Showing 87001 words to 90000 words out of 180103 words
wani Mai kudi dake da motoci da taxi na haya.
Take ya bawa Naseer mota da zai na Lodi daga garin kogi zuwa Abuja ya Kuma yanke masa kudin da zai ringa biyan shi.
Sosai Naseer ya hau murna kwana biyu da bashi motar ya fara aikin sai dai duk yanda Naseer yayi tunanin aikin tukin nada sauki sai yaga ba karamin wahala ne da tukin ba gashi bashida cikakken nutsuwar zuciya Dan zuciyarsa na kano gangan jikinsa ne kawai a Abuja.
Ko abinci baya iya ci Dan idan yazo ci ya tuna iyalinsa sai yaji cikinsa ya cushe ya kasa cin abinci Daddare kuwa tunani baya iya Bari ya samu cikakken bacci idan ma ya rayya daren Yana sallah ba nutse yake yin sallah ba sabida tsabar tunanin su Naeema.
Halin tunanin dayake ciki sai daya kusa saka shi hatsari sau da Dama Inda tuni fasinjoji suka fara Gane shi indai motarsa ce bazasu hau ba sai su ce Yana tafe yana tunani.
Ahaka Watarana garin tunanin ya bugi motar wani Mai kudi Wanda ya Masa asarar glass din gaba sai gashi case din sai daya kaisu ga tafiya police station Alhaji Idris na zuwa motarsa kawai ya karba ya Kara gaba.
Karshe dai sai Dan kudin da Naseer ke tarawa ya biya mutumin kudin glass din motarsa.
Wata biyar da yayi a Abuja a wahalce yyi shi cikin tsananin wuya duk inda ya Kai ga fara wani Abun sai wani sanadin yazo kudin ya tafi.
Yayi garuwa,ya siyar da bonse ya siyar da ruwan Sanyi ba irin Sana'ar da baiyi ba Amma abinda yazo nema a Abujan Bai samu ba ahaka a garin siyar da bonse ya hadu da wani shima dake yawan wucewa ta danger da yake tsayawa ya siyar da bonse yayi parking ya fara tambayarsa ya iya tuk'i
Gyad'a Masa Kai yayi da Sauri.
Kamar Wasa ya zama driver mutumin ya Kuma barshi yake kwana a boy's quaters din gidan
Sai dai rashin nutsuwar zuciya da tunani iyalinsa yasa ya kasa maida hankali a Haka ya Kara cin wata uku da sati biyu a gidan.
Mai gidan kuwa tuni ya Gane Naseer Yana cikin matsanacin damuwa Dan duk Wanda ya San Naseer idan.ya ganshi bazai Gane shi ba sabida yanda ya rame ya lalace ga kasumba ya rufe masa.fuska har wani Dan tsufa yayi.
Cikin tausayawa ya kira Naseer ya hau tambayarsa Mai ke damunsa Haka cikin karayar zuciya Naseer ya fara bashi labarin yanda ya baro iyalinsa sabida talauci.
Yana bashi labari Yana kuka
Shima sosai ya tausaya Masa Inda ya Shiga d'aki ya d'auko kudi Yan dari bibiyu na Dubu dari biyu da a lokacin kudi ne Mai yawa da zai Isa Naseer yaja jari ya cika shagonsa.
Ya Ajiye a gaban Naseer Yana ya d'auka ya koma ga iyalinsa.
Naseer zubewa yayi Yana ta Masa Addu'a Yana ji kamar an tsoma shi a Aljanna.
Sosai ya ringa zumudi Yana murna komawa da zaiyi ga iyalinsa Yana kyautata zaton kudin da ya samu zai Isa yaja jari.
Yaso tafiya a washegarin daya samu kudi sai dai Alhaji Ismail ya dakatar dashi akan ya Bari sai wani satin sabida akwai kudin da yake sa Rai idan ya samu zai Kara Masa baa San Ransa ba ya hakura ya Kara cin sati daya duk a takure Wanda yayi daidai da cikarsa wata takwas da sati uku
Gabadaya hankalinsa yayi gida Ido biyu Ido rufe Naeema yake gani da yayansa a cikin mawuyacin Hali hakane yasa Bai tsaya jiran Alhaji ismail ba ballantana ya Masa Sallama ya kwashi kayansa da kudi ya nufi Tasha da asusuba.
Karfe Takwas suka dau hanyar kano sai dai gani yake kamar ba Sauri driver yake ba.
Suna dab da shigowa Kaduna yaji motarsu taci wani irin birki kafin su ankara mutane masu sanye da bakakken Kaya sun zagaye su
Da manyan bindigogi.
Tuni suka bud'e motarsu suka hau fito dasu Naseer kuwa sallati kawai yake.
Duk kansu a sunkuye Barayin Nan suka caje kayansu suka kwashe komai nasu.
Basu iya dagowa ba sabida bindigar da aka Dora musu akai ahaka suna ji suna gani suka rabasu da komai suka haye motarsu suka tafi
Sallati da ihu kawai Naseer ke yi kamar ya haukace.
A takaice a Haka suka hau motar suka nufo garin Kano wajen uku da rabi ya iso.
Sam hankalinsa ba ajikinsa ba a tashar ma.wani ne ya taimakawa.Naseer da kudin motar da ya iso gida kafarsa ma ba takalmi.
Sai dai Yana isowa unguwarsu tundaga nesa yaga yanda gidan nasa ya canja ya Sha gyara tuni gabansa ya yanke ya Fadi Yana tunanin kila Ma talauci yasa Naeema ta siyar da gidan.
Ba dai ta gudu itama da yaran ba hakane yasa ya taka da sauri ya Isa k'ofar Gidan ya tura da k'arfi a daidai lokacin da Hajara ta hankado Naeema ta fado jikinsa.ya cafeta
"ABBAAAA"
Su Zahira sukace da ihu a lokacin da idonsu ya sauka Akan Naseer da ya zuba min Ido kamar yanda na zuba Masa Ido Ina ganin kamar a mafarki nake ganin Naseer ba gaske ba
Fusge jikina nayi daga nasa nayi hanyar cikin gidan da Sauri na shige adaidai lokacin dasu Zahira suka rungumeshi suna ihun murna Raheema ce kawai Bata karasa wajenshi ba.
Hajara itama daskarewa tayi a tsaye a lokacin da Naseer ya shigo suna had'a Ido ta juya da Sauri ta nufi daki Dan Haka kawai taji Kuma tana Jin nauyin ganin da Naseer yayi Mata a gidansa bayan cika bakin da tayi akan bazata Kara tak'a kafarta gidansa ba.
Itama Safiyya bayanta tabi da Sauri.
Naseer kuwa wani irin Sanyi da nutsuwa ya ji Yana shigarsa a lokacin.
Da ya rungume yayansa a jikinsa.
Kasan zuciyarsa kuwa Allah Allah yake yaga Naeema da idonsa ya Gane masa ta na dauke da tsohon ciki Ashe Dama da ciki ya tafi ya bar Naeema.
Da Sauri ya cire su Zahira daga jikinsa ya nufi d'akin da yake kyautata zaton na Naeema ne da su Umma suka gaje.
Yasan yaga Umma Amma San ganin Naeema yasa yak'i Bari ma tunaninsa ya rabu gida biyu.
"Wai me Kika shigo daki a guje ne tsoron Yaya Naseer din kikeji ne ko me?
"Aaa Safiyya kunyar ganin dayamin a gidansa nake bayan na Gama Shan alwashin ba abinda zai saka na Kara tak'a k'afata a gidansa Kar ganina da yayi a gidansa ya d'auka banida wajen da Zan zauna ne kinsan na cicika Masa baki"
"Tab kiji ki Umma ai borin kunya zakiyi ki hade ranki idan ya gaisheki ma ki amsa da kyar yanzu Yana ganin kina Jin nauyi wlh Raina ki zaiyi kamar yanda Yaya Tijjani ya rainaki"
Tana rufe Baki Naseer ya turo kofa tayi Sauri ta Samu waje ta zauna tare da had'e Rai.
Sai Safiyya ce ta amsa sallamar tana kallon yanda Naseer ke mamakin ganinsu d'akin Naeema Amma ya hadiye mamakin da yake ya zub'e a kasa ya hau gaida Hajara data k'i kallon Inda ma yake sama sama ta amsa gaisuwar sa.
Safiyya tayi caraf ta fara magana tana "sati daya kenan da muka zo dak'yar na samu Umma ta biyoni da mukaji labarin Naeema Bata da lafiya sai da nayita rokon Umma Allah da annabi kafin ta yarda ta biyoni.
"Dama Naeema Bata da lafiya"?
Naseer yace hankali a tashe tare da mik'ewa da Sauri yayi waje batare da ya tsaya sauraron sauran maganar da Safiyya take ba.
Inda yakejin muryarsu Zahira yayi da Sauri sosai yaji dadin yanda aka gyara gidan b'angaren ma da Bai gyara ba ya gansa fes.
Amma Bata gyaran gidan yake ba ta Naeema yake.
Dakuna biyu dake jere ya shiga na farkon daya kasance nasu Zahira Yana daga labulen ya ga Naeema a zaune Akan katifa tana ta share hawaye daga labulen da yayi yasa ta dago ta zuba Masa Ido.
Shima idon ya zuba Mata Yana Jin wani irin tausayinta na nukurkusar koina na jikinsa.
Dak'yar ya iya daga kafa ya Shiga d'akin Naeema kuwa kukan da takeyi kasa kasa ta kasa dannewa ta fara yinsa a fili.
Da rarrafe ya karasa kusa da katifar ya ruk'o hannun Naeema cikin rawar murya ya fara Bata hakuri daya hannun nasa Kuma ya Kai cikin ta Yana shafawa.
A durk'ushen ya hau Bata labarin duk wahalar daya Sha daya tafi da yanda barayi suka tare su a hanya suka kwace Dan kudin daya samo musu.
Sosai Tausayin Naseer ya rufeni Dan ko Bai bani labari ba daga yanayinsa kawai nasan ya Sha bak'ar wahala Dan ba karamin Rama yayi ba.
Nidai ban iya bashi labari ba ya hau min tambayoyi game da rayuwar da mukayi ya akayi yaga na baro wancan d'akin na dawo Nan waye ya gyara gidan Ina muka samu kudi.
Ce Masa nayi ya Bari Anjima Zan bashi labari daga Haka na mike na nufi kitchen Dan na karasa girkina Inda Naga har Zahira ta karasa ta juye a kula har nasu Umma ta zuba musu.
Nadeeya Kuma nata markade.
Namu abincin na dauko na ajiye a karamin Palo Inda na tarar da Naseer a tsaye Yana ta kalle kallen gidan kamar bakonsa.
Su Minal kuwa sai danne shi suke suna Masa surutai.
Kiran Sallah Magriba ne yasa ya d'aura alwala ya nufi Massallaci cikin farincikin dawowarsa cikin iyalinsa dayaga alamar suna cikin rufin asiri sosai ya matsu yaji a Ina suka samu kudi Haka har da engine markade guda biyu.
Naseer na fita kuwa Umma ta mik'e da Sauri ta kalli Safiyya cikin b'acin Rai tana "Kinga Bai ma damu da ya bani hakuri ba ya nufi wajen Naeema Sabida yaji ance Bata da lafiya k'arfi da yaji yake nuna Kaunar yarinya Nan a fili Kinga fa yanda ya rud'e dayaji munce ba ta da lafiya.
"Hmm Umma Naeema fa ba Haka ta barshi ba tun lokacin da ya gwammace ki Masa baki Akan ya rabu da ita nasan ta asirce shi Dan Haka ki daina ganin laifinsa ba a hayyacinsa yake ba asiri aka masa"
Sosai ran Hajara ya b'aci da abinda Naseer yayi na nuna damuwarsa Akan Naeema sai alwashi take ci Akan Naeema Safiyya na zugata.
A faranti daya mukaci abinci da Naseer da ke ta washe baki kamar gonar auduga idan muka hada Ido sai ya sakarmin murmushi.
Nasan ba yanda zaiyi ne Agaban Yara da ya rik'eni a jikinsa.
Duk cika bakin da na ringayi na zanyi fushi dashi sai gashi Nima Ina cikin tsananin farinciki zuwan Naseer at least I felt Safe da dawowarsa (bansan yanda zan saka da hausa ba shiyasa na saka da turanci ayi hakuri)
Karfe Tara su Zahira sukayi bacci.
Sai Dana tofesu da Addu'a na fito daga d'akin tun tafiyar Naseer sai a yau zasu kwana su kadai.
A Gefen katifa na samu Naseer a zaune Ina shigowa ya mik'e ya ruk'o hannuna ya zaunar Dani a gefensa sai wani rawar kafa yake kamar Wanda yayi amarya Ni kuwa dariya yake bani ma Dan ni cikin jikina ma ya isheni.
Tambayoyin da yayi ta jera min Akan Inda na samu kudi.
Yasa na fara bashi labarin duk abinda ya faru bayan tafiyarsa irin wuyan Dana Sha da yanda na Sha laulayi Zahira ta kawo Mana shawarar siyar da ruwa da har gobe shi ya zame silar rufuwar asirinmu da yanda na Tara kudi na siyi engine daya har na Kara samun kudi na Kara siyan wani da yanda na gyara gidan.
Da zuwansu Umma da irin abinda suka ringa mun ba abinda na boye Masa.
Da har zuwan da yayi rigimar da mukeyi da su har ya kai Umma ga tureni ya cafeni.
Naseer sosai ya matse hannunsa cikin nawa idonsa ya kad'a yayi jawur sai sallati yake Yana jijjiga Kai Bai tab'a tunanin har yanzu su Umma Basu daddara ba.
Ni kuwa halin Dana ganshi ciki na b'acin Rai yasa na hau basa Baki duk da kasan Raina Ni nasan na Gama yanke hukunci rabuwar mu idan na haihu Amma bazan Gaya masa ba.
Daga rarrashi Kuma muka farantawa juna Rai duk da cikin jikina.
Sai da muka yi wanka bacci yayi awon gaba damu Mai nauyi.
Karfe Hud'u ciwon Mara da baya ya tasheni haihuwa na shidda take nasan Nakuda ne gashi kasana naji kamar Ana danno ni.
Saukowa nayi daga Kan katifar tare da tashin Naseer.
Ai Yana bud'e Ido naji kamar ya tasomin da Nakuda gadan gadan sallati kawai nake shi kuwa ya zura doguar Riga yayi waje kafa ba takalmi.
A mak'ota ya samo Aron mota Yana zuwa ya taimaka min na mik'e cikin tashin hankali ya hau cemin bashida kudi.
Kasan katifata nasa ya daga ya d'auko jakar kudina.
Jiki na rawa ya d'auki kudin ya dau jakar Dana hada kayan haihuwa Dan Ina shiga watan haihuwa na hada komai na bukata.
Asibitin dake kusa mukaje.
Zuwa lokacin sosai naji kamar Ana dannoni da k'arfi.
Ko tafiyar ma ban iya yi ba sai da gadon marasa lafiya aka zo aka daukeni aka Shiga Dani dakin.
Muna Shiga d'akin kafin nurse ta saka Safar hannu naji faya ta fashe nayi Nishi da k'arfi.
Sai kuka baby mukaji.
Take naji kamar an d'aukemin duk ciwon da nakeji.
Na hau numfarfashi
Ban damu da kallon abinda na Haifa ba Dan nasan macece.
Inaji suka yanke cibi tare da zaro mahaifa daya nurse din ta hau goge BBY dayar Kuma na kaina.
"Juyo kiga Mai Kika Haifa naji nurse din tace"
Ban juyo ba nace "Macece Rabbi ya Albarkaci rayuwarta"
"Sai dai ya albarkaci rayuwarsa Dan namiji ne"
Wani irin juyowa nayi da balain sauri a daidai lokacin data doramin jaririn a kirjina........
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
Hannuna har karkarwa yake wajen d'ago da jaririn Dan na tabbatar da Namijin ne.
Take na hau hawayen farinciki na Kara kwantar dashi a kirjina inata Godewa Allah da Wanan kyautar da yamin a cikin jaririn Nan ne kawai ban saka Rai da samun namiji ba Amma sauran duk saka Rai nake da maza ne sai gashi a lokacin da ban kawo ba na cire Rai da haihuwa Namiji Allah ya bani.
Kasa d'auke idona nayi daga kansa har Nurse din ta saka Mai Kaya bayan ta goge Mai jiki da man zaitun
Yanda taga Ina binsa da Ido Ina murmushi yasa tace halan ban taba haihuwa d'a namiji ba gyada Mata Kai nayi a lokacin da take sake mikomin shi na karbe shi da Sauri na tashi zaune na zuba Masa Ido ba Inda ya baro Naseer kamar an tsaga Kara Haskena kawai ya d'auko.
Sosai na ringa Jin kaunar jaririn a Raina inajin nurse din na Bari tayiwa Naseer albishir tayi waje da Sauri Dan tasan indai ta Gaya masa kila ya mata kyauta
A bakin kofa ta tada Naseer din kamar zai fado d'akin Ana bud'e kofa yyi Kan nurse din da Sauri.
Ita kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata goron albishir
Washe baki yayi daya ga alamar Naeema ta sauka lafiya addua ya hau yi Yana "Na Riga da nasan Mai ta Haifa Allah yayiwa rayuwarta albarka"
Murmushi nurse din tayi tana mamakin yanda daga Naeema har Naseer din suka cire Rai da haihuwar da namiji
"Sai dai Allah ya Masa albarka Dan namiji ta Haifa katoto"
Naseer Ido ya gwallo Yana me kikace.
Kafin ma ta bashi amsa ya fada d'akin da Sauri har Yana tuntub'e.
Daga yanda yaga Naeema na murmushi yasa ya Isa wajenta da Sauri tare da saka hannu ya karbi jaririn Bakinsa har kunne sai hamdala yake Yana kamkame jaririn a kirjinsa.
Sai albarka yake shiwa Naeema ji yake kamar baa Tab'a Masa haihuwa bama inama lokacin da yake da kudi Naeema ta haifi namiji da yaron ya Sha Gata.
Bakinsa ya kafa a kunnen jaririn ya Masa huduba ya d'ago ya kalli Naeema Yana "Allah ya raya Naseer sunana na saka mishi"
Murmushi na saki Ina Jin dadin sunan daya saka mishi nace "Allah yasa ya gaji halin Mai sunan ya bashi ilimin addini irin na Mai sunan insha Allahu addua kawai ce tsakanina da yarana Allah Kar ya jarrabceni da fushi dasu"
Na tsinci kaina da fad'a duk da kallon da Naseer kemin yasa na hadiye sauran maganar.
Karfe takwas na safe aka Sallame mu daga asibitin bayan Naseer ya biya kudin komai.
Hamdala kawai yake a Ransa da Allah yasa Naeema nada kudi da yau asirinsa ya tonu ta Ina zai samu wanan kudin da suka kashe a asibitin.
Naeema sai data saka ya siyi kayan shayi da sauran Abubuwan a zata bukata kamar yanda yake siya idan ta haihu shi kuwa sai dari dari yake baya San kashe kudin Wai Dan Kar ya kare.
Lokacin da muka Isa gida Naseer ne ya rungume jaririn a kirjinsa daya hannunsa d'auke da kayayakin mu Ni Kuma Ina biye dashi a baya Ina takawa a hankali kamar iska zai d'aukeni nakeji sabida rashin kwarin jiki banida burin daya wuce na kwanta sabida ciwon baya danake yi
Bakin Naseer a washe ya Shiga palon
Da Sallama Umma da Safiyya kawai muka samu a palon Umma ta hade Rai tana ta jijjiga k'afa Ina ganin Haka nasan wani rashin mutunci Umma zatayi.
Naseer kuwa tuni Naga ya nutsu duk da gabansa sai daya Fadi da ganin Umma Amma Haka ya nufi wajenta ya tsugunna Ya hau gaisheta.
Wani irin kallo ta Masa ta d'auke kanta batare da ta amsa ba
Shi kuwa ya Kara gyara Jaririn a hannunsa Yana "Umma Naeema fa ta haihu Kinga"
"Sai me dan ta haihu yau ta fara haihuwan?Mai abin murna a haihuwa Naeema da take cike.maka gida da tarin Mata"
"Umma wanan Namiji ne wanan Karin Allah ya azurtamu da Samun namiji"
Ina dab da Isa k'ofar karamin Palo Amma sabida Naga ya Umma zatayi idan taji Namiji na Haifa yasa na tsaya.
Mik'ewa tayi da Sauri ta lek'a fuskar jaririn da Naseer ya juyo dashi Sabida Umma ta ganshi sosai ta gaskata maganar da yake.
Ja da baya tayi tana "Kuma sai ka yarda wanan danka ne.
Sai ka yarda wanan Jininka ne?
Watanmu kusan hudu a gidanan tunda muka zo Maza suke sintiri a gidanan wayanda zasu Zo da safe daban wayanda zasu Zo da Rana daban Sabida Kai dakiki ne an asirceka idonka ya rufe shine zaka ringa murnar ta haifo maka namiji.
Kar idonka ya rufe ka kasa gane gaskiya har Ina Naeema zata samu kudin da zata gyara gidanan Bata tsaya iya Nan ba