Showing 165001 words to 168000 words out of 388021 words

Chapter 56 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9569

bane intentionally, kawai dai haka Allah ya kawo,
Ta dan dafani a hankali tace don Allah don Annabi Meenat kiyi hakkuri, sherin shedan ne,
Nadago idanuna na kalle ta sai naji tausayin ta ya kamani
Nace Salawa ina iya kokarina inga cewa inawa ko wacen ku biyayya don babu sa,a ta acikin ku,
Ta dago idanunta sharkaf da hawaye tana dubana dasu,
A idon nata sai naga babu alamar yaudara cikin su,
Nace a hankali komai ya wuce insha Allah Allah ya yafe muna baki daya,
Ta ansa da fadin nagode,
Sai naga taci gaba da rusa kukanta hankali a tashe tace,
Meenat Yayan ki ya dauki zafi dani sosai don yaki saurare na kamar yadda ke kika saurare ni,
Nace kiyi hakkuri zai sauko shima insha Allahu,
Ta kara cewa ta gode alokacin datake mikewa tsaye don barin dakin nawa,
Daidai lokacin da Maman Bi,u ta shigo dakin tana ma Salawa kallon mamaki,
Sallawa na fita Maman Bi u ta karaso gareni cikin damuwa tana cewa may wanan yazo yi gurin ka, ?
Tanayi tana dan duduba min jikina tana yi kamar tana neman ganin wani abu,
Mama tace Meena Meena kayi hankali fada wanan matan mugune sosai wallahi,
Wanda yai ma dukan har ciki yafita may zaizo yi gurinka kuma don dadin baki,,,,
Nadan murmusa nace Mama na sani nima dai don har dakina tana bani hakkuri,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[8/20, 10:09 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- WADUDU,,,

YAN UWA MUSULUMAI BARKAN MU DA WANAN RANAN MAI TARIN ALBARKA,
YA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMARKA
YA ALLAH KA SADA MU DA NI,IMAN KA
YA ALLAH KA SADA MU DA DARAJOJIN KA
YA ALLAH KA SADA MU DA ALHERORIN KA,
YA ALLAH KA SADA MU DA GAFARAN KA,
YA ALLAH DARAJAN WANAN RANA KA SAUKE MASU CIKKAKAN MU LAFIYA,
YA ALLAH WA YANDA BASU SAMU HAIHUWA BA ALLAH KA BASU,
YA ALLAH MASU MAZA ALLAH KA KARA MASU ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAN HANKALI,
YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA KA BAMU MAZAJE MASU ALBAKA GA DUK WACE MA BATA DA,,,
YA ALLAH KAI MAI,JIN KAN BAYINKA NE,ALLAH KA ANSA MUNA WANAN ADDU,OIN,
KA SA MUNA JIN TSORON KA AZUKATAN MU KA BAMU IKON BAUTA MAKA
BAUTA MAISTARKI YA ALLAH
YA ALLAH MUN GODE MAKA MUN GODE MAKA DA KA YO MU MUSULMAI,
ALLAH MUNGODE MA
ALLAH MUN GODE MA,
ALLAH KABA MU IKON CIKAWA DA KYAU DA IMANI,
ALLAHUMA AMEEN=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?


Kayan fruit's masu yawa Yaya Abubakar ya sayo min kuma na sha su so sai, ba kadan ba
Naji dadin shan wanan fruit din da nayi don bakina yai min dadin test,, yanzu,
Ganin na samu lafiya Maman Bi,u tace zata koma gida su kwana guda kawai tayi a gidan mu din,
Gadiya sosai mu kai mata inda ita kuma kafin ta tafi sai da ta kara jamin kunne akan Sallawa, din,
A lokacin da Mama zata tafi sai naji kamar a ce kada ta tafi gidan su anan zamuyi ta zama tare da ita,
Tafiyan ta yasa na dan kara mikewa don kauda kadaici, na
Ina zama ina kallon tv ina dan fita ina gyaran daki na,
Da neman abinda zanci wa raina don ban girkawa gaba daya, gidan
Ba,don komai ba sai ganin irin yadda har Anty Sadiya wace na ke gani kamar ta saduda, ashe har yanzu tana dani rike a zuciyar ta,
Ta na min daukan kishiya a cikin rayuwan ta boyewa kawai take min,
Sai da nai wanan ciwon na,kara sanin halin kishiya da kyau,
Tsakanin Salawatu da Yaya Abubakar, wasan yar boya akeyi a gidan,
Don haka bayan tazo dakina tai min magana akan inyi hakkuri aikin shedan ne,
Sai ta bani tausayi sosai shigowan Yaya Abubakar dakina nake ce mashi don Allah yayi hakkuri abarwa Allah komai haka Allah ya kaddara, abin zai zo,
Cikin wani kallo mai kama da hararan shiga hankalin ki tare da wani irin tsawa Yaya Abubakar ya daga min hannu yana ce min in masa shiru,
Ni na aje masa ita ko shi ya aje ta da zan gwada mai yadda zan yi, da gidan shi,
Kamar ruwa ya ci ni ban kara ko daga kaina ba tunda ya fara fadan shi kaina ya na a duke har ya fita, daga dakin nawa,
Inda nima ya kara daukan zafi dani sosai don sai ban kara ganin sa ya shigo ba,

****** ********* ******
Iyanzu gidan mu komai lafiya ba wanda ke da lokacin wani,
Idan gari ya waye maza sai su fita gurin neman kudi
Don duk yawancin Iyayyen mu dan kudin da Yaya yake turo masu dubu hamsin hamsin sai suka dan fara sana,ar dogaro da kai da shi,,,
Daga haka yanzu gaskiya abubuwan suyi dama sosai a gidan,
Mama Ladi izuwa yanzu abin Yaya Abubakar ya fara daure mata kai sosai,
Gashi tayi tayi dashi da ya saki Meenatu amma yaki sai ce mata ya keyi akwai abinda yake jirane,
Idan lokaci yayi ai zai sakeni din,
Ita kuma tasha alwashin cewa bazata yarda ta hada da irin zurian mu a cikin iyalin ta ba,
Babana yanzu yan buga bugan shi sun kara yawa don yakan tafi kauye ya sayo abin da zai yi saurin shiga idan ya kawo Birni,
Hakan yasa zaka fahinci samun walwala saosai a tare da shi yanzu sama ga farko,

Hajja wace tun bayan dawo wanta kasan bargu wurin bokan ta batai wasa ba gurin ganin ta yi duk abinda ya umurce ta dayi don ganin dodo ya dawo daidai kamar farko,
Yanzu din ko abin yana da dan dama dama don dodon nata iyanzu ya rage yawan langabewan nan sai aukin shan ruwa don yazu duk yadaina yawan shan ruwan nan sosai,
Ta tara daki a kayan masarufi masu yawan gaske amma bata kaunan ta sai abin koda ashirin ne, tafitar da kudi,
Bata kwantuwa ko kadan sai in ya kai mata dole dole zaka ga tafitar da kudin,

****** ********** ******
A gurin da na idar da Sallah don nafara dazun da rana da naga jini ya dauke min,
Nan nake zaune bayan Salah isha,i ina tilawa a hankali,
Nadauki lokaci mai tsawo ina karatun don babu abinda zanyi, a lokacin,
Anty Sadiya itace da girki, a ranan bayan gama abincin tane, ta gyara guri sama sama,
Aikin duk ya kai mata ko ina sai faman fada takeyi a cikin zuciyar ta,
Tana cewa ita bazata iya wanan aikin wahala ba gaskiya,
Yaya Abubakar ya zauna don ya ci abinci da ta girka masu,
Ga ido abincin ya bashi sha awa sosai har yana jin dadin ganin ta, ta iya girki haka yanzu,
Tun gurin diban abincin zuciyar shi ta fara tsinkewa,
Don yana saka hannuwan shi yaji tuwon yai ruwa sosai,
Bai so ba ya,kai ga bakin shi don azaton shi miya zaiyi dadi yasamu tuwon ya wuce mai,
Ai da sauri ya dawo dashi ya kalli gurin da take a fusace yana cewa yo ga tsiya,
Manene wanan haka Sadiya ?
Sai ta tsuke fuska tace abinci mana ,
Abinci fa ki,kace ?
Yanzu saboda Allah Sadiya shekarunki da zaman ki yar hausawa kuma tallaka ace wai baki iya tuwo ba kamar ki, ?
Ya mike kawai ya sa kai ya wuce sama abin shi batare da ya juyo inda take ba,
Sai cewa Sadiya tayi yanzu saboda Allah menene laifin wanan abinci dai ina dai tuwon ne bai yi karfi ba kawai,
Saidai Itama da kan ta tana kai loman tuwon a bakin ta sai ta tsuke fuskan ta,
Sai a lokacin ta tuna cewa bata saka maggi a miyan ba fa,
Mikewa tayi tabar gurin tare da tatara kwanonin ta,
Daga dakina bayan na tashi yunwa ya isheni don haka na,fito neman abinda zanci,
Naga kula a rufe sai na bude tuwo na gani na shinkafa, saidai tun ga idona tuwon yai min ruwa tuwon sosai,
Amma da yake ina son ci sai na yanka hakana na zubu miya mai yawa kin san mu mutanen hausa da son miyan vegetables,,
Nazo saman dining na soma ci loman farko da kyat na samu na hade shi ya wuce,
A take na kara kallon tulin abincin da ke gabana sai naji wani iri,
Ga wani amai da ke taso min kamar zan kife, don gaba daya na ji zuciya, na ya rufe min ban da sukuni ko kadan,
Da gudu na mike zuwa dakina, kafin in kai bathroom har na fara shekashi, a hanya,
Na dauki lokaci duke ina zuba amai gurin sanan na mike daga tsugunen da nake ina cewa wai, wai ina maida numfashi,
Sam ban san cewa Yaya Abubakar yana tsaye kaina ba sai da na juyo don komawa bedroom dina,
Ya na tsaye hannayen shi harde a saman kirjin shi fuskan shi babu walwala a cikin ta,
Wani kallon tuhuma naga yana min ya, ce mai yasamay ki may kikaci ne haka,?
Ina kokarin goge fuskana da haban rigana sai kokarin kaiwa saman gadona nake yi a lokacin,
Har inda na zube saman gadon ina cewa wai, wai Yaya ya tako yazo ya tsaya a kai,na yana cewa
May ke faruwane haka wai ina tambayan ki ne fa don dai ba zazzabi bane ko, ?
Da kyat na iya daga mashi kai nace ba zazzabi bane kawai dai, abinci naci shi zuciya na ya tashi,
Cikin karaji ya tambayeni wani abincin badai wanda Sadiya ta girka ba ko,
Na daga kai alaman shi daidai lokacin da nake kokarin gyara kaina ga filo,
Sai kuma naji tankar wani aman zaizo min take na mike zaune da sauri aiko aman ne na nufi bathroom,
Sai da na samu na amaye guntun wanda ya rage min a ciki sanan na samu saida,
Yaya yana kaina sai faman tambayana may zanci yakeyi nace mai ban son komai na koma na kwanta,
Sai sauke numfashi guda guda nakeyi a wahalce ina faman cewa wai, ina juyawa don indan ji dadi,
Barcin dole ne ya dauke ba shiri ban san inda nake ba,
Tausayi sosai na ba Yaya Abubakar wanda ke tsaye a kaina yana min duban tausayi,
Shima abinci zai fita nema shine yazo ya tambayeni may nake son ci ?
Daga stairs din da yake saukowa yagan ni na f da gudu,
Bayan yasayo min abinci ya samu still ina barci sai ya aje min su a gefen gado na yajawo min kofan dakina, tare addu,a

Acan cikin dare na farka da wani irin yuwan sai nake jin kamar banda ko hanji a cikina,
Kokarin tashi nakeyi in fito don neman abinda zanci,
Sai idona yakai ga ledan da yaya Abubakar ya aje min a gefen gado,
Na mika hannu na na jawo ledan naji dadin ganin abin dake ciki,
Kaza ce gassa irin na modern dinan yaji kayan hadi sosai sai drinks masu sanyi da kuma snacks,
Kamar ance in kashe tocin wayana don na duba kofana nagan shi a rufe duk da haka saida na sa key daga ciki, tare da addu,a nayo fitsari, sai na hau cin kazan ina dan korawa da drinks din,,,
Idan har ba ki manta ba na taba fada maki cewa nataba jin nishin wani abu a cikin gidan mu har sai da nai zazzabi washe gari
A rin daidai lokacin da naji wancan din yau ma haka naji wanan nishi maiban tsoro,
Tankar ana wani irin huci ne na gajiya ko na wahala,
Dama saura kiris in gama don haka nai shiru ina sauraren shi,
Inajin abin tankar bayan gurin parking space din motocin yaya hucin ke fitowa,
A hankali na kauda ledan na dan jawo jikina tso nahaye gado naja bargo,
Bakina yana dauke da addu,oi ina ja idona na rufesu,
Gabana sai wani harbawa yakeyi tankar zai tsage, don tsoro,
Can kamar minti talatin lokacin har barci ya fara daukana
Sai jin wani irin ihu nayi tankar kunnuwa na zasu tsage,
Numfashi na naji kamar zai dauke don tsoro, ihu nakara ji a karo nabiyu abinda ya tabbatar min da acikin gidan mu ihun nan yake,
Ban san lokacin da nakai zaune ba don tsoro sai naji ihun da yafi na bayan karfi mikewa nayi wuf na nufi hanyan fitowa waje,
Bakina dauke da addu,a, daga dakin Anty Sadiya waban ihun ke fitowa cikin tashin hankali,
Ai gaba dayan mu muka nufi dakin nata dai lokacin da shima Yaya Abubakar ya sauko daga sama,
Muna shiga dakin Sadiyan na hango abin kamar maciji tana kokarin fita ta window dakin ta,
Shima yaya Abubakar ya hango wanan abin da idon shi ,
Sadiya tana tsaye hannuwa a kwandare kamar mahaukaciya sai ihun fitan hankali takeyi,
Da sauri yaya Abubakar ya bi abin baya sai dai baiga komai ba,
Ga Sadiya taki barin ihun da takeyi tankar zautata, hannu a kwandare mata,
Yadawo ya samay mu adakin ina ta tofa mata addu,oi
Shiya kamota yashiga karanto mata ayar Allah sai kallon shi nake yi da mamaki don zakace ko wani alaramma ne,
A hankali nake bin abinda yake karanto mata daga inda nake zaune gefen su Sallawatu tafado dakin a firgice tana cewa,
May ne may ke faruwa ne, wai ?
Hannu yaya ya daga mata batare da ya tsaida karatun shi ba yana mata alaman tayi shiru,
Muna tsaye cirko cirko sai mukaji Sadiya tafara nuna karkashin ta tana cewa a cece zai shige mata a gaba,
A lokacin ji nayi tankar in tsula buli don tsoro daga gurin da nake, tsaye,
Da sauri yaya yace a dauko mashi waya adakin shi,
Daga cikin mu ba wacce ta motsa don tsoro ganin Sallawtu ba zata ba dole na mike don in tafi,
Muryan shi naji yana cewa dakata in tafi nai wani dadeba ya dawo alokacin yana kokarin kiran nomban wani,
Ashe mijin Fattu ce ya kira sai yafita da suka iso ya bude marsh kofan shigowa,
Tare da mama suka shigo tana tambaya cikin damuwa may ke faruwa ne,
Mama ce ta karasa gurin da yake rike da hannayen Sadiya da sukq zage a lokaci guda tankar ta taba ruwan zafi,
Bayani yaya ke masu suma duk hankalin su a tashe yake suka kara fita suka zagaya gidan,
Dai dai gurin window abinda suka iya gani shine tankar wani abu mai mai yabi gurin da jan jiki,
Dole suka dawo aka dauke ta zuwa asibiti sai kokarin bude zanin ta takeyi wai abin yana nan yana kokarin shige mata a gaba,
Tsoro duk ya kara kama mu a lokacin don haka akace Baba Hamza' ya tsaya atare da mu gida su kuma sai su tafi har mama,biu
Mama itace bayan motan zaune tare Sadiya wace take tankar zautata,
Mama tana rike da hanayen ta duka biyu tana tofa mata addua,
Sun isa asibiti ba su gane komai ba sun daiyi mata alluran barci tare da cewa lafiyan ta kalau subari idan ta tash aga reaction din ta,

Wanan abin yai mugun tayar wa kowa da hankali don abune na sihiri,
Har safe muna zaunr a babban falon zaune kowa da abinda take sakawa akai
Nidai a halin yanzu gaskiya gida nake son yaya Abubakar ya maidani
Don kwata kwata duk garin da ya fita raina sam ban son zama
Jinkiran sallah yasamu mikewa kowa ta futa zuwa sallah,
Bayan na idar na shiga kitchen na hada masu breakfast don akai masu,
Batare da tunanen komai ba na kira baba Hamza nace ya kai masu asibiti na bashi key din motan da mukan fita da ita anguwa,
Sosai sunji mamakin ganin yadda na aiko masu da breakfast a cikin lokaci,
Abin da ita kanta Sadiya amatsayin ta na babban a gare ni batai tunanen yi ba,
Yaya Abubakar hankali duk a tashe, yake don abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali,
Duk abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali gashi ba kowa akusa da mu, sai, abokan arziki,
Yaji dadin yadda su Maman Biu ke gwada muna mutunci, abinda farko su da Sadiya basu san cewa zaman lafiya da makwabta yana sa azama daya,
Sai yanzu da farko yaso ya hanani hurda da su amma sai yaga idan ya hanani bazan so ba sai ya kyaleni kawai,
Sai gashi daga baya zama dasu yai mashi dadi sosai tunzuwan Mama Ladi jinya
Dakuma kwanciyana asibiti sai gashi kuma yanzu sun mashi wanan halarcin ,
Don mijin Fattu shike ta zirga,zirga a cikin asibitin,,
Saboda shi yaya duk jikin shi yai sanyi sai faman tunane yakeyi barkatai,
Babu abinda ya ke mai yawo azuciya kaman wanan dodon sihirin da yaga fitan shi daga dakin Sadiya,
Don da bai gani ba da sai yace kila dai mafarkine ko wanu abu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login