Showing 1 words to 3000 words out of 63585 words

Chapter 1 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

FEERYAL

*Littafin kud'i ne ki-ka biya kud'i ki-ka karanta cikin aminci, FEERYAL mallaki na ne ni RASHEEDAT S DIRECTOR*

Ki-ka saka 500 ta cikin wannan a account d'inπŸ‘‰πŸ»3170524141 Rashida Salihu first bank.
sannan ki tura shaidar biya ta Whatsapp number taπŸ‘‰πŸ»08034690723



"Bissmilahi Rahmanurrahim"




Wani irin mummunan sarawa kanta yayi tamkar zai rabe gida biyu.
dasauri tajuya jikinta nabari tana fad'in
"Ammie Ammie karkishiga bayi nan akwai wani abu!."
ganin Ammie bata d'akin tanufi falo da gudu tana cigaba da kwalamata kira
"Ammie! Ammie!!."
Aunty data koma kitchen duba girki tafito dasauri dan jin kiran datake kwalamata da karfi.
take fadin Ammie karkishiga bandakin.
kafin ta rufa baki tawani irin rid'uwa akasa.
tamkar an d'agatane aka bugata da kasa.
tawani kwalla uban qara me rikitarwa.
Aunty tayi kanta dasauri tana fad'in
"Ke Feeryal lafiya mekika gani a bayin meye a cikin bayin?."
takai hannu tana kokarin d'ago ta.

Feeryal tawani irin dago kanta tareda yamutsa gashin kanta ta girgiza kan.
tayi wani irin mikewa tsaye tabubbuga kafafunta a kasa.
saida ilahirin cikin falon yadauki sautin bubbuga kafafun da tayi.
kana tagyara tsayuwanta gijim kamar an aje abu mai matukar nauyi.
bashiri Aunty tayi baya atsorace ganin yanayinta daya canza gaba d'aya.
cikin wani irin murya me rikitarwa take fad'in "Tun da ta b'ata mana shiri to yazamo dole mudauki mataki akanta,
dole mutafi da ita muje mu yasar da ita acan inda babu wani bil'adam d'in da ke rayuwa a gurin,
wannan shine hukun cin da ya da ce da ita."

Tayi wani irin juyawa tarufa aguje tayi waje da gudu,
Aunty tabi bayanta da gudu tana kwallamata kira,
tuni Feeryal tayi bakin gate ganin tana kokarin
fita daga site d'in gaba d'aya.
hankalin Aunty ya yi mugun tashi tana fad'in
"Dan Allah kuyi hakuri karkubari dan Allah tafita a haka,
ku tsaya ku fad'i me kuke bukata,
kada ku wahalar da ita ku d'auki hakkin ta."
tuni ta fice daga side d'in.
Aunty tabita a kid'ime hankali tashe ganin babu wani sutura ajikinta daga ita sai towel dake daure a kirjinta.

A guje ta d'aun hanyar babban get,
Aunty na binta tana kira da kururuwan niman agaji a tare mata ita kada a bari ta fice a gidan gaba d'aya.
Ajmal Zaraddin Shamsuddin Faisal.
da suke hango abin da ke faruwa daga saman benen sashin su, dukan suka sauko suka fice daga sashin nasu,
dai-dai san da Feeryal ta iso zata wuce get d'in sashin nasu.
Zaraddin ya shige gaba da sauri ya yi saurin rukota ya rungumeta gaba d'aya a jikinsa,
yawani irin jan numfashi san da yaji d'umin jikin ta da tattausar fatar jikin ta mai d'umi da laushi da tsamtsi a cikin jikinsa.
ya kifa tafin hannunsa da kyau a bayanta yana dad'a matseta a jikin sa.

Wani irin haniniya tayi tayi jifa da shi can gefe sai da ya had'u da jikin get gau! kake ji,
ya zube kasa warwas yana gantsarewa da rike bayan sa.
ta kuma zurawa a guje.
Aunty ta sa hannu a kai tana fad'in
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un Ajmal Shamduddin Faisal dan Allah kada ku bari ta fita, ku kamo ta ba a hayyacin ta take ba."
suka rufa mata maya da gudu,
dukansu suka rirrije ta.
sunyi-sunyi su iya janyota sun gagara raba kafarta da kasa.
suka daddage da karfin su irin na matasa masu jini a jika, suka kuma janyo ta.
da tayi wani irin ihu mai had'e da gurnani tayi haniniya da su duk ta wasar da su kasa.
ta kuma rufawa a guje.

Ihu Aunty ta fashe da shi hawaye na zuba a idon ta fad'i take
"Ya Allah ka kawo min d'auki ka taimaka min ka taimakawa wancan baiwar taka da bataji ba bata gani ba,
ya Allah ka hanasu cimma burin su a kan ta,
dan Allah security kar ku barta ta fita ku tare ta dan Allah,
innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."


Wani irin karo tayi tayi baya tangal-tangal kamar zata kife kasa sai kuma ta dawo ta tsaya daram.
tana wani huci kamar kububuwa,
tsaki yaja yana kallon wayarsa da ta fad'i kasa,
fitowar sa daga sashin Mommy ke nan yana tafe idanunsa a kan waya baya kallon gaban sa,
ba zato yaji ya yi karo da abu.
bai d'ago ba idanun sa a kasa inda wayarsa take yashe kusa da kafafun ta,
ransa a b'ace ya bi kafar nata da da kallo ganin ba'a d'au wayar an mika masa ba,
kuma ba'ayi magana ba bare a bashi hakuri.
yad'an surawa fararen kafafunta,
tuf-tuf da su masu dauke da zarazaran yatso,
sam kalar kafar batayi kama data kannen sa ba, duk da baya yawan zama da su amma yasan babu mai wannan suffar a cikin su.
har sannan bai d'ago ba yana zaman jiran a d'auko wayar a mika masa,
a fusace ya d'ago kansa.
baiga fuskar da ke tsaye a gabansa ba, sakamakon gashin kanta da ke baze ya rufa mata fuska.
a hankali tayi baya da kafarta d'aya ta d'aga d'ayar zata sa gudu.
da karfi
Aunty ta ce
"Abdurrahi ka rike ta dan Allah kada ka barta ta gudu dan Allah!."

Da sauri ya mika hannu ya fizgota dan tuni ta d'aga kafa ta sa gudu.
ya dawo da ita ta garu da jikin sa.
wani irin garuwa tayi garam tayi baya tana wani irin gurnani.
cikin wani irin murya take fad'in
"He kana da kwari, jiki kamar doki."
ta kuma d'aga kafa zata sa gudu.
a fusace ya kuma fizgota, tayi wani irin tirjewa,
cikin matukar mamaki ya d'ago ya dube ta,
jin yadda ta tike,
kuma wai macece gatanan yar qarama agaban sa,
to ko ba mace bace saboda yanayin sautin muryata da yaji tayi magana da shi amon sauti me rikitarwa har lau fuskarta rufe yake da gashin kanta.

Tsayuwar sa ya gyara ya kai d'aya hannunsa ya ruko nata d'ayan yazamo duk yana rike da hannayen nata, ya janyo ta da karfi, tana tirjewa yana janta yakawota inda su Aunty suke ,
yana zuwa gurin yaturata wa Auntyn Aunty ta ce
"Dan Allah Abdurrahim ka taimaka ka kaimin ita site d'ina
zasu gudu da ita ne."
yadube su Ajmal da suke tsaye cirko cirko kowannansu na dafe da inda yabuga.

ya ce
"Ku kamata ku kaita ciki."
Ajmal ya ce
"Ya Abdurrahim wlhy bazamu iyaba zubar damu tayi dukkanmu."
gajeren tsaki yaja yakuma fizgo ta tana kokarin kuma gudu,
yajanyota ya nufi sited'in Aunty aransa yake fadin
"Wai harda mahaukatane a gidan yanzu."

Aunty dake biye dasu jikinta nab'ari suka wuce har falo ya
ya angiza ta a saman kujera, tafasa wani uban kara tana fadin
"Sai mun tafi da ita tunda ta batamana shiri bazamu rabu da ita ba."
takuma yunkurawa Aunty tafashe da kuka tana fadin
"Dan Allah dan Annabi kuyi wa girman Allah ku kyale yarinyarnan,
Abdurrahim ka taimakeni karkabari su tafi da ita ba ita bace Aljanune karkabari sutafi da ita.

itako junkurawa ta kuma tawani irin shekewa da dariya
tana fad'in
Ba zai iya damuba dole saimun tafi da ita, tun da ta b'a mana shiri ni bakin aljani bana aike ya fad'i a banza, hahahaha."
tadaga kafa tana kokarin guduwa.
yasamata kafa tafad'i kasa rif ta wani irin yunkuri tamike tsaye,
ta kai hannu takunce towel jikinta ta tayi jifa da shi,
tana kokarin cire bra'n jikinta tana wani irin mummunar dariya HAHaHaHa.

Aunty ta sa kuka tana fadin
"Innalillahi wa innailaihirraji'un
kuwasu irin shaid'anune zakusata tayi tsirara haba kukuwa,
baku da imani da tsoron Allah ne."
wani irin runtse ido Abdurrahim yyi cikin takaici da kosawa ya zabga mata wani mummunar marin da saida
takife kasa tana wani irin gurnanani.
Aunty dasauri tadauki towel din tarufemata a jikinta.

Yazauna kan kujerar da take kife a gaban sa tare da d'agota daga kifen da take yazaunar da ita a kasa.
ya saka hannu ya damko gashin kanta da karfi tare da gyara zamansa yasoma karanto ayoyin alkur'ani yana tofa mata,
cikin zazzakar murya tamkar balaraben asali.
ihu ta soma tana fad'in
"Ka daina kona mu kai hatsabibine, ka cire hannunka a jikin mu kana da mugun dafi wane ne kai haka, zamu waiwayo ta kanka zamuyi bincike a kanka kai dafi ne ka kyale mu ka dai na kona mu zamu fitaaaa zamu fitaaa."
bai sakaita da karatun ba har sai da ta sulale kasa tana birgima da shure-shure, da rantse-rantsen yanzun nan zai tafi har a bada."

Ta jera wasu tagwajen atishawa,tana mikewa da kakkalmashe jikin ta,
nan take tayi flat a kasa, tana sauke numfashi.
Aunty rayi kanta da sauri tana dad'a rufe mata jikinta,
da kiran sunan ta.
"Feeryal Feeryal ke ce tashi Feeryal, nagode Abdurrahim."

Baiyi magana ba ya mike tsaye ya fice daga parlour'n.......!





Sai kunyi hakuri fa....



Mommy'n Twins ce



Waziri kutub ya zube kasa bisa gwuiwowinsa,
jiki na rawa idanunsa akan ruwan madubin ganin zahiri daga rayuwar Feeryal.
ya ce
"Ya shugaba na! shin mene ne da lilin da yasa ka hanamu bayyana domin kai mata d'oki cikin gaggawa?
ta fuskanci azabebben wahala daga bakin aljani, kayi mana izini mu cimmasa."
sarki aljani Matip ya gyara zamansa sannan ya ce
"Kariyar da yafi naku ya tinkaro gareta, tabbacin da ke garesa shi ya sa na dakatar daku,
shi d'in sulke ne garkuwar yaki,
kuje ku cimma bakin aljani ku taho da shi a tsare shi."
"Mun karb'i izini ya shugaba na."
nan take waziri Kutup ya umurci dakaru uku da su je su taho da bakin aljani, dake can yana jinyar jikin sa da ke a babbake,
batare da b'ata lokaci ba suka taho da shi aka tsare shi a kurkuku, tare da horo mai tsanani.


Tuni gidan ya d'auki labarin aljanu sun tashi a kan Feeryal,yan kai kawo masu yayata batun sunata fad'in karya da gaskiya harda masu cewa Feeryal tsirara tafita, babu komai a jikin ta.
Hankali tashe Ammah da Miemie suka nufi sashin Aunty.
har lokacin Feeryal na kwance flat a tsakiyar parlour Aunty na ta tofa mata addu'o'i, tana yi tana hawaye.
Ammah ta karaso da sauri ta ce
"Kamata mu kaita d'aki Hajiya Fatima."
Aunty ta mike tana share kwalla suka kinkimeta suka shige da ita d'akin ta.
Miemie ta biyo su tana hawaye cike da tausayin Feeryal.
a kan gado suka kwantar da ita.
Ammah ta ja blanket ta rufe ta, tana fad'in
"Sun sauka fa bacci take yi."
Aunty ta gyad'a kai jiki a sanyaye.
Miemie ta zauna kusa da ita tana sharar kwalla.
duk tausayin Feeryal ya cikata.
Ammah tayi ta karfafa Aunty, sai ana kiran sallar magriba kafin ta tafi,
har lokacin kuwa Feeryal bata farkaba.
Miemie kam tananan suna tare da Aunty a d'akin har wajen karfe 10 na dare kafin Feeryal ta farka.
da taimakon su tayi wanka ta sa kaya har ta d'an tab'a abinci.
sai wajen 11 Miemie ta koma sashin su.

Washegari.

Hajiya ce zaune gefenta Abdurrahim ne zaune yana dan kishingid'e idanunsa a lumshe,
tun da ya shigo gaishe ta Hajiya ta tsare shi da batun wai ta sami labarin shi ya tsare Feeryal bayan da kowa ya kasa riketa.
Hajiya ta bubbugashi tana fad'in
"Kai abokin turawa yanaganka haka kamar mara lafiya,
dama ina kai ina fad'a da aljanu bare yarinyar ma da ita kanta aljanace,
salon kaje taro su sushige maka jiki,
waya sani ma ko sun shige ka, ina da wani ajiyayyen hayaki bari na d'auko kayi."
a hankali yabud'e lumsassun idanunsa ya mike zaune yana jan d'an gajeren tsaki,
Hajiya ta ce
"In banda hali irin na Fatima daga isowarka kasar ko hutawa ba'a bari kayi ba a wani had'aka da kama aljana,
in ba mugunta ta so kulla wa ba, bari naje na d'auko hayakin nan nayi maka, haba dan Allah mugunta kiri-kiri mutane sun iya shi,
Allah kad'ai yasan wasu irin aljanu ne suka shiga jikinka."
Hajiya na kokarin mikewa shi ya rigata.
yatashi yasaka takalmansa yyi ficewarsa.
Hajiya tadaga murya tana fad'in
"Kai abokin turawa kaji iya shege ka tsaya ayi maka hayakin a kora maka su, shine zaka tafi,
bari naje na sami Daddy'n ku,
wlh ba'a isa a salwantar min da rayuwar jikana na fari ba, ina dalili ina mafari."


Daf da zai shiga shashinsa saiga kiran mommy yashigo wayarsa,
yajuya yanufi shashinta yana shiga yagaisheta,
ta amsa a dabarbarce tana fad'in
"Abdurrahim ina ce dai lafiya bbu inda kaji ciwo?
meya kaika da fad'a da aljanu alhalin yarinyarma ita kanta aljanace,
to karnasake jin kashiga sabgar yarinyar nan inma mutuwa zatayi ta mutu ba abinda yadameka,
ta fita zata tafi gun danginta aljanu in da ta fito ina ruwan ka da tsare ta,
imma Hajiya Fatima ce ta ce ka tsaro mata ita,
to ban yadda ba kar na sake ji,
dan in ba kasa sani ba ka sani, yarinyar aljana ce d'auko ta tayi a cikin ruwa babu kalar fitinar da bata haifar ba,
da kage ganin ta yanzu haka fitina ta haifo musu a can Abuja gidan iyayen Hajiya Fatima'n,
shine aka dawo da ita nan mu ta karasa mu,
shine suka fara daga kanka,
tun da sunsan kaine magajin gidan,
suke so su san yadda zasuyi su sabautar da rayuwar ka."

Baki yatabe cike da kosawa da maganganunsu shi an dameshi da maganan da bai shafeshiba,
dan kawai ya taro ta sai abi ayi ta damin shi ana cika masa kunne da wasu maganganu,
to meye damuwar sa shi,
imma aljanar ce sai tayi aljanancin ta.
batare da ya ce da ita komai ba yanemi waje yazauna akan kujera.
ya ce "
mommy ina abinchi?."
ta ce
"Ba nasa a Ameerah ta kai maka."
"Babu wani sai wanda masu aiki sukayi?."
dubansa tayi har yanzu dai d'abi'ar sa nanan na kin cin abincin masu aiki,
wannan gadon da ya yi na Daddy da kakan sa yana b'ata mata rai.
ta ce
"Babu duk masu aiki ne suka girka, to wai meye ne abincin masu aikin yake yi,
manyan ma'aikatan hotel kwararru a fannin girki su ke girki a gidan nan,
meye aibun abincin su, acan waye yake maka girki ba mata kake da ita ba ina masu aikin ne."
bai yi magana ba ya mike ya yi waje.



Tun da sassafe Miemie tashigo shashin Aunty a falo ta tadda Aunty tana aiki,
ta gaisheta tana tambayanta yaya feeryal da jiki
Aunty ta ce
"Dasauki tana daki ma tana bacci haryanzu."
Miemie ta ce
"Ammah ta ce na gaishe ki da jikin ta, bari na duba ta."
"To jice da ita jiki da sauki."
ta ce tom.
tashige d'akin Feeryal tasameta tana bacci acikin bargo.
tazauna a gefenta tana kallon kyakkyawan fuskar ta da yi wasai,
a hankali ta ke sauke numfashi.
cike da tausayin ta Miemie ke kallon ta.
takai awa daya da shigowa d'akin kafin Feeryal tafarka.
tamike da murmushi tana fad'in
"Miemie yaushe kikazo?."
"Tun d'azu nazo nashigo kina bacci."
"Shine baki tashe ni ba."
"Uhm-uhm kiyi baccin dai, Ammah tace a bacci akafi samun sauki."
Feeryal ta kuma murmushi tazamo bakin gado tana fad'in
"Kawai naji bani da lafiya bansan me ke dami na ba,
ina dai jin bana jin dad'in jiki na,
bari nayi wanka Miemie, ko zan ji na d'an ware."
tana mikewa da sauri ta koma ta zauna bakin gado tana fad'in
"Wash!."
da sauri Miemie ta ce
"Ya ya dai Feeryal?."
"Ciwo jikina yake min Miemie, gwuiwa ta ciwo yake min,
Miemie ta ce
"Sannu Allah yasauwaka yi wankan muje ki karya." Miemie nazaune hartayi wankan tafito tashirya
cikin dogon rigan material mara nauyi.
suka fito
falo suka tadda Aunty tagama shirya breakfast.
ta had'asu akan dinnig,
suka haye dinning tare sukayi breakfast har da Aunty.


Feeryal sai yamutsa fuska take tana fad'in wash nan d'inta namata ciwo, can na mata ciwo.
Aunty da Miemie sai sannu sukeyi mata,
Aunty ta ce
"Bari nasa a kawo miki magani ko azo amiki allura ne kawai zakifi jin dad'i."
dasauri taware ido cike da jin tsoro tana fad'in
"Ah ah Ammie karkisa ayimin allura abani maganin kawai."
Aunty ta ce shikenan
"Maganin kawai za'a kawo miki."
Aunty takira family doctor d'insu ya kawo mata magani.

Har azahar Miemie sunatare da Feeryal ashashin Aunty.
kafin takoma sashinsu tana shiga taga Faisal zaune Ammah tana d'uma mishi hanunsa da ruwan zafi.
sai wani raki yakeyi yana fad'in
"Ash wlhy Ammah dazafi anya ba tsagewar kashi ba ce kuwa."
Miemie ta karaso tana zauna kusa da su tana leko fuskarsa tana dariya.
"Kai Ya Faisal wlh kana da raki, sai kace kariya kayi, d'an bigewa ne fa."
hararar ta ya yi ya ce
"Ke wlh ni tunani ma nakw kamar kariyar ce, dubi fa hanuna inda ya kumbura."
Ammah ta ce
"Kai da'alla tafi can kariyar ce har zaka iya kwana da ita."
ya ce
"Allah Ammah hannnun nan fa tayi tsami sosai daurewa kawai nake,
wlh wannan bugun badai mutum ba sai dai aljani,
wlh Ammah in kin ga yadda ta wujijjigamu ni da Ajmal da Shamsuddin kyace jarirai ta d'auka tayi jifa da su,
dama Zaraddin kam na kasa shi aka fara bugawa da kasa."

Miemie ta tuntsure da dariya har tana rike ciki cikin muryar dariya take fad'in
"Lallai kunji hannun mazajen aljanu, haba ai wannan abin kunya ne ace dukanku hud'u kun kasa iya rike aljani d'aya, gaskiya kun bada maza."
"Ke dalla tafi can in da Feeryal d'in ce ba mahaukatan aljanun da suka zo kanta ba,
wanda naushi d'aya nayi wa yarinyar can wlh sai ta suma."
"Ba waninnan kun dai kasa."
Miemie ta fad'a tana kuma shekewa da dariya.

Faisal ya kai mata bugu da d'aya hannunsa yana fad'in
"Ke ni sa'an ki ne, mutum uku sakanin mu kafin ke kar kiga basa nan ki d'auka ke kike bina,
Ammah ki gaya mata wlh zan b'alla ta a nan."
Miemie ta mike da gudu tayi kofa tana cigaba da dariyar ta ce
"Bari naje naga su Ya Ajmal da Shamsuddin da Ya Zaraddin ko wani hali suke ciki ko kafarsu ce aka b'alla musu su, Allah ya taimake ku ma da ya turo muku Ya Abdurrahim,
badun haka ba kam sai asibiti."
"Zan rike ki Miemie na rantse sai na fasa miki baki."
tuni tayi waje tana dariya.

Sashin Mom ta nufa ta tadda Zaraddin kwance ga magunguna a gefen sa,
Shamsuddin kuma na zaune.
ta karaso tana kunshe dariyar ta da fad'in
"Sannun ku Ya Zaraddin Ya Shamsuddin ya jikin naku."
Sahla ta yi caraf ta ce
"Ai wlh shegiyar mayyar aljamar nan sai ta bar gidan nan."
Zaraddin ya d'ago da sauri ya ce
"Ina ruwan ki, babu in da zataje tana nan."
baki ta tura tana kunkuni.
shiko ido ya lumshe babu abin da yake masa yawo cikin ido da kwakwalwa sai suffar Feeryal da tattausar jikin ta,
sai wani shigewa cikin kujera yake yana ji kamar tana cikin kijin sa.
Miemie ta fashe da dariya tana fad'in
"Wai Ya Zaraddin duk bugun da kuka sha ne haka kamar fa ko iya tashi baka yi, gadai Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login