Showing 18001 words to 21000 words out of 26215 words

Chapter 7 - HADUWAR JINI BOOK 1 WRITING by AYESHA CRYSTAL PEN Maman Uwaisu.doc

29 Sep 2025

774

ji Mamie."

"Sai Mamie ta ci gaba da aikinta, yayin da Sarafina ke taimaka mata da nutsuwa"

"Bayan ta gama taimaka wa Mamie a kicin, Sarafina ta koma Waki, ta zauna kan gado tana daddana waya. Tunaninta bai gushe ba daga maganar da Mamie ta yi mata jiya cewa Kalil zai dawo hannunta, kuma aure za a yi da shi. Wannan magana ita ce ke sa zuciyarta rawa da murna"

Ta lumshe ido tana murmushi.
"Wallahi Kalil ba zai kubuce min ba. Komai sai dai ya ja baya, amma aure sai ya tabbata ta faWa a ranta"

Wayarta ta fara ringing. Halima ce.

"Baby S Kin tashi ne ko kina barci ne da safe haka za ki fita ne yau?"

"A a Halima yau dai gida nake kawai. Mamie ta hanani fita, wai kar a ?ara bata suna"

"Tooo Ke dai ki zauna Kina ganin Kalil zai ma kula ki"

Sarafina ta dan dakata kafin ta amsa:
"Ni dai nasan abinda Mamie ta fada. Kuma ta ce tana da shiri, zan bar komai a hannunta"

"Good da gaske Mamienki ta iya. amma fa karki sake ki kasa shahara, yanzu dole ki cigaba da zuwa party don kin san akwai Usman yana jiranki kuma ki ri?ita social media ki zama Queen"

"Ke dai Halima ki bari kawai za mu yi maganan"

"Bayan sun gama waya, Sarafina ta fara gyara make-up Winta, tana Waukar selfies. Har yanzu tana kallon kanta a madubi da murmushi, kamar wacce ta riga ta lashe gasar zuciyar Kalil
amma a can zuciyarta, akwai Wan Wigon tsoro ko Kalil bai yarda da ita ba Ko har yanzu yana ganin laifin da ta yi"

Sai kawai ta ce da kanta:
"Komai za a daidaita, Kalil ba zai guje ni ba Ni ce dai-dai da shi"

***
______Bangaren Kalil

"Bayan hirar da Kalil yayi da Abbi kan batun aure da ginin gidaje zuciyarsa ta cika da nauyi. Ya koma Wakinsa yana jin duniyar na juya masa. Shi kansa bai san me zai ce ba har yanzu hoton Sarafina da zancen Abbi na masa yawo a kai"

Ya zauna a gaban window yana kallon waje, zuciyarsa cike da tambayoyi.

"Sarafina fa  yar kanin Abbi ce"

"Ya Wauki wayarsa, ya sake kallon hoton Sarafina. Duk da ba su taSa yin magana kai tsaye ba, yana jin wani abu dabam game da ita. Yana jin ta kusa da zuciyarsa  amma yanzu ya gane cewa kusancin na jini ne, ba soyayya ba"
Yana cikin wannan tunani, wayarsa ta fara ringing Jafar ne ke kira"

"Kai Kalil, gobe za mu je walimar da aka shirya a gidansu Fannah zan so mu je tare"

Kalil ya dafe kansa, ya sauke ajiyar zuciya.

"Kai Jafar wai sai munje ne"

"Lallai kuwa hakan ya kamata"

Kalil ya dan yi murmushi kadan. In sha Allah, zan je. Amma akwai wasu abubuwan da nake son warwarewa"

"Na fahimta. Amma ka daure,mu taya shi farin ciki ta hanyar zuwa taron Please"

Bayan kiran ya katse, Kalil ya duba sama, yana fadin:

"Ya Allah, ka kare mu daga zabin da zai jefa mu cikin nadama. Kuma ka ba ni ikon fahimtar me ya fi alheri a rayuwa"

"Kalil ya yanke shawarar zai yi magana da Abbi zai faWa masa gaskiyar alakar jini tsakaninsa da Sarafina. Bai shirya aure da ita ba, kuma ya yanke shawarar komar da hankalisa kan aikin gidaje ne don taimaka wa jama a."

***
_____A Sangaren gida kuwa, Dada na zaune a tsakar gida tana siffanta wake da wa ta ?aramar bokiti a gabanta. Da ta Wago kai, sai ta hango Dije na shigowa da sauri, fuskarta Wauke da gumi da ?yalli na Sacin rai"

"Dije Ina kika zauna haka tunda na aike ki ba ki dawo ba sai yanzu"

Dije ta sauke ledojin hannunta cikin kulawa ta ce

"Dada, na shiga gidan matar Malam Mudi kamar yadda kika ce, sai kuma wata budurwa ta buge ni a hanya Daga magana sai fada, ta mare ni Dada"

Dada ta zaro ido cikin takaici:

"Ta mare ki?

Dije ta ce cikin danne fushi:

"Wallahi Dada sai da na rama. Ban taba son rigima ba amma sai da ta bude min kofa na kwada ma ta duka na pasa ma ta Saki"

"Dada ta girgiza kai, ta ajiye waken da take, ta ce cikin tsantsar kulawa da Wan tsawa"

"To ke Dije me na koya miki ai mace ba ta kai hannu a titi haka. Idan da mutanen kirki sun hango ki, me za su ce ke da kike da tarbiyya"

Dije ta sunkuyar da kai tana cije leSenta.

"Na sani Dada Amma ba zan bar ta ta wula?anta ni ba, kuma har da mari fa. Kin san me take faWi Cewa ni yar kauye ce"

Dada ta tsaya shiru na Wan lokaci kafin tace da laushi:
"Na fahimce ki. Amma ki rike wannan darasin rayuwar kar kiyi fada akan titi Ki nuna bambanci, ko da ana ?o?arin cizonki ta kamo hannunta tana kallonta da tausayawa"

"Ki Wan huta, sannan ki shiga ki shirya kayan miyan. mu gaggauta yin girki kafin Babanki ya dawo daga kasuwa"

Dije ta gyada kai tana jin sau?in zuciyarta. Tana shirin shiga Waki, sai Dada ta kara da cewa:

"Allah ya kiyayye ki ?a t amma na ji dadin kin kare kanki, kar kuma ki maimaita hakan a bainar jama'a"

"Na gode Dada. Zan kula"

Ta shige cikin Waki tana dan murmushi, duk da har yanzu zuciyarta na Wan tsuma.

***
_____Bayan Sarafina ta Wan huta a Waki, ta tashi tana murmushi, zuciyarta cike da farin ciki da kwarin gwiwar cewa komai zai daidaita. Ta nufi closet dinta, ta zaro wani wando fari da top ruwan zinariya mai Wan kaifi a kirji da hannu, wanda ya matse jikinta sosai, ya fito da kowane siffar jikinta. Ta sa hula yana nuna gashin kanta kaWan"

"Ta fesa turaruka masu ?amshi, ta Wauki wayarta da earpiece, tana tafe tana sauraron waka. Sai ta sauko daga Wakin sama ta nufi daining domin ta Wan Wauki snack kafin komawa Wakin"

"Koda ta isa daining, sai gashi Zulai na fitowa daga kicin da tray a hannunta"

Kallon farko da Zulai ta yi mata, sai ta tsaya cak.

"Hajiya karama yanzu haka za ki fito cikin gida Zulai ta ce dan mamaki"

"Sarafina ta Wan sunkuyar da kai, tana kokarin kauce wa kallon Zulai, amma tana murmushi kamar bata damu ba"

"Zulai ai gida ne. Ba fita zanyi ba"

"Gida ne Amma kina sanye da kaya da ba su da kunya. Idan Mamie ta ganki fa"

"Zulai kije kiyi aikin gabanki kawai ba ruwanki a tanan naki aikin yana kicthen"

"Zulai ta sauke tray din da ke hannunta a hankali, tana kallonta da takaici
"Ni dai na gaya miki gaskiya. Allah ya shirye mu gaba Waya"

"Amin,Sarafina ta ce, tana daga cup Win juice, ta sha kaWan, sannan ta zauna a daining table"



To me zai biyo bayan wannan? Sarafina dai tana da burin Mallakar Kalil shi kuma yana neman Dije wacce baima san sunan taba amma shin hanyar da Sarafina take bi don mallakar Kalil tana daidai kuwa"


'?
'?WRITING BY Mrs EXCEL
'?
'?

TAKU HAR KULLUM

*AISHA MOHAMMED*


'?ALKALAMIN

* MAMAN. UWAISU (Jr)*



d'?Allah yabar kauna >?2?

*SAKON GODIYA TA GA YAN KUNGIYAR*

JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION =ت?
'?
( J" W" A" )

MAMAN IHSAN=?i?
PENDING QUEEN=?x?
LELE LADY>؋?

MARYAM ANAS BRANDO >?w?

KHAIRAT

SAKINA ISMA"IL CAMEROON

NUSAIBA MOHAMMED IBRAHIM

PRETTY SK

ALLAH YA
KARA MUKU BASIRA AMEEN >?2?>?2?


>?x?HADUWAR JINI>?x?

BY

AYESHA (CRYSTAL PEN)
'?


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JWHderlOBro5xNW5zGvMFU


=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?


=??? Ina mi?a gaisuwa ta na musamman ga

Tare da


Allah ya bar kauna.

*Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin?ai.*
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Mai komai da komai.
_ Ya Allah ka bani ikon rubuta daidai. Amin. _

1?? 2??

______ Kalil ya tashi daga gaban taga zuciyarsa na cikin rudani ya yi tunanin yadda zai fara magana da Abbi ba tare da bata masa rai ba"

Sannan ya fita zuwa gurin Shan iska na cikin gidan.

"A filin shan iska Abbi na zaune yana shan Rufaida yogurt sai ya daga kai ya ga Kalil ya shigo"

"Na ga ka zo ka se ya me ke damunka Kalil"

Kalil ya zauna, ya yi shiru na Wan lokaci kafin ya fara.

"Abbi, akwai wani abu da nake so na faWa maka. ni da Sarafina& akwai alakar jini tsakanina da ita. kuma ba maganan soyyayya a sakaninmu da ita ka fahimce ni Abbi"

Kalil ya tsaya cak, zuciyarsa ta dinga bugawa da karfi yayin da Abbi ya yi masa magana cikin kwanciyar hankali.

 Kalil, kada ka damu. Zamu aura maka Sarafina, kuma na tabbata za ka ji dadin zama da ita. Wannan zumunci ne na jini, wanda zai kara mana karfi da hadin kai a gida.

Kalil ya yi kokarin cewa wani abu, amma zuciyarsa na cike da rudani.

 Abbi, ni dai ina ganin akwai abubuwan da ya kamata mu tattauna sosai kafin mu shiga wannan al amari.

Abbi ya dage masa da cewa:

 Na san kana da damuwa, amma ina da tabbaci cewa Sarafina mace ce mai kirki, za ku dace. Ka ba kanka dama, ka yi hakuri.

Kalil ya dubi Abbi cikin tunani, yana jin kamar an saka masa nauyi, amma kuma ba zai iya musanta maganar uba ba.


Abbi ya ?ara da cewa, "Kalil, aure da ginin wannan gidajen ba su rabuwa ba. Ina so ka fahimci cewa aure wani Sangare ne na rayuwa da zai ba ka ?arfi da kwarin gwiwa wajen kammala wannan babban aikin."


"Kalil ya nutse cikin tunani, yana jin cewa akwai abubuwa da ya kamata ya sani kafin ya Wauki wani mataki"


 To, zan yi tunani, Abbi.

Abbi ya lumshe ido da murmushi.

"Allah ya maka albarka tashi ka je"
Ya tashi ya wuce Wakinsa


***

"Sarafina ta kalli gefenta, ta ga Mamie na shigowa cikin parlour tana Wauke da wani littafi a hannunta"

"Ki kwantar da hankalinki, Sarafina" Mamie ta ce cikin murya mai laushi

"Wannan gida ne, kuma ke ce ke da ikon zabar yadda za ki zauna a cikinsa"

Sarafina ta yi murmushi ta Waga kai "Nagode, Mamie"
Daga nan suka ci gaba da cin breakfast cikin kwanciyar hankali,


"Bayan Sarafina ta gama breakfast tare da Mamie, ta Wan Waga plate Winta, amma kafin ta mi?e gaba Waya, sai Zulai ta shigo da tray a hannunta"

Zulai ta kalli su Mamie tana faWin
"Zan kwashe su Hajiya in kun gama"

Mamie ta Waga kai.
 Toh Zulai, ki kwashe. Sarafina ta gama ma ko?"

Sarafina ta kalli Mamie tana murmushi kadan.
 Na gama Mamie"

Zulai ta amsa da Wan murmushi wanda ba a gane ko na gaskiya bane. Ta fara tattara kayan a hankali.

Mamie ta dubi Sarafina
"Zan je Waki na Wan kwanta. Kar ki fita ko ina har sai na fito kin ji"

Sarafina ta girgiza kai da ladabi.  Toh Mamie, ki huta lafiya.

"Bayan Mamie ta tafi, Sarafina ta zauna shiru, tana kallon yadda Zulai ke tattara kayan cikin natsuwa. daga bisani ta mi?e ta nufi Wakinta a hankali, zuciyarta na harhadawa da sabbin mafarkai, da sabuwar rayuwa wadda take fatan yi"

***
______Bayan fitowarta daga Waki, Dije ta isa kicin tana duban inda za ta fara. An riga an daura tuwo kayan miya ke gabanta, sai ta daura hijabi ta zubo ruwan dumi cikin kwano"

"Ta zauna a taburma kusa da ?ofar kicin, ta fara bare albasa da tattasai. Gidan yana cikin natsuwa, sai sautin kaWa da ke fitowa daga gidan makoci yana biyo iska"

A zuciyarta kuwa, tunani bai daina dawowa ba.

Lawandi shi fa har yanzu banga shi ba. Kuma na tabbata ya manta dani. Amma me yasa zuciyata ke dukan in tuna shi"

Ta sauke ajiyar zuciya, tana Wora kayan miya a tukunya. Sai Nafisa ta le?o daga wajen kofa"

"Ke Dije, bayan kin gama girkin nan zamu wuce gidansu Mubaraka fa yau dai kauyawa day dinta"

Dije ta Wan harareta, "Ni dai sai na gama wannan aikin gaba Waya. Kuma ai ba komai za a yi ba."

Nafisa ta ce,
"Ke dai ko yaushe sai naki tsayuwar natsuwa. Haka kawai mu je mu huta mu ganema idonmu."

Dije ta yi murmushi kaWan
"Bari dai na gama tukunna"

***

____Bayan kusan wata daya yau aka fara shagalin bikin Fahat da Fannah"

"Yau ce ranar da za,ayi mother's day ana Shirin zuwa Fahat da danginsa za su je gidansu Fannah. Gida ya Wauki hayaniya cikin natsuwa, iyayen Fahat suna ta gyara kayan al'ada turaren wuta na tashi, an fesa tulsi da humra, ana zuba kayan zaki da lemo a jakunkuna masu kyau"

"Kalil ya shirya cikin rigar shadda ruwan zinariya da hula mai Winkin zamani. Duk da cewa zuciyarsa har yanzu cike take da tunani, ya daure ya fito da fara'a domin taya abokinsa farin ciki"

Fahat ya shigo Wakin da Kalil yake yana dariya.
"Kai dai yau dole ne ka raka ni. Ba ni da yarda da kowa sai kai. Kar ka bari na shiga gidan nan ina rawar kai babu Kai a gefe na don nasan su Jafar duk siya zasu min nasani"

Kalil ya Wan murmuce.
"Ina tare da kai. Allah ya sa a dace"

Sun fita tare da sauran dangin Fahat suka nufi gidan Fannah da yamma. A gidan Fannah kuwa, an sha ado, an shimfiWa tabarma, an fesa turare, Fannah ta zauna cikin ladabi tana saurarar umarni daga Mamanta"

*Bangaren Fannah:*

"Fannah ta saka atamfa mai launin shudi da ruwan gwal, gyalen ta kwance kadan ya sauka kan kafadarta. Dukkan shigarta cike take da kunya da nutsuwa. Kawayenta na gefe suna ma ta dariya, amma ita kanta ta kasa cewa uffan"

"Wai shi Fahat Win yana nan ta tambayi wa ta kawarta a hankali"

Kawarta ta le?a window tana murmushi,
"Eh, sun iso yanzu, hatta Kalil ma yana tare da su. Ga motoci nan har an fara saukowa!"

Fannah ta lumshe ido zuciyarta na bugawa da sauri.
"Ya Allah ka sa komai ya tafi lafiya ta fada a ranta"

A nan cikin Waki Mamarta ta shigo da fara a.
"Fannah, ki nutsu ki zama tamkar mace kamila. Wannan rana ce mai muhimmanci. Dole ne ki nuna tarbiyyar da muka koya miki tun kina ?arama."

"Na ji Mama," Fannah ta amsa a hankali.

A waje kuwa, an karSi bak'in da hannu bibbiyu. Kalil yana gefe yana kallon yadda Fahat ke murmushi da natsuwa, yana gaida iyayen Fannah. Iyayenta na cike da farin ciki da girmamawa.

"An shige da bak in ciki falon gaisuwa. Fannah ta shigo da sallama cikin tawali u, ta dur?usa ta gaishe su. Kallo Waya Kalil ya yi mata, zuciyarsa ta dan buga  shigarta, natsuwarta, da yadda ta ke kallon ?asa tamkar mace ta gari"

"Tabbas Fahat ya dace," Kalil ya ce a ransa.

"Fahat kuwa ya kasa Soye farin ciki, yana kallon Fannah kamar wanda aka haWa da mafarkinsa. An Wan yi hira, aka ci za ki, aka sha lemo. Muryar dariya ta cika gidan cikin kunya da nishadi"

***

____Dije na kokarin jujjuya miya, tana kallon yadda mai ya fara harbawa da ?amshi.
"Yau sai dai su ce abinci ya yi dadi ta faWa a ranta cikin kwanciyar hankali"

Bayan ?an mintuna, Dada ta fito daga Waki tana gyara mayafinta.
"Dije, kin gama dafawa ne?"

"Eh Dada, gashi nan yana dahuwa. Zan gama nan ba da jimawa ba."

Dada ta kalli kayan miyan, ta gyara murya.
"Ai da gaske na ce, ke yanzu duk girkin gida kin iya. Allah ya miki albarka."

"Dije ta murmusa, zuciyarta ta Wan saki. Duk da nauyin da ke zuciyarta na Lawandi, jin irin wannan yabo daga Dada na sa ta jin kwarin gwiwa"

Cikin haka Nafisa ta sake le?owa:
"Ke Dije! Kin fi awa guda kina dafa miya me kika sa haka? Ko auren girki za ki yi?"

Dije ta dariya ta ce:
"Ai mai girki ke sa a auri mace."

Suka dara gaba Waya.

Dada ta kalli Nafisa da murmushi,
"Ku bar Dije ku tafi idan kun shirya"

"Ai bazan je ni kaWai ba Dada, sai ta gama sai mu wuce tare," Nafisa ta ce.


Bayan an gama aikin gida Dada tace
"Dije kije kishirya ki tafi Amma ki kula da kanki Kar kiyi dare"

Dije ta ji daWin jin haka
" Toh Dada"




'?
'?WRITING BY Mrs EXCEL
'?
'?

TAKU HAR KULLUM

*AISHA MOHAMMED*


'?ALKALAMIN

* MAMAN. UWAISU (Jr)*



d'?Allah yabar kauna >?2?

*SAKON GODIYA TA GA YAN KUNGIYAR*

JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION =ت?
'?
( J" W" A" )

MAMAN IHSAN=?i?
PENDING QUEEN=?x?
LELE LADY>؋?

MARYAM ANAS BRANDO >?w?

KHAIRAT

SAKINA ISMA"IL CAMEROON

NUSAIBA MOHAMMED IBRAHIM

PRETTY SK

ALLAH YA
KARA MUKU BASIRA AMEEN >?2?>?2?



>?x?HADUWAR JINI>?x?

BY

AYESHA (CRYSTAL PEN)
'?


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JWHderlOBro5xNW5zGvMFU


=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?


=??? Ina mi?a gaisuwa ta na musamman ga

Tare da


Allah ya bar kauna.

*Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin?ai.*
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Mai komai da komai.
_ Ya Allah ka bani ikon rubuta daidai. Amin

1?? 3??



AUREN FAHAT & FANNAH

*Wurin Daurin Aure*
"An shirya shi a wata katafaren Event Centre da ke cikin unguwar masu kudi.
akwai kwalliya ta zamani, farin labule da lu ulu u masu kyalli kujeru an rufe su da fararen mayafi masu launin zinariya.Fresh flowers a jere da cinyoyi masu ?anshi a kowanne table"

"Auren Fahat da Fannah ya kasance abin koyi cikin birnin. Komai ya cika da salon zamani da al adun gargajiya. An Waura auren ne da safe a babban masallaci, sannan da yamma aka tafi Dinar wanda aka shirya a babban Event Hall dake GRA, Abuja"

"Gidan ya sha ado da zinariya da royal blue launukan da Fannah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login