Showing 126001 words to 129000 words out of 175038 words

Chapter 43 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6870

rayuwarki ta gyaru Alhmdllh.

Tafiyar da nayi nace ace muku na rasu nan ma ba iya akan kanki bane akwai wani abu a kasa amma zan fada muku sai lokaci yayi zaku sani insha'allah,Yanzu Aayan ya sanar dani rashin lafiyar babansa akwai wani me maganin gargajiya can kauyenmu Insha'allah wani satin zamuje a kaishi ko za a dace,Allah ya kaimu nace Ammah wai Allah yanzu kece? Na furta ina shafa jikin Ammah,tana dariya tace nice ko kin tuna sanda kike kaini toilet ki dauko ni? Sannu Ammah kinji kinga yanda kika kara kyau da haske Ashe kema fara ce Ammah amma da kinyi duhu, bedroom muka kule da Ammah ta bani labari kaf tun daga yanda Aayan da Yarima sukayi ta dawainiya da ita a turai,Aayan ya kashe mata kudi,yanda ya dauketa kamar Uwarsa yake kula da ita kullum sai sunyi waya ba fashi,gashi komai akan lokaci,abinda Aayan yayiwa Ammah ko uwarsa ce abinda zai mata kenan,Ammah ta fada min irin jin dadin rayuwar da ta shiga a turai,tunda naji haka Aayan ya kara shiga raina,na kara bashi wani matsayi na daban,sonsa da kaunarsa ya kara mamayeni,nan take na fara kukan dadi nace Ammah Allah ya taimakeni ban taba wulakanta mijina ba,shi yasa ake son ko yaushe kayi me kyau,da yanzu kunyarsa zanji,Murmushi Ammah tayi na manya tace abinda naji irin son da kike masa har muna waya ina jiyo muryarki wai wace? Macece?kyakyawa ce? Dariya nayi tare da rufe Idona da tafukan hannuna,Mufeeda an girma,nima na zauna na bata labarin kaf bayan rabuwarmu wanda su Meenat basu bata ba na sanar mata,tace Allah ne yake tsare min Ku Allah yaga halin da muke ciki kuma yaga zuciyar kowa,sai mu kara dagewa da addua,yini mukayi muna ta hira da Ammah ba ji ba gani ina kwance a cinyarta muna labari,tana kara koya min yanda zan kula da mijina da gyaran jiki,Wasu magungunan tsumi data hada min ta bani katuwar leda guda da yanda zanyi amfani dasu,tace ga akwatunan lefanki can ki tambayi Meenat suna dakinsu guda goma sha biyar mijinki yayi miki a wajena ya hadasu can turai ni na hana a baki wancan lokacin sabo da baki hankali ba,yanzu kuma ya hada komai ya barsu wajena,akwati biyu kuma tsarabarki ce ni na siyo miki,Sauran kuma guda hudu nasu Meenat ne nayi musu baya min komai na nuna musu,Ammah to kayanki na gani cikin Sip na sawa ga wasu a akwatuna yaushe kika dinka? Aikin Mijinki ne gaba daya tare da Yarima.
Ammah Yarima fa Ma'eesha yake so,ae na sani ai ya fada min rannan ma babarshi tazo wajena mun dade da ita mutanen kirki ne ai,yanzu Ammah Meenat ce kadai ta rage,dariya tayi tace tun yaushe Mijinki yace min yayi mata miji wai shi ya samo mata ban san dai waye ba,Nace ni gaskiya a'a wlh Ameer zan bawa ita sun dace kuma baki ga taimakon da yake mana ba,to Aayan ya rigaki zabin Aayan zata aura Insha'allah cewar Ammah,kamata yayi ma su dawo gida wajena Mufeeda kinga an takurawa mijinki bazai sake ba,kai Ammah ni ki bar min su dan Allah,Bakya gane me nake nufi Mufeeda sabo dake fa nake komai da bakya min musu duk abinda nace shi kike yi me yasa kike haka yanzu?kiyi hakuri su dawo zaki gane me nake nufi,to shike nan Yaushe kike so? Yanzu suje su kwaso kayansu idan nace gobe kuka zakiyi in zasuyi miki Sallama gwara kina nan gidan,Nan take kuwa suka tafi da Ameer suka kwaso nasu ya nasu tas har akwatunan da Ammah ta ciko musu da kaya,na gani kaya masu kyau da tsada duk gasu nan iri iri,nawa kuma an bar min su a gidana.

Aayan ne ya basu Driver guda da mota dalleliya ta gaske za a dinga kai su Meenat schl da kuma unguwa har Ammah.
Su Meenat ne sukayi Dinner Ameer yace dama shima a barshi a gidan Ammah da yafiye masa,nace ai kuwa baka isa ba sai dai ka dinga zuwa kullum,Bayan munyi sallar Isha Ammah tace bana son shaye shayen maganin matan nan barkatai,wanda na baki sun isa ni na hada da kaina da yayan itatuwa,zan koya miki wasu ki kiyaye kinji,nace to,Dauko ki fara shan wasu yanzu ko period kikeyi cike da kunya nace a'a,ta bani wasu nasha tace nayi matsi da wasu duk nayi ina zaune muka ci abinci da komai,ba na so ma na koma gida nafi so na kwana wurin Ammah muyi ta hira ina jin dadi,nace Ammah Abbanmu fa?, Nan take Ammah ta bata rai karki kara yi min zancensa,gidan nan kuma da kike gani na sa an siyar dashi na kai kudin wajen danginsa dama shike nan abinda ya mallaka tare da yan uwansa mukayi shawara,Ammah idan ya mutu fa ya Zama gado fa? Nan gaba zan muku baya ni karku damu,nace to ba damuwa.

8:30pm sai ga Aayan ya shigo da Sallama idonsa na kaina, yace Ammah Yarima yace bazai samu Damar shigowa ba sai gobe zai zo,ba damuwa ai yana kokari ma kullum sai yazo,Aayan ya kalleni yaga ina jikin Ammah a kwance nayi rashe rashe ina danna waya,tashi mu tafi gida,Baki na turo gaba ina shagwaba nace anan zan kwana ni sai nayi kwana uku zan dawo,Su Ma'eesha duk sakin baki sukayi suna kallon irin yanda nake kashe murya,Ammah tace tashi ke ku tafi bana son shashanci shi yasa nasan da ina kasar nan zaman auren ma gagararki zaiyi gashi daga dawo wata zaki fara,Ameer kuwa shima tuni ya tafi gida yace sai gobe.

Aayan na kalla nace dan Allah fa nace sai gobe to ka dawo mu tafi,Har gida Ammah tazo yanda zaki ganta kika ki yarda sai yanzu zaki ce wani kaza kaza,tashi mu tafi kin ma san bazan iya kyaleki ba,Ammah tace ka daina bata bakinka tasar min a cinya ku tafi, gani Ammah tayi ina bata lokaci tace Meenat kuje Ku kwanta suka tashi suka wuce tare da ce min sis sai da safe zamu zo,Na Galla musu Harara nace dalla...dalla..dalla kuje can ku rufe min baki,ance muku bazan iya zama ni kadai ba ko aikin nawa bazan iya ba na gida,Dariya sukayi suka wuce suna yiwa Aayan sai da safe.
Ammah ma tureni tayi daga jikinta ta shige dakinta sukayi Sallama da Aayan tace ka rufe mana kofar,Daukan kayan da Ammah ta bani yayi tare da mayafina ,jakata da takalmina har dankwalina,cikin mota ya kaisu ya dawo ya daukeni cancak tare da cewa zaki san kin min musu yau Allah ya kaimu gida,ina magana kina min musu ko,nace wayyo na tuba Allah ni na isa,wlh wasa nakeyi na tuba pls My Man bazan kara ba,yace ai kin jawowa kanki yau.
Kin san dai Bana son ina magana ana min musu dan kinga Ammah na wajen ko? Da sauri nace a'a am so sorry bazan kara ba.







AsmaBaffa
[2/5, 4:50 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA







111-112








Official







By
AsmaBaffa




AUNTY SUMEE and NAFI ga page nakune an kara muku.

KASUWANCI NA FANS ina godiya da Jinjina gareku,masu Sharhi kuna birgeni sosai.=?
?=?
?=?
?









Gaban mota Aayan ya bude tare da sani a hankali ya gyara min Zama tare da rufewa,komawa yayi ya shiga shima sannan ya figi mota muka bar gidan,sai da yayi mana take Away na kayan lashe lashe sannan muka nufi gida,Allah sarki Ameer yau ba abokan hirar tasa duk gidan sai yaji ba dadi,sai yanzu ya tuno da yan uwansa Frnds dinsa Su Mujaheed,Ummansa ya tuna tare dasu Abbi amma me zai musu tunda sune suka koreshi da kansu,Muna dawowa ni na kwashi wasu kayan shima ya dauka muka shiga ciki,a Bedroom muka ajiye komai muryarsa naji yace tashi muyi wanka,kunya nakeji amma haka na dan daure muka cire kayan mu tare da daura Towel, Aayan so yake kawai ya fisge towel dina ni kuma naki yarda,sai da ya shammace ni ya fisgo dan towel din Allah yasa na rike kam ina kallonsa ta gefen Ido,Dariya nayi nace woo ai ina kallonka dai, da gudu na matsa ya biyoni dole sai ya cire min Towel dariya mukeyi gaba daya har muka shige Toilet,Wanka mukayi tare kusan ma ni nayi masa komai sannan muka fito,bayan mun shirya tsaf damu Nafeela zamu fara nace tsaya a bawa Ameer takeaway dinsa shima kar yayi bacci,kyaleshi yanzu ma maybe yayi bacci kuma yaci abinci gidan Ammah.

A'a amma ai alhakinsa a kanmu yake tunda kai kake masa komai ko bazai ci ba a bashi shima,kawo na kai masa cewar Aayan,ko da yaje ma Ameer dama yunwa yake ji a gidan Ammah bai tsaya yaci abincin ba,tnx yace Aayan ya dawo mukayi Nafeela raka'a biyu sannan muma muka ci kadan Namu sabo da a koshe muke, nayi mamaki yau da Aayan ya kyaleni naji yace naga kin gaji ne, ganin na gaji Tausa ma ya shiga yi min ina lumshe ido kawai bacci me dadi ya kwashe ni,shima bai San sanda ya fara baccin ba, Da Asuba ni fara farkawa da sauri nayi wanka tare da brush sabo da naji na fara period,sai da na fito bayan na shirya kaina na tashi Aayan yayi shima wanka da komai ya fito yayi Sallah tare da azkhar nima duk da banyi sallar ba nayi azkhar dina,Juyowa yayi yana kallona tare da cewa Period kike kuma? Nace ae da Asuba na fara,na ma yi tunanin kin samu ciki,nace wanne ciki tun yanzu ai yayi sauri,Murmushi yayi tare da cewa ba wani sauri a rana daya ma zaki iya samu,yanzu ya zakiyi dani sai da na kyaleki jiya kika huta na gama tanadin yau da safe sai kuma ki wani fara period naji haushi ya karasa kamar wata mace tana shagwaba,dariya na shiga yi sabo da ya bani dariya maganar tasa,na kalleshi cike da so shima haka nace sai dai kazo muyi Romancing zansa kaji dadi Allah sai ma yafi wanda kake so,bazai fi wanda nake bukata ba ke kin San dadin dayan kuwa,Yana saman Sallaya a zaune na koma tare da sakalo da hannayena ta wuyansa na kwanta a bayansa,Ajiyar zuciya ya saki,fuskata tana a wuyansa ina goga masa,Saman bed ya daurani ya shiga murzani cike da kwarewa nima haka ba abinda Bana yi masa har wanda ma ban taba yi masa ba duk yau na dage nayi masa sai da na zautar dashi,Sucking na masa last a nan kuma yace yama fi komai sweet,sai Santi yakeyi ya rude gaba daya,Sai da nasa ya samu nutsuwa kwarai da gaske yana ta jin dadi yana sa min albarka tare da zafafan kalamai.

Ina kwance a jikinsa muna hutawa na manna masa kiss a wuya nace na gode My Man ban ma san da me zan fara gode maka ba,ka gama min komai,abinda kayiwa Ammah,dangina,yan Uwa da duk Wanda ya shafeni bare kuma ni kaina,ban san me zance ba kafi karfin godiya a wajena, shiiiii naji yace kin wuce haka a wajena kasa ganewa kikayi lokacin ta kasuwancinki kikeyi,Dariya nayi nace Allah ba wani nan,ai kaima ba so na kakeyi ba da,ni ai ba kece bana so ba aure ne Bana so a lokacin kinji nace bana Sonki?sai dai nace bana son aure kece baki gane ba,gashi kin canja min rayuwa da tsari kin kawo min farin ciki wanda na kasa samu,kin yarda kin zauna dani duk da cewa ina bata miki amma kinyi hakuri,d angina duk abinda suke miki kin iya jurewa ai Alhmdllh
Addua kawai zamuyi Allah ya barmu tare Babyna,nace Insha'allah kuwa,dan Allah kayi ta sona kaji ni bana son ka kula kowa,ke zaki dage ai ki hanani kula kowa ta hanyar yin abinda ya dace ace matar aure ta gari tana yiwa mijinta shike nan.
Yau banyi dogon baccin safe ba,da wuri na Mike na shiga kitchen na shirya breakfast sannan na gyara ciki ko ina,naje nayi wanka naci kwalliya cikin material black and red nayi kyau,sai kamshi nakeyi ina kitchen ina kokarin shirya Dining,naji Kamshin Aayan kafin nayi wani motsi naji ya rungumeni ta baya yana shinshina wuyana,abinda ko kitchen baya wani shigowa sai yau Ashe sabo da su Meenat ne baya shigowa sabo da kunyar idonsu ba komai zaiyi a gabansu ba,lallai Ammah ta iya gyara Harka na furta a zuciyata Ashe a fili nayi maganar,Murmushi yayi me Sauti yace kin ganki baki da kunya fa kema,Juyowa na nayi tare da boye fuskata a kirjinsa,nace Saura Ameer ma,Baki ya tabe yace ai Ameer ba ruwansa shi har ya canja part jiya in baki sani ba yana daya part din tare da Daddy wai yace Meenat basa nan me zaiyi,Amma ya bani aiki abincinfa sai na kai har can da yar tafiya fa,ga mata nan a gidan ma'aikata nace ya zabi guda ta dinga masa,Amma yau dashi fa nayi ka kirashi a waya yaci a nan,Aayan yace zancen kike so Ameer wai danki ne ko yaro ne shi da kike damun kanki ai ni kadai zakiyiwa wannan.
Shike nan muje to tare dashi muka shirya komai a Dining, cup din tea dinmu daya,plate na farfesu tare dasu chips duk daya ne tare muka ciyar da juna.a Binda nakeyi wajen kula da Ameer da Daddy ba karamin birge Aayan nakeyi ba,hakan yana sawa ya kara so na Sabo da yanda wasu matan ke wulakanta dangi da iyayen mijinsu,ko kuma miji yana rike wata ko wani a wajensa abinci ma idan bai ce a bashi ba baza a kula shi ba,ko a dinga takura musu ga aike komai na wahala su za a Sa,bare miji yazo dasu nama tare da kayan dadi irin su gashashiyar kaza,yogourt etc wanda ake rikewa a gidan bazai ji ko kamshi ba sai dai idan danginta ne wannan su za a basu,amma sai gashi ni dole duk abinda zamu ci sai na bawa Ameer nasa duk da cewa Saurayin matashi ne,nasan zai iya siya ma yaci a waje tunda da kudinsa,Daddy ma dan kalar abincinsa daban ne,kuma na turawa yake ci,masu dafa masa daban suke.
Aayan ne ya kalleni tare da cewa yau zanje Office Amma bazan dade ba da wuri zan dawo,Shagwaba na fara masa dan Allah ka tafi dani kaji,ki zauna anjima su Meenat zasu zo miki fa,Ameer zai kawo miki su munyi waya da Ammah,baki na turo nace ai ni na tsanesu yanzu,haushinsu nakeji gaba daya.
Dariya yayi yace ke fa kika ce Ammah ta iya gyara Harka yanzu kuma kina jin haushinsu ina son ranar da zanga Mufeeda tayi hankali ta daina kuruciya,wai shekarunki nawa? 18 fa nake yanzu,dole kiyi yan mata,kai fa? Dariya yayi yace kin girmeni ai,nace lallai Ashe saurin girma kayi amma dai nasan ka girmeni dan Allah shekararka nawa? Yace 20, dariya na dinga yi nace Ashe ma kusan sa'a na ne ai da kadan ka girmeni,gaskiya kayi mugun saurin girma na shafa sajensa da gemu nace harda gemu na kyalkyale da dariya,shi kanshi dariya na bashi taya zan kalleshi na yarda 20yrs yake inba kuruciya ba.

Nace to muyi goyo goyo dama ni ina yarinya banyi wasanni ba sabo da neman kudi kullum a business nake kaga yanzu sai nayi kara'i tunda mate ne kusan ni da kai,Wai kasuwancin nan naki me Dame kike siyarwa? Dariya nayi nace komai,nan na fara masa lissafin irin abubuwan da na siyar,da komai da komai har lokacin dana fara ganinsa na dawo daga kasuwa,da irin Algus din danayi ina zubawa kosai garrin kwaki da jar color a ganshi sutu sutu jajir sai ace yasha kayan miya=?
?da wahalar da muka Sha har lokacin da yake yawan ganina gidajen yan siyasa,Sai ga Aayan yana hawaye wai na tausayi,ni kaina dana tuna abin sai danayi kwalla,tun daga farkon rayuwarmu na bashi labarin komai, dariyar karfin Hali nayi nace kalli kana kwalla kamar ba namiji ba,da sauri ya goge tare da cewa tausayi kuka bani,amma gaskiya an raina miki hankali ma da muke cewa kina da son kudi, jikinsa ya jawoni na kwanta yana rada min words masu sanyi da kwantar da hankali yace I love u ,love u more My Man,bana son fita ma ina da meeting ne ba yanda zanyi,nace never mind zan iya zama, yace Ok harda tsokanata wai idan na tafi ki cinye abincin nan du tunda bakya iya cin abincin a gabana,dariya nayi nace ka tuna cin abincina a gidanka farko daka sace ni? Dariya yayi shima yace ai naga yanzu kin daina wai dan Allah a lokacin nan kuma kalau kike?nace ras ma kayan dadi ne da ban saba ci ba kuma dama ni inada ci da yawa,lokacin idan naga kayan dadi ko cikina zai fashe sai na cinye,Dariya mukeyi,amma yanzu kin daina ci da yawa amma dai ba laifi akwai cin nan yana nan, ga iya cin abinci abinci a kitchen,sai azo ayi ta min yanga ashe kin gama koshi a tukunya, dariya na dingayi ina rufe fuska tare da cewa ashe ka sani? Ka kureni lallai kamar Aljani haka kake Allah,amma ai gwara naci na koshi ko? Murmushi yayi tare da tura hannunsa a rigata yana wasa da Boobs dina yace ai nafi so wannan su kara girma kullum su zauna a haka kar su rame, oya muje ki rakani zan wuce,Sai da ya kara brush tare da gyara wankansa sannan na rakashi har mota,nan ma a ciki haka muka dinga kissing din juna kamar baza mu rabu ba da kyar na kyaleshi ya tafi ina daga masa hannu.

Ban dade da dawowa ciki ba na gyara upstair dinmu komai kamshi yake a gidan,sai ga su Meenat tare da Ameer sun shigo suna kwala min kira, fitowa nayi cike da murna nace Ina Ma'eesha kuma? Saloon zata je gobe akwai schl,Ameer ka gujeni yanzu gida daya amma su Meenat sun fini ganinka,Haba Anty ni na isa damuna tayi da waya tayi missing dinki nazo na kawota, mene a flask din nan? Ammah ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login