Showing 27001 words to 30000 words out of 180103 words
Ina Mata godiya na karbi zanin na shiga band'akin Dan Ina Jin kunyar cire Kaya a gabanta ko Ina Naseer ya samo mutane masu karamci Haka oho yasan duk tsawon lokacin Nan akwai.mutane irin Haka shine Bai kawoni ba ko wanke wanke na ringa musu indai zasu rik'eni a wajensu.
Sosai na gasa kaina da ruwan zafi inajin dadin jikina yaushe rabon dana jini a sake haka har na manta inama Naseer ya barni a gidanan da yayana inama mutanen Nan su zama iyayena su rik'eni a wajensu da naji dadi.
Duk Inda Umma ta yakusheni na gaggasa Dan kamar ba yakushi ba sabida zafin danake ji gashi jikina yayi rudu rudu abinka da fara ahaka na fito da Daurin kirji.
Ina fitowa tana Gama yiwa Minal wanka
Su Zahira ma har an musu wanka an canza musu kayan jikinsu an kwantar dasu sosai naji dadin yanda matar tayi Mana da alama itace matar Mallamin.
A Gefen gadon ma an ajiyemin kayan da Zan saka da auduga.
Godiya na ringa Mata sosai har sai data nuna b'acin ranta.
Ina Gama saka Kaya ta turomin flask din tuwon Massara da miyar yauki yaji namomi yaushe rabon Dana samu irin wanan abincin gefe Kuma ga shayi Mai zafi Tana Gama shirya Minal ta ajiyeta a gefena ta fita sabida na sake naci abinci.
Banyi falako ba naci na koshi Maganin data bani na ciwon jiki na Sha Ina kwanciya bacci Mai nauyin gaske yayi awon gaba dani
Naseer kuwa Yana ganin Su Naeema sun shige gida ya fara kukan bakin ciki Dan sosai yaji kirjinsa ya cushe idan ba kukan yayi ba bazai ji saukin abinda yake ji ba.
Mallam Musbahu kuwa Bai Hana shi ba sai daya Gama Dan kansa ya fara bashi baki Yana Masa nasiha da yarda da kaddara da hakuri.
Naseer dagowa yayi Yana "Mallam Nagaji inaso na gudu da iyalina ko zan samu kwanciyar hankali hakane yasa Nazo wajenka ka bani shawara wani gari Zan koma"
Mallam Musbahu murmushi yayi Yana "ko da baka zo da maganar ba shawarar da nake taso na baka kenan ka koma Garin Kano da zama batare Mahaifiyarka ta sani ba Kar wani Abu ya Kara maidaka gidanan Sabida kaima kasan bazasu barka Haka ba Haka ma matarka.
Akwai kanina a garin Kano Yana zaune a goron dutse Zan baka address dinsa kaje ka same shi ya nema maka gidan haya ka fara Kama muku kafin komai ya lafa"
"Mallam idan ma na samu gidan siyarwa Zan siya sabida Ina da kudin siyan akwai gidana a Jos Dana siyar wanan Kuma Zan barwa mahaifiyata ta zauna da yayanta Zan Kuma aika Mata sakon kudi idan ta hucce an kwana biyu Zan dawo"
Haka kuwa akayi Washegari da sassafe Naseer ya d'au hanyar Kano cikin Sati d'aya ya samu kato gida ya siya ya zuba komai dazasu bukata a gidan a unguwarsu Kanin Mallam Musbahu ya samu gidan shima kanin Mallam Musbahu mallami ne Mai mutunci da dattako Mallam Haruna.
Sai da Naseer ya Gama komai ya koma Calaba Dan ya d'auko su Naeema.
Naeema
A bakin Matar Mallam da nake cewa mama naji Ashe Naseer tafiya yayi Haka kawai naji babu dadi da Naseer bai nemeni ballantana ya gayamin bansani ba ko fushi yake Dani sabida Dan tirjewar dana Masa Akan bazan koma gidan Umma ba.
Sosai naji dadin sati dayan danayi a gidan Mama tunanin halin da Naseer yake ciki ne kawai ya ragemin Jin dadi.
Har wani Dan kib'ar kwanciyar hankali nayi yayana Suma sun samu gida sai watayarsu suke suna Wasa
sosai nake adduar Allah yasa mu dawwama a wanan gidan Dan babu yanda Zan sake komawa gidan Umma na Sha yunk'urin Sanar da Mama halin da nake ciki Koda shawara ne ta bani sai naji na k'asa Mata maganar sai Naga kamar ban kyautawa Naseer ba idan na fadawa wani halin mahaifiyarsa.
Da magriba Ina zaune a daki Ina shayar da Minal naji sallamar Naseer a bakin kofa da Sauri na dago na zuba Masa Ido.
Su Zahira kuwa suka tafi da gudu Suka rungumeshi.
Sosai Naga ya rame yayi baki sai tausayinsa ya rufeni.
Sai daya Gama dad'agasu
Ya nufo wajen da muke ya sunkuya ya d'auki Minal ya Dan saci kallona sai naji duk ba dadi kamar kunyata yake ji yabi ya canza kamar bashi ba.
Gaishe shi nayi ya amsa ya zauna Akan side drawer jikin gadon
Ni kuwa na mik'e na fita Waje Dan na d'auko Masa ruwa Ina fita naci Karo da Mama da farantin ruwa har da lemon kwalba da kofi.
Godiya na mata na koma ciki na zuba Masa ruwan ya karba ya Sha Ni kuwa nace Masa ya hanya yace Alhamdulillah.
Daga Nan yacemin "Gobe ku shirya da wuri zamu dauki hanyar kano.
Kamar na tashi na dakka tsalle Haka naji sabida tsananin murna Amma tuna ko da Umma zamu koma Kano yasa nace "Kano zamu koma da zama su Umma fa"?
Ambatar su Umma da nayi yasa ya mik'e da Sauri
Yana "anan zasu zauna iya mu zamu tafi gwara mu nisanceta kafin Allah ya warware Mana komai"
"Allah yasa Hakan shi yafi alheri"
Ameen kawai yace ya Ajiye Minal Yana "Bari naje wajen Mallam bamu gaisa bama nashigo.
Sosai naji kamar anmin albishir da gidan Aljanna barin garin Calaba da zamuyi mu nisanci Umma Wanda hakan na nufin Zan samu kwanciyar hankali babu Mai kawo min farmaki.
Wajen karfe Tara na dare Mallam ya aika a kirani Ina zuwa Naga Naseer a gefensa hadamu yayi ya Mana nasiha tare da bawa Musbahu Adduoi Mai yawa Inda Nima ya bani gajeru da yasan Zan iya haddacewa idan na nace ya bamu shawara da duk da zamu bar garin Nan Kar muyi sake da addua mu zage damtse mu cigaba Dan ko shi daya taimakemu sai da suka so kawo mishi Hari Inda basu San shi ya Riga da yafi karfinsu ba daya shiga bayi aka zo Masa a siffar mage shi kuwa sai daya tabbatar da ya makawa Magen Abu a gadon Baya ga mamakinsa Yana ihu yaji muryar mace.
Shi ma yasan da zamanmu a gidan za a Kai ga Haka shiyasa d'akin da aka saukeni ya zagaye shi da Addu'oi da tuni an tab'ani ko an tab'a yayana.
Sosai naji Kuma hankalina ya tashi da maganar Mallam Musbahu Inda na fara kuka shi kuwa ya hau kwantar min da hankali.
A ranar a tsorace na kwana
Washegari da asuba muka d'au hanya......
8/19/21, 10:30 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 11*
A gajiye muka iso garin Kano da tunda muka iso naji wani sakayau Dani iskar ma garin ya bambanta Dana garin da muka baro.
Sosai nayi mamaki ganin katon gidan da Naseer ya siya mana Dan gidan bene ne kasan Kuma shaguna ne da alama sabone fil duk da jikina ba kwari Haka na zage muka gyara gidan washegari nida Naseer.
Gidan sosai yayi kyau Dan d'akinsu Zahira ma yafi k'awatuwa duk da ba abinda muka d'auko a wancan gidan Nan ma komai akwai Dan har yafi na gidanmu dake Calabar
da yamma mak'ota sukayi ta shigo mana naji dadin shigowarsu sosai Dan da alama suna da mutunci Dan har Dan Tayani sauran aikace aikacen gidan sukayi.
Naseer Sam bai wani zauna ba tunda muka dawo ya Kuma canjamin bansan dalili ba Haka kawai naji ba dadin canzamin daya yi hakane yasa na shirya Masa magana idan ya dawo.
Wajen karfe Takwas ya dawo Yana dawowa na bashi abincinsa yaci.
Yana gama ci naga ya koma tsakiyar palon da wani dogon takarda Yana ta rubutu.
Su Zahira sun Dade da bacci Minal kuwa Tana goye a bayana.
Nima tsakiyar palon naje na zauna Ina kallon rubutun da yakeyi da nakeso ya Gama muyi magana
D'agowa yayi yace min "Lafiya kuwa ko akwai wani matsala ne"?
"Aaa Babu wani matsala nadai ga ka canjamin ne tun ranar da abinan ya faru shine nace ko Dan na d'an tirje ranan ne shiyasa kake fushi Dani idan ma shi din ne Dan Allah kayi hakuri.
Ajiye biron yayi akan takarda ya murza yatsun hannunsa sai daya d'auki tsawon lokaci ya fara magana "Ba daga ke bane Naeema abinda ke damuna daban tun ranar da muka Samu sab'ani da Umma nakejin ba dadi Umma Mahaifiyata ce ban Isa na canza ta ba nasan daraja mahaifiya shiyasa nake ganin Kamar ban kyauta Mata ba a matsayinta na wacce ta raini cikina har ta haifeni na fada Mata maganganun da basu Kamata ba duk da na baro garin sai nake jin ba dadi sai nake jina kamar a d'ad'aure Kamar Idan na Bata hakuri ta hakura sai nafi samun sukuni bansan mai kika Mata ta tsaneki ba bansan Mai yasa Umma ta Dora Miki Karan tsana ba abinda ke damuna kenan ba wani Abu ba.
Da Zan samu Umma ta kaunaceki ta rungume ki tamkar 'yarta Naeema da na fi kowa Jin dadi duk Inda na Kai ga na nusar da Umma ta kasa ganewa yau da ace nasan wani dangin Umma Wanda nasan suna gaba da ita da na Kai kararta wajensu sun mata naseeha k'ila taji maganarsu.
Sosai nake ganin ciwon da Naseer yake ji a zuciyarsa da koma waye Dole ya shiga cikin damuwa.
Cikin kwantar da murya na fara kwantar Masa da hankali Ina "Addua zamu cigaba da yi Naseer insha Allahu Umma zata Soni za kuma ta kaunaceni duk da munyi nisa ka cigaba da kyautata Mata kana Mata aike idan an kwana biyu sai kaje da kanka"
"Hmm abin da Kamar wuya Naeema Amma tunda Kika ce Allah ba abinda baya yuwa ga form nan na karbo Miki na islamiyya Dana Boko kina yin arbain Zaki fara zuwa insha Allah"
Kamar na tashi nayita rawa Haka naji da Naseer yace min Zan fara zuwa makarantar godiya nayita Masa shi kuwa ya jawo takarda ya cigaba da rubutu a ciki.
Bansan Haka zaman aure yake da dadi ba sai da muka dawo kano da zama bansan Haka ma'auratan da basu had'u da jarrabawa irin tawa suke cikin kwanciyar hankali ba sai da muka dawo kano bansan Haka mu'ammalla da mak'otan arziki yake da dadi ba sai da muka dawo kano Wai nice yanzu Zan kwanta batare da fargabar komai ba Wai nice yanzu Zan shiga kitchen na dafa Mana abinda ranmu keso muci mu koshi batare da fargabar komai ba.
Babu abinda Naseer Bai wadata mu dashi ba dan Zan iya cewa a wanan lokacin za'a iya saka Naseer a sahun masu kudin unguwar.
Tsabar matsuwar da nayi da na fara zuwa makaranta ko arbain din banyi ba na fara zuwa Dan ba zanyi gangancin Wasa da Wanan damar da Allah ya bani ba inaso na nemi ilimi da Zan kusanci mahallacina sosai na cigaba da Kai Masa kukana.
Cikin ikon Allah kuwa da fara zuwana makaranta na ringa ganewa da wuri sabida na saka San koya Raina.
Su Zahira ma tuni Naseer ya nema musu makaranta suka fara zuwa zan iya cewa banida matsalar komai sai karatuna Dana saka a gaba da rainon Minal danake.
Tsakanina da Naseer kuwa soyayya ce Mai tsafta da girmama juna duk da munyi nesa da Umma Hakan Bai saka mun saki jiki ba addua muka cigaba dayi Dan nima na koyi tashin dare kamar yanda Naseer Naga ya zame Masa jiki.
Sosai dawowar mu Kano ya zame Mana alheri Dan bayan sanin kaina Dana farayi ta hanyar cud'anya da mutane na fara Dan samun wayewa da bud'ewar ido ta hanyar muamalla da mutane Dan daga zuwa na makaranta na had'u da wata Aisha da ake cewa mmn Mannir yanda banida ilimin komai hakane ya kasance gareta hakane yasa tamu tazo d'aya da ita abin mamaki har na Kan Dan nuna Mata abinda bata gane ba nacewar da nayi da San koyon ilimin addini yasa nake ganewa Nan da Nan daga kasa aka fara Mana wato fatiha aka ringa had'a Mana da huruf Wanda ya taimakamin sosai wajen gane bak'i.
Mmn Mannir gida hud'u ne a tsakaninmu tana da mutunci sosai duk da ta girme min nesa ba kusa ba Amma Haka muke Dan kawancenmu da ita takan Dan fadamin abinda ya shafi rayuwar Aurenta Ni kuwa sai dai naji ta kawai bana iya fadan abinda ya shafeni Dan Ni Dama can Ina da zurfin ciki balle rayuwar gidan Aurena a ganina ba abinda Zan fito na ringa labari akansa bane.
Naseer kuwa shagunan dake kasan gidanmu duk sai daya cika su da kayan siyarwa Wanda ya samu wasu suka rik'e Masa shagon a cikin shagunan akwai Inda Nama da kifi kawai ake siyarwa layin namu dayake ba masu siyar da nama da kifi sosai Ake cinikin Nama da kifi inda cikin kankanin lokaci Nan da Nan zai Kare tun Naseer na yanka raguna biyu ya koma Yana yanka Dan Sa
Daya shagon nasa Kuma lemuna yake siyarwa akan sari masu kananan shaguna gurinsa suke zuwa siya.
Daya shagon Kuma kayan awo ne Kama daga su shinkafa gero dawa wake shima buhu buhu yake siyarwa dawowarmu Kano da wata shidda Naseer yayi wani irin kudi Dan Motocin hawansa sai da suka Kai uku.
Har ya Kara siyan wani katon fili a layinmu .
Sosai ya daina samun lokacin kansa tafiye tafiyen da yake Yi Bai fasa ba yakan yi kwana uku Haka ko biyar kafin ya dawo.
Ni kuwa ba wani damuwa nayi ba sabida karatuna Dana saka a gaba.
Har Lokacin ban saki jikina ba Ina Kan addua Naseer da Bai fiye zama ne bansani ba ko ya rik'e addua kamar yanda Mallam Musbahu ya bashi shawara.
Sosai nake addua Allah yasa na samu hutu kafin na Kara samun wani cikin Dan a lokacin ba wani sanin tsarin iyali nayi ba.
Hutu da Jin dadi sosai ya nuna a jikin Ni da yayana Dan har mota Naseer ya Ajiye da sunana akan duk Inda zani wani yaro matuki dake kasan layinmu ya ringa Kai mu Yana dawo damu duk wata zai na biyansa kudaden cinikin shagon sa kuwa Ni ake kawowa duk ranar Jumma'a wani yaronsa ke had'a lissafin kudin ya Kai banki.
Naseer kuwa bud'in dayake samu sosai yasa yake wa Hajara Aiken kudi masu kauri har wasika yake rubuta mata duk da yasan ba ilimi ne da ita ba yasan zata samu Mai karanta Mata wasika ne na neman yafiya da ban hakuri gareta akan tafiyar da yayi batare da saninta ba zai dawo idan ta huce Yana rokonta ta cigaba da saka Masa albarka a rayuwarsa.
B'angaren su Hajara kuwa a ranar da Naseer da Naeema Suka bar gidan ta nufi Kungiya dasu Safiyya da sai data zauna ta gasa musu jikinsu da ruwan zafi sosai zuciyarta ke tafasa da irin dukan da Naseer ya musu Inda take Jin da yau wani ne yayiwa su Safiyya Haka ko duk karfinta zai Kare sai ta aika shi barzahu.
Da isarsu kuwa ta korawa shugabarsu komai.
Take duk suka hau ce Mata Kar ta yarda ta d'au mummunan mataki akan Naseer da Naeema taya zaayi Naseer yayiwa su Safiyya Haka kawai Sabida sun daki Naeema ya zama Dole ko Yaya ne a koyawa Naseer hankali a Kuma dau mummunan mataki akan Naeema tunda a lokacin Bata da tsarki duk abinda aikin da zasuyi akanta zai Kamata Nan da Nan.
Take shugabarsu ta d'auko kwaryar tsafinta dake d'auke da wani irin ruwa tayi surutai tana shafawa Naseer da Naeema Suka bayyana lokacin Naseer na gaban Mallam Musbahu Naeema Kuma tana d'akin matar Mallam Musbahu.
Cikin wani irin murya Shugabarsu tace ta zama Dole su hukunta Naseer tunda ya tab'a musu Yan kungiya har ya fitar musu da jini wato Safiyya da lami
Hajara na Shirin magana Dan tace da a hukunta Naseer gwara a hukunta Naeema
Wani irin kallo Shugabarsu ta Mata ta ja bakinta tayi shiru ita kuwa shugabarsu ta daga wani irin bulala dake d'auke da allurai tana Shirin makawa Kwaryar da hoton Naseer ke bayyane har lokacin.
Taga Naseer ya bace daga ruwan mamaki ne ya Kamata ta Kara surutan tsafi Amma me hoton Naseer ko na Naeema Bai Kara bayyana ba Dan a lokacin Naseer ya shiga Massallaci Naeema kuwa Tana d'akin Mama dake d'auke da manyan adduoi na tsari a kowane kasurwar d'akin.
Duk yanda sukayi Dan su Kara bayyana abin gagara yayi a karshe akan Dole Suka bawa Hajara wani irin tsafi Akan idan taje gida ta zuba a bakin kofa Naeema zata haukace Naseer Kuma sai yanda tayi dashi.
Suna komawa gida ta saka bakaken Kayanta
Ta zauna jiran dawowar Naseer da Naeema sai dai shiru basu dawo ba Wasa Wasa har akayi kwana uku babu su babu labarinsu ahaka suka Kara komawa kungiya Inda sai da suka buga sosai suka gano Inda Naeema take Da Naseer har tafiyar da Naseer yayi ta mudubi Suka gani.
Anan Suka yi Shirin zuwa gidan Mallam Musbahu Dan su Dan tab'a shi sanin Kuma babu Inda zasu same shi batare da su sun fuskanci wani matsala ba sai a bandaki hakane yasa Suka aiki Lami akan taje gidan idan ta samu Nassara akan Mallam Musbahu ta tab'a shi idan Kuma Naeema ce ta kasheta da wuk'ar Tsafi.
Lami kuwa jiki na rawa ta zama katon bakin mage ta shiga ta rufin gidan Mallam Musbahu ta tsaya daga wajen window bandaki.
Wajen Karfe dayan dare Mallam Musbahu yaga komai a mafarki Dan Allah ya Masa wanan baiwar idan Abu zai same shi zai gani a mafarki.
Wajen daya da rabi ya farka Sakamakon fitsarin daya matse shi har zai shiga band'akin ya tuna mafarkin da yayi hakane yasa ya dawo Baya ya d'auki wani katon Sandan daya gani Yana shiga band'akin da Addu'a shiga bandaki yayi Ido biyu da Bakin Mage Yi yayi kamar Bai ga Magen ba ya juya bayansa aikuwa take mage ta fara shirin dirar Masa ta baya ya juya cikin zafin Nama ya maka Masa sand'a kafin magen ya dira ta waje ya Kara mak'a Masa a gadon Baya take yaji ihun mace.
Ya fito daga band'akin da Sauri bakinsa d'auke da Addu'a ya zagaya ta bayan gidan Amma Bai ga komai ba baccin da bai koma ba kenan.
Ya turare gidan da hayakin