Showing 6001 words to 9000 words out of 22164 words

Chapter 3 - SAKE Book 1 Hausa Novels By Maryam K. Mashi.doc

saurin katseshi,
"Daga me zakace mani kuma kamaka (red hand)


hannu da hannu, meye dalilin ka na hadani da jikinka? Matarka ce ni, ko kuwa akan wane dalili ko ina kagani a rubuce, in a littafin karatunku na likita ka gani? To mu a littafin Allah (SWT) babu hk bai kuma halatta haka ba., sannan a littafin al-ada ma banga hakaba. "

Na cigaba da tafiya da sauri da sauri, can sai naji ana kwalla mani kira Rumana! Rumana!! Rumana!!! Dijama, ce ke nemanki,
"Nayi sauri na amsa, sai gata aguje, "ta kamani, "ke gida duk hankalinsu ya tashi anyi zatan kun bata hanya, KO bako ya sace ki", sai naga tayi saurin sa tafikan hannayanta duk biyun ta rufe bakinta, ta tsurawa bayana idanuwa, wannan yasa na waiga naga likita a tsaye yana kallanta.


Ko ban tambayeta ba nasan ganin shine yasata rufe bakinta, nayi gaba kawai na kyaleta a tsaye, ina ji tana gaishe shi, da kyar ya amsa mata, ya biyoni da sauri
"Rumana ki tsaya in yi miki bayani mana, ina da wasu dalilaina nayi maki haka, wlh ba wai..... "
Na juyo na kalleshi, kamar zanyi mgn, amma ganin yayi shiru da maganarshi yasa na juya nima.


Daga lkcn har muka iso gida bai kara cewa komai ba, asalima jerawa su kayi da Dijama suna ta hirarsu, muka isa gida aka dan jajanta, sannan akace mashi ga daki ko zai canja kaya, ina daga kuryar dakin Adda ina cire kaya, shi kuwa daga farkon kofa.


Ba wai ciki da falo bane ba dakin, a'a zagayayyene dai kmr rumbu, to daga tsakiya aka ja katanga, wadda ta raba dakin biyu, ina ji ya basu amsar shi yanzu zai koma nan fa Baffa Surbajo kakanmu kenan, yace yayi hakuri sai gobe, ba abinda zai taba mashi mota, amma yanzu korama ta kawo ba wajan wucewa.


A dole aka shawo kansa yace ya hakura, wanda hakan yasa Baffa Surbajo ya kifa runfarsa akai maganin jikar ruwa, wanda su sun dauketa tamkar lema kenan ya umarci doctor da yazo ya kaishi masaukinsa.


Loading.........
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*
.


Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to marcy Novels

*Ina me neman uzuri na rashin samuna kullum kmr yadda nayi muku Alkawari, wlh munsamu matsalal wuta ne yau kusa sati daya bamu da wuta sai dai mukai charge, amma da izin Allah inde an gyara zaku jini a koda yaushe >?p?*



Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1
Typing,...... 1? 4?
Sanin kowa ne idan sallah takawo kai ruwan sama yakan tsagaita wanda ta sanadinar hkn nasamu nafita domin shanya jikakkun kayana wadanda sukasha wankin ruwan sama, ina cikin shanya naji gyaran murya a bayana, na waiga a hankali likita ne tsaye da jikakkun kayansa ahannu da alama shima yazo shanyane,


Banyi mgn ba sai dai nayi sauri shanya kayana nayi gaba, hakan yayi dai dai da maganar likita
" (one day you understand what I mean),"



A irin aladal garin jandikko idan magariba takawo ankasa katanon kaskon kasa (kwatanniya) azuba bushshen kashin shano ahada mashi wuta, ma'ana shine madadin fittalarsu,
Mata da yara zasu zagayeshi daga nesa adinga hira, a zauna abisa katunan itacen giginya da aka daddatsa aka gewaye gurin dashi, wanda koda yaushe suna gurin ba'a chanza masu guri rani da damuna.



Abu daya ake daukewa katon kaskon kasa shima gudun kada ruwa ya jikashi,
Mazan gidan da sauran mazajen gari wa inda suke zuwa hira suma sukansa nasu akofar gida wanda zakaga rukunin jama'a, tsofaffi daban, matasa daban, yara daban, sunata hirarsu gwanin ban sha'awa,
Anan kowa zai abincinsa ya koshi gaban kaskon wutar nan yauma hk ta kasance,
Shikuwa likita memakon yafita sai ya zauna cikin mata ana fira dashi, sai kayi zaton shine dan masu gidan baniba,
Nikuwa ina gefe daya ina kallon ikon Allah idan anyi abin dariya inyi in abin tausayine inyi nima inyi juyayi,

Saidai kadan kadan ya kalleni wani lkcn ma mu hada ido, inyi saurin dauke kaina, wani lkcn ma inshareshi kmr bana ganisa, hira tai dadi can naji ya cewa
"Adda zandawo garinnan kubani mata in aura
Ta bashi amsar cewa,
"kai alhaji ka rufa mana asiri, kada ka hada rigima agarinnan, yan kauyannan basa bada auran 'ya'yasu a fita dasu wajen gari"
" Haba Adda ai wannan ba matsala bane, inde har zaki nuna mani iyayen yarinya km kun amince "
Yadago muka hada ido
"Nihar naga wacce nikeso dazu a hanyar mu tazuwa gona, kai Adda tana kyau, gashi na ganta ba dankwali akanta, km ba kitso, ta saki gashin nan ya kwanta baya isa nata wasan kura da shi.



Na dago na dan sakar masa harara ya kawar da idansa ya cigaba
"Adda kiga baka ce, mai kyan jiki, Karamin jiki gareta, ko kuwa kananan shekaru gareta? , ga idanuwa, kai Adda ai ni nayi mata kawai,
"Karufa mani asiri yar gidan waye kagani? "
"Tambayi Dambo shiya gaya Mani ko wacece da sunanta da gidansu, da har nace ya rakani gidansu, sai yace a bari a sanar da Baffansa".



Ta juya ga Dambo
"Yar gidan waye? "
Yayi saurin cewa
"Wai Adda yar gidan malan"
"kai, gidan yan masifa",
Gabana ne naji ya fadi, atake nayiwa kaina tmby, kenan likita da gaske yake yi,
"Kai karufa mana asiri, in dai kana son yar garin nan to ka jira a nema maka kafin kadawo, "
"To shikenan na hkra Adda, amma a nemo mani mai kyan hali yar gidan mutunci, mai kyau da kunya kmr dai irin halin Rumana".



Gaba daya wajan suka kalloni, sai Adda ta dauke hankalinsu da magana, ni kuwa dama tuni na rikice dan kunya,
"Kai je ka can, mu Munyiwa jikanyarmu miji tun da dadewa..... "
"Ai dama Adda bance itaba, cewa nayi mai yanayinta, ai ko kun bani Rumana bazan karba ba, sbd ita matsayin kanwata na dauketa, ko yar kanwata ".
Ya zura hannu ya dan dunguro keyata.


"Dama wazai auri wanda baida asali"
Nan naga ya dago kai cikin tashin hankali, kafin kace mai idansa har yayi jajir.
"An taba mutumin da bashi da asali, Rumana ke dai kice malam ya kasashi, ni kuwa kinganni nakasa na tsare ba mai shiga dakinnan sai ni kadai, ko Alhaji? "
Da kyar yace
"Eh"
Can naji anata hayaniyar hira shi kuwa yayi shiru kallanshi da zanyi sai naga yasa hankicif yana share hawaye sai kawai naga ya mike tsaye.




"Adda bari in fita kofar gida km in taya su Baffa hira suma, tunda nayi maku taku "
Atake naji jijiyoyin jikina sunyi sanyi , sbd ganin yanda yatashi a sanyaye, hk akaci gabada hira wanda ni ina can ina kama tashoshin kala-kala na game da likita.


Wata Al'ada ta kauyen jandikko itama, in an gama hira kowa zai nufi dakin barcisa, akan fito da kwaryar madara sabuwar tatsa, guda biyu,daya akai kofar gida tare da yar kananan korai guda biyu, daya ta yan cikin gida ce, a takaice kowa sai yasha wannan madara zai kwanta idanma kuna cikin hira da Kaga an fito da ita to kowa lkcn barcinsa yayi.


To yau ma hk, kowa yasha, sannan naji duk anyi sallama an tashi, na waje duk sun shigo cikin gida, amma wani ikon Allah banda likita , ba damar inyi tmby, hk km ba damar in fita nemanshi.
Nashiga dakin Adda ina shirin kwanciya, sai naji Baffa Surbajo yashigo yana tmbyr Adda,
"Adda me ku ka yi wa bakon naku me? Gashi can kofar gida yaki shigowa, an bashi nono yaki sha? "
"Walla Kaga yarinyar nan ita ta gaya mashi mgn, tun lkcn ya canja mana fiska muma, "
"Me tace masa? "
"Ce masa tayi mara asali, "
"Subahanallahi, sha-sha-sha kenan, waye bashi da asali Umma, zancen wofi, mutumi ya biyo ki dan yaga lafiyarki amma ki dinga yi masa shirme a gaban fiskoki, bai dace ba, yanzu tashi ki kai mashi madarar kinga sai ya dauka wasa kike".



"Haba Baffa...... "
"Tashi nace yarinyar wofi ",
Na mike na yafa mayafina a kaina na tafi rike da kwaryar madarar a hannuna su Adda kuwa har da sa karamin faifai da rufewa.



Tsit garin, sai dai kukan kwari da kwado na irin na yanayin damuna, farin wata kuwa yayi fes, hakan yasa garin yayi kyau,. Har na isa gabanshi bai kalloni ba, hasalima kanshi a sama yake, na daga kaina sama nima, sai naga taurari sunyi shar abin sha'awa, na dawo da kaina na kalleshi,
"Sannu da dare doctor '
Yadawo da kanshi ya kalleni batare da ya amsa ba.



"Bakaji magana ta ba ne"?
"Naji, ina shirin amsawa kika kara wata"
"Baffa ne yace in kawo maka madararka kasha, km yace idan antashi daga hira ba mai kara zama a kofar gida, sbd akwai namin daji, "
"Kina gudun su cinye ni "?
"Kwarai kuwa, ai ba zan so ace kazo garin iyayena wani abu ya sameka ba",
"Naji, amma..... "
"Kayi hakuri kuskure ne na gane ban kyauta ba amma abinda ya faru bayan nan bana farko ba, "
"Umma Rumana Almustapha katsina magana bata wuce ba, amma yanzu a waje na ta wuce, mu isa ciki ki kaimani daki.



Loading......
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1
d'wannan page din na sadaukar dashi ga yan Marcy Novels nagode da addu'ar ku ina alfahari daku=??>?p?d'd'd'

Typing........ 9?
Kunya ce ta kamani, atake nakama yan kame kame, sai da yamatso daf dani sannan naji yayi mgn,
"Kada kiji komi babu abunda zaifaru in natafi, kiyi tunani Allah ne ke tsare da ku, ni ban isa in kula da kuba, yanda Allah zai kula da ku sosai ni iyakata in dan taimaka maku a dan iya sanin da Allah ya bani? "
Yayi shiru tare da danja da baya.

Tsugunawa kawai naga yayi ya dago tafin kafata mai ciwon,
"Ta kusa warkewa Saura kadan "
Kara sunkuyar da kanshi yayi ya sumbaci tafi kafata, duk da nasan doctor yakan yi ma marasa lpyarshi haka balle yara kanana, konima da ina kwance asibiti kullum in yazo sai ya sumbaci hannuna ko goshina.


Sbd hk ban dauka doctor sbd so yake yiman hkba, sai kawai don kulawa da nuna in kwantar da hnkalina, ina jinshi ya mayar da kafar ya ajiyeta, sannan yamike tsaye
"Kin manta ana jiranki a ciki, in kinshiga ki dauko man wayata da hankicif dina dana mantasu a ciki, ki miko man ta tagar falo, sbd kafarki ko".

Bance komiba na raba ta gefanshi zan wuce yayi saurin yi baya yabani hanya, ina isa kofar falon na tsaya na goge fuskata sosai don kar salim yayi zargin wani abu a zuciyarshi
"A salim sannu da jira, muna dakin mama likita nakara dubata da yan dokoki dayasa mata, "
"Badai har yatafi ba? "
"Gashi nan ta taga zan mika mashi wayarshi da hankicif disa da ya mantasu "
"Nima dama ita zan tuna maki, shigowarki na ganta"
Nayi murmushi na dauki wayar da hankicif din waje daya.


Ina daga labulen taga, Doctor Nura na tsaye, hannunsa daya a aljihunsa na wando dayan ya dan dafa kanshi tamkar yana tunanin ya manta wani abunshi mai mahammanci, ko kuwa hangen wani me tahowaWajanshi,
"Gashi likita ".
Nafada ina mai dauke da dariyar murmushi, wacce ni kaina nasan ta takaicice, mai tattare da bakin ciki.

Batare da yace komiba, yamiko hannu ya amsa kayanshi, ya juya,
"Sai nadawo ko? "
Yafada dai dai lkcn dayi taku biyu zuwa uku, ban bashi amsaba nima nasaki labulan hannuna, kokari kam ni kaina nasan nayi, na danne abunda ke cikin zuciyata da fuskata gudun kada salim ya gane wani abu a tsakanina da likita, har nasamu yatafi.


Ni kaina nagaji da kwanciyar, km na gaji da tunani da sake saken ya zanyi da doctor ya gane ina sonshi har ya aureni, ni dai nasan bazan tava zuwa in fada masa wannan mgnr ba har abada, hawaye da suka cika mani fuskata kuwa sunki kafewa suma, wannan dalilin yasa natashi nayi alwalla inyi nafila in roki Allah ya yaye mani wannan masifar dana shiga ta son wanda baisan inayiba.

Nayi nafila ta wadda ta daukeni tsawon lkc ban sallameba sai wajan Karfe uku na dare, hk kuwa yayi dai dai da gyangyadin da nike tun kamin in tashi daga kan abi sallah, wannan yasa ina sallamewa sai gado.

=?O?kuyi hkr ba yawa wlh banji dadi sosai ne =?O?


Loading..........
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1

Typing........ 4?
Ke shigo in kaiki tunda sauri akeyi. Naji anfada cikin wata sansanyar murya da inka jita a take zata sa zuciyarka natsuwa, ko a wane irin kunci kake, atake naso intuno mai muryar tun kamin in juya, amma nakasa, sai bayan idona ya waiga naga ashe Alh. Nura ne,

Tabbas gabana yafadi, amma yanayin da nake ciki na tashin hankalin ciwon mamata ya hana inji komi a jikina, balle har ya gane yanayin dana shiga,

Banyi wata gardamaba na zagaya na bude baya nashiga, yatayar da motar sannan na gaisheshi, duk da gaisuwar mai kuka ba dadi garetaba, tunda murya ta a shake take dama gani mai karamar murya,

Ciki-ciki ya amsa mani, ni dama ban tsaya jiran amsarshiba na cigabada kukana, kamar ance daga idonki, sai na hango shi ta madubi yana kallona, kunyace ta kamani, balle damuka hada ido dashi, atake na mayar da kaina na kife a cinyata na ci gaba da kukana,

Tunda muka fara tafiya babu wanda yakara cewa kala, balle ni ba gwanar surutu bace, karar da naji yasa na dago kaina da sauri, gani nai ya kanga talho din hansa a kune (hand set) shiyasa na mayar da kaina kasa,

E, nike mgn, okay ganinan juyowa, bani mintuna talatin (30 minute) okay no problem, yes, yes, yes, I will call you later, mgnr danaji yanayi kenan cikin natsuwa, azuciyata nace ni kayi sauri ka kaini ka tsaya wata waya can

"Ki sauri da Allah, ana jirana nima", naji yafada a lkcn danaji motar ta tsaya, ni kuwa kai na akan cinyata nayi tunanin kowani round akazo, shiya ban dagoba kaina ba, ciki hanzari na bude kofa zanfita " ke" yafada "ki goge hawayen fuskarki, in zaki shiga sbd hk zaki tayar da hklin yan gidan kina ji", na daga kaina, sannan nasa mayafina Ina gogewa,

Cikin mintuna goma zuwa bakwai nafito ko motsi baiyiba har nagama sa akaya a but din motar na zagaya na bude baya nashiga, munkai mintuna goma amma ko motsi baiyiba, har bakaiga yin mgn "nagama ",
"Ina sane jira nake direban naki yazo ya kaiki"
Gabana ya fadi, me nayi mashi ? na tambayi kaina,.

"Dana shiga gida banga direba ba, amma bari in kara dubawa in gani" nafada a rude na fita, har sai da nafara tafiya sannan na ji yace
"Ke, zagayo nan" na zagaya ta dayan hannunshi daya nuna mani "gani" "shigo ki zauna " nashiga na zauna "rufe kofar" na rufe, sai kawai naji yatashi motar, zuciyata cike take da mmki, sbd ban fahimci bagar mgn ya gaya mani ba, sai yanzu, ashe manufarshi na mayar dashi direba.

Ai kwai Sai naji na tsaya da hawayen danake na buge da tunani shin birge no yayi KO mmki yabani? bansan lkcn dana saki baki ina kallonshi, bai waigoba ya kalleniba, amma sai naji yace "juyar da fuskarki ", nayi saurin juyawa na kalli tafa ban Kara waigowaba saida mukazo kofar kwaya, sannan naji yakara mgn

"Ina direbanku ne? "
"Baizoba"
"Ina babanku? "
"Baya nan, yayi tafiya",
"Wane gari yaje? "
Nayi shiru sbd bana fadar inda Babana ya je in yayi tafiya,
"Yasan mamarku bata da lpy? "
"Alh. Ya'u ya fada mashi"
"Waye shi? "
"Abokin Babanmu ne shi"
Bai kara mgn har muka isa asibitin, nafita sannan na duko nace ngd, har najuya yace
"Ke zonan"
"Sunana Rumana"
"Oh! Sorry, kidinga sa babban mayafi da zai dinga rufe maki kafafunki koda cibiyane kinji"

Kunya ta kamani, amma sai dai nace na gode, har na kwashe kayana yana cikin mota zaune bai ko motsa ba, na dauki wadanda zan iya dauka, nabar ragowar anan manufata sai na kai nadawo nakashe sauran

Ina tafiya da kaya a hannuna amma ina tunanin Alh. Nura Wanda mmk abubawa biyar da yayiman a mintunan da basuwuce talatinba, in ma sunkai, nafarko an isa amma bazai ceman ankawo ba, na biyu wai jiran direba yakeyi, mai makon yace man indawo gaba kawai,

Na uku ya tmbye ni ban bashi amsa ba amma yaci gaba da mgnrshiba, na hudu yace daina kallona kawai saide kawar da fuskarki, na biyar indiga sa babban mayafi, meye dalilinshi nacewa hk"Baya ganina yarinyace ni.

Natsaya nakalli jikina daga sama har kasa, sai lokacin naga ashe gyallen ummi ne, iya kacinsa kuma wuyana, na dubi dinkin rigar jikina, sai a lokacin naga wuyanta a bude yake, sai na sunkuya in aje kayan wai ni dubara, in gani kodai mamana ya gani dana sunkuya yi mashi godiya, subhanalillahi, nace da sauri danaga mamana ya hade waje daya kenan ya hadu da dan uwansa badu bayar da tsakiyaba, dama gashi duk da karamin jikina ina da nonuwa, Wanda yaso ya rinjayeni.

A take kawai sai naji hawaye, nace nashiga uku, abinda yagani kenan, ya cuceni, KO ince nacuci kaina, nayi sauri na dago, nakara kallon jikina sosai, sai naga kugun nan nawa yafito shima sosai a cikin siket dina ga Riga ya iyakarta kuguna dama km tubarkalla ina da dan kugu, kai ko babu tunda siket ya matseni ai dole ya fito.

Loading...........

Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to
Marcy Novels

Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1
d'wannan page din nakune Masoyana nakusa dana nesa nagode da addu'a kud'd'd'd'

Typing.......

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login