Showing 63001 words to 66000 words out of 180103 words
halin daya ganshi yasa ya taso ya karbi mukullin motar yaja suka nufi sharada.
Tijjani sai bashi baki yake Yana rantsuwar Bazai dau abinda umma ke Masa ba shi idan ma Umma zata takura masa.wlh bar Mata garin zaiyi ya siyar da komai nasa ya koma wani garin ya daina wani damun kansa ya shareta.
Naseer Bai iya magana ba har Suka iso gidan Tijjani ya sauka ya Masa Sallama akan zai Kara lekoshi idan ya samu lokaci Dan ya kwantarwa da Naseer hankali yace Masa idan Umma ta sauko zai Bata baki.
Godiya Naseer ya Masa bayan tafiyar tijjani sai daya Dade a mota tunanin Asarar dayayi ya balain tsaya Masa a Rai.
Yama rasa tunanin da zaiyi.
Jiki ba kwari ya fito daga motar ya nufi cikin gidan.
A bakin kofar palon ya tsaya Yana kallon Naeema data zauna a 3 seater da uban akwatuna taci hijab ga su Zahira suma a Gefen ta Suma ta shiryasu
Kallonta kawai yake Yana Jin wani iri a zuciyarsa da alama Naeema bama ta San da shigowar shi ba sabida zurfin da tayi a tunani lokaci lokaci takan share hawayen da ya zubo Mata da hijabin jikinta.
Tunda Naseer Suka fita da Tijjani nake Jin fad'uwar gaba zuciyata a balain cunkushe fargabar yanda Umma zata yiwa Naseer ya cike min zuciya ni dai nasan idan Naseer Yana San yafiyar Umma sai ya sakeni Dan nasan indai ya sakeni taga shaida zata iya yafe Masa
Hakane yasa ban tsaya yaudarar kaina ko sai Naseer ya dawo naji yanda sukayi ba Dan nasan Idan dai Yana da hankali dole yabi umarnin Umma ya sakeni.
Kayanmu na hada Mana tsaf nida Yarana Dan bazan tab'a iya barin yarana da Naseer ba Dan nasan Umma ko Dan ta galazamin zata so na bar yaran sabida taci zalinsu.
Zan tsugunna na roki Naseer ya barni na tafi dasu garinmu na tashi Yan hayan da nake tunanin kila.mai unguwa ya zuba a gidanmu nayi zamana acan na fara neman kudin da Zan kula da yarana duk da nasan Naseer bazai barmu Haka ba zai bamu wani Abu Abu dayane yake San karyamin komai tausayin Naseer ko ya zaiyi idan ya waiga yaga bana Nan yaransa ma.haka Naseer.mutum.ne shi Mai balain San Yara Dan wani zubin idan abin ya motsa Masa d'akinsa yake tafiya da su su kwanta a gadonsa dayafi nawa girma
Shi Kuma ya kwanta a doguwar kujera Ni kuwa idan Naga Haka Akan Dole Zan bisu haka na shimfida bargo na kwanta a kasa yayi ta tsokanata Yana cemin matsoraciya idan na Isa na kwana Ni kadai Mana ba sai na biyo su ba
Idan Kuma Yan tsokanar na kansa idan yaran basuyi bacci ba zaice duk su tashi zaune dashi Dani wane Suka fiso
Hade Rai nakeyi Dan nasan Zahira kadai ce take cewa ni tafiso su kuwa sauran duk shi suke cewa sabida yakan yaudaresu da alewa ko yayi ta musu signa da ido akan zai siyo musu kayan Wasa sabida yarinta da gudu suke cewa shi suke so Zahira kuwa komai zai Bata sai tace ita tafi San Umma hararta zaiyi tayi idan tace.haka Wanda a karshe sai ya koreta daga Kan gadon akan tazo wajena tunda tafiso na Ni kuwa sai nayita Masa gwalo Ina harararsu Nadeeya zaman mu gwanin shaawa da bamuda matsala da Umma Naseer mutum ne shi da nake fatan ya zama miji a gareni har a Aljanna sai dai k'arfi da yaji Umma kesan rabamu.
Tunanin Nan danayi na irin Rayuwar Dana shimfida da mijina da yayana cikin so da Kaunar juna yasa kukan danake dannewa ya k'wacemin na Shigar da fuskata cikin hijabi na naci kukana na gode Allah kukan Zahira Dana fara ji kasa kasa yasa na Dago
Na share hawayena anan idona ya fada Kan Naseer daya zubamin Ido cikin jajjayen idonsa Yana min wani irin kallo da na kasa ganewa.
Mik'ewa nayi na dauki Raheema dake gefena na sab'ata a kafadata daga yanda Naga idon Naseer ya kad'a yayi ja Ni nasan ya sakeni ya kasa shigowa ne sabida Ni.
Umarni na bawa su Zahira akan su tashi mu tafi
Dan so nake idan naje waje na samo Mai mota yazo har k'ofar Gida na kwashi akwatunan kayanmu
Kukan dake San k'wacemin nake ta dannewa
Na nufi wajen da Naseer da har lokacin yakemin wani irin kallo.
Cikin muryar kuka na mik'a Masa hannu Ina ya bani takarda Zan tafi banasan nayi Rana
Murmushiin dayafi kuka ciwo yamin ya matsa daga bakin kofa cikin wani irin murya ya hau magana Yana "Zaki iya tafiya ke kadai ba sai kin tafarmin da yarana ba Naeema baki zabi ki gujeni ba sai da masifa ta tunkaroni Naeema baki nemi rabuwa Dani ba sai a yanzu danake cikin tsaka Mai wuya ?baki nemi na baki takarda ba sai a yanzu da nake neman Wanda Zan Dora kaina a kafadarsa ya rarrasheni shine a yau da Kika ga nayi asarar dukiyata a yau Zaki hada kayanki ki tafi Naeema"
Bansan lokacin da na fashe da wani irin kukan bakin cikin fassarar da Naseer yamin ba na hau magana numfashina Kamar ya d'auke
"Haba Naseer Mai yasa zaka min wanann mummunan Fassarar wlh badan Haka na had'a kayana ba Umma tace indai kana so ta yafe maka sai ka sakeni Kuma fitar da kayi Dan kaje ka nemi yafiyarta ne hakane yasa na hada kayana Naseer wlh ba dan komai haba Naseer bazan tab'a guje maka Dan ka tsinci kanka a cikin wani Hali ba"
Bai cemin komai ba da ga kallon dayake min ya nuna ko kad'an maganata Bata shigeshi ba girgiza kansa kawai yayi ya nufi d'akinsa ya shige Ni kuwa na zub'e a kasa na fashe da kuka Mai ciwo.
Sai danaga yarana suma suna ta kukan na daure na share hawayena na koma Kan kujera na zauna.
Abincin Rana ma banyi ba Sabida tashin hankali Cabin biscuit kawai na rabawa yaran Haka nayita Zama a palon Ina tunanin Naseer zai fito ya tafi massallaci yyi sallah Magriba Amma shiru Bai fito ba.
Nadeeya da Bata da juriyar yunwa ita ta fara min kukan yunwa hakane yasa na tashi na Shiga kitchen na dafa musu shinkafa tunda Ina da Miya na sati nakeyi.
Gabadaya na rasa Mai kemin dadi ga wani irin tsoron gidan da nakeyi sai Naga kamar gidan zai iya kamawa da wuta na rasa Mai ke sakamin wanan tunanin
Har karfe goma na dare Naseer Bai fito ba na buga Masa ko gezau baiyi ba har kuka na Masa Ina Masa rantsuwar ba Dan ya Shiga wani Hali zan tafi ba Amma duk da Haka Bai bud'e k'ofar ba.
Da farko na dauka ko wani abune ya same shi sai danaji muryarsa Yana karatun Qurani hankalina ya kwanta nayiwa yarana shimfida a d'akina naje na kwantar dasu.
Na buga tagumi Ina tunanin halin da muka tsinci kanmu a ciki dayake fashin sallah nake hakane yasa banyi sallah ba surorin Dana haddace a kaina kawai na ringa karantawa ko zanji sanyi a Raina.
Bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba.
A cikin baccina na fara mafarkin Wai shagunan Naseer na Sabon gari Wai Yana ta konewa Ana rik'e Naseer Wai zai Shiga ciki shagon daya ragewa Naseer kenan Umma Wai ita Kuma tana daga nesa tana ta Mana dariya tana kad'an muka gani bamu ga komai ba"
A firgice na tashi da sallati jikina na balain rawa duk na hada zufa sai waige waige nake ganin ba wuta dake ci a d'akin yasa na fita da Sauri na duba Palo da kitchen Naga ba komai har store da d'akinsu Zahira.
Muryar Naseer dake ta karatun Qurani dayake dare yayi muryarsa sosai yake fita daga muryarsa kawai zaka San Yana cikin damuwa.
Bakin kofar naje.na tsaya nayita Kiran sunansa Amma babu alamar zai saurareni a Haka na hakura na koma d'akina Ina tunanin mafarkin da.nayi hankalina na Kara tashi bansan lokacin Dana daga hannu na fara rokon Allah Ina "Ya Allah ka Mana maganin masifar daya tunkaromu ya Allah ka dubemu da idon rahama ka tsayar Mana da Wanan masifa ya Allah Kaine masanin Sirrin sake bayyane da b'oye bamu San komai ba ya Allah mun yarda Kaine Mai bayarwa Mai Kuma karba a duk lokacin daya so ya rabbi ka bamu ikon cinye wanann jarrabawa ka bawa mijina ikon cinye wanan jarrabawa ka Kare Mana shagunan da suke rage mana ya hayyu ya qayyum"
Bansan Mai yake sani tsoro da fargaba ba Ina tsoron wani Abu ya Samu shaguna ukun daya ragewa Naseer.
Ina Nan zaune bacci ya Kara kwasheni cike da.mafarkai marasa.dadi.
Bani na farka na sai da gari ya waye.
Kukan Raheema ne ma ya tasheni.
Zumbur na mike nayi waje Dan na makara k'ofar Naseer danagani a bud'e ne yasa na shiga ciki Amma baya ciki alamar ya fita banji dadin yanda Naseer yamin ba ya kamata ace yafi kowa sanin abinda zanyi da Wanda bazanyi ba.
Ahaka na Shiga kitchen na samawa yarana abinda zasu ci da abinda zasu tafi dashi.
Zahira kuwa har ta Tayani shirya Minal da Humaira Nadeeya itama ta iya shirya kanta.
Ganin babu Mai Kai su makarantar yasa na saka hijabina na dauki naira Ashirin na rufe gidan na tare Mana taxi ya Kai mu har makarantar sai Dana ga shigarsu makarantar na Kara hawa taxi na dawo.
Na sauke Raheema Dana goyata na fara aikina gyara gidan zuciyata kuwa na wajen Naseer.
Naseer kuwa daga Massallaci sabon gari ya nufa jikinsa duk a mace jiya kwana yayi Yana addua Akan Allah ya Kare Masa shaguna ukun da suka rage Masa zuciyarsa kuwa sosai tayi nauyi sabida halin daya ke ciki Haka kawai yake Jin Naeema so take ta rabu dashi Sabida ifitilai data fada Masa alhalin duk ma halin da ya tsinci kansa a ciki Sabida kin sakinta da yayi ne badan Allah ya bashi dangana ba da zuciyarsa na iya bugawa ya rasa yanda zaiyi Umma ta sauko ta yafe mishi.
Sabida Kar ma wani tsautsayi ya gifta duk sauke layin NEPA yayi daga shagunansa ya Kuma gayawa yaran shagonsa su ringa kula da shagon nasa sosai.
Yau ma Bai hau motar tasa ba taxi ya hau Haka.kawai.ma.yake tsoron Hawa motar tasa.
Wajen karfe daya na Shiga kitchen Dan na Dora Mana abincin Rana Dan karfe biyu yarana ke dawowa daga makaranta .
Da yake na gama komai Zama nayi a palon Raheema na d'aga gefena tana bacci Nima sai na Dan kishigida bansan lokacin da bacci Mai nauyi ya d'aukeni ba.
A cikin baccin nawa na fara mafarkin kitchen Dina ya Kama da wuta har ya fara cin ceiling din Palo.
Sai ihu nake inaso na tashi na dau Raheema mu gudu Amma na kasa.
A Haka Wai Naga Mahaifiyata ta shigo palon ta tsaya a bakin kofa Tana "Tashi Naeema so ake wuta ta Kama gidan kina ciki ki tashi nace ki tashi Naeema"
A firgice na tashi idona cike da bacci wutan dake ci a kitchen Dina ne yasa na wartsake na rarumi raheema Ina ihu tare da yin waje da gudu Ina ihun neman taimako.
Cikin Ikon Allah akwai Samarin dake gini a Gefen gidanmu da Sauri suka Shiga gidana da bokitan ruwa suka Yi ta watsawa ni kuwa sai ihu nake jikina na rawa.
Suna watsa ruwan dayake suna da yawa cikin Ikon Allah wutar ta mutu duk da sun kashe wutan kasa Shiga nayi gidan nayita tsoro sai a gidan mak'ota na zauna har yarana Suka taso suka sameni a gaskiya ya zama Dole mu bar gidanan sau.uku kenan gidanan na neman yin gobara.
Ahaka muka zauna har sai da Naseer ya dawo.
Tun Kan ma ya Shiga cikin gidan aka hau Masa jaje Mai gidan mak'otan da muka shiga ne yacemin Naseer ya dawo.
Da saurina muka fito daga gidan muka Shiga gidan mu Inda na tada Naseer a tsaye a tsakiyar palon Yana kallon yanda kitchen din yayi bakikirin har k'ofar kitchen din sabida konewar da yayi Ni kuwa cikin kuka na fara magana Ina "Naseer ya zama Dole mu bar gidanan wlh tsoro nakeji sau uku kenan muna neman yn gobara Ina yawan mafarki Ina tsoron muna ciki da tsakar dare wuta ta tashi Dan Allah Naseer mu bar gidanan ko haya ka Kama Mana"
"Naeema ki daina Mana baki insha Allahu babu abinda zai Samu gidana idan bazaki Fadi alheri ba kiyi shiru Kuma Ni nasan duk sakacinki ne kila Abu Kika dora Kika manta dashi har gobara ya tashi ta Inda Naseer ke shiga ba ta Nan yake shiga ba
Nidai shiru na Masa har ya Gama fadansa
Tunda nake da Naseer bamu tab'a samun Sab'ani Mai tsayin wannan ba ahaka mukayi ta zama cike da fargaba yanzu kuwa ba karamin taka tsantsan nakeyi ba idan na Dora Abu akan wuta Zan iya cewa da Ido daya nake bacci
Sabida fargaba
Dak'yar na samu Naseer ya sauko daga fushin da ya hau.ahaka har muka samu wata biyu da gobarar da mukayi na shagonsa da gidansa.
Hajaraa ke zaune a palonta Safiyya da Tijjani suna ta Bata baki akan ta yafewa Naseer
Bata kulasu ba ta bawa banza ajiyarsu
Tijjani kuwa ganin Haka ya mik'e Yana zai tafi sai da safe
Umma.kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata Dubu ukun da ta tambayeshi.bata San iskanci ahaka tun baiyi aure ba yake neman ya ringa hanata kudi.
Tijjani kuwa hannu ya zura a Aljihu ya kirga Dubu daya Yana "Sai dai kiyi hakuri da wanan wlh hidima ce a gabana badan kin dage kinyi fushi da Naseer ba da ko Dubu goma Kika tambayeshi zai baki"
Tsaki tayi.ta fusge kudin daga hannunsa tana ya fice Mata daga gida
Shi kuwa yayi waje Yana dariya ya rasa Gane wane irin haline da Mahaifiyarsu.
Suna Nan a zaune har Sha biyun dare
Safiyya ta sako Jan doguwar rigarta
Hajara ma ta saka nata.
Safiyya na k'ok'arin yiwa Hajara magana kawai suka ga kitchen din gidan na ci da wuta kafin su ankara har wuta ta fara cin Ceiling din kitchen din .
Ihu Safiyya ga saka tayi waje.
Umma.kuwa da taso tsayawa yanda wutan ya Kama ko'ina gadan gadan yasa itama tayi waje tana mamakin Mai ya haddasa Mata gobarar Nan toh Mai hakan ke nufi.
Tana ji tana gani wutan ta cinye duka.gidan har da mudubinta a ciki sosai hankalinta ya tashi da konewar gidan nasu.
Tsirarun mutane ne suka ringa fitowa suna Mata jaje.
Safiyya kuwa cewa take "Umma Kinga abinda nake Gaya miki ko idonki ya rufe kina San ganin bayan Yaya Naseer kina so kiga ya Shiga ifitilai alhalinn kin manta da kudinsa Kika siyi gidan toh idan ma.arzkinsa konasu kikayi toh gashi Nan har gidan da Kika siya da kudinsa ya kone
Umma Bata iya cewa komai ba ahaka har gari ya Dan fara wayewa makotansu sai ce musu suke su shigo daga ciki gidansu Amma fir Umma Taki kallon gidan kawai take daya ruguje katakwaye naci.
Wajen karfe shidda na safe Tijjani ya taho wajensu a guje kafa ba takalmi duk ya hargitse hajara kuwa ta d'auka labarin konewar gidanta ne.ya je.masa sai dai kalmar daya fito daga bakinsa ne ya kusa sata suman wucen gadi
Agabnta Tijjani ya zub'e Yana "Umma shaguna na duk sun kone haka kawai wuta ta tashi da tsakar dare na Shiga uku Umma komai nawa Yana cikin shagon.
Ko biyar ban tsira dashi ba Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Tijjani yace Yana hawaye.
Safiyya kuwa ta daka tsalle cikin tashin hankali tana asirinmu ya tonu Umma kin jawo Mana.........
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 25*
Wani irin fusga Hajara tayiwa Tijjani cikin tashin hankali tana "Kana da hankali kuwa ko mafarki kake tayaya shagonka zasu Kama da wuta abinda ya rage mana kenan fa da Kai na dogara fa na Shiga uku Ni Hajara Mai ke Shirin faruwa Dani Banda Tijjani fa nace"
"Kikace me Umma zargina ya tabbata Umma wlh kina da hannu a konewar shagon Yaya Naseer da gidansa da
motarsa Umma
,Umma sai danace Miki karkiyi Haka Naeema ce ta Miki laifi ba Yaya Naseer ba Umma karki ce min duk dukiyar Yaya Kika k'ona Ni nasan tunda Kika fara min boye boye nasan akwai abinda kike kulawa toh ga irinta Nan idan ma.da Yaya Tijjani kika dogara toh shima shagunansa ya kone tunda Yaya Naseer ne ya basa kudin"
Hannu Hajara ta D'ora akanta tayi zaman dirshan akasa.
Tijjani kuwa cikin rashin fahimta ya kalli Safiyya Yana "Bangane ba Wai Mai kike nufi ne Umma ce tayi wani Abu Dan arzkiin Yaya Naseer ya k'one ko me"?
Hajara ido ta hau kiftawa Safiyya.
Safiyya dake cike da balain haushin Hajara kau da.kanta tayi ta hau bawa Tijjani labarin duk abinda ya faru ta Kara da "tun Akan hanya nake Bata hakuri tana rantsemin sai Naseer ya talauce ya tsiyace yyi bara Naga dai idan ya talauce ya tsiyace muma sai ya shafemu data ga alamar bana goyon bayanta shine ta daina min maganar Ni dai daga abinda ya faru wlh nasan Umma ce silar komai.ta Kona arzkin Yaya Naseer a kungiya"
"Wane kungiya.kuma Mai nake ji Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Ashe dai maganganun da ake Yi akanku gaske ne kenan Safiyya?
Safiyya sai a lokacin ta tuna Tijjani baisan duk suna cikin kungiya ba
"Umma Ashe dagaske ne labarin da nake ji a Calabar kina cikin kungiya Umma yanzu Sabida rufewar ido da Baki samu yanda kikeso ba Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer?Umma.ina tunaninki ya tafi Umma karki manta fa duk abinda kike takama dashi daga ke har mu wlh shine toh shikenan ai kin huta kin zama silar da na rasa komai nawa yanzu kowa sai yayi ta kansa dan wlh banida shi bazaki Sakani sata ba ko me Naseer yayi miki Bai Kamata kiyi Masa Haka ba Dan kawai yak'i rabuwa da matarsa"
"Marina fa yayi Tijjani Marina yayi Akan Matarsa har Ni Ina mahaifiyarsa ya daga hannu ya mareni"?
"Haka kawai ya mareki ba shake Masa Mata kikayi ba kina neman kasheta Kuma Naga Yana ta baki hakuri akan Bai San ya mareki ba Amma duk da Haka shine Kika k'ona dukiyarsa toh sai ku nemi gidan Zama ai