Showing 69001 words to 72000 words out of 180103 words

Chapter 24 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2505

ya Dan samu abinda yake juyawa.sai gashi an wayi gari kayan.shagonsa.sunyi kwaraf Babu komai sai rufe shagon yayi ya hau buga buga Nan ma yana dan samu Nan da nan kudin zai Kare.

Allah kawai yake kaiwa kukansa

A cikin irin wanan lokacin aka koro su zahira gida sabida school fees kayan abinci suka kare.

Sai Dan abinda.bazaa.rasa. ba Wai ahaka.ma Naeema tana iya k'ok'arinta dan taga asirinsu ya rufu.

Tsanani yayi tsananin da Naseer wani zubin idan ya fita yanda.ya fita haka yake dawowa gidan ba ko sisi.

Hakane yasa Bai shawarci Naeema na ya tafi Modobi wajen yayyensa Dan su Dan taimaka masa a cikinsu mutane uku ne Suka iya hada Masa kudi sauran kuwa daga Mai cewa babu sai Mai cewa shima hidima ta.masa yawa.

Dan dukansu sun wacece mahaifiyarsa sun kuma San Abubuwan da ta aikata hakane yasa suke Tsoron jawo shi jikinsu wasu Kuma suna kyamatarsa.da mahaifiyarsa Mayya ce ko Yar kungiya kamar ma shine Hajaran sabida yanda Suke Masa.

Ahaka ya dawo zuciya ba dadi.

Dan kudin ma daya samo yake tunanin yin jari sai a abinci da zasu saka a bakinsu ya tafi.

Naeema

Bamu tab'a Shiga matsi da tsanani rayuwa ba irin wanan lokacin nayi kukan filin nayi na boyen tausayin Naseer da nakan kamashi Yana kuka daddare Amma bana San na nuna Masa nagani sabida nasan b'oye min halin dayake ciki yake (Ya Allah kayi Mana suttura ka bamu arziki mara Yankewa wlh duk Wanda yake da arziki Allah ya jarrabe shi da karayar arziki Yana cikin tashin hankali da sai Mai Imani ke iya jurewa wlh wani.ma na iya haukacewa idan ya juya yaga abinda yafi karfinsa ya wayi gari.ya gaggareshi Zan takaita wahalar da suka Sha Dan bana so na fadi komai wasu zuciyarsu bazata iya dauka ba Amma Zan Fadi kad'an daga ciki Allah ya doramu akan makiyanmu ameen)


Har ya Kai abincin da zamu saka a bakinmu na neman gagararmu wani zubin ma sai na danyi Yan dabaru muke samun naci

Idan Naseer ya fita Bai samo komai baya iya shigowa gidan Haka zai zauna a waje sai dai idan yarana sun Dan fita waje sun ganshi zasu rugo su gayamin anan Zan Gane Bai samo komai ba Ni Kuma Zan zura hijabina na fita na tsugunna a gabansa na bashi baki akan Kar ya damu Allah na sane damu baya iya dagowa ya kalleni balle yayana da suke kallonsa sabida yunwar da.suke ji gani suke idan suka ganshi ya kawo musu abinda zasu ci ne.

A Haka Zan rik'e hannun Zahira na zaga unguwar neman taimako Ina kuka wayanda suka sanmu a baya sukan tausaya Mana su Dan taimaka Mana idan Kuma ban samu ba Haka zanje tsohuwar unguwar mu da ke da Dan nisa a kafa.
Naje gidan mmn Mannir da bazan taba manta ta ba a rayuwata sabida taimakon da tamin dayake tasan halin da muke ciki Nan da Nan zata hada min kayan abinci mijinta shima ya bamu wani Abun.

Yanda na fita na bar Naseer ahaka Zan dawo na tarar dashi sai ya ganmu da Leda yake samun kwanciyar hankali.ni kuwa Nan da Nan Zan sarrafa abinda.ma samo na bawa Yara na zubawa Naseer naje har waje nayita rokonsa kafin ya yarda.ya.shigo.abinci kuwa sai nayi dgaske yake ci Dan cemin yake kunyar mu yake ji muyi hakuri ya kasa.kalmar Nan na sakani zubar hawaye.

Yarana Kuma sabida yarinta da basu San halin da muke ciki ba ahaka zasu zo suyi ta suna so su koma makaranta basu da wancan basuda wanan ko ma na basu abincin suce min basu koshi.ba.


Ahaka muke ringa rayuwa cikin kunci Naseer kuwa yabi ya saka damuwa a Ransa abubuwa sai Kara matse Mana suke duk inda.naseer yaje neman aiki ko kudi baya samu idan kuwa yayi aikin k'arfi Dan abinda yake samowa Bai taka Kara ya karya ba Yana kawowa xamu siyi abinci muci.

Nasha farkawa daddare nga baya dakin idan na fita Haka Zan tada.shi a k'ofar gida Yana kuka ahaka zamuci kukanmu mu biyu na Masa naseeha ya bani hakuri sai mu koma cikin gida.

Idan bacci Bai zo Mana ba sai mu rayya daren muna kaiwa Allah kukanmu

Ahaka muka samu shekara biyu cikin matsin rayuwa zuwa yanzu ma wayanda nake zuwa neman taimako a wajensu sun gaji Dani Mmn Mannir kuwa sabida Kar ta gaji Dani yasa na daina zuwa wajenta.

Sai dai na Dan shiga gidan masu Hali na musu wanke wanke ko wanki ko shara su bani na abinci Nazo na bawa yarana.

Ahaka Watarana naje gidan wata baiwar Allah da itama bazan mantata ba a rayuwata na nemi ta bani wanki na Mata ta biyani mu samu na abinci.

Ta Debbo min wankin na fara Ina cikin Yi ta Leko Wai na Shiga wancan d'akin akwai kayan yaranta na d'ebo na wanke Ina Shiga d'akin.

Naji ta fara min ihun barauniya kafin kace me Mata sun cika gidan an zagayeni mai dunguremin Kai nayi Mai. Rankwashina nayi ahaka suka rakoni har k'ofar gidana suna min ihun barauniya nayi kukan nayi rantsuwa Amma sun k'i yarda Dani bansan Mai nayi matar ta nemi ta wulakantani ta tozarta tani ba.

Naseer dake gida da Yara da ciwon baya ya Hana shi fita sabida d'aukar Kaya masu nauyin ya fito jikinsa na rawa duk dauriyarsa Haka ya hau hawaye suka.gama.ci Mana mutunci suka tafi.

Naseer kuwa ya ruk'o hannuna ya kaini har daki.
Ya tsugunna ya hau bani hakuri.

Ban iya magana ba sabida halin da nake ciki.


Ahaka Naga ya saka doguwar Riga ya fita.

Bai dawo gidan ba sai wajen goma yarana sun Sakani a gaba suna ta kukan yunwa.

Zahira ce kawai take Gane halin da muke ciki.

Niki Niki Naga ya shigo da kayan abinci.

Cikin murna na mike Ina tambayarsa Ina ya samo yace Kar na damu na dorawa yaran abincin.

Nan da nan na dafa musu abincin

Suka hau ci Kamar basu tab'a cin abincin ba Ni kuwa tambayar Naseer kawai nake Ina ya samo kayan abinci

Sai anan yake cemin a Lukman ne ya taimaka masa yaron shagonsa ya hada Masa da Dubu biyu lokacin da kudi ne Mai Dan yawa.

Sosai na hau shiwa Lukman albarka Naseer kuwa ya ruk'o hannuna Yana bani hakuri halin daya jefamu na gazawar da yayi Ni kuwa na rufe Masa baki Ina ya Bari jarrabta ce ta Allah.

A ranar sai da muka Kai Sha biyu muna Hira cikin siga Naseer na bani amanar yayansa da Sam ban kawo komai ba a Kuma ranar muka samu nutsuwa da juna Wanda rabonmu da samun nutsuwar har mun manta sabida matsin da muke ciki.

A Haka bacci yayi awon gaba dani.

Naseer ya tashi ya tsarkake jikinsa ya d'auko wani Leda ya zuba kayansa kala biyu ya ajiyewa Naeema wasika a karkashin pillonsa.

Ya duka ya sumbaci Goshin ta Yana kuka yabi yayansa ma ya sumbace su daya bayan daya kafin ya Kare musu kallo Yana hawaye cikin sand'a ya bar gidan..............


*Comment*


[6/18, 7:59 PM] Zee Smy: Naga sabon book dinki amma ban fara daga farko ba,yayi kama da lbrn wata amma ita uwar mijin dayar ba yar secret society bace,ruwan asiri Kawai take mata hadda na ta haukace,amma har yau auren na nan,almost 31yrs of marriage...suma sun shiga tashin hankali mara fasaltuwa,itama har danta take ma asiri kada ya cigaba arayuwa sbd kada matar taji dadi,as am reading some pages they’re reflecting the story of someone I know,
[6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Am happy
[6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Akwai Mai irin labarin Amma wasu na karyayawa
[6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Karyatawa
[6/18, 8:24 PM] Zee Smy: Wllhi my dear am a living witness of such
[6/18, 8:31 PM] Zee Smy: The mother in law did everything possible tarabasu but Allah beyiba,kuma harta koma ga Allah bata kaunar matar Dan nata...Wllhi Idan taga kina son matar Danta kema ta tsaneki knn,Idan na baki lbr itama sekin mata kuka...har danta take ma asiri kada ya Cigaba arayuwa,aikuwa ya rasa aikinsa taita farin ciki shima kmr Naseer shine ke riqe da mmn shi dakuma siblings...Allah ya shiryi masu irin wannan halin amma akwai su koba suda yawa
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 27*

Naseer Bai Yi minti biyar da fita ba na Kai hannuna wajen da yake kwance a gefena.

Na shafa naji ban jishi ba mik'ewa nayi zaune da Sauri Haka kawai naji fad'uwar gaba duk da na Saba farkawa ban ganshi ba amma duk da Haka yau sai nake Jin wani irin tsoro.

Durowa nayi daga Kan gadon na fara Kiran sunansa nayi hanyar k'ofa bayan na lek'a band'akin ban ganshi ba.

Haka kawai na tsinci jikina da rawar tashin hankali ban damu da tsakar dare bane na ware murya na fara kwalla Masa Kira na bud'e kofa da Sauri na fita Waje duk tsorona Haka na cigaba da kwallawa Naseer Kira na Kara komawa.dakinmu Wai na duba ko dai Yana dakin nice ban gansa ba.

Ina Naseer yaje da tsohon Daren Nan tuna amanar yayansa da ya ringa bani dazu Kamar Yana min hannunka Mai Sanda yasa na Kara Jin fad'uwar gaba da tsoro na hau kwallawa Masa Kira Ina Kara Shiga band'aki.

Tsabar gushewar hankali har karkashin gado na lek'a ban ganshi ba.

Rawar da jikina ya d'auka yasa na samu waje na zauna a gefen gadon Ina Kara kallon agogo karfe uku da minti ashirin.
Ba yau na Saba farkawa na duba Naseer Naga baya Nan ba Amma baya wuce k'ofar gida Ina Naseer yaje Daddaren Nan"?

Na rik'e zuciyata dake bugawa tunani iri iri na zuwar min Zuciya.

Kara mik'ewa nayi Dan nayi waje a wajen mik'ewa hannuna ya Kai Kan pillonsa hannuna ya tab'a farar takarda daya sakamin wani irin fad'uwar gaba tare da rawar jiki

Cikin kakarwa kamar wacce tayi arba da mugun Abun tsoro na dauki wasikar tunanin Lokacin da na taba ajiyewa Naseer wasika na fad'omin.

Warware wasikar nayi numfashina na sama sama Ina Jan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun



*Assalamu alaikum matata uwar yayana Naeema a lokacin da zakiga wasikar Nan kila na Dade da nisa Naeema Allah ya Miki albarka Ina rubuta wasikar Nan ne cikin raunin zuciya da hawaye da rashin mafita Naeema dauriya nake yi a gabanki Amma Ni kadai nasan ciwon da nakeji a Zuciyata game da rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki ba'a San Raina kike fita neman abinda zamu ci ba har ya Kai Naeema yau a garin nema an kala Miki Sharrin Sata bazan iya jurewa Ina ganin kina Shan wahala ba na kasa Baku kulawar daya dace na kasa sauke muku hakkin ku dake kaina shekara biyu kenan rabon yarana da makaranta da yanzu Zahira da Nadeeya sun Isa Shiga makarantar gaba da primary ganinku a cikin irin wanan halin na iya sawa na yanke jiki na Fadi ko zuciyata ta buga a yau da aka tozartaki Naeema zuciyata tayimin ciwo Ina ganin kamar duk laifina ne da ace na Nemo da Baki fita ba har a.miki wanan tozarcin hakane yasa Ina fita dazu nayita bin mutane irin wayanda na taimaka wa a baya ko zasu taimaka min sai Lukman ne ya taimaka min na samu wanan Kayan abincin da kudin da Kika gani dashi Naeema na gaji da ganinku haka a wahalce hakane yasa na yanke tafiya zuwa wani garin na nemi kudi ko Allah zai saka na samu kudi Dan Allah kisakani a cikin adduarki ga amanar yarana kiyi hakuri da tafiyar danayi nasan zakiji ba dadi Amma gani.nake kamar hakan shine mafi alheri a garemu tunda banida amfani idan na kasa ciyar daku na shayar daku Dan Allah ki kularmin da yarana kiyi hakuri na barku a hannun Allah insha Allahu zai kularmin daku*

Ban iya karasa karantawa ba na fita aguje Ina ihun Kiran Naseer daga Ni sai rigar bacci kafa ba takalmi

Duk da karnuka dake ta haushi Haka na fita aguje nabi layin dazai fita Dani titi kamar mahaukaciya ina " Naseer ka dawo karkamin Haka karka tafi ka barni wlh nasan Allah ne ya jarrabcemu ba kasawa kayi ba ya zaka gudu ka barni da Yara biyar Naseer karka manta fa Kai kadai gareni"

Kuka nake sosai Ina gudu Ina dube dube ko xan ganshi ahaka naje har titi Banga kowa ba Akan titi na durk'ushe Ina ihun kuka Ina surutai.

Ban ankara ba sai Kiran Sallah naji.

Gwiwa a sage.kamar wacce akayi wa mugun duka na tashi na koma gida ji nake inama mafarki nake Taya Naseer zai gudu ya barni muna cikin wanan halin taya Naseer zai gudu ya barni da Yara Ina ilimin Naseer da ya kasa tawakali ya jure jarrabtar da Allah ya mana.

Dak'yar nayi wankan tsarki Ina kuka sallah ma ba a nutse nayi ba Ina iddarwa wani irin Mugun zazzabi ya rufeni.

Takarda daya rubutamin na rukunkume a hannuna.

Ina kallo su Zahira suka shigo d'akina da Sallama Dan suma sun Saba da asuba suke sallah.
Suna iddarwa d'akina suke zuwa su gaisheni.

A Haka zamu zauna Gabadaya Dan karatun da Suka iya mu hau Yi gabadaya

A Haka Naseer ke dawowa daga Massallaci ya same mu shima sai su gaishe shi.

Zahira nada Sha hud'u lokacin tana da wayo da hankali a guje ta karaso wajen da nake kwance ta ruk'o hannayena tana "Umma bakida lafiya ne?

Dukansu zagayeni sukayi Ni kuwa ganinsu yasa na Kara fashewa da sabon kuka

Zahira itama kukan ta fara yi Dan Haka take ko Yaya ta gani a cikin damuwa itama Nan da Nan take Shiga cikin damuwa.

Dak'yar na tsagaita kukan da nake na ce ta dafa musu abinci suci Dan ba laifi ta dan iya.

A ranar dauriya kawai na ringa yi sabida yarana danaga sun fara Shiga cikin damuwa.

Tafiyar Naseer sosai ya karyani ya Sakani cikin tsananin damuwa.

Bana rabo da hawaye.

A Haka muka ci wata daya kullum Haka nake zuba Ido Naga ko Naseer zai dawo har ta kai.ma bana rufe k'ofar Gidan.

Ban fara Shiga tashin hankali ba sai da kayan abincinmu ya kare anan na fara tunanin hanyar da Zan Nemo wa yarana abinci sai nake Jin kamar nauyi ya kararmin kamar bazan iya kula da yaran nikadai ba.


Ahaka na fita Shiga wanan gidan Shiga can ahka na tattara abinda na samu na dawo gida na Dan Mana abinda yarana zasu ci.

Haka nake Hana cikina sabida yarana su koshi idan ka gani zaka dauka na shekara Ina jinya sabida ramar da nayi

Duk dare sai nayi kuka idan na gaji sai na daura alwala na kaiwa Allah kukana Rabin addua ta akan Naseer ne Allah ya karemin shi ya dawomin dashi lafiya.

Rayuwa babu Naseer sosai ya Karamin zafi Kan zafi Dan ya Kai yanzu idan na fita wani zubin bana samo Mana abinda zamu ci.

Ahaka Zan zauna da yarana muci kukan mu tare na basu ruwa.

A ranar Daga Kan Nadeeya zuwa Raheema basu iya runtsawa ba sabida yunwa na Kuma rasa ya zanyi Dan duk Inda naje bansamu komai ba.

Gabanin asuba bacci yyi awon gaba dasu.

Ina iddar da sallah na saka hijabina na fita.

Bansan Mai yasa bana San nayi bara ba

Gidan mmn Mannir na tsinci kaina da nufa.

Bama su tashi ba lokacin Dana je

Kwankwasar da nayi yasa suka bud'e.

Mijin mmn Mannir ne ya bud'e k'ofar Yana ganina yayi saurin cewa na shigo dafatan lafiya.

Ban iya ce Masa komai ba Ina ganin mmn Mannir na zub'e a kasa na hau kuka ita kuwa ta saki sallati Tana tambayata Mai ya faru.

Dak'yar na tsagaita kukan da nake na Bata labarin tafiyar da Naseer yayi ya barni da Yara.

Da irin wahalar da nake Sha har jiya ma bamu samu munci komai ba.

Nan da Nan itama mmn Mannir ta hau zubar da hawayen tausayina ta hau cewa Naseer Bai kyauta daya gudu ya barni ba.

Mijin ta kuwa ya hau fadan Mai yasa banzo sun bani wani Abun ba su kansu sun San halin da muke ciki bazasu gaji damu ba Dan Shima Naseer ya Masa alherin da bazai manta ba.

Cewa mmn Mannir yayi ta tashi ta Dan harhado Mana kayan abinci.
Jiki na rawa ta mik'e ta Shiga store dinsu.


Shi Kuma ya koma cikin daki.

Jim.kadan da shigarsa ya fito hannunsa rik'e da hamsin hamsin sababi Mai yawa

Ya mik'o min jiki na rawa na amsa na fashe da kuka Ina zabga Masa godiya shi kuwa yace "Dubu biyar ne Dan Allah ki ja jari ko Yaya ne ki ringa wani sana'ar a gida da zai na shigo Miki da kudi Allah Yana sane daku watarana sai Labari Allah ya dawo da Naseer lafiya ya Riga rufa asiri"

Bazan taba manta mutanen a rayuwata ba duk kankantar alheri idan kamin bana mantawa shiyasa har na mutu Ina yiwa mutanen Nan addua dacewa duniya da lahira.

Sai daya fice daga gidan dayaga Ina ta Masa godiya.

Mmn Mannir kuwa ta kusa cikomin bakin buhu da kayan abinci har da suturun yaranta da zasuyi wa wasu daga cikin yarana.

Nima ta bani a nata wajen kala hudu Dan Ina fama da rashin sutura har yayana.

Har bakin titi ta rakoni na ringa zabga Mata godiya.


Tana tafiya na fara zabga Sauri.
Kyashin ma taba kudin da suka bani na hau mota nake sabida Kar ya Kare.

Ina Isa gida na tarar da duk sunyi rub da ciki suna hawaye har da Zahira da take da juriyar yunwa suna ganina da buhu suka taso da Sauri.

Tausayinsu yasa na fara zubar da hawaye nima.cikin rawar jikin na bud'e buhun.

Naga har da bredi manya guda biyu mmn Mannir ta hadoni dasu.

Basu tsaya ma jiran na basu ba suka daka wa bredin Wawa har da Raheema suka ringa tusawa a baki Kamar basu tab'a cin abincin ba.

Gefe na koma naci kukana na koshi na share hawaye na na hada katakwaye na Dora Mana shinkafa Mai Dan yawa da zamuci har dare.

Dayake da tumatirin gwangwani na Mana Miya Dan har Mai da maggi mmn Mannir ta bani.

Sai Dana Gama na kara zuba musu Nan da Nan sukaci.

Sai da suka.koshi Zahira da Nadeeya suka gyaran gidan Ni Kuma na zuba nawa na Shiga d'aki Dan naci Nazo nayi tunanin Sana'ar da zanyi.

Sai dai Ina yin.loma biyu.naji zuciyata na tashi kafin kace me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login