Showing 27001 words to 30000 words out of 35284 words

Chapter 10 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

da burin da ya wuce in siyi gida mu tashi mu bar na Bashir Bangis, don haka na shiga adashe wurin wata maqwabciyata me suna Zainun Awaisu Maman Jiniyo. Ta tambaye ni ko ta nawa ni ke so na ce mata ko ta qarshe ta bani ba damuwa.

Tafiya ta tafi, har na soma mantawa da qalubalen Bashir Bangis. Kwatsam! Sai ga saqon zai tura Zainil Abidin garin Lagos ya kai wa wani abokin kasuwancinshi wani saqo.

A take na ji jikina ya xauki kyarma, wadda ban san ko ta meye ba. Naji hankalina ya tashi matuqa gaya, duk da ba yau ne farkon aiken nashi ba amma sai na samu kaina da fargaba ba kaxan ba.

Ya rungume ni a lokacin da zai tafi Lagos. Ya ce, “Zan tafi Lagos Beeba, idan na dawo zan binciki cikin nan naki naji har yanzu shiru, ko dai ba ya karvar ajiyar da ni ke ta bayarwa ne?”

Nayi qarfin halin yin murmushi

“Kar ka damu, ajiyarka na nan na manta ne ban faxa maka ba, wata uku da ya wuce ajiyarka ta tsuro.”

Yayi

kissing

xina yana me bayyana farin cikinshi. Aljanna ta tabbata ga mace tagari irin Beebata, uwar

‘ya’yana. Bari in je idan na dawo da akwai kyauta da goron albishir na musamman.” Da kyar muka rabu ya tafi ya abr ni cikin kewa da zullumi, ashe qarshen ganawar kenan, ashe sallamar bankwana muka yi.

Bawan Allah! Ashe an haxa mishi tuggun kwance burkin mota don ana son ganin bayan shi. Ba tare da ya sani ba ya xauki hanya da qarfin ikon Allah.

Tafiya mai nisa ya hau titin na garin Legas yana cikin sauraren qira’ar Sheikh Sudai motar ta xaukar Shanu da ke gabanshi yana dab da iske ta ya nemi burki ya rasa.

Mota ta soma yawo a kan titi qarshe dai ta silala a cikin dokar daji, bata yi burki ko ina ba sai a kan wani babban dutsi, wanda ya hargitsa komai in da mota ta lanqwashe tare da Zainil Abidin.

Hankalina ya kasa kwanciya duk da sunan Allah da ni ke ambato, hakan bai sa ni natsuwa ba har dare ya raba ina ta neman wayar Zainil Abidin tana ta

ringing

ba a xaga ba. Hankalina ya tashi matuqa gaya.

Misalin sha xaya na kasa haquri da kiran wayar kuma har yanzu

tana ta qara ba a xauka ba. Tashi nayi da nufin shiga gidan Bashir Bangis in tambaye shi ko ya samu yin magana da Zainil Abidin.

Na shiga gidan ana shirin rufe

Gate

xin nayi sallama inda na iske Hajiya Tamadina cikin rigar bacci. Ta dube ni da wani irin kallo wanda na kasa fassara shi.

“Hajiya ina yini?

” Tayi saurin xago min hannu “Dakata baiwar Allah, in ba ki biyo Bashir gida ba ashe

ba karya ba ce ke.” Wani abu ya daki qirjina sakamakon abinda ta faxa min, “Ni fa ai na shiga uku tawa ta same ni, ashe har zamanin yazo da ake bin mazaje har gida, lallai sunanki ya fi kwartuwa sai dai ‘yar ina da maza!”

Kwakwazon da take yi ne ya fito da Bashir Bangis, yana ganina ya soma murmushi “A’a Habiba lafiya dai?” Na share hawayena “A’a me ki ka yi mata Tamadina?” Ya faxa da amon murya.

Ta watso mishi wani kallo “Me fa zan yi mata tunda ta biyo ka gida ai sai dai ko ka tambaye ta me yiwuwa kaxaici ne damuwarta. Kuma yanzu sai ka ce min me a kan zargin..”

Ya xaga mata hannu “Kar ki kawo min maganar banza mana, sai menene in kin yi zargin?” Ya maida dubanshi a kaina “Yi ahquri kin ji Habiba, bata da hankali ne kin san sanyi ya busa. Mene ne

?”

“Dama na kira wayar Zainil Abidin naji tana ta qara amma bai xauka ba, shi ne nazo in ji ko kayi magana da shi?” Ya ce, “A’a ban yi waya da shi ba, wanda na tura shi wurinshi xin ne dai ya kira ni yake ce min har yanzu bai iso ba.”

Hankalina ya qara tashi, inda ya bani haquri a kan in bari zuwa safe za a san abin yi. Na miqe inda ya biyo ni wai ya rako ni, in da zuciyar Hajiya Tamadina kamar ta fashe, ahse dai mijin nata neman matar maqwabcinshi yake.

Da sauri na maido qyaure don naga qoqarin shigowa yake. Batun barci bai taso ba, don haka sai na xaura alwala na gurfana gaban babban Sarki Mai amsa roqon me roqo.

Ina kan sallayar wani bacci ya kwashe ni, wanda a cikin baccin nayi wani irin mafarki me kama da harigido. A firgice na farka saboda abin da na gani, wai Zainil Abidin ne a cikin fararen tufafi masu xigon wani abu a jiki me kamar jini. Ina cikin halin rabe alaqar farin tufafi da xigon jini na jiyo qarar bugun gida. Haka kawai naji jikina na vari da kyarma.

BABI NA SHA BIYAR

N

a buxe gidan inda nayi arba da wasu baqin fuskoki, ganin waxannan fuskoki ya tabbatar min da ba lafiya ba. Cikin rawar

baki da varin jiki na tambaye su ko lafiya? Suka yi min bayanin da ya damalmala xan sauran tunanin da ya yi min saura, wai mijina ya yi hatsari har an kawo shi asibitin General Hospital a

Emergency

.

Ba zan iya shaida maganganun da na iya ji a bakin mutanen bayan wannan ban san yadda aka yi ba na tsinci kaina a gaban gadon da Zainil Abidin yake. Na bishi da kallo, kanshi xaure da bandeji, hannunshi da qafarshi duk naxe da bandejin.

Babban abin da ya ida qarar da nutsuwata bai wuce xaurin da aka yi wa qirjinshi da wani qarfe ba. Na sake duban bandejin da ke naxe a jikinshi wanda ya rine da jini ya koma ja.

Kafin in gama haxa lissafin da zan haxa uku da biyar su bani takwas kawai ji nayi ana wurwura ni ana katantanwa da ni, ban sake sanin abinda ya faru dani ba sai farkowa nayi naga Hajiyar Zainil Abidin tana shafa min ruwa.

Na dubeta inda naga ruwan hawaye a idonta, da sauri na tashi zaune “Sai haquri Habiba, mun yi rashi Zainil ya amsa kiran Mai duka Allah.” Na zubawa bakin Hajiyar ido ina kallo

amma fa na daina fahimtar abin da take faxa bayan na tsinci jin mutuwar Abidin.

Ba zan iya sanin ya ya ni ke a wannan lokacin ba, na miqe tsaye bayan Hajiyar ta shiga xaki sakamakon kukan da ya qwace mata, wanda ke nuni da tsantsar alhini na xan nata.

Ban san in da na dosa ba, na samu kaina a wani wuri da ban san ko’ina ba ne. tafiya kawai ni ke ba tare da nasan in da zan je ba, ban kuma san abin da zai je ya dawo ba. Na dai ga mota ta faka a gabana inda naga Kabir qanin Zainil ya fito ya damqo hannuna zuwa cikin motar.

Ban yi gardamar bin shi ba muka dawo gida in da na iske an kawo gawar Zainil Abidin. ‘Yan uwa na kusa da na nesa duk sun bazamo suna ta faxar alherin Zainil Abidin.

Hajiya ta riqo hannuna “Ina ki ka je Habiba? Kiyi haquri da rashin da muka yi.” Na dinga bin mutane da ido har aka shirya shi aka ce in zo muyi sallamar bankwana.

Na durqusa a gaban makarar, sai a lokacin naji idona ya ciko da hawaye. Haka kayi min Zainil? Me yasa kayi min haka? nayi asararka ba zan tava samun tamkarka ba.

Allah

Ya jaddada rahama a gare ka, Allah yasa kaje a sa’a, ka bar ni a cikin alhini da kewa…” a ka janye ni saboda na soma sakin layi. Wasu maganganun ba na me hankali ba ne.

Ina kallo aka jawo Umar wai ya zo ya yi sallama da Abbanshi ya yi mishi addu’a, sai dai abin tausayin sai

da a ka xauki makarar yaron ya fasa kukan a dawo mishi da Abbanshi.

Hajiya ta riqo shi tana rarrashi idonta da hawaye. “Kayi haquri Umar, Abbanka ya tafi tafiyar da babu dawowa, sai dai fatan mu iske su muna ma su imani.” Haka aka yi zaman makoki ba na uhum bana um’um.

Alhaji Bashir Bangis ya shigo cikin gida wai ya yi

mana gaisuwa, na kalle shi sai na tuno da maganar da ya faxa min a kan wai na kusa zama matar Gado, shi xin zai gaje ni ne kamar yadda ake gadon kayan mamaci, shin ya tara sani ne da Allah a kan rasuwar Zainal ko ko Allahn musuru gare shi?

Idan har ban manta ba ya ce min tarkon da ya xana min ya kusa kama ni a wuya. Lallai kam tarkonshi ya kama ni ba a wuya ba faxawa nayi tsundum! Ya yi gaisuwa ga dangin Zainil Abidin ya kuma juyo gare ni yana min gaisuwar amma ido kawai na zuba mishi ba tare da na iya buxe baki na amsa ba

.

Ya fita waje inda ya aje buhun shinkafa da katan xin taliya da mai da garin masara

, kai sai ya zamo hidima sosai ya yi a mutuwar. Amaka tazo min gaisuwa ita da Meri inda ta ce Babana bai zo ba.

Haka aka miqe inda aka yi arba’in amma har yanzu ban dawo hayyacina ba. Hajiya tasa ana min rubutu cikin ikon Allah na dawo hayyacina har na ankara da lallai nayi rashin Zainil Abidin, rashi kuma irin na har abada sai dai a Darussalam.

Nasiha da nuni kullum Hajiya cikin yi min su take a kan in yi haquri da rashin Abidin, abinda ba ta sani ba shi ne na rasa Zainil Abidin na rasa bangon da zan jingina ba ni da sauran fata ko buri a rayuwa.

In ma ina da shi to bai wuce Yusuf da Umar ba, sai fa ita Hajiyar bisa dole na miqa hannu na karvi

qaddarar da rayuwa ta tanadar min kullum a cikin tattalina Hajiya take inda cikina ya shiga gardamar zama a jikina kullum cikin ciwon mara da ciwon ciki. Daga qarshe dai ciki ya sulale ya zube, inda na fita takaba.

Ana haka Allah ya kawo Babana yazo wa Hajiya gaisuwa ya kuma buqaci da in ko

ma gida tunda na fito takaba saboda varin da nayi. Hajiya taso ya bar ni saboda sanin bani da wani gata amma ya ce in koma gidan dai ba don naso ba na komai gidanmu inda Amaka ta soma maganganu.

“Ni fa gaskiya tsoron zama da Beeba ni ke ji, ina dalili ka zauna da mutum wanda bai yarda da qaddara ba da son qalawa mutum sharri? Haka fa tazo ta xauke shegen yaron can me kama da qiriqu duk don ta ja min sharri. Mun goga da uwarta itama ta dawo gida za mu goga, to don ka gaya mata a yanzu nima na goge sanin da tayi min da daban yanzu ma daban ni ke.”

Ban saurari Amaka ba na barta ita da Babana na shige xakin Innata na zauna ina tariyo yadda rayuwa ke wurwura ni, na rasa Innata na rasa Zainil Abidin, to wa

ya rage min kuma me zai kuma zuwar min a gaba? Ba ni da sauran fata ko buri a duniya.

Na natsa a tunanin yadda Bangis ya yi mana kutse da kancal a rayuwa, yau gashi ya yi min sanadin rasa Zainil Abidin. Tsayin wata biyu a gidanmu sai ga Bangis ya diro a ka sanar da ni ana kirana a waje, na ture mamakina gefe na fito na iske shi cikin shiga wadda ta nuna shi a matsayin me kuxi.

Ya buxe min motar wai in shiga, na kaxa kaina alamar a’a ko a da da ban qarasa saninka ba bana jin zan iya shiga motarka bare yanzu da walqiya ta haska min kai.”

Ya yi murmushi ya ce, “Habiba kenan, komai za ki faxa min ina jin daxin shi koda ko baqar magana ce. Bari ni in fito ai an ce maso xan tsuntsu shi ke bin shi da jifa.” Ya fito yana rufe motarshi.

Ya zuba min ido yana rungume da hannunshi, “Nazo ne don in sanar da ke don kar ki ji abin daga sama, na samu Baba har mun gama magana sati biyu masu zuwa za a xaura aurenmu…”

“Da wa?” na tare shi da azama. Yayi murmushin mugunta ya ce “Da ke mana. Ai kin shigo cikin gadona, duk da ba ayi rabon gadon ba sai kuma nayi sa’a Baban yana da maitar hatimin nasara, inda nayi mishi yayyafi har ya bani aurenki a arha!”

Duk da baqin cikin da ke tafasa zuciyata hakan bai hana ni dubanshi da faxa mishi baqar maganar da ya ce tana mishi daxi.

“Uhum! Ka tafka babban kuskure a rayuwarka. Kai ne mutum xaya da ni ke jin ba zan tava yafewa ba har sai mun tsaya a gaban zatin Ubangiji a kan ta’addancin da kayi min.

Wallahi-tallahi so xaya ne a gare ni kuma tuni na baiwa Zainil Abidin, bana jin zan iya yi wa Zainil kishiya. Aurenmu auren zobe ne wanda ba ya rabuwa ko mutuwa ta ratsa, don haka mutuqar ni kaxai ce mace a duniya to ina tabbatar maka da sai dai ka mutu babu aure.

Wallahi tallahi ba zan tava aurenka ba, idan kuma ka matsa har na aure ka to na rantse da Allah ni ce ajalinka, don sai na tabbatar maka da ni xin ba

qin gado ka samu, da dai na barka da Allah saboda ba ni da qarfin qwatar ‘yancinda ka murxe min, to amma ba wahala kaje ku qullo auren ina saurarenku

.”

Ban tsaya jin komai daga gare shi ba na shiga gida. Da dare sai ga Baba ya same ni yana sababi da masifa, na dube shi yana ta kumfar baki.

“Ai kin yi qarya in yanke hukunci ki ce ba haka ba, idan ba kiyi haka ba ashe ba ki tsotsi nonon tsiya a wurin Binta ba. To na rantse sai kin

auri Bangis, ni na tava ganin mutumin arziki irin Alhaji Bangis? Mota ya siya min kyauta ya kuma bani kuxi masu tsoka.

Shi ne don ke matsiyaciya ce marar rabo ki ce ba ki aurenshi? Tsiyar me ki ka tsinta a auren Xansandan da ya mace? To buxe kunnenki ki saurare ni, matuqar ba za ki auri Bangis ba to maza wallahi ki tattara kayanki

ki bar min gidana ki nemi wurin zuwa ki kuma kama wani uban ba ni ba.”

Hawaye ya cika idona. Ya ya za a yi Baba ya fahimce ni? Ya ya za a yi ya san Bangis shi ya kashe Zainil Abidin? Na zube a gabanshi “Na roqe ka Baba don arzikin Annabi (S.A.W) ka bar ni in ji da mikin rashin Zainil Abidin, ba zan iya auren Bashir Bangis ba, amma ka aura min kowanne irin namiji amma ban da Bangis saboda shi ne silar da na rasa mijina. Shi ne ya kashe min mijina…”

“Ka ji ba? ka ji ko?” In ji Amaka “Ai ke dai kam kin shiga uku, kin zama ma hawayi ke babu me mutuwa sai dai an kashe miki sai kin yi dalilin qalawa mutane sharri.

To kai ka ji shi Bangis xin ne ya kashe mata miji, mutumin da ya yi haxarin mota ya mutu ka ji wanda ta qala wa mutuwar kamar yadda ta qala min sharrin kashe uwarta.”

Ban tsaya sauraren Amaka ba na ci gaba da bai wa Baba haquri amma ya ce in dai ba zan auri Bangis ba to ba ni da wata rana a gare shi, kuma ba zan zauna mishi gida ba. Duk yadda naso in rufe ido in yi wa Babana biyayya sai dai idan na tuno gara in zauna da baqar Gamsheqa a kan auren Bashir Bangis.

Dole ba don naso ba na tarkata kayana inda Amaka ke ta qyalqyala min

dariya. “To kai idan ka koreta ina zata je bayan ta gama feshe dangin uwarta da rashin mutuncin sun kashe mata uwa?”

Ya ce, “Ta je ma ko’ina amma ba gidana ba, don xakin da ta ke zaune ma ina buqatarshi.” Amaka ta dube shi “Kana buqatarshi?” Ta tambaye shi. “Eh, don a kusa xaura min aure, to in tana ciki a ina za a saka Amarya?”

Amaka ta daki qirjinta “Qarya ka ke wallahi Malmo…” ni dai ban tsaya sauraren rigimar Amaka da Babana ba, na fice daga gidan don bana jin zan iya auren Bangis xin, gara kawai in bar gidan.

Gidan Hajiyar su Zainil Abidin na nufa saboda can ne kaxai ni ke da tabbas don ba na jin ko zan shiga halin da ya zarce wannan zan tunkari dangin Innata, don na yanke qauna a gare su.

Hajiya ta tarbe ni da tambayar “Lafiya?” cikin hawaye na kwashe komai na sanar da ita. Tayi shiru kafin ta ce, “To Habiba me zai sa ba za ki auri Bangis xin ba? naga mutumin kirki ne, zai kuma riqe ki bisa ga amana, kuma ai auren shi ne cikar martabar ‘ya mace. Ko ni zan so ki auri Bangis don naga karamcinshi.

Haka kuma Marigayi ya sanar da ni irin alherin da ya yi muku. Kiyi haquri ki aure shi sai dai in ba ki sonshi ne to ba zan matsa ba.” Nayi shiru ina jin ciwon yaudarar da Bangis ya yi wa makusantana har suke kallonshi a mutumin kirki.

Sai na ji ba zan iya sanar da Hajiya cewa mutumin da take yabo take kuma kallon shi mutumin kirki shi ne ya kashe mata xan da ta fi so a duniya ba, sai naga in rufe wannan sirrin tsakanina da ita sai kawai na nuna

wa Hajiya cewa ba zan iya auren Bashir Bangis ba, saboda mun yi zaman amana da matarshi kar ta ce na ci amanarta.

Hajiya ta ce, “To babu komai, Allah Ya yi miki zavi mafi alheri.” Nayi zamana a gidan Hajiya tsawon lokaci ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login