Showing 216001 words to 219000 words out of 388021 words

Chapter 73 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9557

bazan dauki rainin hankali ba don baki da ikon da zaki ce zaki kawo min wani doka a gidan nan,
Don kamar yadda kikazo nima din haka nazo babu wani kari akai,
Daga haka ta juya zuwa dakin ta tana sababi cewa wai an raina mata wayo har za,a saka mata doka agida,
Ita ko Lubuna sai zugata take kan cewa ta dauki mataki akai,
Ba bata lokaci ta jawo wayan ta shiga kiran layin maigidan wanda fitowan shi ke nan daga meeting din su na directors,
A gajiye yake yana bukatan hutu a lokacin sosai don haka yana ganin kiran ta har biyu yasa shi daukan wayan a karo na uku, data kira,
Ba kowani gaisuwan kirki sosai bayan cewan da ta yi Hellon Oga ya aiki,
Ya ansa a dan gajarace da cewa lafiya kalau ya kuke lafiya taba da ansa tun a hakan 6asan da magana a tare da ita,kafin ya kai karshe yaji tana cewa,
Sai ji yayi tace please Oga kayi wa matarka magana don ban son abin fitina,
Saboda babu ruwan ta da ni gaskiya ba abinda ya hadani da ita banda zama gidan ka,
Katseta, yayi da cewa please ban son dogon zance may ke faruwa ne,
Nan take gaya mai yadda sukayi da Sadiya a karya da gaskiya, ,
Tana gamawa ya numfasa yace abar zance har yadawo gida,
Yana aje wayan ya kama haba shi ya mai da kanshi saman kujera ya numfasa yana cewa,
Kai family man are not safe for ever, na yau daban na gobe daban,
Yakara lumshe idon shi sai kuma ga kira daga gareni ya shigo wayan shi,
Ya dauka tare da sauraren may zan fada mai ni kuma, bayan ya dauki wayan da fadan assalamu alaikum na ansa ma shi da , nace mai cikin dan tausa murya wa,alaikum salam,
Dan basarwa yadan yi kadan kafin yace Meenatu ya dai,
Nace Yaya na bugo inji ya office din ya aiyuka yau da kullun,
Ya amsa tare da lumshe ido tankar ina gurin a tsaye ya ce, lafiya kalau meenat ,
Yace kin dawo gida ne ko nace gani nan Anty bata gama gyara maka ni ba,
Abin mamaki sai naji ya kwashe da dariya tankar ba Yaya Abubakar din mu ba
Ya ce hakan na da kyau ai kice mata ina mata godiya ina gaishe ta da aiki
Nai murmushi jin dadi tankar yana a gabana nace Antyn Saloon zataji sakon ka, ,
Na kashe murya ina cewa, tsaraban may zan sawo maka idan zamu dawo,
Dariya na bashi yace cikkn lumshe ido bayan naji sautin dariyan shi a kunne na yace,
Ban son komai sai kaunar Yaya nake so yau kawai,
A hankali na bashi ansa da cewa kasamu insha Allah Yayana,
Shima Yaya yace to Allah ya tsare min yar kauna ta Allah ya dawo min dake lafiya nace Ameen Yayana,
Mu kayi sallama na ajewa wayan na kai kallona ga sauran mutanen dake a shagon a zatona kowa tana harkan gaban tane amma sai naga cewa idon da yawan su yana a kaina,
A kwai wata matar da ta girmay min sosai a lokacin da nake wayan sau biyu muna hada ido da ita,
Tana min murmushin kamar ta sanni, da farko don haka muna gama wayan da Yayana sai nake ce ma matar ina wuni Hajiya,
A sake fuskan ta dauke da murmushi, tace, kauna ta kina lafiya ko ,
Nima da murmushin na ansamata da cewa lafiya kalau Anty,
Tace a wani anguwa kike zaune kaunata kafin na bata ansa sai Anty Saloon ta karba da cewa wanan ai babban mace ce hajiya don kishiyoyin ta biyu da kike ganin ta,
Ido waje matar tace what, ita wanan din ke da kishiyo yi,
Anty Saloon tace kuma fa duk sun girmay sosai don ba age mate din ta acikin su,
Matar ta nisa tace amma ba,a gida guda kuke ba ko ?
Anty tace agida guda kuwa kin san halin hausawa basu da tsoro ai su,

A gaban mirror Anty Saloon na tsaya ina karewa kaina kallo irin yarda nai wani irin fresh dani ga wanan gyaran da aikai min tun daga kaina har kafana yasha kwalliya na koma kamar ranan zan tafi aure,
Ita ma Fattu ba a baya ba don tasha irin na ta kwalliyan sosai,,
Wanan matar aka fara gama mawa tafara tafiya,
Zuwa can sai gata ta dawo dauke da ledan a hannun ta tare da katin ma aikatar ta, tace min ita lauya ce mijin ta kuma doctor ne,
Wai nayi kama da kaunar mijin ta sosai shiya sa take ji na tankar kaunata,
Ta miko min ledan tare da karban address dina Fattu ce ta bata full address dina,
Sosai nai mata godiya inda taji dadin godiyan da nai mata sosai,
Muma bamu wani dade ba muka bar shagon zuwa gida inda muka tsaya a wani plaza muka dan yi sayayya,
Sai dai ni babu wani abinda na saya sai abubuwan da nasan na bukatan Yaya Abubakar ne,

A gajiye nadawo gida duk jikina ba karfi sosai don gajiya,
Nasamu Baba Ramatu tai min komai ta sa a kuloli ta aje min,
Na fada dakin Yaya Abubakar na gyara ko ina kamar yadda ya kamata,
Duk da a gagauce nagyara dakin yai kyau sosai yana kyalli da haske ta ko ina na kawo kayan da na sayo mai na sa duk gurin da ya kamata,,,

****** ********** ******
Bayan na idar da Sallah daga gurin da nake zaune na hagon ledan da matar nan da tace sunan ta maryam
Baba Ramatu da taga ina kokarin bude ledan ta karba daga hannu na ta bude min,
Wani irin kamshi mai dumaita zuciyar mai shakanta, ban taba jin kamshin turaren humura ba irin wanan,
A jiki na dan lakata na shafawa jikina don jin kamshin sa,
Abinda ban sani ba shine ashe wanan kamshin ya kai har kofan falon shigowa gidan ,
Yaya Abubakar wanda dawowan shi ke nan daga office saboda sun dauki lokaci yau a office din sosai ba su dawo ba,
A hankali ya shaki kamshin ya dan lumshe idon shi a hakali,
Dakin Anty Sadiya yaso wuce wa amma sai, ya tako zuwa dakina ina zaune ina latsa waya na,
A sanyaye yayi sallama ya shigo idon shi na gareni yana kallon yadda gaba daya na canza mai a fuska,
Sannu da zuwa nai mai inda ya sauke idon shi a cikin nawa yana amsa min tare da dan lumshe idon shi,
Bai wani dade don yace a gajiye yake nasan cewa sauran dakunan gidan zai shiga kamar yadda ya saba don haka,
Yana fita tsam na mike na bi bayan shi ina saye cikin wata doguwar riga mai kyalkyali, har kasa da yar guntuwar hannu iya hammata, sky colour,
Na kara gyara fuskana a gaban mirror idona ya sauka a cikina wanda ya turo ya zauna min cas,
Da sauri na kai hannu na na shafa a hankali tare da lumshe idona,
Ina jin wani irin dadi yana ratsa min zuciya na a hankali,
Wani irin bul, bul bul naji sakamakon shafa cikin danayi,
Alaman dai abin cikin nawa yana canza position din shi sakamakon taba shin da yaji anyi,
Na kara dan lumshe idona tare da tofa addu,a na a hankali, na shafa aciki na,
Ramatu miko min zani daga cikin wardrobe dan Allah dariya naji tayi tace ni dai nasan cewa maganan boye ya kusa baiyyana,
Dora, zanin da nayi saman rigar yasa cikin nawa ya boye daga cikin zanin dana aza a sama,
A falo na hadu da Salawatu wace ta watso min wani kallo wanda nake ganin kamar bata masan tana min ba ,
Saboda ta kasa boye kishin ta agareni don kitson danayi da kumshi yasa na komawata diyar mutanen Sudanese
Maganan da nayi mata yasa ta gane cewa nazo kusa da ita bata sani ba ina cewa, ko da akwai sauran lemo a fridge
No gaskiya ina ga babu ya kare don dashi nai amfani jiya,
Nace ok barin dan tambayin Ramatu inji na,wuce tabi bayana da wani irin mugun kallo,
Na kara dawowa na bi ta gaban ta again wanan mugun kamshin dadin nawa ya kara dakar hancin ta,
Na haye sama stairs din dakin maigidan ina tako a hankali inda takalman kafana ke sake sauti mai dan kara a gidan,
Nashiga da sallamata na samay shi a tsaye tsakiyan dakin yana balle aninaiyar rigar shi,
A hankali na taka bayan shi na rungumo shi ta bayan,
Wani irin nauyayan ajiyan zuciya naji ya sauke, tare da kokarin juyowa ya fuskance ni,
Idanun shi ya zuba a cikin nawa kaman wanda ke son gano wani abu atare da ni,,
Gabana yaba da wani iri hanjin cikina yadan kada don fargaba da tsoro,
Yace Meenatu na amsa a sanyaye a hankali da fadar naam,


ZEEE MAKAWA YELWA
[9/11, 11:23 AM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-MUBDI

Meenatu, kinfini sanin halin mutanen gidan mu a yanzu don haka nake bukatan shawaran ki akan kowan su,
Shiru nayi tare da,sauke ajiyan zuciya don jin abinda yace,
Dan nazari na shiga yi a lokacin don jin may yace don haka sai nayi kokarin dan zare jikina daga nashi na nufi bakin gado na zauna saboda ban iya dogon tsayuwa yanzu kamar da,
Shima a bakin gadon ya zauna yana mai kura min idon shi yana saurare na,
Na dago kaina a hankali nace Yaya malam tsoho dai ya kamata a ce an,gyara mai wanan majalisar tashi yakoma na zamani,
Murmushi nagani a fuskan,Yayana tare da dan rausaya kan shi da yayi yana dukan ahannuwan shi guda a cikin guda a hankali,
Ganin irin murmushin da ya keyi yasani dakatar da zance na,
Yace ya kikai shiru go on ina sauraron ki ai don dama nasan cewa da masoyinki zaki fara gashi kuma keep n fara din,
Nima murmushi nayi nace Yaya ai kaima malam babban masoyin ka ne,
Amma kuma ban kaiki ba ke sarkin fadar shi ko don kowa yasan hakan,

Sai da na murmusa nace sai Baban makaranta ina nufin Baba Buhari ke nan,
Da shi da mama idan da hali Yaya ai saudiya ya kamata a kai su ko ?
Ko wanan karon murmusawa yayi min irin ta manya murmushi irin na iya fuska kadan,
Ya ce ina da niyan hakan amma sai nan gaba kadan insha Allah,
Nace to Yaya ba sai ka gyara,ma su part din su ba ya koma irin na zamani kaga idan mun tafi mu samu gurin zama mu dan wala,
Yace malam yace nayi gina a,bayan dakun su Baba, dama,
Nace ok, yanzu dai a takaice abinda ya kamata gaba dayan su sauran sai ka basu dan abinda zasu kara ga jarin sana,an su ko ?
Ka naga yana jijigawa a hankali tare da lumshe idon shi ,
Sai yai wani irin jan iska tare da fesarwa, a hankali,,
Yace a daidai lokacin da yake mikewa tsaye daga yanzu idan zamu yi shawara a kan iyayyen mu,
Ban so kina ware min Baban makaranta daban Babana daban,
Don kowa yasan cewa, Baba Samaila ba karamin kokari yayi ga ala,amari na ba duk da dai za ace ba,wani mugun girma sukayi ba amma ya kyautata min sosai a,rayuwan na,
Don haka ni ban mantawa da, alheri a rayuwa na,
Daga haka ya shige bathroom don yin wanka a gurin da ya barni zaune ban daga ba ina gurin zaune har wani dan lokaci ina tunane, duniya,
Zuwa can na mike zuwa bakin wardrobe din shi na ciro mai kayan da zai sa tare da feshe su da turare,
Da sauri na na kara gyara inda ya kamata a dakin badon komai ba fa don dai kawai na burge shi,
Kunsan abu ga mai kishiya duk abin da zakiyi wanda ita batayi zaki kokarta kiyiwa mijin don kawai kiyi galaba akan ta,
To nima sai nake gani ai bankai ajin da zan kara a tsakanin Sadiya da Salawatu, don haka ne na dinga yin aiyukan da karfin jiki na,
Abinda ban sani ba a lokacin shine ashe badaga haka ba shi na miji shi ne yasan jarumar sa a ransa ke dai naki shi kada ki bari a barki baya ko ta halin kaka,
Bayan fitowan Yaya daga bathroom ya shirya acikin kayan da na fitar mai a tare muka sauko ni dashi,
Inda muka zauna don a dining space, don ya ci abincin shi abincin da ya sha gadi wirin Ramatu don gudun a zuba wani abu kamar yadda take tuhuma,
A hankali na bude kulan abincin inda naga tuwon farar shinkafa kulle a,leda ledan ya dauki zafi ya dan sake ma tuwan fashion kama ado
Kulan miyan ganye tayi watau miyar taushe, yaji alaihu da sure sai nama da agusi, tai amfani,
Gaba dayan mu munji dadin tuwon don sai da na cinye ledan da na dauka tare da Salawatu mukaci don tace wai mu take jira,
Gab da zamu kare ne Anty Ramatu tafito daga dakin ta da gani daga barci ta tashi a lokacin,
Ganin mu mu uku yasa ta canza fuskan ta ta,wani daure fuska tamau,
Kishi, sosai ya baiyyana a fuskan ta amma sai ta dan kauda kan ta batare da taiwa kowa magana ba ta ja kujera ta zauna har ta fara ci bata cewa kowa komai ba,
Babu wanda ya tanka mata sai kowa ya shiga yin abinda ke gaban sa,
Mun kai dan wani lokaci a gurin sanan muka koma daga ciki,
A ranan yadda Yaya Abubakar ya gwada min tankar, ranan ce ya fara sani na a matsayin diya mace, saboda wani irin mahaukacin soyayyan da ya nuns min wanda ban taba sanin cewa ya na iya yi wa mace,irin, sa ba,
Sai dare sosai na samu Yaya ya sarara min ya nata fadar wai yaji na canza mai sosai tankar bani bace,abin ya kara rikita shi,
Tun wanan lokacin da na koma girki banda shakat da Yayana don koda yaushe yana manne dani don bai jin na gundire shi,
Hakan yasa bini,bini Yaya Abubakar yana a tare dani, sai ma na manta da zancen bed rest,
Nayi warkewan dole saboda irin yadda yake gwada min dole na jajirce wa zuciyana na daure kada aga gazawa na,
Duk da yana iya kokarin wurin ganin cewa gaba dayan mu yabawa kowa hakkin ta,
Abinda ban sani ba ashe tun lokacin da mukai zancen taimakawa yan gidan mu da Yaya Abubakar tun a lokacin ya yi duk yadda nace ayi don har an gama gyarawa malam tsoho part din shi,,,

****** ********** ******
Yau a gajiye ya dawo gida kaman kullun irin yadda ya saba dawo wa cikin gajiya,
Nice da girki don haka ya shigo tun a kofan falo na karbi jakar kayan shi na ahiga gaba yana,bina baya,
Wani irin tunane ne yazo mai a ranshi fon ganin yadda komai nawa ya sauya, a idon shi,
Muna hawan sama yana tuna hiran da Baba Wadda yai mai na gorin haihuwan da akai wa Baba Buhari akan shi cikin shiyan mu,
Shiyasa yanzu ma da yai wanan tunane da idon shi ke maigizo a kaina yadda siffana yayi kamar na mace mai ciki,
Yai saurin kawas da zancen da cewa subbahanallahi yana mai lumshe idon shi,
Da wanan tunanen muka isa dakin inda a tsakiyan dakin yajawoni ya manna a jikin shi,
Na lumshe idona saboda irin yanayin da na shiga ajiyan zuciya naji ya sauke daidai saitin kunne na,
Saman gado muka fada atare inda yadan shiga aika min da sako,
Hannun shi a saman cikina ya kai, abinda ya haddasa wa abin cikin cikina yin motsi bul,bul wani irin suka naji shima Yaya da sauri ya mike zaune yana cewa ,Ya Allah
Zuciya baki da kyau, wai tunane na har ya kawo min imagination din ciki ajikin ki,
Tausayi maganan da najiya fada ya bani sai naji tankar a lokacin infada mai gaskiyan zancen,
Ya mike zaune yai shiru yana mai dafe kamshi da alaman yana cikin wani irin yanayi,,
Ganin yadda jikin shi yasake yai sanyi yasana yanke shawaran yau da dare zan sanar dashi insha Allah,
Nadan kamo hannuwan shi na kwantas da kaina a saman kan kafadan shi,
Sai naji shi acikin ya nayi yake, a hankali na bude bakina nace mai,
Ya yaka tashi kayi wanka ga ruwan zafi can yana jiran ka a bathroom, tun dazun,
Nace abinci kuma yana ready a falo kai kawai muke jira,
Maimakon ya tashi sai ya kara kaiwa kwance ya dan rike min kwankwaso yana cewa waima kuwa zan iya tashi wankan yanzu kuwa,
Saida nai kokarin mikewa amma sai yajawo min hannuwa nadawo na zauna tare da dan rankwafo mai, cikin wani irin murya nace,
Haba dai Yaya dan Allah dai ka tashi mana kada mutanen gida su jiramu,
Wani irin kallo ya kama yi mun tare da lumshe idon shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login