Showing 1 words to 3000 words out of 14265 words
Chapter 1 - MASARAUTAR ZAZZAU BOOK COMPLETE BY HAUWAU MUSA YELDU.docx
👑MASARAUTAR ZAZZAU👑
Labari mai cike da kalubali, tsafi,soyayya da kuma kiyayya.
Update group link👇👇
: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bwajen
Channel link👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION
(G.A.W A)...✍️
___________________________
kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakar da AL'UMMAR ta.
___________________________
Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑.
👑MASARAUTAR ZAZZAU👑
Magical love story💕
Story and written by
HAUWA'U MUSA YELDU.
Inkiya
Queen Jiddah👑
Baby Nice💫
Pg 01.
Bismillahir Rahman nirrahim.
Kamar yadda nafara rubuta wannan labari lafiya,Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.
**GARGADI*!!*
Gargadi na kokuma nace jan kunnena shine, banyarda wani ko wata ,suyi amfani da LITTAFINAH ba, tareda fasahata tako wacce irin hanya har saida izininah, idan akayi kuma hakki na kanku!!! Saboda haka idan kunne yaji hausawa sukace gangar jiki maya tsira👐👐.
JAWABI!
Littafi na , na MASARAUTAR ZAZZAU kirki rarren labari ne, kamar yadda MASARAUTOCIN guda uku 3 suka kasance, to haka ma mutanen da ke ciki, da duk a binda labarin yakunsa, ina fatar kun fahimta?.
TSOKACI!!!
Babban abin mamaki ne gani barewa a tsugune ,kamar yada yake da ban mamaki kare da sadakar nama!!!!.
Rubuta labari ,basirah ce!! Kuma fikirah ce!! Sannan baiwa ce!! Wacce ba kowa ke da ita ba sai DAN BAIWAH!!! .
Acikin dubbanin al'ummarmu, masu maban banta addini da kuma al'adu,masu maban banta launikan fata ,kalilan ne daga cikin su Allah (s.w.a) ke damkama wannan baiwar a hannunsu !!!!!.
Rubutu ,rubutune, sannan marubuta ma gsky ne saidai marubutan ma suna suka tara kamar yada wani marubucin ya amshi sunan sa!!! Domin wata miyar sai a makota !! A makotanma sai a wani gidah!! Kamar yadda awani gidan ma ,sai a tukun yarda ta amshi sunanta!!!.
Kamar yadda daru ruwan shekaru suka shafe a baya ,karni bayan karni haka zamani ya rinka sauyawa tare da al'adun dubbannin a'l'ummarmu, masu maban banta addinai da kuma al'adu, To Haka ma A MASARAUTAR ZAZZAU👑.
Pg 01.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
A cikin garin ZAZZAU, Akwai al'ummah da dama tare da masarautu maban banta masu mulkin wannan na hiyar .
To haka ma a cikin wannan gari na ZAZZAU, a cikin daya daga cikin yan kunan sa , MASARAUTU NE GUDA UKKU 3!! A farkon garin ,hanyo yine guda uku3 wanda idan kabi gefen ka , na dama hanyar zata kaika direct zuwa MASARAUTAR YAMMAH!! .
Hannun hagu kuwa zai sada ka da MASARAUTAR AREWA!.
Yayin da idan ka fuskanci hanyar tsakiya zata sada ka da MASARAUTAR GABASS!!!.
Gaba daya masarautocin guda uku masarautu ne da suka kunshi kalubali, surkulle, munafurci dakuma zagun kasa.
To bari mu leka daya bayan daya cikin ko wace MASARAUTA dan ganin yadda zata kaya.
* MASARAUTAR GABASS!.
Masarauta ce mai cike da abubuwa na burgewa da kuma kaya tarwa, kama daga kyawawan wurare da manya manyan shashunah dake cikin ta , ga lambunah masu cike da ciyayi 'ya'yan itatuwa , dabbobin ni'ima harma da na kallo domin burgewa ,kamar su zebra dadai sauran su.
To hk ma acikin gidan
MASARAUTAR !.
wanda sarki "JIBREEN JABBAR BN JAFAR " ke mulkinta . cikin masarautar ma manyan shashuna ne guda uku 3 , gefen dama ,sashen bayine da hadimai , gami da dakaru ,kamar yadda gefen hagu sashene na 'yan uwan mai martaba JIBREEN JABBAR BN JAFAR. Tsakiyar kuma shashene na mai martaba da iyalansa, farfajiyar MASARAUTAR kuwa swimin full, ne da garden , sai kuma gidan zoo tare da wasu keban taccin wurare na kiwon dawakai.
Cikin shashen na maimartaba ,
babban falor ne wanda ke dauke da kujeru na alfarma., zaune yake a saman daya daga cikin kuje run, ya daura kafarsa daya akan daya, kana nan kaya ne sanye ajikinsa ,wandon nasa iya guiwa wanda ya amsa suna tree quiter ,sai singlet daya sanya mai dauke da ado ajikinta, sumar kansa ah cike kamar dai ta larabawa ,ga wani dan iskan aski daya yiwa sumar, farine shi sosai jar fata ,hkn yasa shigar tasa tamai dashi kmr wani arne !! Sbd babu inda shigarsa ta danganci SARAUTAH!!!........
"Assalamu alaikah ya akheey "..
Da gowa yayi tare da kallon matashiyar yarinyar da ta shigo falon ,ba tare da ko da digo daya na fara'ah akan fuskarsa bah !!.
Matashiyar yarinya ce da bazata haura shekara goma sha shida ba 16. Sanye take cikin wata lallausar alkibbah maroun colour , kasan cewar ta farar fata hakan ne ya kara fito da kyan alkibbar ajikintah!!!!.
Cikin natsuwa ta zauna a faloun tana sakin murmushi , Ba tare da ya kalleta ba yaci gaba da dannar wayarsa kmr baisan da wanzu warta a wajenba....
"AKHEEEY!"
TA furta tana kallon sa ,ba tare da shurun nasa ya dame ta ba, da gowa yayi tare da watsa rikitattun idanun sa a kanta , INTISAR menene?? Ya motsa jajayen labbansa tare da furta hakan kmr anyi masa dole.......
"Akheey HUSSAIN! magana fa nazo muyi kai kuma ka share ni".
Kara dagowa yayi tare da ci gaba da kallonta , sanin ba zaice komai ba ya saka ta cewa ,
"dama ..uhm..dama... Kheey HARUN ne yace zai zo wurin mai martaba akan zancen mu , dana gaya wa BALMATY shine tace na fara sanar da kai ko AKheey HASSAN saboda babban wa ubah".
Takarashe mgnr tana sissinne kanta kasa alamun jin kunya....
"SHE KARUNKI NAWA?"
TA dago ta kallesa ,kmr bashi yy maganarba .
baki ta turo tareda fadin "SHA SHIDAH 16" .........
"TO kar na kara jin zancen HARUN ko kuma AURE anan gidan sai bayan shekara biyu2!" Ya karashe mgnr yana mi kewa tsaye.
Ida nuwanta cike da kwallah ta fasa uban ihu, tana cin karo da HASSAN , tanufi sashen BALMATY Ba tare da ta tsaya bah.
Shi gowa HASSAN yy dakin cikin takonsa na natsuwa da kasaita , da ganinsa ,kaga jinin SARAUTA!!.
Yana sanye da alkibbah ta alfarma, kara sowa yy kusa da dan uwan nasa HUSSAIN , babu abinda yaban bantasu ,kama daga tsayinsu ,farinsu, harma kamannin fuskarsu, sai dai shigarda, ya daukar wa kansa ,wacce tasha banban da al'adar MASARAUTAR.
"Akheey meyasa ka koreta?"
"mtsweet!! Yanzu fisa bilillah ita wannan 'yar abar har tasan wani abu AURE? " Mtsweet! Ya sake jan wani tsakin ,duk laifin HARUN ne wllh ,idan ba iskan cibah ma taya zai rasa abar so sai wannan 'yar labubuwar? Har tazo tana titsiyeni sbd shirme. To zanga ,wanda zai aurar da ita ah gidan nan ,kuma bari na samesa sai naci........
"Calm down pls, Haba Akheey! , Me yy zafi hk?, Idan kaji zafi kaima kaje kayi auren mana , ya fada maganar cikin kamalarsa......
"tmsweeet!!, To sai kazo kamin auren ai!" Ya fada yana jan zazzalallen wandonsa, yabar faloun .
HASSAN kuwa murmushi yayi ba tare da ya furta komai ba ,ya nufi sashen BALMATY ,dan ya gaisheta sbd daga masallacin juma'ah yake...✍️
Like share and comment pls🙏 mutanen Arziki sai daku much love🤸♂️😘😘💃
Group update link👇👇
: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv
Channel link👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION
(G.A.W.A)...✍️
___________________________
Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.
___________________________
mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑
👑MASARAUTAR ZAZZAU👑
Magical love story💕
Story and written by
HAUWA'U MUSA YELDU.
Inkiya
Queen Jiddah👑
Baby Nice💫
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
Kamar yadda nafara rubuta wannan littafin lafiya, Allah kabani ikon kammala shi lafiya.
Pg 02.
®" MASARAUTAR AREWAH"
kamar dai MASARAUTAR GABAS.
I tama wannan MASARAUTAR ta kunshi masu mulki da kuma hadimai.
Wanda mai marbata " HABIBU BIN IBRAHEEM KHAIRULLAH " Ke mulkinta.
Ya yinda iskah ke kada wa a sararin samaniyah, bishiyoyi da tsuntsaye na shawa ginsu, haka ma hadimai da bayi ke kai da ko mowa a cikin gidan MASARAUTAR.
Ya yinda a cikin gidan MASARAUTAR.
ko wane dan adam ,wanda ke da rayuwa a jikinsa, ke ci gaba da guda narda al'amuransa.
To kamar haka ne suma suke zaune, a bisa gado na alfarma wanda ke a jiye a cikin madau kakin dakin.
"Duba kiga, na saka wannan?"
Ta fada tana karasa fitarda gwala gwalan dake cikin karamin akwatin, wanda duk gold da diamon ne a cikinta.
" wow JIDDAH! pls ki saka wannan" ta fada hadi da daura mata tsadaddar sarkar awuyanta.....
"A a fa JAMILAH! wannan nauyi ne da'ita idan na saka ta duk sai na takura".....
Karar sautin wayarta da ta jine ya katse surutun nasu, ta dauka tare da ka rawa a kunnen ta tana yin sallama.
" wa alaikis salam SARAUNIYA JIDDAH!" ya fada muryarsa na bayya narda farin cikin da yake ciki......
"Hamma Habeeb! mai martaban gobe
barka da war haka", ta karasa tana sakar masa dariya cikin siririyar muryarta......
" Hmm JIDDAH! na kenan, kin rama zolayar ki ko?" .......
"A a ba zolaya bane very soon, zaka ci gaba da amsa wannan sunan".
"To Allah yasa haka"... Ameen.
"Ok mun shigo MASARAUTAR taku yanzu"....
"kai hammah da gaske?" Ba tare da ya ka rasa maganar sa ba ta yanke wayar, tana dirowa daga kan gadon.
Fuska JAMILAH ta bata, ta reda fadin ,
"lpy kike wannan haukar?"....
" Mai martaba na hamma na Habeeb! ya shigo MASARAUTAR nan, bara ma nayi sauri nashirya duk da nasan saiya fara sauka wurin mai martaba HABIBU BIN IBRAHEEM KHAIRULLAH".
" KIce dai zai fara sauka wurin mai martaban gaskiya, ba wanda a ka sanya wa sunan karya na soyayyah bah"..... ....
"Haba JAMILAH! , kamar ya sunan karya? Bayan kinfi kowa sanin hammah Habeeb a yanzu haka shi yarima ne mai jiran gado, kinga kuwa ba arar sunan yayi ba, saboda ko yaushe zai iya zama mai martaba."
"Kuma fa haka ne, am sory pls mantawa nayi"...
"Owk ba komai nasan kin manta ne shiyasa".......
"Owk bari nazo na wuce tinda yazo"...
" haba ba zaki tsaya ku gaisa ba? , a matsayinki fa na babbar aminiyata"....
"Kinga JIDDAH! naso na tsaya wallahi , sai dai kinsa yau juma'a , karamin lokaci ne, banaso dare yayi ba tare da naje inda zani ba".
"Owk a dawo lpy"
"Allah yasa", ta fada tana daukar mayafinta.
kofar dakin taci karo da MAMA FULANI 'YAR AGADAZ, ta sun kuyarda kanta tana kame kame tabar dakin da MASARAUTAR baki daya, yayin da FULANI ke binta da kallo na tuhumah.
"JIDDAH "
"Na'am mommah " ta fada tana kallon FULANI
"Yaushe yarinyar nan tazo gidan nan?"
Sadda kanta tayi kasa, wacce kuma mommah?......
" ba fa nason iskanci JIDDAH!! , JAMILAH nake nufi , meya kawo ta? , ba na hanaki mu'amula da itaba? , ba wai alaka ce ba naso kiyi da tala kaba, A a ko kadan, ita wannan yarinyar ce tun kuruciyarku hankalinah bai kwanta da itabah"...
"Mommah dan Allah ki fahimceta, wllh bata da wata illa, kawai na kira tane ta tayani zabar gayan da zan saka"....
" JIDDAH kenan, a binda babbah ya hango yaro ko yahau bene ,bazai hangosa ba! Sannan su mutane da kike gani wani lokacin shiga jikinka suke yi domin kawai su cuta maka"....
" A a mommah! ki yarda dani JAMILAH tana sona bazata taba cutamin ba".
"Hmm to Allah yasa"
"Ameen mommah na, mommah dubi wannan takalmin yayi kyau ko?".
Murmushi tayi, "
Eh yayi kyau sosai JIDDAH, idan ya gama da mai martaba ya shigo nan sai ki min magana, sannan abincin sa na nan hadimai sun kammala".
" To mommah ta fada tana sun kuyarda kanta"
Murmushi kawai mommah tayi, tana fita daga dakin.
©" MASARAUTAR YAMMAH "
MASARAUTACE wacce mai martaba "USMAN UMAR BIN UBAIDULLAH " ke mulkinta.
Sannan ta kukunshi duk wani abu da sauran masarautu suka kunsa, kama ga iyalanshi mai martaba da kuma bayinsa kamar yadda al'adu suka tabbatar.
*ZULAIHAT , ya isa haka dan Allah, nifa na daukar miki alkawari, to banga abin damun kan kiba , kuma ki kwantar da hankalin ki in dai Habeeb ne aure keda shi kamar an gama.
Dagowa tayi tare da sau karda dara daran idanuwan ta akanta , wa' yanda suka rine da launin jah.
"Ammah MAMA FULANI MAI DAKIN YAMMAH, kina ganin zai yarda ya aureni? Kina ganifa wurin ta yatafi yanzu, naje ina gaisar dashi, ko kulani ma bai yiba, harda cemin wai mayya, kuma sai dai naci kaina".....
" ya subhanallah ZULAIHAT ya isa haka daina fada kar wani yaji"......
."Amma mama"......
"ZULAIHAT daina ,idan nina haifi Habeeb ki sani babu abinda zai hana auren ku".....
"Da gaske ranki shi dade?"
" Eh ZULAIHAT dina kwan tarda han kalinki kinji?".....
"Assalamu alaikum "
Wa alaikis salam , JAKADIYA lafiya?
"Eh ranki shi dade lafiya kalau ,ance a sanar da GIMBIYA ZULAIHAT tayi ba kuwa.
"Owk ga tanan zuwa"
" Na barki lafiya ranki shi dade , 'yar sarki jikan sarki, sannan mahaifiya ga sarkin gobe! Kinga jiya kinga yau , insha Allah gobe ma da ke za a dama".
Murmushi FULANI tayi wanda ke dauke da izza da kasaita , sannan ta gyara zaman Alkyabbar dake jikinta, tana maida hankali wurin ZULAIHAT.
" Tashi kije 'yata , yarda da amincin Allah su tabbata agareki"
"Ameen ranki shi dade" ta fada tana barin dakin da miskilin murmushi bayyane akan fuskarta.
Note edited ....✍️
Like share and Commenr pls🙏 sai daku mutanen Arziki much love😘😘😘💃
Update group link👇👇
: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv
Channel link👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION
(G.A.W.A)....✍️
____________________________
Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da basirarta da kuma tinaninta Adomin kawai ta Fadakarda AL'UMMAR ta.
____________________________
Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen jiddah👑.
👑MASARAUTAR ZAZZAU👑
magical love story💕
Story and written by
HAUWA'U MUSA YELDU, (baby nice).
Bismillahir rahmanir rahim.
Kamar yadda nafara rubuta wannan littafin lafiya, Allah kabani ikon kammala shi lafiya.
Pg 03.
® "MASARAUTAR GABAS".
Keban taccen wuri ne wanda ke dauke da 'ya'yan itatuwa, ga korayen ganyayyaki, da wasu flowers ajiye a gefe da gefen wurin.
Wanda suke jike da ruwa a cikinsu , ga dukkan alamu ma ba a jima da ban ruwa a wajen ba.
Ga wani babban sign board a wajen mai dauke da "BALMATY GARDEN" tare da tambarin masarautar a jikinsa , hakan ne ya tabbatar da wajen ba ko ina bane face lambu inda" MAMA FULANI BALMATY " ke zama domin shan iska.
Tako biyar zuwa shida, zai sadaka da ainihin cikin wurin, wanda kasan sa ke dauke da lafiyayyen center cafet mai tsananin laushi da kuma daukar ido, shimfide a wurin.
Gefe da gefensa kuma kayan marmari ne wa 'yanda ke dauke a cikin korai na alfarma, kama daga kankana, Ayaba, Lemu, Tufa, Inibi da dai sauran su.
Yayin da wasu set din
Silvovi masu sheki da da kuma daukar ido ke dauke da soyayyin kaji da kuma zabbi a cikin su wanda banda tiririn kamshi babu abinda suke yi , ga kuma kofuna na tangaran dake jere a bisa tray na alfarma wanda ko wane daya daga cikin kofunan ke dauke da madarar Shanu, Zuma, lafiyayyar damammar fura mai dauke da hadin nono da kankara a cikin ta, dadai sauran su.
To haka ma a tsakiyar shimfi dadden cafet din . Dattijuwar mace ce zaune yayin da ta kishingida da wani tattausan filo , da ke a jiye a wurin.
sanye take da alkyabba golden color a jikinta, ya yinda launin fatar ta ya kasance fari kal kamar dai Akheey Hassan da Hussain.
Ga kuma fara'a da annuri hadi da kwarjini a fuskar ta wanda duk da kasan cewar jinin mulki da sarauta dake yawo a jikinta bai hana bayyanuwar su ba.
Kusa da ita kuwa, matasan 'yan mata hadimai ne guda biyu 2 a durkushe da fayafai a hannunsu suna mata fifita.
Yayin da wurin kafafuwan ta wata dattijuwa ta kasan ce zaune rike da kafafuwan ta tana mata tausa, "JURMAINATU" kenan hadima kuma babbar amintacciya a wurin "MAMA FULANI BALMATY".
Da matukar gudu ta fado a cikin lambun, ko ganin gabanta bata yi, bata tsaya a ko ina ba har saida ta isa wurin "MAMA FULANI BALMATY" sannan taja burki tana mai fadawa a jikinta, yayinda kuma fuskarta tayi jajir abinka da farar fata, sai dai duk da yanda ruwan hawaye da majina suka garwaye ilahirin fuskar tata, hakan bai isa ya hana bayyanuwar ainahin kyan nata ba.
Mumushi Mama Fulani Balmaty tayi tare da tashi daga kishin giden da take, sa'annan ta fitar da lallausan hannunta daga cikin alkyabbar dake jikin ta, tana mai nuna wani bangare na saman cafet din , aiko cikin dakiku da basu gaza uku ba, daya daga cikin hadiman 'yan matan nan ta sanya mata wani madaidaicin cup a hannun nata, tana mai sadda kai kasa.
Yayin da ita kuma Mama Fulani Balmaty, ta tayar da Intisar zaune tana mai kafa mata wannan sassanyan lemo a bakin ta tare da ambaton sunan Allah.
Da kyar lemon ya iya ratsa tsakakkanin harshen ta sa'annan ya gangara zuwa ga makoshin ta saka makon yanda take kuka mai hade da ciccika.
Ga jeren numfashi ta fitar tare da furzar da iska daga bakin ta, tana mai dago da kanta tare da saukar da dara daran idanuwanta wa'yanda suka rine da launin ja! A cikin na "Fulani Balmaty " tana shirin sake fashewa da wani kukan ...
" Ya isa haka Intisar mene ne"
Fulani Balmaty ta fada tana mai sakin murmushi saboda a koda yaushe rigimar 'yar tata karuwa take yi , ga shegen nacin tsiya sai kace itace last born a gidan, bayan kanne ne da ita har guda hudu 4 .
"Balmaty"
"Na'am 'yata , gayamin mene ne kinji? "
"Meya faru? Waya zageki ko ya dake ki? Wa ya isa ya jada kakar Mai martaba Nana Khadijatu".
" To ba Akheey bane, saida na gaya miki bazani wajen shi ba amma ki kace