Showing 300001 words to 303000 words out of 388021 words

Chapter 101 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9534

yatafi ba,
Saidai wani dan uwanta ya tafi a madadin mahaifina don baza tayarda ba da hakan,
Saida Baba Buhari yai mata kaca kaca amma bai sa ta janye kudirinta ba gare shi,
Sun shirya sunyi bankwana da mutane yan uwa da abokan arziki aka raka su hajji camp har zuwa lokacin Mama sai jidali takeyi,
A waya mu kayi Allah ya kai lafiya da su Anty Sadiya tare da Salawatu, don shi maigidan da jirgin yawo zai tafi sabod yanayin aikin su,
Fatima ce akabar wa gida inda ta dauko yaranta dukkan su biyu wai zasu zauna da ita su debe mata kewa, har matafiya su dawo,
Ba karamin dadi daji ba ganin diyan ta sun dawo gurin ta lafiya, batare da wani hayaniya ba daga dangin mahaifin su da kuma fanin mijin ta,
Hakan yasa ta bude wani sabon rayuwa na cinkaren ta babu babbabaka ita da diyan ta
Ramatu ta roki maigidan da tabarta ta koma gidan ta har zuwa lokacin da zasu dawo daga saudiya,
Haka Fatima da diyan ta suka sakata suna wallawan su gida ya zama na su, sai yadda suka ga dama abin su,
Kafin mahaifina ya tafi sai da Yaya Abubakar ya bawa yaya Ibrahim dina kudi yai masu sayayyan komai da zasu bukata na dangin kayan abinci da sauran a bin bukata,
Sai dan kudin da zasu a je, domin ,wasu, bukatocin su dashi,
Hakan yasa bamu sha,wani wahala ba saboda kasan,cewan samun komai a tare da mu,
Gashi kuma sauran iyayyen mu suna bamu kulawa na musan man wada ba mu da wani damuwa, atare damu, saidai kewa kawai, dake damun mu,
A nawa fanin kulawa ta musan man nake samu a gurin malam, saboda haka hankalina a kwance,.
Jego ya karbe ni dagani har yarona duk munyu bul,bul damu munyi fresh,
Yaro na dan sati uku yayi bulbul dashi yana wani kara haske irin na mahaifin shi,
Yana samu duk wani taimako da jariri ke bukata daga matan kakana wa yanda ke bamu
Kulawa ta musan man daga dangin ruwan zafi ganyen wanka, irin ta yan gargajiya,
Harda wani ganye wai lemon daji wanda idan uwa ta bawa yaron ta zai zama mai hazaka da kuzari,
Idan Allah ya raya shi baya zama raggo duk inda hazikki yakai insha Allahu sai yaro ya kai gurin,
Wanan ganyen lemon Dajin shine Mama Abu take yawan dafawa, take bashi ya sha kuma tai mashi tausa da ruwan,
Inda na fara notices din ganyen shi tun yaron yana dan jariri idan ya danki nono sai nayi ihu saboda yadda yake damkan nono,

****** ********** ******
Zan iya cewa wanan tafiyan na mahajjata tankar basu tafi ba don a kullun mu lake da waya da yayana ko Babana ,
Shi Baba na nice mai yawan kiran shi don kada ya kashe kudin shi, amma yaya Abubakar shi da kan shi yake kirana
Musan man ma idan zai sayi wani, abu zai bugo min waya yana tambaya na akan wanan abin,,
Zamu iya daukan tsawo lokaci muna kan layi dashi muna hira ,
Saidai idan naji shiru nasan cewa yana gurin ibada ke nan babu halin na ji kira,
Abubuwa masu muhinmanci na ci gaban rayuwa sun faru dani dan wanan zaman gidan da nayi saboda hakan ya dan kawo min shakuwa a tsakanin yan uwa na da ada can baya
Kiyayya da ada can baya Mama Ladi ta cusawa mutanen gidan mu a kan mu yanzu a hankali yake wankewa saboda gaskiya dake baiyyana a yanzu,
Samarin gidan mu wayanda suke a matsayin yayyena sukan dan zagayo gurina suce sun zo duba Baba karami,
Sai su dan dinga wasa da yaron a hanakali idan sun faki idon mutane sai suce,
Meenatu don Allah kina da canji na hau yar Vesper banda canji zan tafi wuri kaza
Wasu kuma sai su ce min Meenatu kina da canji na dan sayo abu kaza,
Ire iren hakan ke saka su kara sona kunsan dama ance idan kana son shiri da uwa to kaso Dan ta zaka ga sakin fuska daga gida,.
Yan matan gidan mu duk nai masu gwajon kayan sakawa na wanda Anty Amarya tai min na amarcina,
Badon sun tsufa ko su yi wani abuba na basuba a,a kawai dai don ganin cewa, dai yanzu Allah ya hore min wasu saboda haka nabawa mabukata su ma, tunda yanzu nafisu samu,
Ba karamin farin jini wanan alherin ya jawo min ba daga cikin yan uwana
Kayan dakina na da wanda yaya yacire ya saka muna wasu Baba Wadda ya kwaso min su a tare da wayan anan kayan da na rabawa yan uwana,
A dakin mahaifiyana na kafa wanan kayan yayin da na dakin ta muka mayar a dakin mahaifina,
Tsab mu ka gyara mai dakin shi kafin ya dawo daga saudiya,,

Ina zaune a gurin dana idar da sallah waya ta dake gefe tai kara hakan yasani gane cewa Yaya Abubakar ne yake kiran
Kafin na dauka sai wayan ya katse a lokacin don haka saina rike wayan a hannuwana,
Ba,a wani dade ba ya kara kiran layin nawa na dauka acikin wata murya mai saka kasala ina cewa Yayana ni kadai bada kowa ba,
Hmmm yace tare da jefomin tambaya da cewa ina kika shigene haka waya nata ringing baki daga ba,
Nace wallahi salla nakeyi yaya ina idarwa yana katsewa,
Tambayana yakarayi da cewa Meenat har kin fara sallah ne ?
Na dan yi dum batare da na bashi amsa ba da sauri,
Kara tambayana yayi kamar na farko
Nace ai na kwana biyu ina yin sallah
Sai naji ya sauke ajiyar zuciya yana cewa ashe tunda kun warke da na dawo sai ku dawo,
A take rudani ya kamani don nasan cewa zai iya yin haka ba wasa ba,
Kasa magana nayi sai dan inda inda nakeyi din jin muryan shi da nayi yana cewa ko bazaki dawo bane idan na dawo,
Subbahanallahi nace yayin da nake tunanen cewa, aiko idan nace zan koma yanzu da nawa ya samay ni ke nan,
Muryan shi naji yana cewa yaya ina maki magana baki bani amsa ba
Koko so kike sai idan nazo kice bazaki dawo ba har malam ya saka baki,
Ajiyan zuciya na sauke tare da kokarin tattaro miyauna guri guda don inji dadin magana,
Nace ai sai munyi wata uku kasan kafin mu ce zamu dawo,
Stop that please, kin kuwa san irin halin da nake ciki da har zaki ce hakan,
Kasa cewa wani abu nayi saboda mamaki don har wani irin hali na tsuci kaina,
Mutum mai mata har uku za,a ce wai yana zumudin dawowan na da jegona,
Naji yana cewa, look,Meenat dubi fa yadda na lalace na ramay nai wani irin baki, saboda kewan ku,
Ke ba kya tausayin nane wai Maman Boy, duk fa rashin kune ya ja min hakan,
Shiru nayi ina sauraren shi yayin da naji yana cewa, cikin dan kara tausa murya,
Meenatu Watan ki fa kusan shidda bakya a gidana so kike har sai an shekara daya ba kya gidan,
Cikin yar siriri yar murya, nake cewa Yaya kayi hakkuri lalura ne, ya kawo hakan, don nima ai ba dadina bane na nisan ta da kai,
Amma kin san cewa akwai hakki na akanki daiko, ?
Shiru nayi batare dana bashi ansa ba saboda jin irin yadda yake maganan shi,
Na rasa may zan ce mai sai kawai naji hawaye suna dan silalo min a lokaci guda,
Saboda abinda naji yace wai hakkin shi a kaina abin sai ya sakar min mutuwar jiki,
Ban san ya akayi ba ya gane cewa ina hawaye a lokacin don sai ji nayi, yana cewa don nafada maki gaskiya kike hawaye ko, ?
Idan nace ban yafe maki ba kin san dai kina da kaya a kanki,
Ko so kike sai na zubar da mutuncina nazo da kaina nace zan tafi dake,
Ya sallam na furta a zuciyata don sai nake ganin zancen kamar almara yakeyin shi,
Mutum kamar Yaya Abubakar cikkaken namiji dan boko mai ilimi kamala da zati ne zai dinga fada min wanan kalman haka,
Ga mata manyan mata a gidan shi har uku suna kara kaina a tsakanin su amma shine zai buge da fada min wanan zancen har yana cewa wai na dauki alhakin shi saboda ban tsaya a Abuja ba tsawon wani lokaci??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????,
Ranan ba wani hiran arziki da mukayi haka na muka rabu jiki ba kwari don ko dan shi bai tambaya ba,
Nai nadama kwarai na fada mashi cewa sallah nakeyi da duk hakan bai faru a tsakanin mu ba,
Hakana nake jiki duk yai min sanyi hardare duk na sakawa kaina damuwa,
Sai daga baya naiwa kaina fada na cire duk wani damuwa dake tare da ni,

****** ********** ******
Duniya ba kyau wanan tafiyan da Yaya Abubakar yayi yasa wasu daga cikin yan ma,aikatan su kai sukan cewa wai ya kamata a bincike shi,
Saboda irin yadda yake abubuwan shi cikin waddata da walwala akoda yaushe,
Ba bata lokaci aka shiga binciken al,amura akan yaya Abubakar din wanda bai kasan yana maka gurin sauke farali,
Malam Abdullahi masinja ne ya buga ma Yaya waya yana sheda mai cewa an shigo mai office ana bin cike wai
Murmushi yayi a lokacin yana Haram yana zaune saman carpet sai murmushine kawai ya sake yana cewa kabar su suyi ikin su kawai akwai Allah,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/27, 9:03 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL BATIN

JUMMA,AT MUBARAK YA JAMA,ATUL MUSULUMIN WISHING YOU BEST OF LUCK OF THESE BLESSING DAY,,,


Komai izuwa yanzu ya yi kyau a gidan mu don sai kara samun hadin kai mu keyi a tsakanin parents dina,
Wanan kuma ya samu asali daga tsohon gidan wanda ke ta kokarin ganin cewa kafin ya kaura yabar duniya ya samu hadin kai a tsakani zuri,ar shi, har abada,
Yanzu tsakanin wanan part din da wancan an rage yawan hamaiyya a tsakani sosai,
Lokaci guda jikokin gida sun fara kafa zaman lafiya a gidan fiye da tsanmanin shi,
Don haka yake wa Allah godiya yau da safe da ya fito ya fito ya samu Baba musa a zaune tare da Baba Hamza suna shawara,
Saida ya fito ya samu guri ya zauna a mazaunin shi, tare da dan gyara yan abubuwan da basu zauna daidai ba a gurin,
Lokacin ne suka samay shi zaune sukai mai barka da asuba tare da ankwana lafiya,,
Nan suke fada mashi cewa suna magana ne akan zance yaron wurin Baba Hamza wanda ke gudun karatu yanzu ya kuma fara bin miyagun a bokai yawo,
Malam ya furzar da ruwanda ya gunda a bakin shi don ya kurkure goro yana cewa,
Subbahanallahi assha tir, jam, Allah ya tsare ya kare yaushe har haka ya faru baku fada min ba,
Duk kan su shiru sukayi saboda basu san may zasu ce mai ba akai,
Cikin daurewa Baba musa ke cewa nima jiyane shi Hamzan ya samay ni da zancen,
Wai da cewa malamin su ne yazo har gida yana fada mashi irin halin da yaron ke ciki,
Shiru malam yayi tare da dan jijiga kan shi a hankali yana mai lumshe ido yace Alkah ya kaimu gobe akwai abinda zanyi,
Su kayi wa tsohon sallama suka nufi, wurin al,amuran su na yau da kullun,
Wanan maganar ta tsaya wa malam a rai sosai don bai tsan mani samun yaro maratarbiya irin haka ba a gidan shi ,
Badon komai ba sai kasancewar shi, mai ba da tarbiya a,cikin shiya saboda akasarin yaran uguwar mu a gurin malam suke saukan Al,Quran mai girma,

****** ******** ******
Zaune take falo tare da yaranta yan mata guda biyu, suna cin abinci,
Tv daga dayan gefen falon yana ta fama aiki tashan MBC 3 Ana film din power of rengers,
Hankali yaran naga tv basu damu da cin abincin da mahaifiyar su ta, tsare su su ci ba,
A hankali tajawo kujeran zuwa gaban yaran tana cewa yar babban daga cikin su, wai,ku ba kwa gajiya da wanan kallon shirmay ne,?
Yar babba ta dago kai da sauri tana murmushi tace cikin shagwaba Lah Mama aiko yana da kyau,sosai da zaki kalla ai zaki soshi,
Zan kalla Nusai, amma sai idan kun ci abinci nan dake gaban ku sai mu zauna tare mu kalla,
Cikin murna yaran suka dan fara cakular abincin a hankali suna dan kaiwa bakin su, har suka dan samu su kaci,,
Takira mai aiki ta kwashe kayan zuwa cikin kitchen tare da gyara gurin tsab,
A tsakiyan yaran ta zauna suna kallo yayin da suka fara da kwanciya a saman jikin mahaifiyan ta su,
A hankali Fatima ta sauke numfashi tare da lumshe idanuwan ta, yayin da takai hannuwan saman kan yar karamar yar tata,
Acikin zuciyar ta tana dama ace wanan gidan gidan mahaifin yaran nata aida sai yadda rayuwan ta ya tsaya,
Mama kinga film din yana da dadi, sosai na fada maki zakiji dadin yar tata da ta dafawa kai ke wanan zancen,
Lami mai aiki ce tafito daga dakin ta tana cewa cikin dan tsoro Anty kaman akwai wani abu a gidan nan nake jin shi tun dazu yana wani irin motsi,
Sai lokacin ta dago kai tun da Lami tafara magana ta kalle ta cikin irin yar rainin hankali kawai,
Kar ki ce min kuma sheri zaki kulla wa muatane Lami don halin kune yan aiki kullin sheri,
Cikin nuna alamar tsoro a fuskan Lami tace da sauri ba hakana bane Anty kawai dai wanan abin yai yawa ne tun dazun da nake jin shi a baya,
Dan Allah ki min shuru macuciya kawai ki rasa wanda zakiyiwa kazafi sai maigidan kuma
Ai maganin shi ke ne shi dake nuna tausaya maku tun farko yana fadan cewa wai ana sakaku aiki da yawa shu baya son hakana,
Hawaye ya gangaro wa Lami wace a tsorace ta juya zuwa dakinta, tana dan goge hawaye da bayan hannun ta,
Kallon rainin hankali Fatima tabi bayan Lami dashi tare da rakata da tsuki, mai sauti,
Sun dauki lokaci zaune a falo bayan shigar Lami wacs duk ta ja wani sura da adduan da ta sani a bakin ta ranan,
Fatima ta mike ta kwashi yaranta daya bayan daya zuwa cikin dakin bayan da ta kashe duk wani na,uran wuta dake falon,
Ta so ace ta shiga gurin Lami don tai mata kashedi a kan abinda tai mata yau,
Amma sai tace bari ta canzawa yaran kayan barci ta fito,
Aiko tana shiga sai ta sha,afa da hakan bayan ta gama shirya yaran, sai ta shiga bathroom don ta watsa ruwan wanka,
Ta debo ruwa ta watsa a jikin ta , ta goga sabulu a fuskan ta sai taji wani irin sauti kamar ana huci Fuuuuuuu,
Aida sauri ta bude idon ta tare da saurin mayar wa don yajin Sabulun da ya shiga mata ido,
Idan ba gizo idon ta yai mata ba zata iya cewa taga wani irin halittan abu tankar wani bakin maciji da kaho guda biyu a kai ido tankar an kada garwashin wuta,
Bata tsaya daukan towel, ba tafito daga cikin bath din tana kurma ihu,
Yaranta na saman gado suna barci ta rasa wace zata dauka daga cikin su don tsoro,
Taita maza ta koma bakin kofa ta jawo kofan bathroom din ta saka key daga baya,,
Hankalinta yai mummunan, tashi tabbas zancen Lami gaskiyane, ashe, da abu acikin gidan nan mai mugun kama haka,
Tausayin ta da na yaranta ne ya fara kamata a lokaci guda nadama tare da danasani ya rufe mata zuciyan ta,
Kallon yaran takeyi tana kallon kofa Allah ya taimaketa ta tada babban wace bata da nauyin barci sosai duk da ba wani bude ido tayi ba dakyau haka tafara jan tana sabe da dayan daga ita sai, daura gaba ajikinta,
Tun daga daki take kwadawa Lami mai aiki kira har zuwa tsakiyan falo,
Girman gidan bazai bari Lami taji wanan kiran ba don haka taja jiki har kofan dakin Lami din tana ta buga kofan,
Da sauri Lami wace dama a zaune take bakin gadonta a tsorace ta yo kofan dakin cikin tsoro,
Ganin yanayin Uwar dakinta yasa ta sanin cewa ba lafiya,
Ai bata tsaya jin mai Fatima zatace ba sai kawai tai hanyar fita kofan gidan tana ta yanka ihu tana fadin, da karfi,
Wayyo Allah Wayyo Allah yau mun shigesu Allah ka kawo muna dauki da kan ka ya Allah,
Bayanta Fatima tabi itama da ihun tana kokarin jan yarta guda kuma a kafadan ta,
Turus sukayi don ganin kofan shiga falongida saye da makulli, da kwado,
Sai lokacin ne ta tuna cewa ai gidan ma a kulle yake ashe,
Guri guda suka make daga su har Lami da yaran da suka bude ido don tsoro,
Ihu suke sun manne guri guda dukkan su su hudu ba mai tsayar da wani,
Maigadi wanda yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login