Showing 159001 words to 162000 words out of 180103 words

Chapter 54 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2468

ayi rushing Dina Ana rushing Dina zanyi a gurguje wlh alhalin labarin Bai Kai a Gama ba yanzu nan nayi typing dan karku jini Shiru Ina samu sarari gobe xaku jini idan ban samu ba ayi hakuri jibi na bada Mai yawa*
8/19/21, 10:33 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


Page 59


Nadeeya Ido ta zaro ta kalli Naseer da ya fara kokarin barin wajen fuskarsa a had'e.

Waleed shima wani irin Mugun kallo yabi Naseer dashi kamar ba mahaifinsa ba.

Yan sanda tuni Suka tasa keyar Waleed suka saka shi cikin motarsu

Nadeeya kuwa da hankalinta ya balain tashi da tafiyar da za'ayi da Waleed ta Sha gaban Naseer da Sauri dan duk da rashin Jin da Waleed yake gwada.musu yake Kuma musu rashin kunya hakan bai sa sunji kaunarsa ta ragu a zuciyarsu ba hasali yanzu tausayinsa suke ji tunda Naeema ta gaya musu duk abunda yake yi ba'a hayyacinsa yake yi ba.

"Abba cewa kayi fa idan an tafi dashi Kar a sake shi Abba kaga zasu tafi dashi"?

Naseer bai kalleta ba ya cigaba da tafiyarsa Yana zabga Sauri Dan sosai yaji zuciyarsa na kunna da ganin Waleed din dan ganin daya Masa ma ji yayi kamar ya shake shi yayi ta duka har sai ya daina numfashi.

Wani abu yaji Yana danne zuciyarsa akan San Waleed da tausayinsa

Nadeeya kuwa ganin Naseer ba alamar zai tsaya yasa tayi gida aguje tana kuka.


Idona na Kan kofa tunda su Naseer suka fita da Nadeeya nemo Waleed bani da burin daya wuce irin naga sun dawo tare dashi dan yau ma ban saka shi a idona ba.

Ina Jin Zahira a d'aki da Naseer ya kulleta tana kananan surutai

Ni nasan da ikon Allah kawai nake numfashi har yanzu zuciyata bata buga ba idan na dubi Zahira 'yata da nake jinta duk a yarana sabida hankali da tarbiyya ta na ga yanda ta dawo yanzu yarinya fitsarariya sai naji kamar na cire zuciyata na Yar sabida ciwon da yake min a haka ma Wai dan Inna Amina na iya k'ok'arinta a kaina da yarana da babu ita bana Jin Zan kawo yanzu

Waleed dana daya tilo da yayi hannu Riga da duk wani Abu Mai kyau ya koma Mara kyau ganinsa a Wanan halin kawai na iya sawa zuciya ta ta buga lokaci guda

Na gwammaci ni su Umma suka hukunta suka ma kasheni da barina da sukayi a rayye da banida bambanci da mataciya sabida halin da yarana ke ciki.

Sun watsa min rayuwar yarana da Karfin addua Yata Zahira ta tsaya a iya bin kawaye bata hada da bin Maza ba
da Karfin addua Waleed ke rashin ji da bai had'a da sata da shaye shaye ba.

Nakan hararo da yarana Basu hadu da wanan jarrabtar ba da kila Zahira ta Dade a gidan aure ko tana mataki na biyu a babban makaranta sai dai Kash gata a gabana ko secondary bata gama ba an susutar min da ita.

Shigowar Nadeeya aguje tana ihun kuka yasa ni mik'ewa tare da dafe kirjina da na ji kamar an soka min kibiya.

"Umma 'yan sanda sun tafi da Waleed station saboda ya fasawa wani yaro kai da kwalba Abba yace idan Suka tafi dashi Kar a sake shi"

Tunda ta fara magana naji gidan na juyamin har Naseeru shima ya shigo a daidai lokacin dana tafi Zan zub'e a kasa ya taroni da sauri.

Sai da na jima Ina sallati kafin naji kaina ya daina juyamin

Maganar Nadeeya na Kara maimaituwa a kaina

Ido na sauke akan Naseer Ina "Wai an tafi da Waleed station Kuma kace Kar a sake shi"?

Kamar wanda na kwarawa ruwan zafi ya mike da Sauri yana "Duk ranar da Waleed ya taka kafarsa gidanan sai na raba shi da numfashinsa tunda ya zabi ya Zama dan iska gwara ya je ya cigaba da iskancinsa Kuma ban yarda wani yaje station dan yayi belinsa ba gwara suyita rikeshi acan"

Yana gama fadar haka yayi daki a fusace

Ni kuwa Zan iya cewa tunda ya fara magana nayi suman wucin gadi na kasa yarda Naseer ke furta kalmomin nan daga bakinsa.

Na dauka zai fi kowa Shiga tashin hankali da halin da Waleed ya tsinci kansa lura da irin Kaunar da yake Masa ga mamakina Dan namu yake cewa Dan iska

Bansan yanda akayi na mik'e na isa d'akin da ya Shiga ba yana Gefen gado a zaune

Ban karasa ciki ba daga bakin kofa na Kira sunansa da Naseer dan Abban Waleed nake ce Masa tunda na haifi Waleed na bar ce Masa Abban Zahira.

Indai na Kira sunansa toh ba karamin magana zamuyi dashi ba

dagowa yayi da jajjayen idonsa Yana kallona

"A hayyacin ka kake kuwa Naseer Waleed aka tafi dashi station a gaban idonka baka yi komai ba kace Kuma a idan an tafi dashi Kar a sake shi"?

"Eee Ni nace Kar su sake shi Naeema Kuma ban yarda wani yaje belinsa ba dan bazai yiwu ya ringa jawo mana magana ba yaje can ya karaci iskancinsa"

"Waleed kake jifa da munanan kalamai Naseer waye silar zaman Waleed haka?Mahaifiyarka da kanwarka su suka Zama silar gurbacewar tarbiyyar da na yiwa yarana Naseer Waleed da haka yake?Zahira da haka take a yanzu daka dawo daya Kamata mu had'a hannu wajen ceto yarana daga halaka Amma Kaine na farko wajen cewa yarona Dan iska? Tunda na aureka nake cikin tashin hankali ban taba samun nutsuwa ba daga wanan sai wanan yanzu Kuma an bar kaina an dawo Kan yarana Naseer na gaji wlh Tallahi na gaji idan har yarana basu dawo hayyacinsu ba bazan tab'a yafewa Mahaifiyarka da kanwarka ba"

"Ke ya isa haka akan Waleed Kike jifana da maganganun banza ke yanzu ko tuntub'e kikayi sai kice mahaifiya ta ce,kin ma bar yarda da duk abinda ya Sameki yin Allah ne komai komai mahaifiyata ce da kanwata ki Shiga hankalinki Naeema Kar San Yara ya susutaki bin abokanan banza ya jefa danki a halin da yake ciki da kinsa Ido akansa da duk baa Kai ga haka ba lokacin da nake gari Mai yasa duk hakan bai faru ba sai da bana nan "?

Zuwa yanzu shi kansa Naseer din na fara ganewa ba'a hayyacinsa yake ba yanda ya hayyayako min yasa naji na zo wuya na hau jifansa da maganganu masu zafi dan a lokacin zuciyata gayamin take kamar da biyu ma Naseer yake haka dan Yana ganin ya ruko canjina a hannu.

Musayan kalmomin da muke ne ya dagawa yarana hankali suka hau k'ok'arin janye ni daga wajensa

Amma fir naki na cigaba da jifan Naseer da magangunan da suka shake min wuya har sakina nace yayi idan yasan shi dan.halak ne dan aurensa bai kareni da komai ba sai wahala da nake sha tunda mukayi aure dashi bamu tab'a irin fadan da mukayi dashi ba ban Kuma tab'a ganin ya rufe Ido Yana cimin mutunci ba sai a wanan lokacin

Kukan da inna Amina ta saka yasa na ja bakina nayi shiru zuciyata na wani irin k'unna

Wa'azi ta hau yiwa Naseer
Ni kuwa na saka hijabina nayi waje da Nadeeya dan ta rakani gidansu yaron da Waleed ya fasawa Kai tunda tacemin ta san yaron.

Ga mamakina Ina zuwa ma nagane nasan mahaifiyar yaron.

Cikin kuka na hau bata hakurin abinda ya faru na rik'e hannun dansu da waleed ya fasawa kai da ya Sha bandeji a kansa na hau Masa sannu.

Bamu samu mahaifin yaron a gida ba da shi ya d'auki case din da zafi har aka Kai Waleed station hakane yasa muka zauna zaman jiran dawowarsa dan sai ya yafe Zan samu a sallami Waleed.

Ana kiraye Kirayen sallah Magriba ya shigo gidan da sallama babban dansa na biye dashi a baya.

Gaisuwar da muka Masa kawai ya amsa ya fara k'ok'arin Shiga falon matarsa ta dakatar dashi ta nuna mu tana wajensa muka zo ta Kara da bashi hakuri akan tunda Mai afkuwa ya riga da ya afku yayi hakuri kawai ya saki waleed.

Yanda ya hade rai yasa na fashe da kuka Ina cigaba da bashi hakuri Ina "Kayi hakuri d'a na kowane wlh Tallahi da ba haka yaron nan yake ba daga baya ya zama haka kila Kuma bazaku rasa sanin sa ba yaron nan dake yawan sharar Massallaci a kasan layi wlh shine ya dawo haka lokaci guda muna ta iya kokarinmu dan muga ya dawo hanya ayi hakuri a yafe Masa duk abinda aka kashe wajen maganin yaron Nan Zan bayar ka taimaka"

"Jikinsu sanyi yayi da suka ga yanda nake kuka a karshe mutumin yace ba komai Amma ya zama dole na dage Akan Waleed da yanzu abin yazo da tsautsayi dansa ya rasa ransa fa nasan yanda zanyi na raba Waleed dasu shagari.

Kar Waleed ya jawo min abinda ba shi kadai zaa kulle ba har damu.

Sai da yayi sallah Magriba ya huta duk.muna zaune kafin ya fito yace Mana muje.

Dubu daya na ajiye a Gefen yaron na Kara Masa Addu'a samun sauki

Na Kara yiwa mahaifiyarsa godiya na fito muka tafi station din.

Sai da nayi da gaske da kuka da magiya kafin su yarda zasu bada belin Waleed dan rashin kunya Waleed ya ringa musu.


Kudin da na basu da dan yawa yasa suka sakeshi.

A yanda na fahimci waleed idan ana Masa fada ko aka hukunta shi zuciyarsa Kara taurara yake dan da aka sakeshi wani irin hucci ya ringayi Kamar wani Zaki yabi wani dan sanda da mugun kallon daya sa dan Sandar rantsewa akan duk ranar da tsautsayi yasa aka Kara kawo shi station dinsu wlh bazasu sake shi ba

Waleed wani mugun Tsaki ya Masa ya wuce mu.

Ni kuwa nabi bayansa da Sauri Ina kwalla Masa Kira.

Da kyar ya tsaya ya zubomin Ido daya sa nake ganin kamar bani na Haife shin ba kamar ba dana Waleed dan Umma Dan lelen Abbansa yanda yayyensa kan tsokaneshi.

"Waleed so kake ka kasheni da raina ko"?

"Wai da nayi me har ni Abba zai ce a wuce dani station Kar a sakeni"?

Wani irin girgiza kai yayi ya barni a tsaya ya hau zuba Sauri

A haka muka ringa binsa a baya Ina kuka ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata.

Muna isa gida yayi fatali da butan daya samu a tsakar gidan ya wuce d'akinsu zahira dan palo yayi niyyar Shiga Naseer dake zaune a palon yasa yayi tsaki kasa kasa ya nufi d'akin.

Butar da yayi kwalo dashi na dauko na zuba ruwa nayi alwala.

Na Shiga d'akin Inna Amina dan nayi Sallah Magriba

Nadeeya Kuma ta Shiga d'akinsu.

Ina cikin rakaa na karshe na ringa jiyo hayaniya daga d'akinsu zahira take hankalina ya rabu gida biyu.

Allah Allah kawai nake na iddar na tafi dakinsu Naga Mai ke faruwa

Sujjada nayi naji ihun raheema da k'arfi.

Da Sauri na Sallame sallahr na fito a lokaci guda muka isa d'akinsu zahira da Naseeru.

Waleed ne yake ta kwallo da raheema yayyensa na k'ok'arin rik'e shi.


Zahira na gefe kamar bata San Mai ke faruwa a d'akin ba.

Naseer cikin zafin nama ya isa garesu.

Ya damko Waleed da k'arfi.
Kafin kace me ya rufeshi da duka Yana naushi

Zagin Waleed kawai yake Yana jifansa da mugayen kalamai Waleed sai k'ok'ari Kare kansa yake ba ko tsoro a fuskarsa yanda ya tsaya ma Kamar zai iya rama dukan da babansa yake Kai Masa.

Taurin Kan Waleed ma yak'i bari yaji irin dukan da Naseer ke masa shi ake duka Amma ni.nakeji a jikina.

Tsakiyarsu na Shiga cikin ihun kuka Ina Naseer ya isa haka.kashe shi kake so kayi"?

"Idan ban.kashe shi ba ai shi ya kashemin yarinya Raheema Saar sa ce da zai hau dukanta"?


(Karku manta an Shiga tsakanin Naseer da Waleed shi kansa Naseer baa hayyacinsa yake ba)

"Idan ba yaron nan ya zama dan iska ba""""

"Ka daina cewa dana dan.iska Naseeru kana mahaifinsa kana ce masa dan iska dana ba Dan iska bane"

Nace a tsawace a daidai lokacin da Waleed ya fice daga d'akin a zuciye.

Kafin na ankara har ya fice waje.

A d'akinsu zahira ma ba karamin fada mukayi da Naseer ba kamar zai kawo min duka

Dak'yar su Nadeeya suka janyeni daga d'akin

Sai a lokacin na tambayi su Nadeeya mai ya hada Waleed da Raheema suka ce min Waleed ne yayi fatali da.kayan Raheema da take gogewa akan tayi magana shine ya zageta ta rama daga haka ya hau kwallo da ita.

Dakin Inna Amina na koma Ina kuka itama kukan take tana adduar Allah ya kawo Mana karshen wanan fitintinun Allah ya gaggauta kawo karshen abinda aka yiwa waleed da Zahira.

Naseeha ta hau min akan ta karanci kamar Naseer shima baa hayyacinsa yake ba shima kamar an Shiga tsakanin shi da Waleed.

Na tuna fa ba haka.naseer yake ba a dan zaman da tayi damu ta karanci Naseer na mugun Kaunar Waleed tashi daya daga dawowarsa ya canja na daina biyewa Naseer muna fada akan Waleed

Mu dage da Addu'a banji maganar ta ya shigeni ba dan.gani nake da gangan Naseeru yake haka tunda har Yana neman Kare mahaifiyarsa da kanwarsa daga cutar da suka min.

Sosai nake ji a Raina lokaci yayi da zan ba zama nemawa yarana magani Allah na tuba Inna Amina na iya k'ok'arinta wajen Mana adduoi haka nima inayi Amma inaga sai na had'a da Kara neman taimakon.

Zurfin da Inna Amina taga nayi a tunani yasa ta tambayeni tunanin mai nake.

Ban boye Mata komai ba na gaya.mata abinda ke Raina.

Murmushi tayi tana "Mallamai kawai da Kika bi wajen nemawa Zahira magani da baki samu kin dace da Wanda yayi nassarar cire mata bakkaken aljannu da aka Mata turensu kawai ya Isa yasa ki dau darasi.ki cire tunanin zuwa neman taimako wajen wani mallami.

Ke ma zaki iya zama mallamar kanki ki roki Allah dan wayanda zaki je wajensu suma wajen Allah zasu nema Allahu samiu dua ne zai amsa Miki duk halin da kike ciki Yana sane dake daga lokacin da Kika fara zuwa wajen mallami neman taimako sai Allah ya barki da mallamin shi ya Miki maganin Abunda kike ganin bazai iya ba ko iya fatiha Kika sani ki karanta ki roki Allah dashi ta hanyar bin ladduban Addu'a Ki Kira Allah da sunayensa tsarkaka kyawawa kiyi wa annabinsa sallati ki Kara masa sallati a sujadarki ki yabe shi kiringa addua tamkar kina gabansa idan kin gama ki rufe da sallatin annabi saw insha Allahu zai amsa Miki.

Na Karu sosai dan.a guntun ilimi na ma bansan ladduban Addu'a ba.

A ranar Waleed bai kwana a gida ba Abunda bai tab'a yi ba kwana a waje.

A ranar banyi bacci ba haka na ringa zarya tsakanin gida da waje ko Zan ga dana ya dawo.

Sai dai bai dawo ba sai washegari Sha daya na safe Zahira kuwa ta saci fita duk da kulle ta da Naseer yayi.

Akan Waleed wani irin Mugun fad'a mukeyi da Naseer dan idonsa idon Waleed sai ya dakeshi ko.ya koreshi daga gidan Wanda hakan yasa muke mugun fada har zuciya ta debbeni nace Masa ya barmin gidana ai ba nasa bane.

A ranar yayi zuciya ya barmin gidan kamar yanda na nema.

Inna Amina tayi ta min fadan ban kyauta Abunda nayi wa Naseer ba Bayan duk naseeha data min akan na yiwa Naseer uzuri baa hayyacinsa yake ba

Har da kukanta na hau bata hakuri dan bazata gane ba Naseer ya ficemin a rai burina ma kawai ya sakeni.

Insha Allahu ma.bazai dawo ya sake samun mu a gidanan ba dan mak'otan arziki sun shawaraceni da na bar unguwar hakan kawai zai saka Waleed ya nisanci su shagari


Tuni na saka gidana a kasuwa sai dai duk Wanda yazo baya Taya gidan da daraja ballantana har kudin ya Kai na Kara siyan wani gidan.

Sabida na nisanci Waleed da abokaina na siyar da gidana haka na Kama haya a wani unguwar.

Sauran kudina na hau sana'a gefe guda kuma addua da sadaka daga ni har Inna Amina yi muke.

Komawar mu wani unguwa yasa Waleed ya Kara haduwa da wayanda suka fi shagari hatsabibanci rashin jinsa ya Karu.

Gefe guda Kuma ga maneman Nadeeya da Minal

Ga babbar yayarsu itama da rashin jinta ya karu ta Kara haduwa da kawaye marasa Jin magana.

Abu kad'an zaa Mata ta bar gidan sai nayi dgske zata dawo ta kwana


Banida bambanci da zararriya dan Ina tafe Ina surutu sadakan nan Ina yi addua Nan ina yi Amma duk da haka Banga alamar yarana zasu dawo hayyacinsu.

Ban gayawa Inna Amina ba na fara shirin tafiya Calabar neman su Umma suyi yanda zasuyi Dani su karya asirin da sukayi yiwa yarana......


Wlh banida lafiya Amma haka na daure nayi
8/19/21, 10:33 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

Page 60

Tashin hankali da damuwa yamin yawa bana iya bacci sabida halin da yarana Suka tsinci kansu a ciki burina kawai yarana suyi hutun makaranta na tafi calabar

Zan zub'e a gabansu ko kasheni ne suyi su karya abinda suka yiwa yarana Zan jadada musu na rabu da Naseer har takarda Zan nemi wani ya rubuta min su dai ga shaida ko hakan zai kwantar musu da hankali

Ko ya na rufe Ido sai na ringa ganin Kamar zaa shigo da Waleed hannunsa d'auke da ankwa ya aikata wani Abun.

Zahira kila ta janyo min magana da zai saka Mana tambarin da ba ita kadai ba har mu sai ta shafa Mana bakin fenti gashi duka yarana Mata ne yanzu ma iya kawaye kawai da take bi ana jifanta da kalmar Yar iska har da masu karyar ta zubar da ciki.

Idan Abun jaje ko na alkhairi ya Kama daya Zama dole na Shiga mak'ota haka zanji Ana zaurence ana labari da ni nasan dani suke yara dai a iya sanina duk Inda ka kai ga ka basu tarbiyya sai Allah ya dafa maka a tarbiyyarsu Amma wasu basu gane haka ba masu yin haka ma sai iyaye uwa data Kira kanta da uwa ita zata zauna ta ringa gulmar Yar wacce Yar iska ce bana Jin akwai Uwar da ko karuwa ce zata so yarta ta zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login