Showing 1 words to 1128 words out of 1128 words
Chapter 1 - DARK LUST Book Hausa Novels By Oum Hairan .pdf
*í ½í²§DARK LUSTí ½í²§*
_*(Hot love and destiny)*_
*Fauziyya Tasiu Umar*
_Bismillahir Rahmanur Rahim_
*Page 1-2*
*Mafari*
Ƙauyen Wanzamai dake cikin wani local government a cikin garin Kano a Kano ta Kudu,
jama'ar dake rayuwa a wannan gari ba za su haura dubu ɗaya ba, Allah ya azurta su da ƙasar
noma da kuma arziƙin duwatsu da ke ɗaukar hankalin ‘yan birni, da sukan ɗauko ƙafa su taho
kawai domin ɗaukar hotuna da short video da za su samu na trending a duniya. Yau ta kama ranar Lahadi ce kasancewar tazo daidai da ƙarshen hutun zangon karatu da akayi
ɗalibai sai shirye-shiryen komawa makarantu akeyi, cikin wani babban gida me ƙofa ƙofa zubin
ginin gargajiya, ƙofar Mal Alasan wata yarinya ce da shekarunta bazasu wucce 14 ba tsugunne
gaban murhun duwatsu tana iza wutar karar da take ci da dukkan alamu wani abu ake so ya
dahu a cikin tukunyar.
Faheemah! Faheemah!! Ke Faheemah ina kika shiga ne kizo ki ƙarasa haɗa kayan nan naki
nasan duk inda Mal yake yanzu hankalinsa na kanki yamma ta fara daganan zuwa
makarantarku da nisa kuma" Miƙewa yarinyar da dukkan alamu itace take amsa wannan suna
na Faheemah tayi ta nufi ɗakin da Muryar take tasowa ta duƙa ta shiga domin itan doguwa ce
akan ƙofar wata matashiyar mata ce da itama shekarun nata bazasu haura daga 30 ba zaune ta
mimmiƙe ƙafa da uban ƙaton ciki a gaba da alama dai gaf take da haihuwa.
Zama tayi a gaban adakar dake gaban wannan mata tace “Inna sannu ya jikin? Nifa dama nace
Miki kibar haÉ—a kayan nan Inna Nifa kawai naji kamar kada na tafi na barki a wannan halin kina
ganin irin zaman da kukeyi da Babarsu Lamimi sannan duk matan gidannan ba sanmu sukeyi
ba kowa ita yake goyon baya duk rashin kirkin da zatayi Miki kece mars gaskiya, nidai bari Mal
ya dawo na faÉ—a masa ya barni na zauna dake bayan kin haihu na tafi"
Kamo hannunta Inna Dije tayi tace “Banda abinki Fahim Inna zaman naki zai hana Allah ikonsa
ne? Kinga burina a duniya kiyi karatun boko me zurfi ki zama likita kodon kula da matsalolin
mata fahim Inna Nasha wahala a haihuwarki malaman asibiti sun wulaƙantani nida Babanku da
duk wani daya shafeni kawai don sunga daga ƙauye muke sukaƙi karɓarmu har Saida kanki ya
fara fitowa sannan wata likita ta shigo inda nake taga halin da nake ciki ta É—aukeni ta shiga dani
É—akin haihuwa tanata masifa ta zage ta taimaka min Allah yasa dani dake munada rabon shan
iskar duniya kikazota gashinan tun lokacin har yanzu bamu huta ba" kullum idan mahaifiyarta na
bata wannan labarin takanji tausayin kansu da kuma tsanar likitoci domin kuwa sun nunawa
Innarta rashin imani Amma babu komai tasan wataran zata wankewa Inna zuciya idan itama
tayi karatu ta zama likita.
Sallamar Mal ce ta katse musu hanzari Inna tace “Sannu da zuwa Mal dama yanzu nake cewa
duk inda kake kana hanya" cire hularsa yayi yace “Wlh Hadizatuq inacan daƙyar na samu
wanda yasai akuyar nan shima rabin kuÉ—in ya bani yace rabin sai ranar kasuwa to yanzu dai
zuwa Zamuyi mu tafi indai Allah yasa na kuma samun wasu kuɗi kafin ran kasuwar sai na ƙara
mata guzuri nakai mata, Ince dai kin shirya Heeman Mal" ƙasa tayi da kanta tace “Na shirya Mal
saidai Ni banajin tafiyar nan banason na tafi nabar Inna a wannan halin da take ciki" daƙuwa
yayi mata yace “Ƙundun ubaki nace! tashi muje" miƙewa tayi sumsum ya ɗauki kayan dake cikin
buhu suka fito tana waiwayen mahaifiyarta itama Inna Dije kallon É—iyar Tata takeyi cike da kewa
har suka fita daga É—akin suka fito tsakar gidan matan gida da sukayi da'ira da'ira da kuma yara
sa'o'inta da waɗanda basu kaita ba duk suka bisu da kallo can sukaji an sheƙe da dariya uwar
Lamimi da take ita ce uwar gidan Mal Alasan tace “Ahayye nanaye kaga yan bokoko a wuta an
fito za'a tafi Koyon yahudanci to Allah raka taki gona abinki ya ƙare a kanki keda uwarki" cak
Faheemah ta tsaya Zuciyarta na suya duk abinda zaayiwa rayuwarta takan iya jurewa amma
banda taɓa darajar iyayenta Inna Dije da Mal Alasan mutane masu kawaici da haƙuri domin
Allah ita tasan duk yakanarta da haƙurinta da yan makarantar su suke faɗa bata kama sawun
uwayenta ba domin kuwa data kama da ciwon ma da takeji a zuciyarta bazataji ba.
Waiwayowa Mal Alasan yayi ya hangeta can nesa tana tsaye ya kwala mata kira tare da cilla
mata daƙuwa, ta tako da sauri ya kama hannunta Yace “Heeman Mal ki koyi juriya haƙuri da
kawaici ita rayuwar gabaÉ—aya nawa take, yau ake dakai gobe da waninka za'ayi yau ina
Kakarku Ina Mal Idi mahaifinmu ina ƙannenki na ɗakinku Hassan da Hussaini duk babu su,
Heemah ina ƙawarki Hajara da kuka taso da ita, to idan kikayi haƙuri kema watarana labari zaki
zama sai a faÉ—i alkhairinki bayan bake sukuma Mala'iku su rubuta Miki akai Miki yabon da kika
samu a duniya cikin kushewarki, nidai roƙona dake na yau da kullum ne Faheemah ki nutsu kiyi
abinda ya kaiki banda biyewa mugayen ƙawaye banda wasa kuma banda kwaɗayi ki tsaya inda
Allah ya ajiyeki duk inda kikakai da kasawa wani yafiki kinfi wani, mu mutanen karkara ne kuma
talakawa shiyasa bazakiga komai namu irin na ƴan ajinku yan birni ba kiyi haƙuri watarana sai
labari"
Suna tafe yana mata nisihohin shi masu shiga jiki da zama a cikin ƙwaƙwalwa har suka isa inda
zasu hau mashin ya kaisu cikin garin Rano daganan suka hau motar Tudun Wada kasancewar
anan makarantar tasu Faheemah take, suna tafe tana kwance jikin Mahaifinta duk da ba daÉ—in
rayuwar makarantar tasu takeji ba amma takanso kasancewa a makaranta fiye da gidansu
saboda gidansu gidan masifa ne a cewarta matan aure sunfi Ashirin a gidan su kuwa Æ´aÆ´a
sunkai ɗari banda waɗanda aka aurar da waɗanda suka mutu, a ƙofarsu ma su bakwai ne
Æ´aÆ´an Lantai wadda suke kira Uwar Lamimi su Shida sai ita a É—akin babarta Inna Dije ita kaÉ—ai
koda Inna Dije ta haihu yakai bakwai É—iyoyinta suna mutuwa itadai batasan meye yake faruwa
ba amma takanji tun tana ƙarama idan Innanta ta haihu ɗan ya koma a gidan ana yan
tsegungumin tayi amanta ta lashe, har yanzu tana neman fassarar wannan kalma duba da
yanda ake kyararta da tsangwamarsu a gidan nasu sai take ganin kamar abin yanada alaƙa da
wannan kalmar duk da har yanzu batasan ma'anar kalmar ba.
*Contact me 09031307566*
*Oum Hairan*