Showing 162001 words to 165000 words out of 180103 words

Chapter 55 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2504

Yar iska sai dai idan haka Allah ya kaddarta Mata babu yanda zatayi ni nasan nawa yaran na musu tarbiyya da taimakon Allah makiya kawai ke san ganin bayana.

Har ta kai yanzu Zahira idan tsautsayi ya gifta ta samu matsala da kannenta zuciya take ta bar gidan ba Kuma zata kwana ba bansan a Ina take kwanan ba sai dai washegari ta dawo haka ma Waleed.

Ko kullesu nayi sai sun San hanyar da suka fita daga gidan dan tamkar zaman gidan mitsininsu yake Yana musu zafi.


Inna Amina musamman ta tsiri azumi sabida wanan matsalar da na tsinci kaina a ciki.

Ba karamin damuwa take da rashin Naseer ba

Duk gaisawar da zamuyi sai tace ban kyauta korarsa da nayi ba.

Ni kuwa ban tab'a nadamar Abunda na aikata ba San yarana ya rufemin idon da nake ganin duk abinda ya faru shine sila ni da ban aure shi ba ma da kila ban tsinci kaina a ciki halin dana ke ciki ba yanzu.

Damuwa baya bari ma na tsaya zurfin tunani har na gane halin Naseer ne ko ba halin Naseer ba burina dai kawai Allah ya kawo wa yarana sauki.


Saura sati daya Nadeeya ta yi candy duk makaranta ayi hutu na Kara zage damtse wajen Tara kudin da zanyi tafiya dashi dan ba abinda zai dawo dani har sai sun warware abinda suka yiwa yarana.

Nadeeya kawai da Minal na gayawa inaso na yi tafiya Inda na rokesu Kar su sake su bari Inna Amina ta sani dan bazan iya bijire mata ba idan ta hanani.

Yanda take hanani neman taimako a wajen Mallamai ya sa wani zubin shaidan Kan rayya min kila dan bata San zafin haihuwa bane shiyasa take hanani sai idan naga alherinta Kuma a gareni sai nayi istigifari


Tana iya k'ok'arinta wajen nuna min na rungume kaddarar da Allah yamin dan Allah Kan jarrabci bawansa dan.ya gwada imaninsa.

Bansan Mai yasa akan yarana imanina yake neman yin rauni ba

Ana saura kwana biyar na tafi

Na hau mafarkin Ina hauka tuburan a mafarki kafafuna ba takalmi Ina tsince tsince a bola kaina na zura Leda

Yarana nesa Dani Kuma suna ta kallona suna kuka.

Naseer shima Yana daga gefe yana kuka Yana San zuwa wajena ana ririke shi.


Waleed da Zahira su Kuma haka zan gansu a daddaure an jinginasu da bishiya suma suna kukan

Ina ganin haka zan nufi wajensu a guje kafin na Isa wajensu zanga Mahaifiyata na shara tana "karkiyi tafiyan Nan indai Kika taka kafarki Kikaje garin nan sai kin haukace abinda suke so kenan karki je Naeema ki cigaba da ga yawa Allah Yana sane dake Naeema

Daga haka Zan farka.

A jajjere nayi mafarkin har sau uku kuma mafarkin iri daya.

Sosai jikina yayi sanyi da irin mafarkin da nake yi dan ni nasan bana mafarki da mahaifiyata ya zama ba gaske ba

Iya kan had'uwa ta da Inna Amina ya kara tabbatar min da haka.

Amma kwadayin San yarana su warke yasa wani barin zuciyata cemin nayi ta sadaka insha Allahu mafarkine kawai.

Ba nida kudi kamar da akan abinda ya samu yarana da San su samu lafiya na siyar da gidana ban taba zaman haya ba Amma gani Ina zaune a haya

Sana'ar ma da nakeyi Yan bashi sunfi yawa.
Da taimakon Allah da arzikin Yaya Mata da Allah yamin asirina ke rufe dan Nadeeya da Minal ba laifi ma nemansu suna iya k'ok'arinsu wajen kyautata musu Wanda a hasashena da biyu sukeyi tunda sunga halin da muke ciki.


Duk da mafarkin Ina rufe Ido zanyi hakan bai saka na girgiza da san fasa tafiyar ba.

Addu'a kawai nake da sadaka

Ana saura kwana biyu na tafi da yamma Ina zaune a tsakar gida.

Waleed ya shigo gidan ba Sallama bai Kuma gaisheni ba ya shige daki ya Tara uban gashi kamar mace yaron da bai wuce shekara Sha hud'u zuwa biyar ba Nan da Nan ya Ajiye saje da gemu.

A duk abinan abinda ke kwantar min da hankali bai wuce shaye shaye da ba yayi ba

Da Ido na bishi har ya shige daki.

A hankali na cigaba da sauke numfashin da naji Yana min wahala kirjina yamin nauyi

Daga ni sai Inna Amina ke gidan

Dan duk sun tafi islamiyya.

Mik'ewa nayi na Shiga d'akin da ya Shiga.


A Gefen gado nagan shi a zaune yana gyara wani Abu irin da ake Jin kida dashi da matasa ke yayi (Bluetooth)

Shigowana bai saka ya d'ago ya kalleni ba illa Yan kananan wukakensa daya ajiye a gefensa daya d'auke a mayarsu cikin gidansu ya saka a Aljihun wandonsa

Girgiza Kai na nayi na zauna a gefensa kirjina kamar ya Fado danaga yanda ya Tara farce cikin sanyin murya nace "Waleeed"

Sai dana Kira shi ya Kai sau uku kafin ya d'ago

Hada idon da nayi dashi yasa hawaye hau zubomin.

Waleed ya rame sosai yayi duhu duk da ba fari bane.

Cikin idonsa kawai in ka kalla zaka san Sam dabiun daya ke yi aransa yayi ba halinsa bane.


Yana Nan a yaro Mai hankali Mai tarbiyya canza shi kawai akayi.

Shima rashin Jin Rama yake saka shi.

"Allah ya shiryeka Waleed Allah ya dubeni da idon rahama yasa Kai da Zahira ku dawo yanda kuke a da Waleed nasan duk abinan da kakeyi ba yin kanka bane Waleed ka rage rashin ji kaji ka tausaya min Kar na mutu lokacina baiyi ba.

Dan Allah bani wuk'akk'en nan da ka sa a Aljihunka"?

Tunda na fara magana cikin hawaye naga Waleed jikinsa yayi sanyi Kamar ba shi ba

Cikin bin umarnina daya saka naji kamar na taka rawa ya mikomin wuk'ar

Ni kuwa na cigaba da Masa naseeha

Rabon da na zauna waje daya dashi haka har na manta.

Damar Dana samu yasa nace bari na dauko abin aski na aske Masa uban gashin daya tara da nake ganin kamar zai iya saka shi ciwon Kai.

Ganin bai wani motsa ba yasa cikin farinciki jin Kamar Dana ya fara warkewa nayi d'akina da Sauri dan na dauko.abin askin Dana siya musamman dan shi
dan ni ke masa aski.

Sai dai Ina dawowa naga baya Nan sai wani farin takarda da ya Ajiye

D'aukar takarda nayi Naga yasa "Ina yawan munanan mafarki akanki Umma ki dage da Addu'a"


A ranar nayi kukan da ban taba irinsa ba wato Dana duk da an juyar masa.da.kai yasan yamin magana Mai dadi

Kamar Wanda ya karamin karfin gwiwa nayi tafiya dan na samo musu lafiya.

Na kudunduna takarda na fito daga d'akin

A daidai lokacin da Inna Amina ta hau kwalla min Kira.

Da Sauri na Shiga d'akin Bayan na share hawayena

Ga mamakina ita ma sai cemin tayi "kwana biyu Ina munanan mafarki akanki mamana Ina yawan ganinki a mumunan hali dan Allah ki dage da Addu'a"


Kamar ta sassareni da guduma haka naji ya akayi Inna Amina da Waleed sukayi mafarki iri daya


Tuni na fara Jin tafiyar na ficemin a rai Amma kasan zuciyata kamar ingizani ake akan tafiyar da zanyi shine zai saka yarana su warke.

Ina fitowa itama Zahira ta fado gidan Kamar wacce aka jefo tana sanye da matsassun Kaya Muna hada Ido ta sauke ajiyar zuciya ta kad'a kanta tayi daki.

Itama bin bayanta nayi kamar yanda nabi bayan Waleed itama na hau Mata naseeha kamar yanda nayiwa Waleed ta nutsu kamar gaske duk da bata cemin komai ba

Itama kusanci Dana samu da ita da karantar ta da nayi ya kwantar min da hankali ba kadan ba.

Dan duk abinan tsorona ta wulakanta kanta a rabata da martabarta.

Dawowar su Nadeeya gidan yasa suka haura da Minal ta zuciya ta bar gidan.


Abinda ke ingizani nayi tafiyar tuni ya motsamin naji na matsu jibi tayi na tafi.

A ranar bacci yayi ta daukata Ina mafarkin Ina hauka tub'uran

Wajejan asuba nayi mafarki da mahaifiyata ranta a b'ace tana tamin gargadi Kar k'afata ta bar garin Kano Ina barin garin Kano an samu abinda akeso.

Ba iya Mahaifiyata ba har da mahaifina da ba kasafai nake mafarki dashi ba.


Kamar a gaske nayi mafarkin

Tashina da Nadeeya keyi akan na makara sallah asuba yasa na mike a firgice Ina gumi.

Kirjina na balain bugawa mafarkin da nake bai tab'a dagamin hankali Kamar wanan ba.

Karo na farko da naji bana san yi tafiyar Amma abinda ke tunzurani nayi tafiyar na Kara ingizani.

Nayi Sallah ne kawai amma ba'a nutse ba dan mafarkin da nayi ya tsayamin a rai sosai kwakwalwata ta kasa bani hadin Kai nayi tunani.

A haka yarana suka bar gidan
Jiki ba kwari na shiga d'akin Inna Amina.

Ido ta zuba min har na ajiye flask din kunun dasu Nadeeya suka Dama mata

Na gaisheta a madadin ta amsa min sai cewa tayi "Da kin d'aukeni tamkar Mahaifiyarki Kamar yanda kike fada da baki ringa min boye boye ba Naeema ni nasan akwai abinda kike boyemin da nake ji a jikina ba alheri bane a gareki Naeema sanin da na Miki ba haka kike ba kin kasance yarinya Mai balain hakuri da tunani duk abinda ya Sameki kina Imani cewar Allah ne ya rubuta a takardarki akan zai sameki ba mutum ba sai dai mutum ya zama sila tunda ga farkon haihuwarki har zuwa lokacin da zaki koma ga Allah Allah ya riga da ya tsara Miki rayuwarki babu dan Adam daya Isa ya canja shi


Idan Kika duba baya da Abubuwan da Suka faru dake da Imani da kikayi da Allah kin samu maganin matsalolinki batare da kin wahala ba

Amma akan abinda ya samu yaranki imaninki yayi rauni har kina tunanin sai kin je wajen wayanda muke hasashen sune silar shigar yaranki wanan halin kina nufin Allah baifi karfinsu ba sai har kinje kin rokesu su warware abinda sukayi.

Abaya su ne suke Miki maganin matsalarki?su Kika je Kika samu akan larurar Zahira?

Mai yasa bazaki dogara ga Allah ya isar Miki kamar yanda ya isar Miki a baya ba Naeema"?

Tamkar yata na d'aukeki idan Abu ya Samu bawa Allah yake gayawa ya magance Masa matsalarsa domin Allah Mai jine Mai Kuma gani duk halin da bawansa zai Shiga yana sane sai dai mu muyi gajeran hakuri kamar yanda kike yi yanzu

Karki ga muna ta ga yawa Allah har yanzu shiru wlh Yana sane zai amsa Mana a lokacin da bamu zata ba wuyanta muyi hakuri dan haka kiyi hakuri ki koma ga Allah ki cigaba da gaya Masa Yana sane dake zai amsa Miki insha Allahu.

Domin matsalarsu nayi azumin kwana bakwai da niyyar Allah ya warware duk abinda aka yiwa yaran nan ga ruwan zamzam nan kiyi kokari su biyun su Sha ki Kuma shafe musu jikinsu dashi zamu dace watarana insha Allahu"


Kuka na fashe dashi sosai dan tabbas duk abinda ta fada gaskiya ne imanina yayi rauni akan San yarana su warke.

Ni kaina nasan yanda nake dukufa da Addu'a a baya ba haka nakeyi ba yanzu.

Ina sallah Ina tunani karshe idan naga zuciyata baa nutse take ba sai na hakura da sallah.

Godiya na ringa mata a raina Ina Jin na hakura da tafiyar ba Inda zani Zan cigaba da gayawa Allah sai a lokacin tunanin Naseer ya fad'omin arai.

Har nayi tunanin ko ina yake yanzu na Kuma ringa Jin kamar ban kyauta korarsa da nayi daga gidana da bai kareni da komai bama sai asara dana tafka ta hanyar siyar da gidana

"(Duk.mafarkin hauka dinan da komai ba fiction haka tayi mafarki Allah ya tsallakar da ita)


Calabar
Safiyya
Tunda ta samu cikar burinta akan Zahira da Waleed take cikin tsananin farin ciki zuciyarta v
bata tab'a k'issa mata alheri ba sai sharri

A duk lokacin data bude ido taga hauwa yarta da ta siffantu da d'abba takan ji tsanar Naeema da duk ahalinta.

A idonta gani take ko ta samu nassarar kashe Naeema da yaranta har da Naseer da ya Zama babban makiyinta zuciyata bazata taba sanyi ba tunda duk a silarsu take Kan Shan wuya da hauwa da take Mata fatan mutuwa sabida wahala da take Sha akanta

Dakyar ta samu tayi abubuwan da tayi Bashir ya fito daga prison Wanda ta gwammaci har zamansa a can da sakinsa da akayi.


Mugun barawo ne dan d'abba mashayi.

Da cikin da ta Kara samu da baban Hauwa Bashir ke nada Mata mugun duka idan yayi shaye shayensa

Sata kuwa baa Kama hannun yaro

Halayen Bashir yasa mahafin hauwa sakinta saki uku bayan ya kwashe duka kayansa ya bar gidan

Dan kananan sanaoi da take shi ke sawa ta samu na abinci har yaranta su samu Suma da sun kawo girman da take fatan su fara samun Samarin da zasu na kashe musu kudi.

Kamar yanda taci buri akansu take fatan Yan biyun nata suyi farin jini irin na Zahira sai dai shiru.

Da tsohon cikinta Bashir ya Sha jawo mata a kulle ta dan amfana da Oban keyi da ita yasa yake siddabarun da ake sakinta.

A cikin wahala ta haihu da ita kanta batasan cikin na baban Hauwa bane ko Oban da baya iya Bata ko sisi amma duk wani Abu na mugunta Idan Tana so zai Mata akan bashi.

Rabi ta sawa yarta data haifa Dan kudaden data samo dan ta dan siyi abinci da zasu ci ita dasu Yan biyu

Haka Bashir yazo da wuka yace ta bashi.
Tana gardama ya rufeta da duka Kamar ba uwarsa ba ya dau wukarsa Mai kaifi ya tsage Mata fuska dashi..

Sai da ta Sha Jinya ta dawo daidai baki.kam ba irin Wanda ba tayiwa bashir da tayi mugun nadamar aikin da tayi har aka sake shi ba

Tana tsoron Bashir ya Zama ajalinta watarana

Ta Kan je wajen Oban ya duba Mata halin dasu Zahira ke ciki halin da suke ciki kawai ke faranta Mata rai yanda Naeema take neman haukacewa Akan yaranta.

Yanda Naseer ya tsani bud'e ido ya ga Waleed Yana balain saka zuciyarta sanyi uwa uba fadan da Naseer da Naeema ke yawan Yi komai yana Mata yanda takeso.

Ko damuwa ba tayi da matsalar da take ciki ba tunda ta samu cikar burinta a haka a garin duba halin da su Naeema ke ciki Oban ya gano Mata Naeema na shirye shiryen zuwa calaba nemansu dan ta rokesu su karya abinda aka musu.

Cikin tsananin mugunta Safiyya tace.masa tana san ya Mata aikin da Naeema tana shakar iskar garin calabar a ranar ta haukace hauka da zata na cire kayanta tana bin mutane da gudu.

Oban take ya bata layoyyi masu yawa yace taje tashar da motar Kano ke sauka ta binne layyar a wajen.

A duk ranar da Naeema ta taka kafarta garin calabar a ranar zata haukace Amma idan aka samu akasi Naeema bata zo ba abin zai koma Kan wani nata.


Take ta amince Oban ya dirjeta ya bata layoyyi da kwallin farin jinin da zata kai wa Yan biyunta Suyi farinjini da zasu yi Samari.

A daren taje Tasha ta binne layyar tana murna Naeema na dab da haukacewa wuyanta ta tako garin.

Washegari ta nema kayan gumama ta baza yaranta neman saurayi bayan sunji uban kwalli.

A ranar kamar ta kwana rawa da ta ga Safiyya da asmau sunyi Samarin

Har an hidimanta musu ta samu abun duniya da bashir yazo ya musu fin k'arfi ya kwace.

Gefe daya.tana murna kasuwar da yaranta sukayi gefe daya Kuma tana hanya zuwa wajen Oban dan taga halin da Naeema ke ciki ta taho ko bata taho ba.

A yau ma a k'ofar gida ta bar Asmau da itace hassana sosai take ji da ita sabida tafi Safiyya farin jinin samarin yanzu ma wani dan acaba ne yazo wajenta zance

A ranta ba haka takeso ba manyan masu kudi takeso su ringa zuwa Amma tafi tafi dai tasan zasu Zo.

Wajen Oban taje ya duba Mata su Naeema inda yake gaya mata ai gobe Naeema na tafe.

Dan Yana ta ingiza ta akan tazo

A ranar sabida farin ciki a wajen Oban ta kwana da yarta rabi ya dirjeta San Ransa

Washegari wajen Tara tayi gida zuciyarta fes a idonta hango Naeema kawai take ta haukace.

Har Tasha zata je ta zauna taga yanda Naeema zata haukace

Sai dai tunda ga nesa ta hango k'ofar gidanta dankar da jamaa kafin ta gane Mai ke faruwa


Asmau da aka riririke tsirara ta kwace daga hannun mutane ta Kara fita a guje.............

Kila gobe ajini

Ngd en uwa da soyyaya da Kauna Allah ya biya muku bukatunku na alheri masu San cigabana ngd.


Yar uwa na barar adduarku 👇



Hi sadnaf ykk ya karfin jikin
Allah yasa kaffara ne
Wlh Ina cikin rudani nikam yayata ce uwa daya uba daya takeda yaro marar jin magana

Allah yamasa baiwar karatu takowane bangare dan shekararsa 10- yayi saukar kur'ani saidai a kyale Shima saboda rashin son zuwa makarantarshi gashi Yana Yan dauke dauke Amma a gidansu takai har ya dauki Abu a gidansu yaje ya siyar yau ma abunda yasa take bani lbr tace babansa ya siye bakin Mai na mota dubu 7 da wani Abu shine ya saceshi yaje ya siyar 5k 😭😭 wlh Allah Dan yayatane na farko shidaya ke gâresu lta da mijin Saïda yayi 10 yrs sannan Allah yabata wani yanzu yanacikin 2 yrs
Dazun Nan take gayamini sunkaisa wurin wani malami akace ture akai Masa na bakaken Aljannu masu hanashi karatu Kuma suna sakashi Satan ,Kuma acikin satin da sukaje wurin malam Kuma malamin islamiyarsu ya Kira babban shi yake gayamasa an fara Masa Aiki Kuma tace rubutune ake wankemasa takebashi yanasha wlh tallahi tacemini sai Ranar karshe ta kuskure
Shi malamin ma na farko dasukaje yabasu magani yace idan ya Kare sudawo cemin tayi a Ranar dasukaje wurinsa data dawo batayi kwana ba a ka dinga Bata tsoro tacemin in ma bayanzu datakemini firar ba tsakaninta da babbanshi basu taba dauko firar malamin ba
Amir yanada tsananin ilimi n'a nan mamaki wlh KO islamiya sau 1 akemasa Kari ya hardace DUK da rashin zuwanshi kullum sbd ana kaishi zai tsere wani time in Amma a haka ya sauke malaminsu cewa yayi dayana tsayawa yayi karatun da tun ba'a Kai haka ba zayyi sauka zai kebeshi ba cikin ajiba Yana Masa Kari Amma Ina bayaji
Iyayensu dukansa suke kamar jaki saboda karatu saboda sata Amma baya Bari Ranar akan Keke yaje maradi daga anbashi Dani 37 kilometers daga Nan zuwa maradi Amma yaje
Tacemin yanzu sunbar dukansa ma Tunga aka gayamusu haka akace Kuma mace ce tamasa turen mamansa dai tacemini ita batada wani makiyi Kuma irin ma tace wane ko wance take zargi itadai Babu batadai San ko babanshi ba Kuma mezai hada babbanshi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login