Showing 141001 words to 144000 words out of 180103 words
jikina konamin akeyi wuyana ma kamar garwashin wuta aka sakamin Nadeeya kimin addua mutuwa kinji"
Ihu Nadeeya ta saka duk da zafin jikin Zahira Haka ta rungumeta tana "bazaki mutu ba aunty Zahira bazaki tafi ki barmu ba aunty Zahira waye ya Miki Haka Mai ya Sameki Haka"
Tuni.kannenta suka zagayeta suna kuka
Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na Dora alwala na dauko sabon doguwar rigar da ban taba sawa ba na zura a jikina na dauko sabon hijabina fari Kal shima na saka na na shimfida Sallaya a madadin na tada sallah kamar yanda nayi niyya sai na fashe da kuka na d'aga hannuna na hau rokon Allah akan ya kawowa zahira Agaji kuka nake akan Sallaya sosai goshina a kasa Ina rokon Allah ya kawomin d'auki halin Dana tsinci kaina a ciki.
Sallah danayi ma bazan iya cewa a nutse nayi ba ahaka na shafa na nade Sallaya na nufi wajen Yata da buta a hannuna na Mata alwala na zura Mata hijabi na jinginarta a jikin gado Ina "kiyi sallah Zahira a zaune ki roki Allah Yana jinki Yana Kuma ganinki"
Bata cemin komai ba Naga ta rufe idonta da Kamar Kara waje sukeyi
Bansani ba tayi Sallah ko batayi ba dak'yar na Kora kannenta waje na saka Nadeeya Dora musu abinci Dan kuka take sosai Kamar ma zahiran ta mutu
Yarana ba Wanda ya cin abinci har Waleed dake karaminsu danaga Yana buya a bayana idan Zahira ta kalleshi sabida idonta Dake bashi tsoro
Duk yanda naso taci abinci ko bud'e Baki batayi yi Banga ta zama ba hakane yasa na bazama nemo Mai taimaka min
Gashi lokacin farkon shigowar wayane ba mu Kai ga mallakar waya da har Zan samu hanyar da Zan sanarwa Naseer halin da muke ciki
A takaice wajen Mallam naje mijin aunty Ina kuka na sanar dashi halin da muke ciki mutanen arziki daga shi har aunty da wasu daga cikin Dalibansa Haka Suka biyoni gida
Duk wanda yaga Zahira sai ya girgiza da yanda ta dawo.
Mallam kansa hankalinsa ya balain tashi shima dayake Yana da ilimi tuni yasa na fito da Zahira na shimfidar da ita a tsakar gida Suka daura alwala shi da Dalibansa sun Kai goma suka hau karatun Qurani
Sai dai ba alamar Wai akwai abinda zai fito daga jikin Zahira
Hakane yasa ya d'auko kwanun Sha Naga Yana ta tofa adduoi daya shafe awa guda Yana Yi sai daya Gama ya bani Akan na shafa Mata a jiknta ko zamu samu jikinta ya rage zafi
Cikin Ikon Allah kuwa Ina fara shafa Mata jikinta ya hau rage zafi kanta ya shima Haka take Naga yata ta sauke ajiyar zuciya bacci yayi awon gaba da ita Ashe tunda ta hadu da Wanan masifar Bata bacci
Ko a fuskarta zaka ga alamar taji dadin Jikinta kamar wacce har ta samu sauki na hau Godewa Allah Ina Godewa Mallam Basu suka bar gidan ba sai wajen Sha daya har lokacin zahira na bacci
Cassette din Qurani na kunna Mata a gefen kanta daga Ni har Nadeeya bamu iya bacci ba Haka muka sakata a tsakiya muna kallo wajen daya naje na daura alwala na Zo na hau Kan Sallaya na tadda sallah
Nadeeya kuwa bacci ne ya d'auketa a Gefen Zahira
Wajen biyun dare Ina Jan carbi Ina kuka Naga ta bud'e Ido ni kuwa na zuba Mata Ido Ina kallon yanda ta zama kwarangwal Dan ba yanda ma zaka yarda itace
tashi tayi zaune tana wurga manyan idonta daya Sakani runtse Ido Dan sosai idonta yayo waje Kamar fitilar kwai
Ta zuro siraran kafarta kamar Kara Naga tayi waje Kamar iska zai d'auketa tsaf zaka kirga.kasusuwan jikinta
Ni kuwa na mike da Sauri Dan nabi bayanta sai dai Ina fita banganta ba hakane yasa na hau nemanta hankalina a tashe Ina kwalla Mata Kira
Nishinta danaji a Bayan fridge Dina dake Palo yasa na nufi wajenta da Sauri a tsugunne take a Gefen fridge din tana Kashi
Bance Mata komai ba na Bari ta Gama na Kamata ma kaita bandaki na wanke Mata Ina "ya Kika baro bandaki a tsakar gida Kika zo Palo kina Kashi Zahira Bata cemin komai ba har na kwantar da ita na koma palon na kwashe kashin na goge wajen
Sai dai kafin gari ya wayewa na Gane Kamar kwakwalwar Zahira ta tab'u Dan sau biyu Tana kashin amadadin taje bandaki na biyun a kitchen tamin na ukun Kuma a daya dakin da yarana suke kwana tana ta Abu Haka kamar mage tana kalle kalle abinan ya dagamin hankali daya saka ni kuka har garin Allah ya waye da asussuba na bazama neman Mai taimakamin Dan Kamar Mallam bazai iya da.larurar Zahira ba
Bansan k'afata ba takalmi ba Ina tafe hannuna Dora akaina Ina kuka
Ko ni bansan Ina na nufa ba sai danayi Karo da wata makociyarmu dake can kasan layinmu na dawo hankalina
Rikeni tayi da hannu biyu tana "Lafiya kuwa mmn Nadeeya"?
A sabon unguwar.mu da Sunan Nadeeya ake kirana sabida yanda take da farin jinin mutane sosai
Zubewa nayi a kasa na rik'e kafar matar da ta kasance bafulatana ana ce Mata yaddiko tunda Muka zo unguwa na lura tana da balain kirki ba laifi Dan tasan hakkin makotaka
"Ki taimakamin yaddiko yata zata mutu yata ta samu tab'in hankali"
"Subhanallahi Mai kike cewa Haka Mmn Nadeeya
Ta dagoni Ni kuwa na ja hannunta na cigaba da sheshek'ar kuka Ina bukatar Mai taimakamin Ina bukatar agaji Ina bukatar taimakon jamaa Dan ji nake kamar nayita kwalla ihu yarana ma zagaye suke da Zahira na fito neman taimako bansan Mai yasa nake Jan hannun.yaddiko.dan.tazo taga halin da 'yata take ciki ba kawai Ina bukatar taimakone
Har d'akina na Shiga da ita a madadin Naga Zahira akan gado Kamar yanda na barta acan Gefen sip Dina naganta Tana kashin kannenta sun zagayeta suna kallonta Waleed ne kawai a waje sabida tsoronta da suke ji
Sai wuwurga Ido Zahira keyi Kamar dai mage
Zubewa nayi a kasa na Nuno zahiran da hannu Ina "Yadiko Kinga yanda yata ta dawo Kinga yanda aka dawomin da ita yadikko Kan yata ya tab'u kinga Inda take Kashi ki taimakamin yadikko idan akwai Wanda Kika sani na Kai Zahira wajensa ya Mata addua yaddiko ki taimakamin bansan kowa ba babansu Baya Nan Yana Abuja ba ta hanyar da Zan same shi na sanar Masa halin da muke ciki"
Kuka nake sosai
Yadiko ma Ina gani ta zub'e a kasa sabida tashin hankalin ganin yanda Zahira ta dawo Dan ta San Zahira sosai sosai take Santa sabida kyaunta har tana yiwa Dan autansu shaawarta Dan ya Aureta idan ta Gama makaranta
Cikin tashin hankali tacemin "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mmn Nadeeya akwai Wanda nasani zai iya taimaka Miki Bari na Kira mota mu tafi Amma fa wani kauye ne can gaba da jigawa Nima akwai kanwata datayi fama da Aljannu sai shi ya iya cire Mata su ko baa fada ba Zahira Aljannu ne a jikinta Kinga yanda ta dawo fa Ina zuwa yanzu nan kina da jan miski"?
Girgiza mata Kai nayi da Sauri
Tayi waje Ni Kuma na nufi wajen Zahiran na dagata nayi bandaki da ita na wanke Mata jikinta Nadeeya ta kwashe kashin ta goge
Duk Kayanta sun Mata yawa yawo take a ciki daidai da kayan Raheema da take karamarsu ya Mata yawa sai a Haka na saka Mata pant kuwa Bai zai saku ba Dan ba kugun duk Inda Zan kwatanta muku yanda 'yata ta dawo wlh bazaku gane ba sai wayanda Suka Santa lokacin da abun ya sameta.
Yadiko Bata fi minti talatin da fita ba sai Gata ta dawo da Mai mota datayi shatarsa.
Ni kuwa karkashin gadona na d'aga a cikin kudin sana'ata na dauko kudin da Dan yawa na rik'e a hannuna
Muka fito na roki Nadeeya data kularmin da gidan har ta rame itama.
Idonta yayi jawur dan kuka..
Muna fitowa muka dau hanya
Bamu Isa kauyen ba sai wajen karfe uku shima sai da muka hau machine Nadeeya na zaune a cinyata muka Isa gidan Mallam Mai sallati Haka ma Naga an saka daga wajen gidan
Ga almajirai Nan birjik suna ta karatu
Bamu Sha wahalar samun sa ba Bayan mutane biyu da suka Shiga ciki suna fitowa muka Shiga
Muna Sallama ya d'ago Suka had'a Ido da Zahira Zahira ta kwalla wani mugun. Ihu daya saka kunnena Yinn wani iri
Riketa nayi Kamar jaririya sai gashi ta duro da ga jikina ta hankadani tana k'ok'arin Yin waje.
Da mugun k'arfi na riketa Amma ga mamakina wani irin tureni tayi yadiiko itama tayi saurin riketa Dan Kar dai ta fita a gujen
Shafa Mata Jan miskin Nan a goshi Yi sauri
Mallamin yace Yana k'ok'arin mik'ewa sai dai kafin yaddiko ta bud'e kwalbar miskin Zahira ta Kara sakin wani mugun Karan ta zub'e a kasa ta hau wani jijjjiga hankali a tashe na fara k'ok'arin yin kanta Mallam Mai sallati ya hanani akan Kar na sake na tab'ata
Wani irin iska ne ya kaure a d'akin lokaci guda Kuma komai ya baje Naga Zahira ta bar jijjigan.
Mallam Mai sallati ya tsuuggna a gaban zahiran ya shafa Mata Jan miski tare da daure kanta da farin kyalle yace na ja ta gefe.
Da Sauri na dauki yata na Dora a cinya Dan tsayin kafafune kawai zai saka kasan babba ce amma ya dawo kamar dai yarinya siffar.dai Gata ga kamarta
Kukan da nake Bai saka na iya ce Masa komai ba sai yaddiko ce ta Dan Masa bayani
Shima Bai ce komai ba illa kasko Dana ga ya d'auko ya zuba wani hayaki a ciki ya hau bayani Yana "Kuna shigowa nasan turen bakakken Aljannu arna akayi Mata da har zai rabata da numfashinta zakuji jikinta na d'aukar zafi Bata iya bacci zatayi ta Abu kamar Mai tab'in hankali yanzu Kuna shigowa ma sun San ko yayane sai mun faffata dasu hakane yasa Kuna shigowa suka bar jikinta duk abinda zaayi yanzu basa jikinta Kuna tafiya zasu dawo jikinta Aljannu sun fi su ashirin kowane da aikin da yakeyi a jiknta.
Zaki kashe kudi baiwar Allah Dan yanka zamuyi muyi ta Basu hakuri har mu samu nassarar Mai dasu wajen wayanda Suka Mata turen bakakken Aljannun
Jiki na rawa na Ciro kudadeen Dana saka a Leda na mik'a.masa.
Bai karba ba ya Kira baban Almajiransa akan ya karba ya siyo.masa katon bijimin saa.a daure Masa daddare akwai aikin da zaiyi
A takaice Anan yadikko ta barni da Zahira tare da alkwarin duba min yarana
A ranar a gidan Mallam Mai sallati na kwana matansa sai tausayina suke karfe daya daidai Naga an yiwa Zahira alwala Dan har lokacin Bata bud'e idonta ba Almajirai sama da goma suna zagaye da ita Mai sallati Ma na d'aga gabanta suna ta karatu Yana Yi Yana yarfa mata ruwan addua Yana goge mata jikinta da wani ganye Zahira dai Bata motsa ba Ina kallonsu har sai da Mai sallati yasa aka kawo Masa kasko ya watsa wani irin magani Mai kamar borkono ko mu damuke nesa sai da mukaji zafinsa ya hau shigar mana hanci
Ahaka.yasa.mazan Nan suka d'ago.zahira da tana fara shak'ar hayakin ta bud'e Ido ta fara k'ok'arin fusgewa.ya da Danna kanta akan kaskon Yana saka kaskon a daidai hancinta ta kwalla wani irin Kara ta hau mimikewa idonta duk.ya yo waje
Bulala Naga mallamin ya d'auko ya hau zabga Mata Wai zasu yi.magana ko bazasu Yi ba
Tuni naji muryar yata ya dawo daidai ta hau ihun "Umma Dan Allah kizo ki.kwaceni daga hannunsa wlh Tallahi nice Umma Ni yake.duka"
Aguje na Isa wajensu shi kuwa Mai sallati ya daka min tsawa.akan Kar.na matso.kusa dashi ba Zahira bace Aljannu ne "(Ashe dgsk zahiran ce yake duka ya d'auka.aljannu.ne Dan Wasa sukayi ta Masa da hankali Yana Dan da rukiyya suke.fita idan suka.ga zaiyi wani Abu sai su.shiga jikinta su Yi abinda zaa dauka sune.
Ahaka yata ta Sha bulalai da hayakin Dake juyar.mata da.kai idan akayi har muka samu kwana uku ahaka a Rana na hudu da yace na Kara kawo kudi.
A ranar Naseer ya duro gidan Mai sallati hankalinsa a balain tashe Yadiko ta rakasho
Wanda zuwansa kenan su Nadeeya suka Gaya masa yaje har gidan yaddiko.ya rok'eta ta rakashi.
Ina ganinsa na fashe da kuka Bai kalli inda.nake ba ya nufi wajen Zahira dake shimfide a kasa kamar gawa idonta kawai manya.datake wurgawa tana kalle kalle yasa zaka San tana rayye
Tunda nake ban taba ganin Naseer a cikin tashin hankali Dana ganshi ba a lokacin Daya xube a gaban zahiran jikinsa na wani irin karkarwa cikin wani irin murya yace "Zahira"
Zahira siririn hannunta ta mik'a Masa cikin muryar Yara tana "Abba kayimin addua mutuwa Dan Allah Abba jikina konewa Yake kamar an hura garwashin wuta a wuyana"
Da hannu daya ya wawuro Zahira ya hadata da kirjinsa Yana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha
Allâhumma lâ sahla illâ mâ ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hazana idhâ shi'ta sahlan.
Addua kawai yake Yana kamkame da Zahira a kirjinsa dayake Jin fatarta na kona Masa jiki
Cikin kuka nace "Naseer Dan Allah Dan annabi dan darajar Muhammad sallahu alaihi wa kaje wajen Umma da Safiyya ka Basu hakuri su kyallemin yata Bata musu komai ba ba abinda Zahira tayi data cancanci Haka daga wajensu kazo muje Naseer bana San na rasa yata ni suka tsana sumin hukunci Dan Allah Naseer kaga yanda suka dawomin da Zahira Zahira yanzu Kamar Mai tab'in hankali Naseer ka taimakamin muje na Basu hakuri kaga Zahira yanda ta dawo su sake min ita Dan Allah"
Na karashe Ina kuka
Mik'ewa yayi da zahiran a jikinsa Yana muje banyi gardama ba nabi bayansa
Ko sauraren Mai sallati bamuyi ba Dan nidai a idona Banda dukarmin ya da yayi ba abinda ya iya min sai kudadena daya cinyemin gabadaya Dan sai da na tattaro sauran kudin nasa Nadeeya ta bawa. Yaddiko ta kawomin ta hanyar Mata wasika
Shatar mota mukayi Naseer na rik'e da Zahira jikinsa Yana ta hawaye nidai burina nagani a wajensu Umma na kwanta nayita Basu hakuri
Sai dai muna isowa Kano Naga Naseer na cewa driver ya Kai mu station Inda na Kai kararsu Umma Ni kuwa cikin tashin hankali nace Mai zakayi
"Na gaji Naeema wlh zahira xan nuna musu suga abinda suka Mata wlh sai sun dawomin da yata daidai wlh Mahafina Bai gayamin gaskiya ba Umma ba ita ta haifeni ba Kinga yanda 'yata ta dawo Naeema
Hankalina a tashe nace "Dan Allah karka Kai kararsu
kararsu muka Kai Suka dawomin da ya Haka muje mu lallaba su
Ko kulani Naseer baiyi ba yasa driver ya Kai mu station ban iya sauka a motar ba sai shi ya Shiga da Zahira Yana kuka wiwi
Bayan shigarsa da. Mintina goma Sha biyar sai gashi ya fito da Zahira a sabe a kafadarsa
Wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu shi da Yan sanda wajen shidda da mace Yar Sanda Nan sun duru a motar Yan sanda driverr dayake janmu.ya dau hanyar gidansu Umma Naseer na Masa kwatance motar Yan sanda na biye damu a baya
Nidai kuka nake ina cewa Naseer matakin da zai d'auka bashine mafita ba ya Bari mu lallaba su idan aka kullesu wlh ya Kara jazamin zaiyi ko kulani baiyi ba.
Har Muka Isa gidan gabana ya hau fad'uwa
Yan Sandan a fusace Suka duro daga motocinsu mace Yar Sandan na musu jagora Dan Ashe wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu ya fusata muna Ransa Haka kawai yake tausayin nida Zahira.
Naseer jikinsa na rawa ya fito daga motar Yana. "officer a taimaka min a matse su har sai sun dawomin da yata daidai Dan sai da suka rantse sai sun kasheta.
Ina cikin motar ban bisu ciki ba sai kuka nake ina addua Allah yasa Kar wani balain ne zai kara tunkaroni nidai burina su dawomin da yata daidai.............
Comment
Labarin nan yayimin kala da halin da muka shiga a baya, amma alhamdulillh addua be bar komi ba, wlhi kakarmu da zata sami dama itama setayi abinda yafi na hajara amma inda Allah ya rage ma aya zaki ita din yar dangice sosai dan yanzu hakama su suke Sarautar garinsu amma fa maganar tsafi da asiri ba kalan wanda batayi, ba kalan Wanda batayi mana ba har na gobara😰 ta tura ma qanwata aljani me kunna wuta haka muna zaune waje ze kama da wuta akashe wani wuri yaqara kamawa daga karshe seda gidanmu yayi kurmus
Babanmu ba kalan asirin talaucin da batayi mishi ba amma dayake Allah ba azzalumin sarki bane kuma shi yake ba ma wanda yaso ya hana ma wanda yaso haka tanaji tanagani Ze samu kudin amma sedAi kaman wuta yacinyesu zasu qare abanza baayi komi dasu ba, amma yanzu kumi yazama labari sedai abin da baza’a rasa ba tunda hausawa sunce me hali baya fasa halinshi amma yanzu ko ita kanta tasan munfi karfinta da ita da yayanta goma duka sun tsanemu ba wanda acikinsu baya mana asiri musamman takwaran safiya Tafi kowa mugunta cikin Yayan
Kullum burin kakanmu bewuce baban ya mutuba taga yarda zamuyi, gwara ma hajara hankalinta na tashi in taga be lafia itakam babban burinta ace mutuwa ta riskeshi ace be barmana komi na gado ba mu wulaqanta
Advertisement
*Mg's herbal whitening black soap*
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi