Showing 1 words to 3000 words out of 20751 words
Chapter 1 - ZABIN MAHAIFIYATA Book Complete BY ESHAAT.txt
COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAAPP 08066360176
π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 1 and 2
Ina mika g0diya ta wa ALLAh (swa) daya bani ik0n rubuta wannan littafin. Sannan wannan littafin kageggen labari ne ban yi d0n cin zarafin wata k0 wani ba dan haka idan yayi dai dai da rayuwar ka/ki ayi hakuri. Na sadaukar da wannan littafinne ma Aunty na Aysha biciki (AysM) ALLAh ya kara basira da daukaka... Masoya zaku iya fadan ra'ay0yin ku ta wannan numbern 090649847980 . Nagode.
A fusace ya shig0 gidan yana faman kwalla mata kira kamar gidan zai tarwatse saboda tsabar ihun da yake yi, ke saude! Ke saude! Cikin hanzari ta fito daga daki tana amsa kiran da yake mata. Gani mallam ta fada tana karasowa ya kalleta cikin daure fuska sannan yace se yanxu kikaga damar amsawa? Cike da ladabi tace kayi hakuri mallam wallahi sallah nakeyi shiyasa. Dan ta6e baki yayi sannan yace ina salma take? Ki gaya mata zatayi bako anjuma kuma saura yazo taki fita wallahi ranta seya baci dan nagaji da ganinta a gabana ba miji.
Inna saude ta kalleshi sannan tace haba mallam aure ai lokaci ne idan lokacinta yayi ko tana s0 ko bata so xatayi ai... Cikin jin haushi ya katse ta ke saude na dade da sanin ke kike zugata to bari na fada miki a wannan karon na tsaida magana. Na riga nayima salma miji ke baki isa na canja maganata ba kuma ki ja mata kunne k0 tana s0 k0 bata s0 se anyi aurennan. Inna saude tayi kasa da muryanta tace dan Allah mallam kayi hakuri ni ban isa na zuga salma akan ta bijire ma umurninka ba sbd ni da ita duk a karkashin ik0nka muke, kuma insha Allahu salma bazata watsa maka kasa a ido ba kayi hakuri. Jin abinda saude tace ne yasa mallam amadi sassautawa sannan yace ai kene saude da wata irin magana ya zango ina miki maganar nayi mata miji amma kina cewa aure lokaci ne, ai lokacin yayi kenan tunda har na zabo mata mijin daya dace da ita. Gidan da zata je ta huta k0mai se anyi mata ba tare da tasha wuya va. Inna saude ta matso tana cewa mallam irin wannan k0dawa se kace wanda zata auri govenor
Murmushi mallam Amadi yayi saboda jin ta s0sa masa inda yake masa kaikayi, ai saude mijin da salma zata aura kamar g0venor yake a wajen mu dubi ciki gidannan k0 dan tiles babu balle aje kan abin sanyinnan A.c ake ce masa k0 me ai kuma kinga duk wanda yake da irin wannan a gidansa se dai mu kirasa da govenor a gidannan. Cikin mamaki inna saude take kallonsa k0da yake ba abin mamaki bane awajenta tunda tasan halin mijin nata.
π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 2.I dedicate this page 2 my l0vely sis maimuna dauda guda (ummi) Allah ya bar qauna... Zaku iya fadan ra'ayoyin ku ta wannan numbern 09064984798 ngd
Tunda tasan halin mijinnata mutum ne mara godiyan Allah, wanda k0mai ya samu baya isarshi, a kullum shidai hangen na wani yake yi. Murmushi tayi sannan tace wai ni mallam waye kake ta zuzutawa ne haka? har yanzu banji ka fada min sunan shi ba. ALH. ABDUL ME DALA ya fada yana zama akan taburman dake shinfide a tsakar gidan... Cikin fΓrgici inna ta dafe kirji badai Alh. Abdul dana sani ba? Dan murmushi yayi sannan yace shidin dai nake nupi. INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN. Abinda inna saude take ta maimaitawa kenan. Yanxu malam ka rasa gidan da zaka kai yarinyar nan se wannan gidan? Gidan da kowa yasan ba gidan zama bane, amma saboda s0n abin duniya kake so ka maida 'yarka bazawara. Kai inma zawarcinne ai da sauki indai baza'a kassarawa mutum rayuwa ba.
Inna ta fada tana goge zufan da ke zubowa daga fuskarta wanda yake sauko mata tun lokacin da taji an ambaci sunan ALH. Abdul me dala. Duk kawaici irin na inna saude wanda ko wani irin hukunci mallam amadi zai yanke a gidan zeyi matukar wuya kaji tayi magana koda kuwa hukuncin beyi mata dadi ba. Amma yau sanadin jin sunan ALH. Abdul da tayi ta tanka. Wanda shi kansa mallam amadi saida yayi mamakin hakan. Shiru yayi yayi mata dan besan me zaice mata ba. Shidai yasan ya riga ya gama yanke hukunci kuma ba wanda ya isa ya canja masa ra'ayi
[1:34PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 3.Cikin sanyin jiki inna saude ta zauna kusa dashi.sannan tace mallam wannan maganar fa abin dubawa ne don Allah kabar salma ta zabi wanda take so, har nawa salmar take? da za'a ce an gaji da zamanta ba miji. Kwata kwata fa bata fi 18yrs ba. Dan Allah kabar maganar hadata da ALH. Abdul dinnan. A hargitse ya dago yana mata wani mugun kallo, sannan yace ke saude wallahi fita daga cikin maganar nan idan har kina son mu shirya dake, nan gidana ne salma kuma 'yata ce inada iko da ita da da duk abinda yake cikin gidannan.
Ina da ikon aura mata duk wanda nake so. Ke koda kuturu naso ta aura dole tayi min biyayya balle cikekken mutum me tarin dukiya.
Kuma bari kiji billahillazi ko mallam dattine ya dawo duniya kinga dai shiya haifeni ko? To be isa ya hana na daurawa salma aure ba. Sake baki inna tayi tana kallon shi ba tare da ta'iya cewa k0mai ba. Jin maganar na shi har iyayen shi yake sawa aciki.
Arziki na bin mu kinamana bakin ciki to ta Allah ba taki ba. Ya fada yana miqewa daga kan taburmar da suke zaune. Ya saka takalman sa ya fice daga gidan yana
banbamin masifa.
Bin bayansa da kallo tayi kana tace mallam ina guje maka ranar nadama dan nasan tananan zuwa wallahi se kayi nadamar abinda kake shirin aikatawa. Mikewa tayi ta fara aikace-aikacenta d0n yamma tayi gashi bata gama abincin dare ba.
[1:34PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 4.matashiyar budurwa ce kyakkyawa doguwace amma ba sosai ba, fara ce kar jikin ta dan daidai kirar coca cola. tana da faffadan fuska me dauke da manyan idanu tare da madaidaicin hanci da faffadan baki,.
tana da beauty point a gepen kumatunta hagu da dama. haqoranta farare wanda suke dauke da siririn wushirya a tsakanin su , tana sanye da dogon hijab har kasa ruwan kasa hannun ta yana dauke da al-qur'ani me girma.!!!
da sallama ta shigo gidan tana cewa inna na dawo, inna saude dake kitchen tana tuka tuwo ta amsa mata sallamarta tana cewa salma kin dawo? cikin nutsuwa ta amsa mata da eh nadawo, sannan tace inna bari nazo na taimaka miki kafin a kira sallah.
A'a salma yi zamanki ki huta,keda yanxu kika dawo. ai harna gama daman tuwo ne ya rage ban tuka ba. To inna salma ta amsa tana cire hijab din makarantar hadda da take zuwa dashi,.sannan ta shige daki ta ajiye Al-qur'anin dake hanunta,ta fito ta nemi waje ta zauna tace inna har yanzu baba be dawo bane? inna saude ta amsa da cewa ya dawo ya sake fita ne, amma yanzu zaki ganshi ya shigo tunda magariba tayi.
Inna bata gama rufe baki ba mallam Amadi yayi sallama ya shigo gidan. sannu da zuwa baba cewar salma, yawwa sannu 'yar albarka. Da mamaki take kallon mahaifin nata rabon da taji irin haka a bakinsa har ta manta.
Da Sauri ta tashi ta debo masa ruwa a buta,domin yayi alwalan sallar magriba. sannan itama ta dauki buta tayi ta shiga daki domin tayi sallah itama.
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 5
Bayan mallam Amadi ya dawo daga sallah, ya nemi waje ya zauna inna saude ta kawo masa abincin shi. Bayan ya gama cine ya dubeta yace ina fatan kin fadama salma sakon da na baki???
inna tace ban fada mata ba mallam, amma yanzu zan fada mata insha ALLAhu
Da harara ya bita dashi,sannan yace kira min ita nina fada mata tunda ke baza ki iya ba.kayi hakuri mallam yanzu zan fada mata.
Tsawa ya daka mata yana cewa ki kiramin ita nace, da hanzari inna ta tashi ta shige daki tana me kwalama salma kira.
Amsawa salma tayi sannan tace inna wani abu xan yi miki? girgiza kai tayi tace mahaifinki ne yake kiranki.
Gaban salma ne ya fadi ta shiga maimaita INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI,UNοΌa cikin zuciyarta dan tasan idan taji kira daga wajen mahaifinta, tofa ranar da bakin ciki zata kwana
Inna ta juya ta fice daga dakin tana cewa ki fito yanxu karki bata lokaci. Da hanzari ta biyo bayan mahaifiyar nata,can gepe ta tsuguna cikin girmamawj tace baba gani.Ya dubeta yace dama ba wani magana bane maganar auren kine nagajr da ganinki a haka ba miji,saboda haka na zaba miki miji kuma anjumj zezo saura naji kin masa wani abu. Wallahi jikinki zai gaya miki, yanzu ki tashi kije ki shirya kafin yazo.
a hankali salma ta mike tana hada hanya ta nufi daki,jin irin hukuncin da mahaifinta ya yanke ba tare daya tuntubeta yaji ra'ayinta kona mahaifiyarta ba. tana shiga daki ta fashe da kuka π
tana me cewa ya ALLAh ina rokonka kasa hakan ya zamomin alkhairi a rayuwataπππ
kuyi hakuri da wannan.
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Masoya makaranta novel dina ina jin dadin yanda kuke nuna kaunar littafina. Nagode sosai ALLAh ya bar kauna.
Page 6
WANENE MALLAM AMADI???
Mallam Amadi dan asalin garin Bauchi ne, a karamar hukumar Ningi. kasuwanci ne ya kawo mahaifinsa cikin garin bauchi
Mahaifinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado, su 2 ne a wajen iyanyen su. shi da kanwar sa hadiza wanda take aure a cikia anguwar nassarawa jahun.
Bayan rasuwar iyayen su shiyaci gaba da kula da kasuwancin da mahaifin su yakeyi, yana sayar da kayan yara a kasuwan central.
Mallam Amadi mutum ne me son abin duniya, ko kadan baida godiyan ALLAh.
Matarsa daya inna saude tun auren saurayi da budurwa be sake wani auren ba. macece me kawaici da hakuri.
ko kadan bata da tashin hankali shiyasa suke zaune lafiya da mallam Amadi dan bata ketare umurnin sa.suna zaune ne a unguwar liman.'yarsu daya ce ummu salmawanda baza ta wuce 18years ba. yarinya ce me hankali dan duk halin inna saude ba abinda ta bari. Tayi karatunta har zuwa matakin secondary, taso taci gaba amma mallam Amadi yace ba'a gidansa ba se dai ta fitar da mijin aure.
Hakane ma yasa ta shiga makarantar hadda dake kan tudu. salma yarinya ce me farin jini kowa sonta yakeyi se dai ita ko kadan bata kula su. Gashi duk wanda zezo wajenta zaka samu me kudine.Hakane yasa mallam Amadi yake jin haushinta, acewar sa tana masa bakin ciki ne.
A hakane watarana ta dawo daga makarantar hadda Alh.Abdul-Razak me dala ya ganta. Tunda ya ganta yaji ta kwanta masa arai, hakane yasa yayi bincike akanta kuma ya yaba da tarbiyanta. Wannan ne dalilin dayasa yazo wajen Mallam Amadi domin ya nemawa tilon dansa namiji aurenta.
Daman me neman kukane aka jefe shi da kashin awaki,nan take mallam Amadi ya amince ba tare daya tuntubi salma da mahaifiyar ta ba. Acewar sa koda tana da wanda take so to se dai yayi hakuri.
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 7 and 8
Readers naji korafin ku akan a kara yawan page kuyi hakuri yaronah ne baida lafiya,amma insha ALLAhu idan ya samu sauki za'a kara yawan pages din. ina godiya a bisa comment din da kuke yi ALLAh yabar kauna.
BACK TO STORY
Salma tana cikin kukanne inna ta shigo ta same ta, samun waje tayi ta zauna sa'annan ta dubeta tace salma kiyi hakuri ki dena kukan haka dan ba'abin da kukan ze miki se dai ya jawo miki wani ciwon.
Nasan ki yarinya ce me biyayya, a wannan karon ma ina son kibi umurnin mahaifin ki. Insha Allah zai zamo alkhairi a gareki.
cikin sheshshekar kuka salma tace inna ni damuwata bansan wanda za'a aura min ba, bansan halinshi ba, kuma ma inna nawa nake da za'ace angaji da ganina ba miji?
Dan murmushi inna tayi wanda daga gani bai kai ciki ba,iya fatan bakin ta ya tsaya. Salma addu'a zakici gaba dayi,dan kinsan halin mahaifin ki indai ya fadi magana tofa ba wanda ya isa yasa shi canjawa. to inna wa za'a aura min? salma ta tambaya tana me share hawayen ta.
ALH. ABDUL-AZEEZ ME DALA. Cikin mamaki salma take kallon inna, wai inna kina nufin A-Azeez me dala da nasani?
shidin dai nake nupi inna ta tabbatar mata. cikin gigicewa salma ta fashe da kuka tace inna yanzu a rasa wanda za'a aura min se A.A? Mutumin da kowa yasan halin matarsa,ko iyayen shi fa bata bari yaje wajen su balle 'yan uwansa.
Duk wacce ya aura fa seta raba su ko kuma ta haukatar da ita. gaskiya inna nikam bazan iya auran A.A ba.
se kije ki fada ma mahaifin naki cewa kefa baza ki iya auran wanda ya za6a miki ba.
Kafin salma tace wani abu suka jiyo muryan yaro a tsakar gida yana sallama,inna ce ta amsa. Yaron yace wai ana sallama da salma,kace tana zuwa.
Inna ta dubi salma tace ki tashi ki fita tun kafin mahaifin ki ya fito yazo ya same ki.
Cikin sanyin jiki salma ta tashi ta dauki hijabin ta ta fita.
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 9 and 10
Readers nagode da addu'o'in da kuke min ALLAh ya saka da alkhairi. AMEEN
A jingine yake a jikin wata mota ruwan toka kirar marcedez benz c-class 2018.
Matashin saurayine wanda bazai wuce 35yrs ba, fari dogo kyakykyawa ne ajin farko daka kalle shi zakaga yana maka yanayi da jarumin film dinnan na indi'a wato sharukh-khan.
yana da faffadan fuska da kwantaccen saje, idanuwansa madaidaita ne, yana da dogon hanci da madaidaicin baki wanda ke zagaye da siririn gashin baki, wanda ya dada kawata fuskar shi.
yana da faffadan kirji wanda yake cike da gashi, baida kiba sosai. Mekaratu zanso ka ganshi gayen ya hadu iyakan haduwa ko a kasar india iyakaciπππ
yana sanye da shadda skye blue be saka hula ba, se kwantaccen gashin kansa dayasha gyara atakaice duk yanda ake neman hadadden saurayi to ABDUL-AZEEZ Yakai.
Ba wanda zai ganshi yayi zaton yanada aure. Sallama tayi cikin zazzakar muryarta ASSALAMU ALAIKUM. cike da kasaita da jin kai ya amsa mata, ina wuni? ta fada kanta yana kallon kasa. saida yaja aji dan har tayi tunanin bazai amsa ba sannan yace lafiya.
kamar wanda akayi masa dole,shiru ne yadan ratsa wajen kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa. ita tana tunanin wani irin zama zasuyi da shi, yayin dashi kuma yake tunanin an takura masa da akasa yazo wajenta. A ganinsa tayi masa karama, sunkai wajen 15mnt ba tare da dayansu yace uffan ba.
Cikin izza ya fara magana, ina fatan anyi miki bayanin zuwana? be jira abinda zata ce ba yaci gaba.
inason ki sani a tsarina bani da niyan auren mace fiye da guda daya matata kadai ta isheni rayuwa ban damu da tana haihuwa ko batayi ba, dan ita haihuwa nufin ALLAh ce duk lokacin daya so zai bamu
kisani takura min akayi akan sena aure ki, i love my wife, i dont think zan iya hada sonta da wata 'ya mace a duniya bayan mahaifiya ta. Mahaifina shi ya zaba min ke, saboda haka ke ZABIN MAHAIFINA ce.
ina fatan kin fahimta? shiru tayi masa batace komaiba. tabe baki yayi sannan yaci gaba nazo nan ne saboda umurnin mahaifina, yace na sanar daku baya son aja dogon lokaci. Zaizo ya samu mahaifinki zasuyi magana, kuma bana bukatar a cika min gida da tarkace dan haka ba se an kawo ki da komai ba hope u understand???
Cikin jin haushi salma ta dago tana binshi da wani mugun kallo, cikin kumar rai ta fara magana.
Nima ai kai ba zabina bane kai ZABIN MAHAIFINA ne. kuma da kake cewa kar a cika maka gida da tarkace ai dai kasan komai talaucin mu dole za'a kaini da abinda ALLAh ya hore mana, dan haka maganar kar a cika maka gida da tarkace ma bai tasa ba, we do what ever we want.
iyaka bacin rai Abdul yakai π‘π‘π‘π‘π‘shi mutum ne wanda baya son raini. tunda yake a rayuwar sa ba macen data taba fada masa magana makamanciyar wacce salma ta fada masa. wacece ita? da zata ce shiba zabinta bane. har akwai macen da zata kalle shi ta nuna masa bata kaunar sa??
ke wacece dazan fadi magana kice baza kibiba??? TO wallahi bari kiji kar wanda yazo min da tarkace gidana this is an order. ya karashe maganar yana huci. kuma kisan irin maganar da zaki dinga fada min idan kuma ba haka ba wallahi saina koya miki hankali.
yana gama magana ya shige motar sa yabar wajen. kada kai salma tayi itama ta shige gida tana jinjina rashin mutunci irin na A.A.
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 11
A tsakar gida ta samu mahaifinta