Showing 15001 words to 18000 words out of 28383 words
Chapter 6 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
da na gani a kan Gado ta ida tabbatar min da kin shiga hatsari, ba mu tsinke ba sai da muka auna muka tabbatar D.P.O yaudararki ya yi.
Kwatsam! Muka tsinci hotonki a T
V
har ana shelar kisa ta hanyar rataya.” Rose tayi
murmushi ta ce, “Ai sai su kashe uwarsu da ubansu. Ni kam ai ba yanzu ba, sai ta Allah tayi, ai rai alqawari gare shi, ko zan mutu ko to ba ta hanyar da suke nufi ba (kisa).”
“Ai muna nan ma mu har mun gama shirya yadda zamu tashi yaqin Biyafara a Legos
gobe.” Rose ta ce, “Ah haba dai Beeba?” Beeba ta ce, “Wallahi ko, Deena ta shirya mana yadda yaqin zai kasance a kan zuwa Dajin da abin zai faru, in ya so sai mu fara sace tayoyin motar ta hanyar haxa tarkon qusoshi, idan suka fito daga motar sai mu soma aika musu alburushi, kafin mu sibaroki mu dawo.”
Rose ta jinjinawa Deena hannu tana faxin “Da kyau nawan, nasan akwai qauna tsakanina da ku, Allah ya bar mu tare.” Ta faxin hakan tana haxa hannuwansu wuri xaya.
“Sai mu uku qafafun Murhu, kowwa tava mu ya shiga uku!”
“Uhum! Rose ke fa uwarmu ce, ba mu da idon da ya zarta ki, ke xin uwar marayu ce me uban ma kina mishi gata.” Ta ce, “Eh a mata ba! maza kam ni da su sai ingiza su kushewa. Lamarin bai fara ba ma.”
Beeba ta jera mata girkin da ruwan shayin, ta dubi Beeba “Duk ni xaya Bibalo?” Ta ce, “Duk ke xaya Indodo.” Tayi maza ta sha mur. “Kar ki zube ladarki mana kafin in xura miki ashar.” Beeba ta ce, “Yi haquri na tuba My Roses.” Ta ce, “To yanzu naji daidai.” Ta kai kofin shayin a bakinta tana kurva.
Deena ta maganta “Ina son sanin yadda ki ka zavi sunan Aisha ki ka koma Rose, da kuma Musuluncin da ki ka zava ki ka kuma qi shi
?”
Rose ta numfasa sannan ta ce, “Na zaci yadda na samu kuvutowa za ki tambaye ni Deena, sai gashi kina son in faxa miki abinda ba ni son koda tuno shi.”
Deena ta ce, “Eh to haka ne, amma fa har ita tambayar tawa ta farko ina buqatar na sani, amma ya ya aka yi ki ka fito, ko in ce ki ka kuvuto?”
Ta ce, “D.P.O ya yaudare ni, inda hasashen Beeba ya zamo gaskiya, ashe hotona aka ba shi inda ya yi arba da ni a Jifatu ya fito min ta hanyar da ban yi zato ba.
Lokacin da na bar gida ashe yana tare da wasu mutane waxanda suka taya shi tabbatar da ni ce na kashe Kayode.
Bayan ashe lokacin da muke ganawa da Kayode ashe
Recording
ya ke a wayarshi, inda hoton Bidiyon ya fito da fuskata raxau.
Hakan ya tabbatar musu da ni xin ce inda ya tabbatar min da shi dama aiki yazo yi kaina ba abinda na zata ba, don haka ya kama ni a matsayin me lafi.
Kin ji yaudara ta biyu da aka yi min, naso in tashe shi daga aiki sai dai kash! Domin ko na makara sai shafawa nayi naji wayam! Rashin Bindigar nan shi ya kai ni ga shiga hannu.
Da ace tana tare da ni to da tsinannen D.P.O xin can ya daxe a qiyama. Ina ji ina kallo aka miqa ni Lagos, inda na iske Tukur Sambo wanda bayan doguwar mahawara ta sa-in-sa ya zabga min marika, abin da ban tava fuskanta ba.
Bayan dogon bincike aka miqa ni kotu inda qarya da gaskiya har da qarin gishiri dai daga qarshe aka yanke min hukuncin rataya a gobe, a cewarsu kenan inda aka kai ni gidan ajiya kafin wayar garin gobe, ba su san kallonsu kawai ni ke ba.
Misalin
uku na yamma ina rufe a xakin da aka rufe ni na ke ta silin na fice ta sama, shi ne
dalilin karcewar jikina, kin ga gobe sai dai su shafa shiru ta ba su labari.”
“Ai na zaci gidan kason aka maida ki.” In ji Deena.
“Haba Deena, kin manta uqubar da
muka xanxana a gidan Kaso da har zan yarda in koma? To bari in tuna miki don naga kin manta.
BABI NA BIYAR
K
aton gida ne me doguwar katanga, girman shi ya wuce a bada misali. Xakuna ne jere reras masu xauke da lambobi a goshin xakunan, gidan na mata ne zalla, yayin da na mazan yake can qetaren dogon titin na Qiri-qiri Road.
Mata ne burjik a tsakar gidan masu sanye da
Uniform
mabambanta, wasu kalar koraye, wasu kuma me ruwan qasa. Yaran mata da tsofi, da matsakaita. Kai masu mabambantan shekaru dai waxanda qaddara ta kirawo suka kuma amsa da babbar murya.
Kowa nata aikin gabanshi, yayin da wasu ke ta wankin suturu, wasu kuma suna yi wa junansu kitso, in da wata shaixaniya ke rera waqa daga bakin ta tana kuma taka rawar alanta, kai ka ce da ita aka taka rawar alantar.
Yayin da wata ke can gefe xaya tana ta sharar hawaye, wasu kuma su biyu suna gefe suna ta labarin
duniya. Ga me zuwa ziyara zai yi matuqar jinjinawa qudurar Ubangiji, idan yaga yadda Bursunonin ke rayuwa, ga waxanda suka saba sun xauki gidan tamkar na gyatominsu, ga
waxanda suke baqin zuwa kuma suna jin tamkar ma ace qiyamarsu ce ta tsaya.
Ba su da aikin da ya shige qunci da damuwa, kasancewar duka Fursononin kowane da irin laifin da ya kawo shi yasa aka bambanta musu kalar yadin Uniform.
Wasu bashi ya kawo su da zarar sun gama zaman kuxin da ake binsu ko danginsu sun biya musu, to za a sake su. Wasu kuma zaman shari’a suke, da an qare shari’arsu za su fuskanci abinda shari’ar ta haifa musu, wato hukunci, wasu kuma zama ne na din-din-din wato (life in prison), sai fa in mutuwa ya yi.
Wasu kuma an yanke musu hukuncin jiran ranar da za a zartar ake, yayin da wasu kuma kisan kai
, wasu sata, wasu fashi da makami. Laifuka dai iri-iri.
Don haka ne aka tanadi xakuna mabambanta masu laifi me girma su ne a cikin xakuna a rufe basa fitowa sai da dalili, da kuma sun gama dalilin da ya fito da su to za a maida su a garqame.
Su ko na tsakar gidan masu walawa su ne masu zaman bashi, da ma su jiran shari’a ta
yanke musu hukunci, da masu rayuwa ta din-din-din, sai fa in sun mutu.
Haka na tsakar gidan sukan tallafi junansu amma ba duka ba. Tallafar ko tana zama ta ayi hira ai shewa ko a yiwa juna kitso da dai sauran lamuran rayuwa. Haka kuma mutanen dake waje suna iya kawo aikatau ga matan su yi musu su biya su.
Aikin ko yana kasancewa wankin kaya na suturu na kaya, wasu kuma suna yin wankin mashin a biya su kuxinsu su qulle abinsu idan buqatar wani abu ta taso musu sai su fidda kuxinsu su siya, idan kuma aiki ya fiddo su waje sai su sayi abinda suke buqata.
A gefe guda kuma akwai dogon xaki me xauke da gadaje masu yawa na haxakar waxannan masu walawa a tsakar gidan kamar yadda xakunan can yake da lambobi to suma gadajen kowane na da lambarshi.
Haka kuma Fursunonin sun san lambar gadonsu wanda in yaso sai ya je yayi kwanciyarshi yayi barci. Haka kuma a gefe xaya gidan yana da tsari da doka ta musamman. Haka kuma ba a zuwa ziyara, me ziyara ya keve da Fursuna ba tare da Gandiroba na gadinshi ba.
Kai akwai dai dokoki da yawa. Haka kuma akwai dokar rabon abinci da rabon ruwa, da kuma hatsaniyar Bursunoni (wato rigima ko faxa). Duk sabon xan Bursunan da zai zo to za a karanto mishi dokokin.
Haka kuma da akwai wasanni ga me buqata. Haka kuma da akwai me koyar da karatu da neman sanin Addini ga me buqata. Kai rayuwar gidan Yarin ita kanta wani kundi guda ne wanda idan na ce zan warware ta filla-filla to wannan xan littafin zai cika taf ba tare da na qare ba.
Da yawan matan ciki qabilu ne, tun daga kan yaren Igbo, da Yoruba, da Tubi
, da Igala, da Kambari, da Zuru, yaruka dai kala-kala, kasancewar Legos xin cunkos xakin tsumma, sai jefi-jefin Hausawa.
Wanda ya samu xan’uwan da suka fito jinsi xaya yare xaya sai ka iske su a haxe, komai suna yi a tare, suna hira tare, suna tallafar juna, wadda bata samu hakan ba zata zamo ita xaya qwal ba ta da abokin mu’amala.
Hakan yasa ake faxan qabilanci a gidan da zarar ba yare da addini xaya ku ke da wancan ba. To sai shiga nuninta da baki ana zunxe wadda bata da haquri da zarar ta ankare sai a tashi qura
a ba hammata iska har sai mahukunta sun tsawatar.
To dama rayuwa irin wannan sai an yi haquri, kowa dai in ba qaddara ba me zai kawo ka nan? Haka kuma kowa jiran wa’adi ko hukunci yake. To Allah ya kiyaye mu baqar qaddara, suma kuma Allah ya basu mafita don Nabiyyu Rahamati.
Suna ta hirarsu suna shewa inda faxa me tsanani ya varke a tsakanin Blessin da Atika, inda Atikar ta wulwulo wata qazamar ashar ta xurawa Blessin.
“Don ubanki ni za ki satarwa breziya? Na rantse da Allah sai na kwave miki riga na fizge abuna. Dama sai da na ce ke ke min xauke-xauke ki ka qaryata.”
Da qarfi Atika ta riqe rigar Blessin ta direta har qasa kyayyyy!
Ta varke ta, sai ga breziyarta. Bata yi shayin komai ba ta kwaleta daga qirjin Blessin xin.
Matan biyu da ke hira suna kallon ta’adin da Atikar tayi wa Blessin xin. “Don Allah dubi wannan tonon asiri, ina
tsiya ina wata abu wai Breziya?” In ji Beeba. Rose ta ce, “Uhum! Ba ki san mutanen gidan nan ba kin ji.” Beeba ta ce,
“Ni fa wallahi qyamar undis xin da wata tayi amfani da su ni ke.”
“To kin dai gani, ita bata raina ba. Ke abin sata fa bai wuya a gidannan, har garin quli-quli da garin kwaki sata ake.”
“Uhum! Ai maza sun sha damu Rose, me yiwuwa sakayyar sai a lahira.” Ta faxa hawaye na ziraro mata. Rose ta dube ta “Kar dai kema namiji yayi miki sanadin zuwa nan Beeba?”
Ta gyaxa kanta tana me share hawaye. Rose ta kaxa kanta “Ashe ba ni kaxai ba, nayi zaton ni kaxai ce macen da ya kamata ta faxi kalmar namiji qanin aljali, ashe da akwai ki Beeba?
Yanzu shi kenan maza sun yi nasara a kanmu?”
Sai ta kama kuka, “Ban da ina da qulafucin rayuwa Beeba wallahi da tuni na kashe kaina. A duk sadda zan tuno wai ni ce namiji ya kawo a gidan Jarin, ni ce a matsayin Bursuna, duk gatana namiji ya watsa min shi, duk isata namiji ya qasqantar dani, daga qarshe sai ga sharri. Beeba sakayyata sai a lahira, domin ko duniyar nan tayi mana kaxan.
A kullum fatana da burina shi ne in mutu in huta. Me yasa ni ban yi sa’a irin ta mata ba? Me yasa nazo duniya a banza zan koma a wofi?”
“Naki qalubalen ki ka sani Rose, ba ki san nawa ba.” Rose ta ce, “Duk qalubalenki ba ki kai ni ba Beeba.” Ta ce, “To haka ne, yanzu bari in yi sallah don lokacinta ya taho.”
Ta miqe, Rose ma ta miqe, “Nima bari in je in xan runtsa tunda waxancan matsiyatan sun gama faxan.” Suna shirin wucewa, Gandiroban ya shigo yana tushe da qeyar wata matashiyar budurwa kyakkyawa, hannunta sagale da ankwa.
Hawayen da ke fita
a idonta shi zai tabbatar maka da baqin cikin da ke tare da ita, don yanayinta bai nuna fargabar zuwanta gidan Kason ba, sai dai ya nuna tarin baqin cikin da ke damfare a zuciyarta.
Gandiroban ya cire mata ankwar ya kuma bata korayen kayan na jarin, ya kuma nuna mata dogon xakin me gadaje da yawa, ya kuma bata lambar gadonta.
Sai dai ko kaxan bata fahimci abinda ya ke faxa ba saboda zuciyarta tayi nisa, daga qarshe ma sai rushewa da kuka tayi.
Rose da Beeba suka tausaya mata matuqa gaya, domin ko sun kula tana cikin baqin ciki. Har Gandiroban ya fice ba tare da ta fahimci abu xaya da yake magana a kanshi ba.
Tamkar a yanzu ne al’amuran suke faruwa a idonta da kwanyar kanta, tamkar an tsikareta ta miqe da gudu ta nufi Rijiyar da taga wata Bursuna ta zura Guga da nufin jawo ruwa.
Da qarfinta tayi nufin afkawa cikin Rijiyar, amma da sauri su Rose da suka fuskanci abinda take shirin yi suka riqota har ta zura qafarta huda Rose da Beeba suka riqo hannunta.
Ta dube su da idanunta da suka kumbura ta ce, “Kuyi wa Allah da Manzonsa ku rabu da ni in mutu ko zan huta. Don girman Allah ku bankaxo ni a cikin Rijiyar nan.”
Aka qyalqyale da wata matsiyaciyar dariya. “Shegiya duniya me gida biyu, ku tausata Rijiyar tunda haka ta zava.” In ji me rawar nan ta alanta.
Beeba ta jawota “Me ki ke tsammani idan kin kashe kanki? Anya ko kina iya xaukar zafi biyu na nan duniya da na qiyama?”
Ta ce, “Zan iya mana, ke dai bar ni in mutu tunda na xauki wannan takaicin babu abinda ba zan iya xauka ba, ku qyale ni don Allah. Wallahi rayuwata bata da amfani.”
“Ba za mu qyale ki ba, don ba za
a
so ki mutu a kafira ba.” Suka janyo ta daga bakin Rijiyar.
“Hahaha! Kowar-raba mugun abu bai yi kallo ba
.” In ji gwanar rawa. Su Rose suka wuce da baquwar da ba su san ko sunanta ba zuwa xaki da nuna mata gadonta da kayan da aka bata, waxanda ta saki a qasa.
Beeba ta miqo mata ruwan
Pure water
. Tabi ruwan da kallo tamkar ba ta san ko meye ba. “Ki sha ruwa zuciyarki zata yi sanyi.” In ji Rose.
“Bana buqatar duk wani abu da zai nuna xorewar numfashina. Abu xaya ya kamace ni a duniyar nan shi ne mutuwa, ita kaxai ni ke buqata. Ita kaxai za ku bani ku faranta min, don Allah ku bani guba in sha in mutu, idan har qaunata ku ke domin Allah ku nuna min hanyar da zan bi in mutu ko ku bani guba!”
Suka zuba mata ido suna kallo, lallai ta zarta su haxiyar baqin ciki, sai dai ba su da tabbacin itama namijin ne ya yi mata? oho!
Beeba ta dubeta ta ce, “Baiwar Allah ya sunanki?” Baquwar tayi maza ta ce, “Mutuwar za ki gwada min?” Ta tambaye ta. Beeba ta ce, “A’a ni ba zan nuna miki mutuwa ba, saboda naga kina son nuna wa Allah bai yi miki daidai ba.” Tabi Beebar da ido. “Me yasa za ki yi fito-
na-fito da Ubangiji a kan qaddarar da ya xora miki? Anya ko kina da qarfin faxa da Allah?”
Ta kaxa kanta alamar a’a. “To me yasa ki faxa da faxar Allah? Duk abinda ya same ki bai zamo zai kuskure miki ba kamar yadda ba ki san lokacin da ya qage ki ba to haka ma ba ki da tabbas a kan abin da ya qaddaro a kanki.
Shi ba wai bawa abin da yafi dacewa da shi face yin biyayya ga Ubangiji, da karvar kowace irin qaddara. Kiyi haquri da abinda Allah ya qaddara a kanki, ki dube mu nan duk qaddarar ce ta kawo mu, me yasa muka yarda da qaddarar mu?
Saboda mun yi imani da Allah da Annabinmu, da son mujaddada musuluncinmu da kyautata zato a kanmu. Idan ki ka kashe kanki kin fa mutu kafira. Kin ga nan zafi can zafi, to don me za ki rayu a cikin Musulunci sannan ki mutu a kafirci, ke ko ribar me ki ka ci?
Idan hakan ta tabbata?”
Ta fashe da kuka tana faxin “Ba ku san abinda ya faru a kaina ba shi yasa ku ke bani haquri, na tabbata da kun ga abin da ya faru a kaina to da ku da kanku kun kashe ni don in bar
tunawa. Wayyo Allah iyayena!” Ta faxa tana qara rusa wani sabon kukan.
Duk yadda suka so su rarrasheta abin ya ci tura. Kuka kawai take yi wanda idonta ya kasa tsayar da hawayenta. Tuni suka koma tausaya mata. Haka kuma duk yadda suka so ta kai wani abu a bakinta hakan bai yiwu ba.
Me rabon abinci ma da ya zo ya bata nata kason wanda bai wuce tayi loma shida ko bakwai ba. Ba ma wannan ba, kasa gane ko meye tayi. Shi dai ba tuwo ba saboda dusar ciki, shi kuma ba Teba ba saboda duhu-duhun shi.
Haka wannan baiwar Allah ta kasance cikin kuka da ciwon rai har tsayin kwana tara ba ta shan ko ruwa, duk yadda Rose da Beeba suka so ta kafe a kan ra’ayinta na qin cin komai da kuma neman sanadin da za ta mutu. Haka kuma idonta bai huta da zubar ruwa ba.
Haka kuma koda ta kwanta to ba dai bacci ba sai dai ko don gangar jiki ta samu afuwa, amma idonta biyu da kuma hawayen da ke zuba.
Da ace hankalinta bai yi tashin gwauron zabi ba, to da taga abin mamaki a lokacin da wasu Bursunonin ke sharar barci, lokacin ne kuma wasu daga cikinsu suke baxalarsu.
Amma da yake abu xaya idonta ke hango mata wato mutuwa, shi yasa bata ga komai ba. Ba ta ma kawo mata ranta gani ba. A cikin kwananta na sha biyu ne yayi daidai da cikar shaddar gidan, wadda su Bursunonin ne ke jigilar kwashewa.
Gandirobar mace ta iso da nufin yin jagora zuwa rakiyar Bursonin zubar da bahayar. Bokitan qarfe