Showing 1 words to 3000 words out of 52525 words
Chapter 1 - CI-MA-ZAUNE Book Complete Writing by Maman Afrah.txt
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna siyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/Tiktoc:TikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
*CI- MA- ZAUNE*
*NA*
*MAMAN AFRAH*
Daga marubuciyar:
Malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu,Jalli joga, ƙara,in nna delu, bilal da sauransu.
*09025576222*
🅿️1️⃣
A hankali Dada ta fito daga cikin ɗakin nata tana ƙoƙarin kulle ɗakin da kwaɗo, sai wani taɓe baki take, dakatawa ta yi da rufe ƙofar tana bin bayan kishiyarta Ladiyo da kallo haɓa ta riƙe a zuciyarta ta ce.
'Allah mayar da ƙoƙo masaki tun kike tafiya irin ta guragu kina wani botsaro mazaunai, yo Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, na rasa mai Malam ya gani a jikin matar nan ya auro ta, abu babu kyan gani babu fasali ko mamora babu a jikinta ba gaba babu baya kamar sawun tayar keke, ni dai an cuceni a rasa da wa za a mini kishiya sai wannan mai haƙora kamar kacar keke' Ta kai ƙarshen maganar a zuciyarta tana jin kamar ta yi kuka. Fitowar Malam daga turakarsa shi ya ankarar da Dada ta mayar da hankali wurin rufe ƙofa.
'To ayawu sai ina kuma?" Ya ce yana aika mata harara, karkata kai gefe ta yi cike da kissa ganin Ladiyo ta dawo daga bayin ta ce
"Allah sarki Malam gidan auta zan je mana, yarinya ta yi aure a gidan naira amma ba a leƙota ba, yau kimanin wata guda ban je ba shi ya sa na ce bari na je na ganta ta ganni ka san uwa da ɗa bare kuma ita auta jaja manya auta tafi na fari" Dada ta faɗa cikin sanyin murna tana wani karkata kai gefe. Shi kuma Malam sanin wacece Dada sai bai ji ko wani tausayin sanyaya murya da ta yi ba don ya san saboda kissa da kisisina take domin kishiyoyinta amma da zarar sun ware wuri guda shi da ita za ta sauke masa kwandon masifa.
"Yanzu da tsakar ranar nan za ki je gidan mutane? Bakya gani sirikin ki ne"
"Yo kana ma kenan wai dambe da kishiya, siriki ai ɗa ne, kuma idan mutum zai je ganin yadda ɗansa yake zaune a gidan aure ai sai ya yi bazata wato ya je lokacin da ba a tsammatar zuwan baƙo" Ta ce tana sakin murmushin yake, tare da aikawa Ladiyo harara ganin tana ƙunshe dariya, bata san ita kuwa Malam tun da ya mata kishiyoyi biyu ragas to ya taro aradu da ka don bai isa yake katse mata hanzari ba
"Ni dai a tawa shawarar ki bari sai da dare ki je ku gaisa ku dawo"
"A haba Malam sai ka ce munafurci da daddare mai zan adar to? Ai zuwan dare ba zan adar da baccin makaho ba, tun da dai shawara ce ba umarni ba ni ka ga tafiya ta don da zafi-zafi ake dukan ƙarfe!" Ta ce tana juyawa ta shiga datse ƙofar, shi kuma ya juya ya shige turakarsa ba tare da ya sake cewa komai ba.
"Ai ka haifi mace ka aurar da ita gidan daɗi gidan daloli inda za ta huta kaima ka huta, wani naka ma idan ya raɓe ta ya huta shi ne, amma ka aurar da mace inda sai dai ta kawo maka klin da sabulun wanki ai ci bayan ya yi yawa" Cewar Dada tana aikawa Ladiyo wani kallo irin na kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake.
Haushi ne ya turnuƙe Ladiyo saboda ta san Dada magana ta faɗa mata, cikin ƙufula ita ma ta buɗe baki da zummar ramawa tun da ta san auren jari ne Dadar ta yi wa ƴar tata Amina tun da ba a ce Malam ba tun da shi ma ido ne nasa, kuma auren jarin ma sai aka duba wanda ya haifi Aminar aka bashi aure saboda son hutu da kuma son abin duniya.
"Yarinya an cuce ta an haɗa ta da tsoho, tabbas kwa an cuce ta wa zai mata kalaman soyayya" Ladiyo ta ce cikin waƙa, har Dada ta juya za ta mayar mata da martani sai kawai ta tuna abin da ta faɗa mata na farko ma ya isa ta tuna take jin takaici tun da ta san Ladiyon ma auren mai kuɗin ta so ƴarta Halima ta yi sai dai bata samu attajirin ba, gashi kuma tana so ta je gidan Aminar don ta ci mai daɗi saboda haka ne ma ya sa bata ci komai ba tun safe domin kar cikinta ya cika, gudun hakan ya sa ta juya riƙe da mukullin ɗakin nata da kuma ledar viva marar komai.
Tana shirin ficewa sai ga Mero ɗaya kishiyar tata ta fito daga ɗaki tana aikawa Dada wani kallo, juyawa Dada ta yi ta mata kallo ɗaya ta ce
"Ni in na raina kasuwa ko sautu ba na bayarwa, aikin ɓur in ji tusa" Tana gama faɗa ta fice don ta san Mero ta shaƙa gashi idan aka faɗa maka magana baka mayar da martani ba ta fi yi maka ciwo duk da wasu suna ganin cewar shiru ma amsa ce amma ga mai hankali.
A ƙofar gida suka yi kiciɓis da jikokinta ƴan biyu ƴaƴan Hafsa babbar ƴarta wacce ta rasu a wajen haihuwar su ya bar mata su wato Hassana (Hassu) Da Husaina (Usai) Yara ne masifaffu masu jan magana basa ganin kan uwar kowa da gashi duk wanda ya takalo su da faɗa ya san sauran babba ne ko yaro duk girmanka ka shigo gonar su to za su biya maka karatun rashin mutunci kusufa -kusufa shi ya sa ma mutane suke cewa halin Kakar su ne sak suka ɗakko, saɓanin ita Amina ƙanwar mahaifiyar ƴan biyun dama su biyu Dada ta haifa da Hafsa da Amina. Amina babu ruwanta ga sauƙin hali don ko Alhaji Sabo ma biyayya ta yi wa mahaifiyarta wato Saude wacce suke kira da Dada amma ba wai don tana son sa ba.
"Hajiya Dadansy sai ina kuma da tsakar ranar nan?" Suka haɗa baki wajen faɗa.
"Ku dai ku bari ƴaƴan nan gidan Amina zan je in gano daular da take ciki"
"To ai dama don kin ƙi mu je da tuni mun gano miki ita" Hassu ta ce tana ƴar dariya.
"Yanzu ma ni kaɗai zan je kun ga ledar viva na ɗakko duk wani naman kaji da lemon kwalba a ciki zan zubo muku kason ku, ku ci ku yi nak mu ajiye sauran muke tsakura muna ɗumama wa muna mayar da mugun yawu"
"Gwara dai mu je tare"ɓ zuwa da kai ya fi sako" Usai ta ce tana ɗan ɓata rai.
"Ke daɗi na da ke saurin fishi bana so mu je tare ku musu tijara amma idan na je yau ku sai ku je jibi in ya so muke fashin kwana ɗai-ɗai to ai dama tun da ya aure ta mu duka zai ke ɗaukan ɗawainiya" Ta ce tana tuntsurewa da dariya don ta san su da abincin gidan Malam sun yi hannun riga tun da Allah ya musu gyaɗar dogo ƴarta ta raɓi gidan arziƙi. Su ma dariyar suka yi ta basu mukullin ɗakin ta juya ta tafi tana ta sauri tana tafiya yawu yana taruwa a bakinta tsabar yadda ta saka a ranta za ta yi wankin ciki da na baki ga cikin ta sai ƙugin yunwa yake. Tana tafiya tana murmushi tana godewa Allah da saka wa Alhaji Sabo albarka da ya auri ɗiyarta da ta rage mata yanzu sai jikokin nan guda biyu, tun kuɗin da Alhaji sabon ya bata ƴan ɗari bibbiyu sabbi ranar ɗaurin aure su ne take cancantawa tana kashewa amma yau da safe ta kashe kuɗin ƙurmus don ta san yau idan ta je da kanta ba saƙo ba to tabbas zai bata kuɗin da ya fi wancan tun da ya bata wancan lokacin ma bare kuma yanzu da ta zama sirikarsa ka'in da na'in. Duk da tana mamakin rashin zuwansa gaishe da ita tun da aka yi auren wanda a baya ya saba kullum yana zirya amma sai ta danganta hakan da wataƙila aiki ne ya masa yawa, saboda ita ko tunawa ta yi cewar Alhaji Sabo ya zama sirikinta wani daɗi take ji.
Tun daga ƙofar gidan take jin daɗi a ranta ganin ƙerarran gidan da za ta shiga, wanda take ganin gidan auren ɗiyarta ne ta cikinta, daga can ƙasan bishiya ta hangi Alhaji Sabo zaune a kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wasu zazzaune a kan tabarma. In dai ba idanunta ne suka mata gizo ko ƙarya ba sai ta ga kamar Alhajin ya haɗe rai da suka haɗa ido duk da tana washe mssa baki ita ala dole sirikarsa amma sai ta ga kamar ma bai santa ba amma sai ta danganta hakan da ko don yana cikin mutane ne ko kuma dai bai shaida ba duk da ta san hakan zai yi wuya. Da saƙa da warwara ta wuce su, ta san wata shekarar ma bata cire ran zuwa makkah sauke farali wataƙila ma a haɗa har su Hassu da Usai, da wannan tunanin ta yi wa gidan kutse.
Tun daga farko take rafka sallama, amma ta ji gidan shiru, tana cikin yin sallamar sai ga Amina ta fito daga bayin riƙe da buta ta shiga amsa mata sallamar. Mamaki ne ya rufe Dada ganin yadda ta ga Aminar a rame ta yi wani baƙi tana tafiya salalo-salalo baki sake take ƙare mata kallo har ta kasa haɗa laɓɓan bakinta a yadda ta ga Aminar sai ta ga tamkar wanda rabon ta da ita kamar an shekara ba wata guda ba.
"Sannu da zuwa Dada" Ta ce don katse shiru saboda ta ga Dada ta mutu da mamaki, ko ita ta san ta sauya nesa ba kusa ba amma ya ta iya shi faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi.
Bin bayanta kawai Dada ta yi ba tare da ta amsa sannun ba, falon suka shiga ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ta yi ƙuru ta siyawa Aminar guda biyu duk cikin kuɗin da suka tatsa a wajen Alhajin. Duk da ran Dadar a ɓace amma ganin filas a ajiye an jera su, filas ɗin da duk cikin wanda aka siyawa Aminar sun fi kyau da tsada don a fitar da ita kunya saboda kishiyoyi duk da gidanta da ban. Sai ta ɗan ji salama tun da yanzu dai ta san sai dai jinya Aminar ta yi dama ko a mafarki ba za ta yi gigin yin tunanin rashin abinci bane.
"Wai Amina amma cutar amai da gudawa kike tun da kika zo ko?" Ta jefa mata tambayar tana haɗiye yawun da ya taru a bakinta saboda daga ta kalli filas ɗin nan da aka jera su sai ta ji yawunta ya tsinke kwaɗayinta yana linkuwa.
"Amai da gudawa kuma Dada?"
"Yo cutar mai kike, duk kin fita hayyacinki kin yi baƙi kin rame sai ka ce wacce tukunbu (Tinubu) Ya yi sallama a gidanki"
"Wallahi Dada lafiyata ƙalaw ko ciwon kai ban yi ba"
"Haba Amina ya da haka an ce da kuturu a gama lafiya, kin gan ki kuwa hajaran majaran shiga motar alƙali? Babu nutsuwa irin ta amare, ke da kika yi aure a gidan naira maimakon ki sakata ki wala amma kin zo kina ƙeƙashewa son ƴan hana ruwa gudu su mana dariya?" Shiru ta yi bata yi magana ba ta sunkuyar da kai hawaye yana cika idanunta amma bata bari Dadar ta gani ba. Wurin kwanukan ta wuce ta janyo su guda uku ta kawo gaban Dada ta fita ta ɗakko cokali da faranti.
'Amin da shegen sanabe da shiga shari ba shanu kike yanzu wanda zai ci naman kaza yana karya ƙashi ina ruwansa da cokali bayan ga yatsunsa' Ta ce a zuciyarta tana sakkowa ƙasa ta zauna zaman dirshan ta naɗe ƙafafu.
"Kin ga ma ledar viva da na taho da ita a zubawa marayun Allah su Hassu su mayar da yawu amma ki bari idan na ci na yi nak sai ki juye sauran ki ɗakko wanda kika ajiye a tukunya ki juye mana, kya ɗora wani da dare tun da ku naman kaji kullum ne mu kuwa daga sati sai wata albarkacin auren ki a nan ma ke mayar da mugun yawu" Ta ce tana murmusawa. Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi amma Dada bata lura ba.
Sai da ta buɗe ledar ta ajiye a gefe maganin mantuwa don kar ta fara ci daɗi ya ratsa ta manta da ledar ƴan biyu ta koma ta shiga uku a wajem su duk da ta san ba za a rasa wani naman da shinkafa kaza a gidan ba tun da dai ba a rasa nono a ruga.
Mayafinta ta cire ta ajiye tana gyara hannun riga ta buɗe babban fiɗas ɗin wanda a nan ne take saka ran ganin kajin, buɗewarta ke da wuya har sai da ta zabura tamkar ta ga abin tsoro. Salati ta shiga rafkawa tana kallon Amina.
"Amina mai zan gani? Biski (Burabusko tuwon gero da ake ɓarza geron) Awannan lafiyayyan kwanon da rana tsaka? " Ta ce bata jira amsar Aminar ba ta buɗe ɗaya kwanon faten wake ne ko kayan miya bai ishe shi ba tana buɗe ɗayan ta ga wata miyar kuka ta yi kauri kirtif da ita kore sharrr ko alamar maiƙon mai babu bare a saka ran daɗi. Da ƙafa Dada ta hankaɗa filas ɗin miyar aikuwa kwacar ya kife miyar ta zube, ta shiga surfa bala'i
"Uban me ƙasƙantaccen abincin nan yake a gidan nan wannan wane irin ɗaukan magana ne Amina da rana tsaka ki tuƙa tuwon biski da miyar kuka kalli ko da na zubar da miyar ma ko ƙashi babu sai waken miya " Dada ta faɗa ranta yana ƙuna.
"Dada cimar gidan ce fa a haka kuma ba iya ni kaɗai nake yi ba har gidan matansa kwano uku ne nake tuƙawa da dare kuma sai a yi tuwon dawa wallahi tun da na zo ban ci nama ba in banda irin kifin nan ƙanana masu kamar fara kana ci suna maka ɗaci su ne kazar amarcina"
Wani salati Dada ta ɗauka tamkar an yi mutuwa ko wani gagarumin abu ta shiga tafa hannuwa.
"Amina kike tuƙa tuwon kwano shida a rana? Na rana uku na dare uku yo ba dole ki yi baƙi ki rame ba dama haka auren mai kuɗin yake? Ni ina can ina baza hanci ina ɗagawa kishiyoyi kai ƴata ta yi aure a gidan naira, ko yanzu sai da ta jefarwa su Ladiyo baƙar magama na fito amma in tarar da ke babu yadda kike ke ma kina buƙatar taimako" Ta faɗa tana tashi daga ƙasan ta koma kan kujera ta zauna jin cikinta yana ƙaran yunwa don yanzu yawun nata da yake taruwa baƙinciki ya sa ya kafe tun da babu wani abu na kwaɗayi.
"Ai Dada ki daina cewa ma na yi auren mai kuɗin don cimar gidan nan sai wanda ya gani...
"Wai to wannan rusheshiyar tumbin cikin nasa da ya ajiye yana tafiya tirtsi-tirtsi kamar mai cikin wata tara dama ba tsabar cin daɗi bane?" Ta katse mata maganar.
"Wannan tuwon dai shi yake ci"
"Na ga annabi in na yi hali na gari ni Saude, wane tsautsayi zagin mahaifin ne y kai mu ya baro da wannan sabga lallai an biki a gidanmu wai in gani a ƙasa in ji kare, wannan ai wutar ƙaiƙayi muka kunnowa kanmu garin son banza, lallai Sabo bashi da amana ni da nake ganin girma cikinsa tsabar cin mai maiƙo ne ashe da basir ne ya kumbura masa teɓa, ja'iri mai kai tun na haihuwa ashe shi ya sa da ya ganni ya kawar da kai gefe ya mere baki tamkar ya ga kashi to wallahi mu zuba mu gani ni da shi ɗan halak ka fasa zai shigo ya same...
Ƙaran sawun takalminsa ne ya katsewa Dada maganar da take, a take ta shiga huce tamkar kububuwa tana jiran ya shigo ya durƙusa ya gaisheta ta ƙi amsawa ta ƙare masa cin fuska tas.
"Amina" Ya ƙwalawa Aminar kira yana hura hanci. Amsawa ta yi ta fito jiki yana rawa Dada kuwa da kallo ta bita tana jijjiga kai don yau sai ta nunawa Sabo ya taɓo gidan rina.
MAMAN AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
*CI MA ZAUNE*
*NA*
*MAMAN AFRAH*
*Daga marubuciyar*
*Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beelal da sauran su*
*09025576222*
🅿️2️⃣
"Ki wanke mini farar shaddar nan ki goge mini" Ya ce yana haɗe rai zai juya ya koma waje, da to Aminar ta amsa duk abin da ake Dada tana kallon su ta gefen labule.
"Sabo! Sabo!! Sabo!!!" Dada ta shiga ƙwala masa kiran sunansa muraran yau babu Alhajin ma, ganin ya shigo gidan tamkar bai san tana nan ba, bare ya je ya gaishe ta. Sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya amsa a shelaƙe.
"Iyee" Ya ce a daƙile maimakon