Showing 1 words to 3000 words out of 35284 words
Chapter 1 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx
MANYAN MATA
2
Na
Hadiza Barau Gidan Iko
(Maman Assibi,
Matar Aminu Idris)
08035191669 – 08078500055
Haqqin Mallaka (M) Gidan Iko
Copyright © Gidan Iko 2019
GODIYA GA ALLAH
Allah Ina godiya da baiwarKa marar a dadi a gare ni, ba ni da bakin godiya sai dai fatan in tabbata a cikin salatin Annabi, wanda na ba wa kyautar raina da rayuwata abadan da’iman.
KYAUTARWA
Ga duk inda masoya Annabi suke a faxin duniya, ina qaunarku saboda qaunar Annabi da ku ke, Allah Ka yarda mu so Annabi (S.A.W).
YABAWA DA JINJINAWA
Ga Nafi’u Salisu, jagoran tafa rubutuna ya fito rangaxaxau, Allah Ya qara qwarin ido, Amin.
TUKWICI
Ga Hadizatu ‘yar’uwata. Ina miki addu’a da fatan Allah Ya yarje miki, Ya lumunce miki saboda qaunar Annabi (S.A.W) da ki ke Maman Zee-zee.
SADAUKARWA
Ga matan da suke haquri da duk wani qalubale na ‘GIDAN AURE’, suka yi haquri suka jure, waxannan su ne ‘Manyan Mata.’
BUGAWA A COMPUTER:
NAFI’U SALISU
08038981211 - 08093248661
SHARHI
Na xauki lokaci mai tsawo ina nazarin litattafai biyu na Marubuciya ‘HADIZA BARAU GIDAN IKO,’ wato ‘MUGUN QULLI’ da kuma ‘DA SAURAN KUKA…’ Tabbas dukkannin litattafan nan biyu sun cancanci yabo da jinjina ga Marubucinsu, ban yi zaton cewar Marubuciyar zata iya yin wasu kamarsu ba, ashe duk wannan nafila ne.
Lokacin da na ci karo da littafin ‘MANYAN MATA’ sai naji tamkar waxancan litattafai biyun da nake ba da misalin inganci ta fuskar tsaruwa ashe ma akwai wanda ya dama su ya shanye, wato ‘MANYAN MATA’.
Da labarin Jaruma Habiba (Beeba) kaxai ya isa babban darasi ga mai karatun wannan littafi, don kuwa ta kasance ‘yar Direba kuma wanda ya xauki rayuwar holewa ba a bakin komai ba, a gefe xaya kuma Mahaifiyar Beeba ta kasance mace mai haqurin da a wannan zamanin sai sa’ar gaske ake iya samun me irin shi.
A rayuwar Beeba babu abin da ta tsana kamar Xansanda, sai ga shi kuma wani Xansanda ya kusanci zuciyarta, inda soyayya ta kai su ga aure.
Alhaji Bashir Bangis, shahararren maikuxi, kuma shahararren mai kyauta da Naira, idan ma yaga dama zai iya saye gidan da ka ke haya a ciki kuma ya ce ka zauna kyauta ba tare da ka biya shi kuxin haya ko sule
ba. Mutane da daman kan ce ‘Yansanda suna da sharri, to sai dai kuma Alhaji Bashir Bangiz ga alama shi ya fi ‘Yansandan iya sharrin.
Haqiqa alqalamin rubutun Marubuciya (Maman Assibi) mai kaifi ne.
Lallai a gaida ‘Yar Gidan Iko (HADIZA BARAU).
Nafiu Salisu
(Marubuci/Manazarci)
1 ga Watan Janairu, 2019
11:15pm Na dare.
MANYAN MATA - 2
S
intia ta faka motarta a gefen maqabartar, ta kira wayar oganta ta shaida mishi tana bakin maqabarta, inda ya tabbatar mata da inda zata samu kabarin Rose kamar yadda aka tabbatar mishi.
Don haka ya ce ta bari dare yayi kafin ta xora aikinta na gaba. Tayi zaune cikin mota tana jiran dare. A gefe xaya kuma a cikin maqabartar inda wasu matasa biyu ke aikin gina kabari.
Walqiya ta haska wal! Kasancewar dare ya fara mamaye duniyar, ga kuma hadari wanda yasa garin yayi duhu xunxum! Xaya daga cikin matasan me fuskar matsorata ya taso da sauri yana zare ido, kafin yaja tsaki “Mts! Wai mutum ya baro garinsu yazo Legos neman kuxi amma ya vuge da haqar kabari.”
Xayan gajere me qaton kai yayi dariya. “To ina laifi ma da ka samu haqar kabari ba kwasar bayan garin qabilu ba?”
Ya sake jan tsaki “In ban da qaddara ma
me zai fiddo ni cikin wannan daren haqar kabari, salon in je in tuno kabarin marar haquri ya liqe min ba gaira ba dalili.”
Me qaton kan yayi dariya tamkar ya faxi qasa. “Kai dai wallahi an yi xan Daudu! Tsoronka ko wata macen ma albarka. Wanda ya mutu fa ai duk rashin haqurinshi ya saurara.”
“Naji ba komai, ai tsoro gaskiya ne.” Suka ci gaba da haqar kabarin, xaya na tonowa xaya na fito da qasar
bakinsu riqe da fitilu saboda duhun da Maqabartar ta xauka sakamakon hadarin can.” Me fuskar matsoratan nan ya dubi abokin aikinshi.
“Wai Sabo ba ka jiyo nishi a cikin kabarin can ba?” Ya nuna kabarin da yatsa. Sabon ya dube shi “To ko kana son ce min na cikin kabarin ne zai fito?”
“Hakan ma ai tana iya yiwuwa.” Ya ba shi amsa. “Kai dai Allah ya sauwaqe maka, mutum kamar ba namiji ba…” Iska ya turo wani xan ho
go daga kan kabarin da yazo ya jiyo nishi.
Ai ko ya daka tsalle tare da qurma ihu ya dawo bayan Sabo ya maqalqale shi. Ya ce, “Kai zan fa ci ubanka ka ji, ta ya ya ma wanda ke cikin kabari zai yi nishi bare ka ce min motsi yake? Ko bai mutu ba ai in ya shiga kabarin zai mutu.”
“Ni dai wallahi da na sani da ban zo ba, dole sai na haqa kabari zan ci abinci?” Ya faxa yana sakin sabon kuka. Can ‘yan tsirarun mutanen suka taho da Gawar suka shigo maqabartar, inda su Sabo suka ga wani me zureren rawa
n
i yana gaba, ga alama kuma Shehun Malami ne.
Aka ida gyara kabarin aka saka gawa ciki aka bi da qasa. Allah kasa mu cika da kyau da imani (Gidan Iko), in da me fuskar matsorata ya zubawa kabarin ida ya ce ya jiyo nishi ido
, inda aka ce ayi salati ga shugaban halitta Annabi Muhammad (S.A.W).
Ana cikin salatin ne qasar kabarin nan ta soma bajewa, inda me
fuskar matsorata yaja bayan Liman ya
tsaya yana kallon kabarin kafin mutane su ankara hannu ya soma fitowa tare da faxin “Wayyo Allah!”
Gaba xaya kallo sai ya koma sama, wai Shaho ya xauki Giwa. Kan ka ce me? Me fuskar matsorata ya soma tsallake kaburbura yana qoqarin ficewa. ‘Yan rakiyar Gawa kuma da suka soma salati ba su ko qarasa ba suka rufawa me fuskar matsorata baya, in da Shehun Malami ma ya ranta a na Kare, addu’ar da ba su yi wa marigayin ba kenan sai dai fatan Allah yasa an je a sa’a.
Ta gama fitowa daga cikin kabarin tana maida numfashi inda Sintia ta kula da mutanen da ke tsere, ta fito daga motarta ta doso maqabartar inda tayi arba da Rose ta farfaxo. Da sauri ta qarasa ta kamo ta ta ida fitowa ta maida qasa ta rufe saboda gudun fasuwar qwai. Kan ka ce meye? Ruwa ya sauko da qarfi, in da Sintia da Rose suka shiga mota suka harba titi.
Katafaren gidan ya ba wa Rose mamaki, sai dai da yake a gajiye take sai ta voye mamakinta. Ta dubi Sintia ta ce, “Taimake ni in cire wannan farin kayan na mutan lahira. Kai na ga mutuwa da idona!” ta faxa tana kallon Sintia.
Sintia tayi dariya ta ce, “Ke ai har lahira kin je wanda ya shiga kabari ai ya gama zuwa lahira.” Tayi wanka ta ci abinci “Amma fa na jinjinawa hikimarki Sintia su fa yanzu na mutu a zatonsu, uhm ai in an san wata to ba a san wata ba, don haka ya zama dole in
wuce da ke Abuja gidan ogana saboda tsaro ko ya ya ki ka ce?
”
“Sosai ma kuwa.” Rose ta ce, “Lallai ke masoyiyata ce ta gaske, sai dai da akwai qawayena Deena da Beeba, suma ina son su kuvuta ya ya zna yi Sintia?”
Ta ce, “Kar ki damu suma zan kuvuto da su, sai dai ba yanzu ba saboda idan ki ka
bayyana a yanzu to da akwai matsala, amma kar ki damu hanyar da ki ka kuvuta suma ta haka za a biyo amma ba yanzu ba sai kin shekara.”
BABI NA TARA
S
hekara xaya daidai da mutuwar Rose sun saki komai sun karvi rayuwar da qaddara ta zava musu, sai dai ba su bar tunowa da ita ba, ba su kuma daina kewarta da alhininta ba.”
Gandiroban ya qwalawa Beeba kira a kan ta zo tana da baquwa. Gabanta ya sara saboda babu me zuwa wurinta bare tayi tunanin shi ne ya zo.
Da ta bi bayan Gandiroban da sanyin jiki inda ta isko me son ganinta, ko kuma baquwarta a tsuke da wando da riga na
Body hog
, ga kuma qaton gilashi wanda ya hana a gane ta ta farat xaya.
Don haka ba ta iya shaida fuskarta ba kasancewar kitson kanta na qarin gashi da ke qara voye fuskar tata, suka gaisa inda muryar taso yi mata kama da muryar da ta sani, sai dai ta kasa ganowa.
Rose ta bata abinda ta kawo musu tare da rubutacciyar wasiqar. Da haka tayi mata bankwana ba tare da Beebar ta iya shaida baquwar tata ba.
Da a ce Rose bata mutu ba to da ta ce Rose ce don haka ta iso ga Deena ta bata kayan masarufin inda ta sanar da Deenar ita fa bata shaida baquwar da tazo gareta ba.
“A’a to kuma ba ki nemi sani ba?”
“Ina niyyar hakan ta miqe da shirin tafiya, amma ga wata wasiqa nan bari mu gani ko zan iya gano ta.”
Ta buxe wasiqar ta soma bin rubutun ciki da ido.
‘Nasan za ku yi matuqar mamakin abin da wasiqar nan take xauke da shi, ina fatan dai my Beeba da my Deena kuna lafiya? Kamata ya yi in fara sanar da ku sunana, to amma hankalina yana kanku, tunanina yana gare ku.
Sai dai zan yi muku albishir cewa na kusa kawo qarshen zamanku a kurkuku, me yiwa ko a nan na tsaya za ku iya gano me wannan wasiqar t
o
in ma ba
ku xauki hannu ba ni ce taku Rose.
Ina kuma tabbatar muku da ban mutu ba har gani na zo naga Beeba, sai dai ban ga Deena ba. To ina fatan lafiya lau take, kuma ku saurare ni ina nan zuwa a cikin sati me zuwa.
Sai dai ina so ku zama cikin shiri domin ko Allah ya kawo mana xauki don bai yanke zamanmu a duniya a matsayin ‘yantattu ba, sai na zo taku ‘yar uwarku Rose.
Beeba ta miqe tsaye a ruxe inda Deena ta dubeta “Ke ko lafiya…?” “Ina fa lafiya, duba wasiqar nan.” Ta miqa mata ta karva tana karantawa.
A ruxe ta dubi Beeba “Wai wace Rose xin?”
“Wadda ki ka sani dai.” Bata mutu ba? To ya ya abin yake?” Beeba ta zuba tagumi “Nima abin da ni ke son sani kenan Deena. Ba ni ko tantama qawar Rose me suna Sintia tana da hannu a kan abinda ke faruwa. Amma ta yaya ake haihuwa a ragaya? Lamarin da ban mamaki, ta yaya hakan ke faruwa?
Zamu tabbatar da yadda abin ke faruwa, idan ta dawo sati me zuwa. Amma ko zan yi matuqar farin ciki idan har na kuvuta daga bakin gidan nan in ji Beeba.
Deena ta ziraro da hawaye, ban da kar in butulce da na ce nafi buqatar rayuwar gidan nan a kan ta ‘yanci, irin wadda Rose ta ke mana fata. Wane irin farin ciki zan samu bayan baqin cikin da ke lulluve a zuciyata?
Mutuwa ita nafi buqata da komai a duniya Beeba. Har yau har gobe na kasa afuwanta wa kaina a kan kisan iyayena domin ko ni ce silar komai ta ya ya za su yafe min?
Ta yaya zan ji daxin duniya? Ta ya ya zan manta baqin cikin da na haxiya a duniya sanadin xa namiji? Na yafe Beeba koda Allah zai sa Rose ta yi nasarar kuvutar damu to ni ba zan
je ko’ina ba saboda babu in da zan je in ji daxin duniya da rayuwa.
Idan kuma za ku iya taimakona to kashe ni kawai ya kamata kuyi, shi ne na tabbatar da ku xin masoyana ne…”
“Kinyi kuskure da yawa a rayuwarki Deena, me yasa ki ke faxar irin wannan maganar tamkar ba Musulma ba? ki bari mu ga abin da Rose zata iya yi a kanmu.
Me yiwuwa da akwai abin da Allah Yake nufi a kan hakan, kin gane?” Ta gyaxa kanta “To maza kiyi Istigifari.”
Sati xaya daidai da zuwan Rose xin sai gata ta sake dawowa da shigar baxxa sawu. In da ta kawo wa Beeba abinci me xauke da wasiqa da sirinji da ruwan allura.
Ba ta tsawaita ba ta juya in da Beeba ta karanta dogon sharhin a kan allura da sirinjin. Deena ta zuba mata ido. Tabxijan! Lallai ashe duk tunanin mutum da akwai inda za a zo bai zo ba.
Beeba ta aiwatar da abinda aka sanar da ita kafin wayewar gari itama ta ce ga garinku nan. Deena ta shiga matuqar ruxewa. To idan aka samu akasi fa?
Da haka aka fice da Beeba aka binne, saboda in dai wanda aka yakewa hukuncin zaman din-din-din ne ya mutu babu wani jinkiri ake sada shi da kushewa. To me za a jira? Dama zaman wa’adi yake mutuwa ita ce haddinshi to ya mutu.
A kan idonsu a ka binne Beeba, don hakba su ko bari ta farko ba suka tono ta, inda ta farko taga Beeba. Rose ta dubeta.
“Sannu da zuwa, ya mutanen lahirar?”
Beeba ta yi murmushi ta ce, “Na lahira suna can ai ban kai ga isa ba na juyo. Ina Deena?”
“Deena tana can itama ta kusa dawowa nan.” Beeba ta dubi Rose “Ya ya abin yake ne Rose?” Ta ce, “Uhum, na me fa?”
“Na wannan siddabarun mana.”
“Allura ce me xauke rai da numfashi na tsayin awa biyar ko ma fiye da haka, tamkar dai doguwar suma
wadda za a farfaxo bayan wani
lokaci, ina fatan kin gamsu?”
“Na gamsu my Rose, amma yaushe Deena za ta iso?”
“Kar ki damu
,
very soon
. Ke ce ma me alhakin dawo da ita, ma’ana ke za ki kai mata allurar saboda idan na ce ni zan je to da akwai matsala, me yiwuwa ma qwai ya fashe.
”
Haka kuma aka yi, tsawon wata huxu da isowar Beeba ta matsa da son a fito da Deena. Bisa tilas Rose ta haxa mata kayan mutuwar ta doshi garin Lagos.
Ta kuma isar da saqon ga Deenar sai dai an samu akasi a kan Deena, domin ko lokacin da tayi tata mutuwar da maraice ne, inda bisa tilas aka kaita mutuware cikin gawarwaki, ta kuma farko a cikin gawarwaki inda ta nemi ficewa saboda tsoron gawarwakin.
Sai dai tsaron da ke akwai ya hana yiwuwar hakan, bisa tilas ta tsumayi gobe inda da ta motsa zata gane da motsi kusa da ita.
Tana ji tana gani ta kwana cikin gawarwakin.
Asubar farko tayi nasarar ficewa bayan ta zari kayanta da aka yi mata fit aka jefa cikin matattun. Sai dai ta rasa inda zata nufa.
Da sauri ta yanki hanyar da bata san inda zata kaita ba. tana ta sauri taji an danno mata
Horn
. Ba ta tsaya ba inda Rose ta fito ta riqo hannunta.
“Haba baiwar Allah ina zuwa ne?” da sauri suka faxa motar, Beeba taja suka xauki hanyar Abuja.
Wannan shi ne haxuwar Deena da Beeba da Rose a gidan yarin Qiri-qiri da kuma irin yadda suka samu kuvutowa, suka tare a garen na Abuja har ma suka soma xaukar fansa a kan maza da alwashin da suka sha na qarar da duk wani namiji a duniya, da kuma tarkon da Rose ta faxa, ta kuma samu kuvuta.
Sai mu biyo su domin jin shin ya ya za su qare da maza? Shin za su yi nasarar kashe su kuwa? Mu bi Maman Assibi ‘yar Gidan Iko domin jin abin da ke gaba ga Manyan Mata masu duniyar.
**
**
Koda Rose ta zo qarshen tunaninta sai ta ce “Kun tuna yanzu ko? Kun tuna yadda muka rayu a gidan kason? To ta ya ya zan yarda in sake komawa? Ai ko a mafarki sai dai tashin zance.”
Beeba ta share hawayenta “Tunda a yau xin ranar tuna baya ce a yau xin ya kamata mu san labarin juna, ta yadda za mu fuskanci inda muka dosa da matakin da ya kamata mu xauka.”
Deena ta ce, “Gaskiyarki Beeba, amma ina so in tambayi Rose shin ina Sintia a yanzu? Kuma waye oganta da sana’ar da suke?”
Rose ta dubeta ta ce, “Haqiqa Sintia ma ta taka rawar gani a rayuwarmu Deena, sai dai ki bari mu saurari labarin Beeba idan muka ji nata kema sai ki ba
mu naki, kafin nima in ba da nawa wanda za ki ji ko wacece Sintia a wurina, da kuma labarinta ita da oganta, da ma aikin da ya tara mata kuxin da tayi mana hidima har ta mallaki wannan gidan da muke ciki.”
Suka dubi Rose. “Nayi zaton gidanki ne?”
“A’a gidan Sintia ne, don haka kuyi haquri mu fara da Beeba za ku ji komai a kan Sintia.” Suka dubi Beeba “Ke muke saurare.” Ta xaga kanta sama tana tunanin ta inda zata soma kafin ta ce!.
ASALI
Sunana Habiba, ni haifaffiyar jihar Katsina ce a wata unguwa me suna Saulawa, layinmu sunanshi layin Shaixan.
Mahaifina sunanshi Musa Malmo, amma an fi kiranshi da Malmo. Direban babbar mota ne wanda idan ya lula ya bar gida sai muyi kwanan wata biyu ba mu saka shi ido ba.
Matanshi biyu ne Amaka ita ce babba kafin mahaifiyata me suna Binta. Amaka ‘yar qabilar Yoruba ce amma musulma, sai dai musuluncin Amaka suna ne kawai amma tana buqatar gyara sosai
.
Koda yake an ce asali Amaka
karuwar Babana ce wadda suka xaura dadiro da ita har ta liqe mishi. Wasu sun ce babu aure ta biyo shi Katsina, wasu kuma sun ce ya aure ta sun daxe a tare amma Allah bai sa Amaka tayi ko vatan wata ba, in da kuma Allah da ikonshi ya
haxu da mahaifiyata me suna Binta har ya ji yana son aurenta.
Duk da halin Mahaifina na son sheqe aya da idan ya cira ya tafi sai Baba