Showing 327001 words to 330000 words out of 388021 words

Chapter 110 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9527

Fatima da Salawatu, suna tare da Yaya a zaune suna magana akan wani program da akeyi,,
Ido a rufe nace Maman Aina, yaran basu dawo daga, school bane har yanzu, abinda duk ya dawo da hankalin su a gareni ke nan,lokaci guda,
Kafin taba ni amsa yarta karama ta fito tana magana da uwar, ido a waje na kara cewa cikin wani murya na tashin hankali,
Fatima acan ki bar min yar mutane yau ko na shiga uku a garin mutane, daga haka na juya zuwa hanyan, waje
Muryan shi naji cikin tsawa yana cewa, Ke Meenatu ya akayi ne wai cak na tsaya hankali a tashe nake cewa da zan tafi kitso ne na tafi har dakin ta nace yau Mijin Fattu baya gari don Allah idan zata dauko yara ta hada da Aisha ta sauko min don zan tafi gidan Anty saloon yini, ni da Fattu,,
Juyawa yayi inda Fatima taje zaune tana gyarawa yar ta igiyar riga yace ina yarinyar da tace ki dauko mata,
Batace komai ba sai dan jawo yarta zuwa jikin ta da tayi wani irin murya mai daka tsawa yace wai ba dake nake bane ina kikabar min yarinyar mutans nace,
Ganin yanayin shi ya canza a lokaci guda yasa ta dago kai tana kallon shi ido a cikin ido tace aini bance mata dama zan dauko yarinyar ba koda ta fadamin,
Ita may zai hana ta, tafi tadauko ta daga inda take saini zata aika take nufi ko may,
Mikewa yayi da karfi yana fadin innalillahi wa,ina alaihin rajju,un,
Daga haka ya mike nabi bayan shi inda a tare muka kai waje nan muka fada mota a tare a lokacin Baba Wadda suka shigo gidan a cikin hilux,
Bayan mun fita suke tambayan Ramatu da su Sadiya da suka fito a cikin tashin hankali,
Suna bin mu da kallon tashin hankalin yaya za ayi idan yarinya ta bace a cikin garin Abuja,
Ai suma bayan mu suka bi zuwa school din hankali a tashe
Gudu sosai Yaya Abubakar ke ta kwasa har Allah ya kaimu lafiya makarantan,
Tun daga nesa muka hango get din makarantan a rufe, hakan ya kara tayar muna da hankali,
Bayan mun samu guri mun Parker motar ne, sai, ya fita zuwa, duba get din dake da kwado daga waje ashema a bude gurin yake,
Mun samay ta kwance tana barci a dan gefen dakalin zaman maigadin,
Yana ganin mu ya fara fada yana cewa gaskiya baku kyautawa yarinyar nan ba sam ace tun karfe daya ba ,a zo daukan yarinya ba sai yanzu,
Hakkuri Yaya Abubakar yabawa maigadin yace ai matsala aka samu don bai gari shi wanda kuma yake dauko mu yai tafiya ne,
Bayan mu kama hanya gaba dayan mu har su Baba Wadda sai ajiyan zuciya yarinyar ke ta saukewa alaman tayi kuka harta gaji,
Sai lalashinta nakeyi inadan shashafata ina cewa Aisha yi hakkuri kin ji don Allah ki yi hakkuri ban san cewa ba a dauko ki ba,
Tace cikin murya mai rauni naga maman Aina zata dauke su nazo sai tace min wai najira za,a zo a daukeni ,wai su wani guri zasu, tafi,
Baice komai ba sai tukin motan yakeyi kawai batare da ya tanka muna ba sai dai duk abinda mukeyi yana kallon mu tankar baya ganin mu,
Ashe duk a hasale yake don dai ni ban fahinci yana acikin fushi bane a lokacin,
Mun kusa shiga uguwar mu yake ce min daga gobe Hamza ya fara koya maki mota,
Tau kawai na iya cewa batare da na kara furta wani abuba akai,
Mun iso mun samu su Ramatu a wajen gida har da Fattu da akafada masu, cewa ga abinda ke faruwa,
A folo muka samu su Sadiya sai dai Fatima ita bata gurin kowa sai, tambayan yadda akayi yakeyi,
Sama Yaya ya haye batare da ya kara tankawa kowa ba nima jan hannun yarinyar nayi na shiga da ita bathroom nai mata wanka,
Sai na hada mata tea maizafi nace tasha don zaifi warware mata hanjin ta saboda ta dade bata ci komai ba, alokacin,
Ina zaune a gefen ta Baba Ramatu tana goye da Amir yai barci a bayanta don har tai mai wanka ta shirya shi ko,

****** ********** ******
Yana aiki a saman system din shi ta turo kofa hannun ta dauke da dan karamin flasks na ruwan zafin da zai sha shayin shi,
Saman dan table din da ake ajewa ta a,za tana dan kokarin gyara, gurin da kyau taji muryan shi yana cewa, ki dauka ki fita dashi ban sha,
Juyawa tayi tana dan mai kallon cikin mamakin jin abinda ya fada saboda tasan ka,idan shine shan wanan shayin duk dare,
Ganin bata dauka ba ta tsaya tana kallon shi ya sashi cikin daga murya yana fadin baki ji bane,
Tace, ban taba ganin kayi fashin shan shayi bane sai yau, zakace na fita dashi,
Harara ya watsa mata yana cewa cikin bacin rai will you get,out in my side please,
Kana son jefa kanka a cikin zancen mu ke nan ko don nabar yarinya a makaranta shine zakai min irin wana wulakanci saboda na taba yar gwal ko,
Yace Lalai yau nagane zancen manyan mu da suka ce min ba tarbiyan mu guda da ku ba,
Zata bude baki tai ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????gana ya ce fita min daga daki tun muna m biyu please,
A yadda taga yanayin shi ya canza a lokaci guda tsaban bacin rai a tare dashi,yasata bin umurnin shi tabar mai dakin rai a bace itama,,
Yabi bayan ta da harara yana cewa mara mutunci kawai sai na koya maki wayau,
Yasan cewa zata iya dawowa don ita mace ce mai mugun naci ga na miji yasa shi mikewa yarufo kofan dakin nashi da sakata,
A falo ta wuce Salawatu wace ke zama biyu don ganin kwam kada a bata labari,
Fatima ta wuce zuwa sama gurin mai gidan don kwanciya,
A rufe ta samu dakin ta burda da nufin kofan ya bude amma sai, ta samu kofan a rufe,,
Nan ta fara dan murda kofan a hakali, duk da hakan kofan bai bude ba, sannu a hankali tafara dukan kofan da karfi,
Salawatu da Anty Sadiya suna kasa zaune a lokacin suna hira tare da su Baba Wadda dake cin abinci,
Karan dukan kofan da take yi ya dakatar da su suka tsaya suna sauraren ta,
Tankar wata mahaukaciya, irin yadda take dukan kofan, shiko daga ciki baima san cewa tanayi ba a lokacin saboda ear pace din dake a kunen shi yana sauraren kira,a, a lokacin,
Ganin bazai bude kofan ba gashi kuma ta riga da ta tozarta a gaban kishiyoyi yasa ta juyawa zuwa kasa da sauri zuciya na fisgan ta,
Wata zuciya tace mata je kawai ki samu yar iskan yarinyar nan Meenatu, da dukan tsiya,
Wata kuma nace mata, duk ta borewa kowa agidan don babu wanda baiji dadi ba,a ranshi,
Yanzu ace kamar ta yau Abubakar zaiwa irin wanan tozarcin haka a gaban kishiyoyin da take ganin cewa duk tafisu aji da tsari,
Don dai sadiya hafin uwaye ne ita kuma Salawatu lake mai tayi kamar kaska, a office, sai wanan yar karamar yar iskan da mugun tsohon nan ya hada shi da ita, ba dai so ko kadan a tsakanin su,
Tana saukowa daga saman Direct part dina tanufa a lokacin muna zaune ni da Ramatu da Aisha muna kallon hausa film ,
Babu sallama kawai muka ganta a hasale tafado muna daki kallon guda nai mata na fahinci yanayin ta kawai na watsar da ita,
Ke gurin ki nazo nai maki kashedi wallahi ni ke ba sa,ar yita bace nafada maki daga yau sai yau kada kikara yin sanafin abinda zai shiga tsakanina da mijina,
Wani wawan harara na wurga mata tare da jan tsuki na watsar a gefe guda,
Tace wallahi don kun san cewa duk kan ku wuhumahuhu ne don daku da babu ku duk dayane a gidan nan,
Nice masoyiyar shi ta ainihi badon sherin irin na iyayyen ku ba, da suka shiga tsakani suka raba mu tun farko,
Murmushi maganan ta ya sani tace aidole ki murmysa tunda kin san gaskiya na fada,
Wallahi nida kene a gidan nan tunda ki jefo kanki inda Allah bai kai ki ba
Nidai din da ba,a so nice din tashi, duk wani zzalunci da ha,inci da akayi don shiga tsakanina dashi bazaiyi tasiri ba , don kiji ,
Yarinya,ce nace, bazan dauka da motata ba don na isa sai kije kiyi shela gidan MANYA ki fada masu,,,
Kau taj mari daga bayan ta nda ke zaune kaina a duke saida na gigice don tsoro, saboda ban san shigowan shi ba,
Ashe su Baba Wadda da Salawatu suka kirashi a waya suke sheda mai cewa ga Fatima tashiga fitina a part dina,
Tayu inda yake
tsaye idanuwan ta yaka kawo ruwan hawaye tace cikin wani irin murya mai ban tausayi ni ka mara Abubakar saboda wanan yarinyar,
Yace anmare ki din an so what ?
Ta girgiza kai tace, min lailai ka gwada min cewa kai shanyayye ne
Ya kara watsa mata harara tare, da jan tsaki yace, mara hankali da imani kawai,
Tsaban bala,i da takara hangowa yasa ta juyawa zuwa dakin ta cikin kunan rai, ranta a bace hawaye yana zuba mata,
Idon ta a rufe ta shiga dakin ta ta jawo wayan ta takira, mahaifiyar ta,
Cikin kuka take fada mata abinda yafaru tsakanin ta da maigida da kuma, kishiyan ta,
Cikin wani irin tsawa mahaifiyan ta, ce amma, Fatima, baki da wayyo baki da hankali ashe haka,
Yarinya karama zaki saka acikin kishin ku kefa da bakin ki kike fada min cewa Yarinyar tana maki kokari da yara,
Shine ke yar su guda zaki barta ita kadai a makaranta a gati irin Abuja,
Ai sai kizo ga gidan nan mu zauna idan ya sakoki ba shikenan ba sai kizo kici abinda zaki ci a gidan,
Cikin kuka tace mama ya saya,wa kowar mu, motar ai don may ita bazata dauko Yarinya ba sai ni da ta raina,
Fati kanki daya kuwa, wai ashe bakin,ce wanan yarinyar da kuke zance a kanta yar kaunar maigidan ku bane,
Don ke baki da,wayyo shine zaki nuna mai cewa, ke baki kaunan yar yar,uwar shi,
Idan dai zaman gidan kikewa kwadiyi to ki dawo mu zauna ai gidan yana nan,
Nufin ki a haka zaki shawo kan shi kina nuna mai kiyayyan yan uwan shi a fili,
Kina zaman tayar mai da hankali a,cikin gidan shi a fili, yanzu ki fada min don Allah da kikai wayarinyar nan haka riban mai kikasamu akai diyar yar uwar haihuwan mijikince fa, ?
Tunda mahaifiyar nata tafara fada shiru tayi tana sauraren ta kawai, bata iya cewa komaiba tsawon lokaci,
Uwar tace yanzun ke idan da mai hankali ce bata hanyar wanan yaran zaki dinga samun alheiri daga gare shi ba amma hauka da rashin wayyo yasaka ki yin mahaukacin kishi,
Matakin da ya daukan maki ni yai min daidai wallahi idan kina da hankali sai ki gyara halaiyar ki na zaman takewan ki a gidan,,.
Indan ba hakaba wallahi kina kallo za,a kwace maki miji kizama yar rakiyan mata zuwa duniya kawai,
Sai yanzu tai magana acikin kuka tana cewa na shiga uku mama wallahi ni shi nake so mama shiyasa ban iya boye kishina akan kowa don shi,
Murmushi mahaifiyar nata tayi tana cewa Fati kenan, amma kin san cewa ai yana da mata har uku yanzu kuma kika yarda kika fada gidan hakana,
Mama duk da haka Abubakar yana sona har yanzu wallahi don da bai kaunata da ba zai aureni a matsayin bazawara ba ai,
Uwar tace sai kuma aka fada maki cewa sauran ma baya son su ko sai ke kadai,
Wallahi kin yi shirmay da yawa ashe ko dan nashi da aka haifa mai kishi baya bari ki kula da shi,
Cikin dan muryan kuka tace ni wallahi ma tunda aka haifi yaron har yau ban taba daukan shi ba,
Wani irin salati uwar ta saka, alokaci guda, tare da jefa mata ashar din zagi,
Fati yau na tabbatar da baki da wayyo wallahi rashi hankalin ki har yakai haka ashe ?
Tunda kika fara zancen auren nan na fadawa dan uwanki yace sam bai yarda ba don yasan haliki,
Amma na tauye shi tare da nuna mai, bacin, raina don dole ya yarda ya saka hannun shi aciki,
Har gobe korafin shi guda shi ne na dinga tsawata maki akan yaran nan ki kawar da kan ki akan su don a cikin gdan yawa kike,
Ya fada maki cewa kibi matan nan a sannu do kowace yana son abin shi musan man ita yar uwar ta shi,
Mamani yanzu yaya zanyi don wallahi yau Abubakar yadau zafi dani sosai don kin san shi da hakkuri amma wallahi sai da ya mareni don na zagi yan gidan su na MANYA,
Wani irin tsuki uwar tayi tana cewa lalai Fatima baki da hankali wallahi son kai ya saka maki haukan kishi,
Yanzu duk kin manta da irin wahalan da mu kasha kafin wanan abin ya tabbata,
Ko Dan uwan, ki ta yaya mu ka samu kan shi har ya yadda, da cewa keep shiga gidan,
Uwar ta kara cewa innalillahi, sai kiyi kokari ki kashe aure keep dawo gida mu zauna tare ba shi ke nan ba,
Kin samu mutum da iyalin shi kice da karfi da yaji sai kin watsa mai gida ko ta halin kaka kin zauna ke ka dai, daga ke sai diyan ki,
Barin tuna maki kada ki manta da zancen, da aka fada muna akan yarinyar nan idan har kin manta na tuna maki,
Fatima tace mama ban manta ba ai ni ban zauna ba don har yanzu ina aiki a kai,
Uwar tace to wallahi barin fada maki ki bi sannu don idan kika matsa zaki tsunci kanki a waje
Gaskiya Mama aiko dana shiga uku dan wallahi bazan ita rayuwa bada bukar ba,
Ni kawai bana son na bude ido naga wa yan nan kucakan matar nashi a cikin gidan nan a tare da mu,
Zaki ko wahala wallahi, don kin san yana da su kika ahi ga don haka sai ki zauna da su yadda suke,, tunda dai shi yana son abinshi hakana,,
Yanzu mama wai may ye abinyi, ne don wallahi na fada maki cewa wanan karon ya dau zafi da yawa,
Uwar tace ki bari zan fadawa dan uwanki sai ansa anbiyi kafin akai ko ina,
Da karfi tace a,a Mama don Allah kada ki fadawa Yaya Aliyu zancen nan,
Saboda kin san cewa, bazai yarda da ba zai iya cewa Bukar ya dauki mataki a kaina,
Haba na fada maki may zai sa ya fadi hakan a gaban shi za dai kisha fada kan nasani sosai wallahi,
Cikin marairai cewa tace mama dan Allah kada ki fada mashi don Allah ki bari zan gyara insha Allah,
Mahaifiyar tace ni yanzu abinda zan fada maki idan kin san cewa rashin mutumci zaki dinga yiwa maigidan ki wallahi ki bari don baza ki mayar dani tsuhuwar banza, don ki ji,
Gobe tun da safe insha Allahu zan kira layin wayan shi in bashi hakkuri akai in yaso ke kuma don, Allah kada ki fasa abin da kikeyi,,,,

****** ********** ******
Ranan da kaina na fita zuwa kai Aisha makaranta tare da Baba Wadda, da Hamza,
Daga can mu ka wuce zuwa gurin koyon mota, kamar yadda Yaya Abubakar ya umurce ni da nayi,
Ba fashi, kuwa don tun a ranan suka fara sakar min sitiyarin motar na fara dan ja a hankali,,
Suna kara gwada min yadda zan kara hannuna da taka burki da ribas,
Mun dan dauki lokaci muka dawo gida acikin nishadi don naji dadin wanan, koyan motan da akai min,,
Na samu Amir ya farka daga barci amma yana a hannun, Baba Ramatu tana bashi madara,
Wanka na shiga nadan yi inda nafito saye da dongon riga jar kala da ratsin blue a jikina sai igiyar rigar da na daure daga gefe guda,
Plat shoe's ne na zaman gida a kafana saboda sam bana yarda na fito daga part dina zuwa wani part babu takalma a kafana,
Ba don komai ba sai don gujewa abubuwa da dama da zasu iya faruwa,,
Yunwa nake ji don haka na shiga main kitchen din gidan don naga ko da akwai abinda zan iya ci ,
Kawai sai naji ina son nasha kunun koko da kosai mai zafi,
Ina fadan haka sai naga Baba Ramatu tai min wani kallo sai kuma ta dan fara dariya a ciki, ciki,
Ban damu da abinda take yi ba ni bukatana kawai shi ne, in samu in sha, abinda zuciya ke muradin samu a lokacin,
Aiko babu zaman lafiya don sai da na samu nasha shi sosai sanan hankalina ya kwanta,
Idan anty daga school Baba Hamza' ke zuwa ya dauko min yarinyar daga school ko ya kaita,
A cikin hakane har lokacin dawowa asibitin Mama Ladi yayi gashi kuma jikin nata ya dan motsa a lokacin,,
Muna zaune a falo lokacin da Anty Safiya ta bugo mashi waya tana sheda mai cewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login