Showing 54001 words to 57000 words out of 180103 words
so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d'auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b'ace sai da yaga zahiri.
Sosai.ya Kara k'arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida.
Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d'akin ya shareta
Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b'aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab'a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub'e a kasa suna k'ok'arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d'akinsu ta d'auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu.
Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba
Kafin ma suyi magana har ta b'ace.
Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad'an Bata San abinda zai rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k'arfin.
Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba sai da aka Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci.
Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik'e a firgice
Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik'e yayi band'akin palon ya d'aura alwala ya fito.
Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan.
A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa.
Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta.
"Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak'antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka"
"Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b'ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b'ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah "
"Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b'ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi
Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon.
"Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik'e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure.
Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba"
"Naseer a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta saka ka fice daga hayyacinka"
Naseer tashi yayi ya Shiga d'aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad'a kamar zata Ari baki.
Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan
Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta
Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa
Yana dawowa kuwa gidan ya d'auko Quraninsa a Palo ya hau karatun Qurani Dan sosai yake so su Umma su ma su bashi space ya sarara Amma ga mamakinsa ba Wanda ya tashi a cikinsu ya gudu kamar yanda suka Saba.
Sosai kansa ya daure da mamaki Hajara kuwa sai jefa Masa harara take sai daya Kai Aya ya mik'e zai Shiga d'aki tace "wato k'arfi da yaji kake so mu bar gidanan babu Inda zamuje Naseeru muna Nan tare da.kai zanyi maganin taurin kanka
A Haka rayuwa ta kasancewa Naseer da Naeema.
Acan yake yin komai kwana ne kawai baya yi a gidan shima da an kwana biyu zai cewa Hajara tafiya ta taso Masa ahaka zaije yayi sati ko sati biyu a gidan Naeema sosai suke taka tsantsan Dan Kar Hajara ta gano suna tare.
Duk da lokacin sosai ta matsa Masa da zancen aure har mamaki take yanda Naseer din yake rayuwarsa batare da ya damu ba gashi ba komai na tsafi da zasu iya gano komai a game dashi Koda akwai yanzu idan Suka so ganin Naeema ta mudubi basa iya ganinta har mamaki suke Nan kuwa basu San layyar data saka a kanta bane.ya hanasu ganinta shugabarsu ma sai cewa.tayi kila ma Naeema mutuwa tayi shiyasa basa ganinta
Naeema sosai Jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna Mata har ta ringa tunanin duk wanan lokacin Mai yasa dabaran hakan Bai fad'o musu ba.
Naseer shima sosai ya samu kwanciyar hankali sai zai je gidansa da mahaifiyarsa take ciki yake d'auko wata fuskar ya aza idan yaso ma tsokano Hajara idan tana Masa zancen aure shi kuwa sai yace Mata Shi bazai yi aure ba sai Naeeema ta dawo anan fa Hajara xata hayayyako kamar zata masa.baki tayi ta cewa Naeema ai ta mutu ko ba mutuwa tayi ba Bata isa ta dawo gidansa ba.
Ahaka har sai da suka kwashi watani shidda cas watarana ya dawo daga gidan Naeema.
A Palo ya tarar da Hajara ta balain had'e Rai Safiyya Kuma tana zaune a gefenta.
Gaishe ta yayi ya mik'e zai wuce d'akinsa Hajara ta dawo dashi ya zauna.
Ta fara magana cikin b'acin rai "Naseer kana so kaga b'acin Rai na ko kana so sai na balain Bata maka kafin mu shirya dakai ko ka Nemo matar aure ko na nemo maka da kaina na gaji da ganin ka Haka ko na nemo maka matar auren
Sai ka wulakanta ta kamar yanda ka wulakanta Hindatu na baka Nan da sati biyu ka nemo matar aure idan ba Haka ba wlh da kaina Zan Nemo maka Kuma baka Isa ka wulakanta ta ba"
"Tom Umma Zan nema Ina ta ganinsu babu wacce tamin ne Amma insha Allahu zanyi kokari na nema din"
Daga Haka ya mik'e ya shige dakinsa
Fada Hajara ta ringa yi bayan ya Shiga d'akin Saffiya kuwa ta tab'a ta tana "Umma Anya Yaya baya tare da Naeema kuwa "?
Wani irin hantsulowa Hajara tayi daga Kan kujeran ta dafe kirjin ta tana "Mai kikace Suna tare fa kikace Mai kika gani kikace Haka"?
"Umma kema kinsan yanda ya Naseer yake San Naeema yake Kuma San yaransa banajin da basa tare zai samu kwanciyar hankali Haka ke bakiga yanda.yaya ya danyi kib'a Yana sheki ba wlh kila Raina Mana hankali yake"?
"Zan Miki baki wlh Safiyya karki soma min wanan fatan idan suna tare a Ina ya ajiyeta Naga dai gida yake zuwa ya kwana sai idan tafiya ta Kama shi yake kin kwana a gida kin manta bama.ganinta a mudubi shugaba.kuma data duba da kanta tace kila hatsari sukayi suka mutu"
"Hmmm toh shikenan tunda Kikace Haka Amma nidai gani nake da Yaya baya tare da Naeema bzaki kansa fes Haka ba"
Mik'ewa Hajara tayi da Sauri tana "idan kuwa hakane Safiya na gano rainamin hankali sukayi wlh sai nayi wa Naseer baki wlh sai na kashe Naeema da hannuna Kinga Banga ma ta zama ba ya zama Dole mu koma Calabar muje mu bawa Shugaba hakuri ko Dan na ringa sanin abubuwa da ke wakana wlh tunda ta kwace komai namu banajin dadi Banga ta zama ba ya zama Dole mu d'auki hanya gobe"
Sosai hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba.
Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad'an ya Kara siyan fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari.
Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa.
A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema.
A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji.
Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu'a duk da Bata tab'a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar.
Hajara kuwa dak'yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi.
Satinsu uku a Calabar suka dawo.
Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo.
Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba.
Ahaka ya b'oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa.
Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali.
Yana tashi ta kalli Safiyya tana "Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki"
Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba
Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada.
A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan.
Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa.
Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad'uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har Naseer ya tafi.
Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba
Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran.
Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira
Zumbur ta mik'e tsaye
Tace "Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema"
Yaraf Hajara ta zub'e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik'ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me"?
Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d'auko ta zata hada Masa kudinsa.
Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada.
Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema.
Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu.
Ina zaune naji Ana buga gate da balain k'arfi mik'ewa nayi cikin fad'uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina.
Inna zuwaira ce ta bud'e gidan tana bud'e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya.
Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi.......
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 21*
Kirjina bugawa yake bakina d'auke da sallati ganin Umma tamkar ganin malaikan da zai zaremin Raine bamu tab'a had'a inuwa da Umma Bata nemi cutar Dani ba har ya Kai indai zanyi Ido biyu da ita tsigar jikina sai ya tashi.
Abinda ya bani mamaki irin tsoron danake ji idan naganta banji irin Wanan tsoron ba duk da dai a tsoracn nake.
Kallona kawai take daga bakin kofa jikinta na wani irin rawa Zan iya cewa ban taba ganin ta a cikin wanan yanayin ba wani irin Mugun tsanata nake hangowa a idonta da ace zanje hannunta Ni nasan sai ta rabani da numfashina.
Hakane yasa na tsaya akan kafafuna sosai Ina adduoi a Zuciyata
Saffiya ce ta shigo palon tana ta duramin zagi tana tsinemin sai zagin iyayena take
Inna zuwaira kuwa sai cewa take daga Ina kuke wa kuke nema"?
"Shegiya Mayya nataciya tsinaniya Banda maita ana dolene? munce bama sanki Umma tace Bata sanki ki rabar Mata da D'a Mana shegiya akuya Mai gindin haihuwa kinsamu waje sai haihuwa kike kamar akuya ko akuya ma na Dan bada tazara Banda ke duduu yaushe Kika haifi wancan bak'ar yar taki"
"Kema ki zuciya ki haifi naki Safiyya"
Na tsinci kaina da fad'a Nima cikin mamakin kaina
"Nace ki zuciya kema ki zama akuya ki haifi naki ba ki sakoni agaba ba Saffiya Ni ba Mayya bace Yayanki ne Mayya ya Kuma nace min kije ki nemi miji kiyi aure ki samu ki haihu Safiyya bibiyata da sharri ba naki bane Dan Allah shi ya halliceni rayuwa da Kika ga inayi shi ya tsaramin yayan da kike magana shi ya bani Kuma iya yayan da ya hukunta Zan samu shi Zan Haifa Safiyya babu yanda zakiyi Dani"
Daga Saffiya har Umma wani irin kallon mamaki suke min Safiyya kuwa tuni idonta ya kad'a yayi Ja ta nuna kanta tana "Ni kike fadawa maganganun nan Naeema"?
Maganar mmn Mannir na tuna "duk ranar da Kika kwatar wa kanki yanci zakiyi mamaki wlh sai sun fara shakarki suna tunanin kila akwai abinda Kika tak'a
"Eee ke nake fadawa maganganun nan ko Haka zai saka ki zuciya ki kyalleni Kun takura min Kun sakoni agaba ku kyalleni Dan Allah"
Cikin wani irin zafin Nama Safiyya ta daga hannunta zata kawomin Mari.
Nima cikin zafin nama na tare Marin tare da yarfar da hannunta duk wani Abu da suka Dade suna min na dawomin cikin zuciyata da zata lura da kyau zata ga yanda jikina ke rawa sabida tsoro Amma abinda sukemin ya isheni rayuwata a hannun Allah take iya rayuwar da Allah ya yarjemin shi zanyi na tafi na Kai matakin da na gaji da d'aukar abinda sukemin.
"Karki sake ki Kara yunk'urin kawo hannunki jikina wlh bazan dauka ba abaya na biku na rokeku na shanye duk abinda kuka min Amma yanzu Kun kaini bango Nagaji ku sakarmin Mara nayi fitsari Safiyya kuje ku nemi miji kuyi aure ya zakiji idan kikayi aure kanwar mijinki da mahaifiyarsa na musguna Miki Haka ya Zaki ji Dan Allah ku kyalleni Allah yayi Naseer mijina ne duk Inda kuka Kai da kuga Kun rabamu idan Allah Bai nufa ba wlh babu yanda zakuyi"
Hannu ta Kara kawowa jikina na kauce da Sauri Kafin na ankara ta kawomin shak'a wuyana
"Har Ni kike gayawa maganganu har wuyanki ya Isa yanka Naeema Mai kike takama dashi?
Inna zuwaira ce ta bambare hannunta daga wuyana dayake tana da tsayi ta wancakalar da hannun Safiyya tare da kwasheta da Mari
"Sai na tsine Miki Safiyya idan har baki Gama da yarinya Nan ba Kika bari na karaso da kaina"
Umma tace tana wani irin hucci
Inna zuwaira ce ta tare wawuran da Safiyya taso kawomin ta Kara kwasheta da Mari tana "ke Wai wacce irin Mara tarbiyya yarinya ce ke ya zaku shigowa mutane gida kice Zaki Kama matar gida da k'ok'awa"
"Kina Wasa da wuta idan baki cire kanki a maganarmu ba Marin da kikamin Kuma wlh sai kinji a jikinki ki matsa min tsohuwa babu ruwanki a maganarmu"
"Ta Allah ba Taki ba yarinya Nafu karfin sharrinki ba abinda zanji a jikina Naga alamar baki da tarbiyya ku juya ki koma daga inda kuka fito Dan bazan Bari hannunki ya tab'a jikin hajiya ba Dan Haka"
Safiyya Bata Bari ta karasa ba ta d'auke Inna zuwaira da Mari kafin kace me sun fara wani irin k'ok'awa mamakin karfin halin Safiyya data iya kaiwa Inna zuwaira duka yasa jikina ya fara rawa kafin kace me ta hau ruwan cikin Inna zuwaira ta hau Kai Mata duka ko ta Ina
Hankalina a tashe nayi kansu na fara k'ok'arin daga Safiyya daga jikin inna zuwaira Ina sallati