Showing 123001 words to 126000 words out of 388021 words

Chapter 42 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9535

bugo amma sai ki kaki,
Gashi har uncle din ki ya fara suspecting din ko kin sawa kanko kishi ne,
Da sauri nadan dago kaina ina kallon ta don jin abin da tace uncle yace a kai na,
Jikina ne yai sanyi a lokacin nace cikin wata irin murya tankar zanyi kuka,
Anty ni ba fushi nakeyi da shi ba, kawai dai, ban jin dadi ne,
Hmmm naji tace taci gaba da cewa gaskiya meenatu, baki kyauta ba duk nasihan da mukai maki amma zaki, yi haka,
A sanyaye na dago idona da suka fara cika da hawaye nace,
Kiyi hakkuri Anty Insha Allahu bazan koma kindaukan wayan shi ba,
Ji nayi ta safa min kafada na tana fadin kiyi hakkuri Meenatu nasan cewa hakan nada zafi,
To amma shi namiji ba,a yi masa haka sai yai saurin gano takon ki ya raina ki,
Kiyi a hankali bada garaje ba har ya shigo hannun ki, da dubara zaki wana shi,
Don Allah ki kiyayye Meenatu, ni mai kaunar kice,shi yasa kikaga ina kokarin saki a hanya,
Bawai don bana son ki ba ni dake guda nake daukan mu don kin gwada min kauna kuma ai ko dan kawun ki zan maki abu dole, meenatu,
Na kara cewa don Allah Anty kiyi hakkuri Insha Allah zan kiyayye,,

****** ********* ******
Washegari su mama da Anty Mariya,suna falon gidan yaya, Abubakar zaune,
Sai ganin wasu irin kattan mata yare sukayi sun shigo gidan babu ko Sallama, sai daya daga cikin su ce ta e Sarama,rekum,
Mama Ladi kan tsoro taji da farko ganin irin shigar su kowace da gashin doki akai, an kara mata,
Sannu ku fa kawai suka ce, sai suka fara kokarin shiga duba dakunan gidan,
Suna ta faman gwalanci a tsakanin, su
Kofan dakin da aka nunawa su Anty Mariya da Mama Ladi cewa nawa ne a nan sukaga mutanen sun tsaya sai faman murda marikar kofan su keyi suna jin ta a rufe,
Anty Mariya ce hankali tashe ta nifi dakin anty Sadiya tana sheda mata cewa ga wasu irin kattan arna sun shigo masu gida ba sallama suna kokarin bude daki,,
Da sauri suka fito waje tare da Anty Sadiya a cikin mamaki suke kallon matan,
Tambayan su Anty Sadiya ta keyi da lafiya dai ko,,
Watace daga cikin suke cewa suna son abasu keys din wanan kofan ne don su shiga su gani,
Saboda suna son su shiga su gyara wa Salawatu daki ne,
A cikin muryan mamaki, Sadiya ke ce masu maigidan yasan da zuwan su, ne ?
No sai yasan da cewa zamu zo mu dai munzo ne don mu gyara mata part din da muke so,
Kuma munga cewa wanan yafi saboda yafi tsari da kyau a,duk cikin dakunan da ke gidan,
Ayyee inji Sadiya tace to gashi ko kun makara don wanan din dakin watace,
Wata daga cikin su tayi farin bilicin har jinin jikin ta zaka iya gani da jijiyoyin ta saboda kwandewan da tayi,
Ita ce ke cewa gaskiya sai dai mai dakin ta kwashe kayan ta zuwa wani part don mu wanan mu ke so, yafi kusa da ko ina na gidan,
Wani irin kallon banza Sadiya ta watsa mata tare da cewa Over to you,,
Ta juya kawai a binta sai taji muryan matar na cewa,komai bakin ciki dai mun shigo gida babu yadda za,a yi damu dai,
Daidai lokacin ne Baba Wadda da Hamza makwabcin mu suka shigo gidan,
Anty mariya ce ke fada masu abinda ya kawo matan gidan da kuma wai abinda suke son yi,
Ga yan abu kaza inji Baba Wadda
Ya,kara cewa ko matsafa suke wallahi basu shiga dakin Meenatu,
Mama Ladi wace tsoro da fargaba duk sun kama ta don ganin balai,n da yafi nata,
Hamza ne yai masu wani irin tsawa yace subar kofan dakin nan tun kafin ya karaso gurin,
Sai tambaya sukeyi wai shi waye da zai hana su aiwatar da aikin su,
Daki dai shi suke son sawa yar uwar su kayan ta a ciki, dole kuma abude masu,
Baba Wadda ya ce bari yan iska in gwada masu hauka,,
Wani wayan kebel din wuta yasamu yai cikin su dashi yafara lafta masu, shima hamza ya mara mai baya,
Ihu suka sa da gudu suka fara fita gidan suna ihu, da neman taimako,?
Salawatu ce su ka kira a waya, suna sheda mata karya da gaskiya,
Ita kuma takira yaya Abubakar tana kukan kissa wai ?nty Sadiya tasa yan daban shiyan su sunyi wa yan uwan ta wullakanci har da duka,
A fusace rai bace ya iso gidan tun daga kofa yake kwadawa, Sadiya kira,
Batai wani damuwa ba don ita halin ta sai ita don irin mutanen nan masu halin ko in kula,
Don may zata sa a wullakanta mutane bayan tasan cewa zasu zo gyara daki ma yar uwar su,
Za tai magana ya wani kara daka mata tsawa, tasa kai batare da tai mashi bayani ba ta juya abin ta zuwa dakin ta,,
Waya ya buga masu kaman wanda yai hauka wai su,zo suci gaba da aikin su,
Su za bi duk dakin da take so agidan wanda taga yai mata,
Still dai dakin nan nawa suka kara nuwa cewa shi zasu bude,
Baba Wadda ya kira su Baba, hankali tashe yake sheda masu halin da ake ciki,
A cikin tashin hankali Baba Buhari yakira wayan shi a karo na farko yana mashi kashedin muddin ya bude dakina ban gida yasa wata bai yafe mai ba,
Sai a lokacin ne jikin yaya Abubakar yai sanyi tare da dan dawo wa cikin hankalin shi,
Duk ya najin kanshi cewa bazai iya sabawa Salawatu aduk abinda tace ba to ya kuma zama dole ya,bi umurnin iyayyen shi,
Malam.tsoho wanda tun lokacin da autan shi ya bugo waya yana sheda mai yadda su kayi da Abubakar akan dakin Meenatu,
Duk da rayuwan shi a bace yake bai yarda ya nuna hakan a gaban yaran shi ba,
Sai dai can cikin zuciyan shi yadade yana mamakin wanan rashin mutuncin na Abubakar,
An gyara wa Salawatu daki, wanda ke fuskantar na Anty Sadiya suka zaba saboda girman shi,,
Allah ke nan,lokacin da za,a kawo ni cewa Anty Sadiya tayi bata yarda in zauna a wanan dakin da yanzu Salawatu ke hasashe ba,
Yanzu kuma sai gashi zasu yi zaman makwabtaka a tare,

Washe gari salawatu daga ita sai Lubuna da da kawar ta guda suka rako ta,
Ta dan yafa wani dan guntun mayafi mai shara,shara, a kan,ta, wai ita amarya,
Wanan shine mafarin labarin zaman Salawatu a gidan yaya Abubakar,


****** ********* ******
Washegari da Amarya ta tare, har zuwa wani lokaci, ba wanda ya leko wajen gidan,
Ga yuwan ya addabi Mama Ladi da Anty Mariya, wanda tun daren jiya basu ci abinci ba,
Saboda mamakin yadda dan ta ya koma kamar ba Abubakar din ta ba,
Sai zuwa wani lokaci Salawatu ta sauko daga sashen maigidan,
Daga inda Mama take zaune ta hango ta ko gaisuwan arziki basu samu ba daga gare ta,
Zuwa can sai gasu tare da, Abubakar sun fito daga dakin shi,
Wanan karon tasha kwalliya sai kyalli takeyi don ado,
Gurin Mama suka nufa a tare sai kauda kai Mama ke kokarin yi, don bazata juri ganin wanan irin fitsarar da Salawatu keyi a gaban ta ba,
Duk Mama sai taji ta tsawala ta wani dabur ce, don ganin wanan irin mace wai itace yau sarrakuwar ta
Gata tanka irin matan iya muran da suke gani a hanya idan zasu anguwa,
Yau wai irin sune a gidan dan ta Abubakar a matsayin sarakuwan gidan malam tsoho, mai almajirai,
Kamar yadda ya saba idan zai gaida Mama yau ma hakan yayi inda yadan zauna daga bakin kujera, yana cewa,
Mama,ya kuka kwana ? ya dare, ?
Ita ko salawatu can ta koma daga bayan kujera tana cewa Mama antashi lafiya ?
Daga Mama Ladi Baba Wadda har Anty mariya sai da su kaji wani irin nauyi da kunya,,
Amma sai sukaga shi Abubakar ko a jikin shi bai wani nuna damuwan rashin da,an da ta nunawa Mama ba,
Mama Ladi dai kanta yana kasa duk takaici da imani ya rufe ta a lokacin,
Anty Mariya ce tai karfin halin tambayan yaya Abubakar da cewa kai Abubukar Mama fa yunwa takaji,
Da mamaki yake tambayan Sadiya bata baku abin kariba,
Anty Mariya tace, mu yau ko ganin ta bamuyi ba tunda gari ya waye,
A take rayuwan shi ya baci, ya dan kalli gurin da Salawatu take tsaye daga bayan shi,ya ce,
Ki hada masu abin karyawa please ?
Ba,tace ba,zatayi ba sai dan dan murmushi da ta sake mai daga haka ya tashi ya nufi hanyar fita daga gidan,
Baba Wadda yabi bayan shi suka fita tare a lokaci guda,
Yana tsaye daga waje har yaya Abubakar yaja motan shi yabar gidan,
Baba Wadda gidan su Hamza ya shiga don ya gani ko Hamza' yana gida a lokacin,
Mama Bi,u ce tai mashi tayin, kunun gyada, da sugar,
Sai dai Baba Hamza ya kasa sha yana tunanen su Mama Ladi da Anty Mariya,
Mama Ladi tagane nufin shi don haka ta zuba mashi cikin wani babban jug nasu,
Ta kuma zuba masu faten Irish, da sukayi mai yawa acikin kula tace ya kai masu,
Sosai suka ci wanan abinci da aka aiko masu har suka koshi,
Anty Mariya ta juye saura anjima su bawa Mama taci,
Salawatu tun shigan ta daki tafada saman lafiyayen gadon ta tana tun yadda daren su da Abubakar ya wakana jiya,
Sadiya wace ba kunya ya ishe,ta ba sai kawai ta fito wai tana neman abin karyawa,
Sauran abincin da Anty mariya ta ajewa mama lafi shi ta lashe gaba daya ta kora da goran fanta,
Baba Wadda shi ke ba Hamza labari don haka hamza ya fadawa wa mama bi,u
Dazasu dafa abincin rana aka dafa dasu da kan ta ta kawo mata tana kuma bata hakkuri akan sarrakan zamani,
Anty Safiya ce ta bugo waya daga gida ta noban Baba Wadda saboda ta nan kawai ake samun su,
Bauan sun gaisa ne Anry Mariya take dan kenkyasa mata, halin da,suke cikki kadan,
Hankalin Anty Safiya yai mugun tashi tace su dawo gida da mama ta karasa jinyar ta a gida,
Ta kara tabbatawa da Anty mariya da,su tayar wa yaya Abubakar da hankali don ya turo su, gida,

****** ********* ******
Tun rashin kiran da yaya Abubakar bai min ya na dan damu har nazo na basar nafitar da abin a rai na kawai,
Karatuna nake facing yanzu ban da wani abu dana sawa gaba kamar karatun,
A gajiye nake tafe don tun tea da nasha kafin mufita zuwa school ban kara cin komai ba har zuwa yanzu,
Gab da zan shigo nake jin muryan mummy uwargidan Uncle nake ji daga falo tana bawa wasu da ban sani ba labari kamar haka,
Ai bari kedai aure wata, uku da dan kai, amma wai har miji ya kara wani aure,
Dama fa ba neman ta yayi ba kawai dai kwadayi ne irin na iyyayen su,
Suka daura mata aure dashi,
Ance ma wai mahaifinta shine ya roki kakan wai ya daura da yar shi ,
Yanzu a yadda nake gani, bai ko kulata balle ma yasan da wata Meenatu, can,,,,,
Ido biyu,mu kayi da ita daidai lokacin da take kaiwa nan ga zance,
A hankali nace masu sannun ku da aiki mummy, su kuma bakin na gashe,su cikin ladabi na shige abina,
Da kyat na kai dakin kwanan mu na fada saman gado na sai kawai naji na fashe da kuka,
Nasan dama dole ne mutane su zageni wasu ma harda zargi zasu hada min,
Daga gurin da nake kwance ni kadai a dakin mu don yau Anty Amarya bata gidan ta, tafi taron Anty Zainab din su da tazo daga Kano,
Wayana ne ya fara ringing a lokacin kamar kada in duba amma sai na mika hannu na na dauka,
Yaya Abubakar nagani rubuce a screen din wayan nawa
Wani irin haushin shi da takaicin shine suka rufe ni, sam sai naji bana son jin muryan shi balle ma ingane shi,,
Mutumin da akan shi ake tamun ka,zafi iri iri a cikin yan uwa,
Saboda kawai biyayyan iyayye na hakkura da duk wani yanayin rayuwa da nake gani,,
Hudubar Anty Amarya ne ya fado min a rai don haka na dauki kiran nashi, badon naso ba zuciya na fam da takaicin shi,
Muryan nan nashi dakkakiya mai kama da ta jaruman maza, ya ce,
Assalamu Alaikum Meenat,
Na ansa cikin dassashen murya na da nai kuka har ya isheni, da cewa,
Wa,alaikas,salam,
Kafin yai magana ni,ce na fara cewa ina wuni yaya, ?
Ya sallam, naji yace a lokaci guda sai,kuma cikin daga murya yake cewa baki da lafiyane Meena ?
Da kyat na dan seta muryana, nace lafiya na kalau yaya yanzu na dawo daga school na gaji ne kawai,
Sai a lokacin naji yai wani irin ajiyar zuciya yana cewa, OK, ok, sorry sannu ko ?
To ya kuke nan,?
Still cikin dakiyan zuciya nace mai da Alhamdullahi duk muna lafiya,
Yau shene zakuyi hutu ne wai,?
Akwai sauran time nace a takaice,
Ok, kawai ya amsa da shi,
A hankali nace ya jikin Mama cikin daurewa, ya amsa gami da lumshe idon shi da cewa Alhamdullahi ta samu lafiya sosai yanzu,
Agaishe su na ce batare da na kara furta wani abu ba,
Daga haka nai shiru abina, ban kara cewa komai ba,
Wani irin sha,awar ce ta saukowa, yaya Abubakar don bai san tsawon lokacin da ya dauka, yana kewan na ba,
Sai yanzu ya fara gane cewa ba karamin missing din yar uwar haihuwar shi kuma matan shi yayi, ba,
Jin yayi shiru ya dan sani ajiyar zuciya daga gurin da nake, ,
Yaya Abubakar ji yayi tankar ya jawo ni daga cikin wayan ya rungumay
Ina jin irin yadda ya sauke ajiyan zuciya wanda hakan ya tabbatar min da cewa, ya dan shiga wani yanayi,
Don in takaita shirun nace ina gaida kowa sai anjima, nakashe wayan,
Murmushi kawai yayi don yasan cewa iyakar hiirar mu ke nan dama ba wani mai tsawo bane,
Daga gaisuwa ne sai kuma tambayan lafiyan, junan mu,
Ina katse wayan sai yasake yar murmushi tare da sosa kan shi da key din motar shi,
Yasan dai watara dole aje wanan kunyan nawa zanyi a koma dai,,,,

Wanan wayan da mukayi da yaya yadan sani mantawa da zancen mummy da yan uwan ta akaina,.
Sai dare Uncle ya dauko Anty Amarya da yaran ta suka dawo gida,
Kafin ta iso nagyara ko ina na sashen nata sai kamshi ke tashi,
Da sallama ta shigo sashen nata, tun daga kofa taje cewa wai lalai Meenatu wanan irin kamshi haka ?
Daga dakin mu na yara nafito ina mata sannu da zuwa, tare da rungumay yar ta da ta yo cikina da murnan oyoyo,
Ledan dake hannun anty tamiko min tana cewa ga sakon ki inji Hajiya Mama,
Sai mun zauna zan maki bayani akan kowanin su,
Na amsa da fadin to Anty,
Uncle dina yabiyo bayan ta rugumay da dan karamin yaron ta, wanda ke ta barci a kafadar mahaifin shi,
Sannu da zuwa nai ma Uncle wanda,ke kokarin mikawa matar shi, yaron ,
Uncle yana bada baya cak, naga Anty ta tsaya da yaron a hannun ta tana kallon na cikin son tambayana,
Muryan ta naji tana cewa, Meenatu may ya samay ki har ki kai kuka,
Nace kuka Anty ?
Eh kuka gashi har idon ki sun yi jajajir, don kuka,
Na bude baki zanyi magana amma sai na kasa cewa komai,
Illa ma hawayen da ya dan fara silalowa saga fuska na,
Hmm kawai , tace tare da juyawa tashige nata dakin kwanan,
Nima dakin mu na juya nashige da Ledan vacco da anty ta miko min ,
Ban tsaya jiran komai ba nayi kokarin samun guri in kwanta,
Sai ga Anty dauke da,wani ledan mai tambarin shagon saida kaya,
Naman kaza ne gasassa da fresh milk mai sanyi a kwali,
Ta shi ki ci abinci tace min don nasan baki ci komai ba,
Ba musu na mike zaunen ida Anty ke kokarin bude muna ledan da kan ta, tare da miko min nawa kwalin milk din a gabana,
Nakai a baki sau guda sau biyu sai na ji muryan anty da ke zaune tana ta cin abin ta hankali kwance, tace,
Meenatu Fada min gaskiyan abinda yasaki kuka haka yau,
A hankali nace Anty don Allah abar wanan zancen don fadin shi ba alheri bane zai haifa
Tambayana takarayi ina fatan ba zancen auren Abubakar bane ke damun ki har yanzu ?
Da sauri nadago kai ina kallon ta cikikarshen za kai, na, anty ai na fita wanan zancen ko,
Madallah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login