Showing 180001 words to 183000 words out of 347556 words

Chapter 61 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8290

karshe.
Bayan fitan likitan ya dawo da hankalinshi wurin su gwaggo cikin girmamawa ya soma magana yana fadin
Ok mama mu zamu koma dama daga Abuja muke yanzu munzo mu dubane muga jikin nasa idan ba kulawa a nan sai mukaishi Abuja a gwada can a gani amma mun samu sauki na samuwa insha Allahu kuma ba wani babban matsala bayan wanan.
So Abbas ka ba iyalansa dari biyu su raba ga wasu kaya can a mota a ina za a saukesu ya dan kalloni don jin me zance ni kuma na dan kalli Nura nace Nura kuje a sauke a gida kawai zaifi.
Kudin Abbas ya miko min na karba dakin ya dauki Allah umfana Allah saka da alherinsa Allah ya karawa dukiya albarka .
No ba komai ai Allah ya bashi lafiya ya fada cikin saurin maganan nan nasa da sai mutum ya tsaya zai fahinci me yake fada lokacin .
Sai kuma ya juya gun Abbas ya danyi magana ashe wai cewa yayi sister's dinane nan ko don haka yace a basu wani abu duk ni Abbas din ya mikowa kudin ya dan duka yana masu sallama su mama ana daga murya wajen sallamansa.
Binsu nayi a baya sauran dakunan ya shiga yayi masu alheri zuwa lokacin har driver dayakai Nura gida ya dawo min fito dasu mun sameshi a waje yana jiransu.
Dan magana Abbas din yayi mai yace No ya kalloni ni kuma na noke kai da sauri kasa suka shishiga motarsu mai kama da walkiya suka bar haraban wajen da gudu.
Kodana juyo na samu su mama har kowa a tsatsaye suna kara kallonsu na nufosu kamar kwai ya fashe min a ciki na shiga dakin suma suka shigo Usaina ke fadin wanan ai Ogankine ko Bantu ?
Kai don Allah ai ko don matsayin nan da Allah yai mata a yanzu kwa dan saya wanan sunan nata idan baku iya kiranta da hjy ai sai ku kirata da Fatiman ta zai fi tunda shi kowa ke kiranta dashi yanzu.
Ina fadin kai gwaggo hjy kamar wata tsohuwa ita kuma Samira tana fadin wa yaga makawuya ke nan gwaggo hajjin nan fa duk muna sa rai insha Allahu .
Amma baki kai da zuwan ba ai yar nan itako ta tafi ta taka mukaman ibrahima kasa kasa samira din tace ko mukaman kitchen ba kila ko dutsen albarkan bata hangoba.
Wanan bakin ciki haka har yakai can dan uwanka kewa haka uba daya Samira meyasa kike son kifi kowa danyen kaine a yanzu ko aure haukane wai ?
Mama uwa ke fadin hakan a hasale a,a,a mama ni zancena nakeyi fa kada a dora min kahon zukau kuma yanzu don Allah don zanyi aure ai aure ba banza bane tunda kafin ni wasu naso hakan.
You are very stupid Samira me kike daukan kankine wai yanzu ke wacece ko wa zaki aura da kike ganin kinfi wani a yanzu barin fada maki ke ba kowa bace wallahi face abin tsusayi a garemu koba ya habibi yasa kikewa mutane izgilancin nan ba.
Idan ni ba kowa bace ke wacece din yadda kika san nawa haka nasan naki ko don wa yan nan kattin dake sintiri akanki kikejin ke wata abuce yanzu ?
Mun fasan komai bantu ba abinda bamu sani ba wallahi saidai mu kalli mutum kallon mai a saman ruwa ciki honko
Amma yar nan kin iya sheri saukin abindai sharia da hukunci a hannun Allah yake yanzun yar uwarki kike kokarin lakawa sheri haka Gwaggo ta fada hankali tashe.
Gwaggo ki barta ba Samira ba wallahi ko wanda yafita yace zai min sheri zaiga abunsa cikin kayansa a rayuwana ban bin kowa duniyan nan da sheri balle dan uwana.
Halinta take kokarin fadi a yanzu a zaton ki na taba labarinki da wani a duniyan nan wallahi sam kar kice ban sani ba.
Har satan lamban wayan ya habibi da kikayi a wayata na sani samira da irin rokonsa da kika, kika matani a wajansa duk nasan komai.
Na barkine don a rayuwata ban taba son ya habibi da sunan soyayya ba cikin zuciyana haka kuma duk wani binciken da kike min na gano sirina na sani da gangan nake bari ki duba don na yarda da kaina dari bisa dari saboda nasan ban taba aikata wani abin asha ba a rayuwana ba.
Amma kefa samira baki da bakin magana a gabana ko yanzu nasan abindake zuciyar ki da yasaki hakan shine bakin ciki da hassada shike cinki .
Har kike kokarin bata min suna a banza kina son kice masha,a nake aikatawa da masu zuwa din nan saukin abindai akwai Allah shine mai hisabi.
Babane kamar ya motsa yasa naga mama da sauri ta nufeshi tana fadin kungani ko bawan Allah nan yana samun lafiya kuna kokarin tayar masa da ciwo kuma.
Dama ai abinda take so ke nan kowa ya sani ai gara ta karasa kasheshi kowa ya huta gwaggo ta fada tace ke wace irin ibilishiyar yarinyace wai ?
Kin dauki bakin ciki da hassada a rayuwa kin sakawa zuciyarki kece maita kece kwace kai albasa batayi halin ruwa ba wallahi.
A to inma batayi ba ai tasan inda ta dauko wanan yarone yanzu kowa yasani baka sashi a hanya ba yadda banyiwa yarinyar nan fada ba tun shekaran jiya da aka fara abin nan amma saida yanzu kika ja min bacin rai a banza.
Ni duk abinda mutum keyi idan baishiga gonata ba bani shiga nasa balle insan yanayi kowa dai wajen nan yasan Bintu ba wanan ne a gabata ba yanzu ke ko koyi da abinda yar uwarki keyi na damuwa da abinda ya damu zukatan mutane bakiyi.?
Zatayi tana wanan hassada ai ba hassadane a gabanku ba yanzu kowa ya nuna bajintarshi don ita ta nuna nata kowa ya gani kuma masha Allah.
Ni dai ban tsaya kansu ba kuma ina can gun baba ina duba jikinsa nida mama dasu Usaina mun daga shi mun juya ya bude idanu yana bin mu da kallo saiga hawaye na zubowa a idanunsa.
Ganin hakan yasamu kuka nan dakin ya dauki kuka sosai gwaggo da mama suna muna fada sai yamma na mika masu kudaden da Oga bashir ya basu.
Don nasan kowa na cikin karfin hali kuma su yace abawa dama son haka ban rike ba na basu abinsu har kananan yara dake gida an kasa dasu .
Ganin jikin baba ya danyi sauki sosai satina daya na koma makaranta da Aliyu har makaranta na rakada na kara ba malam hakkuri tare da bashi kudi ai muna saukan kur,ani .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Abin ya raba min hankali a yanzu ga zancen karatuna ga ciwon baba duk da yan uwa da matansa suna kokari a yanzu dashi sosai kuma akwai alaman sauki a tare dashi .
Hakan yasa bani zaria bani kaduna ina sintiri a mota kullum na rame na fige daganina zaki gane ina cikin wani yanayi a zuciyana.
Saidai ban wasa da sadaka a inda ya dace ayishi kamar gidan da nasan suna bukata sosai a unguwa zan dan shiga mu gaisa mu danyi fira idan zan fito na mika masu dan wani abu duk da ba mai yawa nake bayarwa ba amma haka za,a dinga jero min addu,oi da har zanji kamar yan amin sun amsa a lokacin.
Yanzu kan na rage shiga kaduna din sosai don exam da mukeyi duk da kuma nasan zuwana din yana da amfani sosai don sai najene ake sayowa baba wani dan abinda zai karawa jikinshi kuzari.
Amma haka na daure har lokacin da muka gama exam don ni na cinye rabin time dina a saudiya don haka na mayar da hankali ga exam sosai ban kara kwana ba na nufi kaduna a cikin dare na isa .
Asibiti na sauka na samu jikin na baba yayi sauki sosai don yana iya daga hannunsa a yanzu sai dai daya yake iya motsawa dayan yayi masa nauyi.
Kuma a yanzu din ana zaunar dashi a saman kujera yayi dan lokaci a zaune din kafin a mayar dashi ya kwanta saman gadon.
Yanzun ma dana iso zaune na sameshi dashi da mama a dakin Nura ya dan fita dkn shi kadaine a gida sauran yan uwan mu maza basa nan amma sun zo sun kwana biyu sun koma kudu inda wai suke sana,a acan din.
Na tsaya gaisawa da mama naga yana min alaman sannu da zuwa yasa nabar wajen mama din na nufi gun baba ina gaidashi sai kai yake kada min alaman amsawa gareni.
Bayan mun gama gaisawane najuya nake tambayan mama din ko yana cin abinci yanzu take fadin saidai abu mai dan ruwa ruwa haka kamar kafa da dan koko ko ruwan shayi haka.
Yanzuma Nura ya tafi tundun wada ya sayo muna kafanne don wanda aka sayo ya kare tun jiya kuma yaki cin shinkafa Ok sai a tudun wada ake samu tace ehh can dai muka sani kawai inda kedashi.
Zanin gadon na cire ina kakabe masa gadon duk zanin yayi datti ga alaman jirwayen magani nan tako ina a jikin zanin na dago ina tambayan mama babu wani zanin gadone a canza mai tace tun shekaran jiya dana nade akai gida a wanke ba a dawo dashi ba.
Ni dai bance komai ba haka na kakabe wanan din na shimfida mashi yayi alaman a kamashi ya kwanta muka kamashi da mama muka kwantar dashi yana sauke ajiyan zuciya a hankali .
Allah kadai yasan abinda yake jiba rayuwansa saishi kuma da ciwon ke jikinsa yasan hakan abindai gwanin ban tausayi wallahi baba mai zafin nama amma ciwo ya illatashi a yanzu ya koma daga kwance sai zaune ko wani lokaci.
Nurane ya shigo daga sakon daya tafi yana ganina yake fadin ashe harkin iso na zata sai zuwa gobe ai in kindan huta zamu ganki !
Hankali bai keanci idan ban iso yau din nan ba yanzu aina huta a nan ya mikawa mama sakon tare da jan dayan kujeran ya zauna.
Nan muke dan hira jefi jefi har yake fada min soja yazo har sau biyu ya duba baba aj nace munyi waya amma bai fada min daga inda mama take zaune tace ai sojan nan kan gaskiya yayi har yafi muna wanan dake zancen aure a yanzu.
Wai ace malam baida lafiya amma Mahmoud yakasa zuwa dubashi har yanzu yau ko ba zancen auren shi da samira ai kodon diyan Safiya yaci albarkacin hakan gareshi gaskiya.
To mama kinga sun damune ai kinji abinda su Samira din ke fadi watau tunda baba ya dan samu lafiya ba za a tayar da bukin su ba shine yace bai samun zuwa a baku hakkuri sai inyazo buki gabadaya don Allah.
Mama ta kalloni lokacin da Nura ya gama bayani taji me zance ni kuma na gane nufinta sai nace in dai har baba yaji sauki ai gara dai don Allah ayi bukin nan kowa ya hutama.
Tunda ba zasu iya jira har lokacin da Allah zai bashi lfiya ba ayi zamuko zuba dasu idan su bai damesu ba aimu ya damemu tunda yanzu kowa yasan ranansa garemu tunda ya fada ciwon nan.
Mama ku barsu idan sunce hakana don Allah ai hankali hanjine mu dai fatan mu shine Allah yabashi lafiya ya koma har kokinsa don haka kawai gara ai ,,,,,,
Wayata ta dauki kara na ciro sojana nagani a rubuce jikin screen din wayar tawa na dauka yake tambayan kin shigo dinne nace ehh gani asibiti ya amsa da gani nan zuwa yanzu.
Bayan yazone ya bugo waya na fita na sameshi zaune a cikin motarsa daya packer daga can baya kadan shi kadai yazo don darene bai dauko wani dan rakiya ba a lokaci.
Bude motan yayi yace in shigo fita zamuyi mu danyo sayayya banji komai ba na shiga ya rufe muka dauki hanya nan ya fara magana yana fadin baby na duk kin rame kin danyi duhu wallahi exam din ne ko dai case din baba yasaki fadawa haka ?
Murmushi nayi nace ko wani akwai Soja don kaga yau idan akace ba baba bansan makomar rayuwata ba a yanzu don baba bai taba fada min komai ba game da mahaifiyata ba.
Gashi shima yan uwansa bamu san garin su ba don ba,ataba zuwa dani ba gaskiya saidai su da dan dama tunda sukazo shima yana zuwa gida.
Kagako dole in damu ko wanan kadai ya isheni tunane don zan koma ni kadai a cikin yan uwa duk ko yadda suka iya nuna min kauna a gareni.
Wai ban gane ba kina nufin kwata kwata baki san mahaifiyar ki ba dama kome kike nufi da fadin hakan bam fahinta ba gaskiya inda zancen ki ya dosa.
Nace hakane ni bansan mahaifiyata ba ance tun ina shan nono ina bayanta suka rabu da baba yan uwanshi suka hana ta tafi dani tun ranan bata kara wai wayoni ba har yau din nan.
Abinda na sani kawai shine ana cewa ita din gudun hijara sukayi zuwa kasan nan dama daga libiya a lokacin wanan kawai nasani akanta koshi ban tabbatar da hakan ba don ba a bakin baba naji ba.
Iska naji ya furzo daga bakin shi kafin yace dani amma idan Allah ya bashi lafiya gaskiya ya kamata kunyi wanan maganan dashi zaifi.
Allah ya bashi lafiya na fada a kasalance ina mayar da kaina saman kujeran mota ya tsaya a bakin wani super market ki jirani in shiga don naga baki da kuzari a yau din nan.
Yana fadin hakan ya fita daga motan ba tare daya kashe ba ya bar min mota a kunne ina shan AC din motan binshi nayi da kallo kananun kayane saye a jikinshi.
Farar rigar T-shirt mai kyau sai kamshi yakeyi da wando light Brown daya hada wasu takalman mazane farare a kafanshi suna da kamar anyi sakan kwando ta samun su baya da belt amma bai daure ba .
Ya dan jima a cikin shagon kafin ya fito da ledoji niki niki zuwa motan ya bude baya a saka kayan ya zagayo muka dauki hanya muka koma asibitin muna hiran jikin baba din.
Koda na shigo shadaya saura don har mama ta kwanta a lokacin Nura kuma yana waje zaune yana shan iska na kirashi yazo ya dauki kayan ya barni a can muna hira sai shadaya da rabi ya tafi ni kuma nashigo ciki.
Ina fadin har mama tayi barcine wai data tashi ai ta ci abinci don in yakai safe zai lalacene kuma ai barcin baiyi nisa ba dama Nura ya fada yana dariya.
Nama na bude sai yought mai sanyi mai photon bafulatana da kwaryan nono a kai na kwali na nufi gadon baba ina fadib baba kayi barcine da kasha yought din nan ko kadan ne ko zai gyarama baki.
Kai ya girgiza min ashe idonsa biyu na dan duka ina tambayansa da zakasha ko baba ya gyada kai nura yazo ya gyara min shi muka dagashi muna dan bashi a baki kadan kadan ya kuma sha sosai na jingine mar jiki a yayi kamar ya dan zauna don ya fada mai a ciki.
Na mike na koma saman tabarma a nan na samu mama muka zauna mukaci mukasha kafin mu kwanta sai dariya Nura yakewa mama yace ai kowama idan baki nan yana kewan rashin ki.
Washegari ba wanda yazo dubansu daga gida sai wajajen karfe daya su Usaina suka shigo da abincin rana nan suka samu nazo don su basu dauka zanzo ba a ranan .
Tun bayan dawowa soja yake min sintiri a asibitin har sati ya kewayo aka sallamemu muka koma gida da baba da aka dora akan magani zamu kuma rika zuwa check up bayan sati biyu yadda likita ya fada.
Dakina na kara gyarawa na zauna a ciki ina kula da baba duk da yanzu a gida da sauki a waje ake mai shimfida yadda zaisha iska sai darene mai girki zata kwana dashi a daki.
Duk wanan abindai ina kokarin saka ido ga jikin baba din haka kuma ina sayo mai abubuwan kara karfin jiki koda yau don ya kara samun kuzari.
Yau tun safe haka kawai nake jin samira na rera wakan danmaliyo maliyo maliyo gobe da labari


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login