Showing 354001 words to 357000 words out of 388021 words

Chapter 119 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9558

gaske, har cikin ranta tana kaunar su,
A Dubarance ta,sulale zuwa gida, inda ta, samu su, Sadiya take labarta masu cewa aiko da gaskiyane don har ta tafi can asibiti din taga yaran da idon ta kuma taga mutane sai zuwa ake ana photo da su da basu gift,
Jin Salawatu ta tafi yasa sauran shiryawa su tafi su ma don gudun yin laifi wurin maigidan,
Duk wace taga yaran sai taji wani iri a ranta saboda yaran akwai shiga ido, da ka kalle su zakaji kana kaunan su,
Amma su kishi ya rufe masu idanuwan su basu ji basu gani, Sai kyashin yaran da hassada da ya rufe masu idanuwan su da zuciyar su,
Ganin ba,a gani na yasaka su cewa to su zasu tafi idan na farka ace suna gaidani kusan duk wace tazo irin sakon da zata bari ke nan ta wuce zuwa gida rayuwan su bakikirin, rai a bace don fuskan su kawai ke baiyyana, bacin ran su, a fili,

****** ********** ******
Jirgin da ya sauka karfe bakwai na safe tare da Yaya Abubakar acikin shi,
Yana saye da wasu kanan kaya, da suka mayar da shi karamin yaro, kurciyar shi tafito sosai,
Yana shiga Abuja direct drop din taxes din airport ya dauka zuwa har asibitin da nake kwance,
Anan ya samu yan uwa da abokan arziki suna gurin wasu a tsaye wasu kuma a zaune, suna maduyin shiru,
Kowa yai mamakin ganin shi haka tun da wanan safiya daga can kasan IBO zuwa nan arewa,
Dole aka bude mai kofan dakin ya shiga a lokacin likitoci suna a kaina don sunyi mamakin ace tun jiya ban farfado ba har zuwa wanan lokacin,
Haka ya sasu taruwa a kaina suna nazarin abinda ya dace su taimaka dashi,
Sannu da zuwa suke mashi yayin da idon ya na a kaina kyam baya ko kiftawa don fargaba da tsoron da ya hango a tare da ni,
A kwance nake ban ma san suna a kaina ba?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? sai dai numfashina dake nuna cewa yana tafiya dai dai,
Ya tambayi babban likitan da ke kokarin mika mai hannu su gaisa yana cewa, may ke faruwa ne wai haka har yanzu bata farka ba,
Likitan ce zan iya farkawa anytime ba komai bane insha Allah gajiyane da kuma irin alluran da akai min na barci shine bai sake ni ba,
Sunyi yan rubuce rubuce a cikin wani farin takarda suka aje a gefen gadon da nake a kwance,
Kujera ya jawo zuwa gap da gurin bakin gadon ya zauna yana mai daga kai yana kallon ruwan da ake min kari a lokacin,,
A hankali ya mika hannuwan shi ya danke acikin nawa ya dan dago hannun zuwa bakin shi ya subbanta a hankali,
Su Lawal da Mama Dije suka shigo dakin suka samay shi a hakana rike da hannuna yana dan matsawa a hankali,
Hankalin su yana a kan shi yadda duk ya susuce a kan gani na kwance shirim ba motsawa,
Suna magana da Dije amma hannun shi na harde acikin nawa, yana dan murzawa a hankali,
Abinda ya haddasa min bude idanuwana kenan, a hankali sai dai bani iya ganin mutum sosai kuma a zahiri ban gane komai
Amma acikin magagin da nike a ciki na gane fuskan Yayana inda nace cikin yar murya,
Yayana,
Sai kuma na maida idona a hankali na rufe idanuwa na naci gaba da barci,
Irin yadda yaji muryana ya sakashi cikin tashin hankali, yana cewa a hankali Meena,meenat meenatu,
Amma ina idanuwana sun hade guri guda sun rufe yayin danake sauke nfashi a hankali wani irin wahalce,
A hankali bayan ya kura min ido ya fahinci ko barci a wahalce nake yin shi sai kawai idanuwan shi suka kawo hawaye baisan lokacin, da suka fara dan silalowa ba,
Rabon shi da kuka har ya manta da lokaci sai gashi yau ganina acikin wani hali ya saka shi fitar da hawaye,
Tun yana yi a ciki iki har ya kai ga dan fitar wa fili ya fara yin kukan afili,
A, a,a haba maisunan malam don Allah kadaina wanan kukan ai sai ka tayar wa mutane da hankali,
Mikewa yayi tsam yabar dakin a cikin kuka yafita yana goge fuska da handakaci din shi, a hankali,
A lokacin Lawal ya shigo mai da motar shi don haka ya nufi gurin yana goge fuskan shi tare da face hanci,
Duk wanda ya wuce sai an waiga ana mai kallon shi acikin mamaki
Sun kama hanya zuwa gida shida Lawal a motar babu mai ma wani magana daga cikin su,
A, hankali lawal ke tukin motan can ya nisa yana cewa kai gaskiya Hajiya Amarya ta ahala sosai
Saboda jiya gaba daya tabani tausayi don duk tafita hayacin ta tankar ba ita ba,
Yaya Abubakar daga inda yake ya lumshe idanuwan shi can ya furzo iska, ya fesar yana cewa,
Yanzu don Allah Lawal wa zai ce wai meenat ce ta, haifi yaran ,nan
Yara mayan haka dasu ashe shiyasa ta sha wanan wahalar haka ,
Yarinyar ta wahala da yawa wallahi watan ta shidda zur a cikin asibitin nan,
Lawal yace bari kawai maigida, muna mahanan ta sosai a gida ai da Fattu,
Fattu takance yawan imanin Meenatu yai yawa sam bata damuwa da zaman ta asinbiti,
Don idan watace sam zata tayar da hankalinta ne kamar ta mutu kuma duk ta san da hakan na iya faruwa amma sai ta shanye shi ta dake, tabarwa Allah komai,
Wallahi maigida duk sanda nazo asibiti gaida ita, nakan dade ina mamakin ta irin yadda sam bata damu ba sai harkokin ta kawai take da mutane,
Yaya Abubakar bai samu cewa komai ba sai ihummm, din ya furta a hankali yana mai lumshe idanuwan shi,

****** ********** ******
TV falon a kune yake inda ake wani program a cikin wani tasha da gani compation ne suke don idan anci zakaga mutane suna yanka ihu, da murnan jin dadi,
Sai wanda baya a kusa ya zaci cewa a fili ake wanan wasan da ihu haka saboda kure karan TV da a kayi,
Tun da ya fara taka steps din da zai sada shi da falon yake jin wanan hayaniyar, mamaki ne ya kamashi sosai na jin wanan hayaniyan haka yana fitowa daga cikin gidan,
A hankali ya mika hannuwan shi ya murda handle din kofan falon gidan nashi inda yai daidai da anyi wining a cikin TV gidan,
Wani irin ihu da fito mazu kallo ke yi don murnan aci game din a lokacin,
A fusace ya murda kofan ya shiga hankali a tashe yana son ganin abinda akewa ihun duk da ya fahinci daga cikin tv ne, ake wanan ihun haka,,
Acikin irin takon shi ya nufi TV a hankali ya mika hannuwan shi ya kashe kayan kallon,
Abinda ya mayar da gidan ya koma silent ke nan zakace ba,a nan ake wanan rakadin ba da farko,
Baka jin komai sai aikin naurorin wutan dake falon suna aiki,
Daga cikin dakin taji shiru babu karan TV kamar yadda yake kara da farko inda har daga waje zaka iya July n sautin shi,
Ta na kokarin fitowa jikinta saye a cikin digon riga kanta,saye da wani dan yalalon gyale, da ta rufa kan ta dashi,
Take cewa kai waye wanan dan wullakancin da ya kashe min tv ina kallo,
Fitowan ta daga part din ta yai daidai da bada bayan shi yana kokarin son ya shige part din shi,
Sweet Oga har ka shigone ko, ?
Sannu da zuwa tana kokarin zuwa ta karbi jakar dake makale rike a hannun shi a matsayin abokin tafiyan shi,
Hannu ya dakatar da ita dashi a cikin daga mata hannayen nashi da sauri yana fadin No kibar shi kawai,
Ya nausa zuwa dakin shi batare da ya tsaya jiran komai ba,
Kamshin turaren jikin shi da yake amfani dashi ne ya gauraye gidan abinda daga cikin matan shi ke sa su gane cewa ya shigo gida ke nan,
Sadiya na daga zaune tana kallon a wani tashan Korea,
Taji wanan kamshi abinda ya sanar da ita zuwan mai gidan su gari ke nan,
A shakan farko sai take ji kamar hancin tane amma gana biyu sai ta tabbatar da cewa shine dai din a gidan,
Abinda ya sata kokarin mikewa tsaye ke nan don zuwa tatitan shi inda mikewan ta yai daidai da bude labulen dakin ta da yayi,
Irin kallon da ya watso mata shine ya sata shiga wani halin saboda tasan cewa kallo ne na laifi a gare shi,
Ashe ka shigo ne ya amsa a daddare da cewa ummhmmm nashigo, sai ya juya zuwa kofan fita yana cewa ki samay ni falo,
Dakin Fatima ya fada wace take barcin safe da yar ta manne a jikin ta suna batcin su hankali a kwance,
Shakan kamshin turaren jikin shi ta shaka abinda yasakata dan gyara kwanciyan ta don tana gani kamar a mafarki ta shaki kamshin,
Amma sai taji abin so closed to her da sauri ta bude idanuwanta yana tsaye a kanta harde da hannayen shi yana mai kura mata idanuwan shi,
Yaya Bukar ka dawo ne ashe sannu da zuwa yaya hanya idanuwan shi akan yar shi dake barci yace Alhamdullahi ina falo na jiran ki sai kawai ya juta zuwa waje,

****** ********** ******
A falo sina zaune su biyu ya samay su fuskan shi a daure yana kokarin samun guri ya zaune,
Fatima ta fito sagale da yarta a kafada tana kallon su a cikin mamaki yayin da take kokarin gano abinda yasa a kakirasu a nan, din a kuma wanan lokacin da yadawo yana bukatan hutawa
Saboda tasan cewa idan ya dawo daga tafiya yakan yi kokarin samun hutune da natsuwa,
Amna yau shigowan shi ya sha bamban da na kullun don hankalin shi duk a tashe yake saboda ta gane haka daga yanayin fuskan shi,
Wuri ta samu ta zauna yayin da sauran suka bita da idanuwa sunadan kawar da kai gefe saboda kishi don ganin yadda tafito tsaf da ita ga kuma yar ta sabale ga kafadan ta,
Guri ta samu itama takai zaune tana dan gyara kwanciyar yarta ga cinyar ta,
Kusan yan dakiku sha biyar baiyi magana ba sai dai daga cikin su kowacen su da akwai abinda taje kiyasatawa a zuciyar ta,
Sadiya taji ya ambaci sunan ta daga sama batare da ta zaci hakan ba,
Da sauri ta dago kai tana, kallon shi saidai fuskan ta kamar kullun a daure ta ansa da cewa na,am a takaice,
Yace may ke faruwa a gidan nan cikin mamaki take kallon shi don bata fahinci may yake nufi ba,
Yace ina sauraren ki nace may ke faruwa a gidan nan ne wai, don nazo nasamay ku acikin yanayin kwanciyar hankali alhalin yar uwar ku ta asibiti tana bautan Allah yan uwana da abokan arziki duk suna acikin tashin hankali,
Amna sai gashi abin ta kaici a cikin gidana wai na samay ku hankalin ku akwance cikin kwanciyan lafiya babu abinda ya damay ku,
Gaba dayan su tunda ya fara magana fuskokin su yana akan shi suna mai kallon mamaki,
Yace cikin daga murya wallahi wallahi idan bakuyi hankali ba duk zan bata aku rai, fiye da tsanmanin ku,
To yanzu may,ye laifin mu a ciki da zakace haka a gare tundai ba wai zamu koma a kanta mu tare ba,
Ke dakata rufe min bakin ki mara kunya kawai ke idan har kin san kuya har zak iya bude baki kice min wani abu akan Meenat,
Wai kun mata cewa Meenat yar uwata ce taji kuma mata da har zakuyi mun haka,?
May kuke tsan mani ne wai kuna ganin abubuwan da kuke yi ina sa maku ido kaman bazan iya daukan mataki bane a kan ku,
A gidan da yar uwar ku ke cikin irin halin da Meenat take cikine har zanzo nasamu TV yana min ihu a gida kamar gidan yan caca, ko dambe,
Salawatu tace ai ban kaishi karshe ba nice ke kallon program a ciki,
Short up my friend baki da kunya wallahi bakisan may kikeyi ba sam baku da addini kwatata zama daku wallahi, kaddarane don ko nike acikin irin halin nan haka zakuyi min,
Mamaki sosai zancen shi yaba, su don sai sukaga yare masu ya koma kaman tababe sai maganganu yake sakewa,
Ya mike yana cikin fitinan yabar su azaune yanufi hanyan fita waje cikin bacin rai,
Gaba daya suka bishi da kallon mamaki babu wace ta iyacewa uffan daga cikin su, suna zaune zugun zugun inda yabar su zaune,
Saida suka tabbatar da cewa yabar gidan sunji tada motar shi san nan suka fara cewa chabdijam, ashe akwai magana, ke nan,
To may yake nufi don an mai haihuwa sai mutare a sibiti muna nuna murna ko may,
Salawatuce ta fadi hakan yayin da ra wani ja dogon tsuki takawar da kanta gefe, guda,
Ni wallahi yarinya bata kaimin can ba ainima haihuwa nayi amna ban ji yace ataru a kaina ba, sai yau zai fada muna haka, bazanje ba wallahi,
Sadiya tace tau ni ai dole in tafi tunda idan ban afiba karshe duk laifin a kaina zai sauka idan ma na matsa sai yai min gori yace ai Meenatu, tayi dawainiya dani da banda lafiya,
Haka sukai ta zancen su kowa nafadin albarkacin bakinta akan don yace su tafi asibiti su duba lafiyana,
Yana fita ya shiga motar shi yabar gidan zuwa wani shahon sayar da kayan yara inda yasayo masu kaya sakawa Unisex masu kyau da tsada da sauran abubuwan da za,a bukata ga jariri,
Yadawo yasamu ina ta barci su Gwago Habbi da Mama Dije Maman Biu duk suna tsaye a kaina hankalin su a tashe don sunji wai likita yace yana ganin akwai inda aka samu problem ne kila don ya kamata ace na farfado zuwa yanzu
Bayan yaje kayan da ya sayo yadan dade tsaye akaina Mama Dije tana mai bayanin abinda likita yace akaina,,
Ba tare da yan tanka masu ba yajuya zuwa dakin ganin likita baidamu sa ya tsaya daukan excuse ba kawai ya shige abin shi, kai tsaye,
Tare da likitan suka dawo dakin inda likitan yadan kara duba lafiyan jikina a hankali, yai yan aune aune sai yake cewa isha Allahu zan ta farfado bada dadewa ba,
A take hankalin shi ya daga don sai ya fahinci cewa dabara ta kubcewa likitan kawai baida na fadi sai dai rokon Allah, akai,
Durkusawa yayayi bakin gadon, yana mai kura min idanuwa zuwa wani dan lokaci, ya mika hannun shi yakamo
Hannuwana ya rike su gam acikin nashi yana dan matsawa a hankali sai ga hawaye suna zubuwa mai daga idanuwan shi kamar karamin yaro,
A daidai wanan lokacin su Sadiya su ka shigo dakin gaba dayan su idanuwan su idon su na a kan maigidan nasu,
May ya faru may ya kawo hakane ance wani abune wai, akan ta,
A rude Sadiya suke tambaya sai mama Dije ce take cewa jikin ne yai mata ni sa don har yanzu ba ta farka ba daga aikin,
Dan dama dama dazun da safe da maisunan malam ya shigo shine, tadan bude ido takira sunan shi amma daga haka bata kara bude ido ba again,
Allah ya sawaka,auke fadi suna dan lekawa guda guda suna ganin irin yadda nake kwance ina maida numfashi guda guda,
Wayan Yaya Abubakar ce tai kara abinda ya dan sashi mikewa daga dukaqan dayayi ke nan malam tsoho ne akan layin bayan sun gaisane yake cewa,
Wadda ya bugo min waya yake fada min irin halin da kuke ciki da Meenatu,
Abubakar yace hakane malam ala,marin duk yadaure min kai na kasa fahintan abunda akeciki donbsai nake ganin kaman suma likitocin abin ya bayar dasu basu san dalilinta na rashin tashi ba har zuwa yanzu,
Malam tsoho yace saurara kaji abinda zan fada maka da,zaran kashiga,dakin kaje daidai sai tin kunuwan ta na,dama kai mata kallaman shahada sau uku,, sai kadawo nahagu kai mata irin hakana,
Hasbunallahu wani,imal wakil, kafa bakwai a kowani karshe babban ya tsan kafan ta, , saikatofa mata,
Karike goshin ta ka karanta mata shima kafa bakwai da Ya Salam kafa dari saika yo kasa da hannuwanka a hankali harzuwa kan dan babban yatsan kafan nata,
Insha Allahu duk abinda ke faruwa da ita zai baiyya cikin dan lokaci idan da sauki zamuga alama idan kuma ba sauki za,agane insha Allah,
Godiya Yaya Abubakar yayi, yayin da yake kokarin fita daga dakin don yayi alwala ya gabatar da abinda malam ya umurce shi da yai min,
Bayan dan lokaci yadawo yafara gabatar da abinda malam ya umurce shi da yai mata,
Salawatuce tafara fita daga dakin don bazata juri ganin irin abinda yake wa Meenat ba agaban su,
Duk ya wani rude ya susuce yafita hayacin shi takar ba Abubakar da kowa ya sani maizafin rai ba,
Sadiya tace zasu fita daga waje don sai taji tsayuwan dakin nai mata wuya saboda wani irin kishi dake azalzalan ta arai,

****** ********** ******
Baibar dakin ba sai dayafita zuwa yin sallah la,asar yadawo shida Lawal da malam Abdullahi tare dasu wadda,
Duk kan su suna tsaye akanta sai shine kawai yadan duka kamar mai sauraren numfashin ta a lokacin,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login