Showing 153001 words to 156000 words out of 180103 words
da akwatin kudi.
Sai dai har aka Gama birkita d'akin ba'a ga komai ba Dan abokanan Bashir masu irin halinsa ne Suka gudu da kudi da gwalagwalan Bashir shi Kuma aka kamashi San a sake shi yasa yayi niyyar kulawa Safiyya sharrin ita ta saci kudin inyaso a cika shi ita a kamata.
Bai tab'a Jin kaunar mahaifiyarsa a ransa ba hasali wani zubin zuciya Kan raya Masa abubuwa a kanta na ya Mata mugun abu ko ya ma kawo karshenta (Wanan Yana daya daga cikin asirin da Safiyya tayi daya jefa Dan cikinta a cikin wanan halin sanan nayi mistake sosai a wajen tsara rubutun labarin Dan sai da muka sake waya ta Kara fahimtar Dani labarin wajen auren Safiyya na Dan jinkirta shi a rubutun Dan Bashir din sa'a Minal ne 'Yar Naeema ta uku gudowar da Naseer da Naeema sukayi Kano a lokacin da ta haifi Minal a lokacin Safiyya tayi aure har ta haifi bashir
Wanda ta ta sake samu ta aura a shine suka siyar da gidan Naseer.
Zawarcin da Safiyya tayi ne tare dasu ta tsula tsiyarta haka amma dai a karbi labarin Haka sabida ya tafi daidai tunda ban dai cire komai a game da rayuwarsu ba sai na Naeema dana dan rage sabida tsayin novel din zan dan Kara bada labarin Safiyya a takaice sabida labarin ya tafarmin dai dai Kar dai ku rikice sai da Naeema ta bibiyi labarin taci gyarana)
Dan Sandan umarni ya bada a tafi da Safiyya a hada a kullesu tunda har Bashir din yace Yana Bata ajiya ya zama dole itama a bincike ta da kyau dan bashir ce musu yayi idan yayi satar ita yake bawa ajiya.
Wani irin ihu Safiyya ta saka a lokacin da taga ana k'ok'arin saka mata ankwa ko sauraranta basuyi ba.
Suka buga Mata gindin bindiga da suka ga tana tirjewa suka sa.mata ankwan
Suka zuba su a mota ita da Bashir
Sai kuka Safiyya take tana rantse rantse Bashiri bai bata ajjyar komai ba.
A takaice sai da Safiyya ta Sha bak'ar wahala a hannun 'yan sanda ta Sha bak'ar duka daya canja Mata kamani Dan Bashir dagewa yayi akan ita ya Bawa ajiya kudin.
Sai data samu wata guda a kulle kafin wani dan sanda dayaji Safiyya ta kwanta Masa ya taimaka wajen bincikar Bashir din ta hanyar rarrashinsa ya fada Masa gaskiyar wayanda Suka gudu da gwalagwalan da kudi.
Sai da aka kamosu aka saki Safiyya da kyar.
Safiyya kuwa masifar da Bashir ya jefa ta a ciki yasa ta Kara kullatar Hajara a ranta ta ke Kuma Kara Shan alwashin ganin bayan Naseer da su Naeema tunda Dan Naseer Hajara ta fasa mudubin daya jaza wa danta wanan masifa da ita kanta a rayuwata Bata had'a San Bashir da komai ba.
Hakane yasa da fitowar ta ta koma wajen Oban ko zai iya taimaka mata a saki Bashir sai dai duk yanda Suka Kai da suyi aikin ba'a sake shi ba.
Akan dole ta hakura ta saka aka mata aiki akan Ado dan sandan dake santa.
Nan da nan kuwa ya fito ya aureta a madadin ya sata a gidansa sai shine yake zaune a gidanta da Sunan zai cigaba da biya Mata haya.
(Karku rude a takaitacen labarin Safiyya nake Baku Aurenta na fari ta haifi bashir na biyu data tayi ta siyar da gidan Naseer ta haifi Asmau da Safiyya wacce aka sawa sunanta.
Mijinta na fari Saki uku ya Mata daya gano asirice shi tayi ya Aureta
Na biyun Kuma data haifi Yan biyun barinsu tayi a can wanan sai da suka yi wayo ta sa aka Mata aiki akan Umar ta karbo su daga wajensa ta rik'e su amma tabbas Bashir asirin Satan da suka so Zahira tayi shine ya Sha alewar daya saka shi satan bandai canza komai ba dafatan Kun Gane mu cigaba da tafiyar da labarin ahaka karku rikice laifina ne Dan yanzu idan na cigaba a haka kuka ga na Sako Asmau da Safiyya yaran Safiyya a labarin zaku rude bazaku gane ba shiyasa na baku labarin Safiyya a takaice)
Sosai Safiyya take Jin dadin irin wahalar da Zahira take Sha ita da Naeema da Naseer karewar komai da naeema ke dashi yafi komai faranta Mata da zata samu ma abinci ma so take ya gaggaresu ci
Ko sau daya batayi nadamar abinda tayiwa Hajara ba hasali duk lokacin data tuno halin da Bashir.ke ciki a kulle takan ji kamar ta nemo Hajaran tayi ta dukanta sosai ta saka Hajara a jerin makiyanta tsabar masifa ma tana sane da duk halin da Hajara ke ciki.
Haka ma tana da labarin halin dasu Naeema ke ciki dan takanje wajen Oban yayi surkulle ya nuna Mata su
Taji dadi sosai da Aljannu ke fita daga jikin Zahira idan za'a Mata rukiyya sai an Gama azabtar da Zahira angama rukiyya Aljannun ke komawa jikinta.
Taso ta Kara yiwa Naseer asirin Dan ta mugun tsanarsa sabida Hajara data ga bata so wani Abu ya same shi,sosai ta Sha alwashin ganin bayansa dan har yanzu da tab'ab'unan dukan Naseer a jikinta.
ta dan dakata ne kawai Dan wahalar da suke Yi da Zahira har filinsa da ya siyar akan nemawa Zahira magani ya faranta mata sosai burinta ma gidan Naeema shima su siyar a garin nemawa Zahira magani dan tasan kome za su yi bazasu Dace da samun magani da zai yiwa Zahira aiki ba.
Auren ado da tayi ma ba Wanda yasani balle Hajara ta sani
Ahaka har ta haifi yarta hauwa da itama taji tana balain Santa takan tuna yaranta asmau da Safiyya dake gidan Umar har jibi tana Kan bak'anta nasan ganin Bayan Hafsa da ta azabtar da ita a gidan umar.
Sati sati take zuwa wajen Oban dan taga halin da su Naeema ke ciki
A lokacin da asirin da tayiwa Zahira ya Kai shekara da wata uku Oban ya daina iya ganin komai akan su Naeema sosai hankalinsu ya tashi daga shi har Safiyya Oban yayi ta tsubbuce tsubbuce dan yaga halin da suke ciki sai dai har ya gama tsubbunsa bai iya ganin komai ba
A lokacin kuwa Naeema ta had'u da Inna Amina har rabbi ya amsa adduarsu Amina tayi nassarar fitar da Aljannun daga jikin zahira.
Safiyya tunda Oban ya daina ganin halin da su Naeema ke ciki hankalinta ke tashe ta tuna lokutan baya da idan suka yiwa Naeema wani mugun abu toh mudin suka daina ganinsu ta mudubin tsafi toh Naeema ta samu mafita ne tana tsoron aikin da tayi akan Zahira ya dawo mata.
A haka ta kasance cikin Zullumi yau da safe Ado ya fita aiki da sassafe ta gama dan aikace aikacen gida tayi wa hauwa wanka da bata fi wata biyu ba lokacin.
Tamkar gwal take Jin hauwa a ranta
Tun bata girma ba take cin burin girman ta idan tana hararo girmanta har farin jinin Zahira take hango Mata da irin masu kudin da zasu ringa layi akanta idan kuwa Asmau da Safiyya suka dawo gabanta har maganin farin jini zata karbo musu dan sosai taci buri Akansu suma duk da basa gabanta tana balain Kaunar yaranta da bata San wani abu ya tab'a Mata su babban burinta yanzu ma ta Samu Bashir ya fito daga gidan yarin.
Tana kitchen tana k'ok'arin juye tuwon data dumama dan taci taji hauwa ta fara tsalla kuka aguje ta fita daga kitchen din.
Abinda ta gani ne yasa jikinta d'aukar rawa hallitar hauwa ne ya canja gabadaya ta koma wani irin hallita wuyanta ya kumbure exactly yanda Zahira ta koma Kamar wata kadangare haka hauwa ta dawo hankali a balain tashe Safiyya ta saki ihu tunaninta na bata Aljannun zahira ne suka dawo.mata jikin 'ya.
Bata iya daukarta ba sabida zafin da jikinta ya d'auka ta hau kuka ta nananada Hauwa zaninta kafa ba takalmi tayi wajen oban.
Tana zuwa ta zub'e a kasa ta ajiye Masa hauwa da siffarta ya Kara Zama na kadangare sosai
Ihu take akan Oban ya taimaka Mata.
Oban kuwa take ya hau surkulle Yana yare da shi da Aljannun jikin hauwa kawai keji.
Sai dai duk yanda Oban yaso su bar jikin hauwa k'i sukayi akan ba haka akayi dasu ba har sai sun kwashi shekarun da akace suyi tun farko.
Oban kuwa baya so nunawa Safiyya ya kasa fitar Mata dasu hakane Yasa ya yanke Mata kudi Mai yawa akan ta kawo akwai Abubuwan da zai siya ya roki Aljannun su fita dan zuciya sukayi sabida matar data fitar dasu ta kokona su.
Safiyya hannu ta dora aka ta hau zunduma ihu tana ya taimaka Mata bata da ko sisi ado tana aurensa ne kawai Amma ba kudine dashi ba dan matarsa ke karbe albashinsa.
Matarsa Kuma ta fita hatsabibanci tunda har Oban ya kasa aiki akanta kasancewarta itama bayarabiya.
Ba Inda Safiyya bata je neman kudi ba amma Bata samu ba tayi kukan ta tsinewa Naeema da Zahira yafi cikin kwando
Ado kansa guduwa yayi daya ga yanda hauwa ta dawo dan sosai ya tsorata da yanda hauwa ta dawo dadin daya ji Safiyya dama bata San gidansa ba dadin dadawa ma Dama Yana neman hanyar da zai gudu sabida kudin hayan da Safiyya ke damunsa da ya biya.
Sosai Safiyya ta rame ta kanjale a madadin taji tsoron Allah ta yarda Allah ke Kare Naeema tunda duk abinda ta nufeta dashi kanta yake komawa bata ga haka ba zuciyarta k'ek'ashewa tayi tana dora alhakin duk abinda ya sameta Akan Naeema da Naseer har da Hajara sai Kara kula wani sharrin take
Ta Kara komawa wajen Oban cikin tsananin san dai ta ga bayan Naeema da Naseer
Ta karkace ta hau gaya masa abinda take so dan gani take ta haka kawai zata dau fansar yanda yarta ta dawo da ita kanta take fita aguje sabida tsoratatan da take yi
"Kayimin aiki Mai k'arfi Oban inaso na ga bayan Mutanen nan duk Inda kudi suke Zan nemo na kawo maka "tunda Aljannun da aka tura jikin Zahira sun bar jikinta inaso a tab'ata inaso ta sakawa Naeema hawan jini Kar tayi albarka Sam tayi bakin jini Kamar ungulu ta tsufa a gaban Naeema.
Shi Kuma Waleed dinan dana ga Kamar shine zuciyar Naseer inaso ya lalace a saka kiyayya tsakanin shi da Naseer a karshe Naseer ya zama ajalinsa Yan sanda su kulleshi.
Oban kayi min wannan k'ok'arin ni Kuma duk abinda kakeso Zan maka tunda har 'yata hauwa haka Zan ringa ganinta zuciyata na ciwo inaso zuciyar Naseer da Naeema yayi bindiga bana San aikin Kuma ya karye duk Inda zasu Kai ga neman taimako"
Mugun dariya Oban ya kwashe dashi ya d'auko wasu allurai da kwarya ya Bawa Safiyya yana ta jejjera alluran a ciki ya d'auko wani Abu kamar bby na namiji da mace yace ta binne akwai Wanda zaiyi daga Nan indai ta binne aikin gama ya gama Amma fa idan har akayi nassarar karya asirin duk wani Abu da zai biyo baya tayi kuka da kanta.
Batare da tunanin komai ba tace ta amince sabida mugunta tace sauran yaran naeema ma a tab'a su.
Sai da ta kwana da Oban ya ci ubanta yanda ya kamata ta dawo gida tayi zazzabin sati guda kafin ta samu karfin neman abinyi tunda ado ya gudu
Ta dai saka Oban ya Mata aiki Dan ya dawo.
A Haka ta samu ado ya dawo ya Kuma biya Mata haya.
Halin da take ciki da hauwa da ita Gata kamar dabba Kamar mutum yasa ta nemi kudi taje unguwarsu Umar tsohon mijinta a lokacin data Isa Bata sameshi ba sai Hafsa.
Yaranta duk sun tafi makaranta,Asmau da Safiyya nata zuba aiki kamar jakai yaran nata sun girma Masha Allah Kuma kyawawa kamar yanda taso ganinsu.
Sai dai kana ganinsu kasan a wahalce suke dan Hafsa ba k'aramin azaba take gana musu ba.
A takaice Hafsa k'in bari tayi ta kwashe yaran sai da suka ci uwar dambe Safiyya ta Sha kasa dak'yar da kyar Umar daya dawo ya samu Hafsa ta Bari Safiyya ta tafi dasu dan shima kasan tausayin yaran yake ji uwarsu ya tsana Amma Yana san yaransa tausayin yanda hafsa ke gana musu azaba yasa yaji dadin zuwan da Safiyya ta yi dan ta tafi dasu at least zasu samu yanci a wajen Mahaifiyarsu.
Safiyya sai da umar ya Bata kudi Kafin ta yarda ta tafi da yaranta da takejin zuciyarta fari Kal da dawowarsu gabanta.
Hajara
Sosai take Shan wahala da kosai da take siyarwa Bata da burin daya wuce ta samu kudi ta fara tab'a Safiyya da take Shan alwashin ganin bayanta ba ranar da zata wuce Bata tsinewa Safiyya ba takan Yi kuka idan ta tuna irin korar Karen da Safiyya ta Mata Wai ace Yar cikinta data fi so duk a cikin yaranta itace ta daketa har ta koreta daga gidanta yau badan usaini kaninta ba da Bata da wajen da zata zauna lami ma Mai taimaka Mata kad'an kad'an itama ta bar garin calabar.
Mai taimaka Mata a cikin yaranta Kuma Naseer ne shima Naeema ta kwace shi ya Fifita Naeema akanta
Shiyasa a rayuwata ta tsani Naeema takejin itace duk ummul abaisin daya saka ta tsinci kanta a cikin wanan halin dan da ta rabu da Naseer cikin sauki da bata kai ga aikatawa Naseer Abunda ta aikata Masa da har yazo ya shafeta tafi Shan wahalarsa ba tunda da ace Naseer nada kudinsa da yanzu Yana da gidaje ya Kai uku tunda ada din ma ya mallaka Mata gida biyu.
Ba abinda Naseer baya Mata Amma Naeema ta Mallakeshi ta rabata da danta
Tijjani kuwa dama kullum cikin yi masa baki take tunda har ya Fifita Murja a kanta a wajenta Kam yaranta biyun Nan Tijjani da Safiyya idan tana da dama sai taga bayansu ba ma kamar Safiyya da take Jin da tana da dama kasheta zatayi tsaf abinda ke take Mata birki kawai shine kudin da bata dashi.
Da zata iya samun damar da zata Shiga wani kungiya da ta Shiga dan ta samu cikar burinta da ta saka an maidawa Naseer arzikinsa.
Ta rabashi da Naeema ta azabtar da ita da Zahira ta wahalar da Safiyya Murja da Tijjani a rayuwa sai dai ko kudin arziki Bata dashi kudinta ma yanzu na cinikin kosai a magani yake tafiya Dan fama take da wani irin ciwon kafa dake hanata bacci ta Rasa Mai ya haddasa Mata ciwon kafa.
Tijjani
Talauci da tsananin rayuwa yasa baya iya neman Naseer yanzu Dan wayar gari yayi aka koreshi daga aiki duk Kuma buga bugan da zaiyi baya iya samo ko sisi.
Sai Murja ce ke dan iya rike gidan shima cikin wulakanci Sam Baya lallaba murjan tana Masa iskanci ko gori zai nada Mata na jaki ya Kuma bar Mata gidan
Yanzu haka yaransu hudu duka Mata bayan yarsu ta fari ta Kara haihuwa uku da kusan kansu daya gwanin shaawa yaran
Murja ko kuda Bata so ya tab'a Mata Yara Allah ya jarrabceta da balain San yaranta shiyasa duk Inda kudi suka shiga tana k'ok'arin nemowa dan ta farantawa yaranta Rai.
Mahaifiyarta Rabi a haihuwa yarta ta uku Allah ya Mata rasuwa ta hanyar Hatsarin mota sosai Murja tayi kukan rashin ta.
Yaranta kawai da take gani ke faranta Mata rai ko a makaranta aka tab'a Mata su sai taje tayi masifa tayi balai ko yaran makota ne Suka tab'a Mata Yara sai ta Rama musu.
Yarta Murja data ci sunanta nada shekara goma Mai bi Mata Ramlat nada shekara takwas Fareeda na shidda sai ummi nada hud'u.
Tashin hankalin da Murja ta fara fuskanta a rayuwarta Bai wuce rashin lafiyar da yaran nata suka fara lokaci guda ba
Kamar ta zauce sabida tashin hankali
Banda Murja takwararta
Ramlat ce ta fara amsa Kiran Mahallicinta Inda Murja sai da aka dangana da kaita asibiti sabida sumewa tayi tayi
Sati biyu kafin ta Gama dawowa hayyacinta fareeda itama tabi Bayan Yar uwarta hauka tuburan Murja ta kusa yi sai da Karfin adduoi ta dawo daidai
Fareeda itama satinta uku ummi tabi bayanta.
Rasuwar yaran Murja uku yasa Murja ta dan samu tab'in hankali kad'an Amma ba sosai take tab'a haukan ba takan Yi Abun marasa hankali
(Inaso na Dan bada labarinsu Suma gajerce Dan wlh na gaji Bai xama lailai na Kara tabo bagarensu ba Dan yanzu Haka ma daga Naseer har Naeema ba labarinsu sukeji ba tunda suka je suka nemi yafiyar Naeema dasu Zahira.)
Bayan yaranta uku sai data Kara haihuwar biyu sai sun girma ta shaku dasu sai su koma ga Allah a irin haka yasa daga Tijjani har Murja Suka bazama neman taimakon Mallamai anan wani ke cewa Murja taje ta nemi yafiyar yaran data zalinta a baya sai ta nemi yafiyarsu zata ga daidai
(Ba fiction a labarin zalincin da Murja tayiwa su Zahira da Kuma jarrabtar da Allah ya Mata a rayuwa na rasa.yaranta idan ta haifesu bamu sani ba ko ta Kuma haihuwa Dan tunda sukaje suka nemi yafiyar Naeema baa Kara Jin labarinsu ba)
Naeema
Samun saukin da Zahira tayi Yana cikin Abubuwan farin ciki da suka sameni da bana mantasu
Haduwa da Inna Amina danake Mata
Kallon Mahaifiyata dagani har Naseer shima Yana cikin Abubuwan da har gobe bana mantasu.
Inna Amina tsohuwa ce Mai tarin ilimi dan Zan iya cewa har tafi Naseer ilimi shigowarta rayuwarmu yin Allah ne dan ta silarta na Kara samun warwarewa wasu matsalolinmu ba iya ni kadai ba har Naseer.
Satinta uku a gidanmu bayan tafiyar su Nadeeya makaranta muka Shiga wajenta dan mu gaisheta
Zamanta a gidanmu yasa nake Jin kamar ita din wata garkuwa ce a garemu gabadaya
Dan tace Mana zama Bai Kama mu ba makiyanmu zasu cigaba da bibiyarmu da sharri Addu'oi ta bani da Naseer take akan mu ringa yi daga mu har yaranmu.
Zahira kuwa sabida ramar da tayi da kuma shiru shirun da takeyi yasa Inna Amina tace mu bari ta dawo daidai sosai ta samu wata uku tana Shan magungunan data had'a Mata kafin muyi tunanin Mai data makaranta.
Hakane yasa muke kula da Zahira dagani har Naseer muke ririta ta.
Nidai gani nake duk da sun fita kamar yata Bata dawomin yanda take ba Kamar da da nayiwa Inna Amina magana cemin tayi kar na damu zata dawo daidai mu dai cigaba da Bata maganunanta
Koko da kosai da take Sha a lokacin da muka Shiga d'akin nida Naseer tana ganinmu ta saki murmushi muka zauna akan tabarma ita Kuma tana daga Kan katifa
Sai data karasa kokon ta ajiye kofin muka hau gaisheta
Cikin faraa ta hau amsawa