Showing 123001 words to 126000 words out of 180103 words
zasu iya jefani a ciki
Umma cikin wani irin murya tace "Naeema sai kinyi danasanin korarmu da kikayi wlh ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayanki ba dai mu Kika Kora ba wlh Zaki gani"
Umma tace tana yin waje Ni kuwa nace "Insha Allahu ba Abunda Zaki iyamin alheri Zan gani idan Allah ya yarda"
Hannuna Zahira ta ringa ja Dan har fara hawaye
Safiyya kuwa idonta ya sauka Akan Zahira da ta Dade Bata ganta ba wani irin murmushi naga ta sakarwa Zahiran daya sa naji gabana ya tsinke kamar wancan lokacin da idan zasumin mugun Abu kirjina ke tsinkewa.
Tura Zahira daki nayi da Sauri na fito daga d'akin ina "Dalla fitarmin daga gida"
Na karasa wajenta Ina turata waje
Ita kuwa ta Kara sakar min murmushi tana "ki shirya tarbar balain da zan jefo Miki"
Daga Haka ta fice waje.
Ni kuwa na rufo kofata Ina adduar insha Allahu ba balain da Zan gani
Hajara kuwa Tana fita ta hango Naseer daya kusa Isa bakin titi ta dib'a aguje ta bishi abaya.
Tana kwalla Masa Kira.
Naseer Bai tsaya ba har sai data cimmasa ta zub'e a gabansa ta fashe da kuka tana Kar ya tafi ya barta ya rufa Mata asiri Bata da kowa sai shi.
Kafarsa ta rik'e tana rusa uban kuka.
Naseer kuwa hankali a tashe ya Ajiye bakonsa Yana "Umma Mai Haka Zaki taramin jamaa Dan Allah ki mike tsaye wlh Umma Nima bansan Inda zanje ba Ina Zan tafi dake banida gidan da Zaki zauna umma wlh wancan gidan na Naeema ne Dan Haka ki koma gidan Tijjani ki zauna kafin na samu wajen Zama"
"Aaa wlh Dana zauna a gidan Tijjani gwara na kwanta a bakin titi kasan wuyan da muke Sha kuwa agidnsa Tijjani Bai d'aukeni da daraja ba a gaban idonsa matarsa ke azabtar damu Baya ce Mata komai idan na Masa magana sai yace Baya San takura ai Allah ya Isa no-no na da Tijjani ta Sha"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Wai Mai yasa burinki ki yiwa yaranki mugayen kalamai Umma a cikin mu hudu waye Baki yiwa Baki ba Umma kinsan bakin uwa kuwa daidai da shedaniyar yarinya can Haka Kika Yi ta Mata Baki gashi baa je koina ba Aurenta ya mutu ta dawo gabanki da ciki Umma bahaka uwa take wa yaranta ba Umma Yara koda kuskure suke Yi addua ya kamata ki bisu dashi gashi duk kin Mana baki Umma kema abin na shafarki"
A takaice Haka Hajara ta marairacewa Naseer da kuka har sai daya kaisu gidan wani da suke mutunci dasu Akan su kwana daya kafin ya samo musu Inda zasu zauna ya rasa yanda zaiyi da Hajara.
Gidan da suka sauka.kuwa tarb'a Mai kyau aka musu sai da suka ci abinci nutsu suka hau hirar Naeema da irin Abun da zasu Mata idan sun samu wajen Zama.
Shawarar da Safiyya ta kawo akan Naeema ne yasa Hajara mik'ewa ta taka rawa Dan idan suna San su cimma burinsu wajen tarwatsa rayuwar Naeema sai sun hada da makirci tamkar yanda Murja keyi.
Washegari Naseer ya samo musu gidan Haya Mai had'aka da.mutane da yawa a ciki daki dayane sai tabarma da ya saka musu Dan bashida kudin katifa
Cikin murna su Hajara suka koma gidan Dan gwara.munsu kwana a Kan tabarmar da dai zaman gidan Tijjani
Naseer kuwa ce Mata yayi shi a company da yake aiki zai ringa kwana tunda ta koreshi daga gidan Naeema
Budar bakin Hajara sai cewa tayi Kar ya wani damu ya koma gidan Naeeema su zauna ita dai fatanta ya ringa lekosu Yana kawo musu na abinci ya Kuma Bata jari tana siyar da kosai tunda ta lura gidan kowacce na Sana'a
Har hakuri ta bawa Naseer Akan wnan karin da gaske take yayi zaman aurensa da Naeema.
Naseer kuwa ya zub'e a kasa ya hau Mata godiya
*Chapter 3*
*Dama ku barni na huta sai bayan sallah na dawo muku da karfina Dan chapter 3 yafi na daya Dana biyu Kuma wlh na gaji**😟😟😟😟😟😟😟😟😟
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 47*
Nidai tunda Suka tafi naji hankalina ya tashi da irin kallon da Safiyya tayiwa Zahira da alwashin da suka Sha na ganin bayana dauriya kawai nake Amma bansan Mai yasa nake cike da fargaba da Kar su yiwa Zahira wani Abu ba Dan nasan halinsu nasan abinda zasu iya Yi na rasa wane irin masifa da balai ne wanan na rabu da Naseer ma na dawo gidan kaina Amma duk a banza hakan Bai saka sun sararamin ba nikam inaga sai na saka Naseer ya rubutamin takardar Saki na Kai musu sun ga shaida sanan zasu shafamin lafiya.
Ban damu da Rashin dawowar Naseer da sai daya kwashi kwana uku Bai lek'o mu ba Ni kuwa tunda Suka tafi na sake zage damtse wajen yin addua Ina rokon Allah Kariyarsa gareni da yayana addua ma ya Riga da ya zama jikina bana sake idan lokacin da nake tashi idan yayi sai na tashi daga bacci naje gaban Mahallicina
A Rana na hudu Naseer yazo.min da yamma bakinsa a washe ya hau bani labarin Umma ta bashi hakuri ta Kuma sawa aurenmu albarka Wai yanzu ba ta da matsala dani tunda ya Kama Mata gida ya Kuma Bata jari.
Wani irin murmushi takaici nayi ina "Umma ce ta baka hakuri akan ta Kuma yarda mu zauna ba matsala Naseer.kai Kuma sai ka yarda"
Dan rage faraa daya shigo dashi yayi ya cigaba da kallona
"Naseer halan ka manta wacece.umma Taya Umma zata ce maka Bata da matsala da zamanmu tare.har ka yarda Bayan gidana ta zo naki yarda su zauna Kuma Haka kawai sai tace ma ta sawa aurenmu albarka ka yarda Naseer inaga har yanzu baka San wacece Umma ba idan ka manta Ni ban manta ba idan kaga Umma ta biyo ta wanan fuskar toh wlh wani mugun abun zata Mana sai dai na roki Allah ya kareni da yarana haihuwar Minal Haka tace Mana tayi nadama Mai ya biyo baya guba ta zuba a kunnu ta bawa Safiyya ta kawomin.na Sha Akan zan samu ruwan no-no akan naki Sha Suka rufeni da duka Naseer har sai da ka shigo ka k'waceni a hannunta Naseer har ga Allah na gaji da abinda umma kemin wlh Nagaji na rasa wanan masifar da.mai yayi kama tunda na aureka ban taba samun kwanciyar hankali ba daga wanan sai wanan da Ido daya nake bacci sai a yanzu Dana fara samun nutsuwa Umma da Safiyya suka Kara durowa ranar da.suka.zo sun Sha alwashin ganin bayana Safiyya ta kalli Zahira ta girgiza min Kai Naseer idan wani Abu ya Samu yarana ko Ni wlh Tallahi bazan yafe wa Umma da Safiyya ba sai na Kai kararsu gaban Allah nidai ka koma wajenta kar.ma tayi tunanin kana gidan Nan ma ringa lek'omu idan ka samu sarari"
Na karashe Ina fashewa da kuka Dan har ga Allah su Umma sun isheni Naseer.ya bani takarda ta kawai na huta Zan jure komai banda su tab'a min yarana ba dole bane sai nayi rayuwa da Naseer auren Naseer ya isheni ya gundureni bazan karashe rayuwata Su Umma na wahalar Dani ba.
Naseer rarrashina ya hau yi Yana "Yana Naeema wlh da ikon Allah kawai nake rayuwa har.yanzu rabona Nima da kwanciyar hankali tun ranar Dana budi Ido nasan Umma a matsayin Mahaifiyata na Sha Zama nayi tunanin Anya Umma ce ta haifeni kuwa Dan har yau danake yawo.ban tab'a ganin Mai irin Halin mahaifiyata ba ko a tarihi Umma gaba take da kwanciyar hankalina nayi kukan nayi naseehan duk a banza Nima data ce min naje ba komai a zuciyarta nasan ta fada ne kawai Bai Kai zuci ba Amma koma menene Zan cigaba da Addu'a Allah ya shiryeta ta Gane gaskiya wlh Naeema nasan tsinaniyar yarinya Nan ce ke zuga umma.na balain tsanarta duk wani mugun Abu ita kesa Umma amma karki damu insha Allahu ba Abunda zasu iya Miki ko yarana kema shaida ce akan yanda nake Addu'a"
"Duk da Haka ka koma wajenta Naseer zamanka a gidana hatsarine"
Nace na mik'e tsaye Dan har ga Allah banasan zaman Naseeru a gidana Ni nasan zamansa a gidana sai saka Umma ta cigaba da nufata da mugunta
"Taya Zan koma gidanta alhalin haya na Kama Mata daki daya"
"Naseer kayi hakuri ka koma wani wajen da Zama ka ringa zuwa kana ganinsu Waleed wlh zamanka anan zai saka Umma ta ringa kuntata min Amma idan taga baka gidana Zan samu saukin wani Abun Dan idan ma Dan Kai zata min wani Abu idan.taga bama.tare zata kyalleni.
Rai a Dan bace Naseer ya mik'e Yana "Mai yasa kike sawa a ranki Umma zata iya Miki wani Abu duk wani Abu da kika ga ya samu bawa daga Allah ne Umma Bata Isa ta Miki Abunda Allah ya Bai hukunta zai sameki ba wuyanta ki dogara ga Allah"
"Naseer inaga ka manta Abubuwan da Umma tamin ne inaga ka manta Kuma wacece ita shiyasa kake fadar Haka ganganci ne ma na saki jiki nace Umma bazata min komai ba duk wadancan data min a baya ai ita ta ringa min Allah na kareni din"
Katseni yayi a tsawace Yana "kice na fita na bar miki gidanki kawia Naeema ba sai kin biyo min ta wanan hanyar kina fakewa da Umma ba Karki.manta Nima ba a San Raina nake zaune a gidanki ba Naeema a matsayinki ta matata Naeema kaddara ce ta hau kaina na rasa komai nawa amma.kinsan badan kaddara ba Ni Mai bawa wani kyautar gidane Amma ba komai Naeema Zan tafi bazan zauna a gidan naki ba Allah ya bani arzikin da Nima zanyi gidan kaina idan na samu sararin Zan ringa zuwa Ina duba yaran nawa kamar yanda kikace"
Daga Haka ya juya ya fice daga gidan Kamar zai tashi sama
Kan kujerar na koma na zauna Ina fashewa da kuka mumunan fassarar da Naseer yamin Dan har ga Allah bazai Gane Mai nake fada ba da abinda nake gudun Amma Ni nasan watarana zai Gane
Idan nace fushin da Naseer yayi Bai dameni ba karya nayi Dan Naseer nada hawan jini na Kuma San duk a dalilina yak'i rabuwa Dani yake ta fuskantar wadanan tashe tashen hankulan Amma Allah yasan na gaji bazan iya cigaba da jure abinda mahaifiyarsa kemin ba abinda na jura a baya bazan dauka yanzu ba sabida Kar ma ya fassarani yasa ban nemi ya sakeni a halin yanzu ba har sai idan ya Dan farfado daga karayar arzikinsa.
Ban Bari na saka wani damuwa a Raina ba na maida hankalina Kan sanaoina da yarana da na balain sawa ido.nake.kuma addua kariyar Allah a garesu
Safiyya da Hajara a hankali Suka fara karantar mutane da suke zaune dasu wayanda.zasu iya yin talatin sabida gidan katon gaske ne.
Wasu matan Aurene wasu zawarawa har da Yan bariki ma ahaka suke.gwamutse a gida daya.
Sati d'aya kawai da sukayi a gidan suka fahimci mutanen gidan basuda mutunci ko kad'an kowa ta kansa yakeyi
Ga balain Sa Ido da munafirci da suke dashi.
Amma ahaka Safiyya ke fito da tabarma bakin kofar d'akinsu tayi ta kallon mutane dake gidan tana musu shishigi tana Shiga abinda Bai shafeta ba a cikin kwana goma ta Gama Gane matan da suke da aure da zawarawa da Kuma Yan barikin
Akwai wata Iyyatu da hankalinta yafi karkata wajenta matar aurece Mai Yara biyu hatsabibiya ce lamba daya data maida mijinta tamkar yaron cikinta Dan mijinta shi yake Mata wanki ya Mata girki komai dai daya Kamata ace ita takeyi mijinta keyi ita kuwa Iyyatu tana zaune tana karkad'a kafa tana zuba mulki hakane yasa Safiyya fara shishige Mata Amma Iyyatu na shareta
Sai data Sha kwandunan wulakanci a wajen Iyyatun kafin ta fara sakar Mata fuska suna Hira sama sama ahaka har suka Saba Safiyya fa fara bugar cikinta Tana gaya Mata yanda ta mallaki mijinta ta hanyar wani kungurmin boka dan kafin ta aureshi Yana da Mata daya da Yara biyar daga shigowar ta gidansa ta asiriceshi ya saki matarsa ya Zama Kamar bawanta
Safiyya kuwa kamar ta Kama rawa take ta hau rokon Iyyatu ta sadasu da bokan.
Cikin kwana uku Hajara ta bawa Safiyya kudin mota itama zuciyarta cike da farinciki Dan kosai ma da ba wani ciniki take ba a kudin ta bawa Safiyya kudin mota akan taje.
Yanayin zaman munafirci da ake Yi a gidan yasa suka Gane Safiyya da Hajara basa sallah wanda take suka.hau kirnsu da basa sallah aka hau ma kyamatarsu Akan Dole Hajara da Safiyya suka hau sallah Dan su samu mutanen gidan su so su.
Safiyya kuwa Basu dawo
Gidan ba sai wajen Goman Dare.
Jiki a sanyaye Hajara ko Zama bata bari Safiyya tayi ba ta hau tambayarta ya sukayi.
Safiyya jiki a sanyaye tace mata "Hmm Umma mutumin ya iya aiki Dan ko shegiyar Shugaba Bata kamo kafarsa a iya aiki ba sai dai matsalarsa sai ka ajiye Masa mugun kudi Mai balain yawa Dan yau ma sai danaga Naeema da su Zahiraa Kwaryar ruwansa bance Masa komai ba ya hau bani labarin komai game damu da abinda muke San muyiwa Naeeman
Sai dai a dubawar da yayi Yaya Naseer baya gidan aunty naeema Yana wajen aikinsa anan yake.kwana kamar dai sunyi fada da Naeema ne"
"Hmmm daya kwana a gidanta da Kar ya kwana a gidanta wlh sai Naga bayanta tunda har ta koremu daga gidanta Badai yanzu tayi kib'a ta samu kwanciyar hankali tana ganin yaranta Agaban ta zuciyarta na sanyi ba zata Gane kurenta Dan ko cewa nayi a Kona arzikin ta bazata wani damu ba idan tana ganin yaranta agabanta Amma idan na hargitsa Mata lissafi fa zata Gane shayi ruwane yanzu dai a Ina zamu samu kudi a Mana aikin Nan Kinga yau ma ko cinikin kosai bamuyi ba yanda na soya Haka na shigo dashi shi zai xama abincin darenmu"
Umma kiyi karyar rashin lafiya kawai kamar Zaki mutu Yaya Naseer da Tijjani su Shiga su fita su nemi kudi Dan na matsu Naeema ta fara hawaye da idonta wlh wlh Umma banida burin daya wuce na samu cikar burina akanta dukan da Yaya Naseer yamin duk sai na dau fansar sa Akan Naeema"........
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 48*
Tuni Hajara kuwa ta hau rashin lafiyar karya
Safiyya ta tasa cikinta gaba ta nufi gidan Tijjani duk a firgice Kamar gaske.
Wajen karfe biyar na yamma ta Isa gidan
Sai dai tana zuwa gabanta ya yanke ya Fadi.
Dan Naseer da Tijjani ta samu a k'ofar Gidan suna zaune a Kan tabarma
Tuni jkinta ya dau rawa kamar ta juya Dan idan akwai Wanda take balain tsoro Bai wuce Naseer ba sosai take.ganin kiyayar da yake Mata a idonsa.
Sam Bata kawo zata sameshi anan ba Dan so tayi ta gayawa Tijjani shi Kuma ya gayawa wa Naseer.
Har ta juya zata koma ta tuna yanda take San ta samu cikar burinta akan Naeema.
Wajensu ta nufa tana matsar hawaye kamar irin ta Dade tana kukan Nan
Tana Isa gabansu ta zub'e ta hau sheshek'ar kuka tana "Yaya Tijjani Yaya Naseer umma na kwance tun jiya ba lafiya sai suma.take.ku taimaka Mana Kar ta mutu"
Naseer Bai kalli Inda take ba Dan sabida tsanar da yayiwa Safiyya yasa ma Baya Shiga gidan ko kadan Baya San ganinta.
Sai dai ya tura a kaiwa Hajara Dan kudin kashewa
Wani irin kallo Tijjani ya watsawa Safiyya dake.ta sheshek'a.yana "toh Dan Bata da lafiya shiyasa Zaki dira gabanmu Haka a firgice ba Sallama yanzu da Kika zo Nan mu zamu Bata lafiya uban me ya Hana ki kaita asibiti da yanzu bama Nan ya zakiyi kenan"?
"Yaya banida ko sisi shiyasa ban kaita asibiti ba"
Tsaki Tijjani yayi ya k'au da.kai Yana Allah ya sauwake
Naseer kuwa ya saka hannunsa a Aljihu ya Ciro duk kudin dake jikinsa ya mik'awa Tijjani Yana Bata ta Kai ta asibiti gobe na dubota Dan yau aikin kwana nake"
"Kai kake wahalar da kanka Yaya Naseer Ni ban yarda da shegiyar yarinya Nan ba tashi muje Naga jikin nata
Ya maidawa Naseer kudinsa.
Safiyya mik'ewa tayi da Sauri tana ji kamar ta rufe Tijjani da duka a ranta kuma sai zagin Naseer da shima take Jin kiyayarsa a ranta take bakin cikinta ma ko kallonta baiyi ba ballantana yayi tunanin binta suje gidan Hajara ta tilasta Masa Nemo kudi ya kawo Mata Dan.tasan Tijjani shegen kansa ne Bai Zama lailai ya bada ko.sisi.ba.
Tana ji tana gani suka hayye vespan Suka tafi
Naseer Kuma ya mik'e ya nufi titi dan.ya koma wajen aiki
Tijjani.ke tilasta Masa zuwa.gidansa cin.abincin Rana Dan ba Abunda ya b'oye Masa game da abinda ya had'ashi da Naeema da hutun da yake so ya Bata tasamu kwanciyar hankali kafin ya koma gidan.
Safiyya ce tayi ta Masa kwatance har suka iso gidan
Yanda Tijjani ya had'e.rai Yasa tayi gaba ya bita a baya tana Addu'a Allah yasa Hajaran a kwance take Kar ta tona musu asiri.
Sai dai suna zuwa suka ga Hajara tayi dare dare a tsakiya d'akin tana ta zabga Loma abincin da ta siya Dan taci kafin Safiyya ta dawo Dan idan ba cika cikinta tayi ba Safiyya na iya rabata da kudin hannunta ta siyi abinci ita Kuma ta barta da Shan garin kwaki ko sandararen kosai.
Shigowar su Tijjani yasa ta ture abincin da Sauri ta hau yamutsa.fuska
Tijjani kuwa Safiyya ya kalla Yana "Inaga daga fitarki umma ta samu lafiya ko tunda gashi har abinci Naga take ci Umma ya jikin naki Tijjani yace Yana guntsa dariyar Dan sosai ta dage take yamutsa fuska.tana kakarwa ga hannunta duk.miya da Gefen bakinta
Safiyya kuwa kamar ta fashe Dan bakin ciki sai hararar Hajaran take.
Tijjani kuwa ya Kara cewa " toh nidai Bari na tafi Umma Bari na siyo Miki pcm na kawo Miki inaga zazzabi ne"
Bakin ciki ne yasa Hajara mik'ewa ta hau zagin Tijjani
Tijjani kuwa ya karasa Kan tabarmar ya zauna Yana dariya
"Ka