Showing 3001 words to 6000 words out of 22164 words

Chapter 2 - SAKE Book 1 Hausa Novels By Maryam K. Mashi.doc

naga yana aiki , ko karatu hk zansa ya siyo kujeru muna fitowa Shan iska



Ai ban karasa tunaniba nasaki kayan da ke hannuna ji kake kwaratsatsatsa, yanda saukar kwalabar nan ta kasance , hk tabana ya fisu faduwa, Hamsa ta juyo tana galla mani zagi Wai na fasa mata kaya, ni kuwa ja baya nike kmr wacce damusa ta tsira a dokar jeji, ballema da naga mutumin da matar sun mike tsaye hankalinsu ya dawo kanmu.






Ido cikin ido muke kallan juna ni da mutumin a lkcn da ya nufo in da nike cikin sauri, sai da naga ya kusa kawowa sannan na samu da kyar nace
" Hamsa , na kirata ita da take tsugunne wajan kayan Dana fasa tana ta zabga masifa da zagina.




Kara cewa Hamsa nayi da karfina Ina nuna mata mutumin nan yana tahowa , waje na,
*Hamsa likita ne , doctor Deen ne da matarshi, ashe yana da mata ban sani ba, Hamsa doctor ne da ma...ma....ma..."

Ban karasa ba na juya na ruga a guje , sbd ganin shi ya zo kusa dani yana Shirin kamani, zuciyata ce ta karya take yi ko kuwa kaxafi ne?



*Alhamdulillahi*

*Mu hadu a littafi na biyu*




Loading.......
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

Writing by *Mama Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1
Typing...... 7?
Sannan yace a shiga dani, mutum biyu muka samu a ciki, sannan sai lebirori biyu dasu ke tura kujerar danake a zaune ina fitar da hawaye, aka shiga dani dakin karamar tiyata (minor thetre) ni kaina nasan bazan iya taka kafataba, balle har in iya kwantar da kaina a gadan da ke gabana, lebirorin nan har sun yunkura zasu daukeni sai naji yayi mgn,
"Ku tsaya"
Kawai naji yace, shi yazo da kanshi ya daukeni ya dorani bisa gadon ya kwantar dani, sannan ya dauko blue zani ya rufa mani a jikina.

Yana fara kwance daurin daya yiman naji wani masifaffen zafi ya ziyarci kwakwalwata
"Zafi, zafi, ciwo, kafata, wayyo, "
Su na jero a lkc daya, banji yanda yace ba, hannu yasa yana shafa gashin kaina kmr ana lallashin karamar yarinya, sai naji yana cewa,
"Sorry my lovely sister, I am feeling the pain in my heart too" idan ba a dinke ba yanzu, zata iya zame maki babban ciwo, dama ya yanka ki sosai, dan dai bakya gani ne
"Doctor ayi mata ( Anasthia) ne"?

"Dole dama, tayi wajan awa uku fa da jinshi, kun san kuwa yayi tsami yanzu"
Ina kallo aka dauko wasu allurai guda biyu, daya naji an cakaman ita a tafin kafata, dayar km aka zagayo akuguna, anan ne naji yace abashi, ina jinshi ya tsira mani ita a kuguna, sai na matsi jikina alamar zafi.

"Kiyi hkr, saki jikinki kada tayi maki ciwo ", ya fada, nayi yanda ya umarta, sannan naga ya dago kai ya kalleni ta cikin gilashin dake a idanshi, wanda ya kayata mashi da fuskarshi sosai
"Da ciwo"?
Ya fada yana yiman murmushi tare da wani guntun hankicif ya goge mani hawayen fuskata, ga ciwo ga kunya, sai kawai na kawar da kaina gefe,

Inaji ana tattaba man kafata amma ba zafi ko kadan, wanda kadan kadan mun hada ido da Docter Nura, sbd yanzu zuciyata ta aminta da Alh. Nura likitane, saidai har yanzu in son ganin Doctor Deen din da ake ta fada a asibitin nan.

Da kan shi ya daukeni ya dora a kujera, yana a gefena, har dakinmu, sannan ya shiga shima yasamu mutanen dake ciki wanda daga kannan mahaifina sai yayyansa, sai kannan mamata da abokan arziki, sai Babanmu dake zaune a kujera sabanin wasu da suke a kan tabarma.

Inaji suna gaisawa da doctor, sannan yacema Babanmu zai bani daki a kusa damu, amna(for emergency) ba kudi za'a biyaba, sbd kwai in samu in fara taka kafar da aka nan-nade mani ita da bandeji da wata uwar audiga a ciki, kai kace karayar tsakiyar tafin kafa nayi.

Nan take Babanmu ya amince, sannan ya gaya masu kwalbace na taka ta shige man cikin tsoka sosai, yankan km da girma sosai, ni kuwa daga in kalli wancan sai in kalli wannan, anan take aka hadani da kannan mamata biyu akace su zauna dani, banda kusan gabadaya dakin da suka biyo mu don suga dakin da aka kwantar dani.

d'kuyi hkr wannan baida yawa wlh yau bansamu time ba sai yanzu d'

Loading.......
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book1

Typing.......... 3?
Lpy qalau mamace ta aike ni, ina kwana, lpy lou yaja motarshi yayi gaba, Nikuwa nabishi da kallo a inda na hango shima kallo na yake ta mirron tsakiyar motarshi wanda ni kallon mamaki nake masa yadda yaja mota bai kara cewa kalaba


Mama karima da kannanta da abokin Babanmu, sai makociyar mu Hajiya(Magajiya) da mijinta wanda shine yakawo mu asibitin, mazan na tsaye matan ne ke zaune bisa wani bencin dake kallon dakin tiyata, duk sunyi tagumi.


Ni kuwa Ina tsugunne gefen wata kujera sai sharbar kuka Ina kwananku nake naji an fada cikin wata murya da nasan nasanta sbd dadinta na dago Inga kowaye sai naga Alh. Nura tsaye yana gaishesu.


Sannan ya waigo gareni
"waye bashi da lpy? " cikin kulawa nace mamarmu ce
"tun yaushe rashin lpyr yakamata"?
Jiya da dare
"Ina kikaje dazu dana ganki"?
Dama dama
"dama me"?
Kenan zuwa kika gaya masu bata da lpy, amma ni na tmbyeki kika ki fada mani"?
'a'a
"a'a dame"?
Nifa bana son karya, tana daya daga cikin abinda yake hadani da mutane.

Yayi shiru alamar tunani, tana Ina maman?
"Tana cikin tiyata "
"Subahanallahi, ba komi inazuwa,
Yajuya ga iyayenmu maza
"Alh.inazuwa, ku jirani"
Sai kawai naga ya danna kai cikin dakin tiyarta. A take zuciyata take tmby ta ko lebira ne? Ko km likita? Amma sai na tabe baki nace oho.


Ansamu sama da awa daya, sannan mukaga an turo mama a gadan da ake tura marasa lpy, muka mike da sauri, wanda kmr ance in juya sai naga Alh. Nura cikin rukunnain wasu likitocin sun biyo bayan mu suna maganganu da suke fada

Sai de me? Yanayin kayan jikinshi sun sha bamban dana sauran likiticin, Tunda su Riga da wando ne na kot( suit) sannan suka dora farar lab coat. Dukkansu kallo daya zakayi masu kagane likitocine da yanda suke taku cikin natsuwa


Shikuwa wando da Rigane na tazarcen shadda a jikinsa, wadda zaka iya kiran shaddar da galila sbd yarda take daukar ido,

Lebirori kuwa suna tare da uniform bulu ( blue) Riga da wando suna tura mama, to shi awa yake?
Na tmbyi kaina, can dai naji hayaniya sai nada na daga kaina sannan naga ashe ankawo dakin da za'a kwantar da mama

Dakin mutum daya ne sbd da gado daya Nagani a dakin, muna tsaye suka shigo likitocin amma sai naga Nura ya tsaya daga waje yana mgn da wani likita, bayan duk lebirorin sun gama gyara ma mama kwanciya sannan daya daga cikin likitocin yadaurama mama Karin ruwa tare dayin allurai a cikin Ruwan

Ya waigo ya Kali yayan Babanmu yace masa "Doctor Deen ne zai cigaba da kula da ita, sbd shine babba likita a bangaren ciwonta, kada kusamu damuwa, tunda har Doctor Deen da bakinsa yace zai cigaba da kula da ita


Ya waigo ya kalli gaiyar matanan da muke tare dasu, amma Alhaji dan Allah munson mutane su rage sosai sbd ba'a son hayaniya tayiwa mara lpy yawa, km kunsan ka'idojin asibitin nan, shine
mutum daya ake bukata ya tsaya wajen mara lpy,
Har dare ma mutum daya ke kwana
Ziyara kuwa daga Karfe hudu na yamma zuwa shidda na yamma. Ina fatan kun gane


"In sha Allahu za'a kiyaye Doctor " inji abokin Babanmu, ana hk naga Alh. Nura ya shigo,
Gani bayi likitocin sun ja baya, ga wasu na biye dashi, shiyasa na yiwa kaina tmby a take, ko dai kudi gareshi ne shiyasa suke girmamashi hk? Ban tsaya neman amsar tmbyta ba ballantana in samu mai bani ita to balle ni kukama nake, tsurku ne ma kesani yan kalle kalle,

Sun dan jima kan mama sannan naga ya juyo
"Alhaji kada kusamu damuwa insha Allahu an samu nasara, amma tana bukatar kayayyakin amfani"
Eh ai yanzu Rumana zataje ta taho da su, bamusan abin zaikai da kwanciya ba ai shiyasa Alhaji
Yajuyo gareni tare da sa hannu Aljihu ya mikoman naira dari biyu"maza Kije ki hau babur kije ki hado mata kayanta, kinji"
Nace to cikin kuka
"Kidena kuka hk nan mana"
Inji Alh. Nura


Ai hk take ita komai sai kuka, gatanan sam ba dai tayi maka mgn ba akan Abu, saide tayi kuka" mama karima ce tayi mgn Alh. Ya'u ya mayarmata da amsa "ai Rumana akwai hakuri irin na uwarta har tausaya mata nake yi Wlh, shi yasa nacewa Alhaji ya barta ta dan huta agida kada ayi mata aure yanzu badan komiba sbd mu samu mai hkr muma, mai hankalu"

Kunya duk ta kamani sbd dakin a cike yake ga likitocin nan sun kai su takwas banda Alh. Nura da lebirorinsu, kaina a sunkuye na rusuna na amsa kudin, ban tsaya komai ba nayi waje cikin natsuwa.

Tafiya nake ina hardewa sbd yarda siket dina ya kamani ban an karaba naji karar hon a bayana ban waigaba na matsa gefe don in bada hanya, naji ance ke shigo in rage maki hanya tunda sauri ake.

Loading............

Takuce
*Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1

d'ina nika sakon gaisuwana ga yan marcy Novels km ina godiya da irin kaunar da kuke nuna ma littafin na badan kuba da tuni na daina typing sbd wahala amma don in faranta muku nake daurewa inayi d'

Typing.....,... 6?
"Alh. Nura", yadago ya kalleni, idanuwansa naga sunyi ja, nima da hauka sai nakama hawaye, ya zaro ido "Rumana, kina tausaya mani ne? _kinsan rayuwata ne? Ko kinji ana lbr a gari?

Ban bashi amsaba, sai dai na kwantar da kaina gefen kujera na rasa me zance, mikewa tsaye yayi, ya zagayo ta bayana yadafe kujerata da hannuwansa duka biyun
"Ni yanzu nazama malami akan harkar rayuwar duniya, sbd tuni na yaye kaina daga cikin dalibai, Umma, ina son in sanar da ke wata mgn, itace kiyi...,....... "

"Doctor Deen! Doctor Deen!! "Mukaji ana kira da karfi a bayanmu, nayi saurin waigawa domin kawai in ga waye wannan doctor Deen din dayaki zuwa duba mamata, abin mmki banga kowaba, sai mai kwala kiran doctor Deen din, amma ina kallo ya karaso da gudu wajen mu yana isowa naga ya rusuna, irin alamar girmamawa.

"Doctor matar nan dake a ( Room 3) daki na uku, gatacan a kwance ta fadi wajen zuwa ban daki, yan hanjinta gabadaya a zube a kasa, "
"Wai wacce ciki? Ta wanne daki?
Ta (Amenity room 3), ta dakin sarakai daki na uku, wacce aka yima aikin tiyata yan hanji
"Mamata,? Na fada da karfi, ya waigo ya kalleni, "Eh doctor mamanta"

Ban kara tsayawa sauraren komiba na ruga aguje, inajin Alh. Nura na kwala man kira, amma ban ko waigoba, wani abu naji yashige man kafa cikin sakan da bai wuce dayaba.

Da sauri suka iso in da nike, wanda ban iya shaida komi ya shige man a tafin kafa ba, sbd jini ya riga ya gama bata mani kafa gaba daya, cikin hanzari ya km kafata yasa hannunshi a jinin, sai naji yana cewa, Subahanallahi, kwabace"

Daga hk sai ji nai ya fizgota da karfi, wani irin ihu nasaka tare da wawuyar cakuma na rikeshi gam, wani farin hankicif mai km da tawul shinaga ya zaro daga aljihunsa ya ninka yadaure mani kafa dashi amma jinin saida ya batashi, cikin rawar jiki ya zaro dan kwalina dake kaina ya kara daure mani kafata da shi.

Ni kaina na manta rike nake a jikinshi, sai da naji ya dagoni yana sannu, na kalleshi gumi duk ya bata mashi fuskarshi "kai samo mani kujera ka dauketa ka kaimin ita bakin dakin tiyata idan naga ma mamanta sai ashiga da ita tunda kafar tayi rami sosai.

Jin an ambaci mamata yasa na mike da saurina, sbd sai naji ciwon da nakeji ma ya gushe kwata, -kwata ina ji yana kirana, amma har nayi hanyar dakinmu, sai dai kafin in karisa naji kafata ta rike naka dagata,.

Kuka na dinga yi ina kiran mamata, jin hk yasa mutane suka fito da sauri har yan dakinmu, nan nasamu masu rikeni, wanda tuni Alh. Nura yashi ga dakin wajen mamata da aka hana kowa shiga

Bazan iya auna mintunan da aka daukaba, sai naga ma'aikatan asibitin sun cika kofar dakin namu da gadan tura marasa lpy


Da gudu aka fito da ita kwance ba alamar rai ansa zanin asibitin blue an rufeta dashi, suma likitocin suna biye dasu da saurinsu, amma sai naji Alh. Nura ya cewa
"Ina Rumana "
Ban amsa mashiba amma wa inda ke rike dani sun amsa mashi da gata nan bai kara mgn ba, sai dai kujera na gani a gabana ya bada umarni a dorani samanta akaini bakin kofar tiyata kmr yanda ya bayar a baya.

Wai ban tashi jin wani mugun ciwo ba sai da na dauki kusan mintuna ashirin zaune a kofar dakin tiyata amma ni cikin kuka nike, sai kuwa ya zama biyu, gana mama gana ciwon da yake neman rikita mani kwakwalwata

A rakaice koda ban duba agogoba Nasan munfi karfin awa biyu zaune bakin tiyata sannan mukaji alamar turo gado da ya karyar mana da zuciya, wanda nasama suna mankarar asibiti.

Layi guda likitocin nan suka fito amma banga Alh. Nura ba, duk dashi bazan kirashi da likita ba, tunda banga alama ba, mmki da al'ajabi suka saukar mani a lkcn daga Alh. Nura yafito daga baya da kayan aikin likita a jikinshi wasu Green yana bayar da umarni ga likitocin dake gabanshi, na su kula da mamata sosai kafin ya fito.

Loading.........
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*


Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to marcy Novels

d'inamai matukar nuna farin cikina da godiyata ga Allah (S W A) da yasaukeni lpy yakuma azirtani da Samun Umar farouk Allah yaraya mani su ya shirya yasa suna cikin masu yima addini hidima yasa subiyo masu sunayen d'
=??Bazan taba mantawa daku masoyan wannan littafin ako ina kuke naga sakonku ta privet chat nagode Allah yasaka da alkhairi km naji dadin addu'ar ku Allah yabar zumunci >?2?=?O?=?O?=??d'd'd'

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1

Typing....... 1? 3?
Ya waigo,
"Rumana taso mana "
Sannan na mike na bishi, kafin muyi tafiya mai nisa tuni ruwa ya balle mai yawan gaske, cikin sauri naga yaruko hannuna ya kama yana sauri muka isa wata katuwar bishiyar cediya wacce ta bayar da rufaffiyar inuwa.


Ina kallonshi yana karkade jikinsa, nikuwa ina makure a jikin bishiyar, yazo ya zauna jikin sauya daya, nima ganin haka yasa na zauna, cikin ruwan wani iska bakikkirin yataso tare da tsawa mai tsanani guda uku ajere, tabbas bansan lkcn dana ruga aguje ba, Ina kiran (Inna Lillahi wa inna ilaihir raji'un) wanda karshe na dinga kiran
Babana! Babana!! Babana!!!


Dakyar doctor yakamoni, cewa yake
"Ke Rumana! Ke Rumana!! Ke Rumana!!! "
amma ban saurareshiba sbd na rude, Sam bansan abida ke faruwa ba ,
Sai can zuwa wani lkc da bazan iya fadarshiba, sai naji na dawo dai- dai, inda na juya na jini matse gam, na daga kaina, sai na ganni kwance a kirjin likita ya matseni gam, wanda zan iya cewa zaune yake kasa ya jingina da jikin bishiyar, koma ince ya kwanta jikin bishiyar, sannan ya kwantar dani a jikinsa.
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wani dadi ya kamani na mayar da kaina na kwantar harda lumshe idanuwana wanda nan take na tuni da littafin turancin dana karanta(love scene) na kuwa dade ina tunanin wa zan samu wanda ya iya soyayya irin ta namijin littafin da ya nunawa yarinyar ciki kauna, da kulawa wannan dalilin ne ma yasa bana kula samari sbd duk wanda ya zo wajena ko ba hadu dashi a hanya da yayi magana uku zan gane (he does not know love) to balle yasan darajar shi.


Ganin farko da nayi ma likita, sai naga kawai za iya yin duk abubuwan da na akaranta a littafin Novel, wannan yasa ya dinga birgeni, yau ga mafarkina ya tabbata, nayi murmushi nakara gyara kwanciya ta, kmr km antasheni daga barci, sai naji na firgita na mike, a inda zuciyata a dayan ban garen ta karato man cewa likita ba sona yake ba, irin kulawace ta likitoci yake nuna mani, da sona yake da tun a asibiti ya furtamani, ko ya nuna wata alama ta yana son aurena.


Zuciyata takara karanta mani cewa yawancin likitoci fa yan yaudarane, kada inje ya yaudareni ballema da kaganshi Kaga mai wayon tsiya, shin me yahanashi zama da matanshi,ko dai suna da labarin yana yaudaran matan asibiti ne?


Wannan nazari da karatun ta natsu da zuciyata ta karanto mani yasa na mike da sauri batare da nace mashi komai ba, nasaka takalmana nayi gaba, ina ji yana ta kwalamani kira ban tsaya ba, wannan yasa naji ya biyoni da sauri yatari gabana, na goce na sake hanya, yayi sauri fizgoni a jikinshi ya matse,
"Ki tsaya yayi sauki"
"Ka sakeni na gaya maka, dama abinda yasa kabiyoni kauyenmu kenan sbd kazo ka yaudareni, ashe kai dan iskane ina ganin ka da mutunci, ina girmama ka"



Na fizge, nayi gaba, ya biyoni da sauri,
" Umma me ya kawo wannan mgnr kuma naga... "
Nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login