Showing 15001 words to 18000 words out of 22164 words

Chapter 6 - SAKE Book 1 Hausa Novels By Maryam K. Mashi.doc

nan kuwa ?"
"Kwarai yana nan , sati uku ma da suka wuce iyayenshi sun zo neman aurena ,amma Baba yace abari ya dawo daga tafiya zaiyi masu mgna ,ban sani ba yanzu ko sun dawo , na dai ji Baba na cewa wata biyu kawai za'a sa biki....."



"Dakata ya isa hakanan "
Ya koma ya zauna sosai
"Ruman in na tmbyki zaki fada mani gaskiya?"
*Me zai hana "
"Kina son Salim har cikin zuciyarki?"



Loading...,....
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*




writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to marcy novels


Bismillahi Rahamanurrahim

Book 1
Typing........ 1? 5?
Ina isa na ajiyemasa na juyo nace mashi sai da safe, ya amsa da Allah ya nuna mana, har nakai kofa naji yakira sunana nayi saurin juyawa sbd nima zuciyata cike take da kaunarshi dan dai nasan ba sona yakeba shiyasa nima nake jan jikina daga gareshi.



"Dama cewa zanyi ki araman zaninki In rufa sbd sanyi"
Najuya na fita, dalilin da yasa ban amsa mashiba sbd duk kayana babu zani saina les shima na wannan sallar ne dakyar na amince akayi mani zani.



Adda nasama a daki nasanar da ita yana son zanin rufa,tayi shiru sannan tace
"Tofa baki da Zane ke? Koda yake naga kayanki duk buje ne"
Ban bata amsaba na wuce na zaro zanin les dina, sannan nace mata
" sai wannan ban KO tsayaba nayi gaba, yana zaune saman katifar nayi sallama na isa ga katifar na ajiye masa"
Nagode kawai yace nikuma na juya nafita abina.



Yanda rana tabullo daga gabas shi ya nuna mani bakwai saura na safe, wanda mutanan mu sukace hantsi yayi su kuwa matan gidan gaba daya suna gona tunda duhun asubahi sai dai ni da Dijima akabari sbd bakona likita, Wanda dama sbd dashi akace mu zauna har yatashi ya karya kumallo, su kuwa dama a gona suke karya kumallo



Bayan na shiga mun gaisa dashi, sai naga Dijama ta shigo anan ne take ce mashi ga ruwan wanka can ta Kai mashi, ya juyo ya kalleni tare da yar guntuwar hirar shi, sannan sai naji yace
" manzo (SAW) , said we should respect our guest,"
Da harshen turanci, na mayar masa da cewa
"Bakone ya bayar da haushi "
Ya mike yana murmushi yayi gaba,.


Akan hanyarmu ta zuwa gona nasha dariya, sbd shi da Dijama sai suka zame mani ina kallan wasan turanci nan na ban dariya (Mr Brown) sbd irin tmbyoyin da likita kewa Dijama sannan duk bishiyar da ya gani sai ya tmbyi sunanta da km maganin ciwon da take , daga hk har muka isa bishiyar farar kaya inda take ce masa maganin mayu ce, aiko nan da nan naga likita yasaketa harda gudu kadan wai tsoranta yake ji.



Kai ni Rumana narasa mema zankira kaina, me km zan kira likita Nura? Sbd ni nakasa nuna ma likita ina sonshi afili shi km nakasa gane shima sona yake ko kuwa mutunci muke dashi, kmr yasan mgnr da nakeyi yayi saurin watso man ganyen wata bishiyar da ke hannunsa, yace
"Sister yaushe aka yanke mani intafi? Gobe ko yau? Domin inason dawowa nan da wani satin sbd zan duba kafar kawu Jalo"



"Kai kafar kawu Jalo tayi shekara biyar fa ahaka"
"Murja hu nefa a kafar "Dijama ce tayi caraf ta bashi amsa,
"Duk da hk zanyi kokari in gani ko zansamu nasara ko sister ",
Na daga mashi kai,
"Ke wlh ban yardaba, ko hk za ayi zumuncin ba kyayin mgna tunda kikaga na saki jiki a garinku nima dole ki karbi bakuntar zumuncina",
"Kanka kawai ake ji"
Nafada ina tafiyata, yace
"To yanxu kuwa za a ji naki"
Yabiyoni naga da gaske yake sai na ruga, ina kiran Adda.



Dijama kuwa ta biyomu itama aguje cewa take
"Kamata Alhaji, kamata sai tayi magana, hk take yi mana a gida"
Gudu nake har na gaji na tsugunna ina dago masa hannu, shima yana zuwa ta tsugunna a gabana, muka cigaba da mayar da numfashi, wlh ban san lkcn da na kurawa likita idol ba, sbd son shi da naji ya karu a zuciyata.



Hannuwana duka biyun naji ya kama ya sunkuyo da gaba daya fuskarshi, ban tashi jin komai ba sai ji nayi ya sumbaci (kiss) yatsun hannayena nayi saurin na fizgesu
"Likita....... "
"Kin manta abinda kika bani na karanta a asibiti"?
Nayi saurin mikewa tsaye ya kamo hannuna daya shima ya mike.


Yarage sautin muryarshi ta zamo mai sanyi gaske
"Baki bani amsaba"
Nakara matsawa sbd matse manj yatsu da yayi
"Kuma me? "
Yafada a dai dai lkcn da yamatso da jikinshi kusa danj
"Kuma su basu da addini "
"Amma ni ma ke na zaba a matsayin kanwata wadda nake so da kauna, nike so mu hada zumunci mai karfi a tsakaninmu (My heart has chosen you to be my fiancee). "



Nayi saurin ja da baya, likita mu tafi, mutafi gona, ya matso
"Zan tafi gona Amma sai kin amince zaki zabe ni a matsayin yayanki, wanda kike so da kauna na zumunci mai karfi sannan kin tsayar dani in zama (fiance) dinki"
Nazame hannuna da rawar jiki tare da kyarmar murya nace
"Dijama! Dijama "
Yayi saurin sa hannunsa a labbana,
"Ko ta zo ba zan tafi ba sai kin ce kin amince da maganata. "


Ni bansan ma'anar kalmar (fiance) da hausaba to balle in ce na amince ni km bazan iya tmbyar shiba sbd kunya, na zame sannan nace
" zumunci dama ai yariga ya kullu tun a asibiti, sai dai kaine baka so yayi karfi ba, tunda har muka gama zamanmu a asibiti baka kawo mana matarka da 'ya'yanka sun gaida mama ba, ko wani naka, amma har doctor Deen ya turo abokansa mun gasa".




Loading........
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*


Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to *~Alkawari hausa novels~*


Bismillahi Rahamanurrahim

Book1


Typing.....2? 0?
Ina fitowa kofar gida na ganshi zaune ya jinjina da bishiyar durumin kofar gida, gabana ya dinga faduwa gudun kada ya yi mani magana , ya dago Kai ya kalleni ya mayar ya sunkuyar , ni kuwa Ina isa ga motarshi na zare zoben hannuna na dora mashi samanta na wuce abina.



Ba abinda zan iya yi in bayan kuka , gindin bishiyar danyar gonar su Adda na zauna na ci kukana koshi , sannan na gangara korama in da ake kwalfar ruwa na tsuguna nayi Alwallata , dankwalina na shimfida nayi sallah ta , sannan na cire hijabin da dankwalina gaba dayansu na ajiyesu a inuwar , sannan na tafi inda nike zama.




Kasa zama nayi ,kawai sai zuciyata ta raya mani in shiga cikin koramar ma in dinga dan zagayawa , wata kila na danji sanyi a zuciyata, hk kuwa nayi na cire takalmana na dira cikin koramar, inda ruwa mai kyau kata gudu na dage siket dina na dinga tafiya a hankali ina kallan yanda kafafuna kr nutsuwa cikin rairayi




Kamar wata wacce ke safa da marwa , sbd sai nayi nisa , sai km in juyo in dawo inda nike sannan in koma ga rana a take bata wani karya ba amma ko kadan bana jinta.




Limshewar rana ita tanuna mani la'asar ta wuce, hkne yasa nayi Alwallata na koma ga bishiyar dazu nayi sallah ta, ban tsaya addu'ar komai ba nadawo nakara dirawa cikin koramar, sai dai ruwan yanzu yasha babban da na dazu , sbd ruwan yanzu akwai sanyi , sabadi na dazu dake da zafi, amma ba mai kona kafa ba .




Isaka mai sanyi tabuso , hk nane yasa natuna ranar da ruwa ya taremu nida likita a cikin gona, nadaga kaina sama, amma ba gizagizai ko daya , sai dai saman tayi fari tas abin sha'awa, hawaye na shatata, nadaga hannuna sama, nace Allah nagode maka dana rokeka ka km amsa mani cikin gaggawa ka km tabbatar mani da likita na sona amma km iyayena sabani abinda mukeso, Ya Allah nakara rokanka kacire son doctor Nura daga zuciyata in jar ba alheri a ciki, kasa mani wanda iyayena keso koshi waye.




Na shafa addu'a ta na juya naci gaba da tafiyata, amma km wani abu hawayen fuskata sunki daina zuba,
Nayi nisa sosai sannan na juyo, juyowar da zanyi sai na hango likita cikin koramar nan, kafar wando a tattare duk da dama (T-SHIRT) ce da wando a jikinshi.




Dabara ta kwance mani a nan take, shin me zanyi? In juya in gudu ko kuwa in haura in gudu gida, Wanda dole da wajajanshi zanbi in tafi, amma sai nakasa yin kodaya daga ciki.
Ina nan a tsaye har ya iso kusa dani nayi dabara nayi duk yanda zanyi hawaye sudena fita daga inaduwana, kamin ya iso amma hk ya gagara.





Dan nesa Dani ya tsaya kansa a sunkuye, hakan da yayi kuwa ya dauki mintina kmr biyu , sannan ya dago kanshi ya kalle ni , nai saurin sunkuyar da kaina, sbd kunyar shi da ta kamani ,
A gaban iyayena nace ban sonshi,
"Ina son magana da ke don Allah, amma ba a cikin nan ba, amma sai in ba takura"
"Ba wata takura"
Na fada Ina rawar murya.




Bamu tsaya gindin bishiyar danyar nan ba, sai dai ya umarta da mutafi bishiyar nan damuka fake ranar da ruwa tsaremu ,sbd can yafi waje zama a cewar sa,



Cikin sanyin murya yafara magana,
"Ni nasan duk ni najanyo har hk tafaru, amma atunanina kin gane duk wani abu da nake nufi ,dama shiyasa tun farko na fara da nuna maki ina sonki ta cikin hikima, yayi shiru, kiyi hakuri don Allah nayi maki kuskure , ni agani na kamar kina sona, ke duk nama rasa me zance maki , sbd da ban taba tsintar kaina a halin dake ciki yanzu ba , nagode da saurarata dakikayi, na km San ke yariyace me mutunci, yadan dakata tare da saukar da numfashi yamike tsaye, duk na rude zan koma gida sai kin dawo katsina km in muna da rabon haduwa, Ina maki fatan alkhairi ga duk Wanda zaki aura"





"Au na manta, ya fada , ya matso kusa dani ya tsuguna, Nai rashin hankali babba a baya , daban sanar da ke koni waye ba , ki tuna yan kwanakin baya da kika kirani da mara asali"
Nadago Kai na kalle shi, yayi murmushi





"Nasan ke kin manta, ni kuwa ban mantaba, bazan kuma taba mantawa ba, ballema yanzu dana san na rasaki"
"Kayi hakuri"
Nasamu na fada cikin murya kuka
"Ba komai , Umma , amma yau zan dan gutsura maki asalina"




Ni mutumin Azare ne awata unguwa da ake Kira kofar gabas iyayena yan asalin garin ne , yanzu haka km suna da rai, mahaifina yana da yar guntuwar sarauta ta dagacin wani kauyen Azaren , Ina da kanne wajan ashirin, tunda babban gidane gidanmu , ko da kina son cikakken tarihin gidanmu kina iya zuwa Azare ki bincika ainihin tarihina, ragowar kuwa sirri nane.




Amma ni ne doctor Deen din da kike son gani na asibiti, na kalleshi sosai , yayi murmushi ya matso sosai, ya jawo hannuwana,
"Na gode da baki boye mani sirrin zuciyarki ba na bakya sona "
Zuciyata ta daku da karfin gaske , hawayen fuskata suka kara saurin gangarowa ,yasa hannu ya goge mani hawayena
"Bana son in ga kina kuka , haba My little sister, yayi murmushi da ya baiyanar da sirrin bakin cikin zuciyarshi , ya lakaci hancina da dan yatsansa
"Zan koma , amma inkin dawo katsina ta yiwu in zo miyi bankwana a matsayin big brother dinki , in kinji shiru kuwa ta yiwu na canza shawara ne"
Yasa hannusa a aljihunsa sai ga zoben nan ya fito dashi
"Nayi maki kyauta kin dawo mani da ita , ni kuwa wacce kyauta za kiyi mani yanzu wacce zan dinga tunawa da My little sister, kin San in kinyi aure zumunci dole ya yanke a tsakaninmu"
Nayi shiru na rasa me zan bashi , a iya duk tunanin da nayi , tunanina na karshe shi ya bani da in bashi tsakuyoyi kawai, na sunkuyar da kaina na tsinci tsakuyoyi masu kyan gaske kwaya uku na mika mashi , da dunkulan rairai, bai raina ba yasa hannu ya karba , ya zaro hankicif daga Aljihunsa ya zuba su, ya kudundune ya mayar a aljihunsa.





"Na gode"
Ita kwai yace ya mike ,
"Na tafi "
Ina kallon shi har na daina ganin kafafuwanshi , sbd ganyayen bishiyar sun kare mani na Mike da sauri na fito sai na hangoshi yana tafiya a hankali , murna, haushi, bakin ciki , dadi, godiya ga Allah, shi naji sun taru gaba daya a zuciyata, na farko dole inyi murna da Allah ya amshi addu'a ta ya sako sona a zuciyar doctor Deen , Wannan kuma dole inyi godiya ga Allah madaukakin sarki da baisa na makance a sonshi ba har ya kaini ga sabama iyayena ba





Haushina daya kuwa shine nayi ma kaina sakiyar da ba ruwa , bakin ciki na kuwa ga samu ga rashi nayi a lokaci daya , anan inda nike tsaye na zauna ba zan iya auna me na zauna yi ba ko km matakin mai zan dauka a kan Wannan matsala ba.




Ban iya tashi daga nan ba har sai da naga duhun magariba ya karyowa dajin sannan na Mike na nufo cikin gari . Mamaki da al"ajabi suka saukar mani a lokacin da na hango motar likita a kafar gidan su Adda, nayi kokarin in tmbyi kaina dalilin yin hkn amma tmbyr ta kasa samun shiga balle har in samu in tunano amsarta.




Ina kaiwa kofar gida na ganshi zaune a mulmulan iccan giginya ya baje hankicif nan a gaba da rairayin a ciki da tsakuyoyin nan uku yana ta zane zane aciki Ina kallanshi ta wutsiyar ido ya dago ya kalleni ya mayar da kanshi ya sunkuyar.




Mai kunne na yaji Ina shiga gida, Wai Baffa sirbajo ne yake cewa shi yana son in auri likita Wai baidace a doramashi zargin da ba'a tabbatar ba, sai naji yana gayawa Babanmu duk irin taimakon da yayi madu, da irin tsarabar da ya kawo masu, da irin yadda ya mayar da gidanshi a matsayin gidan iyayen shi da yanda ya taimakawa kafar kawu Jalo gata nan yanzu yana taka ta sosai.





Ina shiga dakin Adda sai naga duk matan gidan zaune da alama suna sauraren abinda su Baffa suke fada sukeyi ,sallama daga kadai nayi nashiga kuryar dakin domin dauko hajibita sai naji Adda na cewa gaskiya ai Wannan yaron shine sirikin kirki tun kafin ya aureta ma fa kenan ji yadda baya kyamar abincinmu ga hidima.





Inna Jumma tace
"Gaskiya Adda walla muna so nai mudai"
Ina fitowa neman buta in zuba ruwan alwala sai naji Baffa yace
"In dai Ina da iko da Kai to ka aurawa yarinyar nan likita, inkuwa ban isa ba to ka dauki diyarka yanzu ku barmin gidana ni kuwa gobe bada nisa ba, zan aura mashi Dija inyatifi da ita ya kasheta tunda ita Ina da iko da ubanta.....




*Kubiyo n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i donjin yanda zata kaya baba zai amince ko bazai aminceba km likita me yatsaya yi bai tafiba*


In naga comments anji in kara maku wani in babu sai batan kwana biyu=?
?




Loading........
Takuce *Maman Sadiq*
[2/15, 5:11 PM] Maman Sadiq=?K? *SAKE*
=???=???=???=???=???=???=???=???
*LITTAFIN MARYAM K MASHI*

Writing by *Maman Sadiq*
Dedicated to ~*Alkawarin hausa novels*~


Bismillahi Rahamanurrahim

Book1

Typing......1? 9?
Karfe goma sha daya na safiyar juma'a su Babana suka iso, shi da mamanmu , aka yi murna zuwan su kmr yarda aka saba yan hidimomi na sannu da zuwan baki duk aka gama masu , bayan nan kuwa basu zame ko inaba sai dakin Baffa, inda Baffan da kanshi yayi masu izinin shiga.




Awa daya zuwa biyu da shigarsu aka ce inzo ana Kira na , Ina shiga dakin naga fuskar Babanmu ba wani annuri , gaskiya ko ban San abinda ke faruwa ba, amma gabana yayi mummunan faduwa, sannan zuciyata ta raya mani ko mgnr doctor Nura Baffa ya yiwa su Baba , amma bazan iya tabbatar da gaskiyar komai ba sai naji daga bakinsu .




Bayan zaman da nayi gefe daya na natsu tare da cewa gani, ko motsi ban iya karayi ba , dama ga zuciyata da tsoron baba to yau ko mamar ma ba walwala a fuskarta .




"Ke meye ma sunanki?"
Gabana ya kara faduwa wai ni baba ke tambayar sunana, kmr ba 'yarsa ba
"Da ke nike"
"Ummal-Rumana "
Na bashi amsa,
"Waye mahaifinki?"
"Cikin rawar murya da take nuna abu biyu, tsoro da faduwar gaba na bashi amsa da "Kai ne"
"Kin amince da ni na haife ki?"
"E' Baba"
"Me yasa har kika samu Wanda kike so baki sanar mana ba, sai dai ki turashi ya aika da iyayenshi?, Wani abun bakin ciki ma ba mutumin kirki ba , mutumin da jama'a ke zaginshi suna tsine masa , mutumin da bai San darajar dan Adam ba , balle yasan ta matar auranshi , mutumin da ba'a san asalinshi ba, mutumin da ba inda za"a bit ayi binkican shi waye , su waye iyayensa"
Ya mayar da numfashi ,
"Da ke nike, me ye hadinki da shi , da har zaki sa ya tura mana neman auranki , tamkar ke ke da iko da kanki"
" Waye Baba,? Wlh ban tura kowa ba"
Na fada cikin rawar murya,Wanda tuni hawaye sun cika gurbin idanuwana.




"Kada ki mayar da mu shashashu kmr ki "
"Ya isa tsaya in tambayeta da kaina"
Maganar Baffa sirbajo ke nan.
"Umma gaya mani gaskita kinji, ke kika tura wannan yaron ko kuwa , shin kina sonshi ko kuwa?"
"Baffa wane yaro?"
"Me zuwa nan likita"
Gabana ta daku , kaina ta sara da karfi
"Wa! Wa!!! Wlh Baffa ban San zai je ba , ba ruwa na bani na turashi ba , wlh Baffa bana sonshi shima hk",
"Kiyi mana shiru mutuniyar banza "
Mgnr Baba,
"Ba kya sonshi ya kwaso yaye yaye ya turo mana su neman auranki , dagani cikin su ba wani dan uwanshi , balle a sa ran iyayenshi, to tsaya in gaya maki , da in aura maki Wannan yaro gara na ajeki a wajen massalaci Wanda naga yana so ya dauka har sadaki na bashi kyauta sbd hk in na kara jin labarin an ganku tare , ke ko sunansa kika ambata sai na yanka ki".....




"Kaga tsaya Wannan ai shirmen banza ka ke yi har kake Ikirarin yankata ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login