Showing 18001 words to 21000 words out of 35284 words

Chapter 7 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

yayi

kissing

xina

. Na haxa mishi ruwa ya yi wanka ya ci abinci inda Yusuf ya yi barci. Na dube shi “Ina ga ba sai na tambayi Baba ba, tun safe fa na xauko shi amma shiru na zaci Amaka ta biyo sawu ta tambaye ni ba’asi amma shiru, kuma ban san lokacin da Baban zai zo ba.”

Da haka dai na rufe babin bin ba’asin Baba na riqe Yusuf a wurina kafin ka ce me? Yusuf ya yi kyawun duba, ya yi qiba kullum cikin tsabtarshi, haka zan zube su shi da Umar in yi ta kallonsu ina jin daxi.

A yau Zainal ya bar gida saboda aikin dare gare shi, don haka na saya gidan ina kallon wani fim xin Hausa na (Ado Gwanja), sai ji nayi ana bugun qofa, na zo na tambayi wa ye?

“Ni ne, har kun rufe ne?” Na gane muryar Alhaji Bashir ce, sai na buxe ina shirin gaishe shi kawai naga

ya shigo cikin gidan, don haka sai na biyo shi don in yi mishi fashin baqin Maigidan ba ya nan.

Bayan mun gaisa ne ni ke faxa mishi Maigidan ba ya nan yana Dutsinma aikin dare gare shi.

“To Allah Ya ba da sa’a, ina mutumina?” Ya tambaya wato Umar, na sanar da shi ya yi barci. “To ba damuwa a shafa min kanshi.” Ya miqe muka yi sallama in da na zo na rufe gidan.

BABI NA SHA UKU

Y

a dafa kafaxarshi ya juyo suka yi ido huxu.

“Haba Bangis, sallamata uku amma ba ka san ina yi ba, me ka ke tunani?” Ya cire hularshi ya aje a kan tebur xin da ke gabanshi ya shafi fuskarshi kafin ya dubi abokin nashi Alhaji Barde.

“Wallahi ban ji sallamarka ba Barde.” In ji Alhaji Bashir.

“Wai me ka ke tunani ne haka?”

“Mts! Kai dai bari, ina matar Xansandan nan da na faxa maka?”

“Na gane?”

“Wallahi Barde jiya kwana nayi ina mafarkinta, na rasa yadda zan yi in mallaki yarinyar nan.”

“Mts!” Barde yaja tsaki, “Amma shaixancinka ya tashi a banza matuqar ka kasa mallakar yarinyar nan! Nayi mamaki kai me kamar Tamadina ka tsaya sauraron wata mace.”

“Ai gaba ma da gabanta Barde, babu abinda Tamadina ta fi Beeba sai tsufa! Na rasa yadda zan yi Barde, wallahi ba qaramin ka mu Beeba tayi wa zuciyata ba.

Amma nayi alqawarin matuqar kuxi suna da amfani sai na mallaki Beeba, babu ranar da ba na mafarkinta har ya zamo ba ni da wata sha’awa sai ta Beeba.

Rannan fa har suvul da bakan kiran Tamadina nayi da sunan Beeba, amma da yake na iya ta sai nayi saurin

gyara kwavar da nayi. Don nasan Tamadina da shegen tsegumi.”

Ya dube shi “Amma ina ga kamar fasuwar maganar nan Bangis zata iya

zubar da girmanka a idon Xansandar can. Ba ka ce tsohon yaronka ba ne?”

“Haka ne Barde, sai dai kasan ni wata irin zuciya gare ni wadda idan tana son abu matuqar ba ta same shi ba to babu sauran zaman lafiya sai na bata ko zan huta ni da zuciyata.

Amma na gama yanke shawarar da zata fisshe ni, zan yaudare ta da kuxi duk da nasan mijinta ya koyar da ita sonshi ta hanyar so da qauna da kulawa, amma na san duk yadda so ya yi daxi bai kai daxin da kuxi suke da shi ba, ko ba haka ba Barde?”

Barde ya ce, “Ba fa kowace mace ce ke so don kuxi ba, matuqar ta kasance so xaya take yi wa mijinta, bana jin za ka yi nasara. Shi mijin ya kamata ka yaudara da kuxi ta yadda zai sakar maka ita ka aure, in yaso sai ka nuna mishi in dai yana da kuxi mata huxu ma sai ya tara su, ko ba haka ba?”

Suka tafa Alhaji Bashir ya ce, “Wannan maganar taka dutsi Barde, amma bari in tunkari ita matar tukunna, nafi shakkarta a kan mijin, don in ta yarda shi dole ya yi mata yadda take so.”

Da haka suka yi sallama ya nufo gida. Hajiya Tamadina tana zaune ya shigo ba ta ko dube shi ba bare ya samu arzikin sannu da zuwa. Ya qaraso ya zauna kusa da ita.

“Wani abu ya faru ne Tamadina?”

“Babu abin da ya faru illa na soma gajiya da kirana da Beeba da ka ke, wai don Allah meye gaminka da Beebar nan ne? Xazu ma fa da Beeba ka kira ni, shin sunan nawa ne ka manta? Ko ko ita Beebar ka ke muradi?”

Ya riqo hannunta. “Kai Tamadina rigima, kin san Allah ya saka min qaunar yaronsu Umar, shi ne nayi mafarkin zata jefa shi Rijiya, shi ne fa abin ya tsaya min a rai.” Ya shara mata ita (wato qarya).”

Tamadina ta ce, “To in ma ta jefa shi Rijiyar meye naka? Ina ce ita ta haifi xanta ko ka fi ta sonshi?”

“Yanzu dai kiyi haquri, ni ban son tsegumi.” Ya miqe ya nufi xaki ta raka shi da kallo kafin tayi kwafa.

Ina cikin yi wa Yusuf wanka Hajiyar su Zainal tayi sallama. Da sauri na tarbeta muka shiga xaki muka gaisa, inda taga Yusuf.

“A’a, Yusuf ne ya yi haka?”

“Aiko dai Inna.”

Na kwashe yadda na iske shi a gida na sanar da ita. Ta ce, “Allah Sarki Habiba, da ba sai ki kawo min shi ba? marayan Allah da bai fito a zanin goyo ba ai ba a bar shi cikin qalubale ba.”

Ta rungume Yusuf yana mata dariya, kafin ta dubi Umar “Kai dai babu ruwana da kai tunda raggon miji ne da ba ya iya ba da cefane.” Ta faxa tana lakace hancinshi.

Yayi dariya don ya xauka wasa take mishi. “A’a Inna in dai

cefane ne sai kin rasa inda za ki zuba.” Hajiya ta zube mana kayan da ta riqo mana, Garin Xanwake da kayan haxi da dai kaya masu yawa.

Na xauko kek xin da na yi wa Zainal na zuba mata a Kula. Tayi ta sa min albarka da nasiharta irin ta uwa tagari. Muka yi sallama.

A yau ma Zainal aikin dare yake, don haka na yi wa yara wanka suka yi bacci, ni kuma na buxe littafin Hausa na Fatima Hussaini El-Ladan me suna (Baqar Saqa) in da naji labarin jarumar, ya so ya yi shige da nawa labarin na rayuwata.

Don haka na shagala da karatun, kawai sai ganin mutum nayi. Tsoro ya kama ni me tsanani.

“Ina ta sallama ba ki ji ba.” Ya faxa yana zama kan kujerar falon. A tsorace muka gaisa saboda ni dai gaskiya bana son ya ke zuwa Maigidan ba ya nan.

Ya dubi littafin hannuna “Ashe kina karanta littattafan nan?” Na ce, “Eh ina yi.” Na ba shi amsa cikin yaqe. “Ai ko zan siyo miki su.” Dam! Qirjina ya amsa. Ya miqo min ledar da ya shigo da ita ta Sajuma Plaza me xauke da gasasshiyar kaza da

drinks

me sanyi, na amsa jikina a sanyaye.

“Na sayowa Tamadina ne sai naga bai kamata na siyo mata ita kaxai ba shi yasa na siyo muku a tare.” Na soma kyarma a zaune, kenan matsayina ya kai na matarshi da har ya ke haxa kafaxarmu? Na tambayi kaina.

Kafin in samo amsar ya xora da abinda ya kusa kashe ni a zaune. “Kar ki ji komai Beeba, ni xin ki xauke ni tamkar Zainal Abidin, duk abinda ki ke so ki tambaye ni kanki tsaye ko meye shi, duk tsadar shi zan yi miki, in ma kuxi ki ke so to kiyi min magana kin gane?”

Ya faxa idonshi a kaina, sai ya zamo wasu maganganun bana fahimta saboda ruxani, duk da bai fito ya faxi wani abun assha ba, to da akwai abin da yake so ya ce ko ya faxi.

Da haka

ya fice daga gidan ya bar ni ina tufka da warwara. Ban tashi tunawa da ledar kazar da ya kawo ba sai washegari, shima Zainal ne ya ganta ya kuma nemi ba’asi na faxa mishi.

Ga mamakina zai shinshino wani abu amma da yake Allah ya wanke mishi zuciya ba ya da xora zargi sai ya ce “Haka yake da alheri, Allah ya biya shi.” Na kasa amsawa, ina son in faxi abinda ni ke tunani a raina amma ina tsoron abinda Zainal

zai yi wa fahimtata, bisa tilas naja bakina nayi shiru.

Kwana uku a jere ina yawaita mugayen mafarkai, wasu a kaina wasu a kan Zainal Abidin. Mafarkin ko me son raba tsakanina da Zainal.

Bisa tilas na dage da Azkar da addu’o’i har Allah ya taimake ni komai ya daidaita. Kwanaki suka gangara inda har na manta da wani Alh. Bashir Bangis bare wani tarnaqinshi.

Zainal ya dawo daga aiki inda na dubi idonshi ya yi ja sosai. “Abban Faruq me ya samu idonka ne haka?” Ya ce, “Kawai naji yana min raxaxi amma ban san ko meye ba.”

Na ce, “Ina ga bari kayi wanka da akwai maganin ciwon ido sai ka saka.” Bayan ya yi wanka ya ci abinci na xiga mishi maganin ciwon ido ya kwanta bacci, sai dai me? Tashin da zai yi ido ya ce bai san zancen ba.

Ina tsakar gida ina aikina na jiyo shi yana kirana, na isa da sauri inda na iske yana lalube, na kamo hannunshi meye? Kina ina Beeba? “Gani nan kusa da kai ba ka ganina?”

“Bana ganin komai Beeba, idona duhu kawai yake gani.” Dam! Qirjina ya amsa. “Ba ka ganina Zainal?” Ya ce, “Bana ganinki Beeba.” Kawai sai naji kuka ya rikito min, na soma kuka inda ya shiga lalubena.

“Haba Beeba, me yasa za ki yi kuka a kan lalurar idona? Ba ki san ko wane bawa tare yake bisa siraxin rayuwarshi da qaddara ba? ai abu ya zo da sauqi tunda bai yi sanadin rai ba ya tsaya ga ido.”

Ya yi nasarar lalube ni ina ta sharar hawaye, ya rungume ni yana faxin “Daina kuka don Allah kin ji.” Na share hawayena “Na daina kuka Zainal, Allah ya baka lafiya, alfarmar Annabi (S.A.W) da Alqur’ani zan yi duk yadda zan yi insha Allahu sai ganinka ya dawo daidai.”

“Na gode Beeba, Allah ya bar min ke, ke ce gatana, ke da Hajiya.” Haka muka kwana ni dai ban yi barci ba.

Washegari na faxa mishi zan je gidan Hajiya in sanar da ita don a kai shi asibiti. Tare da Hajiyar muka dawo ta iske shi idanu basa gani.

Hajiya ta riqe baki cikin mamaki tana kallonshi ta ce, “Allah Mai iko! Abidin kai ne haka? haka qaddara tazo maka? Allah Ya baka mafita, Allah ya sauwaqe maka.” Ya amsa da “Amin Hajiya.”

Muka nufi asibiti ina sharar hawaye Hajiya na bani haquri. Mun xauki lokaci a asibiti amma babu wani ci gaba da aka samu, dole muka tarkato muka dawo gida. Duk inda Hajiya taji me magani zata anso, daga ni sai Hajiya ke kanshi yayin da (

Headquarter

) xinsu sun dai zo kusan sau huxu duba shi sun kuma bada kuxi dubu goma amma daga haka ba mu sake ganin qeyarsu ba.

Alhaji Bashir Bangis ma ya yi rawar gani sosai har na soma da na sanin xora zargi a kanshi ashe da na san shi ne silar ciwon Zainal qila da na kashe shi, sai dai ban kawo wani ko wata a ciwon Zainal ba, na dai xauka ciwo ne daga Allah.

Don haka sai na soma karanto ayoyin shifa’a ina tofawa a ruwa ina wanke mishi idon, inda a duk sadda zan wanke mishi ido da ruwan ayoyin to zai kwana lafiya ba tare da idon ya ishe shi da ciwo ba.

Ganin haka yasa na qara kaimi sosai, ina kuma ji a jikina cewar insha Allahu zan yi nasara ganinshi ya dawo. Haka zai rungume Umar yana shafa kanshi da yi musu wasa ba tare da yana ganinsu ba, haka kuma

komai sai na yi mishi jagora, idan tausayinshi ya kama ni sai in yi ta kuka ba tare da na bari ya san kukan ni ke ba.

Amma abin mamaki sai ya ce “Beeba kuka ki ke yi ko?” In yi maza in ce “A’a.” Ya ce “Ba ki iya qarya ba, faxa min gaskiya.” Sai in ce “Ai na daina.” Haka zai yi ta rarrashina yana shafata ina kallon idonshi da ke farare tas amma wai ba ya gani da su sai in tofa mishi addu’a a idon.

**

Suka qyalqyale da dariya tare da kashewa. “Ka ce yau zai yi kwanan makanta!” In ji Barde. “Ai tunda ya yi alwala da ruwan can to shi da gani sun yi bankwana. Ta haka ne matarshi zata gaji da xawainiya da makaho har ta tsere ta bar shi, kaga kenan sai ka bita ka aure abinka.”

Alhaji Bashir Bangis ya ce, “Gaskiya ban so ka makanta shi ba Barde…mutuwa ma yana iya yinta in dai ya qi rabuwa da matarshi to zai mutu ka aureta. Ai tunda ka faxa min kana sonta to ka aureta har ka gama.”

“A’a Barde, ko za a sako kisa to ba yanzu ba sai naga iya gudun ruwansu, idan naga ba shi da niyar sako min ita to zan barka da shi in yaso in ma kauda shi ne sai ayi, amma ni yadda naso so nayi in haxa su faxa ta yadda kowanensu zai tsani juna har su rabu da kansu, amma yanzu ma wata hanya ce ta samun nasara.”

“Ahab! Ai in dai ina duniya babu kai babu kukan rasa wani abu.” In ji Barde, wanda ya zamo Bafade saboda yanzu biye yake da Bangis sakamakon karayar arziki da ta same shi wanda ya xora zargin wasu ne suka yi mishi.

Shi dama bai yarda da qaddara ba, don haka sai ya zamo xan kore wanda yake wawuce shi a fakaice. Da haka Bangis xin ya lasa mishi wani abu suka yi sallama

.

Abin da ya faru ko shi ne, magani suka zuba a cikin ruwan alwala inda suka yaudaro shi a kan ya zo suyi jam’i. Haka ko aka yi, zuciyarshi xaya ba tare da hasashen komai ba inda ido ya soma raxaxi kafin ganinshi ya xauke xaf!

Duk wannan abin ya faru ne ba tare da na sani ba, sai da dubu ta cika. A kullum da safe zai shigo ya duba Zainal har ma ya aje mana kuxi, bisa tilas na saki komai na yarda Bangis me qaunar Abidin ne, ni kuma duk me qaunarshi abin sona ne.

Muna zaune ina bai wa Zainal kalacinsa a baki, qwai ne da dankali sai ruwan shayi, rashin ido ne kawai matsalar Zainal amma bayan shi ko ciwon kai ba ya yi.

Ya yi qiba, fatarshi ta murje ya daxa kyau. A kullum cikin tsaftarshi zan gyara shi in taje mishi sumar kanshi. Muna gamawa na rungumo shi a qirjina ya yi murmushi.

“My Darling meye?” Ya faxa, na sumbaci goshinsa tare da shafo sumar kanshi. “Da ina so mu je mu gaida Hajiya idan ka yarda.” Ya ce, “Me zai hana

darling

?”

Na miqe ina riqe da hannunshi muka fito in da na saka mishi gilas xin (Dark spees) wanda ya qara fito da haibar shi, na tsaida (Keke Napep) muka shiga.

Hajiya ta ganmu ta taso da murnarta ta tarbe mu, muka gaisa. “Sannu Habiba, haqiqa ke mace ce tagari, dubi yadda ki ke kulawa da Abidin babu abin da zan ce miki sai dai Allah ya jiqan Innarki.” Na amsa da “Amin.”

Zainal ya qara sanar da ita irin yadda ni ke kulawa da shi. Tayi mishi addu’ar Allah ya buxi idonshi lafiya.

“Hajiya ni fa Zainal uba na xauke shi wallahi ko zai shiga halin da yafi haka ina tare da shi, rasa Zainal a gare ni shi ne cikakken maraici fiye da ubana ya mutu

.

Mun daxe a gidan Hajiya sai yamma muka nufo gida. A qofar gida na haxu da Alhaji Bashir Bangis, idonshi a kaina ina riqe da hannun Zainal har muka qaraso qofar gida idonshi dai a kaina.

Muka gaisa inda shima Zainal suka gaisa, na buxe gida muka shiga

.



Bayan

na gama abinci

yara sun yi bacci inda Zainal ma ya yi bacci saboda yau idon ya matsa mishi. Nayi mishi addu’a na wanke mishi idon har ya samu bacci.

Ina zaune ina karanta littafin ‘Gwanin Na Iya’ inda ni ke jin tamkar xanjuma da xan jummai muke da gwani wurin rashin halaccin da aka yi wa iyayenmu na

fara hamma na aje littafin ba don na gaji da karatun ba sai don bacci.

Ina shirin tashi ne ya sanyo kai, na koma na zauna. Murmushin da ke fuskarshi shi ya kada min gaba, muka gaisa inda ya ke tambayar Zainal na faxa mishi yana bacci.

Ya zuba min ido “Wato Beeba magana na zo muyi da ke ta fahimta.” Gabana ya ci gaba da faxuwa na bishi da ido. “Ina tausaya miki

ta yadda za ki qare rayuwarki a wahala da kuma xawainiyar makahon mijinki.”

Raina ya vaci a kan kiran Zainal makaho, sai dai nayi shiru in ji inda zai suaka. Ya ci gaba da magana.

“Maganar gaskiya inda ina da iko a kanki to da raba aurenku zan yi saboda cutuwa. Amma idan aka raba ku sai ki samu wani ki aura shi kuma a samu wata makauniya a aura mishi.

Habiba kina da kyawu, kina da quruciya, bai kamata ki qare a jagora ba. shi fa ba zai tava warkewa ba ya makance kenan.”

Na duqar da kaina ina hawaye, “Me wannan mutumin yake nufi da waxannan maganganun?” Ya katse min zancen zucin da nike. “Bari in fito fili in faxa miki gaskiya

, domin ko an ce ranar wanka ba a voyon cibi.

Tun ranar da na fara ganin ki a ka jarrabe ni da matsananciyar qaunarki, a kullum ba na barci, na

dannewa zuciyata ne saboda sanin kuna son juna ke da mijinki.

Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login