Showing 345001 words to 348000 words out of 388021 words

Chapter 116 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9570

fadin Alhamdullahi,
Kujera ya jawo ya zauna tare da,dan fuskan ta na yana min kallona cikin mamaki, yace
Ashe wai yau za,a yaye Amir ne, nace cikin wata irin kasalaliyar murya nima Mama Dije ce da za su wuce zuwa gida tace nabata shi dashi zasu tafi,
A sanyaye naji yace Allah ya kayauta to, Allah ya raya muna ahi rayuwa irin na addinin musulunci,
Ban san lokacin da hawayen tausayin kaina da kuma tausayin yaro karami kaman Amir a rabashi da mahaifiyar shi da kuma abincin shi,
Daga inda yake zaune ji yayi tankar ya rugumoni ya lalashe ni,
Saboda dan kukan da yaji ina saukewa gwann ban tausayi,
Idon shi ya dan gimtse guri guda, don wani irin radadi yake ji can kasan ran shi,
A hankali yadan mika hannun shi ya kamo hannuna ya hade a cikin nashi,
Ya ce kiyi hakuri Meenat, nasan kin yi karama da wanan irin laluran amma idan kinyi hakkuri sai abin ya wuce don jarrabawane daga Allah,
A hankali na dan lunshe idanuwa na a daudai lokacin da naji hannayen mu su hade guri guda,
A hankali muka sauke numfashimu a t?re irin yanayin da kowan mu ke ji yasani dan daga idona na dube shi,
Ya wani ramay sosai dashi, yayi baki ya koma mara kuzari kamar da can baya,
A haka mu kai shiru kowa da irin abinda yake sakawa a zuciyar ba komai bane banda tausayin junan mu da muke ji a lokacin,
Can naji ya wani nisawa ya dago idanuwan shi da suka canza kala yana cewa, da kyat zamu tafi gida Meenat saboda naje gurin bakin mu na gida don naga kowa ya samu guri kwana,
A hankali na bude bakina nace ai kowa nai mashi masauki, don na saka Ramatu da ta gyara madu guri,
Har zai mike still hannun shi yana sakale da nawa nace mai a hankali ka ci abinci kuwa Yayana,
Ya dan murmusa yace ban jin cin komai ne amma zan sai abu mai dan ruwa nasha kafin na kwanta,
Yaya ka daure dan Allah ka dinga cin abinci please, Iam Ok now,
Ya amsa a kasale da cewa tau Meenat insha Allah zanci idan na koma gida,,
Yana a tsaye amma bai saki hannuwan nawa ba nadan dago na kalle shi muka hada ido
Take naji wani irin faduwan gaba ya kamani alaman kuka nagani a idanuwan Yaya Abubakar,
Na zare hannuwana daga nashi cikin karfin hali nake ce mai saida safe,


ZEEE MAKAWA YELWA
[12/2, 10:56 PM] MAKAWA:=?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL JAAMI

Alhamdullahi domin zuwan yan uwana ya kara min samun kwanciyar hakali
Inda likita ya baiyana kara samun lafiya na acikin yan kwana kin nan,
Anty Safiya ta nuna fatin cikin ta sosai ga irin rikon da yar ta tasamu a gareni,
Wanda suke cewa abinda suka gani duk daba,a gida nake zaune ba ya gamsar dasu domin yarinyar duk abinda zata fada sai dai tace Mamana,
Amma gashi su Mama Ladi da Anty Mariya, sun nuna cewa yarinyar bata a cikin walwala sosai,
Amma sai gashi sunzo sun ga sabanin hakan don sun tabbatar da irin rikon da nakewa yarinyar,
Anty Samira tace wallahi anty mariya bata da halin alheri don may mutum zai k fadan gaskiya abinda ya gani, don sheri kawai,
Sun zagaya gidan abokan arziki sun gaisa dasu ta ko ina tare da dan zaga yawa gari,,
Inda Fattu ce tai masu jagoran wanan fitan sun dan sayo abubuwan bukatun su da suke so,
Kwana biyu suka so suyi amma sai yaya Abubakar yace su dakata har zuwa ranan Thursday ko Friday su tafi,
Kamar kullun sunzo ziyar na mun yini a tare da zasu tafine tafiyan nasu yai daidai da shigowan yaya Abubakar inda yake cewa Yaya Mustapha ya karbi key din motan shi ya kaisu gida,
Yaya Mustapha yace, ba zai iya gane gida ba kuma ba wai ya iya tukin mota bane sosai,
Baba Waddane ya shigo aka bashi key da yakai su ya bawa Lawal, mijin Fattu key ya dawo, ya dauke shi,
Bayan tafiyan su na zauna dagani sai Yayana a dakin wanda akidar shi ce, duk dare zai zo ya zauna dani har zuwa wani lokaci,
Yau ma kamar kullun bayan tafiyan yan uwan mu , muna zaune ni dashi yana ta aiki a cikin system din shi dake a gaban shi,
Nace Yaya ya amsa da Umm,ummm,
Nace yanzu may zamu sallami su Yaya dashi idan zasu koma, tunda shi yaya Mustapha bai taba zuwa nan ba sai wanan karon,,
Bai bani amsa ba nasan da wanan halin nashi bawai bai jini bane kawai dai time din bada amsa na baiyi bane,
Kusan minti goma sha naji ya dago kai yace, ai, may kike son abasu ke ?
Gyara kwanciya nayi yayin da nai dan filo da gefen jikin shi ,
Nace ni dai gaskiya na ga yakamata kasamu alheri mai dan tsoka ka taimakawa Yayyen mu maza,
Bai tanka min ba sai ci gaba da yayi da aiyukan gaban shi, a cikin system din shi,
Can naji yace Meena na amsa da Naam Yayana, ?
Yace motata wace Hamza ya buga kwana tunda aka gyarata ban shiga ina ga sai abawa Mustapha ita ko,
Ai ban san lokacin da nai wani cakumo mai wuya ba na rugumo shi zuwa jikina ina cewa wayyo yayana nakaina,
Allah ya kara rufa maka asiri,
Ido naga ya kura min kaman mai mamaki har na dan tsargu, sai naji yace Meenatu kin manta kin bed rest ne wanan irin ihun haka dan Allah,
Nace wallahi Yaya ban san irin farin cikin da nake ji ba ne yau,
Yaya Mustapha da mota kasan cewa shi dan gaye ne na sosai dama,
Sai naji yace to su Salis fa da sauran su, nace gaskiya ya kamata su ma aduba al,amarin ,
Nace a kage yaya su Anty Safiya fa, may za,a basu, su ?
Yace matane su kudi mana su gyara dakunan su ko,
O ,o Yayana mun gode wallahi Allah ya saka ma da alheri ,
Murmushi kawai naji ya dan yi ciki ciki batare da yai magana ba,
Da farin ciki na kwana a ranan saboda ina matukar jin dadin ace Yaya Abubakar ya taimaki mutanen gida,
Hakan yasa shi gane cewa wanan daya daga cikin halina ne in dai ji cewa ya kyautatawa yan uwan mu sai yaga ina jin dadi da farin ciki, hakan,
Murna a gurin Yaya Mustapha ba zan iya musultawa ba don abinda bai taba zato bane ya faru,
Yan uwan mu sun dawo a cikin farin ciki inda suke ta murna tare da fadan irin cigaban da yaya yasamu,

****** ********** ******
Abin duniya ya kai mata ko ina yanzu don bata taba zaton cewa zai iya shere ta har tsawon hakan ba,
Don haka ta yanke shawaran kawai ta shirya ta koma dakin ta kai tsaye badon komai ba sai don tserar da mutuncin ta gurin yan uwa da makitan da suka fara mata shagube, akan zamanta gida,,
Ba bata lokaci tafara shirin komawa akin ta batare da kowa yasan da hakan ba,
Mahaifiyar ta ce kawai ke da wan,nan labarin don basu fada wa kowa zancen komawan nata ba,
Saboda basu san yadda alamarin zai kaya acan ba,,
Ana fitowa daga sallah asubahi driver motan da tai shata yazo suka shiga daga ita sai yan diyan ta da tarkacen kayan ta,
Alhamdullahi sun iso lafiya inda suka samu mutanen gidan lafiya,
Isowan su yayi daidai da dawowan, Salawatu daga unguwa ,
Salawatu yanzu sai harkokin ta takeyi don gida ya zama nata sai yadda tayi aciki don Sadiya ita babu abinda ya damay ta da zancen wani gyara can,
Acikin mamaki ta ke mata kallon kwam don sam bata tsan maci zuwan Fatima a wanan lokacin,
Salawatu tawani dan yi kiba dama gata doguwar mace sai tai wani bajewa kawai,,
Tana kokarin parking din mota idon ta akan Fatima wace ke kokarin sauke kayan ta daga cikin mota da suka zo da ita,
Tafito gidan hajiya harka mai sayar da kayan mata yanzu Salawtu sai kokarin ganin ta gyara komai nata don ta samu shiga a gurin Ogan ta, ita kadai,
Daidai hanyar shiga cikin gida, din Salawatu take tsaye fuskan ta kawai zai nuwa mutum cewa tayi bakin ciki sosai da dawowan Fatima,
Kiba mu guri mu shige don Allah Fatima ce ke fadawa Salawatu hakan,
Daga gefe kadan ta dan shige inda fatima ta shige daga ciki da yaran ta,
Kallon mamakin irin yadda duk ta canza a lokaci guda tankar ba ita ba, ce Fatiman da ta sani a baya,
Duk wanda ke agidan sai kallon mamaki ya kewa Fatima wace bata damu da kallon da ake mata ba,
Tsab ta gyara part dinta tare da saka kamshi kamar yadda ta saba yi a baya,
Salawatu wace abin duniya yakai mata ko ina arayuwan ta
Sam bata taba tsamanin cewan Fatima, zata dawo gidan ba a wanan lokacin, amma sai gashi da rana tsaka ta dawo gidan ba zato ba tsanmani ga kowa,
Ramatu ce tafara ganin cikin dake manne a jikin Fatima amma sai taja bakinta tai shiru don gudun kada ta taso,
Shigowan Yaya Abubakar wanda yazo duba lafiyan jikina da sauran yan uwa al,umman Annabi,
Don dabiar shi ce idan yashigo sai ya gayar da sauran makwabtan dake a kusa dani, kafin ya karaso guri na,
Ya shigo yana saye da shadda mai ruwan light blue dinkin ba wani mai tsawo ba iya gwiwa kawai take mashi, haka ma dinkin hannuwan rigar iya gwiwa hannu ta tsaya mai,,
Hannun shi guda saye a cikin aljihun shi yana tafe cikin kwarjinin shi da Allah ya bashi,
Ina daga zaune a bakin gado Gwago Habbi tana wade min lemon da nace zan sha,
Sun gaisa da yan tsofin suka bar dakin don ganin cewa ya dace su bamu guri a lokacin,
Sannu da zuwa nai mashi a daidai lokacin da yake kokarin jawo farar kujerar roban dake gefe guda a cikin dakin,
Wayar shi tai kara wanda hakan wani babban al,adace ta ko yaushe busy yake gurin waya ko receiving din call,
Salawatu ce a layin sun gaisa take ce mai, Sweet Oga a she kasan cewa Fatima zasu dawo yai shine baka fada muna ba,
Cikin dan daga murya yace Fatima, wace Fatima wai please,
Ta bashi amsa da cewa, Fatiman ka dai ta nan gidan wace ka sani mana,
Jin abinda yake cewa ya sani dan dago kaina ina duban shi a hankali inda nake dan jin muryan ta daga cikin wayan tana magana a hasale, rai bace,
Bai bata amsa ba saima kashe wayan da yake sauraren ta da yayi,
A cikin sake fuska da nuna jin dadin jin sun dawo nake cewa Fatima ta dawo ne she, ?
Fuska a daure ya dan dago yana daga min kai alaman eh
Yace cikin wata muryan bacin rai nima yanzu nake samun labari a gurin Salawa,
Azuciya ta na ce yar kyashem ke nan ta man,ne da sarki, har ta kai karshen zance ko,
Amma gaskiya Salawatu munafukace ina ruwan ta da zancen kishiya,
Ganin irin yanayin da fuskan shi ya nuna ya sani dan yin shiru nace a hankali,
To may ye don Fatima ta dawo kuma na wani bugo maka waya dama Fatima ba matar ka bace, da don ta dawo shine wani sabon zance kuma,
Ko dama bata bukatan dawowan ta gidan ne wai da har zata bugo maka waya,,
Da wani irin fuska na ga ya kalloni, cikin bacin rai yace "Ke,
Ban,son zancen banza haka kawai zata dawo min gida batare da izini na ba may ta mayar dani da zata kwaso kayan ta ta dawo min gida haka na,
Shiru nayi kamar bazan ce mai kala ba sai zuwa yan wasu mintina nace,
Amma gaskiya Yayana ya kamata kayi nazari kan fin ka dauki wani mataki akan zancen nan,
Idan da bata son ka bata ra,ayin zama da kai, at da bata dawo ba don Allah don Annabi Yaya ka kwantar da hankalinka ku fahinci juna da ita,
Don gaskiya, wanan zancen al,amarine, babba wanda ke bukatar natsuwa da kwantar da hankali,
Saboda akwai, dubaiyya ta hanyoyi da dama da suka kama a duba,
Hannu ya daga min tare da dan kawar da kan shi gefe guda, yana mai mayar da kan shi baya ,
Sai kuma naga ya saka hannun shi a kai ya shafo gashin kanshi har zuwa fuskan shi, a hankali,
Yace, ban son rainin wayyo wallahi wanan ai rashin sanin ciwon kaine,
Dariya ma zancen ya bani magana kamar ba a kan Fatiman shi ba,
Ina gyara kwanciya nace aiko don Aliyu da mahaifiyar shi, zaka iya yi masu hakkuri kabar su dan Allah dai yaya,
Wani irin kallon wanan bata san ciwon kanta ba yake min batare da ya ce uffan ba naga ya mike tsab zuwa hanyar fita daga dakin yana cewa ni zan tafi sai na dawo anjima,
Nace Allah ya kaimu amma ba,a yanke hukunci a cikin fushi dan Allah,
Bai tanka min ba amma nasan yaji may na fada baki na tabe, nace ai kunfi kusa kai da ita,
Don haka banga abinda zai sani wahal da rayuwana ba akan kishin ku, ba don dai nasan tunda shi mutum ne mai ra ayi aure koda ya rabu da Fatima wata ce zai kara jajibowa again,
Tafiya yakeyi yana yana tunanen wai ita wanan yarinyar batada wayyo ne ko kuwa ,
Ita ko dan irin kishin nan na mata bata gwadawa akan kowa ce kishiyar ta duk ta wani fita zancen kowa sai al,amarin gaban ta takeyi kawai,
Gurin aikisa ya koma inda ya na aiki yana tunanen yadda zai kara kora Fatima ta koma gida don yanzu bai bukatan irin fitinan ta a rayuwan shi, sam,
Zuciyar shi duk tana a cikin rudani don ya tabbatar auren shi da Fatima kaddarace kawai, da tausayi ,
Idan ya tuna da irin fititinun da tashin hankalin da take haddasa mai agida da irin izigilin da takewa sauran matan shi tankar tafi su aji da class duk yana a sane amma sai ya kawar da kai tankar bai san da su ba,
Badon komai ba sai dai tana da iya nata kokarin gurin kyautata ma nashi rayuwan don tana bashi kulawa iya yadda ya dace da kuma yadda yake bukata daga mace,

****** ********** ******
A gajiye ya shigo gidan don har ya manta da zancen dawowan Fatima da akace tayi saboda aikin dake a gaban shi lokacin,
Yana shiga gida su Aina da yar uwar tane su kai mai Oyoyo Uncle, cikin jin dadi da farin ciki,
Rugumay yaran yayi zuwa jikin shi cikin so da kauna tare da dan sauke numfashin sa, a hankali,
Ya dan dago yaran daga jikin shi yana cewa har kun dawo ashe suka ce eh, Daddy
Ba maman mu ta dauke mu takai mu can gurin kaka ba muna cewwa ta dawo damu amma sai taki ko school bama zuwa acan din,
Wani irin tausayin yan marayun yaran ne ya kamashi yaji yaran sun bala,in ba shi tausayi sosai a ran shi,
Dan kara rugumay su yayi yana cewa kubari yanzu zaku dinga zuwa school insha Allahu,
Daga inda take tsaye ta sake ajitan zuciya mai karfi don duk abinda ke faruwa tsakanin shi da yaran tana ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gani daga inda take labe,
Salawatu wace take zaune zaman jiran azo aiwa Fatima rashin mutunci sai gashi taga, an rungumay yaran Fatima, har ana firan arziki da su,
Ido qaje acikin mamaki taje kallon shi don har ta kasa bude baki tai mai sannu da zuwa,
Sam Salawatu bataso haka ba don ita so tayi da ya shigo yai wa Fatima rashin mutuncin sai ta wulakanta sosai,,
Paet din shi ya nufa da dan sarsarfa har ya ahiga dakin shi inda sai a lokacin ta kawar da idon ra daga gare shi a cikin kutawa,
Fatima ta sake labule tana cewa yar iskan mata ai kadan kika gani wallahi don yadda na bar gidan nan sai kubar shi kuma,

Wanka yashiga inda ya fito yana tsane ruwan jikin shi da da dan karamin towel din shi,
A sanyaye tai sallama a dakin inda ya dago kai ya dan dube ta kallo daya ya kawar da kanshi daga kallon ta,
Har gaban shi ta karaso inda takai gwiwar ta har kasa a gaban shi, acikin ladabi tace,
Ina wuni Yaya Bukar ?
Abinda ya tuna mai da baya ke nan ,
Kalman da take kiran shi a zamanin da suke soyayyan saurayi da budurwa, a tsakanin su,
Wata ajiyar zuciya ya sauke gami da fesar da iska irin ta relief din nan,
Bakin gado ya koma ya zauna yadan daga kai ya kalleta tana inda ya barta a tsugune,
Hawaye sai sintiri suke a fuskan ta yayin da ya kara kallon ta yaga cikin jikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login