Showing 45001 words to 48000 words out of 180103 words

Chapter 16 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2457

a cikinsu kamar ma bad'asu nake magana ba hannu na Dora a kaina na fara zabga Sallati na Kara d'aukar hanyar waje a guje ko Humaira danake juyo kukanta daga d'aki ban bi ta kanta ba


A bakin kofa na ci Karo da Naseer da tunda ya fita massallaci Bai dawo gidan ba Dan yaje kasan layinmu adduar mutuwar wani bawan Allah daya rasu.

Ina ganinsa nasan shima lukman ya Gaya masa Banga Nadeeya ba


Kara tambayata yayi "Wai baa ga Nadeeya ba"?

Ban iya bashi amsa ba na cigaba da kuka Ina na shiga uku da Sauri Naga ya hau saman Benen batare da yabi ta kaina ba nabi bayansa da Sauri..........
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 17*

D'akina ya shiga kansa tsaye Yana kwallawa Nadeeya Kira ya fito ya duba koina yana "Wai kamarya Ba'a ga Nadeeya ba sai kace almara Taya ya daga yiwa yarinya wanka ta fito kice baki ganta ba"?


Wajensu Umma da har lokacin basu nuna sun San Mai ke faruwa ba ya nufa Yana "Umma Dan Allah bakiga Nadeeya ta fito daga d'akin Naeema ba?

"Toh ko Ni na saceta da zaka zo kana min tambaya"?


B'acin Rai ne yasa Naseer yace a Dan tsawace "Umma daga tambaya sai kice ko saceta kikayi wanan wane irin magana ne"


Tsaki da Bai shiryawa fitowarsa ba yayi ya wuce waje fuu Hajara kuwa ta girgiza Kai tana har dasu Tsaki yayi kyau"

Zuwa lokacin Ni nasan jinina ya hau sabida tashin hankali.
Daga farkon layinmu zuwa karshen layin mu Haka muka zaga muna kwallawa Nadeeya Kira Amma shiru.

Mmn Mannir da itama ta fito ita da yaranta tuni ta fasa fita suka hau tayamu Neman Nadeeya makotana suna da balain kirki Dan ba iya matansu ba har da mazajensu Haka suka hau tayamu neman Nadeeya Inda sukayi ta mamaki idan nace musu daga wanka ta fito na nemeta na rasa Kuma duk Wanda yasan Nadeeya yasan Bata iya saukowa daga Sama.


Kukan ma kasa wa nayi sai sallati nake har komawa nake gidan na shiga d'akina Naga ko zan ganta har zazzaga kayan wardrobe Dina nayi ko shigewa tayi Amma ba Nadeeya babu labarinta Humaira kuwa har ta gaji da kuka tayi shiru a bayan Zahira da itama ta hau kuka.

Sosai nake mamakin Umma da ta kasance kakar Nadeeya da Bata nuna ta damu da neman da muke wa Nadeeya ba hasali ma tea Dana dafa Suka zubo ita da Hindatu da kwai suka dauko gwangwnin Madara Dana Milo suna Shirin hada shayi su sha

Waje nake so na sake yi Amma na tsinci kaina da nufar wajensu Sabida daga murmushi danaga.umma na min yasa nasan tana da masaniyar Inda yata take.


Agaban Umma naje na zub'e Ina "Umma Dan Allah na hadaki da Wanda ya halliceki ki gayamin Inda Nadeeya take Umma daga d'akina ta fito Kuma Kuna zaune anan ta fito daga d'akina Dan Allah Umma kimin komai idan ta Kama yau na hada kayana na bar gidanan wlh Zan hada Dan Allah ki dawomin da Nadeeya na tuba Umma Nadeeya bata Miki komai ba Ni na Miki Aunty Dan Allah Kuyimin Rai karku yiwa Yata komai"


Nace Ina k'ok'arin kamo hannun Hindatu

Adaidai lokacin da Naseer ya shigo da Sauri kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake

Turus yayi Agaban mu Yana yiwa Umma da Hindatu wani irin kallo da yaga kayan shayi a gabansu

Cikin wani irin murya ya fara magana Yana "Umma Anya ke Kika haifeni kuwa Umma Anya Gaskiya Abba da Baba Suka gayamin da sukace ke Kika haifeni Umma 'yata ce fa ta b'ata ake nemanta Umma jinina fa yata da ta kasance jika a gareki ita ake nema Umma Kika zauna ke da Wanan tsinaniyar zaku hada shayi ku Sha alamar ba Abunda ya shafeku Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma Dan da kina kaunata bazaki ringa min abinda kike min ba Zaki so farinciki na Umma mak'ota da masu wucewa ma suna tsyawa sabida su Tayani neman Yata amma ke kin zauna Zaki sha shayi wane irin kallo kike so a Miki Umma ga wayanda suka san ke Mahaifiyata ce Umma Koda baki hada jini Dani ba Bai Kamata ace mutum Mai Rai sukutum guda ya b'ata batare da kin nuna damuwarki ba Umma,Umma lamarinki ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro Umma insha Allahu Zan ga yata Kuma zan kawo karshen komai Dan Nagaji Umma"


Daga haka yayi ball da flask din gabansu ya shige daki ya canzo kayan jikinsa ya fito da Sauri hannunsa d'auke da mukullin motarsa da k'aramin passport din hoton Nadeeya da aka Mata lokacin da zaa Saka su a makaranta ya fice da sauri.

Ni kuwa na durk'ushe a wajen na cigaba da kuka na kasa yarda Wai Nadeeya ta b'ata yarinya da nayiwa wanka da hannuna ko wando babu.

Maganar da Umma keyi cikin huci yasa na tsayar da kukana Ina kallonta

"Yau ni Naseer ya ke d'agawa murya yake min ihu sabida yarsa ta Bata lailai Naseer yayi Nisa ba karamin asiriceshi wanan tsinananiyar tayi ba ba dai Dan Nadeeya kike wanan kukan ba ba Dan Nadeeya Naseer yamin ihu Ina mahaifiyarsa ba toh sai ku ganta nagani"


"Duk wannan Abun fa laifinki ne Hajara ke Kika bar yarinya nan ta zauna dashi har yanzu har ta juyar Masa da kwakwalwa ace yau sati biyu da auren mu ya kasa kallon Inda nake tsabar wanan kanjalalliyar ta asirice shi ki barwa Umma komai ta Miki maganin shegiya"


Ta ce tana jefomin harara
Umma kuwa tayi wani irin murmushi ta mik'e tana k'ok'arin shiga daki.

Da Sauri na rik'e kafarta na saki ihu Ina ta taimaka ta fitomin da yata wlh idan Naseer ne Zan rabu dashi a yau

Tureni tayi ta shige daki.

Zahira dake lab'e a bayan kofar dakina ta fito ganin Ina ta rusa kuka Ina Kiran sunan Allah Dana Nadeeya ba irin tunanin da ba darsu a Raina ba Kar dai su Umma kashemin Nadeeya sukayi.

Zahira Humaira ta mik'o min dake ta tsalla kuka daga ita har Minal ba Mai Kaya a jikinsu sai Zahira karbar Humaira nayi na sa Mata no-no a baki take ta karba na umarci Zahira ta d'auko wa Minal Kaya ita da Humaira.

Tana tashi Mmn Mannir ta shigo ita da wasu makotana wasu ma ban San su ba duk sun zo min jaje sai Kara tambayata suke Taya Nadeeya ta b'ata ban ma iya musu magana ba sai bani baki suke suna kwantar min da hankali akan za'a ganta an Kai cigiya gidajen radio har da tv dayake Naseer nada Abun hannu duk an raba musu passport din Nadeeya.

Ni dai har lokacin sai Naga kamar zanga Nadeeya ta fito daga d'aki.


Mmn Mannir kuwa Humaira ta karba daga hannuna ta goyata Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na daura alwala na fito na hau Kan Sallaya na tadda Sallah karatun Sallah ma da k'arfi na ringayi Ina kuka a Sujadda kuwa Haka na ringa rokon Allah ya Kare min yata a duk Inda take ta dawo gareni cikin koshin lafiya Ni nasan su Umma ne suka daukemin 'ya har tsawon wane lokacin Zan ringa irin wanan rayuwa a yau na gaji wlh na gaji ya zama Dole na dau mataki.

Ina iddarwa na fito nayi k'ofar gida Inda duk makotana suke tsaye duk Yan layin ban gansu ba sun tafi neman Nadeeya daidai da masu shaguna duk basu bud'e ba sabida mutuncinsu Amma ace uwar mijina ita Tana daka ko a jikinta.


Waje daya na samu na zauna Ina ta tunanin ganin ta Inda zanga Nadeeya ta b'ullo addua kuwa na fili Dana zuci Haka na ringa Yi.

Lukman da danladi Mai Kai su makaranta sun dawo gidan yafi a kirga Akan suji ko an ga Nadeeya Amma shiru ba a ganta ba ahaka har Yamma tayi babu Naseer babu dalilinsa.

Kuka nake sosai Ina rokon Allah ya karemin Nadeeya har yanzu na kasa yarda Wai daga fitowa Nadeeya wanka an nemeta an rasa.



Naseer kuwa kudi ya saki sosai ya bada cigiyar Nadeeya gidajen radio da unguwa unguwa har Inda baa yi tunanin zuwa ba Haka aka ringa neman Nadeeya da passport din hotonta Sallah ma Naseer ba a nutse yake Yi ba har kunyar ya cewa mutane daga wanka Nadeeya ta fito aka nemeta aka rasa sai kace wata Kaya.

Ahaka suka danganta neman Nadeeya kusufa kusufa lungu da sako kwaryar Kano baa ganta ba wajen Magriba Naseer da wasu Yan unguwarsu suka tsayar da motarsu Dan suyi sallah a wani unguwa kawo dayake unguwar Bata fiye cika ba a wanan lokacin Kamar daji ne sai a lokacin ake yankar fili ake ginawa.

Daya daga cikinsu ne ya nausa wajen daji dajin da yayi fitsari ya fito yayi alwala daga nesa dashi ya hango wani katon Rafi ruwa nata Dan gudu gashi wawakeke wata Yar karamar yarinya ta bada baya tana Dan jefa abu a ciki ba Kaya a jikinta.

Murza idonsa yayi ya sake murzawa idonsa duk da Bai ga fuskar yarinya ba sai yake ganin kamar Nadeeya Amma Dan ya gasgata zargin da yake ahaka ya ringa matsawa kusa da yarinya kafin a hankali yace "Nadeeya"

A hankali Nadeeya ta juyo idonta yayi jawur hancinta duk Majina kana gani kasan taci kuka ta gode Allah wajen a ruwan yake ma da alama baa fiye wucewa ta wajen ba

Ihu ya saka ganin Nadeeya na ganinsa ta fara k'ok'arin mik'ewa tana mik'a Masa hannu Dan Dama Mai kawo Mata d'auki take nema shi kuwa cikin zafin nama ya Isa wajenta ya tarota da Sauri Dan kiris ya rage ta fada ciki.

Wani irin ajiyar zuciya Nadeeya ta ringa saukewa tayi lamo a jikinsa jikinta yayi zafi zau.

Shima Salisun kamkameta yayi yayi wajen da suka Parker motarsu da har Naseer ya iddar da sallah ya gaji da jiransa.

Kamar a mafarki ya hango ya fito da Nadeeya rungume a kirjinsa Bai San lokacin da ya nufesu da Sauri Yana "Mai ya sameta? A Ina ka ganta"?

Yace Yana karbe Nadeeya daga hannunsa ya hau tattab'a jikinta Inda Nadeeya tana ganin Abbanta ta fashe da kuka tana Kara kamkame shi.

Naseer kamar ya maida ta cikinsa ya rungumeta Yana shafa jikinta


Salisu kuwa ya hau bashi labarin yanda ya ganta ya Kuma ringa Al ajabin yanda Nadeeya ta iya zuwa tunda Goron dutse zuwa Kawo idan ba mutum ne ya kawo ta Nan ba Taya zaayi tazo Nan

Naseer Bai iya Jan motar ba sai salisu ne yaja motar shi kuwa ya zauna daga bayan motar da dayan makocinsa suna ta mamakin Inda suka tsinto Nadeeya Naseer kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin kukan Nadeeya a kirjinsa Yana Jin wani irin suya a kirjinsa shi ba yaro bane yasan d'auke Nadeeya akayi Kuma ba wasu ne.suka d'auke.ta ba sai Mahaifiyarsa tunda yasan wacece ita.


Baiyi magana ba har suka iso gidan da mutane ke cike Suna jajanta b'atan Nadeeya.

Naeema kuwa taci kuka ta gode Allah tayi zaman dirshan a kasa Ana ta Bata baki


Tsayuwar motarsu yasa ta mik'e da sauri Inda Naseer shi.kuma ya bud'e motar ya fito rungume da Nadeeya

Mutane na ganin ta suka hau hamdala suna "Alhamdulillah Anga Nadeeya a Ina aka ganta"?

Sosai mutane Suka nuna farincikinsu da ganinta suka hau tambaya inda aka ganta.

Naeema kuwa da Sauri ta ture mutane ta karbi Nadeeya daga hannun Naseer tana sauke wani irin ajiyar zuciya.

Ta rungume Nadeeya Gam tana hamdala


Hajara da Hindatu ihun Murnar anga Nadeeya ne yasa Suka fito daga d'akin da Sauri suka lek'o ta saman bene cikin tsananin mamaki Dan bakin ruwa Suka kaita Kuma suna da tabbacin fad'awa zatayi ta mutu Amma ga mamakinsu Wai an ganta Kuma su sun San Inda suka kaita sai anyi dagaske xaa San wajen.


Wani irin ihu Hajara ta saka ta sauko daga Kan benen ta zub'e a kasa ta hau buburwa ta cire zaninta ta Yar ya rage daga ita sai Dan skirt sai kuka take Tana zubawa kanta kasa.


Mamaki ne ya rufe mutane suna kallonta tare da mamakin Mai ya kawo ihun nata ita da zatayi farinciki anga Nadeeya (wlh page dinan babu fiction ko daya a gaske Haka matar Nan tayi Dan bakin ciki an ga Nadeeya)


Ni kuwa ko kallonta banyi ba na rungume yata na haye sama

Naseer kuwa kamar kasa ta bud'e ya shige Dan kunyar yanda take ihu tana watsawa kanta kasa Wai Nan da Sunan Mahaifiyarsa ce wato gawan Nadeeya taso gani

Mutane kuwa da basu San Mai ke faruwa ba hakuri Suka hau bata suna ba kuka zatayi ba ta Godewa Allah da aka ga Nadeeya ba Kuma abinda ya sameta.

Naseer shima da Sauri ya hau saman bene Yana Jin kamar kirjinsa ya fad'o

Sai Hindatu ce ta sauko ta dauko mata zaninta ta mikar da ita suka koma ciki.

Da yawa ta basu mamakin abinda tayi sabida tunda aka fara neman Nadeeya Bata lek'o ba Amma abin mamaki ana ganinta ta fito tana ihun kuka Mai hakan ke nufi.
Wasu Kuma basu kawo komai ba sun dauka kukan farinciki take da ganin Nadeeya.


Ni kuwa Ina shiga ciki d'akina na wuce da Nadeeya na kullo k'ofar na kwantar da ita na fara duba jikinta Naga babu abinda ya sameta sai kafafunta dai da suka balain suntume sukayi budu bud' da kasa

Sai jikinta da yayi zafi sosai.

Bana rabo da ruwan zafi hakane yasa na hada ruwa Mai balain zafi na wanke Nadeeya tas na Kara zuba wani na hau dadanna Mata kafa sai danaga ya fara Sab'ewa sanan na dauko robbb na shafe Mata jikinta dadin wankar yasa take bacci ya d'auke ta tana ta sauke ajiyar zuciya Ni kuwa na zuba Mata Ido hawaye na sauko min ko a Ina su Naseer suka ganta.

Naseer kuwa a Palo ya zauna ya rik'e kansa sabida azabar ciwo da tunanin halin mahaifiyarsa ahaka su Hajara suka hawo sama tana ta kuka

Suna dab da wuce Naseer


Naseer ya dago Yana "Umma ba Haka Kika so ba ko?kin so ace gawar Nadeeya na shigo dashi gidanan Umma Mai na Miki Haka Dan Allah Dan annabi Umma Mai na Miki Dan Allah Dan annabi ki gayamin na nemi yafiyarki Umma"


Naseer yace Yana durk'usawa Akan gwiwar sa kukan dayake d'annewa ya kwace Masa.


Hajaran Bata ce komai ba ta Shige d'akinta tana Jin kanta na ciwo sabida a rayuwarta Bata da burin daya wuce taga Naeema ckin bakin ciki a Rayuwa tunda ta kasa rabata da Naseer gwara ta Taba abinda tasan sune ranta Dan taso Zahira ta d'auke Dan ta lura itace Mafi soyuwa a wajen Naeema sai Zahira bata futo ba Nadeeya ta fito sai gashi cikin sauki wai har anga Nadeeya bama ta mutu ba da ranta lailai Naeema tabbas akwai abinda ta taka da Bata iya cin Galaba Akan ta.

Har wani zazzabin bakin ciki tayi


Naseer shima halin mahaifiyarsa da matsanacin tunani sai daya saka Masa zazzabi

Ni kuwa Ina daga d'akina Ina Jin duk abinda Naseer ke cewa Umma kukan da Naseer keyi ya tab'ani sosai hakane yasa na Sha alwashin kawo karshen wanan matsalar da muke ciki.

A Daren ranar duk mu ukun babu wand yayi baccin kirki Dan Naseer zazzabi halin mahaifiyarsa ya hau Yi ko shigowa d'akin baiyi ba a palon yayi kwanciyarsa ko sallah daya Saba yi daddare ma a ranar baiyi ba Ni Kuma hanyar da zata bille Dani ya hanani bacci ita Kuma Umma bakin ciki. Duk Abubuwan da takemin Ina tsallakewa gashi shugabarsu tayi fushi tace zata kwace komai daga hannunta tunda Naeema tana neman fin karfinta.

Washegari Nadeeya ta tashi fes ba wanan kumburin ahaka na had'asu na musu wanka na rufo kofata na nufi kitchen Dan na Dora Mana abinci banyi tunanin shiryasu su tafi makaranta ba Naseer ma ban ganshi a palon ba Dan tunda ya fice da asuba bana Jin ya sake dawowa sosai naji Ina tausayinsa.

Daga Umma har Hindatu banji motsinsu ba har na Gama Abunda nake na ajiye musu nasu a Palo na Kai Mana namu daki Dana Naseer.

Dan nayi alkawarin har na cimma burina bazan Kara Shiga dakinsu ba.

A faranti daya muka ci Abinci da yayana Sansu na ratsani Ina kwarara musu addua a Zuciyata.

A hankali Kuma Ina tambayar Nadeeya yanda ta ba ce bamu ganta ba Bata iya min magana ba Dan tana da Dan nauyin baki.

Har Minal ta Dan fita baki.

Wajen karfe goma na safe na fito daga d'akina bayan na kulle k'ofar dakina har lokacin Naseer Bai dawo ba Kuma banji motsinsu Umma ba Naseer nafi damuwa nasan halin da yake ciki ba Umma ba hakane yasa nayi waje.

Ina su lukman suka hau gaisheni suna tambayar Nadeeya Ni kuwa nace Tana Nan lafiya Lau daga Haka na wuce gidan mmn Mannir Dan zuwa yanzu banida dai Sama da ita bayan Naseer dan naji Dadin yanda ta nunamin damuwarta jiya tamkar yar uwa ta Haka nake ganinta.


Banyi tunanin Zan sameta a gida ba Dan na d'auka taje makaranta amma Ina zuwa na sameta taji dadin ganina anan muka gaisa taso ta tada maganar abinda ya faru tsakaninta da Umma har ta Dan sakomin zancen tana zargin ita ta d'au Nadeeya Ni kuwa na Kau da zancen na hau Gaya Mata abinda ke tafe dani da taimakon danake so tamin Dan Nagaji da irin wanan rayuwar da muke nida yayana Kuma idan na biyewa Naseer Haka zamuyi ta zama muna cutuwa.

Sai data Yi Dan Jim kafin tace zata taimaka min ta hau tsaramin yanda zamuyi take naji dadin shawararta Inda ta tsaramin duk yanda zamuyi Amma fa tana tausayin Naseer.

Murmushi kawai na nata Dan Mai daki shi yasan Inda yake Masa yoyo.

Sallama na Mata akan Zan dawo anjima

Ina koma wa gida Naga Naseer ya dawo idonsa ya fada sosai yayi wani sanyi kalau kamar mara lafiya Bai cemin daga Ina nake ba na Shiga d'aki na dauko masa abincinsa Ina k'ok'arin ajiyew yace min azumi yake bance komai ba na dauke abincin na mayar kitchen na fara k'ok'arin Dora Mana abinci Rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login