Showing 303001 words to 306000 words out of 388021 words

Chapter 102 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9551

zaune daga waje ya na jin irin yadda suke ihu cikin tashin hankali
Ya nufo kofan yana duka don ya tambaye su ko may ke faruwa,
Jin dukan kofan maigadi daga waje yasa su kara kwarma wani irin ihu acikin firgici,
Yau Fatima tayi nadama sosai a ratuwan ta inda take ta tunane duniya kala,kala a zuciyan ta ,
Maigadi kan dayaga cewa bazasu bude kofan ba gashi kuma basubar ihun ba,
Yasa shi rugawa da gudu zuwa gidan Lawal mijin Fattu wanda shine mai yawan zagayen su bayan tafiyan maigidan,
Daga Lawal har Baba Wadda wanda ke tare da Hamza su ka biyo bayan Lawal suma,
Suna kiran sunan, Fatima wace ta ke can tana ta kuka, da sharban majina ,
Yaranta duk sun yi yabe yabe da majina a jikin su,
Muryan Baba Wadda ne ta sheda cikin masu kiranta,
Yace mata ku bude kofan da kyat ta samu ta saita kanta ta iya bude kofan,,
Tanaganin kofan ya bude tai waje buta daga ita sai daurin zani agaba da diyanta a hannu tana ja,
Basu daina kuka ba da ihu da kaduwan jiki yayin da jikin su sairawa yakeyi don tsoro,
Maza suka shiga gidan suka duba ko ina babu alamar komai a cikin gidan,
Dole, aka kai, su gidan Lawal, don su samu natsuwa, sosai,
Tare da fatu da Maman biu suka zauna a falon gidan kowa, ya saka masu, ido,,
Duk mutanen dake gurin idon su akan su yanayin su yabawa mutanen tausayi,
Lawal ne ya ja yaran ajikin shi ya runguma su har suka danyi barci a cikin firgita,
Ranan a zaune suka kwana gaba dayan su yayin da aka kulle gidan tunda sun kasa bada bayanin abinda ya tsorata su,

****** ********** ******
Tun bayan wayan mu da Yaya Abubakar sai na fahinci cewa yadaina yawan kirana hakan yadan sakani cikin yar damuwa,
Amna kuma daga baya na sa kawa kai na hakkuri da dangana kawai,
Don bazan yarda namiji mai mata hudu ya,wahalar min da zuciyata ba abanza,

Barci na keyi mai nauyi amma ina magana acikin barcin, yayin da nake wani dan shure shure,
Mama Dije wace bata taba ganin nai irin wanan ba a cikin barci ta mika hannun ta a hankali tana tashina, tare da kiran sunana,
Abinda ya farka da malam daga gyangyadin dayakeyi a zaune gurin da yake sallah ke nan,
Har taga dakin Dije ya zo ya tsaya ya tambayan may ke faruwane,
Wani irin zufa ne sai tsiyaya yake min alokaci guda sai wani dan ajiyan zuciyar da na ke sauke wa a hankali,
May ya faru Meenatu, a hankali nadago kai na ina kallon malam da idanuwa na da suke nuna firgita a cikin sa,
Muryan malam ne ke cewa Dije kyaleta ku koma ku kwanta Allah ya tsare, mafarki ne ba wani abuba,
Saidai yanzu idan zaki kwanta sai ki juya ta hannun daman ki ki kore shedan daga hannun hagun ki,
Jiki a sanyaye na koma na kwanta tare da aiwatar da abinda malam yace nayi,
Ke Dije bude min kofan, nan , da sauri ta mike ta bude kofa malam ya ce miko min yaron nan,
Ta dauko yaron dake barci daga gefe ta mika mai nan ya shiga yi muna addu,oi ya tofa muna,
Mun ka koma muka kwanta saidai zuciya ta tab da tsoro wanan mafarkin da mu kayi,,
Al,amarin barci barawo ne kawai yasani samun yin wani barcin idan bashi babu yadda zan iya yin wani barci a ranan,
Da safe har da makara nayi saboda sai asuba barci ya dauke ni,
Nai wanka nai sallah tare da gyara jikina saidai kuma ina zaune ina karyawa a saman tabarma
Sai ga malam ya shigo dakin ganin yau har zuwa wanan lokacin bai fita ba kofar gida ba
Ya saka ni mamakin hakan, saboda nasan cewa, bai kai karfe shiddan safe a cikin gidan shi idan ba wani muhinmin abu ne ya faru ba,
Daga kofa naji yana cewa Meenatu kin tashi lafiya ko yaya makarin jikin naki,
Na mike don na fito zuwa waje ina cewa Alhamdullahi malam aidama sai yace dakata basai kin fada ba mafarkine akan yaro ko ?
A hankali na gyada mai kai alaman eh hakane sai naga yadan murmusa tare da dan girgiza kan sa cikin takaici,
Ya juya inda Mama Abu take yana cewa wanan al,amarin sai ankai inda ba,ason zuwa,
Yace Allah da Annabinsa sunyi gaskiya gurin fadar cewa ko aura wa 'ya'yan ku mata na gari haka su samawa yayan su uwaye na gari,
Yace Hajja ba mutumiyar arziki bace don sai ya gwada mata ko shi waye zata kama kan ta tunda har yayi yayi da ita ta daina saka mai jika a gaba amma ta kiya,
Zan gwada mata cewa komai sihirinta bazaiyi ba akan jinina insha Allahu,,
Yanzu Wadda ya bugo min waya yana sheda min cewa wanan dayar matan mai sunana da aka bari a gida,
Mama Dije tace wanan yar gidan zabarmawa ke nan ko ?
Malam yace wai daren jiya ba,abarsu sun kwana gidan ba ita da yan aiki,
Salati suka saka,a lokaci guda suna masu tafa hannayen su don mamaki,
Ido na zaro cikin tashin hankalin da ya baiyyana karara a fuskana, ina cewa Subbahanallahi
Sosai naji zancen a raina don abin da sai kuma tsoro da fargaba su ka kamani a lokaci guda,
Ka dafa ya kasance Fatima tai zargin cewa Yayana ne keda wani dodon sihiri a gidan shi,
Malam tsoho yace, dole ne a dauki mataki daga wanan karon don gaba ba mu,san may zai iya faruwa ba,
Ku saurara kwanan nan insha Allahu, zakuji abinda zai faru idan har tana da hannu acikin wanan al,amarin, kai koma waye sai asirin mai shi ya tonu,

****** ********** ******
Lawal bayan ya dawo massalaci haske ya haska sosai ya shigo gidan shi,
Ya leka dakin Fattu don yaga irin halin da Fatima take ciki
Ganin ta yayi daga ita har yaran da mai aiki sun samu barci don haka sai bai tashe ta ba don ta samu ta dan runtsa saboda kwana rayen da,sukayi,
Zuciyar shi fam cike da zargin indai har ba wanan mumunan abin bane ya dawo wanda ya tashi cutar da Sadiya a baya,
To amma idan har shine aikuwa sun karbi kafin wanan mugun abin cewa bazai kara shigo wa gidan ba,
Fita yayi yayin da ya samu su Baba Wadda suka shiga gidan a tare gaba dayan su,
Don su kara dubawa su gani idan abin baya gidan ko kuma yana nan,
Kaf sun kara zagaye ko ina na gidan babu Alamar komai a gidan,,
Sai a cikin bathroom din Fatima suka ga alaman jan cikin abu da dan maiko maiko,
Wanan ya tabbatar masu da cewa killa a na
ne ta ga wani abin don samun ruwan famfon da sukayi daren jiya yana ta tsiyaya, batare da an kashe ba,
Sai wajajen takwas na safe tafarka inda ta bude ido a hankali ta ganta a wani gidan na daban,
Hakan yasa ta saurin tuno da abinda ya faru a daren jiya da sauri ta kai zaune tana waigen yan diyan ta, ganin suna barcin su normal yasa ta sauke ajiyan zuciya,
Sai a lokacin ta dan waigo tana duban dakin a hankali don wanan ne karon na farko da ta,shigo gidan ma gaba dayan sa,
Fattu ce ta shigo dakin dauke da ture din kayan break fast tana cewa, har kin farka,
A hankali ta sauke, kafanta daga saman gadon Fattu din,
Tana cewa sannu da aiki don Allah ina ne bathroom din ku yake ina son in kewaya,
Wanka tayi tare da dauro alwala don tayi sallah, saboda ta makara yau, din don barcin fargaban da tayi,
Kayan sawan ta dana yaranta da Baba Wadda ya shigo mata da su tabi da kallon,
Inda ya samu guri daga gefen kujeran dakin ya zauna,
Yana cewa mai aiki tace wai ita zata bar gidan ne wucewa zata yi,
Sai lokacin Fatima ta dago jajjayen idanuwan ta tana cewa cikin wani murya mai ban tausayi,
Ko ni zan koma gida ne don gaskiya wanan gidan yafi karfin zama na,kuma,
Sai ga hawaye yana kokarin silalowa daga idanuwanta tace Baba Wadda bakaga abinda na gani a bathroom dina bane,
Lawal ya shigo dakin suka gaisa yake tambayan ta yaya yaran su ka kwana tace cikin taushin murya Alhamdullahi saiga hawaye sun kara sulalowa daga idanuwan ta,
Nan dai ta kwashe tun daga lokacin da Lami ta fada mata cewa tana jin yau gidan ya canza mata,
Har zuwa lokacin da ita kanta taji fucin a bu mai ban tsoro da kuma arba da tayi dashi, lokacin da tafara wanka yana kokarin zuwa gurin ta,
Duk sai suka saka salati yayin da Lawal ke cewa ashe wanan mugun abun bai mutu ba kenan duk kokarin da mukayi akan kada ya kara shigowa gidan nan,
Insha Allahu kai Baba Wadda da Hamza sai ku shirya mu tafi suleja gurin mutumin nan mu fada mai abinda ya faru,
Yanzu ku kwantar da hankaliku tunda Allah ya tsare bai kaiga tabakuba irin yadda yai wa ita,Sadiya,
Idanu a,waje tace cikin bude baki, Sadiya ma ta taba ganin shine ashe,?
Take shedan yace mata ai ajiyan maigidan ne indai har hakane,
Nadama da dana sani suka ziyarci zuciyar ta fuskanta cikin dan lokaci ya canza zuwa wani yanayi,
Ashe shine silan arzikin Abubakar da yake ta facali da naira har tabiyo, kuran shi,
Ganin yanayin ta ya sauya yasa sugane cewa ta shiga wani hali ke nan na tunane,
Baba Wadda ne ke cewa ai ita sadiya za,a ce abin su ne ya bisu,
Lawal ne ya katse shi da cewa ku tashi mu tafi kada rana yayi,
Don haka suka mike, zuwa garin suleja gurin wanan malamin da yai tabawa Sadiya taimako
Har ya fada masu cewa idan ba,ayi abinda yace ba zai iya sake dawo wa

****** ********** ******
Yinin ranan haka nayi shi a cikin mutuwan jiki saboda har zuwa rana, jiki na ba katfi,
Saboda mafarkin da nayi ya zauna min a zuciyata sosai, domin matar da banga fuskan ta ba saboda duhun gurin da take,
Amma sai hannu take ta mikomin wa sai nabata Babana, wanda ke goye abayana yana barci, a cikin mafarkin
Kaina na daga ina kallon dan yaron dake gefena yana barcin shi a cikin kayan sanyi na na jarirai,
Addu,a naiwa yaron tare da gyara mai kwanciyar shi, yayin da yai dan motsi da bakin shi tankar mai shan nono, ina cewa Allah ya raya munakai ta farkin addinin Isalama Baba na,
Daga waje nake jin zancen su Mama Sa,a kishiyar Mama Ladi wace gaba daya yan part din su Mama Ladi da Baba Buhari sun tafi sauke farali,
Nan part din mu Mama Sa,a take yawan zuwa gurin mu hira tana cewa tazo dauka maigidan ta ne,
Ina jin muryan ta da su Mama Abu suna dan zancen kus, kus cewa wai ashe, Hajja tasha alwashin cewa baza,a haihu ba acikin gidan Yaya Abubakar don,
Duk mahaifan macen da zaiyi amfani da ita Dodon ta zai dinga lashewa,
Amma sai gashi Meenatu ta buwayi ta da sherin ta ta yi ciki dashi har ta haihu,
Banji dadin jin irin wanan zancen shirkan da su keyi ba don gaskiya wanan ai hiran shirka ne kawai,
Ita ai bata isa ta hana ko tasa ayi abinda Allah bai tashi yi da mutum, ba,
Nan suke fada da cewa wai amma idan har mace ta rabu da shi Abubakar din zata iya samun haihuwa a wani gurin,
Ban san yadda akayi ba sai ji nayi bakina yana cewa, to ni yaya akayi na haihu da shi Mama Abu,
Gaba dayan su suka juyo gurin da nake tsayw a kofan dakin Dije suna kallona,
Yaron dake hannuna na mikawa Mama dije uwar daki na,
Mama Dije ce tace ke kin san irin abinda malam yayi a kan ku tun lokacin da kika shiga gidan nan,
Wallahi tun wanan lokacin tsaye yake kyam a kan ku Meenatu yana ta iya kokarin shi gurin ganin, Allah ya tsare ku daga sherin wanan azzaluman matar,
Shiru nayi ina sauraren irin bayanin da suke min akan irin cutan da Hajja takewa Anty Sadiya yar cikin ta da kuma Yaya Abubakar dan aminiyar ta,
Zancen su nada kamshin gaskiya don dai banyi ciki a gidan ba sa da muka tafi Niger Republic Allah ya bashi kyauta,
A take jikina yai sanyi badon komai ba sai tunawa danayi cewa kila wanan zancen ne maimaganin Suleja ya fada masu
Lokacin da suka tafi da ita har ta dawo gida tana ta fadan cewa anwa uwarta kazafi da sheri
Wanan zancen ya saka har ta kori Baba Ramatu wace ke tai maka mata da wasu abubuwan, a lokacin da take jinya
Tunawa nayi da girman irin halittan da naga yana fita adakin ranan da muka shiga,
Nan nake basu labarin yadda abin yafaru sai suke ce min ai shi mai sunan malam ya bugo waya yai masu bayanin komai dake faruwa a gidan,
Na sauke ajiyan zuciya tare da dan gyara tsayuwata ina mai bin lafiyan bango,,
Mama Sa,a tace ai a fara gane ta sai lokacin da takai matar Danta asibiti haihuwa,
Saita samu gawo tahaye sama tai zaune abin ta ga mata tana ta faman wahala hai huwa yaki zuwa,
Likitan ance wani mutumin zuru ne yana fitowa inda suke zazaune har da yaron nata mai matan,
Sai likitan yace to ai sai ki tashi a saman gawon da kika hau kika hana ta haihuwa tun dazun,
Tana yar borin kuya take cewa ni na hana a haihu da nayi may fa,
Ya nuna matagowon wani raggan zani da ta nade ta haye sama ta zauna yace walwale wanan tsuman mugani tana walwallewa matar dan nata na haihuwan yaronta,
Tun lokacin yaron nata ya hana ta shiga gidan shi yace idan yana son ganin ta shi zai zo,


ZEEE MAKAWA YELWA
[11/1, 9:51 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL WA,ALI


Fatima dole sai da Lawal ya tura mata Maman Biu ta dinga taya ta kwana a gidan, kuma a falo suke kwana gaba dayan su,
Baba Wadda da Baba Hamza suna taya su daga dakunan dake ta bayan part dina,
Har zuwa lokacin da Yaya Abubakar zai dawo gidan domin mai magani yace shi da kan shi zai shigo gidan ya yi wasu abubuwa da ya dace ayi, a gidan,
Sannu a hankali ana kwantar mata da hankali har ta yarda da cewa ba wani abu kuma agidan,
Sai dai a koda yaushe tana kokarin kafa, kafa da yaranta gudun kada wani abu ya samay su,
Bata yarda sam ta yi nisa da mutane don tsoron dake a ranta saboda ita har yanzu tunanen ta akan cewa Dodon na maigidane na sihiri,
Haka yasa bata sheda mashi cewa ga abinda ke faruwa dasu a gidan ba,
Uwar ta kuma da ta fada mata sai ta hauta da fada tana cewa so dai kawai take yi ta kashe auren ta ta dawo gida tazauna masu,
Kuma idan tai haka wallahi ta bata kunya tunda tasan irin wahalan da tasha kafin a samu ya amince da auren nata dashi,
Don dole badon taso ba ta bawa kanta hakkuri ta zauna har zuwa lokacin da maigidan zai dawo su san abin yi akai,
Bayan kwana biyu mahaifiyan ta ta kara bugo mata waya tana mai lalashin ta tare da bata hakkuri akan zaman a gidan mijin ta,,
Duk yadda taji kewan mijin ta daurewa tayi taba zuciyar ta hakkuri akan son da take ji na shi,,

****** ********** ******
Alhamdullahi, sun kammala ai,yukan su lafiya, har da ziyar sun karasa yi a gurare da dama,
Zaune yake a masaukin su yana tunane abu guda ke daure mai shine rashin jin kira daga matan shi da ya bari a gida,
Ita dai Meenatu yasan cewa sarkin jan aji ce idan bashi ya kirata ba bawai ta damu da kiran shi bane sai in ta so hakan,
Tun yana damuwa da rashi kiran na shi da bata damu dayi ba yanzu har ya saba da hakan sosai,
Sai dai kuma rashin jin kira daga Fatima ya matukar daure mashi kai don wanan ba halinta bane wace har yake gajiya da yawan kiran shi da takeyi ko yaushe,
Amma sai gashi yau kusan kwana biyar ke nan baikirata ba itama bata kirashi ba,
Sai dai idan yana son jin lafiyan su ya kira Lawal ya tambaye shi labarin lafiyan su sai ya fada mai,,
A daidai wanan lokacin ne da yake zaune yana wanan tunanen aka iyalin na shi wayar shi tai kara,
Wayan ta dauki ruri wanda hakan ya sa shi saurin daukan wayan, yana dubawa,
Mamaki yayi sosai da yaga ko wacece ke kiran shi a wanan lokacin, bayan yai received


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login