Showing 165001 words to 168000 words out of 180103 words

Chapter 56 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2489

mata har a turoma dansa wani abun
Tacemini bazata manta ba lokacin suna tsohon dakinsu Amir Kuma Yana falo Yana bacci itakuma Tana tsakar gida acikin baccin yatashi ya rike kansa Yana ihu yanata kuka tun Yana primary 2 tace tayi tunanin ko cinnaka yacijesa a kunne amma yace aaa bayan gayama kukan ta tanbaya meyasa meshi yace wani suka harbamasa ball a Kai
Tacemini wlh koma minene a lokacin yasamesa
Kinsan Allah saboda hakinshi na daukar abun mutane yafita Raina ko inada Abu ban iya basa Yana batamini Rai kullum cikin warar sa nake Dan babbu jimawa an taba daukemini kudi bayan jaka 4500 Kuma Yana wurin Koda Naga bangansu ba nace shine Daman ma aikesu nabi bayansu su 3 shida autan Mu da dan yayata guda dana hangosu niyata idan n'a ISO na daukeshi da Mari Amma sai na fasa nacemusu Kai an daukemini kudi kutsa in lalubeku ke in karemiki karshen zance shidaya na lalube nace bakowa bane Kaine sai cemini yayi ya hade hannayensa haka🤌🏽ya daura a kirji yace yanzu tanti mina Ni kadai kike zargi na daukarmini kudi bakomi sai yabani tsananin tausayi jikina yayi sanyi
Nasan fa Yana dauka Amma wadannnan bashi ya daukaba amma wlh har yau Abun Yana Raina dayacemini yau da mamansa ke gayamini saina Goda Allah da alokacin ban marésa Yanzu aji daya yake a secondary Amma exam na karshe bayyishiba Ashe koyafita gidan bazuwa yakeba
Sai bayan angama iyayye suka sani
Kinga sai Kora ko indai ba gyara akamasa ba
Ya fa Yi sauka Amma har gobe saï akaishi islamiya muddin ba'a kaishi ba bayazuwa
Saidai dayafita gidan ya tsere
Wlh data ke gayamini lbrn zahira ya fadomini a rai
Muma muna barar addu'a idan Kuma dawasu addu'o'i ataimakamana Allah ya taimakemu😭😭 Wlh hankalina yabtashi
8/22/21, 9:25 AM - Alhmdllh: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Ngd masoyana da suka nuna min kauna Kaunar da kuka nuna min yafi faranta min fiye da komai ngd*


*Page 61*

Hankali a balain tashe Safiyya ta bi Asmau a guje tana zunduma ihun a taimaka mata a ruk'o ta Amma duk yanda aka so riketa kasawa akayi

dan ko an riketa sai ta kwace ta Kara fita a gujen

Safiyya zub'ewa tayi a kasa ta hau birgima tana ta Shiga uku ganin Asmau a cikin wanan halin ya kusa sawa zuciyarta ta buga.

Wajen Oban ta koma da isarta ta zub'e a kasa kafin ta Masa bayani yace mata "Naeema ce ta fasa zuwa shiyasa haka ta faru ga yarki duk iya k'ok'arina dan na ga na ingiza ta tazo taurin kanta yasa ta fasa zuwa matar Nan tana da wahalar shaani bansan ya akeyi take tsallake duk abinda mu ka mata ba yanzu abinda za'ayi kiyi Sauri kije tasha Inda Kika binne layyan nan ki hak'o ki kawo min nayi aikin da Asmau zata dawo daidai.

Da balain sauri ta mik'e ta nufi Tasha dan ta d'auko layyar da ta binne sai dai tana Isa ta kasa gane Inda ta binne layyar.
Kamar zautaciya ha ka ta ringa bin waje waje tana tonowa mutane sai kallonta suke.

Mutanen da yawa sun d'auka itama hauka cewa tayi hakane yasa aka fitar da ita daga tashar ta karfi haka ta Kara komawa wajen Oban tana kuka akan bata gane wajen da ta binne layyar ba ya taimaka Mata yayi aikin da yarta zata dawo daidai.

Oban haka ya hau tsubbuce tsubbuce ganin ba abinda zai iya yi akai yasa ya d'ago ya hau cewa ta nemo Abubuwan daya San ba yanda zaayi ta samo su Koda kudinta.

Safiyya haukacewa ne.kawai bata yi ba.

Haka ta koma gida tana rusar kuka.

Tsanar Naeema da San ma rabata da ranta na darsuwa a ranta har yau Bata ga ribar data ci akan Naeema ba duk abinda take Mata kanta yake dawowa tunaninta bai tab'a bata Allah ne ya tsayawa Naeema Sharrinta ke komawa kanta ba hasali gani take duk abinda ya sameta laifin Naeema ne
Bashir babban danta babban barawone, Asmau yanzu ta haukace Hauwa ga ta Nan kamar ba mutum ba Safiyya da Rabia jaririyar ta kawai ne wani Abu bai same su ba duk wanan tashin hankalin ta dalilin Naeema ne dan haka ta Sha alwashin sai dai idan mutuwa tayi sai ta samu cikar burinta akan Naeema zata samu kwanciyar hankali

Dak'yar ta samu wasu matasa Suka kamo Mata Asmau da sai da tayi sati uku a waje tana bin bola tana bin mutane a guje tsirara ba kaya a jikinta

Abinka da budurwa a haukace haka aka rabata da budurcinta kafin Safiyya ta gano Inda take ta saka a kamo Mata ita ta saka ta a d'akin da ta kulle hauwa ta datse da mukulli.

A gaban idon Safiyya takwararta Safiyya ta fara bin mazan.

Yar iskar da take San Zahira ta zama sai gashi Safiyya ce ta Zama a gaban idonta zaa Zo a d'auketa a dawo da ita washegari ko sisinta ba Kuma zata bata ba daga ita har Bashir Basu d'auketa a matsayin uwa ba ubanta kawai suke ci.

Abu goma da ashirin haka suka hade mata duk lokacin data duba yaranta ta ga halin da suke ciki zuciyarta kamar ta buga sabida bakin ciki ga mugu mugun tsanar da ta yiwa Naeema da iyalanta gabadaya rashin nutsuwa yasa ta kasa komawa wajen Oban da ayi Mata mugun aikin da zai Saka Naeema ta mutu Tama bar Mata duniyar duk da tana ganin ko Naeema ta mutun hakan bazai sa taji sanyi a zuciyarta ba sabida tsabar tsanar da ta mata.

Tana sane da Hajara bata taba tunanin waiwaiyar ta ba Dan gani take itama tana cikin wayanda Suka jawo mata Kara lalacewar Bashir.


Haka Safiyya ta kasance cikin tashin Haukacewar Asmau da ta lura har ciki ne da ita.

Wajen Oban ta koma ta cigaba da rokonsa ya Mata aiki Asmau ta dawo daidai shi kuwa Oban ya ringa kwasar rabonsa a jikinta Yana saka ta Nemo kudi ta kawo masa akan Kar ta damu Yana aiki akan Asmau zata samu lafiya.

Haka tayi ta saka Rai da samun lafiya Asmau da ke haukanta tuburan da ciki har ta haifi yarta mace a cikin halin hauka.

Safiyya tana ji tana gani tayi jika shegiya da Bata San ubanta ba haka ta hau rainon jaririyar cikin bakin cikin duk halin da ta tsinci Kan ta a ciki da take ganin duk Naeema ce ta jaza Mata.

Wanan kenan

Hajara

Rayuwa ba karamin wahala ya Mata ba dan ciwon kafar da take yasa dan kosai da take soyawa ta daina iya fita soyawa dan canji Kan da take dashi haka duk ya kare a hannunta haka ma kudin hayan gidan da ta Kama

Tana ji tana gani aka koreta daga gidan.

A ranar da aka koreta da Jan kafa ta nufi gidan Safiyya dan bata da Inda zata je daya wuce wajen

Sai dai da isarta Safiyya ta rufe idonta ta koreta akan bazata zauna Mata a gida ba itama ta kanta take abinci itama sai tayi da gaske take sa mu taci taje wajen Naseeru da ta zabeshi da sabida Kar ta Masa komai ta gwammace ta fasa mudubi danta Bashir ya Kara zama katon barawo.


Hajara kuwa bakin cikin abinda Safiyya ta Mata yasa ta ringa tsinewa Safiyya tana jawo Mata iftilai rayuwa


Zagi in zaga Haka sukayi kamar ba uwa da 'ya ba

Hajara na kuka ta baro gidan Safiyya ta hau laluman Inda zata zauna dan Bata Isa ta soma tafiya Kano wajen Naseer ko Tijjani ba Safiyya ta Riga da ta cutar da ita intaje Kano ma kila Yan sanda su Kamata

Yau da ba dan Naeema ba da rayuwata duk bata juya haka har wajen Zama ya gagareta ba.


Haka ta ga ma kewaye unguwar Bata samu waje ba kamar tsinuwa duk Inda taje sai an koreta

Sai a wani rumfa da Rabinsu mahaukata ne anan ta samu wajen kwana

Anan Kuma ta mayar dashi gidanta


K'arfin hali irin nata yasa ta hau bara tana neman kudin da zata ga bayan Safiyya da Naeema.

Dan tsana take Mata da take Jin wani Abu ya tokare Mata kirji har sai ta samu cikar burinta zata samu sausauci a zuciyarta

Wanan kenan.


Naeema

Tunda Inna Amina ta min fada na watsar da komai na maida lamurana wajen Allah nayi k'ok'arin rungumar duk jarrabtar da Allah ya min da hannu biyu addua Shiriya kawai nake yiwa Waleed da Zahira.

Inna Amina na Tayani

Dauriya kawai nake da muka tafi shekara biyu Naseer bai neme mu ba Ina tsoron ko wani abune ya same shi sai dana dawo hankalina na fara tunanin duk halayyen da ya ringa nuna min ba halinsa bane kila shima tab'a shin akayi.

Addu'a nake akan Allah ya kareshi ya sa ya dawo hankalinsa ya dawo ko dan Nadeeya da yanzu ta fara jamia maneman Aurenta na ta zuwa ko ta Ina neman aurenta.

Burina yanzu ko Humaira ce ta samu miji aurar da ita zanyi.

Zahira da waleed Kam addua kawai Zan cigaba da tayasu dashi akan Allah ya shirya min su duk da bana San yaudarar kaina sai nake ganin kamar sun fara dan canjawa tunda Waleed na dan zama a gida yanzu inya ga dama har ya kwana.

Zahira ma ta fi bani mamaki dan tana zama yanzu a gida sai idan an b'ata Mata Rai take fita.

A yau da yamma muna zaune gabad'ayan mu atsakar gida har da Inna Amina dasu Nadeeya suka tilasta mata fitowa tsakar gida.

Suna ta tsokanar ta itama tana tsokanarsu.

A rayuwata ba abinda ke Sakani farinciki sama Dana ga yarana gabadaya a waje daya suna hira ko ban sa musu baki ba Ina Jin dadi a Raina.

A hankali na ringa binsu da kallo dukaninsu sun girma sun Zama Yan Mata Masha Allah har Raheema dake da shekara goma Sha shidda.

Abinda ya ragemin Jin dadi Bai wuce halin da yarana biyu suka tsinci kansu a ciki ba.

Ko yanzu ma Zahira bata nan haka ma Waleed

Ina zaune ne kawai amma zuciyata na wajensu.

Shigowar Waleed da Sallama kasa kasa yasa na amsa da Sauri Ina lalubar kwayar idonsa

Ina ganin canji sosai a tare dashi tunda aka juya Masa Kai bai tab'a shigowa gidan da sallama ba sai gashi kwana biyu na lura Yana shigowa da sallamar duk da kasa kasa yake sallamar.

Girman jikin da yake dashi da kwarjini yasa k'arfi da yaji yayayensa suka koma shakkarsa idan ka ganshi zaka iya tunanin ya girmesu

Sabida naseeha Dana wa yayyensa yasa suke hakuri da duk wani rashin kunyar da yake musu.

Kitchen ya Shiga ya d'auko abincinsa har zai Shiga d'aki Inna Amina ta Kira shi akan yazo gefenta ya zauna.

Gefenta ya zauna ya fara cin abincin kallona da Inna Amina tayi yasa na mik'e na Shiga d'akinta na dauko ruwan Addu'ar Waleed da Zahira na tsiyaya a Kofi na Kai Mata ta mik'awa Waleed ya karba.

Jansa Inna Amina ta fara yi da hira

Sai gashi Waleed ya saki jiki Yana hirar shima alhamdulillah Ina ganin canji sosai a wajen yarana.

Kamar Dani yake hiran haka na zuba Masa Ido Inna Amina na Masa naseeha cikin siga har tana idan ya gama cin abinci yaje yayi sallah

Yana kuwa gama ci yaje yayi alwala.

Ya Shiga d'aki da zumar yin sallah Dan tsakar gidan namu karami ne sosai.

Sallamar da akayi tare da shigowa yasa dukan mu muka kalli bakin kofa.


Yarana Suka saki ihun murna sukayi wajen Naseer dana kasa d'auke idona akansa.

Shima hadesu yayi ya rungumesu.

Kwalla ya cikamin Ido Dana ga yanda ya rame har furfura ne suka firfito Masa

Inna Amina kuwa tsabar murna tafi ta ringayi daga zaune tana Masa oyoyo.

Dak'yar ya bambare su Nadeeya daga jikinsa

Ya nufo wajen da muke Zaune yana zuwa ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau gaisheta.

Cikin murna ta ruko hannunsa ta hau amsawa tana had'awa da Masa tambayar Mai yasa ya Dade haka Bai waiwayo mu ba a matsayinsa na da namiji ai hakuri ya Kamata yayi bai Kamata yayi fushi ba.

Fada da naseeha Inna Amina ta Masa ta had'a da bashi hakurin Abunda na Masa akan yamin uzuri idona ne ya rufe akan su Zahira shiyasa na Masa haka

Murmushi yayi yana "Ba komai Mama wlh ban riketa a raina ba korar da tamin daga gidanta yasa Nima na samu Allah ya dafamin na nemi kudin da Nima na siyi filin nayi gini naje wancan tsohon gidan nata anan nake Jin labarin Kun tashi dak'yar na gane Kuna nan nima nasan Ina da laifi da Abubuwan da na ringayi a baya da Nima sai daga baya nagane ban kyauta ba sai dai na baku hakuri Allah ya kiyaye gaba"

Sai a lokacin muka hada Ido dashi ya dan sakarmin murmushi Nima na sakar masa.

Nadeeya ya kala Yana "Inna Zahira"?

Nadeeya na k'ok'arin Magana Waleed ya fito daga d'akin.

Na zubawa Naseer Ido naga ya zaiyi idan ya ga Waleed zai Masa wanan kallon tsanar daya Saba Masa

Kallon kallo sukewa juna da yasa na kasa karantar kallon da Naseer ke yiwa Waleed har Waleed ya d'auke kansa yayi waje ba tare da ya gaishe shi ba

Inna Amina da Sauri ta hau Masa bayanin halin da Waleed da Zahira ke ciki har yanzu da muke ta addua Allah ya shirya su.

Girgiza Kai yayi Yana insha Allahu shima Yana addua Akan Allah ya warware abinda aka musu

Daga haka ya cewa Nadeeya ta fita ta nemo masa Zahira

A Dan karantar da na Masa sai Naga kamar har lokacin ba soyayar Waleed a Ransa

(Duk da asirin da aka musu na karyewa har gobe Da nake rubuta wanan labarin wani zubin idan abin ya motsa Naseer da Waleed basa Zama inuwa daya bi maana Babu wanan soyayya d'a da uba Mai k'arfi a tsakaninsu)

Nadeeya ya tasa a gaba suka je neman Zahira gidan kawayenta da wasu mun San gidansu wasu bamu sani ba da suka Taki saa gidan kawarta da muka sani anan suka same ta.

Naseer ya taso ta gaba suka dawo gida.

A Palo ya zaunar da ita ya hau Mata naseeha

Inda ni Kuma jikina yayi balain sanyi da na ga kamar da Zahira kawai ya damu Banda Waleed.

A ranar nayi kukan da na dade ban yi ba dan duk da a gidan ya kwana ya Kuma bani labarin Dana koresa daga gidan bai koma Abuja ba motarsa ya siyar ya hada da kudaden daya samo ya siyi fili Rabin filoti a gyadi gyadi ya hau gini ta hanyar neman kudi Yana buga buga har Sana'ar hannu sai daya koya dan kawai ya samu kudin da zai gina gidansa.

Ko abinci baya iya sawa cikinsa sosai sabida kawai ya samu kudin gini Addu'ar da ya dage dashi yasa ya dawo hayyacinsa.

Yana Kuma Kai karar mahaifiyarsa wajen Allah Dan ta cutar dashi.

Cikin siga na hau shigar Masa da maganar Waleed da naga rabi yafi damuwa da halin da Zahira ke ciki har Yana cemin yanzu so yake idan mun koma gidansa ya dukufa da Addu'a Zahira ta samu Lafiya idan na Shigar Masa maganar Waleed sai ya Sako min wani zancen.


Washegari da sassafe aka hau jiddar kayanmu Ana kaiwa sabon gida

Ina ganin ya fita naje na samu Inna Amina cikin damuwa na hau gaya mata karantar da nayiwa Naseer akan Waleed.
Hakuri ta bani tace na bi komai a hankali Kar na damu kila Abunda akayi a tsakaninsu bai gama warware bane mu cigaba da Addu'a.

Yarana murna kawai suke zasu koma sabon gida Nima a kasan Raina na ji dadi sosai da Naseer ya samu ya Gina gidan kansa tamkar ni nayi gidan haka na ringa ji shima fuskarsa kawai zaka kalla kasan Yana dokin sabon gidan da yayi kamar bai tab'a gidan kansa ba.


Ranar tashin namu daga Zahira har Waleed ba Inda suka je a ranar duk da Ina lura da Waleed da Naseer suna Yar kallon kallo Wanda hakan ya dameni sosai.

Da yamma na shishiga mak'ota muka musu Sallama

Inna Amina ita ta ringa lallaba Waleed dan kar ya botsare Mana yace bazai bi mu ba.


Su Nadeeya dama sun dade a can dan tun safe Naseer ya Kai su dan su shirya Mana kayayyakin mu.


Iya ni da Inna Amina sai Waleed da Zahira ne bamu tafi ba sai daddare Naseer ya kawo taxi muka hau Muka tafi gabadaya.

Gidan yayi kyau ba laifi duk da gidan bai Kai girman gidajensa na baya ba dakuna hudu ne a gidan da falo kitchen da band'aki a kowane daki.

Dan karfin hali har da dan kujeru sababi masu saukin kudi.

Daga ni har yarana Sai murna muke Dakunan duk a cikin falo suke d'akin da bai Kai sauran girma ba aka sawa Inna Amina karamin katifarta da kayanta.

Su Nadeeya Kuma suka dau d'akin tsakiya suka saka katifarsu guda biyu.

Daya d'akin Kuma shine nawa dayan na Naseer.

A Raina naso Waleed nada d'akinsa ba d'akin daya dace ya d'auka Sama da Wanda Inna Amina ke ciki Amma insha Allahu zanyi k'ok'arin sama Masa d'akin.

Ban dawo daga tunanin dana tafi ba naji Waleed cikin dan daga murya Yana "Ni a wane daki Zan ringa kwana"?

Naseer d'auke kansa yayi ya shige dakinsa

Tuni naga Waleed na k'ok'arin Hawa wanan dokin zuciyar tasa dake sa yayi zuciya ya bar gidan

Allah cikin ikonsa Inna Amina tayi saurin cewa a d'akinta zai ringa kwana ita a dakinsu Zahira zata ringa kwana dan Sam Bata San kwana ita kadai


Inna Amina ce ta taimaka min aranar waleed bai zuciya ya bar gidan ba.


Tunda Muka dawo gidan na lura Naseer bai fiye baccin dare ba yakan raba daren wajen sallah da Addu'oi tamkar dai yanda ya ke yi ada.

Hakane yasa nima na Kara akan Wanda nakeyi da.

Dawowar mu sabon gida tamkar k'ofar samun warakar yarana ne dan a hankali naga Zahira da Waleed sun fara nutsuwa suna Jin maganata har sallah da suke Wasa dashi yanzu suna maida hankali suyi duk yawace yawacen nan da sukeyi yanzu basa yi duk da Basu dawomin dai yanda Suke gabadaya ba Amma ko hakan suka zauna alhamdulillah.

Allah kawai nake Godewa daya amsa Mana adduar mu akan yaranmu.

Abu daya ke damuna Naseer da Waleed Dana ga Kamar basa ga miciji dan yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login