Showing 138001 words to 141000 words out of 180103 words

Chapter 47 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2463

kina tsoron Allah kuwa?Anya da Zuciya a kirjinki kuwa Umma tunda nake bantaba Jin uwar data ke azabtar da danta ba irinki ban taba ganin uwar da Bata da burin daya wuce taga bayan danta ba irinki duk burina na faranta Miki na miki biyayya har gidana Dana mallaka Kika siyar har gobe kece silar jefani a halin da nake ciki har yanzu ko bulo yanzu banidashi balle gida Amma iya Haka Bai isheki ba Umma har sai kin tab'a diyata toh insha Allahu idan Ina rayye ba abinda zai Samu yayana Naeema Kuma tamin daidai data Kai kararku wajen hukuma daga Rana irin ta yau duk abinda ya samu yarana wlh Umma kece Kuma ko ta kai kararku wlh Ni Zan Mata shaida"

"Baka burgeni ba da tundazu banji ka d'aukeni da Mari ba Naseeru Ni nasan ba a hayyacinka kake ba Naeema ta Dade da asiriceka Dan da a hayyacinka kake mataki zaka dauka akan tsinananiyar yarinya Nan Naeema Ina mahaifiyarka tasa a kullemu har mu kwana"


Naseer bakinciki ne yasa Bai iya ce Mata komai ba ya fito daga d'akin a fusace Safiyya dake labe San Bata San fitowa zaiyi ba kafin tayi k'ok'arin b'uya har ya Kai Mata wani irin cafka ya hau kwallo da ita.

Dak'yar aka kwace ta a ahnnunsa bayan Hajara ta fito aguje tana zaginsa bakinta daya Saba da tsinuwa na tsine Masa Haka ta ringa Shan alwashin ganin bayan Naeema ko da zata mutu

Naseer kuwa Haka ya fito Ransa a tsananin b'ace ya tari abin Hawa ya nufi gidan Naeema.

A lokacin daya Isa Bai samu Naeema ba sai su Zahira.

Shima Bai tambayesu ina taje. Ba ya Shiga d'akinta Agaban mudubi Yaga an ajiye Kwaryar

Hakane yasa ya Shiga bandaki ya d'aura alwala ya fito ya dauki Kwaryar

Yayi waje sai dayaje nesa da gidan ya fasa Kwan ya Kuma binne layar ya dawo gidan

A daidai lokacin da Naeema itama ta dawo.

Daga shi har Naeema ba Wanda yayiwa wani magana Dan Naeema ma wani irin hade Rai tayi hakane yasa Bai samu zarafin Yi Mata magana ba.


Sai daddare da Yara sukayi bacci ya hau Bata hakuri Bata ce Masa komai ba Dan tasan ba abinda hakurinsa zai Mata ita dai yanzu mataki kawai zata dauka bazata tsaya mahaifiyarsa ta salwantar Mata da rayuwa ya ba

Kwana biyu a tsakani akayi ta zuwa ganin gidan

Wanda Sam Naseer Bai Gane zuwan da ake ba har sai da ciniki ya kankama

Naeema ke Gaya masa matakin data dauka na siyar da gidan Dan ta bar unguwar.

Naseer sosai yaji zuciyarsa ta sosu da hukunci da ta yanke batare da ta shawarce shi ba sosai yaga Dan tana takamar gidanta ne hakane yasa tayi Masa Haka Amma kasan zuciyarsa Kuma sai yake ganin Dan tsira da lafiyar yayansu yasa kila takeso su bar unguwar

shima kansa hakan yaso yayi dan so yake ko haya ne ya Kama musu acan Abuja su koma can da Zama inyaso ko aike ne ya ringa yiwa Hajara Amma tunda ma Naeema ta Riga da ta yanke siyar da gidan shikenan

Dashi akayi cinikin gidan da ba laifi an siye shi da daraja da saka hannun Naeema aka siyar da gidan

Masu siyen Kuma suka bada kudi tare da notice din wata guda.

Kayan shagon Kuma tayi niyyar siyarwa wani Mai shago dake can bakin titi da har Naeema ta Masa magana.

Da injin markadenta kawai zata tafi

Sai da Naseer ya tambayeta Inda take so su koma ta ce Masa garinsu zasu koma gabadyaa yanda su Hajara ma bazasu San Inda suke ba sosai Naeema ta shirya Yana Mata gardama tace ya Bata takarda sakinta Dan har ga Allah ta gaji sosai

Naseer kuwa take takenta ya gani ya hau lallaminta akan ba sai ta Kai ga barin Kano ba ta nemi wani unguwar ko Dan makaranta yaran nasu

Dak'yar da sidin goshi ya shawo Kan Naeema Dan tuburewa tayi bazata zauna a kano ba duk Abubuwan dake ciciyar ta a zuciya ta hau amayar dashi har da cewa ita dai ta gaji da aurensa indai wani Abu ya Samu yaranta bazata yafe ba Naseer Haka ya Shanye duk maganganun data ringa kwaba Masa har ya samu kanta

Abinka da tsakanin Mata da miji tuni dai ya shawo kanta ya kwantar Mata da hankali Inda ya Kuma Bata shawarar Inda ya kamata ta samo.karamin gidan unguwa ne nesa sosai da Inda su Hajara suke.

Hakane yasa Naeema ta sakar wa Naseer ragamar komai Inda ya nemo.mata karamin gidan Kamar dai wancan data siyar sai dai wanan Din ya Dan fi girma kawai matsalar ba shago a gaban gidan

Sai da Naeema taje taga gidan taga komai yayi suka biya kudin gidann

Cikin sati biyu suka dawo kawo dake unguwar hotoro Bayan anyiwa su Nadeeya transfer zuwa wani makarantar

Zahira kuwa boarding Naseer ya dage zata tafi a fadarsa.

Hakane kawai zai saka masu sintirin zuwa nemanta su daga kafa Zahira Kuma zata maida hankali tayi karatu sosai tunda yanzu zata tafi ss1

Nadeeya Kuma ta tafi jss.2


Dayake da Yan canji a hannun Naseer shi yayi cuku cukun sabon makarantar dasu Nadeeya suka koma dake unguwar da suka koma.

Zahira kuma.aka hau Mata siyayyan boarding Dan itama an Mata komai.ta fanin registration.

Har ga Allah ba a San Raina Zahira zata tafi boarding ba Dan dai Naseer yamin fin k'arfi ne kawai a matsayinsa na Mahaifin zahiran a rayuwata banasan abinda zai nesanta Ni da yarana nafiso ko yaya ne na ringa ganinsu a gabana har ya fara shirye shiryen Kai ta jikina a sanyaye yake ita kuwa zahira murna take sosai tana doki data ga yanda babanta ke mata siyyaya

Nidai addua kawai nake akan Allah ya karemin ita Dan har yanzu gani nake su Umma zasu iya jefo min wani masifar amma.ina gayawa sarkin sarakuna duk gudun da zanyi nasan sai dai idan Umma basu so cutar damu ba kasan zuciyata Kuma sai nake ganin zuwan Zahira boarding zai.nisanta ta daga sharrinsu umman.

Hakane yasa na kwantar da hankalina nayiwa zahira komai na jawota jikina na Bata shawarwari yanda zata kame.kanta da dagiya da addua

A Haka nida Naseer muka Kai Zahira makaranta yata ta rungumeni muna kukan rabuwa dak'yar Naseer yaja hannuna Muka tafi

Kamar Mara lafiya dai na dawo sai Dana fi sati kafin na fara Dan sabawa da rashin zahiran

A Haka na maida hankali na fara tunanin Sana'ar da Zan Kama Kuma bayan.markaden Dan da alama unguwar akwai.masu markade.da.yawa ba shago a k'ofar Gidan ballantana nace Zan zuba provision kamar wancan unguwar da muka baro

A Haka dai na yanke siyar da Zobo kafin na samu babba Sana'ar da zan ringa yi tunda kudin Sana'ar tawa suna ajiye

Ba laifi kuma Ina Dan cinikin zobon


Naseer wata biyu ya min ya koma Abujan.

Ni kuwa na cigaba da kula da yarana sau biyu Ina zuwa ganin Zahira ba laifi hankalina ya kwanta da yanda naganta kawarta ma da kusan dabiarsu daya sunanta jameela sosai na yaba da hankalinta hakane yasa na Kara samun kwanciyar hankali.


A Haka rayuwar ta ringa tafar Mana ban taba sakin jikina ba kullum cikin addua nake Dan nasan duk da anyiwa su Umma gargadi nasan halin su kila idan sun ga an kwana biyu zasu iya waiwayomu da sharri kullum cikin sadaka nake Dan nasan sadaka maganin masifa ce

A Haka su Zahira sukayi first term dinsu a ss1 sukayi hutu suka dawo

Fes Zahira ta Kara Yi kyaunta ya Kara fitowa tabarkallah Masha Allah Dan acan ma Mallamai santa sukeyi.

Hakane yasa na yanke a Raina indai ta Gama din mu aurar da ita kawai inyaso ta cigaba a gidan mijinta

Naseer shima a daidai lokacin da sukayi hutu ya dawo

Cikin farincikin kudin daya samo inda yake cemin fili xai siya da kudin sosai na Taya shi murna Dan Kamar Wanda Bai taba gidan kansa ba yake murna da filin da yake San siya

Gaba da gidana wajen bakin titi ya siyi katon filin a ranar ko baccin kirki baiyi ba sabida murna.

Ahaka ya Mana sati biyu ya koma.batare da waiwaiyar umma ba

A Haka aka Gama hutu Zahira na rakata makaranta


Sati.uku da komawarta na fara mugayen mafarkai akan Zahira

Daya dagamin hankali na hau sadaka Ina Addua Haka kawai naji Kamar wani Abu ne zai sameta daga yanayin danake.ganinta a mafarkina hakane yasa naji Sam na kasa samun kwanciya hankali na fara shirin zuwa dubo ta a ranar Dana shirya da sassafe Dan na dubota a ranar da bazan taba mantawa ba a rayuwata Mallamai biyu ne maza da mallama Mace daya sai kawar Zahira jameela da wata da suka ruk'o zahira Kamar matacciya suka shigomin da ita Suka shimfida min ita a tsakiyar gidana.

Juyawar da kaina keyi da kirjina da nakeji kamar zuciyata ce zata fito yasa na kasa motsi na daskare a tsaye

Kwantar da Zahira da akayi yasa na rik'e zuciyata tare da kallon zahiran.


Abinda na gani ne yasa jiri d'ibana na zub'e a gefen zahiran.......


Kuyimin.hakuri abubuwa ne Suka Sha kaina sai Sunday Zan dawo daidai ayi maneji pls.


A next episode insha Allahu Zan k'ok'arin Yi dayawa Dan muyi mu Gama ngd
8/19/21, 10:33 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page 53*

Na saki ihu tare da dagota Ina "Mai ya samu 'yata Haka Mai ya sameta waye ya kwakulo Mata idonta waje Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"


(Nafeesa sai dai na takaita Miki wuyan da Zahira ta Sha a cikin irin kaddarar data budemin daga auren Naseer wahalar da Zahira ta Sha yafi komai bani wuya tunda Nima sai Dana Zama tamkar tab'abb'iya wuyan data Sha shima labarine Mai zaman kansa sai dai na takaita Amma kyakyawan zuciya irin nata cewa take ta yafe musu abinda Suka Mata ko yanzu da Zan baki labarin wuyan da yata ta Sha ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata ko nida Zahira mun yafe Sai Allah ya Mana sakayya"

Ta fashe da kuka labarin da baa bani ba kenan a ranar sai washegari)

Badan nasan Zahira 'yata bace bazan yarda ita Suka kawomin ba Dan gabadaya hallitar Zahira ta canja cikin sati uku kawai da Zahira tayi da komawa makaranta ta dawo kamar kwarangwal idonta ya firfito waje gabadaya wuyanta kuwa ya wani irin kumburo waje kallo daya zaka Mata ka d'auke idonka daga kanta sabida Dole ka tsorata da yanda ta dawo

Ihun dana cigaba da yi Ina tattab'a zahiran da ba magana takemin ba illa manyan idon da kamar Kara Mata su akayi kawai take kallona hawaye na zararo mata

Wuyanta daya kumburo kuwa sai motsi yake kamar ta hadiyi wani Abu kanta da jikinta kuwa har wani hucci yake sabida tsananin zafi

Cikin azabar kuka yata rungume dani a kirjina na kalli mallaman da suka kawomin ita Ina "Ku min bayani Mai ya samu 'yata ta dawo Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na Shiga uku na lalace jameela Mai ya samu kawarki Haka ki gayamin jameela"?


Nace Ina Kara tab'a wuyan Zahira daya ke numfashi shi kadai

Zahira kuwa har lokacin Bata cemin A ba sai kallona take da idonta tana zubar hawaye


Daya mallamin ne yayi karfin halin magana Dan dukansu kuka sukeyi jikinsu a sanyaye suna kallon Zahira da Bata da bambanci da mataciya sai numfashi kawai da takeyi


"Washegarin da suka koma hutu daddare wajen karfe Tara Zahira ta tafi bandaki ita da jameela Wai zasuyi fitsari

Jameela ce ta fara Shiga ta fito kafin Zahira ta Shiga

Zahira na Shiga ba dadewa sai ihunta jameela taji da ba iya jameelan ce taji ihun zahiran ba har b'angaren Mallamai munji wanan ihun hakane yasa duk muka bazama mukayi b'angaren daliban sai dai muna zuwa muka ganta shame shame a kwance tana wani irin jijjiga hakane yasa mukayi tunanin ko Aljannu ne suka shafeta a band'akin.
Da addua muka fito da ita daga band'akin hankalinmu a balain tashe mun Saba ganin cases na dalibai masu Aljannu sai dai na zahiran sai ya bamu tsoro Dan bayan mun fito da ita daga band'akin wani irin zafi jikinta ya d'auka Kamar garwashin wuta idonta ya Zama kamar jini jikinta kuwa Banda rawa ba abinda keyi

Mallamin Dake karantar dasu ta fanin islamiyya muka Kira Dan indai case ya taso irin Haka shi yake yiwa dalibai rukiyya sai dai duk Inda ya Kai da rukiyya ba alamar sauki kwana mukayi a kanta sai gabanin asuba Muka ga ta daina girgiza ta rufe idonta.


Duk dauka mukayi bacci ne ya d'auketa hakane yasa muka Yi hayaki a office din da muka kwantar da ita

Yan aji uku wajen su shidda.muka saka su karatun Qurani a fili tunda duk sun sauke Dan duk mun yarda gamo tayi a band'akin

Wajen karfe Tara na safe ta kwalla wani irin ihun daya saka mu toshe kunnuwan mu Dan Kamar ba Dan Adam ne ya saki wanan karar ba fusge fusge ta hau Yi zata fita a guje muka riketa Gam sai dai abinda ya tsorata mu Bai wuce hallitar ta da muka ga Yana canjawa ba idonta kuwa kamar sunyo waje wuyanta ma ya kumbure duk da Bata da jiki sai Muka ga Kamar Naman jikinta ramewa yake kasusuwanta na fitowa na hallitar jikinta har d'auke hannunmu mukeyi sabida azabar zafin da jikinta ya d'auka kanta kuwa kamar baa Jikinta ba sabida zafi

Hankalinmu tuni ya tashi.mukayi asibiti da ita sai da tayi sati biyu a asibiti Ana Bata taimakon gaggawa Amma a amadadin taji sauki.ma sai azaba take Sha hallitarta na Kara canjawa likita da kansa yace mu nemi na gida larurarta bana asibiti bane muna tsoron dawo Miki da ita Haka hakane yasa muka nemi mallami a can shima yayi iya kokarinsa Muka ganin Abun kamar Kara girmama yake Kar tazo ta mutu a hannunmu batare da kunsan halin da take ciki ba yasa muka yanke dawo da ita Dan tabbas abinda ke damunta bana asibiti bane kamar dai jinnu ne.


Girgiza kaina kawai nake Ina rungume da Zahira da zafin jikinta ke Kona min jiki cikin ihun kuka na Dago da yata da ta tashi daga siffar mutane ta zama wani hallita daban Ina "Mai na muku Haka Umma Mai Zahira ta muku Umma Dan Allah kuyi hakuri da laifin Dana muku ku kyallemin yata Bata muku komai ba Umma Ni na muku laifi na tuba Umma ku cikamin yata da Bata ji ba Bata gani ba Umma Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Naseeru Zo kaga yanda Zahira ta dawo Naseeru kana Ina kazo ka kawomin agaji.kar Yata ta mutu"


Kuka nake sosai Ina surutai mallaman kuwa sai Baki suke bani jameela kawarta da mallamar su mace da daya yarinya sai kuka suke suma

Horn din da ake musu a waje sabida da motar makaranta aka kawo su.

Yasa Suka hau min Sallama suna ajiyemin kudi

Jameela kawar Zahira kuwa data ci uban kuka ta rik'e hannun Zahira daya Zama tamkar Kara tana "Allah ya Baki lafiya zahira idan mukayi hutu Zan Zo na duba ki ya Allah ka kawowa zahira Agaji ka Bata lafiya"


( Wlh Allah indai Zan tuna labarin wuyan da baiwar Allah nan ta Sha sai nayi kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Allah ya Miki sakayya duk da ya wuce wlh Ina rubutu Ina kuka)


Haka suka fita Suka barni da Zahira da har lokacin idonta Dake warwage take kallona dashi hawaye na zubo Mata Haka na d'auketa kamar ba mutum ba sabida rashin nauyi na kaita d'akina Ina kuka na shimfidar da ita Akan gado na cire Mata rigar jikinta ko no-nonta ma.shafewa yayi a kirjinta sai kasusuwa kawai kankara na dauko na zuba a katon roba da ruwa na dauko zani na na hau Danna Mata jikinta da ruwan Dan jikinta yyai zafi da yawa da kanta gani nake zata ji dadin Jikinta idan Ina matsa Mata ruwan sanyi a jikinta sai surutu nake kamar mahaukaciya kamar ma har sabo nayi Ina "Allah Mai na maka ka jarrabceni Haka Allah duk addua Nan da nakeyi nake Hana idona bacci sabida Kar wani Abu ya Samu yarana Kar wani Abu ya Samu Zahira Allah sai da Umma suka ci Galaba akanta Allah kaga yanda Zahira ta dawo Allah kaga yanda idonta ya firfito waje"

Maganar da Zahira tayi yasa kukana tsayawa cak muryarta ya dawo na Yara sosai.

Da sirirrin hannunta ta rik'e hannuna tana "Umma Dan Allah kimin addua mutuwa Umma indai kina kaunata kimin addua mutuwa Dan Allah Umma jikina kamar an hura mun wuta Umma"


(Gaskiya bazan iya cigaba da rubuta wajen Nan ba Allah yasani kuka nakeyi ku Bari na tsallake kawai nayi shi a takaice)

Jawota nayi na rungumeta cikin ihun kuka Ina "Bazan iya Miki adduar mutuwa ba Zahira sai dai na Miki adduar Samun lafiya yata da ki mutu gwara Ni na mutu Zahira Zahira ke yarinya ce Mai biyayya Mai tausayin iyaye albarkar annabi Muhammad Saw Zaki samu lafiya zahira Ni na musu laifi bake bace Baki musu komai ba Bai Kamata su tabamin ke ba wayyo Allah ka dubi halin da yata take ciki ka kawo Mata agaji ya Allah ban hada bautarka da kowa ba Kai kadai nake Kira nake kaiwa kukana bansan boka ba bansan Mallam ba Kaine mallamina Kaine Mai sharemin kukana Allah ga zahira Nan ka sasauta mata wuyan da take Sha ya Allah ka dawo da ciwonta jikina"

Kuka nake sosai Kamar Zan shidde ahaka su Nadeeya suka dawo daga makaranta

Suka shigo har cikin d'akina suna shigowa Naga duk sun ja da baya a tsorace cikin tashin hankali da ganin yanda Zahiran ta dawo


Zahira kuwa hawaye na zubo Mata ta ringa binsu da Ido a karshe ta tsayar da idonta Akan Nadeeya tana mik'o Mata siririn hannunta cikin muryar yaran tana "Nadeeya Zo gareni"

Nadeeya kallonta kawai take jikinta na rawa tana "Aunty Zahira Mai ya samu idonki Haka Mai ya Sameki Haka "?


Hannu kawai Zahira ke mik'a Mata hakane yasa ta Isa wajen Zahiran.

Tare da Kama hannun da take Mika Mata ta zauna a gefen gadon tana fashewa da mugun kuka Zahira kuwa tace "Nadeeya kimin addua mutuwa kinji Umma tace bazata min addua mutuwa ba Nadeeya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login