta ba shi amsa kai tsaye.
'Auwalu mij; ba ne.
'Mijinki ne?' ya sake tambaya, don ya tabbetar. Kwarai kuwa mijina ne.
'Okey Congratulation a yanzu kina daulle da juna biyü yau tsawon wata uku.'
A lokaci guda fuskarta ta sauya fiye da yadda ka ke zato, shi da kansa ya dan yi mamaki na ganin bacewar walwala daga da fuskarta da hanzari haka.
'Malam ban fahimceka ba."
'Ina nufin kina dauke da jaririn ciki tsawon wata uku.' Ya kuma nanatawa yana dubanta ido da ido.
Duk da matsanancin ciwon dake addabarta a wannan karon sai ta ji ta wasai, kai ka ce da dai ba ta yi ciwo ba, idan ka dauke rama. Fuskarta kunshe da, matsananciyar tsana da kiyayyar wannan likita, a bisa abin da yake kokarin lakaba mata.
Malam ta yayá ake daukar ciki ne? ko ko ana shansa a ruwa?"
'Oh!, wannan kuma sai ki je ki tambayi mijink. Ransa a bace, wannan karon.
'Likita bani da miji, hasalima tun tashina ban taba kusantar da namiji ba, abin da nake nufi da cewar Auwalu mijina ne, da shi aka vi mana alkawarin aure. Ta dan saki ranta a wannan karon.
'To, idan ya kasance haka ina ganin a ruwan ki ka sha kenan. Ya fada yana kallonta shekeke. saboda tana kokarin raina masa hankali.
Ta bude baki za ta yi magana, ya dakatar da ita a lokacin da yake yi mata nuni da hannu.
'Tashi maza ki fita waje mara kunya.'
Ta hassala, a lokacin da ta gimtse bakinta da nufin hadiyar yawu, amma sai ta yi rashin sa'a ya kafe.
In kuma ar saini akasin haka ubanka ne ya yi min ko? ta fada masa tana kuma kallonsa, babu tsoro ko kyas! A cikin zuciyarta.
Wannan shine karo na farko a tsawaicin rayyuwarta, da ta zagin wani mahaluki ido da ido. A lokacin da shi kuma ya zaro idanunsa alamar kaduwa don mamaki, shima wannan shine karo na farko a rayuwarsa a bangaren aiki, da aka taba yi masa cin fuska, kamar haka.
Ya yi mata kallon natsuwa, sai kuma ya firgita da ita don kallon kwayar idonta kadai, ya isa ya fassara maka cewar yarinyar bata ki a mutu ba. Kuma ta fadine tana nufin hakan har zuci don haka sai ya ajiyeta a gurbin mahaukata, ya fita abinsa.
***
Hankalin iyayen Hauwa'u ya tashi, suka kidime da jin abin da likita ya fadi. Basu yarda sun bar wannan asibiti ba, sai da aka sa wani likita daban ya sake aunawa, shima ya ce ciki ne. duk da haka basu amince ba musamman ma saboda irin kidimewar da Hauwa' la vi ta rinka rantsuwa da girman zatin Allah akan cewa bata taba zina ba, haka ta sanya su zuwa wani asibitin daban nan ma dai duk sakamakon daya ne.
Daga nan fa dangi suka yi mata cah! Har da duka akan sai ta fada wanda ya yi mata ciki. Bakin lauwa'u bai mutu ba, rantsuwa dai take da da yi, tana mai-maici akan bata taba zinaba. Bakin ciki dubu da miliyan a
gurin Hauv'u a wannan lokaci ubanta mahaifi malam Isa, shi ya tsawatar ga barin duka da tsangwamarta, tare da gargadar ga masu kokarin tursasata, akan sai ta fadi wanda ya yi mata ciki, don ganin halin da take ciki na rashin isashshiyar lafiya, ga kuma bakin cikin da ke damuuta kashi-kashi, in an ma dauke abin da cikinta ke dauke da shi. Hangen wadannan ya sa ya fahimci hadari da yarinyar take ciki da wanda su da kansu masu kokarin tursasata suke ciki yana da yawa.
Ku kwantar da hankalinku, babu wani abin daga hankali akan wannan. Hauwa'u dai ai kowa ya san mijinta a garin nan, gaggawa ce suka yi ma juna, saboda gajen hakuri, amma duk garin nan dk wanda ya san lauwa'u, to yana iya bada shaidar ya santa da Auwalu, ba ta da wani saurayi sai shi, muma shi muka sani, don shi ta nuna mana, kuma mun yarda ta yarda Auwalu, ma ya amince haka zalika iyayensa, a inda har ta kaimu ga batun aure. Sadaki ya rage ya ida cika cikakyan aure, wannan kuwa ko ni ina iya biyansa, kakaf! Sharuddai sun cika in kun dauke sadaki. Shi kuwa dama akan yi shi lakadan, au ajalan, don haka babu komai, wannan ba cikin shege bane na Auwalu ne, Allah Ya ba shi lafiya.' In ji Malam Isa.
Sai kuma hankalin kowa ya kwanta don gamsuwa da abin da Malam Isa ya fadi.
Bakin ciki da takaici ya turnuke Hauwa'u amma kuma duk da haka bata tanka ba, abin da ya fi daga mata hankali guda daya ne, shine masoyinta Auwal, ya ya zai ji idan Allah Ya ba shi sauki, ya kuma sami labarin tana da ciki, bayan kuma shi da ita basu taba ko da shafar jikin juna ba balle a kai ga ciki? Shin ko dai ana daukar ciki a mafarki ne? ta yima kanta tambaya, 'Kwarai kuwa sai in
ana dauka a mafarki, ko kuma kamar yadda likita ya jaddada min cewar na sha ne a ruwa. Amma kuma in dai ba haka ba ya ya aka şi na yi ciki ni Hauwa'u?"
Tana zubar da hawaye bata sani ba.
To, ko kuma aljanu ne? idan ya kasance kuma aljanu ne to, wacce hanya suka bi haka babu ko da alama, shin ko kuma tsafi aka yi mini ni Hauwa'u? shima kuma ai babu ko da alama, ba kuma sanadi. Sai kuma ta kara fashewa da kuka mai jijjiga zuciya, a duk lokacin da tunanin nata ya zurfafa, ta kuma kasa gano bakin kullun, kuka shine abin da ita kan dan yi ta sami sawaba.
Allah Kai Ka jarrabeni da wannan al'amari, wanda ya gagari tunanina, ya fi karfin hankalina, ga shi gangar jikina ma ta kasa daukarsu, cuttuttuka a jikina sun hana mini ko da cin abinci, ga bakin cikin da na san shine sanadiyyar komawata gareka Allah, tun da ka kaddari haka a rayuwata, ina yi maka godiya Ya Allah, ina kuma rokon ka daka bayyana askiyar wannan boyayyen al'amari, tun ina da sauran rayuwa kafin in mutu, Allah ka baiwa masoyina Auwalu lafiya, ka tashi kafadunsa, Allah ka sanya ni daga cikin matansa na aljanna, idan ina da rabon shigarta, don rahamarKa Allah, Allah don isa da Carfin mulkinka, ina kuma tawassuli da kaunar da nake yiwa fiyayyen halittarka Allah, na yi tawassuli da kaunar ahlubaiti da ka wajabtata akaina Allah, hade da ayyukan alkhairi da na yi karbabbu.
sai kuma kuka ta hanyar kwaranyar da hawaye masu kuna, zazzafan zazzabi da ciwon suka yi mata dirar mikiya, ta inda a duk sa'ar da ta sauke numfashi ko ta ja, ba ta tsammanin zata sake yın wani ba a kiyama ba.
ALHAMIS
15 ga Afrilu, 1998
D ukkanin wani kai kawo, Alhaji ya gama shi a game da shirin da ake, na mai da Auwalu kasar INDIAN, kasar da suka yi fice suka kere sa'a a Bangaren kwararrun likitoci. Lallai kam a yau duk wani abin da ka ji an ce an kasa shi, to kudine suka gaza, haka ma abin da ka ji ana ce an yi, to akwai wadatuwar kai din zamani. kudi abokin aikinmu a yau
Ba a fuskanci wata mushkila ba, jirgi ya daga da Auwalu zuwa kasar (Hindu) masu kuka na yi, don tunanin ba lallai bane ya komo masu kuma farin ciki na vi, wadanda ke da yakinin mutukar an je zai samu lafiya, sai