Showing 30001 words to 33000 words out of 35284 words

Chapter 11 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

ta sana’ata hankalina kwance.

Ranar wata

Laraba na shaidawa Hajiya cewar zan je tsohon gidanmu in kwaso kayana. Hajiya ta ce hakan ya yi, ki ma kwaso kayanku duka kin ga megidan idan zai zuba ‘yan haya sai ya zuba.

Na tafi da niyar kwaso kaya, ashe wata qaddarar ta kira ni. Na buxe gidan na shiga inda rayuwata da Zainil Abidin ta dawo min tamkar a faifan Garmaho. Na soma haxa kayanshi tun daga

sutura, da takalma da turarenshi da agogo, na haxa komai na kammale na haxo nawa kayan kaf na tattare.

Ina cikin haxa kayan sai ga Bangis tamkar an wurgo shi gabana, ya bada dammm!

Ya shigo cikin xakin ya maida qyaure ya datse! Na dube shi a tsorace yana murmushi.

“Kin manta na faxa miki tarkona a wuya zai kama ki? Me yasa masoyi ya zamo maqiyi Habiba? Kin manta duk so da qauna ne yasa nayi abinda nayi? Aurena gare ki shi ne qarshen zance. Matuqar dai kina son zamanki lafiya to ki aure ni kawai.

Ni ban ga aibuna ba, shin bani da kyau ne kamar mataccen mijinki? Ko ko ban kai

matsayin da ki ke so in kai ba? ki faxa min abinda ki ke so zan yi miki shi.”

Na rikice matuqa har na rasa abinda zance mishi saboda ganin ya rufe mu a xaki. Na ce, “Ka buxe min qofa zan fice.” Ya dube ni “Ai yau ranata ce tunda na kula ba ki san ina cikin kukan so ba, ki fa bar raina allura qarfe ce!”



Ban tsinke da lamarin ba sai da naga ya fito da wata kwalba kamar turare ya soma fesawa a take xakin ya game da wani qauri shaqar wannan abin shi ya sabbaba mutuwar jikina, har ta kai ga ina kallo Bangis ya keta alfarmata, duk da ina cikin rashin tsarki.

Ina rungume a qirjinshi ya soma shafa fuskata wadda ke fidda

hawayen baqin ciki, wai yau ni ce aka keta wa haddi, ina ma a ce ina da ikon da zan

haxiye zuciyata in huta da baqin cikin da ke ta bibiyata?

Haka rayuwa take? Ni kam ban zo duniya da sa’a ba. ganin hawaye yasa ya soma magana “Bana son kukanki Habiba, yanzu na soma sonki, yanzu na soma qaunarki, ina kuma tabbatar miki da kina xauke da xana ko xiyata a cikinki. Don haka ina ga na kawo qarshen matsalar sai ki zo mu rungumi juna tunda mun zama xaya.”

Ya tashi da shirin ficewa, ya aje min kuxi ya kuma ce zai turo Direba ya kwasar min kayana. Ya fice inda ya bar ni a tsaka me wuyar fita. Kayan da ban samu zarafin xaukowa ba kenan.

Hajiya ta dube ni a firgice ganin idona da hawaye. “Ya Rasulillahi, me ya faru?” Na zube a gabanta ina kuka me cin zuciya.

“Hajiya ya cuce ni, ya yi min fyaxe. Hajiya na shiga uku na lalace ya keta alfarmata.” Hajiya ta soma share min hawaye “Daina kuka Habiba, faxa min abin da ya faru.” Na kwashe labarin komai na faxa mata.

“Hasbunallahu wani’imal wakil, Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, saboda kin qi aurenshi ya yi miki wannan tozarcin? To wallahi sai nayi qararshi, sai an bi miki haqqinki…”

“A’a Hajiya, ki rabu da shi da akwai abubuwa da yawa wanda sakayyar su sai a lahira, koda an bi min haqqina ba zai tava goge baqin cikin da ya dasa min ba, na bar shi da Allah.”

Hajiya ta taya ni kukan har na soma bata haquri. Sai dai me? Wata biyu da yin haka na tashi da qurajen baki masu nuna min ina da ciki kasancewar bana laulayi sai da qurajen baki idan ina da ciki. Na sanar da Hajiya halin da nake ciki, ta kwashe ni zuwa asibiti aka kuma tabbatar min da cikin muka dawo gida.

Hajiya ta ce, “To Habiba, ina ga dai haquri kawai za ki yi da auren

Bangis don kar ya zmao ana zunxen yin abin kunya, idan kin aure shi tunda dama haka ya so kin ga za ki haihu cikin rufin asiri ba kuma za a zarge ki da cewa kin yi cikin shege ba

, ko ya ya ki ka gani?”

“A’a Hajiya, zan zubar kawai…” “A’a ba za ki zubar ba, zamu rungumi qaddarar da aka jarrabe mu da ita.” Ciki na da wata biyar Bangis ya zo gidan Hajiya suka gaisa da hajiyar, inda ya shaida mata ya zo a kan maganata da kuma cikina.

Wai zai aure ni in haihu a gidanshi. Hajiya ta ce, “Bashir ba ka yi wa Habiba adalci ba, ba haka ake yi ba, don ta ce bata sonka kayi mata fyaxe don tayi ciki ka fake da cikin a aura maka ita don dole ba. Ai babu aure a tsakaninku yanzu sai in ta haife cikinta.”

Ya ce, “Kiyi haquri Hajiya, sonta ne ya ingiza ni ga yi mata haka, ki rarrasheta na yarda idan ta haihu sai a xaura mana aure, xiyata ko xana kuma ba shege ba ne don ban son a kira ta shege ne yasa naso ayi auren ta haihu a gidana.”

Suka rabu da Hajiya a kan sai na haihu ko za a yi auren mu. Bayan watanni huxu na haife cikina wanda Allah da nashi ikon na haifo yarinya wadda ba ta ma zo da rai ba sai dai abin mamakin yarinyar fara ce tas irin farin nan marar fasai, wanda ake cewa zabaya.

Dama ya zo a cikin littafi cewa yaron da a ke samun cikinshi alhalin uwar tana cikin rashin tsarki to zai zamo zabiya ko makaho, ko wata tawaya. Hajiya ta kira Bangis ta damqa mishi gawar ‘yarshi don yi mata sutura.

Bayan hakan da tsayin lokacio sai ga shi wai ya dawo a kan maganar aurenmu, inda Hajiya ta ce mishi ita duk yadda na ce haka za’ayi, idan ina muradin shi to ita addu’a kawai zata yi mana, don haka ya zo gare ni ya nemi so da yardata.

Na dube shi na ce, “Babu abin da zan ce maka illa Allah ya isar min abinda kayi min. ni dai ina jin nazo duniya ne don baqin cikinka ya kashe ni, to don Allah

kasa wuqa ko bindiga ka kashe ni in huta da mugun qullin da ka ke mini.”

Maimakon jikinshi ya yi sanyi da maganganun da na faxa mishi, amma abin mamaki sai yayi murmushi yana shafar sajenshi.

“Tabbas maganarki haka take, kin zo duniya don ni kaxai matuqar kuma ba ki yarda da aurena ba sai in ce tabbas baqin cikina zai kashe ki, don haka shawarata gare ki kawai ki ce in fito in aure ki, idan kuma ba haka ba to sai in ce duk abin da ya biyo baya ba laifina ba ne.

Don haka daga yau ba zan sake bibiyarki ba, sai fa in cewa ki ka yi in zo muyi aure, amma fa ki sani babu wani namijin da ya isa ya aure ki bayanni

.

Duk kuma wani abu da zai biyo baya to kar ki xauke shi me sauqi, aurena shi ne tabbatar zamanki lafiya tunda ki ka ga na kawar da mijinki saboda ke to babu abin da ba zan iya yi a kanki ba, sai an jima.”

Ina kallo ya tashi motarshi ya bar gidan, nabi qurar motar tashi da kallo. Tabbas duk abinda ya faxa a kaina ba a samun kuskure sai ya tabbata amma dai nasan dama can Allah ya zana hakan a cikin qaddarorina, ban da tsanarshi ta mamayi raina da na rufe ido na aure shi ko don in zauna lafiya.

To amma ai bai yi ya Allah ba, kuma ko zan mutu babu aure ba zan auri mushiriki marar tsoron Allah ba, bare kuma wanda ya kashe min Zainal Abidin, ya kuma

keta alfarmata har na zamo nayi ciki na haihu ba tare da aure ba.

Lokaci ya ja sosai inda na ci gaba da kitso da qunshi har ma da Alkaki, ina kuma samu sosai in tallafi kaina har in agaji

Hajiya da bata gajiya da hidimtawa Umar da Yusuf.

Sai dai me? Dare xaya babbar qaddarar ta sauko min, ba tare da sani ko shiri ba bare kuma sallama lamarin ya soma daga kan wata yarinya da na yi wa kitso da qunshi, ana wayar gari tace ga garinku nan (mutuwa).

Babu wanda ya kawo komai a rai sai ya zamo ina yawan shiga fargaba a duk ranakun Laraba da Asabar, ban san ko me hakan ke nufi ba, sai ya zamo a duk ranar Laraba ko Asabar duk wanda zan yi wa kitso ko qunshi to in sha Allahu gari na wayewa za a tsinci labarin mutuwarshi.

Da tafiya tayi tafiya tun mutane ba su ankara ba har dai suka ankare. Na soma fuskantar qalubalen rayuwa, a ka soma yawo da ni a duniya ana yaxa ni cewar duk wanda na yi wa kitso ko qunshi to in sha Allahu kwananshi ya qare.

Kan ka ce me? Sai ya zamo babu me zuwa gidan Hajiya da sunan ya zo kitso ko qunshi, kai sai ya zama ma mutane suna tsoron shigowa gidan Hajiyar don kar su baqunci qiyama.

Na rasa kuxin da zan yi hidima, sauqina xaya Hajiya na samun tallafi wurin qannen Zainil Abidin, Kabir da Ukashatu.

Hajiya tana yi min nasiha a kan maganganun da ke yawo a gari “Kar ki damu kanki Habiba, haka duniyar take, haka mutanen cikinta suke. Komai da ki ke gani yana faruwa ne idan Ubangiji ya ce zamo (kun) sai ki ga ya zamo (fayakun).

Don haka kar ki yardar wa kanki wani abu zai zo ba daga Allah ba, duk da ina tunanin mutum marar tsoron Allah a cikin lamarinki ba zato ni ke ba Allah shi ya fi mu sanin abin da kenan, amma ki bar wa Allah.

Zan je wurin Yayana, Malami ne wanda ba ya aiki da Aljani bare shirka, zan sanar da shi abin da ke faruwa nasan

insha Allahu komai zai wuce, kema sai ki dage da addu’a.”

Na share hawayena “Babu komai Hajiya, na gode da irin kulawarki, wallahi Hajiya kin maye min gurbin Innata da ubana wanda bai mutu ba. Hajiya rayuwar nan ta ishe ni…”

“Kar ki furta wata kalma akasin godiyar Ubangiji, ba ki san sai Allah yana son bawa ba yake jarabtarshi? Ba mu fi Allah sanin halin

da ki ke ciki ba kuma da yarda

r shi zai kawo miki

mafita.

Ana cikin haka Hajiya taje wurin Yayanta Malam Ahamad, ta zayyane mishi komi, inda ya ce ta bashi kwana talatin ya kuma ba da sadaka a kan Allah ya bada rinjaye. Sati xaya da yin haka na kwanta bacci inda nayi mafarki da Hajiya Tamadina wai na shaqeta ban sake ta ba sai da ta daina numfashi.

Na farka a firgice ina karanto addu’ar mugun mafarki, kawai gari na wayewa sai jin mutuwar Hajiya Tamadina nayi. Na shiga tsananin ruxani, ta yadda abubuwan ke faruwa wannan ta wuce kusan sati biyar sai kuma na kuma yin mafarki da qawata Maijidda tun ta talla, wai na saka wuqa na soketa

a

ciki jini ya yi ta zuba har ta faxi qasa a mace.

Gari na wayewa itama na samu labarin mutuwarta, wai an shiga gidanta an soka mata wuqa. Zuwa wannan lokacin na gama fita hayyacina saboda sanin abubuwan da ke faruwa babu shakka da akwai wani mugun qulli wanda ke faruwa a kaina.

A take maganganun Bangis suka shiga dawo min a kwanyayar kaina, na abinda zai biyo bayan qin aurenshi da ma abinda zai same ni, qarshe kuma tarkon da ya ke faxar zai kama ni a wuya

,

m

e

ye alaqar mafarkina da mutuwar mutanen da na mu’amalan

ta? Me yasa ni ke ganin sababin mutuwarsu kafin

gari ya waye mafarkin ya zamo gaskiya?

Ban voyewa Hajiya ba, duk abin da nike gani a mafarki kafin gari ya waye ya zmao gaskiya sai da na faxa mata. Hajiya tayi shiru alamar nazari kafin ta ce, “Mu barwa Allah Habiba, Yaya ya ce mu ba shi kwana talatin, to muyi haquri har kwanakin su cika, da ikon Allah komai zai kwaranye, ke dai ki dage da addu’o’i.”

Haka na dage da addu’o’i amma maimakon abubuwa suyi sauqi sai abu ya yi ta gaba-gaba, matuqar dai zan kwanta bacci to da ikon Allah sai na hango me qarar kwanan da ina farkawa zan tsinci mutuwarshi.

Sai ya zamo idan na fito na zama abin gudu, ana ganina za a soma guje-guje tamkar an ce ga mutuwa nan. Koda yake ni na san bani da maraba da mutuwar sunanmu ma xaya ne.

Ba ni da damar shiga jama’a bare wata sabga ta taro, haka kuma matuqar dai zan kwanta barci to zan yi mugun gani da me qararren kwana kafin gari ya wayi in ji

labarin mutuwar a cikin waxannan baqaqen lamuran ne na kwanta bacci inda na ceto wata tsohuwa da ke can unguwar me suna ‘Yarkulu, amma ita kuxi na bata ba kisa kamar yadda na saba gani ba.

Sai dai me? Itama ‘Yar kulun labarin mutuwarta da samu sai ya zamo na gane dai ba lallai sai na sa

makami na yi kisan a cikin mafarkin nan ne ake mutuwa ba. A’a, indai zan za

n

ga mutum a

a cikin mafarkina to ya zamo marigayi.

To in ko haka ne na gama barci a duniya matuqar barcin zai zamo ajalin bayin Allah. Haka ko aka yi, a lokacin da dare ya yi mutane suke sharar barci abinsu, ni kuma ina gurfane a kan sallahaya ina roqon Sarki me yawan rahama da ya dube ni da rahamar shi mayalwaciya da kawo min

xauki don arzikin Annabi (S.A.W).

Sai dai me? Ashe shi bacci ba a cin bashin shi. Wani lokacin ma ina kan sallayar zai kwashe ni wanda a ciki zan hango wanda ya riga mu gidan na gaskiya. Sai naga shin me zai sa mafarkina ba zai hango min Alh. Bashir Bangis ba ko don in rage raxaxin da ya qunsa min?

Sai na gane da ina da iko a kan shi mafarkin to da na taka mishi birki ko don xauki xai-xan da ake yi wa al’ummar Annabi, waxanda ba su ji ba su gani ba.

Haka kuma lokacin da Ubangiji ya qagi halittarsu ban sani ba, amma kuma ina ganin sanadin mutuwarsu me yasa? Allah don qudurarKa da buwayarKa, in dai a cikin barci zan riqa mugun gani ka sauke min barci a rayuwata.

Ana haka nayi shirin zuwa gidanmu don in xauko wasu daga cikin kayan da na baro a can, na iske

Amaryar Babana ta tare, yarinya qarama sai dai ga alama idonta a buxe tar-tar kallo xaya nayi mata na gane ‘yar bariki ce ta sosai.

Amaka ta dube ni

“Shi kenan tamu ta same mu, annoba ta iso ai Beeba ta zama mahawayi duk in da ta shiga to bala’i ya shigo.” Ban tsaya na ji qarshen zancen na Amaka ba na fito.

Sai dai me? A daren na kwanta inda nayi mafarki da amaryar Baba

wai ina son shaqe ta amma ban yi nasarar shaqe ta ba, saboda kokawa muka yi da ita inda ta gaggartsa min cizo har wuri uku.

Na shafa wurin ina mamakin yadda lamarin yake faruwa zuwa yanzu dai na gama yanke tsammanin da akwai wani qulli a kaina me wuyar kwancewa. Anya ko zan ci gaba da zama cikin mutane ina kallo ana qarar da su a kan idona? Kar fa wata rana

in hango Kabir ko Hajiya, ko Umar ko Yusuf a cikin mafarkin mutuwata?

Babu ko shakka barin gidan Hajiya shi ne mafi alheri a gare ni, dama sauran mutane, in yaso sai in koma dokar daji in da zan kalli namun dawa wanda ko sun mutu babu me asara. Idan kuma sun cinye ni to huta roro waken Gizo ya qi ‘ya’ya.

Na tashi na shiga xakin Hajiya don in yi mata sallama in kuma faxa mata abinda na yanke. Ta dube ni ta ce, “Babu inda za ki je Habiba, ki bari kwana

talatin xin da Yaya ya xiba ya cika nasan da akwai abinda zai yi.”

Na ce, “Hajiya ina tsoron mafarkina ya hango min xaya daga cikin bangayen da suka rage min. Hajiya ina tsoron in hango wanda ba na son rasawa, da ace mafarkina zai nuna min Alh. Bashir Bangis ko Babana ko Amaka da Kawun Innata da zuri’arshi to da ba zan damu ba. Hajiya ya zama dole in bar ku don ku zauna lafiya, bana son ta silata ku haxu da wani tuntuve a rayuwa…”

Hajiya ta ce, “Kenan ba ki xauke ni uwa ba Habiba..?” Nayi maza na ce, “Wallahi Hajiya ban da uwar da ta zarta ki, ina son zamanki lafiya ne

shi yasa zan yi haka.

Duk uwa bata gujewa xanta duk abin da zai faru da shi insha Allahu zamu yi nasara kuma idan mafarkinki ya hango miki ni Habiba kwana ne ya qare, don haka in dai na isa in faxa miki to kar ki je ko’ina, Allah yana sane da ke kuma babu wanda ya isa ya tilasta shi yanke miki matuqar ba shi ne ya kawo qarshen lamarin ba.

Shi fa bawa umarni ne kawia nashi da godewa a kan abind a aka jarrabe shi. nayi shiru ina sauraren nasihar Hajiya wadda tayi kama da ta Zainil Abidin.

Tafiya ta miqa

in da na dage da lallai ba zan kuma yarda in yi bacci da dare ba, ko zan yi to sai dai in yi

na rana. Ashe ban sani ba baccin ranar shi ne tonon asiri a gare ni, saboda shi baccin daren rufin asiri ne a gare ni, domin ko lokacin da ni ke hango mutane a mafarkina to ni da kaina ce ke zuwa ina aiwatar da abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login