Showing 126001 words to 129000 words out of 180103 words
dauka.wasa nake maka ko ka tashi ka fitarmin daga gida.
Wlh yanda nakejin zuciyata Tijjani Zan iya fasa.maka Kai
Tijjani hannun Hajara.ya ruk'o.da k'arfi Yana cigaba da dariya har.sai daya zaunar da ita Yana
"Allah ya bar.mana ke hajiarmu kiyi hakuri muyi magana"
"Umma Dan Allah Dan annabi na hadaki da girman Allah ki daina duk abinda kike wa Yaya Naseer da matarsa Umma na rasa Mai Yaya Naseer ya Miki Kika saka shi a gaba kika.hana shi zaman lafiya da matarsa,
Umma yanda kike da hakki Akan Yaya Naseer shima Yana da hakki akanki Umma karki biyewa tsinaniya yarinya Nan ta Kai ki ta baro tun muna Yara nasan yarinya Nan Shaidaniya ce babu alheri sam.a ranta Umma komai Naeema ta Miki ya Kamata ace kin hakura ko Dan zuria dake tsakanin ita da Yaya Naseer a iya sanina ba abinda ta Miki shima.yaya Naseer ba Abunda ya Miki da ya cancanci Abubuwan da kike Masa Umma har gidansa daya rage Masa kuka.siyar da.ke da shegiyar.yarinya Nan Umma idan ba Yaya Naseer ba wa zakuyi.wa.haka ya barku"?
"Umma duniya ga ba gidan Zama.bane wlh watarana dole.mu mutu mu koma ga Allah Allah ya hallicemu ne Dan mu bauta Masa Umma.Allah baya san.zalinci ki daina amfani da.ikon da Allah ya Baki akan yaran ki.ki ringa cutar.dasu Umma Ni.ba yaro bane.duk.abinda.kikeyi ba akan daidai.kikeyi.ba ya Kamata ki gyara.kafin lokaci ya kure Miki Umma yau ba Dan kin Kona dukiyar Yaya Naseer ba da kema.kanki Baki tsinci kanki a irin wanan gidan Sabida wani.biyan bukatarki kiyi.karyar.ciwo ba umma nidai shawara ce nake Baki kibi Allah da manzonsa.ki tsarkake zuciyarki ki zauna da.kowa.lafiya ki koma.ga Allah kalau Umma mutum.da kansa yake Gina lahirarsa idan ya gina da kyau kiga da kyau idan ma.baki Gina da.kyau ba Umma ke Kadai Zaki zauna a kabarinki ki guji.hawayen.wanda Kika zalunta Dan idan.ya barki da Allah wlh Sai Allah ya saka Masa ko bajima ko ba Dade Umma wlh akwai rayuwa Bayan mutuwa wayanda suke kwance a kabarinsu karki gansu a kwance ki dauka bacci sukeyi wlh rayuwa ce sukeyi Mai tsayi cike da irin Rayuwar da.sukayi a duniya Wala khairan ko sharran
"Umma.kiringa sallah kiringa azumi ko Zaki samu haske a rayuwarki ke Kuma Safiyya Ina tausaya Miki wlh Dan ke macece bakisan ya gaba Zata kasance Miki ba nasan halinki gabaki daya daga auren da kikayi Kika fito.ya isheki ishara.kigane ba akan daidai kike ba duniya gidan aro ce duk sharrin da kikayi ko Wanda Zaki saka ayi wlh zai dawo kanki ko bajima.ko ba Dade.
Umma Dan Allah kiyi hakuri ki yarda makamanki Allah yayi aure Bai Kare tsakanin Yaya Naseer da Naeema ba ki Sanya musu albarka sukoma su zauna idan Baki sani ba ki sani Yaya Naseer Yana d'auke da hawan jini tunda kuka siyar Mai da gidansa yake fama da ciwon kirji umma.naseer dinan ke Kika haife shi ya Kamata ki tausaya.masa iya abinda Kika Masa ma.ya Isa Ni Zan tafi umma.ga wanan ba yawa Zan ringa lek'o ku akai akai"
Daga haka Tijjjani.ya mike ya fice daga gidan.batare da ya ko kalli Safiyya data sada Kai tana tsine Masa ba.
Hajara kuwa kamar wacce aka sawa Gam aka like Mata Baki Haka ta bi Tijjani da kallo Yana fita
Safiyya taja uban Tsaki Tana "kawai Dan ance su kawo kudi ya hau waazi sabida tsinannen rowa ke Kuma Umma sai kikayi shiru Kamar bakida Baki"
"Taya duk abinda Naeema ta.mana ma.mu kyalleta korarmu fa tayi.daga gidanta Yaya Naseer ya zabeta akanki daya rabu da ita har.ya gwammace ki Masa baki keda danki wata ta kwace Miki shi nidai karki sake ki saurari wanan Yaya Tijjanin bakinsa daya da Yaya Naseer Naeema ma.tana ganin Haka zatace taci Galaba akanki"
Hajara sosai maganganun tijjani.suka shigeta hakane yasa jikinta Yi sanyi idan akwai abinda taji ba dadi Bai wuce Naseer data zalinta ba ta hanyar siyar Masa da gidansa
Amma Naeema Kam ba abinda zaayi taji tana Santa Dan abune kamar ya tsaya Mata a kahon zuciya har sai ta fito dashi zata ji dadi fitowar kuwa shine ta samu cikar burinta akan ganin Bayan Naeema da take ganin ma duk halin da take ciki yanzu itace sila maganganun Safiyya Kuma ya Kara.tunzurata tana ganin tabbas idan ta bar Naeema ma taci Galaba a kanta abu daya ne tasan zatayi shine ta daina takurawa Naseer akan Naeema Amma fa Naeema sai ta kwashi kashinta a hannu
Sannan sallah da azumi da Tijjani ya Bata shawarar ta ringayi zata ringayi Dan babanta cikakken musulmine Mai addini ko Kafin ta hadu da Yan kungiya tana sallah shigarta kungiya yasa ta daina sallah Amma yanzu zata cigaba da sallah da duk wani Abu da musulmi zaiyi na ibada tunda Bata cikin kungiya yanzu.
A takaice Safiyya sai data Kara taso da maganar kudurinsu Akan Naeema data ga Hajara tayi wani sanyi
Tsabar bakin Hali da mugunta ita ta cigaba da neman kudin da zata kaiwa bokan da zai Mata aiki akan Naeema
A cikin irin wanan halin ta haihu Inda ta samu da namiji ta saka Masa suna Bashir
Tunda Safiyya ta haihu duk rayuwarta ba abinda take so sama da Bashir danta sosai take cin burin inganta rayuwar Bashir Amma tana burin tarwatsa rayuwar yaran naeema.
Ko arbain bata yi ba ta samo wani gida ta fara aikatau duk Wai Dan ta samu kudin da zata kaiwa boka ya Mata aiki
Akan Naeema Dan duk wani motsin Naeema ta sani duk da tazarar dake tsakaninsu.
Hajara kuwa itama.tana.kan.bakanta akan Naeema da yarta Zahira Amma Bata matsa can Kamar yanda Safiyya ta matsa ba Dan abinci ma wahalar samu yake.mata Dan aiken da Naseer da Tijjani ke mata ma idan Safiyya ta kyalla Ido taga kudin to Bashir zata kashewa kudin tana ji tana gani Bata Isa tayi Magana ba.
Naeema
Ban fasa adduoina akan yarana ba ban Kuma takura kaina da tsawon lokacin da Naseer ya d'auka Bai lekomu ba duk da Naseer Yana Raina inaso.naji ko lafiya yake.
Ga yaransa.dake.balain takuramin da tambayarsa balle Nadeeya da har sai na hada Mata da Bugu wani zubin take kyalleni sadaka kuwa bana Wasa dashi.
Dan Indai Zan tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira sai kirjina ya buga
Gashi zahira girma take tana Kara Zama kyakyawar budurwa.
Kullum sai an aiko ana Sallama da ita bakina har gajiya yake wajen cewa bana barinta zance
Kuma.masu neman zahiran manyan mutane ne masu kudi daga Mai Mata sai samari.
Yau daya kasance alhamis Ina zaune a tsakar gida Ina Yankewa Waleed farce shi da Raheema Zahira Kuma tana kitchen tana girki
Nadeeya kuma tana wanke musu uniform dinsu tana ta zabga surutu a cikin surutun nata naji tana "Dazu fa Naga Aunty Safiyya a Gefen makarantar mu tana lek'omu tana ganin na ganta ta b'uya da Sauri"
Cikin fad'uwar gaba na ajiye rezar hannuna Ina "kin tabbata Anty Safiyya Kika gani Nadeeya ba Mai Kama da ita Kika gani ba"?
"Tab Umma ita na gani Mana sau uku kenan. Ina ganin ta idan taga na ganta sai ta b'uya mantawa nake ban Gaya miki ba sai Yau na tuna"
Haka kawai naji hankalina ya tashi Dan Ni nasan ba alheri ne yake Kai Safiyya makarantar yarana ba har na Dan saki jiki danaga an tafi shekara ba abinda ya biyo baya Kuma abinda ya bani mamaki Bai wuce yanda take zuwa makarantar ba lura da ba unguwar mu daya ba Dan Isihu ya bani labarin suna zaune ne acan tsohuwar unguwarmu Dan Yana yawan zuwa gidansu aunty duk inada labarin zaman da sukeyi a can da haihuwar da Safiyya tayi da aikatau din da takeyi ita Kuma Umma na siyar da kosai a bakin titi
Labarin Naseer ne kawai bani dashi
Zurfin Dana Yi a tunani yasa Sam bansan Naseeru ya shigo ba sai ihun yarana naji suna ihun murna Abba
Gabadaya zuwa sukayi Suka rungumeshi sun ma ki Bari ya Ajiye manyan ledojin daya shigo dasu.
Ni kuwa Ido kawai.na zuba Masa Ina kallonsa ba laifi ya Dan ciko ba Kamar kwanaki ba Kuma har ga Allah naji dadin ganinsa
Ido muka had'a ya Dan saki murmushi Yana "Hajajju Mai gida.zan.iya shigowa ko na koma"?
Bance Masa komai ba Dan nasan magana ce yake gayamin a fakaice da Sunan gidana ne Bai Isa da gidan.ba
Har Kan tabarma danake Kai ya karaso ya zauna yaransa suka ja manyan ledoji gabansa Ashe har da kayan abinci ya taho.mana dashi manja da doya dasu Dankali
Ledojin Kuma Kaya ya siyowa su Zahira
Ledar Waleed kuwa daban yake dan Waleed.ma Dora shi yayi a Kan cinyarshi Ni nasan a yaran mu gabadaya Waleed na daban ne a zuciyar Naseer yanda nakejin Kamar Zahira itama ta dabance a yarana ba Kuma komai ya jawo haka ba sai hankalin zahira da yanda take nuna tana Tausayina banida babbar kawa ma daya wuce Zahira yanzu tunda idan Abu ya dameni Ina Gaya mata ko Bata iya bani shawara ba Ina Jin sanyi a Zuciyata.
Koni sai da Naseer ya cikomin Leda da Kaya na Kuma ji dadi
Sai danayi dagske na nuna Masa b'acin Raina ya daina cemin Mai gidan
Bamu samu kebb'e wa ba sai da Yara sukayi bacci
Muka hau hira na dawo da maganar dalilin daya sa naki Bari ya zauna a gidana sabida yaranmu ne.ba komai ba
Shima.yace min
"Badan kin bijire bama da bansamu wanan aikin da nake yi ba dake Dan shigomin da kudi ba Dan a gaskiya a ranar Dana bar Nan naji Haushin abinda kikamin ban Kuma boyewa Tijjani komai ba na Gaya masa yacemin Kar na damu na Miki uzuri ba laifinki bane dole tasa kikamin Haka nayi hakuri har sai kin hucce sai na dawo ya Kuma nunamin kila yanzu idonsu Umma na kaina na daga kafar Kar Nazo
Da shawararsa nayi amfani nake kwana a company mu kamar wasa. Mai gidanmu yamin tayin aiki a company su dake can Abuja ya Kuma bani Dan matsayi sabida rukon amanar daya ce Ina dashi
Da wanan na koma Abujan na fara aiki ya bani daki daya nake kwana acan
Ke.kadai ce bana yiwa aike Dan nasan kina da kudin da Zaki kula da yaranmu Amma Ina yiwa Umma aike na Kuma ringa Tara kudina har sai Dana ga sun isheni nazo.gida na duba ku na muku kwana biyu na koma Kinga dalilin dayasa ma Kika ga na kwana biyu ban lek'o ku ba banida burin daya wuce na samu kudi na siyi fili nayi gini Naeema inasan Naga Nima inada gidan kaina"
Sosai nayi murna da aikin da Naseer ya samu da ke nuni Ana Dan biyansa albashi
Na Kuma ji dadi daya kasance ba a garin nan ya samu aiki ba dan nasan ko bibiyarmu Umma keyi zata ji baa gidana yake zama ba.
Zuwan Naseer ya mantar Dani batun ganin da Nadeeya tace tayiwa Safiyya.
Sai da Naseer yayi sati kafin ya shirya yacemin zaije ya dubo Umma Dan gobe yake San wucewa
Sosai naji dadin cigaban da Naseer ya samu
Kamar nace Masa ya dib'arwa Umma Mai dasu doyan daya kawo Mana na Kuma fasa Dan bana San Masa shishigi yanda bayamin maganar Umma Nima bana San na Masa maganarta.
Naseer kuwa a lokacin daya Isa gidan jikinsa ne yabi yayi sanyi dayaga yanda Hajara ta hade girar sama da kasa Tama k'i amsa gaisuwar daya Mata Dan a ranar daya dira garin Kano sai da Kawar Safiyya dake unguwarsu naeema ta Bata labari Saude da itama ta kasance bazawara tana aiki.a wani gida dake kusa da gidan da Safiyya ke Aiki
Da biyu Safiyya ta kula kawance da Saude Dan ta ringa gaya Mata komai Akan su Naeema da yaran nata cikin Ikon Allah kuwa sai halinsu yazo daya ta mugunta da balain San bin Mallamai da bokaye saude ta tsani Naeema ne sabida ta daina Bata bashi idan taje Dan sako Naeema tayi da karbar bashi ba dare ba Rana Naeema tun tana.kawaici har sai data daina Bata bashin Dan idan saude.nada.kudi wani shagon take tafiya idan Kuma Bata da kudi sai ta taho shagon ta bashin data daina Bata sai ya tsayawa saude a wuya ba iya Wannan ba yarta dake Saar Zahira maimuna da ajinsu yake daya sai zahira tafi maimuna kyau da k'ok'ari sai hakan ya Kara asasa tsanar da take wa Naeema
Safiyya na Mata maganar Naeema ta karbi maganar da hannu bibiyu hassada da kyashi yasa itama take San ganin Bayan Naeema data Mata fintinkau.
Idan sun tashi daga wajen aikatau gidan su Safiyya take zuwa ta hau Basu labarin ai taga Naeema yau taga kaza taga kaza ahaka Hajara da Safiyya ke samun labarin duk motsin da Naeema tayi da yayanta
Washegarin da Naseer ya dira garin da sassafe ta je gidansu Safiyya ta hau Basu labarin zuwan Naseer da lodin kayan daya kawowa su Naeema cikin akori Kura ta karkace ta Kara Gishiri da maggi.
Sosai Hajara taji ranta ya b'aci ta hau jiran zuwan Naseer Amma ko gezau Naseer Bai zo ba ahaka take kwana da bakincikin zuwan Naseer gidan Naeema batare da ya waiwayeta ba ba abinda ya Kona Mata Rai kamar uban kayan da akace ya kaiwa Naeema wato ita Tana Nan tana soya kosai a Rana Naseer Kuma ya tare a gindin Naeema
Safiyya kuwa a gefe zuga Hajara kawai take akan taci mutuncin Naseer.
Sai gashi Naseer Bai tashi zuwa ba sai daya kwashi kwana bakwai a Rana na takwas kuma.haka.yazo musu babu ko.leda a hannunsa
Naseer kuwa jiki a sanyaye yace "Umma ko akwai lefin da na Miki ne"?
Girgiza masa Kai tayi tana "ba wani laifin dakamin Naseeeru ya wajen aikin ya wajensu Naeema yaushe kazone?
Da Zuciya daya Naseer yace "kwana bakwai kenan da zuwana Umma na Dan yi.ziyarce ziyarce gobe Zan koma nace Bari Nazo na Miki Sallama dafatan.sakona Yana Isa wajenki"
"Eee Yana isa wajena Kam Ashe kwana bakwai.kayi a garin Nan Amma sai yau kazo ganina Kuma daka tashi zuwan sai.ka.taho Haka"
"Yi hakuri Umma nayi laifi Abunda yasa banzo da komai ba Dama kudi nayi niyyar Baki shiyasa ban taho da komai ba"
"Toh yayi.kyau Naseeru"
Daga Haka Bata Kara cewa komai.ba ta ringa kudurta Abubuwa a ranta.
Naseer kuwa banza ta bawa ajiyarsa sai daya gaji Dan kansa ya ciro kudi Mai Dan yawa ya Ajiye Mata a gefenta Yana "Umma bari na koma inaso naje gidan Tijjani akwai maganar da zamuyi gobe Zan koma insha Allahu"
"Allah ya bada saa"
Daga Haka Bata Kara cewa komai ba ya tashi ya tafi
Safiyya dake labbe a d'akin kusa dasu ta fada d'akin tana "Mai na Gaya miki Umma wlh Naeema ta kwace Naseer yanzu ya fara samun kudi a madadin ya kawo Miki sai ya ringa kaiwa shegiyar Naeema da take da uban kudi
Kinsan kuwa saude tacemin layi akeyi a gidan ta masu San wanan shegiyar Yar tata mai.kama da Aljanna Haka suke cicika ledoji suna kaiwa Gidan
Mu kam muna Nan a wahalce kina siyar da kosai
Cikin bakin ciki Hajara ta dau kudin da Naseer ya Bata tana "Hada da kudin Nan da kike tarawa kiga idan ya Kai kije gurin mutumin nan ya Mana aikin Nan nida Dana ta rabamu ta karfi da yaji zata Gane shayi ruwane
Maza jeki duba min kudi Nan idan sun Kai gobe da sassafe ki tafi wajensa
Cikin murna Safiyya ta jawo gwangwanin kudin da suke Tarawa ta fito da kudin ciki ta had'a taga kudin ya Isa ta hau murna
Dak'yar tayi bacci sabida tsananin mugunta da asuba suka dau hanya.ita da Saude.
Sai da aka Dade layi yazo kansu cikin mugunta Safiyya ta karkace ta hau gayawa boka bukatar ta akan Zahira 'Yar Naeema data tsone Mata Ido sau uku tana zuwa makarantar Dan kawai taga wayanda ke muammalla da zahiran
Sai Kuma abin yazo a daidai makarantarsu Zahira daya da Yar Sauden.
A gajiye Suka dawo gida suna dawowa
Suka.samu hajara suka.hau Kora Mata jawabi Kamar Haka "Umma Kinga abinda ya bamu Kamar yanda na fada Miki ayi Mana Aiki Akan zahiran ta ringa sata Kamar b'era toh gashi ya bamu wanan yace mu samu zahiran ta Sha alewa ne Kato kamar suga yace ko kad'an ta diga a bakinta wlh b'era ma.bazai Kai ta sata ba kuma ko a Ina ta zauna sai tayi satar"
Wani.irin dariya Suka kwashe dashi gabadaya Hajara tace "Haka nakeso Saude gashi nan ki bawa yarki Maimuna ta jawo zahira jiki ta Bata tunda kince ajinsu daya idan.ta kama.ne.ma ta siyi alewa da Sunan sadaka ta rabawa.yan ajin gabadaya yanda zahiran zata saki.jiki ta Sha"
Jiki na rawa Saude.ta karba tana doki Dan ta tsani Zahira sabida yanda ta yagawa yarta ko ta Ina
Haka.kuwa akayi tana zuwa gida ta siyo alawa Mai irin gidan alewar da zaa bawa Zahira ta bawa maimuna akan gobe ta rabawa Yan ajin wanan Kuma ta tabbata ta bawa Zahira ta Sha.
Washegari kuwa Haka maimuna tabi Yan ajinsu da alewar.ta dau na maganin ta mik'awa Zahira
Sai dai me duk yanda taso Zahira ta karbi alewar kin karba tayi tace ita Bata Shan alewa kashe Mata hakori yake Rai ba dadi ta taho gida da alewa a hanya ta Dan bude alewa taki yawunta ya tsinke ta gutsuri kad'an ta Sha
Ta maida cikin ledar ta kaiwa Saude ta Gaya Mata yanda sukayi da zahiran
Saude.kuwa cikin Jin Haushin ta karbi alewar taje gidansu Hajara ta Gaya musu
Safiyya kuwa ta karba tana Kar ta damu wlh gobe sai ta danne Zahira ta Sha alewar Nan
Hajara kuwa cewa take ta tabbata ta danne ta Dan bazata yi asarar kudinta a banza ba.
Da mugun nufi Safiyya ta ajiye alewar tana Shan alwashin har aji zata je.ta danne Zahira ta saka mata alewar a Baki.
Daddare ta fita Dan ta siyowa Bashir danta kamu ta Dama Masa tana dawowa taga ledar alewar a hannunsa Yana mumul mumul da Baki.
.
Cikin tashin hankali ta saki ihu ta nufi wajen Bashir din..........
*A DAINA BIYONI ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NAGA TA KAINA A DAINA KIRANA ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NA GA TA KAINA DUK MAI SO YA CIGABA DA BIBIYAN LABARIN A DAINA CEMIN DAGASKE NE KO BADA GASKE BANE SANAN DAN ALLAH DAN ANNABI A DAINA CEWA NACE ZAHIRA ZATAYI KARUWANCI NI NAFEESA BANCE HAKA BA BA KUMA A JI A BAKINA BA DUK WANDA YAKE GANIN BAZAI IYA CIGABA DA BI BA DAN ALLAH BAN MASA DOLE BA