Showing 192001 words to 195000 words out of 388021 words

Chapter 65 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9528

itace tauraruwan gida agare su,,
Nace wallahi anty wanan maganan naki haka yake ba wai ba, don tun ina gida nake ganin haka ga mazajen garin mu,,,
Munyi sallama ba don munso ba saboda Uncle danaji muryan shi ya shigo wurin anty

****** ********** ******
Ido a rufe Salawatu ta isa gidan Lubuna, wace ke kokarin shirin fita gurin aiki,
Da mamaki tabi salawatu wace ta wuce direct saman kujera ta zaune rai a bace ,
Tsaya tayi tana kallon aminiyar nata duk da tasancewa ba lafiya ya fito da ita gida ba da wanan safe haka,
Kuka Salawatu keyi riris kamar karamar yarinya, kamar ranta zaifita,
A hankali Lubuna ta taka zuwa gare ta ta dafa ta cikin tausayawa tace,
Wai may ke faruwa ne haka Salawa ni baki fada min abinda ya faru ba kin barni a duhu haka
Cikin dan tsagaita kuka tace Lubuna Oga ya wulakantani ya cuceni don ya ci min mutunci agaban kowa nagidan
Wani irin takaici Lubuna taji tai tsaye tana ma Salawa wani irin kallo,
Tace gaskiya Salawa ban san irin ki ba wallahi shin Oga Abubakar ne namiji kadai a duniyan nan, ?
Karki manta ko yau ya sake ki zaki samu masoya da yawa to may zai saki dinga wahalas da rayuwan ki akan shi haka wai,
Bafa kwantai kikayi ba Salawa, kece dai da irin nacin ki kika lake masa,
Har yana jin dadin wulakan ta ki yadda ran shi ya so a gaban kowa,
Auren sa fa ba dole bane idan zaki rufawa kan ki asiri ki rabu dashi kirufawa kanki,
Ki gwada mashi cewa kema fa din mace ce mai aji sosai,
Kai ta daga tare da kallon Lubuna tace, ke ma kin san cewa ina son Oga ba zan iya ba sam, don shine kadai zai iya hakkuri dani yadda nake so,
Lubuna ta tsuwa Salawa idanu tana kallon ta acikin takaici,
Can tace saboda wana yarinyan ce again ko yai maki wani abu,
Tace wallahi kanan kin sani fa don tane yai min cin fuska tun a daren jiya yafara,
Don nace masa ina son cin shawarma, nako wani irin piza ne sai ita ma tace wai ya sayo mata Ice cream da fresh Fruit's ,
Bayan yadawo naga bai sayo min ba maimakon nida ce mai ina so ya fara zuwa guri na kuma fa nice da duty a ranan sai kawai ya nufi gurin ta dakin ra ya kai mata nata sakon,
Da naji shiru shine na bishi tundaga can muka fara fada dashi wai don maye bazan jira shi har yazo ba,,
Cikin takaici Lubuna tace you see akan karamar yarinya kina ganin wulakanci, haka,
Yanzu dai tunda har ya kai ga haka ai sai ki kara zage damtsen ki,
Don dama matan hausawa dinan kina ganin su haka wallahi is not easy kafi karfin su ,
Mistake dina shine da ban bari sai jima da fitaba sai kawai na samay ta kitchen daniyar inci mata mutunci sosai ashe yana gida bai fita ba,
Yaji irin yadda na dinga zagin iyayyen su da kakan su wanda ya bashi auren yar iskan yarinyar,
Yanzu dai dakata kiji inji Lubuna wace ke kokarin kawai, zaune gefen hannun kujeran da take a zaune,
Tace yanzu fa dole ne sai mun mike tsaye so that we should rideout that foolish girl away,
Salawatu ta ce hmm kin dai sai koda yaushe ko nawa nake kashewa akan irin hakan amma abin yaki,
Murmushi Lubuna tati tace Salawatu ke nan ai yanzu tunda har kina son shi haka dole ne sai mun dage sosai don mu kwata maki shi,
So kada ki damu ki dan bani time kadan please akwai inda zan tafi maki,
Sai dai yanzu dole ne mu samu mu dan lalabashi ki koma dakin ki,
Salawatace bakiji may yace bane cewa fa yayi sai natafi har garin su naba wanan witch din tsohon hakkuri,
Da wani irin karfi Lubuna tace WHAT ?
May yake nufi da hakan impossible, hakan ma ba zai yuyuba gaskiya,,
Tace dole ne mu samu mutane anan wa yanda yake tare da su , subashi hakkuri gaskiya amma idan yace wai sai kin tafi can ai bai kyauta muna ba,
Kuma wallahi yan uwan shi zasuyi hating naki ne sosai har ma yaran ki idan kin aihu dashi,
Wani irin ajiyan zuciya ne Salawatu tayi tare da ce o,o wallahi Lubuna nayi hating din wanan yariyan sosai ,,,

****** ********* ******
Tun lokacin da wanan abin yafaru yaya Abubakar yake jin wani irin zafin Salawatu a ran shi har yake ji gara kawai ya sallamay ta tafita daga rayuwan shi don shi gaskiya bazai iya zama da macen da ke zagin iyayyen shi ba haka,
Yayi nadama sosai ga hanashi da malam tsoho yayi amma ya dage akan sai yayi,
Yanzu gashi baida kwanciyan hankali ko kadan da ga gare ta, duk ta hana gidan shi shakat,
Yasan cewa babu wanda zai tunkara da wanan zancen , dole ya daukan wakanshi mataki akan fitinar ta,
Driving yakeyi amma hankalin shi tankar baya a jikin shi a lokacin,
Wayan shi tai kara sai dai bakuwar noba ce ya gani don haka ya dauka da sallama,
Saidai murya mace ce yaji bayan sun gaisa tafara bashi hakkuri a kan case din su da Salawatu,
Dif ya katse layin tare da sake guntun tsuki, yana cewa a fili rubbish ,
Yashigo gida a gajiye ya nayin tafiyan shi mutum zai gani ya fahinci hakan,
Muna zaune gaba dayan mu a falo muna kallon wani season film na hausa,
Jin shigowan shi yasa gaba dayan mu muka,waiga don ganin mai shigowa,
A irin yadda ya samay mu zaune a falon har Ramatu mai aiki yasa shi jin dadi,
Duk da dai ba wai fira mukeyi ba amma yanayin zaman mu ya nuna kwanciyan hankali,
Mikewa nayi daga inda nake zaune, don zuwa gurin shi in karbi case din shi,
Ya zuba min ido daga inda yake a tsaye har lokacin da na iso gare shi,
Sannu da zuwa nai masa tare da dan rusunnawa kadan,
Murmushi yasaki tare da sauke a jiyan zuciya yace Ya gida Meenatu,
Alhamdullahi,
Daga gurin da Anty Sadiya take a zaune ta mashi sannu da zuwa,
A daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana mai cewa wassh Allah na duk na gaji wallahi,
Ina saukowa da part din shi nahango shi zaune afalo tare dasu Anty don haka na shiga kitchen, na dauko mashi ruwa, a gora tare da dora cup a ture din,
Ina tafe cikin bakar jallabiya mai fitar da sharp, din mace
Zakace ko wata yar larabawa ce, rigan yasa ina tafiya kamar da gaiyya nake rausaya ,
A gaban shi na aje ruwa a saman stol din dake gefen shi,
Zan dauki ruwan da nufin in tsiyaya mashi a cup yace No barshi kawai kawo goran,
Nayi saurin dago kaina na kalle shi da mamaki nace abar cup din kuma,
Ya daga min kai kawai alamar eh,
Daga haka ya dauka ya kafa goran a bakinshi bai cire ba saida ya kwankwade, shi gaba daya san nan ya aje goran a saman tire din yace min ya gode tare da dan lumshe idon shi ya koma saman kujeran ya zauna,,
Nadauki turen da cup na mayar kitchen na wurga gora a dustbin,
Ramatu tamike a hankali don tabar falon saboda ganin yaya Abubakar azaune,
Yace No dawo kawai ki zauna abinki zau hau samane ni,
Daga gurin da Sadiya take a zaune take cewa, maganin ta na sha ya kusa karewa fa,
Yace ok zan tura Baba Wadda da Hamza gobe insha Allahu su karbo maki,
Daga haka ya mike zuwa sama yana mai rike karfen da akai matagalin steps din dashi,
Bayan shi nabi inda muka hau steps din a tare dashi don a tare muka shiga dakin,
Daga gurin da Anty Sadiya take tabimu da kallon tare da sauke ido da sauri tana mai tabe baki,
Ramatu na gani haka tai saurin kawar da kanta daga kallon ta ta ci gaba da kallon tv abinta,
Amma can kasan zuciyar ta mamaki takeyi na yadda nake ma Anty halarci amma akwai burboshin kishina a zuciyar ta,
Muna shiga daki na riko Yaya Abubakar tabayan shi na rungumo shi, tare da sauke ajiyan zuciya,
Naji ya sauke ajiyan zuciya again akarona barkatai kenan tun shigowar shi,,
Hankali cikin wani irin murya nace, Yaya Abubakar ka yi hakkuri damu please kasan mata sai hakkuri,
Yaya yadan yi wani jim kamar yana tunane, sai naji ya juyo dani ta yadda zamu fuskanci juna, da shi,
Kai minkiss yayi a goshi yana cewa Meenatu bana son fitina arayuwa na sam wallahi,
Nakara dan narkar da murya na nace yaya kayi hakkuri don Allah ka yafe muna please,
Yasa dan ya tsanshi a saman lebbana ya ce Shiiii alaman inyi shiru kawai,
Yace gaba dayan ku nasan halaiyan kowan ku don haka nasan abinda nakeyi,
Ina judge din kowa akan laifin shine, bazan yarda da yawan fitina ba agida na, sam,
Azuciya na ce ashe zancen Anty Amarya gaskiya da tace koda namiji baya gida ya kan fahinci halaiya iyalin sa daya bayan daya,
A hankali na ke kokarin zamay jikina daga rikon da yai min ina cewa barin hada maka ruwan wanka ,
Ya ce no ki barshi idan natashi zan hada da kaina,
Ya shiga shinshinan wuyana har zuwa wasu part na jikina yayin da na lumshe idon cikin wani irin tsiga, yarrrr da na ji,
Kokarin juyawa na keyi don barin dakin, naji ya riko min hannuwa ,
Najuyo muka hada ido naga idanuwan shi sun kade sunyi jawur,
Nai saurin kauda idona daga gareshi sai naji yana rada min a hankali haba, Meenat,
Ya kuma zaki wuce ki barni bayan nasan cewa kinzo ki ga farin ciki na,
Na dan sunkayar da kaina kasa cikin jin nauyin shi nace bazan tafi bane girkine sa ban sauke ba nake son zuwa na sauke kada ya kone,
Na san ba dai ya yarda bane, just kawai yabarni ne in fita kawai,

****** ********** ******
Salawatu da Lubuna agaban malamin su a zaune,
Lubuna ce bayan sun gaisa da malamin nata take cewa,
Boka ko malam mun zone gurin ka dama wanan kawar tawace ke da dan matsala da mijin ta shine nace muzo gurin ka, da ita ka duba mata,
Don Allah ina son ka taimaka muna ai mata aiki mai zafi wanda zai girgiza abokiyar zamab nata.
Boka ko malam yai murmushi yana mai gyara zaman shi tare da duban shi yana cewa,
Yanzu may kike so ai mata a rabata da gidan ko a haukatata ko a barta a dambalata kawai,
Salawtu tace ai matsalan shine, zuri,an su guda mana,ana gidan su guda don iyayyen su gudane,
Amma in akwai yadda zaa ayi na mallakeshi ni kadai zan so hakan gaskiya duk su sauran biyu ayi waje da su,
Murmushi Boka ko malam yayi yana cewa wanan ai ba wani babban aiki bane,
Nan yashiga yin irin abinsu na bokaye sai da yadauki dan lokaci mai tsawo zuwa can ya dan dago kai ya kalle ta,
Yace gaskiya akwai babban al, mai girma agidan ku,
Don akwai abu akasa zube yanzu haka wanda ba wai lalai kusan da zancen ba a halin yanzu,
Amma yanzu bari muyi binda ya kawo ki kawai saurin idan bukatan su ya taso zaki dawo,
Ga jahilci irin na Salaqatu sam bata fahinci maganar mutumi saboda idon ta yarufe ita dai bukatar ta shine taga an fitar da Meena da Sadiya agidan,
Yace amma dai ita wanan yariyar daga cikin su akwai ta da babban al,amari bawai lalaine kiga yadda kike bukata ba gaba daya,
Lubuna tace kawai Boka malam kafita batun ko ma wacece kai mata aiki akan maigidan ta yadda ba wata agaban ta sai ita kadai kawai,
Salawa da ke daga gefe tace gaskiya hakana ne Boka,
Ni agaskiya idan son samu ne ai masu duk abinda ya dace da kowan su,
Nan suka zube mai kudade masu yawa suka mike suna zabga godiya ,
Shi kuma yai masu alkawari tare da basu time,
Salawatu taji dadin zuwa gurin wanan mutumin don har sai take ganin kamar ai har aiki yaci ko,,

****** ********** ******
Nagama shiri inda ban wani tsaya yau bata lokaci ba don nasan basai Yaya ya sauko ba,
Yau ma kamar kullun don sai da na tabbatar da cewa na fitar da duk wani damuwa daga zuciyar Yaya Abubakar wanda sai faman ajiyan zuciya yake saukewa a hankali daga gefena,,
Kamar wace aka sakowa wani irin amai nan na mike da sauri na hari hanyar bayi yabi ni da kallo acikin maki sai na rufo kofa don kada yaya yajini,
Ganin na rufe kofa yashi sauke ajiyan zuciya don sai yake zaton ai toilet zan yi,
Nafito duk jikina babu karfi yayin da zuciyana ke gaskanta zance Anty Amarya,
Watau cikina yana ajiki a har yanzu bai fitaba kenan abinda yasani kai hannuna nashafa cikin a hankali tare da dan lumshe idona,
Addu,anayi tare da neman tsari daga duk wani sheri ,
Hannun yaya Abubakar naji a saman marana yana dan shafawa a hankali ya na cewa,
May kikaci cikin ki ya rude nasauke ajiyan zuciya nace kila fruits din da nake shane,,

****** ********** ******
Baba Wadda da Hamza sun isa gurin karban magani a nan ne mutumin ke cewa su fadawa yaya cewa sai yazo don fa akwai aiki a gaban shi sosai,,
Bayan dawowan su basu tsaya komai ba suka fara fada mashi sakon mutumin,
Bai samu zuwa a ranan ba sai washe gari ya tafi nan malamin yai masa bayani akan cewa akwai matsalonlin da zasu taso amma sai ya bashi addu a da sadaka da zaiyi don kaucewa fitana,
Suna dawowa mijin Fattu ya fara yin yadda malamin nan bagware ya umurci suyi don tsari agidan,
Nan kuma bayan ya shigo dakin shi yakira malam tsoho ya sheda mashi duk abinda wanan bagwaren ya fada mashi,
Malam ya kwantar mashi da hankali ta hanya nuna mashi cewa, ba wai lalaine abin ya zama gaskiya ba kawsi da yai sadaka don riga kafin masifu masu taso,




ZEEE MAKAWA YELWA
[9/3, 9:36 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 6?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL -MATIN,,,,,

Allah sarki yan uwa hakika Allah da Annabinsa sunyi gaskiya
Inda Annabin rahama ke cewa *Iyyakum Wal Zannah,
Kashedin ku da zato,
*Fa,inal zanan akazabul hadisi,
Do min zato mafi karyan zance, ne,,,,,
Ni Zainab na gode ma Allah da har so da kauna yasa masoya suka jamin barnan suna a lokaci guda,
Wanan abinda wata sister tayi yasa mu, nagane irin dinbin masoyan da muke dasu acikin mu,
Alhamdullahi Allah na godema nagode ma da wanan baiwan da ka bani don duniya tasan dani,
Allah kaine abin godewa domin kowani bawanka da irin hanyar baiwar da kai mashi,
A dalilin online novel na samu masoya da wallahi ban san iyakan su ba,,
Haka kuma nasamu makiya masu son bata min su na a banza banji bangani ba,
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Allah na gode ma da wanan baiwan na ka gare ni, banda abinda zance sai ma in kara godema,
Sai dai ina son ku sani yan zauren beibei Isa wallahi wallahi bakuyi min adalci ba a rayuwa,
Don in ma sanin hali ne ku ya kamata ace kunsan halina don ni wallahi ko a fili magana aikine, gare ni,
Kuma a group ban cewa komai idan kuna hiran ku don gudun batawa wani rai acikin ku don ban san inda zan hadu daku ba mu yafe ma junan mu,
Amma sai gashi kuna fadin zancen da bai dace ba a kaina
Mutun gudace ta bugomin waya tana mai bani magana don a rashin kwantar da hankali kukai min mumunar fahinta,
Don wallahi nasan cewa da zaku kwantar da hankali ku karanta post din da akai ta yawo dashi a kai na da bakuyi min rashin adalci ba, haka ?
Saboda wallahi wallahi banda masaniya akai don ko ita mai posting din ta nuna amadadin tane take wanan zancen,
Sai kawai aka shiga suka na da sara ta ko ina haba dai yan uwa,
Kamata yayi duk wace ta karanta tai zanari kafin ta ce komai akai,
Nafarko ta duba shin daga gareni ni sakon yake ko daga masu karatu da suka matsu suji ni, ?
Masu cewa zasu daina karanta littafina kada ku manta da cewa abin daga Alla ne fa ba yin mutum bane,
Lokacin da mai shi ta dai na karantawa Alokacin ne wasu dubbai za su soma karantawa,, Insha Allah,
Insha Allahu ko Data bazan roka ba don in maku posting, balle kudin waya
Wayana fa dan minor problem ne yasamu na bayar a duba min


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login