Showing 72001 words to 75000 words out of 180103 words

Chapter 25 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2458

na kece da amai.

Sai Dana Gama amai na hau kuka Dan na Gane cikine Dani Dan bana Aman banza sai a dalili.


Banji dadin samun cikina a irin wanan lokacin ba shaf na shaafa Dan Ina yawan zazzabin dare.

Kuka naci na Godewa Allah sai Dana Sha magani na fito wajen yayana hannuna rik'e da kudin da mijin mmn Mannir ya bani na zauna a tsakiyarsu


Nan da Nan suka zagayeni suna washe baki budar bakin Nadeeya sai cewa tayi "Yauwa Umma tunda kin samu kudi Dan Allah ki samu a makaranta wlh.inasan komawa makaranta".

Minal kuwa cewa tayi "Umma ki siya Mana kayan abinci Mai yawa sabida mu daina Jin yunwa"

Humaira kuwa cewa tayi Umma ki siyamin sabon takalmi takalmana duk ya tsinke

Raheema dake karamarsu itace Bata ce komai ba sai a lokacin na kalli Zahira nace Mata "bakice komai ba"

Murmushi tayi tana "Umma nidai ki dafa min Abu na ringa fita Ina siyar miki sabida karki ringa rasa kudi a hannunki Umma Wai yaushe Abban mu zai dawo"?

D'auke hawayen dake neman zubomin nayi na kalli Zahira Ina "Abbanku Yana Nan ya kusa dawowa Zahira yanzu wane Abu kike ganin ya kamata mu siyar unguwar Nan sabida na samu kudin da Zan saka ku a makaranta na siyawa Minal takalmi na siya Mana kayan abinci da yawa"?

"Umma ki ringa siyar da kankankara Ana siya sosai"cewar Minal


"Umma ki ringa siyar da abinci Amma fi siyan shi" Cewar Nadeeya mayyar abinci

"Umma kiringa siyar da kayan Yara da Yar tsana"

Cewar Humaira

Sanin Raheema bazata ce komai ba yasa na kalli Zahira ita kuwa tace "Umma kiringa siyar da kosai a k'ofar gida tunda Babu masu siyar da kosai a layinmu"


Murmushi na saki Dan shine a Raina Ina mamakin kaifin tunanin Zahira Ina ganin siyar da kosai shine mafita kawai.

Hannun yarana na ruk'o gabadayan su Ina "Allah ya muku albarka ya rayamin ku ku kadai kuka ragemin a rayuwata nake Kuma ganinku Ina Jin dadi.

Zan saka ku a makaranta insha Allahu Zan siya muku Kaya da duk abinda kukeso lokaci yayi da Zan taka rawar da mahaifi yake takawa akan yayansa"

Hira da nakeyi da yarana kowaccensu inajin abinda take buri a rayuwa.naji na Dan rage damuwa.

Da yamma Zahira ta siyomin komai na bukata da zamuyi kosai.

Tabi mak'ota duk ta Gaya musu.

Washegari tun karfe hudu na tashi duk da inajin zazzabi sabida laulayin da na fara haka na wanke wake Ana iddar da sallah asuba na Kai markade Ina dawowa na hada wuta.

Ina zazzabi a Haka na fara saka kosai Zahira na d'aga gefena cikin Ikon Allah kuwa masu wucewa suka fara tsayawa suna siya.....


Yau bak'i nayi wlh wata fans din Naga ta kaina tazo ganina Kamar nice Naeema ngd ER uwa Allah ya bar zumunci


Habeenart Naga sako Allah ya bar zumunci ngd

*Comment*

Allah sarki Naseer da Naeema😭kuntunamun halin dana taba tsintar kaina nima aciki,wallahi Sadnaf ina karantawa ina ganin kamar labarina kike rubutawa,yanda Naseer zai fita neman na abinci yadawo bai samu komiba yazauna waje yakasa shigowa,wallahi haka muka taba tsintar kanmu,Naira biyar dazamu samu musai gari da suger haka zai wuni yana yawo bai samuba😭ya dawo yakasa shigowa,banbanci kawai su gidan kansu ne mukuma family house ne,wallahi kuma duk sharrin makiya ne,gashi saidai inbada labari,wanima inna fada sai yaga kamar karya yakalleni yace yanzu kece kikayi irin wannan rayuwar? Nakanyi😊kawai ince kina mamaki ko?.
Allah kashiga tsakaninmu da makiyi ka karemu sharrunsu dun inda muke.
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 28*

Ban kawo Zan siyar da duka kosan ba sai gashi kafin Tara na siyar gabadaya har Ana Kara tsayawa a tambaya ko da akwai.

Zahira sai washe baki take tana murna cinikin da mukayi.

zazzabin daya rufeni da k'arfi yasa na dauki gwangwnanin kudin na bawa Zahira umarnin ta kashe itacen ta shigo da komai.

Daki na shige na kwanta na rufe kaina.

Dan Sosai Nake Jin wani irin Sanyi

Bansan Mai yasa wanan cikin yazomin a Haka ba Dan ban fiye laulayi ba iyakacina zazzabin dare Ina tashi Kuma shikenan Amma wanan kuwa amai da zazzabi nake wuni har dan yawu nake yi Wanda duk cikin da nayi ban taba yinsu ba.

Zahira kosan Dana zuba musu a flask ta juye musu a faranti ta had'a musu da ruwan Lipton suka Sha sai da suka Gama gyara gidan ta shigo d'akina tana min Sannu.

Dan ta San banida lafiya
Kosan da ta rage ta zubomin har da tea tana "Umma ki daure kici abinci sai ki Sha magani"

Ganin duk ta damu yasa na mik'e da kyar na Kai kosai bakina sai dai ko uku banci ba na fara kwara amai.

Sai Dana Gama nasa ta d'auko min pcm na Sha da ruwan shayin na koma na kwanta Nan da Nan bacci ya d'aukeni

Zahira kuwa Bata tsaya jirana ba dayake ta Dan iya girkin ta kirba musu jollof din shinkafa a kula jifa jifa Kuma tana lek'o Ni taga ko na tashi.

Bani na tashi ba sai wajen karfe daya na Shiga bandaki nayi wanka Dan na d'an ji kwarin jikina nayi Sallah na fito na tarar da Zahira da kannenta da tsofaffin littafinsu Wai Nan gwaji take basu itace mallamarsu


Sai tausayinsu ya rufeni nasan suna San komawa makaranta Babu yanda zasuyi ne.

Suna ganina Suka hau min Sannu na musu murmushi na zauna Ina ganin rubutun da suke.

Wa zai ce yarana sunyi makaranta.mafi tsada a gadon Kaya da sharada Amma ji yanda duniya ta juya damu ko makaranta gwamnatin ma sun kasa zuwa sabida babu

ko wane Gari Naseer yaje ko ya yake rayuwa yanzu dan nasan ko a Ina yake Yana can ne zuciyarsa na Nan.

Gwangwanin kudin nasa zahira ta d'auko min na fito da kudin ciki na kirga kudin abinda na kashe na ware na kirga ribar da shima ba laifi mun samu.

Kudin na Kara Bata ta siyomin komai na kosan gobe na saka ribar a gwangwani Dan inaso ko yayane na nema musu makaranta yaran nawa girma suke Kara yi

Sai dai Mai washegari kasa tashi nayi Sabida azabar zazzabi jikina kamar garwashin wuta amai kawai nake Ina Jin jiri

Kosan da ban iya fita na soya ba kenan har cikin gidan aka ringa kwada Sallama Ana nema.

Kafin ma Rana tayi jikina yayi wani irin laushi ko kaina bana iya dagawa na bud'e baki ma na yiwa Zahira magana na kasa.

Ina dai kallonta ta Dan gyara gidan tayi musu abinci suka ci.

Ta dawo gefena tana min Sannu hannun data kawo jikina taji da zafi yasa ta mik'e ta fita.

Bata fi minti ashirin da fita ba ta dawo tana "Umma ki tashi muje asibiti jikinki yyi zafi da yawa na Kira Mai taxi"

Gwallo Ido nayi Ina kallonta Taya zanje asibiti banida kudi canjin wajena da ribar Bai fi Dubu da dari biyu ba Kuma shima banaso na tab'a.

Bansan ya akayi tasan yawu ne a bakina ba ta nemi gwangwanin Madara ta kawomin tare da dago kaina na zuba yawun a ciki Ina "Zahira sabida mai yasa Zaki Kira Mai mota banida kudin zuwa asibtii fa ki barni na Sha magani Zan warke"

"Aaa Umma gwara muje asibitin bakida lafiya sosai gwara likita ya dubaki Dan Allah ki tashi muje"

Ba yanda zanyi Haka na mike tana rik'e Dani na zura hijabi muka fito ta d'auko kudi a cikin gwangwanin muka fito waje ta cewa Nadeeya ta rufe gidan Kar ta bud'ewa kowa har sai mun dawo

Muna zuwa asibitin daga su dubani suka bani gado sabida jikina ba kwari Ina Kuma bukatar Karin ruwa.

Abu kamar Wasa sai gashi kamar zuwa na asibitine yasa jikina ya Kara rikicewa.


Duk kudin da ke ajiye a gida sai gashi duk ya kare.

Zahira ke Tayani kwana ta roki makotana akan su Nadeeya zasu ringa kwana a wajensu.

Kwana na hudu a asibiti na Dan ji sauki.

Ahaka aka sallameni muka dawo gida.

Kayan hadin kosan kuwa tuni Zahira ta girke Dan abincin da mmn Mannir ta bamu ba wani yawa ne dashi can can ba tsitsinta Mana tayi.


Ganin babu kudi Kuma bbu kayan abinci yasa na fara neman yin wani rashin lafiya abinda muke dashi Bai wuce Kofi hudu na shinkafa ba sai dari da ashirin ni nasan badan rashin lafiyar Nan da nayi ba da Kila na Dan samu kudin ta silar siyar da kosai

Inaji Ina gani duk burin Dana ci na juya kudin Nan ya Kare a hannuna.

A ranar na kasa bacci Ina tunanin Kuma abin yi dan da kunya na Kara komawa gidan mmn Mannir to daga Ina Zan fara.


Washegari sauran abincin Zahira ta dafe musu.

Ni kuwa na rik'e dari da ashirin a hannuna Ina juyawa.

Har d'akin Zahira ta shigo ta zauna a gefena tana "Umma ya baki Fito ba ko jikin naki ne"?

"Zahira ba jikina bane Ina tunanin Inda Zan samu kudi na Kara siyo kayan yin kosai Zahira bamuda komai a gidanan abincin daya yi saura Kika dafa muku yanzu anjima daddare Mai Zakuci babu abinda ya rage mana sai dari da ashirin din hannuna shiyasa ranan nace Miki bazanje asibiti ba Yanzu Ina zanje na samo Mana abinci daga Ina Zan fara mutane sun gaji ma da taimaka min"


Kamar wata babba na hau yiwa Zahira maganganu Ina kuka

Itama kuwa ta hau kukan ta kawo hannunta ta karbi kudin hannuna tana "Umma wannan ma zai isa muyi wani Abun ki kawo kigani"

Bata Bari nayi magana ba ta fita da hamsin tare da ajiyemin sabain.


Ina zaune a daki Naga ta shigo da farin Leda irin na kulla kankara.

Ta Shiga kitchen ta d'auko Kular ruwan Sanyi mu ta wanke sosai.

Sai a lokacin nace "Wai Mai zakiyi ne Zahira"?

Murmushi tamin ta dauki bokiti Mai kyau ta taro ruwa Dan muna da pampo a gidanmu Mai dadi kuma.

Ina kallonta Naga ta dauki farin ledar ta fara diban ruwan Tana zubawa a Leda tare da kulawa.

Nidai kallonta kawai nake Ina mamaki Dan Ni nasan bamuda freezer ballantana nace so take mu fara siyar da kankara.

Tana gamawa ta rufe ta Kara fita Bata Jima da fita ba sai gashi ta dawo da kankara manya guda biyu ta faffasa ta zuba tana "Umma naira biyar biyar ake siyar da ruwan Sanyi a bakin titi Ana ciniki sosai anjima zanje na siyar zamu samu kudin da zamu ci abinci"


"Aaa Zahira bazan Bari kiyi talla ba Ni da kaina zanje indai kinsan Ana siya"

"Umma bakida lafiya fa ki Bari naje Zan iya wlh"

Kare Mata kallo nayi Zahira duk doguwa ce sosai fara gashi ta ma Dan fara kirgan dangi bazan iya Bari ta tafi talla ba mutane basu da Amana Kar su yaudare min ita.

"Na warke Zahira Bari ayi sallah naje ganin tana San sake Musa min yasa na hade Rai baa San ranta ba ta fice daga d'akin

Cikin Dana samu na yawan Sakani Jin bacci ko Yaya naji iska ya kadani bansan sanda bacci ya d'aukeni ba.


Sai wajen biyar na mike a firgice tare da yin palo da Sauri.

Nadeeya da kanenta ke wasan Yar baby


Da Sauri nacewa Nadeeya Ina Zahira

Sai tacemin ai tundazu ta fita da kula a kanta.

Banji dadi ba Dan har ga Allah Ni naso zuwa.

Daki na fad'a da Sauri
Na daura alwala nayi Sallah La'asar duk da jikina ba kwari Haka na fito na dau hanyar titi kafin na isa titin na hangota tana ta zabga Sauri daga yanda yake cila Kular nasan ta siyar.

Tana hangoni ta nufoni da Sauri Ni Kuma na tsaya jiranta.

Tana karasowa ta mikomin ledar hannunta d'auke da biyar biyar Lodi guda har da goma goma

"Umma Kinga na siyar da duka har yanzu nema ake"

Damke ledar nayi cikin murna Ina "Shikenan Zahira mun samu Sanaa Amma daga yau bazaki Kara fita da kanki ba da kaina Zan ringa fita"


Muna karasawa gida.na zazzage kudin na kirga Naira dari uku har da Sha biyar.

Kamar waccce akayiwa kyautar dubunai Haka naji.

Naira dari na Bata ta siyo Mana gari da suga har da gyada Wanda zamu Sha daddare .

Tana dawowa tacemin na Bata dari ta siyo min kayan hadin zobo mutane suna so Dan har tambayarta ake tayi.

Kamar Wasa na Bata ta siyo komai har da suga da yake komai lokacin da sauki ba kamar yanzu ba suga ashirin ma zaiyi Kofi uku a lokacin.

A ranar ban kwanta da fargaba ba Dan Ina kyautata zaton mun samu hanyar da kudi zai ringa shigo Mana Dan har kudi na bawa Zahira ta kaiwa Mai kankara akan gobe zamu karba har farin Leda na Karo.

Washegari na bada kudi Suka siyo Mana koko da kosai.

Da Rana ma garin muka Kara Sha.

Biyu da rabi na Gama hada Zobon dayaji kayan kamshi da suga na kukula na zuba a babban kula dayafi Wanda Zahira ta fita dashi jiya

Wanda Zahira ta tafi dashi kuma.na kukula ruwa muka zuba kankara

Ana iddar da sallah La'asar na dau babban Zahira ta d'au karamin muka Mika bakin titi.

Muna isa Kamar irin mu ake jira ko mu kadai ne masu siyar da ruwan Sanyi da zobon.

Nan da Nan aka hau siya ko awa daya bamuyi ba ya Kare.

Hamdala kawai nake a raina.

Dan na rubanya kudin Dana kashe sosai.

Daga Ni har Zahira sai murna muke.

Kayan abinci na Dan tsitinta na siya Mana mukaje gida.

Zahira ta Dora Mana abinci.

Farinciki danake ciki kamar Naseer ne ya dawo.

A takaice tundaga lokacin nida Zahira muke fita siyar da ruwa da zobo.

Allah kuma.ya saka Mana albarka Dan har sawu biyu Mukeyi.

Cikin wata guda sai gashi na Tara kudin da banyi tunani ba.

Dama rashin kudi yasa ban saka yarana a makaranta ba.

Wani karamin private school dake kusa damu.na Kai yarana gabadaya


Sai dai kudin dake hannuna iya mutane uku zai Isa a saka babu kudin biyu Raheema da Humaira kuma.ya Zama Dole na saka su

Tsugunna wa nayi nacewa Mai makaranta ta karbi dukansu Zan ringa mata.aikin nanny har na Gama biyanta.

Cikina daya fara fitowa.ta kalla tace zan iya kuwa

Nace Mata Zan iya kamar Wasa kuwa washegari yarana suka tashi tun asuba suna ta murna zasu fara zuwa makaranta Nima sai murna nake.

Abincin Dana dafa musu Basu wani ci sosai ba Haka na kulle gidan muka tafi.

Naci saa Mai makarantar nada mutunci duk da arniya ce

Sannan Zan na musu aiki yasa ta bawa yarana uniform har da littattafai duk akan bashi.

Ni kuwa na wanke band'akin makarantar na share koina sai Dana Gama naji bayana namin ciwo.

Karfe daya ake tashi gabadaya yarana sai su kirani idan na Kara gyara makaranta sai mu dawo gabadaya

Ina dawowa Nadeeya zata Tayani Dora musu abinci Ni Kuma a lokacin Zan huta na awa daya Ina Kara tashi sai na dau Kular zobo da ruwa Dan na sama musu makarantar Allo da biyar kawai suke kaiwa duk sati sai Dana Yi dagaske Zahira ta yarda ta fara zuwa Dan dagewa tayi sai ta ringa Tayani neman kudi.

Tuni na Saba da wahalar aikin duk da cikin jikina Mai tausayi daya Saba ganina yasan Ina cikin wahalar rayuwa cikina daya fito sosai da a lokacin zaiyi wata shidda yasa wani bawan Allah ya bani shawarar danaje siyar da ruwa da zobo Akan na nemi almajiri Mai Amana na ringa Dora Masa tallan Ina bashi Lada ko abinci Dan Yana tausayamin idan yaga yanda nake Dora Abu Mai nauyi a kaina.

Godiya na Masa dan tunanin hakan Bai tab'a zuwarmin ba.


Ya d'auko hamsin hamsin guda goma ya bani.

Kamar hadin baki Haka aka taramin kudi wanda sai Dana hau zubar da kwallar farinciki.

Na koma gida cikin murna akan hanya na tsaya na Mana cefanen da zai Mana kwana biyu har da Naman Miya


Yarana kuwa sai murna suke da suka ga abincin Dana dafa da.nama sai da suka koshi na fara gayawa Zahira shawarar da wani bawan Allah ya bani.

Cikin farinciki tace min akwai wani isuhu a makarantarsu zata Gaya masa gobe.

Ita kadai ce take da wayon sanin mutum ne a cikina Amma kannenta duk sun dauka ciwon ciki nake idan suga ga cikin Haka zasuyi tamin sannu

Sosai na Dan fara samun kwanciyar hankali daga ranar da isihu ya fara d'aukar min ruwa da zobon Yana kaimin dayake yaron nada kwazo har sahu biyun yake Yi Kuma Yana da amana.

Haka Zan bashi kyautar kudi na bashi abincin dare.

Abinda ke fita Dani kawai shine aikin makarantarsu Zahira itama matar a Karan kanta tace na daina zuwa na bari sai na haihu.

Sosai naji dadin mutuncin data min

Kamar a mafarki Naga Ina wayar gari Ina cin karfin bukatun gidana ta silar siyar da ruwa da zobo na hada da siyar da kananan abubuwa a gida Yarana kuma suna zuwa makaranta islamiyya Dana boko ba abinda Zan cewa Allah sai dai godiya abinda ya ragemin a rayuwata shine ganin Naseer Yana Raina kullum dak'yar nake samun bacci Mai nutsuwa sabida tunaninsa idan kewarsa tamin yawa Haka Zan hau shafa cikina Ina tuna ranar karshen da muka rabu da shine yasa na samu wanan rabon Kaunar abinda ke cikina nake sosai inajin yana ragemin kewar Naseer idan na kalli cikina.


Murja

Hatsabibiya ce ta karshe kuma makira Mai fuska biyu.

Wani irin wahaltacen zama Hajara da Safiyya sukeyi a gidan
Dan duk Inda suke tunanin sun Kai da mugunta ko makirci ta zarce su Dan sosai take musu biyayya Agaban Tijjani Amma idan ya bada baya Haka take musu rashin mutunci San ranta.

Hajara kuwa Bata tab'a tunanin bazata iya cin uban Murjan cikin sauki ba

Har wani horan yunwa Murja ke musu Dan ko Tijjani ya samo abinci ya kawo ta dafa Haka zata juye a kula ta Kai d'akinta ta kankaro kanzo ta basu .

Hajara kanyi zuciya Taki ci Safiyya kuwa Haka zata ci Tana zagin Murja

Hajara kuwa Tana Kiran Tijjani Dan ta Gaya masa Zai daga hannu ya hau cewa baya San tashin hankali Kar tazo ta daga Masa Hankali shi bazai jure ba idan taga bazata iya zaman gidansa ba Dan Allah ta tafi sosai yake Jin Haushin Hajara sabida yasan duk masifar da suka tsinci kansu a ciki itace sila .

Hajara har da kukanta Dan Tijjani ko kad'an yak'i binta sau da kafa balle yabi umarninta ya saki Murja da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login