Showing 1 words to 3000 words out of 52236 words
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002)
Bright pens 3rd batch.
(2025)
Bismillahirahmanirrahim.
*Labarin BUZU ƙirƙirarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.*
⚠️ Labarin mallakina ne, ban yarda wani ko wata, su yi amfani da shi ta kowace irin siga ba, sai da izina.
AISHA ADAM
(Ayshercool)
08081012143
Arewabooks; Ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
Page 1
Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.
Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.
"Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?"
Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba"
"Dans quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".
"Bai fi awa ɗaya ya rage ba"
"Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka"
Ya yi maganar yana haska fuskar wani matashin mutum, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar.
Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin matashin, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!.
Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi"
Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar.
*****
Misalin ƙarfe shida da mintuna goma sha biyar na safiyar ranar asabar, ɗaki ne madaidaici, wanda ya samu kyakkyawan ginin ƙasa ma ƙwarin gaske, duk da kasancewar sa na ƙasa, amma adon da aka yi masa ya bayyanar da darajarsa.
Can daga kusurwar ɗakin wata matashiyar mace ce, kwance a kan matsakaiciyar katifa ta yi ɗaiɗai ta na bacci, zaninta ne kawai ya kare bayyanar tsiraicinta, amma idan ta yi kyakyawan yinƙurin za ta yi tsirara.
Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi daga baccin, amma abu ya gagara a sakamakon sleep paralysis, wanda a hausance da kuma fahimta ta mutane suke kira da dannau, a cewar mutane wani aljani ne mai suna dannau, yake danne mutum ya kasa motsi, alhali idanunsa biyu, kamar a zahiri haka ta din ga ganin abubuwan da suke faruwa da ita, amma ta kasa motsawa.
Tamkar an cire mata wani abu mai nauyi, haka tayi firgigit ta tashi zaune, ta na mayar da numfashi, a sakamakon fafutukar da ta sha, kafin ta samu ta iya farkawa daga nannauyan baccin da take yi mai kama da na mutuwa.
Ware ido tayi, ganin yadda gari ya yi haske, ba tare da ta gabatar da sallar asuba ba.
Ta yinƙura za ta sauka daga kan katifar, ta ji duk gaɓoɓinta na yi mata ciwo, jikinta kamar wadda aka yi wa dukan tsiya, zanin jikinta ya yaye.
Shiru ta yi ta na ƙoƙarin tuna abin da ya faru a daren jiya, a iya saninta ninkin kaya take yi, ba ta kai ga kwanciya ba, daga nan ba ta san abin da ya faru ba.
Ita dai ta san sanye take cikin suturarta, amma yanayin da take ganinta a ciki, yana sanya mata wasi-wasi.
A hankali ta tashi ta gyara zaman zanin ta nufi banɗakin da yake cikin ɗakin, domin ta kintsa jikinta ta gabatar da sallar asuba.
*****
Sannu a hankali yake buɗe idanunsa, da suke yi masa wani irin zugi saboda hasken da ya cika masa su, sai ya ji tamkar hasken wani baƙon abu ne a cikin idanun nasa. Yanayin ya yi masa kama da farkawa cikin wata duniya ta daban.
A hankali ya daina jin zugin da idanun suke yi masa, ya buɗe su tanagrau, ya ƙurawa wurin da yake ido, yana ƙoƙarin gano a ina yake.
Wani dogon mutum ne baƙi, fuskarsa ɗauke da jan rawani hannunsa rike da ɗan ƙaramin kofi, ya shigo cikin tantin.
Jifa yayi da kofin hannunsa, ya nufi mutumin da yake kwance da matuƙar hanzari.
Taimaka masa yayi ya tashi zaune, fari ne amma ba tas ba, irin mai sirkin yellown nan, ya na da ɗan siririn hanci, dai-dai da siririyar fuskarsa, sai gashin baki kaɗan da ya haɗe da ɗan madaidaicin gemunsa, sai kuma manyan idanuwa da yake da su, da su ka kaɗa su ka yi jawur tamkar jini zai kwararo daga cikinsu.
Zaman da ya yi, ya bawa gashin kansa damar kwanciya a kafaɗarsa zuwa bayansa, tamakar mace.
A hankali ɗayan ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Sannu ya jikin naka?" Maimakon ya bashi amsa, sai ya yi shiru ya na bin sa da kallo.
"Akwai abin da yake yi maka ciwo ne?"
A hankali ya motsa bakinsa ya ce "Ina ne nan?"
Baƙin ya kalli gurin sannan ya mayar da idonsa kan shi ya ce "Mun shigo Nigeria ne yanzu haka"
"Nigeria?" Ya maimaita.
"Eh Nigeria" ya amsa masa.
Ya yi shiru ya na ƙoƙarin tuna a ina ma ya taɓa jin sunan.
"Ya na ga ka yi shiru ne? Ka gane ni ma kuwa?" Ya ɗago ya kalle shi a hankali ya girgiza masa kai alamar a'a.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ba ka sanni ba ka ke nufi?" Ya jinjina masa kai.
"To ka san sunanka?"
Yayi shiru yana ƙoƙarin yin tunani, amma ya gaza tuna komai, sai ma wani irin rugugi da ya ji a cikin kansa tamkar an yi aradu, hakan ya tilasta masa dafe kansa yana rintse idanunsa.
"Shi kenan ya isa, ba sai ka tuna ba, amma ka san alwala da salla?"
Ya ɗaga masa kai alamar eh, ba tare da ya yi magana ba.
"Sallar asuba raka'a nawa ce?" Ya ɗaga masa yatsunsa guda biyu.
"Azahar fa?" Ya nuna masa huɗu.
"Ka san salla, amma ba za ka iya tuna komai ba bayan haka?"
"Eh" ya amsa a taƙaice.
"Shikenan, ka zo ka yi alwala sai ka rama sallolin da suke kanka, ka yi ƙasaru, tun da mun yi tafiya mai nisa daga Nijar".
Shiru ya yi ya na son tuna a ina kuma ya taɓa jin sunan Nijar, sai kawai ya bar shi a sunan da ya ji ya faɗa ɗazu ne Nigeria.
Cif ya jera sallolin kamar yadda wanda suke tare da shi, ya gaya masa waɗanda su ka tsere masa.
Ya ɗaukko abinci ya bashi, ya saka hannu ya karɓa ya fara ci.
Bayan ya kammala cin abincin, ya tsiyaya masa shayin da ya dafa a cikin ɗan ƙaramin kofi ya miƙa masa.
Ya karɓi shayin ya fara sha, hakan ya sanya shi fara ƙoƙarin tuna wani abu, amma abu ya ci tura. Bayan ya gama shan bunun, ɗayan ya fito da wani ƙyalle ya tattare masa dogon gashinsa, ya naɗe masa shi, sannan ya naɗa masa rawani ya kamo hannunsa su ka fito daga cikin tantin.
Tsayawa yayi, ya yi wa wurin ƙuri da ido, jeji ne babu kowa a wurin, sai bishiyu sai kuma wani raƙumi da yake gefe a ɗaure ya na ta taune-taune.
Ya tafi ya kwanto raƙumin, ya janyo akalarsa zuwa gabansa, ya kalle shi ya ce "Ka san menene wannan?"
Ya jinjina kai.
"Mene ne shi?"
"*Le chameau*" (Camel/ raƙumi ne)
Yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce "Hau mu tafi" ya taimaka masa, ya hau kan raƙumin, shi kuma ya ja akalar raƙumin su ka tafi.
*****
Tafe take sannu a hankali, ta na ratsa matsakaitan gidajen da su ka haɗu suka samar da rukunin gidajen da suka samar da wani ɓangare na unguwar.
Mamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin ƙwarya awanni kaɗan da suka shuɗe, ya wanko datti da ƙazanta daga mabanbanta wurare, sai dai rashin kyakyawar hanya da magudanan ruwa, ya sanya ruwan shiga gidajen mutane, wani kuma ya kwanta a cikin layuka, ta yadda ba a iya banbance kwata da hanya, duk sun haɗu sun shafe.
Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, abin da take tsoro da fargaba ta tarar, tun da hadarin nan ya taso aka fara ruwa, hankalinta ya kasa kwanciya.
Daga in da take ta na hango tsakiyar tsakar gidansu, a sakamakon fiye da rabin katangarsu ta zube.
Ta lallaɓa ta ƙarasa, duk mutanen gidan su na tsaye sun yi cirko-cirko su na jajanta abin da ya faru.
Sai dai abin da ta tarar ya fi wanda ta hanga daga nesa, domin ƙarasawarta gidan ke da wuya, ta tarar rijiyar gidan ta burma, ta haɗe da masai kasancewar daf da juna suke, daga in da aka yi rijiyar babu tazara.
Wani babban mutum ne ya fito daga cikin banɗakin, ya dubi matashiyar ya ce "Nana kin dawo?"
Jiki a sanyaye ta amsa ta ce "Eh Baba"
"Kin ga abin da ya faru ko"
Nana ta ce "Eh baba, tun ina makaranta da aka fara ruwan nan, hankalina yake tashe nake a tsorace"
"Ai mu na cikin jarrabawa, yanzu lalubawa zaki yi, ɗan abin da aka samu a hannunki, ki kawo a samu ko katangar a fara tayarwa".
Saroro Nana ta yi baki buɗe tana bin Baba da kallo, duk da ba abin mamaki bane ba, jin hakan daga bakinsa, cikin ƙarfin hali ta ce "Baba dubu bakwai ne fa albashin nawa, kuma yau goma sha ɗaya ga wata, ko sisi ba ni da ita ka manta dubu biyar ka karɓa ka bani dubu biyu"
"Kai Nana, ina ki ke kai kuɗi ne? kullum da an taɓa ki babu, ai shikenan sai ku zauna haka, duk wanda ya ji turotso sai ku bi maƙwabta ko ku tafi jeji ku yi, ni ba ni da yadda zan yi"
Wata mata da tun da su ka fara maganar ba ta yi magana ba, sai yanzu, ta kada baki ta ce "Ai kuwa sai ka san yadda za ka yi, haka zamu dauwwama mu na gantalin yawon kashi a maƙwabta kai ko kunya ma ba ka ji, Nana ka tsare ka na ta baka kuɗin da zaka ɗaga katangar gidanka, kai fa take miƙawa albashin nata, dubu bakwan nawa take, ka bi ka kashe zuciyarka, wallahi dole ka nemi yadda za ka yi"
Nana dai ba ta sake cewa komai ba, ta nufi hanyar wurin kwananta, ta na jiyo ɗaya daga cikin yaran gidan ya na cewa "Abu mai sauƙi, a samu ƙaton bokiti kawai, kowa ya din ga juyewa a ciki, a tara a sayar zazzafan taki ne fa, tsaf za a samu kuɗin ɗaga katangar gidan nan, gwargwadon ƙwazonmu wurin tarawa da yawa gwargwadon.....
"Za ka rufe mini baki, ko sai na daka ka a wurin nan, shashasha mara tunani kawai"
Baba kuwa waje ya yi, saboda tijarar da mama ta fara yi masa, maƙwabta duk sun fito waje, ana jajanta ɓarnar da ruwan yayi a layin, tare da jajantawa su Baba abin da ya faru da su.
Jiki a sanyaye ta shiga wani ɗan madaidaicin ɗaki, bakinta ɗauke da sallama.
'yan mata biyu ne a kwance su na danna waya, da ƙyar ɗaya ta amsa, ɗayar kuwa ko ɗagowa ba ta yi ba.
Nana ta ajiye jakar hannunta tare da faɗin "Jamila, ashe ruwa ne yayi mana gyara haka?"
Jamila ta ce "Aikam, ɓarna ma ba ƙarama ba, kin ganni nan lissafi nake yi yadda zan tsallake na bar gidan nan, wannan abin kunya da mai yayi kama, ace in da zaka tsuguna ka juye najasarka babu, sai dai ka bi maƙwabta, wannan gidan Allah kaɗai ya san lokacin da za a gyara shi".
Nana ta nemi wuri ta zauna ta ce "Idan kin bar gidan nan, ina za ki je?"
Cike da takaici Jamila ta ce "Ko ma ina ne, tun kan jarabar talauci ta kashe mutum, kullum gida babu cigaba ba a ɗauki ɗawainiyarka ba, amma ana nema a wurinka"
Nana ta girgiza kai ta ce "To, Allah ya sa mu dace, ya bamu mafita".
"Amin, kalli wurin kwanciyar ki ma duk ya jiƙe, nan wurin ma zuba yake yi".
Nana ta kalli wurin tare da yin ajiyar zuciya, ba tare da ta ce komai ba.
Haka gidan su Nana suka kwana, rabin katanga a zube, kowa ya zo wucewa ya na kallon cikin gidan.
Washegari da asuba da 'yan kame-kame su ka kama ruwa, wasu su ka zagaya maƙwabta wasu kuma suka yi a wani wurin, su ka yi alwala su ka gabatar da sallar asuba.
Tun daren da abin ya faru maƙwabta suke shigowa yi musu jajen abin da ya faru.
Jamila sai masifa take yi tana mita, "Wallahi na san ikon Allah ne kawai zai sanya a gyara katangar nan, haka zamu ci gaba da zama da zubabbiyar katanga, ni matsalar banɗakin nan ba ta dame ni ba sama da katangar nan, duk asirinmu a tone, kodayake wane asiri ne ma da mu, banda damin talauci da tsiya"
Nana ta na jin ta ba ta ce uffan ba, ta ɗaukki Alqur'aninta tana dubawa.
*****
Tsura masa ido yayi, yana nazarinsa, sannu a hankali yake cin abincin gabansa, ya gama ya wanke hannunsa, ya gyara zaman rawaninsa ya rufe fuskarsa.
Habu ya dube shi ya ce "Ka ƙoshi?" Ya jinjina masa kai alamar eh.
"Yanzu za ka iya tuna sunanka?" Ya girgiza kai alamar a'a.
Habu yayi ajiyar zuciya yana sake jinjina lamarin, ya sake kallonsa ya ce "Babu abin da yake iya zuwa kanka ka tuna?"
"Eh" ya faɗa a taƙaice.
"Shikenan, kar ka matsawa kanka sai ka tuna wani abu, amma a duk lokacin da ka tuna wani abu ka sanar mini, dole in fara tunanin nema maka magani kafin yin komai, amma sai mun samu wurin masu amana" shi dai yayi shiru bai ce masa komai ba.
Ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa, ya ɗaukko waya, ya duba wata lamba, ya kara wayar a kunnensa.
Mintuna kaɗan ya amsa sallamar sannan ya ɗora da cewa "Mun iso Nigeria tun jiya, yanzu mene ne abu na gaba?" Ya ɗan yi shiru tsawon wasu mintuna sannan ya ce "Ka tabbatar babu matsala? Ba na son azo a samu matsala, dole ayi taka tsantsan da lamarin nan, kafin mu san ma in da za mu nufa neman maganin" ya sake yin shiru sannan ya ce "Shikenan, ina sauraronka" har ya kammala wayar bin sa yake yi da ido, kamar zai yi magana amma bai ce komai ba.
*****
Kwanaki uku suka shuɗe ana tsilla-tsillar makewayi a gidan Malam Isa, wato gidansu Nana, ƙarshe katanga sai buhu aka saka aka rufe ta.
Cikin ikon Allah, maƙwabta su ka yi ta kawo masa gudunmuwa, sai dai idan kuɗi ne sai ya karɓa ya saye abin sa, tun da matarsa rabi ta fuskanci haka, ta sanya shi a gaba da tijara, da masifar ya fito da kuɗi a san abin yi.
Nana ta na ɗaki tana shafa mai, amma hankalinta yana kan su Baba sa suke ta faɗa.
"Amma rabi da kuɗaɗen gudunmuwar nan, nake ta baku kuɗin cefane, kuɗin nan fa ba isa za su yi ba ayi aikin katangar nan"
Ta hayyaƙo masa cikin ɗaga murya ta ce "Wane cefanen, ba wata tsiyar ka bamu ba, makewayi ya gagari mutum, kamar mun fi kowa talauci a tsukin nan"
Nannauyar ajiyar zuciya Nana ta yi, ta tashi ta ƙarasa shirinta, ko sallama ba ta yi wa su Baba ba ta fice, dan wannan rashin girmamawar da suke yi wa juna ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba.
Kamar yadda ta saba, tana ƙule a gefe guda, tana dudduba cikin Alqur'ani, yayin sa sauran 'yan ajin suke ta tilawarsu daban.
A hankali ta fara jin jikinta yana wani irin sanyi, ta fara jin tamkar daga wata duniyar take jiyo karatun 'yan ajin nasu.
"Nana" ta ji muryar Amira ƙawarta.
Tayi jarumta ta ɗaga kai ta kalleta, Amira ta zauna a kusa da ita ta ce "Na biya miki makaranta, ashe abin da ya faru kenan, Allah ya mayar da alkhairi ya tsare gaba, na tarar da baba yana ta faɗa, wai kowa ya nemi in da zai tafi kafin Allah ya hore masa abin da zai gyara gidan"
Sai Nana tayi da gaske take fahimtar me Amira take faɗa, ganin yadda Nana ta ƙura mata idanu ko ƙiftawa ba ta yi, ya sanya ta ɗan matsa baya kaɗan ta ce "Nana lafiya kuwa? Ko baki da lafiya ne?"
Ta girgiza mata kai, ba tare da ta ce komai ba. Amira ta koma gefe ta ɗaukko Alqur'aninta, ta koma nesa da Nana.
kamar wadda ake zarewa laka, take ji, wani irin sanyi jikinta yayi zuciyarta ta din ga bugawa cikin matsanancin tsoro da fargaba, numfashinta ya dinga sama-sama kamar zai bar gangar jikinta, ji tayi kamar ta kurma ihu, sai dai jikinta babu wannan ƙwarin, ji take kamar ajalinta ne ya risketa.
Alqur'anin gabanta take kallo, zuciyarta ta din ga raya mata, ta yi jifa da shi.
Ganin yadda yanayinta ya sauya, ya sanya 'yan ajijsu darewa suka koma gefe daga kusa da ita.
Malam Auwallu ne ya shigo, 'yan ajin duk suka yi shiru, hankalinsa ne ya sauka a kan Nana, da take ta fizgar numfashi idanunta sun yi jawur.
Girgiza kai ya yi ya ce "Nana Asma'u" kamar wadda aka jonawa shocking, haka ta ja da baya a razane, tare da sunkuyar da kanta.
Ya janyo kujerarsa zuwa gabanta, ya ce "Yau haddar ki zan fara ji, matso ki karanto mini, kin san ina son ƙira'arki" ba ta yi magana ba ta ci gaba da sunkuyar da kai tana haki.
Ya kalli ta kusa da ita ya ce "Amira dawo nan gefe ki fara ke"
Cikin damuwa Amira ta tashi, tana kallon Nana cike da tausayawa,