Showing 135001 words to 138000 words out of 180103 words
Umma daga Nan su taho station.
Ni kuwa Ina Jin Haka nace Masa Ni ba wani Abu nace a musu ba katangar karfe kawai zaa Mana tsakaninmu a Kuma ja musu kunne na karashe da su taimakamin.
Cemin yayi kar na damu na je Amma inza a d'auko uwar mijin nawa Kar na bisu na hau wani motar Nazo da Kwaryar da kuma Zahira yata da suke ta San ganin bayanta.
A haka na hau motar Yan sanda nida mace Yar Sanda ta Bayan motar su Kuma mazan Suka hau gaban daya najar motar dayan nada ga gefe
Ni na ringa nuna musu hanya har muka iso k'ofar gidana
Inda na tarar da yarana a k'ofar gida duk sunyi Cirko cirko ciki kuwa mmn maimuna bubbuga k'ofar Gidan kawai take Tana su bud'e Mata ta tafi.
Ina saukowa daga cikin motar yarana suka yo kaina a guje Ni kuwa Ban tsaya saurarsu ba na bud'e gidan
Mace Yar Sandan na biye Dani a bayana Ina bud'e k'ofar mmn maimuna ta fara kokarin fitowa daga gidana
Yar Sandar data gani a bayana yasa ta zub'e a kasa ta hau magiya
Yar Sandar Nan kamar namiji Haka ta damko kafadar mmn maimuna ta jata cikin motar Tana ihun nayi hakuri Kar na Bari a tafi da ita.
Dan Sandan dake zaune a daya B'arin ne ya daka Mata mumunan tsawa akan ta musu shiru ta Kai su gidan su Safiyya.
Dayake tana da balain tsoro da hannu biyu ta rik'e bakinta ta shige baya ita da matar Dan sanda ya tadda motar ta hau kwatanta musu gidan dasu Umma ke zaune
Ni kuwa Suna tafiya na Shiga ciki na d'auko Kwaryar Kwan da layar na saka a bakin Leda daga yanda na hade Rai yasa yarana Basu samu zarafin min tambayoyi ba
Nadeeya na bawa umarnin kullemin gida kafin na dawo na rike hannun Zahira Dake sanye da uniform mukayi titi na tare Mana abin Hawa muka nufi station d'in
Haka kawai Kuma naji jikina yayi sanyi sai nakejin kamar bai Dace na kawo Umma Kara ba Amma ya zanyi inaga hakan kawai shine mafita a gareni duk da a kasan zuciyata ma na yanke wani shawarar da nake tunanin insha Allahu shine zai kawo min karshen komai.
Mun rigasu Isa station din haka yasa Muka zauna a benci nida Zahira Wanda ya dau statement Dina na dazu ya hau min tambayoyi Na cigaba da bashi amsa Yana mamakin Wai Zahira Dake karamar Yarinya ake San ganin Bayan ta haka
Kwaryar Kwan da layyar kuwa daya karba a gefe ya Ajiye Yana jiran isowarsu ni kuwa na cigaba da rokonsa Kar ya musu komai kawai so nake ya Shiga tsakanina dasu na Kara jaddada Masa banasan ayi musu wani Abu sabida Umma uwar mijina ce Safiyya Kuma kanwar mijina.
Baicemin komai ba ya cigaba da rubuce rubucensa
Safiyya kuwa Jin Saude ta Dade Bata dawo ba yasa ta gudu daga gidan Saude Dan gani take kamar Naeema ta Kama Saude ne idan kuwa hakane gwara ta gudu
A hanya kuwa kukan kudinta take Tana Kara tsinewa Naeema tana ce Mata Mayya sosai takejin itama akwai asirin da Naeema keyi shiyasa duk abinda suka Mata asirinsu ke tonuwa a kasan zuciyata kuwa tana adduar Allah yasa Saude ta jefa layar a masan ta matsu taga bayan Naeema ta matsu taga Naeema a cikin tashin hankali.
Koda ta Isa gida ta bawa Hajara labari itama sosai taji Haushin yanda Naeema ke tsallake duk abinda suke Mata
Hajara ta hau cewa ita tasan Naeema Dole akwai abinda ta taka da take tsallaka duk wani Abnda suka Mata yanzu iya kudaden da suka kashe ya Isa su siyi karamin fili tasan ma Asirin tayiwa Naseer take juya shi San ranta
Safiyya na k'ok'arin Magana wata Mmn ayuba ta watso Bashir da baifi shekara biyu da watani waje tare da murd'e Masa kunne tana "Naga masifa da jarraba a gurin karamin yaron Nan kamar Danan yasan ya Shiga karkashin gado ya bud'emin tukunyar Miya ya hau tsamar.min nama Ke Safiyya wlh ki ringa rike danki duk Inda zakije Dan ya galabemu da kananan d'auke d'auke Yana mitsitsin shi dashi anya ma yaron Nan naki shi kadai ne kuwa ba wani Abu a jikin sa"?
Ta karashe tana cika kunnen Bashir dake tsalla ihu.
Safiyya kuwa wani abune ya tokare Mata wuya tama kasa mik'ewa sosai itama hankalinta ke tashe da yanda Bashir ke Shiga Dakunan Yan gidan yake musu d'auke dauke tun Bai girma bama abinda dai zai iya ci yake dauka Bai fara satar kudi ba tukunna har wajen wasu bokaye taje sabida su karya Mata asirin satar sai dai Kamar a banza sosai abubuwa ke cakude Mata a madadin tayiwa kanta fada aaa Sai take ganin kamar ma Naeema ce ta jefata a halin da take ciki a madadin tayi nadama cigaba da neman hanyar da zata ga Bayan Naeema take yanzu ma Allah ne yasan uban kudin da ta kashe wajen karbo layyar nan sai gashi babu Saude babu dalilinta tana zaune ne kawai a Nan Amma hankalinta na can burinta kawai taji Sallamar Saude Akan ta aiwatar Mata da aikin da ta Sakata.
Mik'ewa tayi Dan ta dauko bashir dake ta kuka a bakin kofar mmn ayuba sauran mutanen gidan kuwa na ta kananan surutu Akan Bashir din ko kallonsu batayi ba Dan yanzu hankalinta baa jikin ta yake ba
Shigowar mace Yar Sanda da excuse me ne yasa ta Dago tana kallonta kanta tsaye Yar Sandan cikin gurguraren hausa tace wacece Safiyya mmn Bashir da Hajara mmn Safiyya
Da Sauri mutanen gidan da suka nutsu suka hau nuna Safiyya da ta daskare a tsaye tana kallon Yar Sandar data Kira sunanta kirjinta kuwa sai bugun Tara Tara yake Dan idan akwai abinda take tsoro a rayuwarta Bai wuce masu bakin kayan Nan da bindiga ba
Kamar numfashinta zai d'auke a lokacin da Yar Sandar ta karaso gabanta ta damke hannunta tana Ina mamanki"
Kinkina Safiyya ta hau Yi ta daka Mata mugun tsawan dayasa ta Nuno Hajara da tashi tsaye tana gyara daurin zanin jikinta sabida tashin hankali shigowar Yar Sanda.
Da hannu daya ta rik'e Safiyya har suka karasa gaban Hajara
Yar Sandar tace Musu su tafi station Ana nemansu
Safiyya fusge hannunta tayi tana "Mai mukayi da zamuje station Anya mu kike nema kuwa ko dai b'atan Kai kikayi"
Marin da Yar Sandar ta d'auke ta dashi daya d'auke jinta gabadaya ta barin kunnenta na hagu yasa tayi tsit
Hajara kuwa Marin da Safiyya ta Sha yasa Bata tsaya gardama ba tayi gaba matar Kuma ta hau Jan Safiyya sukayi waje Basu Kara gingin magana ba suka hau motar Yan Sandan sai a lokacin Suka ga Saude data ci kuka idonta ya kad'a yayi jajjur
Gaban Safiyya Dana Hajara sai daya balain fad'uwa tsoron Yar Sandar yasa ba Wanda ya iya magana a cikinsu duk da Safiyya nata yiwa Saude magana da Ido.
Saude na dauke kanta
Hajara da Safiyya sosai Suka rude hankalinsu ya tashi suna tunanin Mai ya faru Haka Saude ta d'auko musu Yan sanda ko dai Kamata Naeema tayi shine ta d'auko musu Yan sanda cikin wasu wasi Suka iso station din jiki na rawa suka sauko daga cikin motar Yan Sandan na daka musu tsawa suka Shiga ciki
Suna shigowa muka had'a Ido da Umma da Safiyya da mamaki sosai ya bayyana a fuskarsu da ganina a zaune Akan benci nida Naeema.
Take jikin Safiyya ya hau rawa Umma kuwa ta kasa hakuri ta nuna kanta tana "Naeema Ni Kika kawo wajen Yan sanda"?
Wani mugun tsawa Wanda ya dau statement dina ya daka Mata tayi saurin rufe bakinta fuskarsa a balain had'e ya kalli wani daga cikinsu yace a saka su Umma a cell bama zai sauraresu ba sai Naseer mijina ya dawo"
Ni kuwa Jin abinda yace yasa hankalina ya tashi Dan har ga Allah ba Dan a ci zarafinsu na kawo su ba kawai tsakani nakeso ayi Min dasu.
Sai dai Dan Sandan ko kallona baiyi ba duk da uban magiyan da nakeyi Ina kallo aka tasa keyar Umma da Saude sukayi Bayan canter ita kuwa Safiyya sai da Yar Sandar Nan ta Kara Bata Mari biyu dayasa kanta juyawa.
Ni kuwa na hau kuka Ina rokon Dan Sandan Dan har ga Allah ba abinda nasa yamin kenan ba nayi nadamar Kai kararsu Umma wajen Yan sanda Dan sai Dana gwammace na kwashi yarana na gudu na bar musu garin da abinda ya biyo baya.
Dan Sandar kuwa cemin yayi bazai sakesu ba sai mijina yazo shi yayi mamakin Jin uwar mijina da kanwarsa ke yiwa Yar yarinya da Bata ji ba Bata gani ba irin wanan mugayen asiirn ganin inata magiya yasa yace na tafi gida gobe karfe Sha daya Na dawo zai min abinda nakeso din Amma sai fa sun kwana a yau.
Inaji Ina gani badan Raina naso ba muka dawo da Zahira
Gida a ranar ko baccin kirki banyi ba Dan sai nake ganin kamar kwanan da su Umma sukayi na bud'e musu wani k'ofar da zasu Kara nufana da mugunta ne nasan halinsu yanzu bakina zasu gani har ga Allah banji dadin abinda San Sandan Nan yamin ba idan Yana ganin ma taimakona yayi wlh bai taimakeni ba Dan nasan halinsu Umma
Rashin nutsuwa zuciya yasa ranar ko sallah Daren banyi ba da asuba na tashi na hau aikin gidan Dan so nake naje station da wuri Dan hankalina gabadaya Yana can
Su Nadeeya na Gama shiryawa suka tafi makaranta Zahira kuwa nace Mata ta shirya mu tafi station duk da lokacin dayace muzo baiyi ba Amma banida nutsuwa Sam gwara dai a fito dasu umman hankalina ya kwanta
Ko abinci na kasa sakawa cikina.
Yanda nake a hargitse yasa Zahira ta hadiye tambayoyinta mun fito kenan Ina k'ok'arin kulle gidan.
Taxi ta Parker a k'ofar gidana Naseer ya fito daga taxin fuskarsa d'auke da faraaa yayi kyau har da kib'ar kwanciyar hankali
Mai taxin kuwa booth ya bud'e ya hau firfito Masa da kayayyakinsa .
Shi kuwa Naseer yanda yaga nayi zuru zuru yasa ya iso wajena da Sauri Yana "Lafiya kuwa Naeema ya naganki Haka Ina zaku Naga kuna kulle gida"
Kuka na fashe dashi ban iya ce Masa komai ba Dan har ga Allah wandanan Abubuwan sun isheni na gaji da Naseer da Mahaifiyarsa Nagaji ma da komai Ni
Hankali a tashe ya bud'e gidan
Ya ja hannuna muka Shiga ciki ya umarnci Zahira data kwaso kayan ta kawo ciki
Ya Jani har d'akina ya zaunar Dani akan gado shi Kuma ya duka wajen k'afata Yana cigaba da tambayata abinda ya faru
Ban ce Masa komai ba nace Masa muje dai yagani da idonsa bazan iya Masa bayani da Baki ba
Duk yanda yaso na Masa bayanin abinda ke faruwa k'i nayi.
Hankali a tashe ya kulle gidan ya biyoni a baya shi da Zahira.
Abin Hawa na tare Mana muka hau Bai Kara min tamabyaa ba har muka iso station din ganin ciki zamu Shiga yasa ya rik'e hannayena Yana "Naeema Dan Allah ki gayamin me ke faruwa mai mukeyi a police station na Shiga uku Ni Naseer"
Ban kula shi ba na fusge hannuna na Shiga station din ya bi bayana shi da Zahira hankalinsa a tashe.
A Kan benci Muka zauna Dan Wanda case Dina ke hannunsa Bai zo ba ance sai karfe goma zai iso.
Naseer har tsawa ya ringa min akan Gaya masa abinda ke faruwa ban Gaya masa ba har sai da Dan sandan yazo
Yana shigowa ya kallemu Yana "wanan ne mijin naki"?
Gyada masa.kai nayi
Ya karewa Naseer kallo ya shige wani office shigarsa ba jimawa wani Dan sanda yace mu Shiga ciki Naseer Haka ya bini office din Dan sanda.
Muna Shiga Dan Sandan ya umarcemu mu zauna gaban teburinsa Kuma Kwaryar da kwai da layyar ke ciki ne a gabansa.
Muna Zama aka shigo da Umma dasu Safiyya da sukayi zuru zuru Safiyya kuwa jikinta duk ya kumbure Dan ta Sha bak'ar duka a wajen wanan mace Yar Sandar .
Saude kuwa tayi wani irin laushi Kamar Mara lafiya
Umma ce dai naganta fes muna hada Ido da ita ta min wani mugun kallon daya tsinkemin zuciya
Zahira kuwa ta Kara matsawa kusa Dani Kamar zata shiga jikina
Naseer kuwa hankali a balain tashe ya mik'e tsaye Yana "Umma"
Umma ko kallonsa batayi ba ta zauna a kasa kamar yanda su Safiyya Suka zub'e a kasa sai wani irin vibrating take
Naseer kuwa hankali a tashe ya fara k'ok'arin nufar wajensu Umma
Dan sanda yace ya koma ya zauna ba Dan Ransa naso ba ya zauna hankalinsa a balain tashe.
Dan sanda Kwaryar ya nunawa Naseer Yana ya iso ya gani da idonsa
Naseer kuwa ya nufi wajensa ya dau Kwaryar ya sunkuya ya hau ganin rubutun da akayi da Sunan Zahira Sam bai gane Mai hakan ke nufi ba
Hakane yasa ya daga kansa ya kalli Dan Sandan ya dawo da kallon sa kaina Ni kuwa na dauke kaina Dan duk na bawa Dan Sandan labarin komai
Dan Sandan kuwa cewa yayi Saude duk ta bashi labarin abinda sukayi da bakinsu kafin yasa a canja Mata kamani Dan taurin Kai ma Safiyya ta gwada musu Taki magana hakane yasa ta Sha mugun duka
Yak'i Bari a daki umman ne sabida yanda Naeema ta daga hankalinta Kuma Yana ganin umman babba ce duk da akwai masu laifiin da Suka fita shekaru suke Kuma musu hukunci
Jiki na rawa Saude ta hau bada labarin duk abinda Suka so yiwa Zahira Bata rage komai ba ta tonawa Umma da Safiyya asiri har asirin satar da suka so yiwa Zahira Allah ya mayar musu Kan kayansu
Tana bada labarin Ina kuka Naseer dake tsaye sai gashi jikinsa na balain rawa har kafafunsa Suka gaza daukarsa ya zub'e a kasan
Yana kallon Umma da Safiyya da suka sunkuyar da Kai
Saude kuwa sai bada hakuri take tana a yafe Mata sharrin shaidan ne
Zahira kuwa kukanta ne ya cika office din dan duk ta fahimci Abunda ke faruwa.
Dan Sandan kuwa ya kalli Umma Yana "Mai jikarki ta Miki Haka har kike San ganin bayanta"
"Babu komai"
"Ke Kika haifi babnta kuwa ko tsintarsa kikayi ki gayamin gaskiya"?
"Ni na haifesa ba tsintarsa nayi ba"
"Amma ke kika haifeshi kike San ganin bayan yarsa data kasance jikarki Mai yayi zafi Haka ko wani Abu mahaifiyarta ta Miki shiyasa kike San ganin bayan yarta"
"Ba abinda tamin yallabai sharrin shaidan ne ayi hakuri"
"Ke Kuma uban me ta Miki kike kulla irin wanan makircin"?
Murya a dashe Safiyya tace itama ba Komai ta hau bada hakuri Kamar yanda Umma ta bada hakuri.
Naseer kuwa shima tunda ya sunkuya da kansa Bai Kara dagowa ba
A takaice Dan Sandan kuwa ya jawa su Umma kunne sosai ya ce musu ko tari nayi Dani da Zahira ba Kuma iya Zahira ba har yarana gabadaya wlh sai sun Kama su Kuma an kullesu na har abada
Duk da Basu iya rubutu ba sai da aka d'auko takarda Suka saka hannu Akan sun yarda ba abinda zasu Kara min na sharri indai kuwa anyi sune
Ahaka aka Sallame mu gabadaya muna fitowa Saude ta dib'a a guje Umma kuwa da Safiyya wani azababen kallo Mai dauke da mugun tsana sukamin nida Zahira Suka dau hanya Naseer kuwa a ba yanda zaiyi yabi bayansu Amma ko kallon Inda yake basuyi ba
Ni kuwa hannun Zahira Naja muka hau taxi muka koma gida.
Duk da anmin tsakani dasu banji hankalina ya kwanta ba hakane yasa muna isa gida na bazama neman dilallai Dan wlh siyar da gidana zanyi da komai nawa na bar unguwar in ta kama ma na koma garinmu dan bazan iya ba.
Naseeer kuwa har gidan yabi su Hajara
Suna Shiga gidan.
Safiyya ta d'auko danta daga wajen mmn ayuba data taimaka ta rikeshi
Hajara kuwa a tsakiyar d'akinsu ta tsaya ta kalli Naseer cikin tsananin bacin rai tana "har ni Naeema zata Kai wajen Yan sanda ta kulle mu wani irin girgiza Kai Tayi"
Naseer kuwa dake Jin yazo har wuya ya hau zabga masifa Yana .........
Karku manta nace Zan na tsallaken kwana daya
*Comment*
Haka aka taba yimun 😭niy yarana duka akasa sunansu su 7 aka hada da likafani da sanduna guda bakwai da duwatsu da turare irin na aikin junnu,akaje aka saka wani wuri ,wai yanda akayi dinnan haka yarana zasu zama kamar gawa bazasu taba tsinana ma Kansu komiba a rayuwa,shikuma duwatsun zai zama yadanne zukatansu bazasu taba tunanin nema ma Kansu maganiba,kuma ko annema anbasu bazasu iya amfani dashi ba ,ke mugun abudai😭kawai Allah yanuna mun a barci da kuma yarona guda daya shima Allah yanuna masa da asuba kuwa yazo yake fadamun,nayi mamakin yanda mukaga Abu daya duka lokaci daya,wallahi danayi magana kuwa saiga Abu ya bayyana shine akaje aka dauko abun shinefa akaga wadannan abubuwan Dana lissafa da sunayen yaran nawa duka aciki,aka fada mana kuma abunda akayi asirin yasamesun,Allah yakare ya nuna mana😭
*Advertisement*
Yan uwana yan kasar Niger,chad,camaroon,ghana dama ko ina afadin duniya masu son siyan kaya a nigeria harda ma yan cikin nigeriar amma suna tunanin ta yadda zasu rika siyan kaya cikin aminci to ga dama ta samu cikin sauki da rangwame zaku samu kaya kamarsu kayan kitchen,atamfofi,shaddoji,laces,jakunkuna da takalma toga dama ta samu kawai ku tuntubi Oum_Aabid Herbals and more
08178586888
Whatsapp group
https://chat.whatsapp.com/CRsFCyoGq3i628AujmbxvV
domin samun kaya cikin sauki da rangwame.
Masu fama da ciwon sanyi kunyi magani harkun gaji to kuma ga dama ta samu ku tuntubeta zaku samu magani sadidan insha Allah
08178586888
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 52*
"Mai na Miki Umma Mai na Miki a rayuwata kike San ganin bayana Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma na rasa Kuma laifin Mai na Miki yanzu Umma Zahira yata kikesan ki watsawa rayuwa?
Yanzu Zahira kike yiwa asirin Sata kike mata asirin wari Dan kawai Kar ta samu Wanda zai Aureta Umma Zahira yata ce fa innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma tsanar da kikamin har ya Kai Haka Umma bayan kin watsa min rayuwa umma iya Haka Bai isheki ba sai kin taba min yata da bata Miki komai ba?
Umma Anya