Showing 30001 words to 33000 words out of 180103 words
daya San basu Isa su Kara dawowa ba
Ko kusa da Gidan bazasu iya zuwa ba.
Lami kuwa sosai Mallam Musbahu ya sameta a baya a lokacin da ta koma siffar ta ta koma kungiya Inda Sam Bata iya mik'ewa tsaye.
Sosai hankalinsu ya tashi Yan kungiya duk dabarun da sukayi Dan suga Lami ta warke Amma abin yaci tura abinda ya d'auke hankalin Hajara kenan daga Kan Naseer da Naeema har tsawon wata hud'u tana jinyar gadon bayan lami da take Shan alwashin in ta warke babu abinda zai Hana ta kashe Mallam Musbahu.
Wata biyar da barinsu Naeema Calabar taje kungiya aka bincika Mata Inda su Naseer suke da irin kudin da yayi da irin hutun da Naeema ta samu.
Anan ma sukayi ta k'ok'arin wajen kashe Naeema ta hanyar tsafi Amma abin ya gaggara Dan yanzu Naeema ta Dan samu ilimi Kuma tana adduoi Dan saken da Naseer yayi da adduoi sabida neman kudin da yake ba dare ba Rana yasa Suka Dan karkato da zuciyar Naseer wajen Hajaran ya hau Mata aike Yana Mata wasika.
Anan shugabarsu ta Bata shawarwarin hanyoyin da zata bi wajen mallake danta ta Kuma kau da Naeema ta bar duniya na har abada sosai take ganin sabon salon da suka d'auko zai bille dasu su kau da Naeema cikin sauki wanan kenan.
A cikin kwanakin Nan Haka kawai na tsiri mafarki da Umma a mumunan yanayi tana ta Bina zata kasheni.
Ganin inata mafarkin a jejjere yasa na sake dagewa da Addu'a dayake Ina da kudi kuma muna cikin wadata sai na tsiri Sadakan dafaffen abinci duk ranar jumaa tunda Sadaka maganin masifa ce.
Kamar zanyiwa Naseer zancen mafarkin da nake yawan yi da Umma sai Kuma na fasa Sabida nasan zaiji ba dadi zai ga ma kamar zargin mahaifiyarsa nake.
Zuwa yanzu Naga ya danyi sake da Addu'oi ba kamar da ba Dan yanzu Inya dawo ya Dan Yi nafilfili takardarsa yake daukowa ya hau lissafi da rubuce rubuce.
Ahaka wani zubin bacci ke daukarsa ni Kuma sai na dauke takarda da biron na ajiye idan na Gama adduoi na sai na tofa Masa adduar kwanciyar bacci da yarana.
Dan wata shidda danayi Ina zuwa makaranta na San adduoi sosai na Kuma San daga fatiha zuwa izu uku.
Watan Minal Tara na samu wani cikin a ranar Dana San ciki ne Dani a ranar sukuku na wuni Dan banji dadin samun cikin yanzu ba naso ko shekara biyu tayi kafin na samu wani cikin.
Zuwa lokacin nasan nayi nisa a makaranta.
Sai dai ya zanyi kana naka Allah na nashi.
A Daren ranar na shirya gayawa Naseer cikin danake d'auke dashi
A dakinsa na same shi ya janyo akwati Yana ta had'a Kaya.
Na dauka wani tafiyar ne ya Kara taso Masa kamar yanda ya Saba shiyasa ban Masa magana na na je kusa dashi Ina Taya shi had'a kayan.
Shi kuwa ya dago yacemin.
"Gobe idan Allah ya kaimu zanje Calabar dazu an turomin wasika Umma Bata Jin dadi an kwantar da ita a asibiti Dan Haka gobe asubanci zanyi na tafi.
Bansan rigarsa ta sub'uce daga hannuna ba gabana ya yanke ya Fadi take jikina ya hau rawa.
Hakane yasa yace min Lafiya.
Ni kuwa cikin dauriya nace Masa ba komai Allah ya sauwake ya Bata lafiya.
Bai Kara cemin komai ba ya gama karasa hada kayan ya shige bandaki
Ni kuwa na fice daga d'akin da Sauri na koma dakina hankalina a balain tashe Allah yasa ba wani Abun ke Shirin samuna ba sabida yawan mafarkin danake da Umma bansan Mai yasa hankalina ya tashi da Naseer yace zaije Calabar ba Ina tsoron Umma Ina tsoron abinda zuwan Naseer zai haifar.
A ranar ko runtsawa banyi ba Sabida yanda na dage da Addu'a.
Washegari da assusuba Naseer ya d'au hanyar Calabar ni kuwa ya barni cikin Zullumi da tashin hankali ya zanyi toh mahaifiyarsa ce ban Isa na rabasu ba Allah ya dubeni da idon rahama ya kareni da karewarsa nidai da da yanzu ba daya bane bazan Kara yarda Umma ta bani wahala kamar yanda ta bani a baya ba.
A ranar da Naseer ya cika kwana uku da tafiyarsa Calabar da yamma na dawo daga islamiyya Ina girki a kitchen su Zahira Kuma suna Palo naji Ana kwankwasa kofa.
Da Sauri na fito daga kitchen ganin yanda ake kwankwasawa da k'arfi hannunsu Zahira Bai Kai handle din ba ballantana su bud'e.
Ina bud'ewa nayi tozali da Umma da Safiyya ga manyan jakankuna a gaba bayansu Kuma Naseer ne ya d'auko musu sauran kayansu daga cikin taxi.
Murmushi Nan da Umma kemin dake tsinkemin zuciya shi ta sakar min Ni kuwa jikina ya hau b'ari na Kuma kasa basu hanya su shiga sabida mutuwar tsayen da nayi Ni nasan da zaa auna jinina ba karamin Hawa yayi ba bugun zuciyata kuwa tun daga nesa zaka iya jiyowa.
Maganar Naseer ne ya dawo Dani hankalina.
"Ki bawa su Umma hanya su wuce Mana bakida hankali ne Zaki tare musu hanya"
Naseer yacemin a tsawace Ni kuwa na matsa da Sauri na zub'e a kasa Ina musu Sannu da zuwa Naseer kuwa hannunsu Jaye da akwati ya shige Safiyya ta bi bayansa tana kalle kalle
Umma kuwa muka tsaya kallon kallo har lokacin Fuskarta d'auke da Wanan murmushin sai data zo dab Dani tace "kin Kara d'aukar wani cikin kenan"..........
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 12*
Cikin tsoro da mamaki na kalli cikina da baifi wata biyu ba cikina a kwance babu alamar ma cikina ya taso ballantana ince tsinin cikina ta gani.
Da Sauri na Kara d'agowa na kalleta ta sakarmin murmushi tana "ke Kuma aikinki kenan ko Naeema kin samu Naseer Zaki cika Masa gida da 'ya'ya toh yayi kyau"
Daga Haka ta wuceni tana karewa palon kallo.
Jikina Banda rawa bbu abinda yakeyi ahaka na rufe k'ofar na juya na nufi palon Ina zufa.
A daidai lokacin da Umma ta zauna a kujera ta kalli su Zahira da shigowarsu yasa Suka mik'e tsaye suna zazzare Ido.
Hannu ta mik'a musu tana "Kuna ganina bazaku zo wajena ba ko har Kun manta Dani ne?
Tace tana kallon Naseer
Zahira da Nadeeya da Sauri suka yo wajena suka fara k'ok'arin b'uya a bayana.
Naseer kuwa ya daka musu tsawa Yana "bazaku je ku gaida Umma ba"?
Da Sauri suka nufi tsakiyar palon Suka tsaya nesa da ita Suka hau gaisheta
Ita kuwa ta amsa tana murmushi nima na karasa tsakiyar palon na zub'e a kasa Ina gaisheta cikin rawar murya.
Wani irin kallo tamin ta amsa da murmushi nan nata da babu alheri.
Kafin na mik'e Naseer har ya kawo musu ruwan Sanyi da lemo jikinsa sai rawa yake Yana ajiyewa ya koma ya juyo kazar da nake soyawa gabadaya a faranti yazo ya Ajiye musu.
Nima mik'ewa nayi nabi bayansa Dan na zubo musu abincin tunda na Riga da na Gama dama kwashewa nakeso nayi.
Kafin ma na isa kitchen din har ya Kara fitowa da wani farantin Mai dauke da soyayayyen kifi da nama dan Dama Haka nake soyawa da yawa na zuba a fridge kawai idan zanyi girki sai na dib'a da yawa ake kawo Mana daga shagonsa.
Mamakine ya Dan kamani ganin bama d'ebowa yayi ba juyowa yayi gabad'aya.
Bance masa komai ba na shiga kitchen.
Na jawo kula na zuba musu shinkafa da miyar.
Na koma palon na ajiye a tsakiyar palon.
Naseer kuwa na zaune daga gefensu a kasa ya tankwashe kafa sai murmushi yake Yana su fara cin abincin Mana.
Umma kuwa farantin da ya jere Mata a gabanta kawai take kallo tana gyada Kai Safiyya kuwa tuni ta sauko ta fara yagar kaza.
Ina Shirin juyawa na zubowa su Zahira abinci naji Umma ta fara Jan majina kamar Mai kuka tana "Naseer yanzu Haka kuke Jin dadi kuka gudu kuka barmu a can abinda zamu sakawa cikinmu ma na neman gaggararmu kasan kuwa mun Sha kwana da yunwa akan karamin kuskure Naseer ka d'auki matarka ka gudu ka barni bayan kasan Kaine babban Dana babu Mai iya d'aukar dawainiyarmu idan ba Kai ba.
A garin nemawa Lami kudin magani na gurd'e a k'afata Haba Naseer abinda Kayi baka kyauta ba karka manta Ni Mahaifiyarka ce Bai Kamata ka fifita matarka a kaina ba a baya nasan bana San Naeema Sabida shaidan daya sakoni a gaba Amma yanzu na gane Dan Haka kuyi hakuri da Kai da Naeema bazan sake ba"
"Haba Umma Mai yasa kike bamu hakuri ke ya Kamata mu bawa hakuri mun Miki ba daidai ba Dan Allah kiyi hakuri da matakin da muka dauka bazamu sake ba insha Allahu fatana kawai ki cigaba da saka Mana albarka Naeema Kuma zata kasance Mai biyayya a gareki insha Allahu"
Naseer yace Ni Kuma na koma na zauna hankalina a balain tashe shekara biyar ba Wasa bane zuwa yanzu na gama sanin wacece Umma ciki da Bai gwara Umma ta fito ta nuna min kiyayyarta data fito min da Wanan fuskar tata daya fi kowane hatsari Ni nasan Umma ba karamin shiri tayi ba kafin tazo Ni nasan idan ban dage ba wanan Karin sai taci Nassara akaina bansan Mai yasa Naseer ya kasa Gane wacece mahaifiyarsa ba gani nake duk abinda zaayi babu abinda zai saka tayi laushi Haka a Karan kanta sai dai idan Allah yaso ta da rahama ya ganar da ita gaskiya.
Daga yanda Naga Naseer na rawar jiki nasan shima ba'a barshi Haka ba.
Sosai nayi k'ok'arin b'oye tashin hankalina na Dan saki fuskata cikin yak'e Ina Kara bawa Umma hakuri wanda naga Naseer ya ji dadin hakan sosai
Mik'ewa nayi Sabida cikina danaji Yana juyamin Dan idan na tsorata Haka ko na shiga tashin hankali sai na shiga bandaki.
Kafin na Kai ga shiga dakin naji muryar Naseer Yana in gyarawa su Umma d'aki suzo su huta.
Sai Dana fito daga band'akin na fito na nufi d'akin dayace na gyara musu Dan dakuna biyune bama amfani dashi shima babu abinda babu a ciki.
Kafin na shiga d'akin inajin tana Masa tambayoyin Inda ya samu kudi Haka shi kuwa cikin rawar jiki ya hau Bata labarin yanda ya samu da kudaden dake shigo Masa.
Sai Dana gyara na fito na nufi dakina Dan nayi Sallahr Magriba.
Ban Kara fitowa ba sai da nayi sallar isha shima sai Dana d'auki Qurani na Mai izu goma na karanta surorin Dana iya kafin na fito wajen Taran dare.
Ban ga kowa a palon ba sai su Zahira da bacci ya d'auke su a tsakiyar palon.
Daukarsu nayi na kai su dakina Dan Dama a d'akina suke kwana idan Naseer na gari Kuma sai na kwana a d'akinsa.
Sai Dana kwanatar dasu na tofe su da Addu'oi na kunna wani karamin radio mai daukar cassette daya Dan biyu ne damu ko uku ma akwai Mai d'aukar cassete biyu akwai Mai d'aukar daya (Kila ku gane radio danake magana ba plate ba cassete Mai zare a ciki)
Taro shi nayi sai daya faro daga Suratul Baqarah na ajiye musu
A gefen gadon.
Na fito daga d'akin na nufi kitchen Dan na d'ebo abinci Ina Jin muryar Naseer a d'akin Dana gyarawa Umma suna ta Hira.
Abincina na zubo inata mamakin yaushe Kuma Naseer ya fara sakewa da Umma suyi Hira Haka ko duk cikin Salon da Umma tazo dashi ne Haka na zubo abincin ba nama Dan duk Naman Naseer ya kaiwa su Umma Kuma a palon ma Banga farantin ba Nan kuwa su Umma Ashe da farantan Suka shiga d'aki.
Dayake Haka ma ake jibge Mana lemo a store Kuma bama rabuwa dasu a fridge lokacin lemon kwalba ne coke Haka Pepsi na d'auko daya Mai sanyi
Na koma d'akina sai Danaci na koshi na Kara fitowa wajen goma na dare har lokacin Naseer na d'akin Umma ta rik'e shi da labarai babu yanda zaiyi Nan kuwa ya gaji Kuma Yana Jin yunwa Amma bayaso ya tashi Umma taji ba dadi.
Ni kuwa kwanciyata nayi Ina jiran daya da rabi yyi na dare na tashi Dan yanzu Banga ta bacci ba sai na dage da Addu'a Ina Kuma fatan Naseer ya lek'o dakina na Dan Masa maganar dagewa da Addu'a.
Gani nake irin azabar da Umma ta gana min lokacin cikin Minal Haka zata ganamin da Wanan cikin tunanin Haka kawai da nayi sai daya Saukar min da fargaba Wanda tuni bacci yayi nashi gurin na tashi na daura alwala na hau kan Sallaya.
Naseer kuwa Bai samu barin d'akin Umma ba sai Sha biyu Dan ahaka sai daya ce Mata Sallah zaiyi .
Ita dai ba Haka taso ba sosai take so ta jawo Naseer jiki yanda zai na shagala sosai da ibada
Ba karamin kokari tayi wajen Kai zuciyarta nesa ba Dan ta lura sai ta biyo wa Naseer da Naeema ta bayan gida zata ci Galaba a kansu Kamar ta Kama da wuta data ga Naeema tayi wani irin kib'a ta samu kwanciyar hankali Karin bakin cikinta tana zuwa ta Gane Naeema na dauke da ciki Mai Naeema take nufi da ita ne wato bazata rabu da Naseer ba sai dai tayi ta haife haife ta haifi cikin jikinta tagani.
Sosai taji bakin cikin daular data ga Naeema a ciki hakane yasa ta ringa Dan bugar cikin Naseer game da dukiyarsa aikuwa ta samu yanda takeso Dan Naseer ya Gaya Mata komaii game da dukiyarsa a duk hirar da sukayi Bata ji ya mallakawa Naeeema wani ba Amma duk dahaka kaji da namomin da take ci ma ai Jin dadi ne
Ina zaune akan Sallaya Naseer ya shigo d'akina hannunsa d'auke da abinci da lemo.
A kasa ya zauna ya fara cin abincin Yana "Ai na dauka kinyi bacci"
Girgiza Masa Kai nayi Ina "Baka shigo ba tayaya zanyi bacci"
"Ai Umma ce take ta Jana da Hira tundazu dak'yar na fito"
"Kayi Sallah kuwa"?
Zaro Ido yayi Yana "Subhanallahi wlh Banyi Sallah ba Naeema banyi Magriba da Isha ba innalillahi yau Mai ya sameni Haka"?
Yace ya mik'e da Sauri ya shiga band'akin d'akina ya d'aura alwala ya shimfida Daduma ya tadda Sallah.
Lailai Umma ba k'aramin Kama Naseer tayi ba sosai naji jikina ya Kara sanyi Dan Naseer mutum ne shi jajirtace Mai ibada Zan iya cewa Yana bacci Yana mafarkin Sallah Amma sai gashi Wai shine ya shagala Haka Bai Yi Magriba da Isha ba.
A haka na cigaba da Jan Hasbunallahu wa neemal wakil Yana iddarwa Naga ya fara Hamma idonsa ya kankance Sabida bacci daya cika Masa ido.
Ganin Yana k'ok'arin mik'ewa yasa na saka hannu na dafe cinyarsa ya koma ya zauna Ni kuwa cikin murmushi nace "Wai har kayi me"?
"Nayi Sallah Mana wlh yau bacci ne a idona Naeema bazan iya adduoi Mai tsayi ba"
Rik'e Masa hannu nayi cikin Dan fargaba yanda zai dau maganata nace "A gaskiya Naseer Bai Kamata ka shagala da.hira har Sallah Magriba da Isha ya kwace Maka ba Haba Naseer yaushe Kuma Abu ya fara Sha maka Kai da zaka na mantawa bakayi Sallah ba ka manta Shawarwarin Da Mallam Musbahu ya bamu ka manta da addu'ar da yace mu dage dashi Sabida mu samu kariya daga wajen Allah ko ba Dan kariya ba ko iya Niimar da Allah ya maka kake Samun bud'i ko ta ina ya Kamata ka Kara kusantarsa ka cigaba da gode Masa Kar bud'in daya maka yasa Kuma ka manta dashi.
Daga yanda Naga ya nutsu Ya bani hankalinsa sosai yasa nasan maganata ta shige shi
A Haka na cigaba da shigar Masa maganata cikin siga wajen dage Mana da Addu'a na Kara da "kasan kafini zurfin Ilimi Dan Allah ka dage Mana da Addu'a Kar mu koma gidan Jiya Naseer ka mantani da sai Dana kusa mutuwa ka dawo hayyacinka yanzu Haka Ina d'auke da k'aramin ciki na wata uku bansani ba sai a satin Nan ranar da nake Shirin Sanar maka a ranar kayi tafiya kaga kuwa Ina bukatar addua Akan Allah ya saukeni lafiya"
Hannuna ya ruk'o da k'arfi cikin farinciki Yana "Dan Allah dagaske kike cikine dake"?
Gyad'a Masa Kai nayi ya daga hannu Yana "Alhamdulillah naji dadi Alhamdulillah Naeema banida burin daya wuce yanzu ki Samu ciki ki haifomin namiji Ina yawan mafarki naje Massallaci da Dana Yana kiran Sallah Allah yasa Rabon da namiji ne a jikinki Na gode da tunatar Dani da kikayi da Shagalar da nayi insha Allahu Zan gyara Dan Allah kiyi hakuri ki Kai zuciyarki nesa akan Umma kinsan wani zubin Tana iya rikicewa duk da Ina kyautata zaton insha Allahu ta Gane gaskiya kamar yanda ta fada Dan da naje bakiga kukan da ta ringayi tana neman yafiyar mu ba Akan tayi nadamar Abubuwan da ta miki"
Murmushi kawai nayi ban Kara ce komai ba Dan Naseer bazai Gane ba kila sai Umma ta Kara gwada halinta da zai balain bashi mamaki zai San wacece ita.
Sosai Naga Naseer na farincikin da cikin Dana samu Inda ya balain kwallafa Rai da insha Allahu namiji ne ahaka ya Kara mik'ewa ya kawo nafiloli ya karanta Qurani Inda lokacin Ni Kuma naji bacci na neman daukata hakane yasa na mik'e da hijabin jikina na d'auki plate din da Naseer ya shigo dashi Dan in mayar kitchen Ina bud'e kofa Naga na buge Umma dake bakin kofa ta sunkuya Haka ta Kara kunnenta a jikin k'ofar da alama dai lebb'e take Mana
Cikin borin kunya ta ja da baya tana "dama k'afata ce ta matsamin nace bari nazo ko zan samu magani a wajenku"
"Wlh babu maganin ciwon kafa sai dai paracetamol"
Nace Mata jikina na Dan rawa Dan indai Zan tsaya kusa da Umma sai naji Kamar zata zaro wanan kaifafen wuk'ar ta cakamin
Wani irin kallo tamin ta juya tana toh shikenan
Dawowa nayi d'akin Dan Haka kawai naji tsoron ma zuwa kitchen din na ajiye plate din na kwanta Ina mamakin Halin Umma yanzu har ta Kai Umma lab'e take Mana da Naseer da yanzu kwanciyar Aure mukayi da Haka zata na Mana lab'e ko Kuma ta lek'o mu kenan.
Zan iya cewa tunda muka dawo kano sai da Umma tazo gidan na kasa bacci cikin nutsuwa sai wasu irin mafarkai nake.
Akan Sallaya bacci ya d'auki Naseer Ni kuwa sai Kiran Sallah ne ya tasheni.
Inda na tashi Naseer ni Kuma na nufi