Showing 45001 words to 48000 words out of 347556 words

Chapter 16 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8287

boye duk wani abinda bata kaunar ya gani a tare da ita bayan yin tafiyanshi don sam bata tsamaci dawowansa ba a ranan .
Ya fito yana saka riga a jikinshi cikin kuncin da takaicin ta ta fado mai dakin cikin wayence komai take magana dashi tana fadin .
Honey gaskiya kayi surprice dina da yawa daka kirani da ban fitaba dana tsaya na hadama abinci magana tayi tayi bai bata amsa ba sai zuwa can ya juyo ya fuskanceta yana fadin.
Wanaga ya saukeki yanzu Wasila ?
Gabatane ya fadi lokaci guda amma haka ta dake tace wai wanan Ruth cefa ta saukeni muke magana yasan Ruth din yar jos ce itama kuma a tare dasu ya santa.
Daga hakan baice da ita komai ba sai falo daya koma ya kunna tv har lokacin ranshi a bace yake da ita fitowa tayi zuwa dakinta ta samu wanirigan ta sauya ta fito.
Baisan da zuwanta ba lokacin sai ji yayi ta fado masa saman jiki tana fadin yanzu me zamuci ke nan honey a dan hasale ya tureta gefe daya.
Ya juyo gareta yana fadi a cikin fada kada ki kawo min rainin wayau a nan kin fito daga wurin gantalinki zakizo kina mun wani narkewa yanzu.
Inda ban dawo din ba me zakici ko kin manta kina da gida da mijine yanzu da zaki fita sai wanan lokacin ki dawo gida to be frank Wasila na fara regreting a kan haduwana dake wallahi don ni ba haka matata ta farko ta saba min ba.
Fadin hakan wai ita taji zafin abinda ya fada tace malam dakata ya isheni haka sai muna magana zaka dinga sako min zancen wata matarka can data riga data mutu ko in kasan zaka zauna kana min zanceta ko wani abinda ya shafeta can.
Hannu ya daga da niyar kai mata mari ta noke daga nan ta daga tayi dakinta da kuka ta dauka zai biyota don idan dan matsala ya hadasu yaga tana kuka zai rasa inda zaisa kansa ya shiga lalashinta har ta sauko.
Sai da a ranan taji shiru don tana shiga ya kashe komai shima ya nufi dakinshi cikin bacim rai ya rufo nadaman nan dai daya saba yi na aurota shine ke yawo a zuciyarshi
Wanan ya jawo masu zaman gaba a tsakanin su don tana daki tayi zaton zai shigo wurinta sai kawai jin karan motanshi tayi ya fita gidan.
Ta gyara kwanciya tana jan tsuki shima tunda yaje bakin aikinshi ya manta da zancenta yaci gaba da tarin aiyukan dake jiranshi a wurin tunda ba tafiyan mota yayi ba alokacin don haka ba gajiya a jikinshi.
Ada can baya lokacin rayuwansu da antyna da mota muke zuwa gida a wahale amma bamu ganin wahalan hakan mudai burin mu shine mu ganmu a gida.
Wanda nima a karshe idan munje saidai inta rakube rakube ina walagigi a tsakar gida sai wanda yaga Allah ya dan taimaka min .
Sai renon yara da nake famanyi wanda hakan bai damuna saidai nakan matsu mu koma don banganin yawan aikin da nakeyi a can tunda ba matsi ba hattara a gareni lokacin iya dai komai na wahala nice maiyinsa a gidan antyna din duk da lokacin shekaruna baikai dana tarin hakan ba.
Sai yanzu daga bayane nake fahintar wani abu a cikin zaman namu wanda a lokacin anyi amfani danine saboda rashin gata akai amfani dani amma kuma hakan da sukayi min sai ni yazami min sauki a wurina don nayi nisa dasu mama a lokacin.
Ashe zamana dasu bai kareba tunda ta Allah ya kasance ga anty din yanzu zaman nawa ya dawo a tsakiyansu yanzu ba yadda kuma kowan mu zaiyi da dan uwa.
Nagodewa Allah daya tausayawa rayuwana ya barmin baba a raye yai min gata ta sanadin ubana wanda Allah ya dora mashi sona da kauna wanda ba hakan akaso ganina ba.
Zamana da Samira zance ya baci a yanzu don kowa tasa ta fusheshi ne a tsakanin mu ba kamar yadda muka bar gida ba da farko kanmu a hade da juna har ana jin haushin mu ga hakan.
Nidai duk da nice mai dan zuwa gida ina dan lekowa amma ban fasawa kowa halin da muke ciki da itaba zancena daya shine tana lafiya karatu ya riketa.
Amma zuwa na karshe na fahinci canjin fuska a wurin mama Lanto don gaba daya ta daure min fuska sai na wayewa kawai mukeyi da ita har na dawo bayan na dawo da kwana biyune saiga wayan baba da yamma ina fitowa daga lectures.
Na dauka ina gaidashi ya amsa yake tambayana Fadimatu kada ki boye min komai dake faru tsakanin ki da yar uwanki tunda kinzo gida baki min bayanin komai ba.
Sai bayan kin wuce uwarta ta sameni da wani zance akan tanason yarta ta koma can wurin kwanan dalibai da kwana idan hakane saidai a bar karatu na fadawa uwarta duk da nasan ba zan fahinci komai a wurinki ba.
Amma ki fadawa gwaggon naku cewa zan shigo a cikin makon nan insha Allah ki gayar min da ita sosai nagode.
Da mamaki naje gida amma banyi maganan komai da kowa ba kan wanan zancen da mukayi da baba a waya na zancen samira da mahaifiyar ta.
Itako samira din sai wani busan iska takeyi tana wani zabure zabure tana nuna ita ta isa da kanta kowa yasa mata ido har gwaggo din.
Kwatsan kamar yadda baba ya fada ya fado muna gidan da yamma muka ganshi lokacin na dawo ina aiki a tsakar gida gwaggo na zaune tana tatsan kasarin koko.
Ina aka saka dashi gwaggo ta rasa yaddama zata saukeshi don murnan ganin dan uwa dan buhun da baba din ya shigo dashi na karbo na aje a gefenta bayan ta zauna suna gaisawa da baba din.
Bayan sun gama gaisawa ne baba din ya fara magana yana fadin Lami yaya yaran naki sun fada min irin kokarin da kikeyu dasu nagode saidai duk da hakan a yanzuma nazo na dubasune na kumaji abinda ke faruwa a zaman su na nan wurinki.
Don uwar ita yar nan Samira tazo min da wani zance wanda kunuwa basu dauka akan wai zamanta daku nan a yanzu akwai matsala .
Subbahanallahi mu din har yaran nan da basu zama a g??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ida sai dare amma yar nan me akai mata harta fadawa uwarta abinda ba daidai ba ta shiga tsakanin mu dakai kuma muna zaune kalau dasu.
To tace wai Fadimatuce take shiga tsakaninsu ku ta hanaku zama saboda hakan zata hadaku da ita gara wai ta koma wurin kwanan dalibai haka kuma ita wanan din kuma bata taba fadin min komai ba a zamansu na gidan nan.
Ina takene yanzu kira min ita tazo muji a bakinta da sauri gwaggo din tace ai bata gidan nan kuma wanan ne dalilin dayasa rigima a tsakaninsu don kawai yar uwa tana fada mata abinda takeyi ba daidai bane duk wanan zancen nasan bai wuce hakan a tsakaninsu.
Baba din ya kalloni daga inda nake zaune bakin kofan dakin namu yace ina kika bar yar uwantakine Fadimatu nace tana school baba a can na barta.
To ai ina nan idan yakama na kwana nan zan kwana idan ta dawo naji ta bakinta sai in tafi asheko zaka kai dare a garin nan don yanzu gaba daya yar nan sai daren kwana take shigowa gidan nan da safe kuma tayi sammako ta fice.
Nan suka zauna suna hira nina karasa abincin na kawo masu har mijin gwaggo daya dawo shima ya saka baki a zancen gashi nayi kiran samira din tun shigowan baba taki daga wayata har zuwa lokacin.
Karshema saina fahinci tayi blocking din layina a wayanta fahintar hakan yasa na daina kiranta sha daya saura kwata ta dawo tun a soron gidan ta fara jin muryan baba dake firan dole amma hankalinshi a tashe ga abinda idonsa ya gano masa akan Samira din.
Haka ta shigo sukuku tana gaidasu mijin gwaggone ya amsa shi baba bai samu bakin amsawa don mamaki zata wuce ta shiga daki muryan babane ke fadin Samira kwaso kayanki kizo mu wuce gida.
Malam mijin gwaggo yaso saka bakinshi baba din yace malam Audi yi hakkuri zuwa gida da ita a yanzu ya zama wajibi a gareni jeki ki kwaso kayan ki kizo mu tafi.
Kodata shigo ta sameni kwance ina kuka zagina ta farayi bandai kulata ba taci gaba da fada min maganganun da bai dace ba bandai bata amsa ba muryan babane ke fadin ina takene tazo dare nayi masu fa.
Haka ta fito ya sakata a gaba suka wuce zuwa kaduna a cikin daren nan koda suka isa gida sun samu gida harsun rufe saidai basuyi barci ba ya buga mama uwa dake aiki a tsakar gidace ta bude mashi gidan suka shiga.
Sai ganin samira dake bayanshi tayi tace malam lafiya kuwa na ganku hakan har lokacin baiyi maganan komai ba yace jeki ki kwanta a dakin uwarki.
Ta nufi dakinsu tana kwankwasawa mama Lanto kofa tace waye mama nice bude min kofan na shigo da sauri mama din ta bude kofan jin muryan diyanta mafi soyuwa a gareta.
Tana shiga dakin ta fashe da kuka tana fadin makirci bintu da gwaggo lami suka hada min a wurin baba don kawai su bata min suna.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Nasan cewa ina da test a yan kwana biyun nan wanan ya hana min zuwa kaduna saidana gama rubuta test dina na shirya don zuwa gida nasan ni kadaice zan iya shawo kan mahaifinmu ya bar Samira ta dawo ga karatunta.
Don nasan irin yadds take da burin son ganin tayi karatu gaba da secondary a rayuwanta sai gashi kuma tana zuwa ta juye a lokaci guda tana son lalata rayuwanta.
Saida na gama shirina tsab na fito nacewa gwaggo zan tafi gida in dan dubosu cikin mamaki take fadin dama satin nan zaki gida baki fada min ba ?
Gwaggo hankalina bai kwanta bane gara naje naji me ake ciki da zancen Samira tunda yanzu jerabawane zamu yan kwanaki masi zuwa nan kadan.
To ki saurareni don nasan yanzu abinda ba,ayi ba shine zasuce anyi don haka nasan a jirace suke dake su sauke haushin komai a kanki don hakan ki kama kanki dasu don Allah.
Duk abinda zasu fada danne ki daure don nasan yanzu suna can hake dake kan zancen yar nan da akayi jin me gwaggo ta fada yasa na dago kai na kalleta tare da fadin .
Na sani gwaggo kuma na saba ai yanzu da duk wani abinda zasuyi min asalin ma abinda zai kaini ke nan gidan inba baba hakuri ta samu ta dawo ta zana jerabawan ta.
Allah sarki ke kina binsu da alheri su kuma suna kokarin kulla maki sheri a kullun burinsu suga yadda zaki durkushe a duniyan nan suji dadi.
Ba komai gwaggo nasan sai mun kwasa zasuzo su gane bana bin kowan su da sheri a rayuwana sai alheri barin isa gwaggo kada yamma yayamin a hanya.
Karfe shida da dan wani abu na yamma na iso gida duk da a gajiye nake raina naga in fito wurin sana,ata don haka ina sallama sai mama uwace ta amsa min tana fadin mutanen zaria ashe kuna hanya ke nan ?
Eh mama sannu da gida na gaida ita na wuce zuwa kofan maman biyu dake zaune kofanta nagaida ita ta amsa min ciki ciki na juya ina fadin ina mama Lanto ba wanda ya ban amsa na shiga da sallamana dakin.
Suna zazaune har mama din da samira na gaida ita kamar ba abinda ya faru ta amsa min cikin makoshi na juya gun samira din ina fadin keko kinsan ana test zakizo gida ki zauna.
Bata ko dago kai ta kalli inda nake ba ganin hakan yasa na juya cikin ko in kula ina fadin barin fita inga su Auwalu a waje nakai kofa naji mamadin na fadin.
Ta koma a kara kulla mata sherin dayafi wanan don kawai bakin cikin da akeyi da ita ban taba zaton hakan ba a rayuwana don dan uwanka ya samu zaka nuna masa bakin ciki a filin Allah.
Waje kuma dana fito naji mama na fadin dama ai ramin karya kurarene ai ido muka saka muga inda za a in takaman mutum iya munafunci yakai karshe yanzu.
Ban dai tsaya a cikin gidan ba na fice waje wurin yan uwana masu suya akofan gida ina can har aka shiga sallah magariba aka fito ban shiga gida ba sai ga mama uwa ta labe bayan shagon isah ta aiko yarta karama wai inje.
Nabarwa Auwalu na mike zuwa wajenta din jana tayi mukaje baya ina dai biye da ita don dukkansu da mama Lanto idan suna son maganan siri dani sukanyi hakan dama tace.
Bintu duk abinda Lanto zatayi maki kada ki yarda aji kanku a gidan nan har ta koma na fada mata tayi bincike tun farko taki hakan ta nuna samirace tata idonta ya rufe akan yarta.
Yanzu ido yaya da yaranta suka saka kuyi tonon asiri a tsakaninku ku fallasa kanku kowa yaji tsakanin ku naji ta fara sakin magana tun shigowan ki don Allah kada ki yarda ki kula mata har ku saida hali.
Insha Allahu hakan ba zai faru ba a tsakanin mu nan dai nayi mata rantsuwa akan bansan komai dake faruwa ba kuma ban taba fadawa wani alherin ta ko sherinta ba.
Tace nasani Bintu kadama ki rantse don nasan komai nasan halin kowan kuma jeki kada a gane nazo nan don an zugata ta zugu tunda wawiyace ita dama ana son aga yadda zamuyi ita bata gane ba ta hau wai kunwa yarta sheri duk da malam baicewa kowa komai ba tun zuwanta gidan nan.
Mundai gama maganan da zamuyi mama din ta juya zuwa gida da sauri don kada wani ya ganta a lokacin daga cikin gidan mu.
Inda sabo na saba da wanan don mutum wani abu ya hadani da dansa ya shigar masa wanan ba sabon abu bane a wurina saidai nayi kukana ba mai ban hakkuri in share hawayena.
Bamu samu ganawa da baba ba ranan sai washegari naje na gaisheshi tunda safe don kada ya fita ina barcin safe har na daga zan wuce bayan mun gaisa yake fadin kira min yar uwarki samira.
Gabana ya fadi babu halin nace wani abu dole na wuce kiranta basu bude daki ba don haka na tsaya sai na juyo baba yace yaki koma dakin ki kwanta zan kiraku anjima.
Kodana koma sai barcin ya fita min rai na fara kimtsa dakina daya hargitse kafin wani lokaci na gama gyaran daki na shiga nayi wanka na fito nazo na shirya a cikin dogon rigar atamfa mai dan ruwan duhu.
Muryan babane yake kwalla muna kira nida samira lokaci guda nice na fara karbawa kafin ya sake maimaita kiran ita samiran ta amsa masa ciki ciki ta fito.
Muka shiga dakin yana zaune a kasa ya saka abin karinsa a gaba wanda koko da kosaine a ciki muka shigo muna gaidashi ya amsa gefe muka samu wuri muka tsugunna gaba dayan mu.
Shiru baba yayi yana kallon kasa na dan lokaci kafin ya dago kai yace Samira dake da Fadimatu ko zaku tuna yadda nayi daku kafin na yarda kuje wanan karatun da kukeyi a yanzu ?
Kowan mu yayi shiru ya sake maimaita tambayanshi karo na biyu yana kallon mu a cikin rawan murya na fada mai yadda mukayi dashi har ya yarda.
Budan baki sai cewa yayi dani Fadimatu ban taba zato ko tsammanin cewa zaki munafunceni ba ga saurin rayuwan da yar uwanki ta dauko yi ga rayuwanta a yanzu din.
Baba kayi hakkuri ba hakana bane ko ranan da kazo akasi aka samu don na barta a hostel tana karatu da yan uwan karatun ta bansan ya akayi tayi dare hakaba kuma nayi mata maganan yin hakan.
Humm yatintar ke nan da babu komai Fadimatu uwar samira ba zata sameni da zancen cewa zata sauyawa yarta wurin zama ba.
Hakan data fada yasa na gane cewa akwai matsalan dake faruwa a tsakanin ke Fadimatu dake yawan zuwa gida kike boye minshi.
Don hakane na yake shawaran nayi maku zuwan bazata don in gaskanta zarigin da nakewa Samira din sai gashi nagani a zahiri.
Don a kalla nakai awa biyar a zaune kafin Samira ta shigo gidan nan kuma a gaban wanda muke tare ya iya sheda min yaga wani jan mota ya saukeki alokacin.
Nasan nan duk zakuyi zargin cewa Fadimatu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login