Showing 114001 words to 117000 words out of 180103 words
kishi masifafiya a unguwarsu kowa yasanta shegen bin Mallamai ne da ita dan wanann bashine Karo na farko da yake neman aure tana wargazawa.ba Har mallake Umar din tayi sai yanda tayi dashi.
Karfin kwallin tsafine yyi tasiri a wajen Umar din ya kamu da San safiyya dayazo.kano.wajen abokinsa da Safiyya ke aiki a gidansa.
Ita kuwa Tana ganin Yana da Dan canji yasa tana dawowa gida ta hargitsa d'akinsu har sai data samo kwallin daya shiga rububi ta rambada kwallin a idonta ta koma.da.sauri tana adduar Allah yasa Bai tafi ba
Tana kuwa zuwa taci Karo dashi a bakin kofa yazo fitowa daga wanan hada.idon Umar ya kamu da San Safiyya.
Kwana uku yayi a Calabar ya dawo ya sanar da Safiyya duk yanda sukayi da kanin mahaifinta Nan da wata Mai zuwa zaa daura aurensu.
Safiyya sosai hankalinta ya tashi dataji wata guda kanin mahaifinta yasa Dan tasan Basu tanadi komai ba
Hakane yasa Yana tafiya ta sako Hajara da maganar kayan dakin da za Mata harda kukanta.
Akan Hajara tasan yanda zatayi da ita Dan Bata San kishiyar ta ta rainata tunda Umar yace a gida daya zasu zauna.
Hakane yasa Hajara itama ta Sako Naseer agaba da maganar kayan dakin
Har fargabar dawowa gida yake Dan shi Dan kudin da yake tarawa so yake idan ya tashi zuwa gidan Naeema ya Dan yiwa yaransa siyayya Kar ya tafi haka hannu na dukan cinya
Dan ya je har gidan Alaramma ya tambayi matarsa ta Masa kwatance Gidan da Naeema sosai yaji dadi da Naeema ta zauna a kano bataje garinsu ba da yasan ma Tana garin Kano Nan kusa dashi da tuni ya nemeta.
Hakane yasa ya Tara kudadensa da zumar yiwa su Zahira siyayya har Naeema ma sai ya siya Mata wani Abun.
Rabin kudin kuwa Dama Waleed zai kashewa Dan yayi kewarsa sosai shima
Gobe ya ke Shirin siyayyan daga wajen aiki ya shirya shi da Nadeeya su wuce Yana shigowa gida ko palon Bai Kai ga shiga ba Hajara ta tare shi da maganar kayan dakin Safiyya.
Baya San wani Abu ya dameshi sabida farinciki da yake ciki
Cewa Hajara kawai yayi toh zai nema suka shige shi da Nadeeya
Ta kaiwa Nadeeya rankwashi akan Bata gaisheta ba ta hau bambamin Kar ya Kara fita da Nadeeya Bata San iskanci idan Nadeeya ta zauna ta tayata aikace aikacen gida laifine.?
Naseer Bai dai tanka mata ba ya d'aura alwala ya tafi massallaci sallah Magriba
Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi sallah Isha ya tsaya a shago ya Dan Yi aski.
Daga nan ya Kara sa Bakin titi yayi siyayar da duk zaiyi a wani shago Dan da safe yake San suje wajen Naeema.
A shagon ya bar kayan akan gobe idan zai wuce zai dauka.
Ya dawo gida ya tarar da Safiyya tasa Nadeeya ta wanke Mata Kaya tana ganin ya shigo ta hau zunduma kuka
Sabida har Dan zaneta sai da Safiyya tayi.
Naseer kuwa a fusace ya Shiga har d'akin Safiyya ta buya a bayan Hajara
Naseer kuwa hakan Bai hana ya cire belt ya tsula Mata ba
Hajara sai Masifa take akan me zai daketa Dan ta daki Nadeeya ai Nadeeya Bata da kunya ne.
Haka ya fito daga d'akin Ransa a bace
Ya rik'e hannun Nadeeya sukayi d'akinsa.
Nadeeya kuwa ta hau ce Masa ya Kai ta wajen Umma Aunty dukanta takeyi.
Murmushin Naseer yayi yana ",Kin fasa Zama a wajena"?
Gyada Masa Kai tayi ya saki dariya Yana "daga aunty ta dakeki shine Zaki gudu ki barni"
Kara gyada masa Kai tayi tana ita dai ya kaita wajen Umma.
Naeema
Sosai naji dadin makarantar da yarana ke zuwa da alamu Kuma suna Gane abinda ake koya musun
Har islamiyya na Nemo musu idan suka dawo daga Boko sai su wuce sai karfe shidda suke dawowa.
A yau ma bayan na rakasu har makaranta gida na dawo na gyara ko'ina Hassana Bata Nan ta tafi bikin Yan uwansu Nima sai anjima Zan je idan yarana sun dawo daga makaranta Dan yau ba islamiyya.
Isihune keta markaden.
Ni Kuma duk abinda aka zo siya Zan fita da kaina na bayar dayake na fitar da kofa ta cikin gida.
Gidan na gyara na Dora ruwan tea Dan nida Isihu bamu karya ba
Zobon Dana hada na kukula na zuba a kula na Kai bakin shago Dan Sana'ar zobon shima ya karbeni alhamdulillah duk da Ina siyar da lemon kwalba
Duk Sana'ar Dana Dan gwada Allah Yana Sanyamin albarka
Zuwa yanzu engine markaden nawa ma biyune
Har kujeru masu Dan saukin kudi na saka Mana a gidan
Isihu na mikawa shayinsa ya fita shago
Ni Kuma na koma ciki na Shiga wanka Dan nasan kafin na fito shayin ya Dan hucce.
A band'akin d'akina na Shiga wankan Ina fitowa Naga Naseer a zaune a Gefen gadona Waleed rik'e a hannunsa.
Wani irin ihu na kwalla na koma band'akin aguje Dan gani nake gamo nayi idona yake ganemin Kamar Naseer na gani..............
*AYIMIN HAKURI BANJI DADI BANE JIYA SHIYASA AKA JINI SHIRU SHEKARANJIYA KUMA AIKI NAYI NAGAJI SHIYASA BANYI POSTING BA INA MASOYAN SADNAF TRUE LOVERS NGD DA KAUNARKU A GARENI KU DIN MASOYANA NE NA HAKIKA BAZAN MANTA ALHERIN KU A GARENI BA ALLAH YASAKA DA ALJANNATUL FIRDAUSI YA BAR ZUMUNCI*
*WANAN SHAFIN NAKINE UMMA YAHAYA MUSA NGD DA KAUNARKI A GARENI MAI KAUNARKA SHI ZAIYI TUNANIN KYAUTATA MAKA ALLAH YA FARANTA MIKI NGD*
*NAGA TA KAINA GRP 1 KUN NUNA MIN KAUNA KUMA NGD SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI*
*SAKON GAISUWA GA DUK MASOYANA*
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 43*
Muryar Nadeeya dake dariya tana Umma mune fa
Yasa kirjina ya bar buguwa na sauke ajiyar zuciya na bud'e k'ofar Ina mamakin yanda suka Gane gidan.
Nadeeya ma Sam ban lura da ita ba
Ko kadan ban sa Rai da zuwan Naseer gidana kurkusa ba
Ban kalli B'arin dayake ba na fito
Nadeeya dake zaune dirshan a kasan d'akina na nufa kofin shayin Dana ajiye da zumar na Sha shine a hannunta,
Gaisheni Nadeeya ta hau Yi
Ni kuwa nace "Yar babanta Mai kikazo nema wajena acici daga zuwanki kin dau min shayi"
Duk maganar da nake wayancewa nake Dan bana San hada ido da Naseer dake ta kallona kamar ya hadiyeni.
Nadeeya uwar surutu take ta hau zuba tana surutu har da dukan da Safiyya ta Mata jiya ta sakata wanki
Naseer kuwa yace mata "uwar surutu fita waje kiyi Wasa daga zuwanki kin hau surutu".
Kofin shayin ta d'auka tayi waje.
Ni kuwa nasan dalilin dayasa ya koreta
Sai data fita na juyo Muka hada Ido
Na saki murmushi na gaishe shi bai amsa ba ya Ajiye Waleed dake hannunsa ya nufo wajena
Wai sai na tsinci kaina Kuma da Jin kunya Yara shidda Yana Abu kamar wani saurayi ko sababin Aure
Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya rungumeni Nima rungume shin nayi Dan nayi kewarsa har ga Allah muna San junanmu Umma ce ta dage sai mun rabu
Mun dau tsawon lokaci a Haka sai danaga Yana neman wuce gona da iri na janye na koma gefe baa San Ransa ba ya koma bakin gadon ya zauna ya Kara d'aukar Waleed Yana "Ashe a garin Nan kike shine baki gayamin ba ai da tuni Nazo"
"Ai bazan so kazo ba sabida Kar Umma tagane Ina Nan din Dan nasan Idan tasan Ina kano Kai kanka bazaka samu kwanciyar hankali ba
Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya hau karewa ko'ina kallo Yana "Naeema kinyi kokari duk da Baki tafi da komai ba shine har Kika siyi kayan gida Haka Ina yaran nawa suke ganinki ma yasa na manta ban tambayesu ba"?
"Suna makaranta"
Washe baki yayi cikin murna Yana "Allah ya saka da alheri ya Kara bud'i naeema hakika ke matar rufin asiri ce Umma bansan Mai yasa ta kasa ganin haka ba.
Yanzu ma Naga engine dinki ma biyu anan har da shago a k'ofar gida
Gyada Masa Kai nayi na hau bashi labarin komai har gidan da muke ciki yanda na siya da kudin gadona.
Sosai ya ringa murna yanda Allah ya bud'amin yace "Ni kuwa ba irin wahalar da ban Sha ba Naeema Amma kudi yak'i samuwa aikin ginin ma da nakeyi wlh bai taka Kara ya karya ba Nima kudin da Kika ajiyemin naso Na juya Amma abin bai yu ba"
Murmushi nayi Ina "Karka damu Allah na sane dake watarana sai Labari insha Allahu ka cigaba da gayawa Allah"
Gyada min Kai yayi ya nuna min manyan ledojin daya zo dasu Akan na duba.
Bud'ewa nayi na hau fito da kayan ciki
Kayan sawa ya jiddowa Waleed su zahira ma Bai barsu a baya ba sai turmin zani da undies da ya siyomin nima.
Dagowa nayi da zumar nayi magana ya girgiza min Kai akan Kar nace komai.
Idan nace banyi murnar ganin mijina ba nayi karya Ido nake ta daukewa da naga Yana ta nunamin Yana bukatata Dan ban shirya tarben nasa ba haihuwa na Allah ne bana San nayi ciki yanzu kullum adduata ma Allah yasa haihuwa ta tsayamin kenan
Duk yanda naso Bijirewa sai da na barshi ya samu nutsuwan
Nayi sauri na fada bandaki nayi wanka na fito shi Kuma bacci ne yayi awon gaba dashi
Hakane yasa na dau Waleed muka bar d'akin na rufo Masa Kofa
Waje na fita na tarar da Nadeeya nata zuba ita da Isihu ga layin markade Nan suna jirana
Dan shagon ma a cike yake da mutane masu siyan Abu
Isihu na fama da mutane ahaka yake biyewa Nadeeya dake ta bud'e alewa tana Sha
Tsawa na daka Mata Akan ta fito Dan Nadeeya dai ba yarinya bace sosai
Engine na kunna nace ta hau markaden Dan wani zubin Tana Yi tsayine dai Bata dashi sosai Amma inta taka Abu shikenan
Sai danaga ta markada biyu
Naga Kuma ta markada yayi laushi.
Na koma kitchen na fara had'a hadan girkin Rana
Yanda dai na Saba Miya Mai yawa anan ma Haka nakeyi Dan nafi ganin aukin kayan miyan idan na siya da yawa ganin inada miyan yasa na Dora Mana shinkafa.
Na fito wajen Isihu na bashi dari biyu ya siyomin naman Miya
Wanda a lokacin Naman dari biyu Mai balain yawa ne
Sosai na tsinci kaina cikin farincikin ganin Mijina da kuma iyalina guri daya yanda nakejin kadaici tunda na dawo gidanan
Zuwan.naseer yau yasa naji na daina Jin kadaicin
Inama mu dawwama Haka Astagafurullah a wanan lokacin har sai danace inama Umma ta mutu mu samu kwanciyar hankali Dan itace babbar matsalar mu.
Naseer kuwa baccinsa yake Sha Mai dankaren dadi daya Dade baiyi irinsa ba.
Dawowarsu Zahira daga makaranta da ihun murnar ganin Nadeeya yasa ya farka daga baccin daya daukeshi.
Mik'ewa yayi zaune Yana murmushin Jin dadi Dan har ya fidda rai Kara kasancewa da iyalinsa waje daya rigarsa ya saka ya fara k'ok'arin fitowa.
Su Zahira suka Fado dakin gabadaya suna ihun murna Nadeeya tace da abbansu Suka zo
Naeema kuwa duk yanda taso hanasu Shiga d'akin ko sauraranta basuyi ba Suka fada d'akin
Cikin murna duka Suka rungumeshi.
Shima Naseer cikin tsananin farinciki ya rungumesu sai dayaga suna neman kayar dashi ya janye jikinsa ya zauna a gefen gadon hannunsa cikin Na Raheema dayaga har wani kib'a tayi sabida kwanciyar hankali
Binsu ya ringayi da kallo cikin tsananin farinciki ganin yanda Suka canja gabadaya sunyi fes dasu ba Kamar lokacin da suke can wajensa ba
Zahira har canjawa tayi a idonsa ta zama budurwa Dan ita Bata Yi haukan da taga kanenta nayi ba inama ya dauwaama Haka daga shi sai iyalinsa da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi duk Wanda ya tsinci kansa da karayar arziki irin nasa mutum.kan dauwaama bashida wani buri daya wuce kudin su dawo wajensa kota halin k'ak'a ne Amma shi karayar arzikinsa Bai dameshi Kamar yanda rabuwa da iyalinsa ya dameshi ba.
Da tarin kudi gwara ya dauwama da iyalinsa cikin rufin asiri.
Sai da Naeema ta shigo d'akin ta koresu kafin Naseer ya samu ya Shiga wankan ya dauro alwala
A palon gidan yajasu Sallahr azahar.
Suna iddarwa Zahira taje kitchen ta d'auko musu abinci har da zobon da Naeema ta had'a.
A faranti daya sukaci abincin gabadaya duka fuskarsu dauke da farinciki Naseer da Naeema ji suke.inama su dauwaama Haka ba abinda zai sake rabasu.
Su kansu kasancewarsu waje daya yasa yaran cikin tsananin farinciki sai cewa suka Abba Dan Allah ka zauna anan Kar.ka Kara komawa.
Yinin bikin da Naeema Bata je ba kenan
Bayan tafiyar yaran islamiyya har da Nadeeya
Hira Naseer da Naeema suka.hau yi Inda Naseer Duk yake Bata labarin halin da yake ciki da Hajara da yanda ta matsa Masa yayi wa Safiyya kayan daki.
Sosai nayi murnar da auren da Safiyya zatayi Dan gani nake Rabin matsalar mu ya k'au sai dai Yar muryar da Naseer kemin akan idan inada kudi na bashi ya Basu zai bani idan ya samu yasa na hade girar sama da kasa nace Masa banidashi Naga duk halin da muke ciki su suka jawo Mana ko Naman jikina nake yanka musu ba burgesu nake ba Dan Haka ko sisina bazan iya bayarwa ba
Naseer Bai ja zancen ba dayaga yanda na hade Rai muka cigaba da Hira da aka fara kawo markaden yamma kuwa shi yaringayi Ni kuwa na Dora Mana girkin dare
Dan inaso ya cika cikinsa kafin ya tafin nasan yanzu tunda yasan gida zai na zuwa ganinmu akai akai hankalina yanzu a kwance yake.
Sai dai me a lokacin da muka ci abincin daren da nayi tunanin Naseer zai tafi k'in tafiya yayi yacemin kwana zaiyi na Bari ya Dan samu kwanciyar hankali na kwana biyu Dan idan ya koma gidan ma yasan bashida kwanciya hankali Umma Sako shi zatayi a gaba.
Ni kuwa.dage Masa nayi ya tafi Dan idan Bai tafi ba Umma zata xargi Yana wajenmu kafin kaceme zata gano Inda muke.
Ba yanda banyi ya tafi ba yak'i dayaga ma na dameshi sai ya shige daki ya barni dayake a tsakar gida muke Zaune.
Ba yanda na iya ahaka na hakura yarana Suka kwana a d'akin da hassana ke kwana nikuma da Naseer da Waleed muka kwana a nawa d'akin
Namiji a gida ma wani abune Dan a ranar ko juyi banyi ba har gari ya waye Ina rungume a kirjin mijina.
Har makara nayi Dan sai wajen bakwai da rabi na farka.
Agurguje nayi Sallah na fito sabida Na Dora musu abinci su karya su tafi makaranta.
Sai dai Ina fitowa ma na tarar suna cin abincin sun ma saka uniform sosai naji dadi Dan yanzu Zahira duk ita kemin komai tama Riga da tasan duk abinda nakeyi da safe Inda yarinya ta Kara kwanta Min arai fiye da sauran kanennta kenan.
Nadeeya ce kawai Bata saka uniform ba hakane yasa na Shiga na koma d'akina na dauko uniform dinta na Bata Dan Dama an bani uniform dinta littattafai ne ban siya Mata ba
Sai da suka shirya tafiya na koma daki Naga har lokacin bacci Naseer keyi Bai tashi ba
Tashinsa nayi na fito na raka su har makaranta na karbawa Nadeeya text books Dan na Bata littattafai da pencil
Primary 4 aka Kai Nadeeya da aka Mata gwaji.
Sai da duk suka Shiga aji na dawo.
A takaice tun Ina damun Naseer akan ya koma sabida Kar Umma ta gano muna tare k'i yayi akan Dole na hakura ya Mana sati daya
sati dayan da naji inama mu dawwama Haka batare da ya Kara Mana nisa ba inama Umma ta Sanya Mana albarka Naseer ya ringa Zama a shagon k'ofar gida.
Ni Kuma na ringa markade Ina kananun Sanaa a gida da nakeyi yanzu kudi na shigomin da nasan sai munfi kowa farinciki tunda munfi karfin ci da Sha alhamdulillah
Shima Kamar bazai tafi ba sai Dana karfafa Masa gwiwa akan ya tafi idan yaje yace Abuja yaje neman kudi na Kuma bashi Yan kudaden dai da Bai taka Kara ya karya ba.
Dan sati dayan dayayi har Dan murmurewa yayi.
Sai daya hau taxi na dawo gida duk jikina ba dadi
Dan nasan yau sai dai na rayya Daren dadin ma.danaji yace zai na zuwa ganinmu kullum idan Bai zo bama kullum xai na zuwa akai akai
Safiyya
Sosai ta Sako Hajara a gaba da kananan koke koke Akan Aurenta na matsowa Anki a Mata kayan daki
Hajara kuwa sosai itama ta damu da kukann da Safiyya keyi hakane yasa ta Sha alwashin tarar Naseer a Daren da Bai kwana a gida ba Akan idan ya dawo yasan duk Inda zai nemi kudi ayiwa Safiyya kayan daki.
Sai dai Haka Suka karaci zaman jiran dawowarsa Bai dawo ba daga shi har Nadeeya.
Washegari ma Haka hakane yasa hankalin Hajara ya fara tashi tana tunanin Inda Naseer yaje shi da Nadeeya
Safiyya kuwa kuka ta saka Akan Naseer guduwa yayi ita.kam ta Shiga uku ta lalace asirinta zai tonu.
Fadar hakan da Saffiya tayi tana kuka wiwi yasa hankalin Hajara Kara tashi tana "Yanzu sai Naseer ya gudu sabida nace ya Miki kayan daki Safiyya ko dai wajen Naeema yaje ba guduwa yayi ba"
"Guduwa yayi Umma Dan idan Kika tuna Bai tashi guduwa ba sai daya ga kin Kara Masa maganar kayan dakin nidai Umma wlh kisan duk yanda zakiyi Dani Aurena nata matsowa ace ko cokali Baki siyamin ba karki manta fa kishiya ce Dani tayaya ma zanyi aure batare da kayan daki ba da kunya na tareshi nace Masa an kasa.min.kayan d'aki"
Safiyya tace tana Kara fashewa da kuka
"Ki bar kuka Safiyya nace ko wajen kanin mahaifinku zamuje muga ko zamu samu wani Abu"
Wani irin harara Safiyya ta d'auke Hajara dashi tana"kin manta katifa kawai ya siyawa Lami Taya zanje na same shi wlh bazan je wajensa ba"
"Toh yanzu ya zamuyi Safiyya kinsan dai banida ko sisi gashi Da Naseer na dogara shi Kuma kince guduwa yayi
Tijjani kuwa Dama ba mutunci ne dashi ba kinsani Dan Dana Masa magana anan dariya ya ringamin ya maidani mahaukaciya Haka ma.ya tafi ko sisi Bai bani ba Naseer ne dai zai iya kukutawa ya Miki kayan gashi yanzu wajen kwana biyu kenan bai dawo gida ba"
"Yanzu ya zamuyi toh Safiyya "
"Nidai a siyar da gidanan Umma a fitar Dani kunya idan ba Haka ba kinsan ba Inda zamu samu kudin da zaa siya min kayan daki"
Gwallo Ido Hajara tayi tana "A siyar da gidan Naseer Kuma Safiyya Taya Zaa siyar da gidan Naseer kawai Dan a Miki