Showing 147001 words to 150000 words out of 388021 words

Chapter 50 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9532

har guda uku sun tashi daga dakin ta zuwa, Saman rufin dakin basu bukatan wai saman ya bude duk da rufin kwano da dakin ke dashi,
Bata kara barci ba tana zaune har zuwa asuba sai ganin tsuntayen nan sun dawo suna ta amai a tsakiyan dakin ta zaban tausayi,
Hakalin matar ya tashi matuka saboda yadda taga wanan halittan suna amai,
Kafin wani lokaci sai taga kamar hayaki sun koma cikin kwaryan da ta aje a bayan gadon ta sun zama kamar duwatsu,
Juyowan da zatayi sai ganin wanan aman da sukayi tayi ya koma mata kudi gudan mai yawa,
Innalillahi ta fara fadi ga bakin ta tana cewa wanan mugun maita ya bani ashe,?
Badani ba sam bazan karbi wanan fitinar ba gaskiya sam da sake,
Tun da safe da kudin da kwaryan ta kwasa ta mayar mai da abin shi tana kokarin tara mashi mutane a gida,

****** ********* ******
Anty Samira bata bata lokaci ta turo da account din wata kawar ta,
Ya Abubakar ya tura mata da dubu dari a ciki, ina barci da rana musalin sha biyun rana,
Saboda girkin Salawatu ce gaba dayan mu ni da Anty Sadiya muna daki kwance abin mu,
Ta manta cewa mu mutanen hausa ne kishi dashi aka haife mu na tsabata bawai na sheri ba, don tun muna yara muke taya uwayen mu kishi, mun san kan zama da mutane iri, iri,
Zaka fan mu kamar kauyawa amma zama da mu wahala gare shi don kar muke kallon ka,

Karan wayan Anty Samira ya tayar dani barcin da na keyi badon naso ba,
Cikin muryan barci nace Anty Samira ya kuke ya gajiya,
Tace Meenatu an bansan ko me zancewa ba, don na rasa kalman da zan maki godiya,
Na ce, a,a wallah na mi anaty ?
Shin Meenatu ke ko ga kudin da yaya ya turo min?
Har fa dubu, darin ya turomin dasuwa,,
Nace cikin sakin fuska kai Anty Samira am nai maki murna,
Sai atai zuwa shagali ko ?
Cikin wani murya tace wani shagali zanyi da su duka,
'Dariya na sa mata don jin abin da tace,
"Tace ke san dama ina son jari in fara yar sana,an gida irin na mata,
Na, ansa da fadin gaskiya na Anty ke ga sai dai ki saro kayan su, turaren wuta, takalma da su manshafi masu dan dama,
Tace Allah dai ya barki Meenatu, kaman kin san shawaran da ni ke nema ke nan,
Cikin zolaya nace amma dai sai kin tai kin gwada ma Mama kudin ko kafin ki fara taba su,?
Cikin wani irin murya da karfi tace,
Wata,?
Niya ?
Ai in kin gani lahira maza su ka kaini,, ta dai jiya ga baki amma koshi sai angama sha,ani zan fada mata,
Nace a,a ke ko Anty kaman yadda tace ki kai mata ko dubu goma kice ga su nan suna kin ka samu kawai,
Shiru naji tayi can ta numfasa tace to shike nan ance ba,a kin shawara zan gwada yin haka mugani,
Takara min godiya tare da kashe wayan ta,
A hankali na juya ina mai lumshe idona wanda zuwa yanzu barcin da nake yi ya fita min ga ido ko,
Don haka namike na bude drawer mirror na dauka comb da masillan kitso,
Nafara sance kaina da ya fara yi min kaikayi don yana neman agaji,
Tsab na sance na daure shi da ribon ta baya, sai dai ina a gaban mirror na ga ya dace inje wankin kai, haka nan,
Waya na jawo na kira Fattu muka gaisa na dan tambaye ta mutanen gidan ta
Sai take ce min Mama tana nan ta na biski wai zata kawo maki,,
A take na tuna da zancen Yaya Abubakar gashi kuma ina sha,awancin wanan biskin da akai min tayi, a gidan Fattu,
Don haka na kira Yaya Abubakar ina sheda mashi cewa ina son in dan mika kafa gidan su Fattu,
Bai ha,na ni ba sai ce min da yayi a dawo lafiya na amsa da fadin Allah ya nufa na gode,
A gidan su Fattu can na dan sake jikina muka ci abinci tare, da ita muna fira jafi, jefi,,
Maman Bi,u sai dadi take ji na shigo gidan su duk ta rasa inda zata sani saboda murna,
Munyi da Fattu zata rakani gurin wanke kai kamar yadda mu ka taba zuwa tare da ,
Sosai,naji dadin zama da su saboda sai nake ji tankar a gida Birnin Kebbi nake ,
Tunda na tunkari hanyar shigowa, gida sai naji duk jikina yai min sanyi ,
Zuciya na ya cunkushe min na dinga jin babu dadi, sam a rayuwata,
Mutum yai ta zama batare da yai magana da kowa ba saboda kishi, da mugun hali,
A falo na samu Salawatu, zaune tare da wata farar mace wace mai ya kodar da ita har zaka iya ganin kwancin jijiyoyin ta,
Sallama nai ma su ban tsan mani sun karba min ba don haka ban tsaya ta kansu ba,
Don ina kallon yadda gaba dayan su da zan shigo suke wurga min harara tare da jan dan guntu tsoki,,
Nashige part dina ina kokarin bude dakina da key,
Kunnena ya jiyo min lokacin da bakuwar Salawatu ke cewa wana ai batafi sha takwas ba ma,
Murmushi nayi kawai na shige abina ba tare da na tsaya jin su ba don duk basu gaba na,
Matar tace wa Sallawatu yanzu ma akan wanan kika tayar da hankalin ki haka,
Shiru Sallawatu tayi tana sauraren abinda matar ke, fadi, can ta nisa tana cewa,
Wata Adah baza ki gane bane aikin san dai koni wacece ko ?
Matsalan na daga gurin maigidan nan don duk wasu dokoki da ya aza muna sai kiga komai a dole ya zama equal a gidan sa,,
Matar tace ba matsalan komai na san yadda zamu fito mata,
Sallawatu, ta gyara zama tace kin gane ne Adah nafi son ace, babu wata mace a tare da shi ko a gidan nan sai ni kadai,
Matar da take kira da Adah tace kar ki samu damuwa, yanzu kifara kawo wanda zan fara zuwa dashi mu gani,,

Yau manyan matane ke girki, a gidan don haka ta kasa ta tsare, taki gusa daga falon tana zaune don zan iya cewa a nan ta wuni ranan,
A gajiye ya dawo gidan daga office don haka yau sai a hankali,
Salawatu sai rawan kafa ta keyi da don ta na haka kada wata daga cikin mu ta samu kafan shige mashi,
Ya shiga yai wanka ya fito duk muna daki babu wace ta fito, daga cikin mu,
Hakan yadan sashi fara dube duben kofan shiga dakunan mu a lokacin,
Anty Sadiya akai sa,a tafito daki a lokacin don tai mashi sannu da zuwa,
Fuskan Sallawatu yana kicin,kicin, don may Anty Sadiya zata fito gaida maigidan,
Ita ko Anty Sadiya kar take kallon ta don ta fahinci may take nufi da daure fuskan da tayi haka nan ,
Cikin irin sakin fuska shi da ba wani fara,a yace Sadiya ya gidan dai,?
Yana saye da doguwar jallabi????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ya a jikin shi kafanshi plat shoe's din mazane,
Direct part dina ya dosa a lokacin don ganin halin da nake ciki,
Wani kunci Salawa taji ya rufe ta tabi bayan shi da harara,
Komawa tayi saman kujera ta zube don takaici, da bacin rai

Ina zaune Tv na yana aiki na kai Africa TV 3, suna program na addu,oin marance,
Daga gurin da nake a zaune ina dan bin su a hankali, kamar yadda suke yi idona a lumshi,
Kamshin turaren Yaya Abubakar ne ya daki hanci abinda ya haddasa min bude idon nawa a hankali,
Cak muka hada ido dashi yana tsaye kallo guda nai mashi na gane cewa tun dazu ya shigo kena, don har yai shirin fita sallah magrib can kasan mu
Kokarin gyara zamana nayi ina cewa sannu da dawowa Yaya,
Ya an,sa da cewa,, lafiya kike daki bangan kin fito gaidani da dawowa ba ?
Lafiya lau Yaya na ba shi ansa da hakan ina cewa, wani program ne ya dauke min hankali ban san time yayi ba,
Ya maida kallon shi ga tv don yaga kowani tasha nake kallo,
Kan shi ya juya, yana cewa ai ina ce ko har yanzu jikin ne ?
In ce mu tafi asibiti hakana dai,
Na girgiza kaina da sauri ina cewa, ai naji sauki yaya don ko alaman fever na daina jin sa yanzu,
Ya ce ni zan fita zuwa massalaci saina dawo,
Allah ya tsare hanya nace tare da fatan adawo lafiya,
Har ya kai kofan daki na na manta Yaya mun fa gode Allah ya saka da alheri Allah ya umfana dukiya,
Murmushi yayi daga gurin da yake tsaye yace har ta sanar da ke, ke nan ko ?
Nace Yaya kasan abin dan uwa ai yadda yake ko ?
Daga haka ya sai kai ya fita dakin fuskan shi dauke da murmushi,

Sallawatu wace ke zaune ta hau tayi fan a motar kishi,
Sai faman jijiga kafa takeyi tana leken han fitowa daga part dina,
Hango shi da tayi tafe, yana dan murmusawa, yasa ta mikewa tsaye,
Kafin ya karaso gurin ta, ya kara daure fuskan shi tam, do ya gane nufin ta tun daga nesa,
Dan dabur cewa tayi tana ce har kafito ga time ma yana son ya kure maka,
Batare da yai magana ba ya sa kai yabar gida tare da turo kofan shiga falo,

****** ********** ******
A bangaren Mama Ladi Yaya Abubakar yakira ta sun gaisa yake tambayan ta akan zancen haihuwan Samira,
Sai cewa tayi dama tana son fada mashi cewa ya turo da abinda za,ai mata, hidima dashi,
Don dai yasan cewa yanzu ita bawai wani karfi ne da ita ba,
Kuma gashi haihuwan Samira na farko ke nan a gidan,
Don haka kaga ba karamin sha,ani za,a yi ba ke nan don haka katuro da abin kwarai,,
Yace to Mama zan turo ma Baba Wadda sai ya kawo maki,
Sai naga sakon ke nan ta fada kai tsaye kamar mai fada a lokacin,
Suna kashe wayan ya numfasa tare da lumshe idon shi, don lamarin Mama yana bashi, mamaki sosai,
Don ita ko diyan da ta haifa bata barsu ba sai tai mashi nasu kalan,
Sam ko yan uwan haihuwan shi,mama bata kauna yai masu wani alheri a tsakanin su,
Don sai dai sakon yafito ta hannun ta dole saboda tadan samu ta tsankwara,, daga ciki,,
Amma yanzu wanan shawaran da Meenatu ta bashi haka zai dinga yi a tsakanin su,,

Bayan ya dawo daga sallah ne, Salawatu wace ke zaune daga bakin gado,
Ogana ina son zamuyi magana da kaine please idan har ba damuwa,
Ba tare da ya kalle taba ya natsaye daga bakin wardrobe yana ciro kayan da zai saka a jikin shi,
Gaskiya Ogana ina son inyi request a wurin ka irin yadda kaduty kana shiga wani daki please,
Da sauri ya juyo yana mata wani irin kallon mamaki,
Yace are you out of your mind,,
Ta dan fadi a hassale, da cewa gaskiya mind dina is not styling idan kana haka,?
Ya ce so da wanan kika shigo min gida ?
To dakata kiji bazan yarda ki kawo min matsala acikin family na ba,
Ke da su wa ya fara shigowa gidan nan first ?
A hankali, tace sun rigani zuwa gidan, gaskiya,
Yace may yasa su basuyi bakin ciki dake ba sai ke ce zaki nuna bakin cikin ki a kan su,,
Shiru tayi tana cewa, gaskiya ni bana jin dadin hakan ?
Amma kin san cewa suna gidan ki shigo ko don haka sai kiyi hakkuri amma idan bazaki iya ba hanya a bude yake gaskiya,

Ni dai a ranan kaman nasan yadda sukayi da Yaya Abubakar,
Haka kawai naji ban son fita falon kamar yadda ya ya umurce mu dayin haka kullun,
Sai ma da na tabbatar da suna falon a lokacin na mike don in gabatar da Sallah da na idar kuma zan kwanta ne kawai abina,
Saboda irin yadda naga take taken ta tun da rana yasa nace barin kama kaina,
Ina kokarin shimfida sallaya Salawatun da kan ta tashigo dakin daga kofa tadan tsaya tana ce min Oga yana magana da ke a falo wai,
Nace mata cikin alaman nuna ina sallah da cewa uhum, uhum,
Ta juya batare da tace komai ba ta nufi fallon don ta sheda mashi cewa ina sallah,
Bayan na idar na kawo nafilfili na dora akai, dafa bisani kuma nazauna naci gaba da yin addu,oi na,,,
A takaice dai sai da na ga time ya kusa na barin falon yasani tashi don in tafi falon,
Idona ya fara kawai ga kayan dake saman table din a cikin ledoji guda uku duk da alama iri dayane,
Kamar kullun na nufi kasan carpet na zauna irin yadda na saba yi,
Sai da ya gama tura sakon nan shi a,system yadago kai ya dubi time yana cewa,
May kika tsaya yine haka baki fito ba yau da wuri haka ?
Nace, Sallah na gabatar Yaya sai kuma, na tsaya nadan watsa ma jikina ruwa,
Ok kawai ya furta, tare da kokarin jawo ledejon dake gaban shi,
Inda Anty Sadiya take yace kizo ki zabi guda daga ciki,
Anty Sadiya tamike tazo gaban table din ta mika hannu ta dauko wanda tagani can daga karshe,
Sai ya juyo gurin da nake zaune saman carpet ya ce oya zaki zaba ko ?
A lokacin ne naga Sallawa tana wani kada kafa, kamar yadda idan ran mutum ya baci yake yi,
A hankali na dan karasa bakin table din na dauki ledan dake gabana,
Tare da cewa cikin wata irin murya mun gode Yaya, Allah ya kara dukaka,
Naji lokacin da Yaya yai wani irin ajiyan zuciya tare da cewa hmmmmm,
Sai ya juyo gurin Sallawa wace ke ta wani irin taunan baki tagefe tana karkada kafa,
Ta mike, jiki ba kwari zuwa gaban table ta dauki ledan karshe din ,
Nikan ina zaune na jingina bayana ga kujeran da nake zaune a kusa da shi,
Kafana yana daga mike ina karkadawa a hankali batare da ma na kalli ledan ba,
Hankalina yana gurin TV da,nda suke wasan tseren ruwa,
Karan bude ledojin da ke gefen su nake jiin suna tayi,
Nidai ban bude ba sai ma mikewan da nayi a hankali ina cewa zan kwanta sai da safen ku,
Na mike tare da daukan leda na wanda Sallawatu ta kura,wa ido kamar tana son ta kwankwance abinda ke cikin Ledan nawa,
Nikan ina shiga daki, na aje Ledan saman mirror dina na rufo kofana na kwanta kawai,
Sai da na jero addu,oina na shafe ko ina na jiki na sanan na jabargo na kwanta,

Barci na soma yi amma sai nake jin kamar hayaniya daga cikin gida,
Tun ina daurewa har yakai na bude idona inajin muryan su su uku ana ta masifa a tsakani,
Saida yaya ya daka masu wani irin tsawa su kayi tsit gaba dayan su,,,
Magan ganun da nake ji jefi,jefi a kan ledan kayan da yaya ya siyo muna ne sukeyi,fada,
Don naji anty Sadiya wace bata magana ma ko banza tana cewa daga kawai,
Nshiga kitchen dauko ruwa zaki canza min leda an fada maki cewa ban gane kallah roban man dake ciki bane,
Tsuki nayi kawai tare da gyara kwanciya na ina mai jin haushin su a zuciya na,



Afuwan yau ba yawa sosai please,,,,,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA,,
[8/15, 10:46 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-RAQEEB,,,,

Alheri, Rahama Ni,ima, Gafara, Daukaka, Daraja, Baiwa Dake a cikin wanan Watan mai albarka ya Allah muna rokon ka , ka sada mu da shi gaba dayan shi,,,,=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?


Yau Anty Sadiya ce da girki, don, haka na tashi tun da safe na fara gyara gida,
Kagin kowa ya tashi ko ina na gidan mu sai kamshi ya keyi,,
Ko da Sallawatu tafito don ta sa girkin breakfast ta samu kitchen din mu na wani irin kyali saboda yasha gyara don har store din kitchen sai da na sharo,
Gaba dayan su duk wanda ya fito sai ya ja ya tsaya don mamaki, saboda gyara shine gida,
Dining table din mu har kafafuwan shi sai da nagoge su tas, don tun daga nesa zaka gane hakan,
Wai duk wanan aikin da sha babu ko mutum daya da ya fito daga cikin gidan a lokacin,
Na kare na koma dakina don in yi wanka indan sarara,
Na dade zaune a gaban mirro ina gyara jikkina tare da yan shafe ,shafe,
Sai a lokacin na hango ledan kayan da Yaya Abubakar ya bamu adaren jiya,,
A hankali da gurin da nake na mika hannu na bude ledan don inga abinda ke ciki,
Sabulai ne na wanka da man shafi,masu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login