Showing 18001 words to 21000 words out of 180103 words
lokaci ne"
Umma tace tana Kara min wani irin murmushin daya sa na Dora hannu a aka na fara kuka.
Tuni na nemi yunwar da nakeji na rasa yau kalaman Umma sun tsoratani sun saka min balain fargaba da na hau nadamar Mai ya hanani tafiya lokacin da na haifi Zahira a Palo duk suka watse suka barni.
Ni kuwa Jin zazzabi na neman rufeni sabida tashin hankali yasa na rarrafa na shiga d'akina.
Ina kwanciya wani irin Mugun zazzabi ya rufeni.
Nadeeya da Zahira kuwa na gefena suna ta min Sannu.
Bansan ya akayi bacci ya d'aukeni ba
A cikin baccin da nake Naga kamar mahaifiyata ta shigo d'akina ta tsaya daga bakin kofa tana kallona tana ta hawaye Ni kuwa sai mik'a Mata hannu nake Akan ta tafi Dani ita kuwa ta ringa girgiza min Kai sosai nake ta kokarin mik'ewa Dan naje gurinta naji jikina yayi balain nauyi na kasa tashi a Haka na zuba Mata Ido Ina kuka tana kuka sai gani nayi ta nufi dakalin dake tsakar gida ta d'au buta ta hau alwala tana gamawa na ga ta shimfida Abu ta tada Sallah tana iddarwa ta daga hannunta sama tana ta maganar da ba jinta nake ba tana ta hawaye sai jijjga hannunta take alamar rok'on Allah take.
Idona na bud'e a hankali sai Dana kwashi Sakani nasan Ashe mafarki nake ba da gaske bane mafarkin Nan da nayi kamar ba mafarki ba.
Yanda naji jikina yamin nauyi a mafarki yasa na fara k'ok'arin mik'ewa sai dai me Ina duba jikina Naga duk na kumbura kamar wacce aka hura k'afafuna ma sunyi wani irin nauyi da kumburi jikina yayi wani irin Haske Kamar wacce Bata da jini.
Take maganganun da Umma tamin dazu suka fad'omin mafarkin danayi da Mahaifiyata tana hawaye tana rokon Allah a mafarki shima ya fad'omin.
Girgiza Kai kawai nake hawaye na zubomin Ni nasan tawa ta zo karshe mutuwa zanyi haihuwa da Umma take ta cemin nayi tagani Ashe mutuwa zanyi bazan haihun ba mutuwar da zanyi Ashe shiyasa Naga Mahaifiyata a mafarki tana kuka tana rokon Allah.
Kuka na fara sosai Ina tausayawa kaina ganin ban shirya ba mutuwa tazo min tausayin yarana da zan tafi na barsu a hannun Umma kawai ya balain Sakani kuka banso a yanzu zan mutu ba naso Na haihu Naga abinda ke cikina inkare yarana daga sharrin Umma da yayanta naso nasake ganin Naseer muyi magana kafin na mutu naso Na samu ilimi da zan San Mahallicina Sabida na bauta Masa na samu guzurin da zan tafi kabarina.
Kuka nake sosai Ina Kara kallon jikina dake ta kumbura kamar Ana hura min iska.
Hannuna kawai nauyi yayi min Kamar dutse ballantana na iya daga jikina na tashi nayi alwala nayi Sallah idan akwai abinda nake San Yi yanzu bai wuce nayi Sallah ba inama inada ilimin addini inama yanda Naseer ya iya Karatun Qurani dake balain Sakani nutsuwa idan Yana karntawa da yanzu na karanta naji nutsuwar da zanyi addua na roki Mahallicina ya kularmin da yayana dan shi kadai gareni yanzu.
Ni nasan mutuwa kawai zanyi daga yanda nake ta kumburan Nan Ashe Umma tasan kasheni zatayi shiyasa kwana biyu ta shareni ko Mai nayi Mata haka da take ganin kasheni shine mafita a gareta.
Bansan tsawon lokacin Dana d'auka a kwance a Haka ba ko kaina bana iya dagawa ballantana na kalli window naga ko dare yayi.
Sallatin da iya shi na iya da fatiha da iklas kawai nake yi a zuciyata Dan nasan kowane lokaci zan iya tafiya yayana dake ta bacci a gefena nake wa kallon tausayi Ina hawaye.
Yanayin danaji garin ya dau shiru sosai sai Haushin karnuka sama sama yasa nasan dare yayi sosai ko karfe dayan dare ko biyu.
K'ofata da aka bud'o yasa na kalli bakin kofar.
Umma ce ta shigo cikin jajjayen Kayanta hannunta d'auke da wani bak'in tunkunya an rufeshi da farin kyalle Fuskarta kuwa d'auke da murmushi.
Kallonta kawai nake hawaye na gudu a fuskata na rasa Mai nayi Mata rayuwa ta tsaneni Haka.
Ajiye tunkuyar tayi bakin kofa ta karaso kan gadon cikin murmushin daya bayyana hakoranta.
Tace "Kai da wuri Haka aiki ya fara ci lailai Shugaba aikinta yayi kyau Nan da wani satin Ana Nan ana zaman makoki Naeema Kinga illlar taurin kai ko toh Allah ya jikanki.
Daga Haka ta koma wajen data ajiye tukunyar ta tsugunna a bakin kofar Naga ta Ciro wani Abu kamar Sand'a ta fara taune kasar bakin kofar.
Nidai Ido kawai na zuba Mata Ina kallonta
Tana Gama hak'a kasar ta d'auko wani Abu Mai siffar mutum mace da ciki ta zura hannu ta d'auko farin kyalle ta nanade abin dashi ta zura a Ramin ta saka kasa ta rufe tana gamawa ta juyo ta kalleni ta sakarmin murmushi ta d'auki tukunyarta tayi waje tare da rufemin kofa
Tana fita Naga na cigaba da kumburi jikina na wani irin rawa
Rufe idona nayi na tuno iyayena na tuno fuskar Naseer da rabon Dana saka shi a idona da ganin danayi Masa na karshe ta gefen idona hawaye ya ringa zubomin inajin idona namin nauyi shima sabida kumburin danayi Sallati kawai nake Ina jiran mutuwa tazo ta d'aukeni.
Naseer
A ranar shima wuni yayi da zazzabi a jikinsa gabansa na balain fad'uwa hakan da ya gani ne yasa ya nufi wajen wani Sheik Musbahu daya zama babban mallamin da Mallamai ma suna zuwa wajensa daukar karatu.
Da Magriba Naseer ya Isa Massallacin sa da mutane ke cike suna sauraran tafseer daga wajen Mallam Musbahun
Waje Naseer shima ya samu ya zauna ahaka har sukayi Sallar Ishai
Wajen takwas da rabbi aka Dan watse daga Massallacin ya rage daga Mallam Musbahu sai wasu guda biyu da Naseer.
Naseer shi dai shiru kawai yayi kamar mara lafiya aka kawo abinci daga gidan Mallam Musbahu suka had'u suka ci.
Anan Musbahu ke fad'a musu zasu iya tafiya shi a Massallaci zai kwana sabida akwai wani addua da yake so yayi.
Naseer da bayajin zuwa gidan shima da Sauri yace shima bazai je gida ba zai kwana a Massallacin haka ma sauran biyun
Ahaka suka fara adduoi da karatun Qurani Naseer kuwa ya balain dagewa ko kad'an bacci Bai zo Masa ba.
Wajen karfe biyu bacci ya dauki Mallam Musbahu da ke rike da Qurani.
A hannunsa.
Ko minti goma baiyi da fara baccin ba ya farka da sallati ya Ajiye Qurani a gefensa ya kwanta a hannun Dama bacci ya Kara daukarsa.
Kwanciyarsa da minti goma ya sake farkawa
Ya Kara juya kwanciyarsa ya sake farkawa da sallati a bakinsa.
A hankali ya Kai kallonsa Kan Naseer dake ta karatun Qurani ya zuba masa Ido Yana kallonsa tare da tuno mafarkin da yayi .
Bai ce komai ba ya mik'e ya fita waje ya daura alwala ya dawo ya tada sallah sai daya jima Yana sallahn yaja manyan adduoi.
Tare da yin istihara.
Wajen karfe ukun ya Gama ya kalli Naseer da ya Ajiye Quraninsa a gefe ya mik'e Yana Shirin tada sallah.
Gyaran murya yayi ya kirashi
Naseer kuwa ya nufi wajensa ya zauna ya tankwashe kafarsa Yana kallon Mallam Musbahu.
"Ina iyalinka take Mallam Naseer"?
Wani dum Naseer Yaji a kansa kalmar iyali na Masa wani iri a kunne.
"Iyali"?
Naseer yace shima cikin tambaya.
"Ee Ina nufin Ina matarka take"?
Wani irin dum yaji kansa ya Kara Masa ya rik'e kansa da hannu biyu kalmar matarsa na amsa kuwwa a kunnensa.
"Baka San Inda matar taka take bane"?
Naseer shiru yayi yana so yayi tunani take fuskar Naeema ta hau gilma Masa a Ido.
"Matarka na da ciki ne"?
Kalmar da Musbahu ya sake jefawa Naseer kenan.
Inda kalmar ta tarwatsa duk wani shiri da akayiwa Naseer.
Naseer ya mik'e zumbur Yana kwala Kiran sunan Naeema tare da tuna karshen ganin da yayi Mata a dakinsa tana Masa zancen cikin dake jikinta da take fatan ya kasance namiji Mai Kama dashi.
Murmushi kawai yayi Mata ya rungumeta yayi waje da Sauri sabida Latin da yayi karshen ganinsa da ita kenan sai yanzu daya dawo hayyacinsa.
Naseer hankali a tashe ya fara k'ok'arin yin waje still Yana Kiran sunan Naeema.
Mallam Musbahu kuwa ya jawo hannunsa ya zaunar dashi.
Yana "Alhamdulillah daka dawo hayyacinka dazu Allah ya nuna min a mafarki a ciki dalibai na matar wani a cikinsu ta rasu da ciki munje mun binneta da zamu dawo sai na juya na hangoka a Kan kabarin kana ta kuka sau Uku nayi mafarkin a jejjere hakane yasa nace Bari dai nayi istahara sai Allah ya nuna min matarka tana d'auke da tsohon ciki shaidanun mutane zasu kasheta Amma mutane zasu dauka da tazo haihuwa ta mutu yanzu Haka kwana bakwai ya rage su cimma burinsu Dan Haka zan baka adduar da zakayi na kwana bakwai a ranar da zaka cika kwana bakwai kana adduar a ranar ka siyi tunkiya Mai tsohon ciki da ta Isa haihuwa itama sai ka yanka ta ka binne insha Allahu a ranar matarka zata haihu lafiya batare da ko ciwon Kai ba Amma fa daga yau karka sake sake irin wanan Dan kana dab da rasa matarka kaje idan matarka ta haihu ka dawo zan baka wasu adduoi Allah ya Dora ka akan makiyanka Dana matarka.
Naseer dak'yar ya tsaya Mallam Musbahu ya nuna Masa adduoin cikin Quraninsa tsabar matsuwa da yayi yaga Naeema.
A cikin Daren kafa ba takalmi hankali a balain tashe da gudun balai Naseer ya dauki hanyar gida kuka kawai yake Yana tuno maganganun Mallam Musbahu.
Ki yafemin Naeema wlh bana cikin hankalina shine kalmar da yayi ta fada har ya Isa k'ofar gidansa.
Bai tsaya ma kwankwasa k'ofar ba yayi wa k'ofar wani irin Bugu ya fada palon hajara dake zaune a Palo da tukunyar kasarta tana ta murmushin cikar burinta ta mik'e da Sauri tana kallon Naseer daya fad'o palon kamar an jefoshi.
Naseer ko kallonta baiyi ba ya nufi d'akin Naeema aguje Yana kwalla mata Kira.
Ihu Hajara ta saka ta Sha gabansa hankalin ta a balain tashe adaidai lokacin da tukunyar kasr ta fado kasa ta tarwatse shi kuwa Naseer da idonsa ya rufe ya ture Hajara data Sha gabansa ya banka k'ofar d'akin Naeema ya tsaya a bakin kofa yana kallon Naeema data kumbure kamar ba ita ba zubewa yayi akan gwiwarsa jikinsa na kwasar wani irin rawa.
Kamar a mafarki Naga Naseer ya banko k'ofata ya tsaya a bakin kofa yana kallona.............
Duka page dinan wlh babu fiction
8/19/21, 10:30 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 8*
Da kumburarren Fuskata nayi murmushin tare da Kara rufe idona ganin Fuskar Naseer da nake tunanin a mafarki yazo min Dan Ni nasan babu yanda za'ayi Naseer ya zo Inda nake naso ace na ganshi na bashi amanar 'ya'yana.
Zuwa yanzu farinciki barin wanan azababen rayuwa dana tsinci kaina nake Ina Kuma bakin cikin rabuwa da Nadeeya da Zahira ko ya rayuwarsu zata kasance bayan Raina.
Gunjin kukan Naseer ne ya saka na Kara bud'e idona na kalli Naseer dake durk'ushe a bakin kofa jikinsa na rawa ko ta Ina hawaye na zubo masa.
Umma kuwa Tana daga bayansa hankalinta a balain tashe sai rawa jikinta yake tana Kiran sunan Naseer da k'arfi Dan Had'uwar Naeema da Naseer na nufin duk aikin da tayi akansa ya wargaje ita kanta Naeema duk Shirin da tayi akanta wargajewa zaiyi Dan tasan Naseer sai yayi tsayuwar daka akanta.
Gashi tukunyar da ta tsaface mutane da Dama ya fashe Wanda hakan ke nuni duk a yau zasu dawo hayyacinsu waye ya Mata wanan danyen aikin Naseer ya dawo hayyacinsa Bata da burin daya wuce janye Naseer Kar ya Kai ga isa wajen Naeema dan ita tasan wahalar da ta Sha kafin ta iya shiga tsakaninsu da iya karfinta ta cigaba da Kiran sunan Naseer.
Ni kuwa ganin Naseer na ta kuka Yana kallona tare da Kiran sunana yasa na d'an runtse hannuna sabida Naga kodai ba mafarkin nake ba.
Ganin tabbas ba mafarkin nake ba yasa naji wani irin hawayen farinciki ya zubomin da Allah ya amsamin addua ta da zan Kara ganin Naseer na bashi amanar yayana kafin na mutu.
Ganin Naseer bashida niyyar tasowa sai sharbar kuka yake Yana Kiran sunana yasa na gwada magana
"Naseer karaso gareni Dan Allah na baka amanar Zahira da Nadeeya kafin na mutu"
Naseer mik'ewa yayi Yana Jin kafafunsa kamar bazasu d'aukeshi ba halin da yaga Naeema a ciki ya balain daga Masa Hankali yanzu Naeemarsa ce ta dawo haka.
Duk tsawon lokacin Nan tayaya take rayuwa a Haka ita kadai anya ya rik'e amanar da Iyayenta suka bashi kuwa Ina hankalinsa yake duk lokacin Nan ya iya manta matarsa uwar yayansa.
Kuka yake sosai jikinsa na rawa yanda ta kumbura yasa hankalinsa ya balain tashi a Haka ya Isa wajenta.
Tun kafin Naseer ya karaso wajena wani irin kuka ya k'wacemin sai da mutuwa tazo min Naseer zai zo wajena Mai nayi Masa Haka ya watsar Dani.
Hannuna daya ruk'o cikin nasa hawaye na ta zubar Masa yasa na fara magana Ina
"Haba Naseer Mai nayi maka Haka Dana cancanci Haka daga wajenka? Mai nayi maka da zafi Haka Naseer da zaka watsar Dani bayan kasan banida kowa sai Allah sai Kai idan wani Abu ma nayi maka Naseer Mai yasa bazaka gaya min na nemi yafiyarka ba Naseer kasan rayuwar da na ringa Yi kuwa a cikin gidanan sai daka ga mutuwa tazomin zaka zo Naseer"
"Bazaki mutu ba Naeema insha Allahu bazaki mutu ba yanzu na dawo gareki Naeema wlh duk abinda ya faru ba a cikin hayyacina nake ba Naeema ke Mai bawa wani labarine wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ballantana ke da Kika kasance rabin rayuwata wlh Naeema sai a yau na dawo hayaccina wlh duk tsawon lokacin nan kaina a juye yake Dan Allah ki yafemin Naeema"
Mai ya kumburaki Haka Naeema Mai ya Sameki Haka? Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"?
Kawai Naseer ke iya maimaitawa Yana tattab'a jikin Naeema dake kumbure.
Cikinta ma yayi wani irin tsini da kumburi kamar zai fashe
"Naseer ga amanar Zahira da Nadeeya Nan Dan Allah ka Kular min dasu karka Bari a cutarmin dasu Naseer mutuwa zanyi"
"Insha Allahu bazaki mutu ba Naeema Zaki samu lafiya insha Allahu yanzu ba abinda zai Kara samunki Ina Nan tare dake Zaki haihu lafiya kinji Naeemata"
Girgiza Kai kawai nayi Dan ni nasan Mai nakeji a jikina.
Naseer da Sauri ya shiga band'aki ya d'aura alwala ya fito ya shimfida Sallaya dama da akwai Qurani a d'akin ya bud'e ya tadda sallah ya fara adduar da Mallam Musbahu yace yayi sai da ya kusa awa a tsaye baiyi rukuu ko Sujadda ba Haka ake yin adduar sai da ya fara Jin Kiran Sallahr asuba yayi ruku'u da Sujjada yayi ta kaiwa Allah kukansa Yana nemawa mahaifiyarsa Shiriya da yafiyar Allah.
Ni kuwa kasancewar Naseer a d'akin da Karatun Qurani da ya fara Yi ya Sanya min wani irin nutsuwa bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba.
Naseer kuwa kasa ma fita massallacin yayi a d'akin yayi Sallahr Asuba daya iddar kuwa ya cigaba da Addu'a da Mallam Musbahu ya bashi.
Sai daya Gama wajen karfe bakwai ya bar Kan Dadumar ya kalli b'arin da Naeema take Yana Jin wani irin tausayinta Zahira da Nadeeya daya ga sun tashi yasa ya karasa Kan gadon ya sauko dasu.
Ya zauna a Gefen Naeema da har a lokacin a kumbure take ya fara totofa Mata adduoi Yana shafe Mata jikinta shi kansa yasan wanan kumburin ba na lafiya bane.
Ya dade Yana tofa mata adduoi kafin ya rik'e hanunsu Zahira yayi waje sai a lokacin Hajara ta fado Masa ko Ina tayi oho.
Bai kalli ma Inda d'akinta yake ba ya shiga dakinsa yyi wanka a gurguje yayiwa su Zahira brush ya fito ya shiga kitchen ya had'a musu breakfast dayake ba abinda Naseer bai iya ba
Har a lokacin baiji motsin kowa ba Yana gamawa ya fito daga kitchen din tare da breakfast din daya had'a ya nufi d'akin Naeema ya Ajiye ya had'awa Su Zahira tea har a lokacin Naeema bacci take hakan kuwa ya Dan kwantar Masa da hankali ya Ajiye abin karyawar ta a Gefen gadon ya fito waje.
Duk abinda Hajara zatayi Masa bazai tab'a iya canzata ba itace dai Mahaifiyarsa Bai Isa yayi fushi da ita ba.
D'akinta ya nufa ya tura k'ofar yaga ba kowa har su Safiyya ma Bai gansu ba hakane yasa ya fara mamakin Inda suka kwana ba Inda Bai duba ba Bai gansu ba.
D'akinsa ya koma ya dauko radionsa da cassette din dake d'auke da Karatun Qurani izzu Sittin ya jona radion ya saka cassette din aciki tare da kunnawa.
Take Suratul yunus ya fara tashi ya karasa wajen Naeema ya fara tashinta.
Kamar a mafarki naji Ana tashina daga d'add'an baccin daya d'aukeni wanda rabona danayi irin shi zan iya cewa tun farkon Aurena.
A hankali na bud'e idona Naga Naseer a tsaye akaina.
Na rufe idona na sake bud'ewa Ashe dai a gaske Naseer yazo dakina ba mafarki bane yanda gari yayi haske yasa nasan gari ya waye kuma ban mutu ba kamar yanda nake tunanin a jiya zan koma ga Mahallicina.
A fili na fara Hamdala Ina nanatawa jikina dayamin nauyi da nakejinsa a d'ad'aure yanzu duk babu sai kumburin dai da nayi da ban sace ba har a lokacin
Shima Naseer Tayani Godewa Allah yake
Na mik'e zaune Ina "Naseer ban mutu ba Alhamdulillah"
"Karki damu Naeema bazaki mutu yanzu ba insha Allahu.
Mik'ewa nayi da Sauri Naseer yayi saurin taroni Yana cemin nayi hankali nace Masa Kar ya damu Sallah kawai nakeso nayi.
Sai Dana yi wanka na wanke Bakina na daura alwala na fito na saka doguwar Riga na tadda sallah duk Sallar da banyi ba jiya na Rama na zo nayi Sallah Asuba Ni nasan ikon Allah yasa har yanzu nake rayye.
Naseer yana Gefen gado a zaune Yana kallona Yana ganin na iddar ya kawo flask din kayan karyawar gabana ya had'a.min shayi Mai balain kauri ga kwai shima da kaurinsa daya soya.
Tankwashe kafarsa yayi ya fara k'ok'arin bani.
Ni kuwa hawaye suka hau zubomin Ina ganin Kamar dai mafarkin nakeyi yaushe rabona Dana Sha shayi Haka yaushe rabona Dana ga mijina a d'akina ko Ina Umma take data min adduar Allah ya jikaina
Kofin shayin ya