Showing 336001 words to 339000 words out of 388021 words

Chapter 113 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9568

may je damun ki ne wai haka, saida na dan musguta kadan na gyara kwanciyana nake cewa zazzabine kawai ke damuna,
Ina Ramatu ta shiga ne ga yaron nan ko wanka ba aimai ba ga hannun Aisha ma na karbe shi a falo,
Cikin dan tausa murya nace Aisha Aisha tana ina ta kira min Ramatu a back yard,
Baice komai ba naga ya fita da yaro sagale a kafadan shi yana mai wasa,
Ramatu ce tashigo dakin cikin dan rudewa tana cewa Uwar daki bakya jin dadi kuma yanzu Alhaji ke fada min ina can muna gyaran gida,
Nace Ramatu don Allah yiwa yaran nan wanka ki basu abin karyawa su karya,
Tace to amma kema din aida kin tashi kin yi wankan ki samu abinda kikaci sai kisha magani ko ?
Kai kawai na iya gyada mata tare da dan juyawa na gyara kwanciya na,
Daga haka barci ya kara daukana bayan Ramatu tadawo dakin taga irin yanayin danake barci sai na bata tausayi, don duk wani yanayi na jin jiki ya baiyyana min,
Na farka tare da jin yuwa bathroom na shiga, nai wanka tare da dauro alwala wanan dabi,a nane yin alwala bayan wanka,
Na idar da sallah daga zaune nagyara jikina inda namike tsab zuwa gaban mirror ba wani kwalliya nayi ba mai kawai na shafa na zura wata doguwar rigata mai yar guntuwar hannuwa ta gaban shi da fadi,
Gyalen kayan na tsuke kaina a cikin sa tare da, dan shafa mai a bakina,
Yaya Abubakar ne dakin tabayana naji ya rungumay ni a hankali,
Abinda ya haddasa min lumshe idanuwa na ke nan a hankali,
A sake nace a hankali Yaya love ina kwana Saida ya dan rugumoni sosai zuwa jikin shi yace a hankali daidai saitin kunnuwana yace,
Sweet sister jikin ki da zafi mana ko har yanzu zazzabin ne,
Wani irin amaine yazo min a daidai lokacin da nake kokarin bude bakina na bashi amsa,,
Kokarin jaye jikina nakeyi daga gare shi amma ya rikeni tamau,
Jin ina kakarin amai yasa shi sakina da gudu na fada bathroom dina,
Amai sosai na ke ji amma sai kumfa kawai nake zubuwa don babu komai a cikina,
Yana zaune a saman gafon dakina har na fito ina cewa wassh Allah na, o,o wai, na fada gefen gadon a hankali tare da dan noke kaina a filo,
Meenatu naji ya ambaci sunana yana cewa cikin dan bubuga kafan shi a hankali saman ties din dakin,
Saka hijab dinki muje asibiti yanzun nan ga Lawal nan zai fita da mota,
Sai a lokacin na dan dago kaina a wahalce nace basai naje asibiti ba ai zai bari insha Allah,
Fuska a murtuke yace min ki tashi ki saka hijab din ki nace maki,
Mikewa nayi daga kwancen da nake ina cewa, Yaya aman zai bari ai a cikin yar shagwaba,
Yace kina son sai nayi fushi zaki tashi ko ,
Hannu nasa nadan dafashi namike daga zaune da kyau ina cewa zan sha tea yunwa nake ji, tukun,
Mikewa yayi don kiran Ramatu a falo yasamu mutanen gidan kamar wasu masu jiran fitina,
Sadiya ce kawai bata a cikin su amma su duk suna zaune dagani masifa suke ji,
Bai ko kalli inda suke ba ya kecewa Lami ta kira mai Ramatu a waje,,,
A lokacin ne Lawal ya shigo gidan yana masu ina kwana Yaya Abubakar ke ce mai, kabari ta yi breakfast don ba komai a cikin ta ,
Kallon, kallo suka fara yi a tsakanin su, suna mamaki da tuhuman ko may ke faruwa,
Cikin son jin kwam Salawatu ke cewa lafiya dai ko dakin Maman Amir,
Dan kallo ta yayi kamar zaiyi magana, sai kuma ya kawar da kai ba tare da tace uffan ba,
Inda ya barni zaune da farko a nan ya samayni zaune Ramatu tana kada min tea,
Yadda nasha tea din haka na amayar dashi atake kuma na fara dan fita hayacina a hankali,
Da sauri, sauri yafara kiran sunana acikin dan firgici,
Da sauri ya kamoni inda a daidai falon gidan yake cewa Lawal, tayar da mota mutafi,
Cirko, cirko su kayi, suna kallon mu yadda duk Yaya Abubakar ya rude da yadda na koma,
Saida su kaji cewa mun wuce, asibitin Fatima tafara cewa tau wani sabon kuma yanzu don kawai maigidan hankalinshi ya koma agareta shine takirkiro ciwon karya,
Salawtu ta tafa hannayen tana, cewa ai, zakiga abu agun wanan yarinyar small girl da ita amma ta, iya abin manyan mata,
Wuri ta samu inji Fatima, tana cewa, wallahi, sai nayi maganin shegiyar yarinyar nan yar iska kawai muna fuka,
Jifa yadda tawani langabe kanta a kafadan shi ita a dole mai,wayyo munafukan yarinya kawai,
A lokacin Sadiya ta shigo falon da alama abu zata dauka tana da daura gaba na zani da dogon rigar barci a jikin ta,
Batare da tace masu uffan ba, , zata shige taji suna cewa towai ma may yasamayta hakane adaren jiya lafiya kalau fa suka shigo gidan nan a tare,
Kitchen ta shiga tafito dauke da goran ruwa tana cewa har yau zancen fitan su Meenatu din ne,
Ina a sibiti suke ance jikin Mama ne ba dadi jiyan ma duk ta bata jiki sauda ita Meenat tai mata wanka,
Kin,gani ko, ai in tace iyeiyene gashi nan yau, tajawa kanta ciwo,
Waye ba lafiya kuma Sadiyace ke tambaya a dakile, Salawatu tace Meenatu mana,
Meenatu kuma may ya samay ta yau din ke dai fadi,
Yanzu akafito da ita a kafada wai za,a asibiti ta kwana tana amai,
Amai Sadiya ta tambaya a gagauce amai fa kedai wani irin dassss taji azuciyan ta kada dai ace wanan yarinyar wani ciki ne kuma ta kara samu, again,
A take yanayin ta ya canza sai cewa tayi a fili watan danta nawa yanzu wai,
Fatima tace what ke kada dai ace ciki yarinyar nan ta kara samu,
Aiko da abin ya zama zalama Ciki da wanan dan karamin yaron haka,
Daga haka Sadiya ta wuce tana cewa, Allah ya kyauta amna zuciyan ta tana mai tir da halin uwar ta koda yake idan tai imani da Allah kila dama ba zata haihun ba uwar ta Hajja dai ce ta saka nata ruwan a ciki,
Ramatu tafito da Amir goye a bayan ta yana barci, da alama ya dan jima yana barcin, a bayan ta,
Gaba dayan su suka watso mata idanuwan su akai,
Salawatu ce cikin muryanta hausa gwarigwari take cewa, Ayya Ramatu yaron yana barci ne ko baida lafiyane,
Ramatu ta fahinci may suke nufi wani gulma,ne suke son yi don haka tana cewa kalau yake kawai ta shige abinta, fuuu,

****** ********** ******
Kwance nake drip din ruwa tan shiga jikina daga kafan hannuwana a hankali,
Yaya Abubakar yana tsaye a gefe Maman Biu tana rike da hannuwan nawa,
Likita ya shigo dakin da farar takarda da a hannun shi yana dan dubawa,
Yace cikin gyara farar glass din dake idon shi, yana may mika wa Yaya Abubakar hannu,
Yace, bata farka ba har yanzu suka amsa mai da cewa eh. Yace saboda alluran nan na amai da akai matane yasata wanan barcin ,
Amma shi lamarin ciki hakan yakan zowa wasu da wahala sai zuwa karshe a samu sauki,
Jun ya ambaci ciki yasa Yaya Abubakar saurin kallon likita acikin mamaki,,
Likitan yace, hakane maigida ciki ne na Sati shidda a jikin ta shike bata wahala haka,
A sake ya juya yana mai kallona cikin tausayawa yana kallon yadda nake sauke numfashi a hankali,
Maman Biu dake gefe rike da hannuna tace haba nima nayi tunanen wanan abin ko cikine,
Shiru Yaya Abubakar yayi, na dan wani lokaci yana mai kura min ido kawai, batare da ya kifta ba,
Wani irin so da kauna nane ya ke shigan shi a lokacin ga tausayi ga kuma murna da yakeyi min a lokaci guda,
Har kwana biyu ina asibiti inda nake samun kulla daga maigyaya da kuma maman biu da Antyn Saloon,
Daga bakin anty Saloon nake jin cewa ciki ne ga jikina inda hankalina yai mugun tashi sosai alokaci guda,
Sai nake ganin cewa zan rasa Amir ke nan tunda yasha ciki a wanan stage din, haka,
Sai addu,a nake raina cewa Allah yasa cikin ya bare kowa ma ya huta, da shi don ban san yadda zanyi daciki ba ga yaro karami haka wata takwas yake batun shiga
Yau ma kamar kullun kowana barci niko ina kwace ina tunane barci ya ki zuwa min,
A hankali kuka yadan fara zomin ina tunanen yadda zan zauna da matan gidan mu ga fitina ga goyo ga ciki, kuma,
Muryan Mama Biu naji tana cewa haba Meenatu kina son kinunawa Allah cewa baki godewa Allah irin baiwa da kyautar da yai maki bane,
Addu,a zakiyi kuma ki godewa Allah dayai maki wanan baiwar don baiwace daba kowace mace ke samun hakan ba a rayuwan ta,
Abin alfahari saidai mata basu ganewa cewa wanan ai wani gatane Allah kewa mace,
Tayi haihuwan ta alokaci guda ta kare yaranta su taso kan su guda gwanin sha,awa
Yanayin maganan Maman Biu ya saka zuciyana yin sanyi inda nadan fara goge hawayen dake fito min a hankali da bayan hannuna,
Muryan Anty Saloon wace nake zaton barci takeyi tace idan zaki zage kikula da dan ki da kuma cikin dake jikin ki dake kan ki har mijiki da ya fi maki alheri
Don yanzu haka da zaran kishiyoyin ki sun samu labari zakiga sun tayar da hankalin su zasu ce ai kece kawai matar so, ga maigidan ku
Tsawon wani lokaci suna kara bani hasken rayuwa ina sauraren su a hankali,
Nace ni yaron nan ke bani tausayi wallahi sukace ba wani tausayi ki fara bashi multivitamin madu kyau masu gina jiki nikuma zan samo mak nq gargajiya masu kyau sai adinga bashi a hankali har zuwa in da za,a yaye shi,
Ajiyan zuciya nayi don jin na samu mafita akan Amir addua kawai ya rage min yanzu akan al,amarin,

Washegari aka sallamay ni na koma gida da saidai har zuwa lokacin ba, da karfin jiki don haka muka zauna tare da maman Biu,
A lokacin ba fita nake sosai ba amma duk da haka da girki ya zagayo a kaina dole nakarba don maigidan yace nayi,
Badon komai ba nasan don ya samu kebawa danine muyi zancen, ni dashi,
A hankalina shirya jiki ba kwari nasab Amur akadata muka hau sama zuwa turaka,
Nasamay shi zaune abakin gado saye da bathrobe din shi a tunanen shi bazan shigo dakin ba,
Yana ganin mu yamaida kallon shi a garmu, yana maidan jijiga kan shi,
Na zagaya na shimfide yaron sanan nadawo kusa da yayana na zauna a hankali,
Nan ya bude baki da nufin magana kenan aka kira layin wayan shi inda yai shiru yana kallon wayan nashi
Ganin haka yasani dan kwantawa a hankali kafin yakare wayan nadhi,



ZEEE MAKAWA YELWA
[11/24, 10:39 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH DHUL JALAL WAL lKRAM,,, ,,,,,,,,,,,,,

JUMMA,AT MUBARAK TO ALL MUSLIMS UMAH IN THE WORLD MAY ALLAH BE OUR NEEDS PROVIDES ALLAHUMA AMEEN YA ALLAH=?O?=?O?


Idona a rufe suke har zuwa lokacin da yafara karba, wayan ahankali kaman wanda baya son naji may yake fadi a wayan,
Idon nawa a rufe tankar mai barci nake jin yana bada amsa da cewa
Yanzu dare yayi amma tunda jiwane kawai maishi ta bari har zuwa safe sai su tafi asibiti,,
Hakan yasani gabe cewa daya daga cikin matan shine yake waya da ita, mai shi tana bukatan ya kai ta asibiti ne a lokacin,
Ban san may tace ba sai naji a cikin daga murya, yana cewa na fada maki dare yayi yanzu saboda juwa babu inda zan tafi yanzu,
Wayan dai ba,a kareshi da dadin rai ba don, da fada aka karasa shi, don yace bazai fito ko ina ba,
Ina dunkule guri guda saboda irin yanayin da nake jin jikina ba kwari,
Hannuwan shi yamika daidai wuya na yadan shafa a hankali inda jikina yai dan dumi, alaman akwai zazzabi a tare dani,
May ke damun ki yanzu kuma saida na dan gyara kwanciya na a hankali sanan, nacd bakomai. Ok kawai yace naga ya mike yaje gaban mirror,
Yadauki dan lokaci tsaye a faban mirror hannu shi rungumay, a kirjin shi, da alaman tunanen wani abu yake a lokacin,
A hankali ya dawo ya zauna a bank n gado tare da dan duban wayan shi dake gefe guda,,
Dan rage muryana nayi ina cewa waye baida lafiya ne wai,
A takaice yace min Fatima ce fita batun ta magana take nema zanyi maganin ta,
Cikin murya ta mara lafiya nake cewa, ai da ka dubata kaga ko may ke damun ta cikin daren nan,
Gyara kwanciyan shi yayi tare da fara karanto addu,an kwanciya a cikin yar murya, yashafa a jikin shi da namu,
Ya juya ya rugumoni izuwa jikin shi yana sauke ajiyan zuciya kawai,
Idanuwana na gyara lumshewa, tare da jin wani son mijina a raina, inda na kara makewa a cikin jikin shi daga haka barci ya dauke mu

****** ********** ******
Na dauki wani lokaci ban sauko ba daga sama saboda irin yadda nake jin jikina,
Don nasan cewa ko na fito ba wani abinda zanyi hakane yasakani kwanciyana kawai,
Ramatu ce mai min komai daga abincin da ake kaiwa su mama har wanda zan bawa maigida,
Ramatu wace ke kasa itace ke ganin darama a gurin matan gidan don wanan tafito ta wuce fuuu, wanan ma tazo fuuu da ita,
Sai da Amir ya fara kukan neman abinci na tashi na sauko a lokacin har yaya yai ma yaron wanka ya shirya mn shi tsab da kayan shi dake cikin baby bag din mu,
A yayin da zan fito daga part din na Yaya Abubakar a falo na samu su Salawatu, kamar masu yin wani abu,
Wanan ba wani bakon al,amari bane daga halaiyyan su domin inda sabo ai na saba ko,
A daidai tsakiyan falon gida, naji muryan Salawatu tana cewa wai wani sabon salo kuma,
Wanan ai zalunci ne ace wai kirikiri ake nuna wa mutane fifiko ko dan uwan ka baida lafiya ba a kula da mutum,,
Tankar ban fahince ta ba nasakai zuwa dakina don banda lokacin ta ni,
Ina shiga Ramatu ta samay tana min sannu ya jiki,
Na bude baki da nufin magana, kenan aka turo kofan dakina,
Gaba dayan mu muka maida duban mu ga kofan dakin don ganin ko waye mai shigowa
Ya Abubakar ne dauke da Amir a kafadan shi yana cewa Ramatu a bashi madara yasha don Allah,
Don kada ya damu Maman nashi da tsotso tana fama da kan ta ne ita,
Dan guntun murmusawa nayi kawai ba tare da nace mai komai ba,
Yacewa Ramatu don Allah itama a bata abinda zatayi break tasha maganin,ta,
Har zai fita sai ya ja ya tsaya yana cewa au don Allah kibawa Big man maganin sa kamar yadda suke, a rubuce,
Ta kara amsa da tau sabbaynil yanzunan insha Allahu zanbashi,
Bin shi nayi da kallo cike da jin tausayi, shin ganin irin yadda duk ya shiga damu a kan mu,,
Inda Amir yake zaune a gefena na kalla sai yaron kuma ya bani tausayi sosai,
Nono yake bukata don haka daga kwance na bude mai yafara tsotsawa a hankali ya saida na tabbatar da cewa ya tsoho sosai nacewa Ramatu ta tafi dashi ta kara mai da madaran shi,
Ina daga kwance nake mamakin yadda akayi babu wace ta iya yi min sannu, daga cikin su har izuwa yanzu dama Sadiya takan ce a,a ki mike fa kodai kina taya, mamanki ciwo ne,
Murmushi kawai na keyi, idan tace min haka sai takan dan yi wa Amir wasa ta wuce,,

****** ********** ******
Zai fita daga gidan ne yaji muryan Fatima tana cewa, aini wanan mutumin ya bani mamaki sosai wallahi,
Duk da na samu dubara mai karfi don na rama amma wai mutumin ga shine yai kemay may yafita batuna yace bazai fito ba wai dare yayi a lokacin,
Salawatu tace ai na fada maki cewa, bazai fito ba kika dauka magana tace kawai,
Kai kawai ya girgiza tare da ficewa gidan batare da sungan shi ba daga inda suke zaune suna hiran,
Asibiti ya wuce direct gurin Mama don ya duba su da kwana duk da tana sa ran cewa, za,a sallamay ta kwanan nan insha Allah,
Ya samu Mama a zaune bakin gadon asibitin tana dan shan lemon da aka wade mata a hankali,
Yana shigowa dakin suka gausa inda yai dan mata tambayoyi akan jikin nata tace da sauki,
Abin mamaki sai yaji muryan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login